You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce banyi gaban maza amma ina zuwa aunty maryam na samu tana cikin mutane sunanta korafin yadda ka biye min aka ki yin Partyn tana

bada hakuri.

Koda na shigo akan hanci suke kallo na suna bata rai shan kanshi na fara tare da dage kai ina

hura hanci na jujjuya musu mazaunai na da basu zauna ba Dan ni albarka kirji gareni amma mazaunai na basuda girma na bazo a gani daidai kamar na kowa ne.

Gefe naja aunty maryam nace so Nike a Kira mini ma kadan fada ayi mana ganga kura (ganga kura shine kidan da kanurai keyi wadda yawanci suke hawa kan layi ko sahu a taka rawa iri daya bawai a girgije Dan mu a tsarin kanuri babu rawar girgiza. Ada kakannin my kanurai suna ganin kowa Arne Dan lokacin a borno empire kadai akeda musulunci tun kamin ya shiga su

sokoto. Any way ba historynazo Baku ba wannan ma wani fanni ne na daban )

"Tace toh babu matsala komawa mukayi na daura liffaya ta blue wato shudi (ba lafaya ba and also kurkum not kurkur, Dilke not dilka fatan mun gane?) muka fito anata shan kamshi kamar iyayen Mata. Fili aka buda mini dan dama nasa an sanar da abokan ango cewa da na fito susa a bude min fili."

Dangwala nayi amma memakon na shafa masa a hannu sai na muka masa a gemu sannan na ciro bandir din 50 wato dubu 5 na cire hularsa nasa aciki harara ta yayi nayi masa gwalo yayinda abokansa suka saki baki suna kallon mu uku Niko kara dage gira nake Dan karma suyi shawagin cewa suna sona kuma abinda zai baka haushi ko kwalliya bamuyi ba Dan ni ka'idata ban kwalliya bawai Dan inada kyau yasa nake haka ba sai Dan ba kowa ya dace yaga

kwalliyata ba! Nafi karfin wannan.

Bayan mun dawo cikin gida ne na kyalkyale da dariya Dan nasan yadda uncle aliyu keson gemunsa Kamar me. Masu ganga ne suka iso aka sanar wa maza suka shigo sannan akyi rawa ta al'ada karfe biyar ummi tayi mana surprise da masu kidan kwarya Dan haka maza suka fice waje inda ake Kari tare da me ganga yayinda Mata suka rufe kofa bayan an tabbatar babu namiji muka girgije nan na naje na karkade jiki su nana sai makemin mazaunai suke wai haka ne rashin iya rawa. Nide nace kanku. Da daddare ne akace ankai amarya aiko ni da nana da mama mukace toh muma can zamu kwana aka hanamu.

Mama ce ta samu uncle Samir ta roka mana shi Dan taga alamun sa Santa yake amma bai fadi

ba saboda karantarta shekarunta Goma ne.

Aiko babu wata wata ya yarda ya daukemu mu uku a Motansa ya kaimu muku muka saka wayar mu a plane mode toh amma ba zuwan ba abinda muka tarar ne yasa zan iya ce muku

ana gwarama ko kuma akwai kura hajiya!

UHM IKO SAI ALLAH KO MECECE KURAR NAN? NIDE BARI NA SAMU BAKIN GADO NAYI

SHIRU SANNAN NAJI DAGA GAREKU!

AFWAN KUN JINI SHIRU WAYATA TA DAN SAMI MATSALA NE AMMA ALHMDLLH KOMAI

YA DAWO NORMAL DAN HAKA ACI GABA DA GASHI KAWAI.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty

"18th June,2020."

"[6/20, 9:16 PM] My Samsung: * YARINYAR CE TAYI MIN FYADE *"

" *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* "

by miss untichlobanty

Feel free to contact me on :

WATTPAD miss_untichlobanty

INSTAGRAM miss_untichlobanty

"TWITTER, miss_untichlobanty"

TELEGRAM miss_untichlobanty

Your little sis loves you and don't forget to follow me!

"*Indai sunanki maman wani ko ummu wata toh wannan page din naki ne, da Wanda sunasu ya"

fara daga A-Z wannan shafin naku ne kuma* Allah yabar kauna

*CHAPTER 17*

AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....

Not edited

LUBA'S POV

"Muna isa muka fara kalle kalle , shikam uncle aliyu baya gajiya duk sanda zai sake aure sai ya canja pant na gidansa. Kuma cikin matan daya aura wannan yama sunanta? Ladidi tafi sauran kudi Dan kayanta masu kyau."

Nide had yau bani taba magana ba banda gaisuwa Dan bama haduwa ma bansan ko gudu na

take ba.

Shiga dakin amarya mukayi kamar yadda muka saba direct gado muka nufa matan dake dakin suna binmu da kallo. Wata me kananun ido tace ku kuma fa? Zaku wani shigo ku ajiye mutane kazamin a gado? Nana ce tace sai akace naki yafi namu? Nikam gyara zama nayi na ware su liffaya ta Dan zafi nakeji ashar ta dirma Zara yo kaina ladidi ta fito a nayi ta hura hanci meke

faruwa ake min hargagi a gidan miji nifa kar ku sake kimin fada Dan zanci mutum ne.

Wannan me kananun idon ne tace AI da fada muke da sauki dubi fa kallona tayi ta danyi

murmushi tace to AI su luba ne yayan shi ne fa suma sakin fuska sukayi sukace au AI mun

dauka gaiyar sodi ne.

Mama ce tace ni da nana ne yayan sa amma sis luba matar da zai aura ne da sauri ladidi ta

juyo tace ban gane ba. Nace zama ki gane da alamu kece wacce be fadawa ba toh aunty ladidi tun ina yar karama akayi alkawarin sure tsakanin mu wani ashar ta lailayo tace Sam bazai

sabu ba.

Wato abinda yake ta cewa zai fadamin kenan? AI yasin bazan zauna da me kama da ifiritai ba. Jimin yarinya daga kirji sai hanci kamar tsinke saura jiki kuwa kamar an fere tsabar siriranta ace

inyi kishi da ita? Kallonmu tayi tace ku Dan ku fita min a daki.

Sauka su nana sukayi Niko na koma bangaren dama na gadon na kwanta.. kallona suka tsaya yi nace gurin mijina na kwanta ba naki ba danko nasan barni dama yakeson kwanciya. Tace toh

sannu shegiya karuwa zanko ci.....

Wata ce ta shigo tana fadin angwaye sun iso Dan haka muka fice muka buya kar uncle aliyu

yasa a mayar damu gida hakan yasa ladidi tasha ban mayar Mata da magana ba. Ni yasin gashinta nikeji kuma saina fadawa uncle aliyu abinda tayi min.

Munajin shewarsu da alamu kudi aka basu can muka jiyo hayaniya kamin ta lafa da alamu sun tafi ne mukam muna dayan dakin Dan dakuna 3 ne a gidan sai parlour biyu madaidaita. Neman liffayata na soma yi lokacin da zamu kwanta akan sai in rufu dashi amma ban Ganshi ba sai

lokacin na tuna da cewa yana dakin ladidi tsaki naja na kwanta abina.

ALIYU'S POV

Kaina a kasa bance komai ba aka gama duk hirar abokan ango da kawaye danni kunya nakeji kuma idan Baku sani ba ladidi shekarunta 19 ne dukda bannwani girmeta and azo a gani ba amma ni AI nayi aure dayawa ba wannan ne na fari ba. Sanda suka tashi tafiya tukunna na

rakasu

Koda na dawo liffayar ladidi na gani akan gado yana reto Dan murmushi nayi a raina nace ita kuma har an shiga kintsawa ba kunya ne? Dagawa nayi Dan na gyara naji kamshi ya daki hanci na rikewa nayi ina shinshina ina jiran ra fito nima na shiga alwala amma me ? Tana fitowa na

ganta da gyalen ta kanta kuma babu alamun alwala a fuskarta.

Nace a ah hajiyata ashe ba gyalenki bane wannan? To ko wata kawar ki ce tayi mantuwa? Nadau gyalenki ne ma ashe ga naki ... wani harara ta balla min tace dalla malam kamin shiru idan ba renin hankali ba sarai kana ganin gyalen yar iskar yarinyar nan ce zaka wani ce kawata

tayi mantuwa? Kuma sarai AI kaga gyalen dake kaina sanda akayi sayan baki...

Da yake inada Ilimi nasan yan Mata basu iya magana ba kawai nayi murmushi nace Allah sarki

aiko bakin nan ansiyo mini shi ina Dan dariya toh ke banda abinki ai kaina na kasa ban lura

da gyalen ba kuma wace yar iska kike nufi?

Tace duba ka gani dakyau... kallon liffayar nayi dakyau sai yanzu na tuna inda na Ganshi nace

au ashe ma na luba AI sai yanzu na tuna dazu na ganta dashi a wajen Kari na.

Tace zama ka karashe sauran zance wato ma matar da zaka aura ce baka sanar dani ba?

Ajiyar zuciya na sauke nace yanzu dai muje muyi alwala muyi sallah zan fada miki komai. Turo baki tayi kamin de ta juya....

Haka mukayi sallah muna cin abinci ina fada Mata yadda akayi zan auri luba tunda matarka abokiyarka ai babu aibu idan na fada Mata kuma babu wacce ta taba tambaya ta a mata na shiyasa ma ban fada musu ba aiko ta nuna fahimta sosai naji dadin haka muka kwanta ban Mata komai ba banda rungumarta da nayi ina shinshinan kamshinta na tuno na luba murmushi

kawai nayi har bacci ya dauke mu...

LADIDI'S POV

Koda mukayi sallah muna cin abinci ya labarta min yadda yar iskan yarinyar nan ta bi min miji... aiko nace in tasan wata batasan wata ba a gabansa in nuna komai kalau da ya juya ko inci

ubanta taci sa'a ma bazamu dinga haduwa ba da na gasa yar banza.

"Duk rashin mutunci Dana buga masa baya nuna damuwa nasan sarai bai kulani bane Dan yanason ya shiga kasan Dan kamfai na Niko nace nasan maganinsa ga mamaki na babu abinda yayi min. Inaji shi daya yana murmushi har ya fara sauke numfashi, nina da tunane"

tunane na nayi bacci.

LUBA'S POV

Cikin dare na tashi yunwa na kwakulata na nufi kitchen anan na Sami kirjin kaza da guntun

madara dasu dabino harda fruit na dauko nazo na naje ciki na hanka abina yo zan cucina kaina ne ince wani wai ni yar Gaye? Ko wanke hannu banyi ba na koma bacci.

"Da safe wajen karfe 8 na tashi Dan wata yunwar nakeji wanka nayi banida wani kaya kwai sai nasa half vest Dina da da leggings Wanda nasa kasan lace Dina na fice Dan ban tsammaci su fito yanzu ba kitchen na shiga babu abinci na leka store aiko ga su bakilawa,su doughnuts da cake na dibo Abu na tun a kitchen na fara hankama... da uncle Aliyu nayi karo yana dawowa"

daga waje har kunya nadan ji na Dan haka nayi sauri na buya bayan labule.....

Bude labulen yayi ya yaba minnwani Abu a gashi na yana min dariyar mugunta... lakatowa nayi naga kakashi yamutse fuska nayi nace uncle aliyu ka bata min gashina. Dauke doughnut daya yayi daga kwano na yana fadin bashi na biya daga yanzu na daina kyaleki kiyimin tsiya son

ranki tunda kin fara girma.

Biyoshi nayi kamar zaki ina kukan ya bani abinci na kawai ladidi ta fito tana hamma tace nawan wai wake sallama ne. Wasu flask ya nuna Mata yana fadin baki fada min anan su luba suka kwana kallona tayi da sauri kamin tayi murmushi tace au mancewa nati kwi yadau zafi bari nakai abincin kitchen ko? Shiga daki yayi yayinda ta kalleni kamar zata gutsireni tace Dan ubanki wa yace ku kwana mun a gida kuma fa nan ba gidan karuwai bane da zaki samin

tsinannun kayan nan. Kodan banyi mamaki ba abinda mutum yasha a nono.

Iya haushi naji haushi amma sai na godewa Allah da ya bani wayo sai nace Allah sarki yayata kinsan fa anko mukayi dake. Tace kan bala'I bala'I wato yayarki ok? irin nono daya muka sha

ko? Wato a wajen uwata kika gado? Toh zan ci kuma ni banason sata!

Gwaliyo nayi Mata ta nufi kitchen tana fadin zan hadu dake bayan ta dawo ta ganni bakin fridge ina kora lemo zatayi magana uncle aliyu ya fito ya dauketa yana fadin in kika biye wannan acikin hira baya kare Mata zo ni in baki wani labari sannan sukayi ciki. Nikam wani juice din na dauka nasa a hanata bayan Wanda ke hannuna sannan na wuce daki don bawa su nana labari

bayan na karo doughnut daya Wanda uncle aliyu ya dauke min.

TOH FA GASKIYA A GIDAN UNCLE ALIYU ZA'AYI SHAGALI BA KADAN BA! NIDE KU BIYONI

KUJI YADDA ZASU KASANCE.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

miss untichlobanty

"20th June,2020."

"[6/21, 3:48 PM] My Samsung: * YARINYAR CE TAYI MIN FYADE *"

" *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* "

by miss untichlobanty

Feel free to contact me on :

WATTPAD miss_untichlobanty

INSTAGRAM miss_untichlobanty

"TWITTER, miss_untichlobanty"

TELEGRAM miss_untichlobanty

Your little sis loves you and don't forget to follow me!

*CHAPTER 18*

AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....

*Not edited*

AHALI NA DA MASOYA LUBA NA WATTPAD WANNAN PAGE DIN NAKUNE DUK WANDA

YAYI KOKARIN YI MUKU KEACE KU HADASHI DA YAN SANDA

ALIYU'S POV.

Ko da nayi sallar asuba dawowa nayi na samu ladidi na sallah Dan haka na koma na kwanta abina. Inaji ta kwanta a baya na tana me sakale hannunta ta ciki na kamawa nayi na rike a haka

mukayi bacci... wayata da aka Kira ya tashe ni wai aunty maryam ce ta aiko mana abinci....

Lokaci na duba naga 8 da rabi ma ta wuce Dan haka na fito naje na karbo ina shigowa naji kara a kitchen Wanda nasan tabbas ba ladidi bace danko ladidi tana bacci lekawa nayi naga fara ce tafi ladidi haske da siririntaka nasan ba ko wa bace sai luba amma abinda yadan mota ni shine

kayan dake jikinta.

Tanaso ta ballowa ladidi jagwal danni ka ida ta idan na auri mace ranan farko bazan miki komai ba saboda kidan Saba kar a hada miki zafi bibbiyu sannan kar ma ki dauka na aureni ne Dan wannan Dan haka inde bawai naga alamun kema kinaso ba toh ranan farko kinyi escape

saboda nasan yadda ake tsinka musu gaba.

Gashinta dake tsefe bata daure bane idona ya fada akai rabon da na ganta babu lillibi tun ranar

da aka kamamu na ganta da Dan kamfai daga ranan da kaya me mutunci nake ganinta harda hula sanda ta soma girma kuwa harda hijab.

Gashinta ya kara cika da tsayi Dan yanzu yakai tsayin wajen bra strap. Amma fa ghar tanzi baiyi baki ba kuma ni nafison shi a haka ... dungure kaina nayi ina cewa kaji shirme yarinya ma ke damunta da tayi wayo zata ce bataso dama nima ba sonta nake ba Dan ci ne da ita kamar gara amma bata kiba. Cikinnan kamar faranti tunowa nayi da iskancin sa tayi min jiya aiko

dama na daure guntun karkashin hiya na ajiye Dan na Rama daukowa nayi naje na dauko

flask din Dana ajiye bakin kofa na ajiye kan centre table na parlour fitowa tayi bakinta a cike amma a haka tana kokarin tura wani cake.

Tana ganina ta shige bayan labule da alamu taji kunyar yadda na ganta ne bude bayan labulen nayi tana shirin kutsiran doughnut haka kawai naji nima inason ci Dan haka ina Mata wani murmushin mugunta Dan nasan me zanyi na dauki daya kanta yana kasa tayi tsimu tsimu

kamar kulya da ruwa yayi wa duka amma da shike akan abinci ne da sauri ta dago tana turo baki matsa Mata karkashin nayi kuma da alamu ta wanke gashin lakatowa tayi ta gani kuma

gashi na dauka Mata doughnut biyoni tayi zata kwace bayan tayi min raki cewa na bata Mata

gashi.

Ladidi ce ta fito ni daga nan na nuna Mata abincin na shige ciki danko luba ta tsokalo min haja jin shiri ladidi bata dawo ba gashi a matse nake yasa na fito da alamu surutun nan na

tsiya luba ke Mata. Dauketa nayi ina fadin in ta biye wa luba hira bazai kare ba tazo na bata

wani labari aiko muna shiga daki na canja salon labarin.....

AUNTY MARYAM'S POV

Tun jiya da daddare aka nemi su luba aka rasa an Kira wayar su duka uku amma a kashe sarai nasan bazai wuce gidan aliyu suka tafi ba dukda na hanasu Dan haka na jira su dawo bayan siyan bakin amma shiru har 12 wayar aliyu zan Kira na tuna yayi aure yanzu bai dace na kirasa

ba.

Samir na kira nan yake tabbatar min AI shi ya kaisu ma amma a dawowa bai gansu ba ya dauka sun dawo da wuri ne. Nace masa babu matsala toh sannan na kashe wayar bazan

nemosu ba su da kansu zasu dawo su sameni.

Washe gari ma aika akai abincin su Aliyu ina tsammanin ko zasu biyo shi amma shiru nidai na

baza ido naga sanda zasu dawo in basu dawo Dan Allah ba AI sa dawo Dan Kayan su.

LUBA'S POV

bayan na shiga daki na samu mama ta shi nana muka make Dan itace sarki bacci kuma munada style din tashin ta tare zamu daga hannu muka balance sannan mu lafta Mata duka.

Wanka sukayi mukaje kitchen abincin da ladidi ta ajiye muka dibo mukayi shagali abin mu.

Shiru basu fito ba har azhar ta kusa kuma inason daukar liffaya ta knocking nayi naji shiru

Dana gaji kawai na shigewata. Cikin bargo na gansu suna murkususu take suka dago suna harbo min wata kallo nikam tabe baki nayi na bude drower aiko naga liffaya ta. Juyawa nayi zan fice uncle aliyu yace ke luba kanki daya kuwa? Ya zaki tsirmo dakin mutane babu sallama?

Tabe baki nayi nace da farko de nayi knocking har na gaji na biyu kuma wata tsiyar kuke da

kake haki kamar kayi dambe da zaki?

Ranshi ne ya baci sosai amma dinshi kawai ke fadin haka yace abinda kikeso na miki sanda kike karama muke ko zaki jona mu ne? AI da gudu na fita danko an Dan bani katin haske akan abun kuma ba'aso ko maganarta anayi rashin kunya ne inji ummi sannan masu aure keyi. AI ko kirjina kamar zai fado sanda na isa wajen su nana dan aunty maryam tace in mutum yaje yayi

ko maganar abin ne mutuwa zaiyi cab bab shirya mutuwa ba da din ma yarinta ke damuna.

Hanya muka kama har gida su nana na fadin madam kode uncle aliyu ya biyoki da wuka ne. Irin wannan gumi da kike haka? Kasa cewa komai ma nayi me napep ne ya nemi ya kawo mana

shirme wai kudin da muka bashi yayi kadan Dan rainin hankali dari dari ake kaiwa mu uku mun

bashi dari biyar zai mana hauka aiko mu uku muka dunkule hannu yadda super heroes na

cartoon keyi mukace ko yabar kofar gidan mu ko mu canja masa halitta.

Hmm ashe Dan daba ne ba kawai mutuminka ya sauko ba man kace me ya zaro wuka... take cikin su nana ya duri ruwa da gudu suka shige gida nima na tsure amma Nasan idan ban saita

shi ba zai iya dawowa Dan nasan halin yan shaye shaye.

Hade fuska nayi ya kasa gane meke raina Dan baiga alamun tsoro a idona ba sai hargagi yake yayinda cikina har kugi takeyi Dan tsoro ina nazarin barkonon tsohuwa wato tiya gas da almajiri ya koya min jiya bayan mun cashe. Toh na hada gwanin farko amma bansan tayi daidai koko da matsala ba. Kut!! Na hadiya yawu nayi shahada kawai zaro na fasa mai a fuska sannan na

warce woman bayan na rushe hanci na da liffaya ta.

"Yankar sa nayi da wukar nace kai Dan mahaukaciya nima nan da kake gani na dabancin nan Yinsa nake, yasin ko ta anguwar na ka sake bi saina zaro yayan hanjin ka na wulla masa wukarsa na gudu. Tun daga bakin gate na fara tari Dan duk dabarata na shaki gas din kawai de banason ya gane ne ya kawomin wargi aiko abinda ban sani ba shine ya mugun tsorata da"

yaga tiya gas din bata min komai ba gashi akwai yuwuwar idonsa ta Sami matsala.

Ina shigowa su aunty maryam suna fitowa a haukace Dan yadda su nana suka fada Mata Dan daba ne har wuka gareshi ta tsorata. Ganin na shigo a jigace yasa akayi ciki dani nasha su ruwa bayan tari da hawayen da nake ya lafa kawai na fara dariya. Tsayawa kallona sukayi

waiko kan da kwalabe ne?

Nan na basu labarin yadda akayi ina dariya aunty maryam tayi ta fada wai na dena fada da maza sannan uban wa yace na kiyi hada barkonon tsohuwa kuma me zanyi dashi. Tsilli tsilli nayi daidai lokacin wayar aunty maryam tayi ruri dagawa tayi tana fadin ango kasha kamshi take naji wani kullu a cikina jin yadda yake daga murya bai gama ba aunty maryam ta kashe

wayar tare da sambodomin wani kallo

TOH ANAN ZAN BARKU KUYI MANAGE DA WANNAN. KAR KU MANTA KU SAMBADO MIN COMMENT DAN NAJI DADIN BAKU UPDATE DA WURWURI. YAN WATTPAD KAR A MANTA

DA VOTE FA! INA YINKU KAMR BA GOBE.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty

"21st June,2020."

"[6/22, 10:10 PM] My Samsung: * YARINYAR CE TAYI MIN FYADE *"

" *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* "

by miss untichlobanty

Feel free to contact me on :

WATTPAD miss_untichlobanty

INSTAGRAM miss_untichlobanty

"TWITTER, miss_untichlobanty"

TELEGRAM miss_untichlobanty

Your little sis loves you and don't forget to follow me!

*CHAPTER 19*

AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....

*Not edited*

LUBA'S POV

"Wayar caja ta janyo ta fara tsulani aiko take na soma kuka ina burbuwa itako fadi take da izinin wa kukaje gidan aliyu harda kwana? Ke Dan iskanci da rashin sanin ya kamata kika fada musu daki kai tsaye kaman gidan ubanki, su nana ta cafko ta hada dasu tayi mana tas tas sannan sannan ta kora mu daki tana zaune ta ganni da jaka niki niki dama yanzu nafi dadewa a"

gidanta amma tunda nasha assauda nace babu dawowa.

Ganin ina saukowa da jaka niki niki yasa tace ina zuwa? Cikin bacin rai na abinda aliyu da aunty maryam suka min nace gidan ubana inda zan fada ko ina ba tare da anga laifina ba. Baki ta saka Dan ban taba Mata rashin kunya ba saide taurin kai take taji wani iri a zuciyar ta Dan

tunda na fada mata magana kuma na tafi toh naji haushi kila ina da gaskiya da ta

tambayeni....

Kiran sunana ta soma nikam kara sauri nayi Dan banaso na dawo gidan. Direct gidan mu na nufa ko napep din banhau ba jakata na daura aka ummi na gani na da kaya da hawaye ta

taso tana salati luba yar umminta ya akayi? Rungume ta nayi ina kuka wiwi ta zaunar dani a

kujera dama tasan abinda ke sani farin ciki ABINCI amm da ta bani ko kalla banyi ba har juice

ta bani na dauke kai toh tasan maganar ta girmama.

Gaba daya ta rikice tace luba hankalina yana tashi me akayi miki ? Fada Mata komai nayi

amma na tsallake fada ta da ladidi tayi ajiyar zuciya tace kema de luba harda laifinki ya zaki

fada musu daki ? Nace toh ummi sanda nayi knocking sosai fa amma ba'ayi magana ba sai na dauka ko basanan ne race toh nikam bance miki akwai abinda Mata da miji keyi Wanda

ba'ason kowa yaji ko ya gani ba? Nace kin fada kince za'a mutu tace yauwa toh nan gaba indai

suna daki a tare karki sake shiga kinji daga kai nayi badan na hakura ba.

Kwakulo tasono nayi zankai baki ta make hannu na tace kede kin shiga uku katuwa dake na

dauka an dena halin ta canja zani ashe da saura ? Kai aliyu yanada aiki ... turo baki nayi nace ni kar ki kara min maganar sa. Tace au yanzu zancen aliyun ma bakya so?

Tashi nayi na tafi dakina tace aiko yarinya kina ruwa tunda shi zaki aura kaji min shirmen banza. Dauko wayata nayi na fara kiransa har sau uku bai dauka ba aiko na cika na batse Dan dama

so Nike na dan masa rashin kunya na basa haushi.

ALIYU'S POV

Bayan na Kira aunty maryam na sanar da ita abinda luba tayi min da ina Dan tunanin in yarda in aureta amma yanzu ta sa na soma sanja tunani. Yarinya ahaka in ka ganta kamar sallah ashe ko alwala babu? son kowa kin Wanda ya rasa yar budurwa amma da ka kwankwashi hankalinta

sai kaji shiru kamar mushriki yaci shirwa yasha ruwa?

Yar amarya ta ladidi ne ta fito an karya dankwalin nan gwanin ban sha'awa flask din abinci ta dauko mana ta kawo tana budewa mukaga an

Please Login or Register in order to submit comment