You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng  😭😭HAK'K'I NE 😭😭
*NEMESIS*


πŸ–ŠUmmu Asma'u(Sa'adatu)


Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi masu Rahama.


*Bismillahirahamanirrahim*



*Page* 31πŸŽ—32


Zainab Bello jumu'are, cikin uniform din makarantar su masu kalar dark purple an light tayi kyau sosai, bak'aken takalmi da bak'ar school bag, pupple food bag, Zainab tana shiryawa tana kuka, bata tafa tunanin zata samu wannan gatan a rayuwar ta ba, tabbas ikon Allah yawa ke garesa Mumy sai fada take mata, komai kuka, bata son hakan.



Zainab aka fara ajiyewa, Audu driver da yaga Zainab yaji tsoron yi mata magana, tayi kyau fiye da yaran Hajiyar kamar ba yar aiki ba, wani Malami makarantar Hajiya ta ha'da Zainab da shi, receipt din da aka biya kudin ya amsa aka kaita ajin su jss3 suka dauke.



Sai karfe biyu Zainab ta dawo cike da farin ciki duk abun da aka koya mata ta gane duk da makarantar nada bambanci da inda suke zuwa jumu'are, sosai ta maida hankali a kan abun da ake koya mata, tana da guri sosai a kan karatun ta, tana son magana da Magaji tana jin nauyi Mumy tasan kudi ake sakawa, duk yanda ake yi Mumy tayi mata, kasa tambayar Mumy tayi, bayan ta k'are sallar azahar, ta fara gyara dakin Mumy zuwa k'asa, su Lailah sai karfe ukku suke dawowa hudu suje islamiya.




Zuwa hudu saura duk ta k'are share-share da goge-gogen ta, Zainab akwai zafin nama, wannan aikin tana ganin ba komai bane kan wahalar da Baba Delu ke saka su, shine take jin ba da'di in ta tuna Magaji, sauk'in ma Mumy tace Maman Sadiya tasa almajirinta ya rik'a taya shi, in Baba Delun bata gida. Ranar asabar Mumy tace Zainab ta gyara dakin Hashim tare da Zara suka bude dakin, dakin ba wani datti yayi ba,lokaci lokaci Mumy nasa su Zara su gyara.





Toilet din Zainab ta fara wankewa, bayan ta k'are ta gyara dakin tsab ta gyara ko Ina, lokacin da Mumy ta shigo, da'di sosai taji tace Ummina zaki shirya da Hashim ko yaushe su Lailah suka gyara masa dakin zaice baiyi ba, wanan gyaran nasan zai so hakan, kinyi masa yanda yake so, komai a muhalinsa, sannu da aiki Ummina. Zainab murmushi tayi, a ranta tace wannan ne aiki, kasuwa Mumy tace suje da Lailah list Mumy tayi masu kayan da zasu siyo.




Zainab sai mamaki take yi wannan dan gata ne duk siyayyar nan saboda zuwan mutun daya, tana son taga wannan Hashim din, sai kusan magarib suka dawo, Lailah ta dibi kayan ta wuce, Zainab ta dauko sauran kayan, Audu yace Zainab, 'dagowa tayi tana kallon sa, irin kallon da take masa ya kasa cewa komai, Zainab kayan ta dauka ta wuce. Audu taikaici yaji ga dama ya kasa yiwa Zainab din magana, ya rasa dalilin da duk ta kallesa tsoron yi mata magana yake ji.



**** ****


Magaji Bawan Allah tun lokacin da Muktar yaje wajen
Baba Ladidi, duk safiya zaije makarantar har islamiya, aikin gidan dai ne, komai shi keyi, in Baba Delu ta fita Mamman Sadiya ta turo a taya shi, in tana gida duk aikin shi keyi, yana aikin yana kuka. Akwai ranar da Baba Delu ta dawo gida ta ajiye yar jikar ta shiga bayi kamin ta fito Abu ya shigo gidan, yana ganin jikar ba kowa ya bude ya kwashe kudi dubu ukku da dari biyu.



Da sauri ya fita, a kofar gida ya hadu da Magaji, Magaji na ganin Abu na sauri yasan akwai abun da yayi, kamar kar ya shiga gidan, ya yi tunanin duk bai kai mata aikan ta ba, Baba Delu zata dake shi don ta aike shi ya siyo sugar ne. A tsakar gida ya sameta rik'e da yar jaka tana salati, wuyan Magaji ta shak'o tace bani kudina.


Magaji cikin mamaki yace Baba ban dauki kudin ki ba, marin shi tayi sai da ya fadi zaune tace dan ubanka dagani sai kai ke gidan nan, yanzun in shiga bayi in fito ace ba kudi har dubu ukku da dari biyu, wallahi ko ka bani kudina ko in kasheka in kashe banza, shege b'arawo anyi gadon sata uwarku har ta mutu sata take yi, Magaji yace wallahi ban dauka maki kudi ba, Abu naga ya fita yana sauri, Baba Delu marin Magaji ta k'ara yi tace kar ka lak'awa Abu duk zuri'ar mu ba b'arawo, ko ka bani kudi ko jikin ka ya fada maka.


Wayar injin nik'a ta dauko, ta fara dukan Magaji, ta rik'e hannunsa daya, dukan sa takeyi har bayansa na jini da yaji azabar tayi yawa ya cije ta a hannu dole ta sake shi, ya fito waje ta biyo sa, dai-dai kofar shiga gidan su Maman Sadiya ya fadi, yayi tuntufe da dutsi nan ta samesa ta hau dukan sa, mutane dake wucewa suka fara tsaya ana bata hank'uri ko kallon su batayi ba, Maman Sadiya na cikin gida yara suka fado mata da gudu ta fito, janye Magaji tayi, duk jikin sa jini ne, wani tsoho a nan unguwar yake yazo wucewa ya tsaya, yacewa Baba Delu taji tsoron Allah wannan dukan da takewa yaron yayi yawa.


Ta guji ranar da HAK'K'IN yaron zai kamata, zaluncin da takewa yaran yayi yawa, aiko nan Baba Delu ta hau zagin sa, ta matso ta janyo hannu Magaji, Mamman Sadiya, ta tura Magaji cikin gidan su, sai ta fara zagin Maman Sadiya, tace ko Magaji ya fito mata da kudin ko ta illata shi.



Mutanen unguwa duk aka fito kowa na bata hank'uri tak'i ji, Maman Sadiya, ta kira Baban Sadiya, tace ya kira Malan Bello, Malan Bello ana fa'da masa yazo gida, sai da ya biya Delu, ya dauki Magaji suka wuce asibiti, mutanen unguwa sai tsinewa Delu suke yi, da yawa sunce Magaji bazai dauki kudin ba.



**** ****


Mamee bata gane Maryam bata gidan ba sai sha biyu na rana da wasu abokanin ta sukazo, suka ce Amarya ta zo, aka nemi Maryam aka rasa, hankalin Mamee ya tashi sosai, abun da Maryam zatayi masu kenan wayar Maryam din ta kira bata zuwa, Mamee kuka takeyi sosai, tsoron ta kar Maryam ta kashe kanta don tace duk suka aura mata Auwal zata kashe kanta, Abba Lawal ta kira cikin tsanin tashin hankali, zasu wuce masallaci kenan.


Call din Mamee ya shigo cikin kuka take masa bayani, wani irin zufa ya ketowa Abba Lawal, ya zaiyi da dimbin jama'ar da ya gayyata, jama'ar da Alhaji Muhamud ya gayyata me zaice wa duniya 'diyar cikin sa tafi karfin sa, yace gashi nen zuwa, gidan ya wuce ya kira Chiroma da Dan iya misau yayan Amina, Dan iya ma ya firgita, su Anty Amina na aiki labari yazo masu Maryam ta gudu, Anty Amina a ranta tace nasan zaa yi hakan, Maryam rawar kanta baza ta auri Auwal ba.


Mutane aka baza Neman Maryam ko labarin wanda ya ganta duk gidan yan uwa anje bata nan, har lokacin masallaci yayi, dole suka wuce sallah, ranar Abba ya dai yi sallah, bayan an k'are sallah Dan iya da chiroma Abba Lawal suka ke'be suna tunanin mafita karfe ukku zaa daura aure, lokacin biyu ta wuce, chiroma yace a daura da Farida k'aunar Maryam din, Abba Lawal sai lokacin yaji sanyi a ransa.



Ummu Asma'u(Sa'adatu)


08182654508.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE 😭😭
*NEMESIS*


Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.


*Bismillahirahamanirrahim*



*Page* 33πŸŽ—34



*Chiroma* ya dibi *Dan iya* yace shawarace meka gani? naga ha'da yaron da Farida zaifi, mutuncin gidan mu bazai zube ba a idon duniya, Dan iya yayi shiru yana nazari yace gaskiya ne, a nawa shawaran mu kira Faridar muji raayin ta, zaifi kar muzo muyi abun da zaa dawo ana yin danasani, Chiroma yace hake, Abba Lawal suka ce ya kira Farida da Mamee Balkisu, cikin mintuna suka iso Babban gida.





Mamee Balkisu ta gaida su muryar ta bata fita sosai tayi kuka har muryar ta shak'e, tashin hankalin ta, rashin sanin halin da Maryam din take ciki, Farida tsaye tayi k'erere ba ko gaisuwa tacewa Abba Lawal Daddy ance kana nema na, Chiroma ransa ya b'aci sosai, tsawa ya daka mata yace don ubanki ke baki iya gaida mutane ba, Farida zama tayi komai bata ce ba.






AbbaLawal duk'ar da kansa yayi, kunya duk ta cika shi, duk yaran Chiroma ko dan iya zasu gaida shi har k'asa suke duk'awa, duk da fa'dan da Chiroma ya yiwa Farida bata gaida su, Mamee takaici ya isheta daman tana bak'in cikin ace yaranta basa da tarbiyya, Farida ko sai kallon su take yi idon ta tsaye, abun da basu sani ba, Farida cikin kayan aiki take, abotar su da su Fadila yaran Hajiya Rabi Fadilan ta koya ma Farida shan kwaya sai dai kadan suke sha bada yawa shine mutun bazai gane kai tsaye ba.






Dan iya ne yacewa Chiroma yayi hank'uri lokacin daurin auren na gabatowa, sun bar mutane a waje, Chiroma ya kalli Mamee yace zaa mayar da aure kan Farida, tun kan ya kai aya, Farida ta tashi cikin daga murya tace kar ma ku fara wallahi bazan auri mahaukaci ba, ko ina bazan gudu ba, duk wanda ya daura min aure da mahaukaci zanyi k'arasa a 'human right' Abba ya tashi cikin fushi ya dauke Farida da mari, sai huci yake yi yace don uwarki yayun nawa zaki ciwa mutunci, Mamee ranta ya baci don me Abba zai dakar mata yarinya dole ne auren dan Alhaji Muhamud din, tuna tayi su Chiroma na wajen ta fara yiwa Faridar fa'da.






Farida ko a jikinta, tsaye take tana jijikar jiki, Chiroma ransa ya baci sosai bai tafa ganin rashin kunyar yaro a zuri'ar su ba irin wanan, duk yaran zuri'ar su masu biyyya ne, akasarin yaran dan iya shi ke zafa masu mijin aure. Farida kallon su tayi tace duk wanda ya daura min aure zan yi k'ara sa don na san yancina fita tayi abun ta, Mamee ma fita tayi tana kiran Farida.







Dan iya sosai ransa ya baci, Abba zaune yake ya kasa cewa komai, tashin hankalin yayi masa yawa, kallon su Chiroma Abba yayi yace zai kira Alhaji Muhamud ya bashi hank'uri, har ya tashi Dan iya yace ya zauna, yace me zai hana a daura da *Ummi Khadija* ba yaran Balkisu kadai ne yaranka ba.





Abba Lawal shiru yayi yacewa Dan iya kar ita ma tace baza ta yi ba, Dan iya yace ya kwantar da hankalin sa komai zai dai-dai ta, tashi sukayi cike da farinciki suka wuce wajen gidan inda zaa daura auren kofor gidan ya cika da mutane, gefe Abba ya kefe da Alhaji Muhamud ya fada masa abun da ke faruwa, Alhaji Muhamud godiya yayi sosai, yace da Maryam da Ummin duk daya ne, ya gode.






An biya sadaki shaidu sun shaidu an daura auren *Auwal Muhamud kazaure da Ummi Khadija Lawal misau* Auwal na cikin lalura ya mance ko shi waye ne, ko me zai faru in tunanin sa ya dawo?, Mutanen da suka san yaran sai mamaki sukeyi yanda abun ya juye kan Ummi. Ummi haka taji gabanta na faduwa taje cen bedroom din kakar su ta kwanta.






Anty Amina suna zaune da su ya Maryam yaron ya Maryam ya shigo yana cewa da Ummi aka daura, Anty Amina wani irin faduwar gaba taji, cikin mamaki duk suka tashi tsaye su ya Maryam da kannenta har suna ha'da baki wajen cewa Ummi fa, yace da Ummi aka daura, Anty kasa motsi tayi, ana haka Dan iya ya aiko a kira Anty Amina, cen bayan gida suka koma. Ya yi mata bayanin duk abun da ya faru har kiran Farida da rashin mutuncin da tayi masu, ya fada mata shi ya kawo shawaran aurawa Ummi Auwal yasan Ummi baza ta k'i yi masu biyyya ba, yayi hakan ne don yana ganin ya isa ga yaranta







Anty Amina gabanta sai faduwa yake yi, tana jin nauyin yayan nata, ta rasa wane irin tunani zata yi, duka Ummi shekarun ta nawa, yarinyar da ko secondary bata k'are ba, cikin girmamawa tace yaya, in, har yarana masu biyyya ne a gareku, zafin ku shine zafin Ummi, nasan Ummi zata kasance mai biyayya gare ku.





Dan iya hamdala yayi, yacewa Amina in bak'in sun rage zasu yi magana da Ummi, ki kwantar mata da hankali da yardar Allah Ummi bazata yi danasani tunda tayi biyayya ga Mahaifinta. Anty Amina bayan Dan iya ya wuce hawaye ne suka zubo mata, anya wanan danne HAK'K'IN baiyi yawa ba, tsoron ta gaba kar Auwal din ya sami lafiya yak'i Ummi, cikin gidan ta wuce tayiwa su ya Maryam bayanin abun da ya faru, ya Maryam tace tayi ta addu'a da yardar Allah komai bazai faru ba sai alhairi.






Bayan an k'are daurin auren Alhaji Muhamud da jama'ar sa suka wuce, Hajiya Rabi bak'in ciki yayi mata yawa ana ta ganin Mamee ha'da kai tayi da yaranta, Hajiya Rabi ko sallama batayi wa Mameen ba ta wuce, Mameen ma kayan su, suka ha'da za suyi sammakon wucewa da safe.





Abba bayan Alhaji Muhamud ya wuce cikin gida ya shiga da su Chiroma Anty Amina da su ya Maryam suka ce a kira da Ummi duk abun da ake yi Ummi na dakin Umman su Abba tana bacci, Mubina ce ta tashe taje Abba Chiroma na kiranta, faduwar gaba taji, laifin me tayi, tacewa Mubina ina Anty Mubina tace tana falo da su Abba, Ummi saukowa kan gadon tayi, ta dauki Hijab ta saka ta wuce, sosai hankalin ta ya tashi ko me tayi ake kiranta.






Ba wanda yayi mata maganar daurin auren har ta wuce falon,ya Maryam tace kar wanda ya fada mata, da sallama ta shiga har k'asa ta gayar da su Chiroma ta zaune gefe daya ta duk'ar da kanta. Chiroma ne yace Ummi, ta 'dago ta kallesa yace kisan duk 'da na kwarai bazai ki maganar iyayen sa ba, 'daga kai tayi, ya cigaba Mahaifinku ya ha'da auren Maryam da Auwal yaron Alhaji Muhamud Maryam ta gudu ranar daurin aure, yaso ya daura da Farida tace in yayi zata yi k'arasa, muka yanke shawara daura auren dake, domin musan ke.






Mai biyayya ce ga Mahaifanki, Ummi wani irin abu taji tun daga kanta har yatsun k'afar ta, a hankali ta d'ago kanta ta kalli Mahaifiyar ta, Anty 'daga mata kai tayi allamun ta amince, Ummi duk'ar da kanta tayi k'asa cikin ladabi tace Abba zafin ku shine zafina, Abba Lawal ajiyar zuciya yayi Chiroma yace Alhamdulilahi, tabbas ke jinin Chiroma da Dan iya ce, Allah yayi maki albarka, Allah ya sanyawa auren ki albarka, Dan iya ma albarka yake ta sama Ummi, ya Maryam tace ki kwantar da hankalin ki Ummi, ba abun da auren zai rage maki, munyi magana da Abbanku zaki cigaba da karatun ki har university sai kinyi Ummi da sauri ta kalli ya Maryam taji da'di sosai tana son karatun.






Sun tashi cike da farinciki, Abba gida ya wuce yana godewa Allah da Ummi ta rufa masa asiri, mutuncin sa bai zube a idon duniya ba, ya samu Mamee sai kuka takeyi Maryam shiru ba labari, duk rashin kunyar da Farida tayi, asiri ne ba haka yaranta suke ba, Abba sai hankuri yake bata duk abun nan da ya faru bai ji haushin Mameen ba, tausayi ma take bashi, yace gobe su wuce Abuja aje neman Maryam .






Bayan Abba ya fita Mamee ta kira kakar ta tace ko kadan Abba baiga laifin ta ba, Hajjo dariya tayi tace ya zaa yi kiyi laifi ai bazai iya ganin laifinki ba, kamin ki wuce ki k'aro kudi zan k'ara masa aiki, damuwata Maryam bamu san inda take ba, Mamee tace zan k'ara kudi kisa ayi min aiki ta dawo gida, Hajjo tace ai an fara tun da kikace ta guda nasa ayi mana kirayen ta zata dawo, yace a bashi kwana biyu, Hajjo duk shekarun ta, bata tunanin HAK'K'IN da take kwasarwa kanta.





**** ****



Baba Ladidi lokacin da Alhaji Muhamud ya kira ta yana fa'da mata da Ummi aka daura auren kuka tayi tana godewa Allah, tabbas addu'a bata faduwa k'asa banza, wajen Auwal din taje yana zaune yana kallon carton, kanshi ta dafa tace Allah ya baka lafiya, yau kasamu mata yarinyar mai natsuwa da hankali, hawaye na zubuwa a idanun Baba Ladidi, Auwal kallon ta yayi yace mata sai yayi murmushi.




tashi yayi ya share mata hawaye, ya jijiga kai almar tayi shiru, Baba Ladidi nafila tayi ta godewa Allah, taji da'di hakan, sosai hankalin ta ya kwanta da auren Ummin, bayan ta k'are Hajiya Rabi ta kira har ya katse baa 'daga ta sake kira, baa 'daga ba, tace Allah yak'i aniyar ki Rabi, da yardar Allah HAK'K'IN Auwal bazai barki ba, da HAK'K'IN mijin ki.




Maryam bayan ta sami Zero inda zasu hadu da gudu suka bar wajen suka wuce Bauchi,tun a hanya Zero yace ga coke nan har ta fara k'ankara, sanin tana son coke din sosai, desire tablet ya sawa coke din, Maryam hankali kwance ta shanye coke din, basu dade ba suka isa Bauchi, Maryam wani irin feeling take ji, hannun Zero ta rik'e tana lumshe idanu, hotel suka wuce suka kama daki, suna shiga dakin Maryam ta fara cire kayanta, Zero murmushi yayi ya fara tayata, ba tausai ba komai Zero ya afkawa Maryam.






Duk da zafin da takeji a k'asa ta wani muguwar sha'awa take ji, haka zero ya maida Maryam kamar jaka, shi ko yaushe cikin Shan desire tablets yake Sam baya gajiya sun da'de ana abu daya da
kyar duk sukayi releasing
Maryam ta kwanta wahalce, Zero gefe ya kwanta yaji da'di sosai taraya sa da Maryam anjima zai k'ara mata magani, pain relief ya bata da maganin bacci, bacci tayi sosai sai dare ta tashi, abincin ta nema don yunwa take ji, tun da lokacin Zero ya mayar da Maryam kamar matar sa tun tanajin zafi har ta bari, da ta fara cewan ta gaji ya bata tablets su hau aiki, yayi mata alkawalin zai aure ta, ranar da sukayi kwana biyu ta kira Mamee, Mamee kuka tasawa Maryam tace ta dawo gida an daura da Ummi, Maryam tace tana tsoron Abba.







Mamee tace komai bazai yi ba, Maryam na saman jikin Zero duk maganar da sukeyi yana ji, Maryam tace gobe zata koma gida Zero yace a cen ma zamu rik'a haduwa tace ba matsala bazan iya yi bada kai ba sweet heart, Maryam shaidan ya kida mata ganga sosai take jin da'din abun ganin takeyi tun farko tayi kure da tak'i yarda.



**** ****






Magaji sai da yasha allurai suka dawo gida, Malan Bello yaji ciwon abun Delu tayiwa Magaji komai ya kasa ce mata, bayan sun dawo Baban Sadiya yace Malan Bello ya bari suje da Magaji gidan su har goben kar Baba Delun tayi masa wani abun godiya yayiwa Baban sadiya suka wuce, ya shiga gida, Baba Delu ko kallon sa batayi ba, hararasa take yi tana jiran yayi magana komai bai ce mata ya wuce dakin sa.






Da safe da Magaji ya shiga gidan tace ga aikin ta nan kowa ya yi masa tsaye sai yayi, duk da rashin karfin jiki haka ya fara aikin sauk'in yaci abincin gun Maman Sadiya ranar aiki sosai yayi duk jikin sa ciwo yake yi, yana aikin yana kuka, sai yammah Delu ta fita Maman Sadiya ta turo almajirinta ya isuwa aikin, Magajin kwantawa yayi sai baccin wahala.







Ranar assabar Mumy da su Lailah su je airport tarbon Hashim basu jima jirgi ya sauka,mutane suka fara fitowa cen na hango wani kyakyawan matashi yana saukowa Mumy sai washe baki take yi, su Zara da gudu suka rungume Hashim, Hashim ya isa wajen Mumy ya rungumeta, shekaru biyu rabon sa da gida yayi fari ya k'ara jiki, wajen mota suka wuce cike da farin ciki, Zainab gida suka barta tace zata k'ara gyara gidan.








Bayan ta sa turare ko ina gidan, wanka ta shiga, tayi k'waliyya ta shirya cikin doguwar riga da mayafin ta cikin kayan da Mumy ta bata, tayi kyau sosai, jin tsayawar mota ta sauko k'asa, kicin taje ta dauko sauran kayan abincin, tana jerawa suka shigo, Mumy tace Ummina sannu da aiki, Zainab tana 'dagowa suka ha'da idanu da Hashim.



Ummu Asma'u(Sa'adatu)

08182654508
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*

Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.


*Bismillahirahamanirrahim*


*Page* 35πŸŽ—36




Zainab faduwar gaba taji da suka ha'da idanuwa da Hashim, Hajiya Mairo tace Ummina ga Hashim, Zainab cikin ladabi ta rusuna tace sannu da zuwa anzo lafiya, Hashim ya amsa lafiya lau, ya wuce dakin sa yayi wanka, yana ta mamaki ina Mumy ta samo wanan, baya son kwashe_kwashe, gyaran dakin yayi masa, murmushi yayi yace yaran Mumy sun fara girma, duk zuwan da zaiyi gida basa gyara masa daki da kyau kamar haka.




Bayan yayi wanka ya fito cikin kyakyawaar jallabiya mai guntun hannu, yayi kyau kamar balarabe,Hashim fari ne sosai duk yaran Hajiya Mairo yafi su haske Mahaifin su ne fari, Hashim tun tashin sa yake sha'awar karatun Islamic, tun yanada shekaru goma ya sauke alqur'ani, bayan ya k'are secondary, Mahaifin su ya turasa Madina yayi karatun sa kan Qur'an an Hadith's, Hashim yanada illimi addinin sosai bayan ya k'are ya samu aiki a Madina.




Lokaci lokaci yake zuwa hutu gida, falo ya fito suka fara cin abinci, Zainab kicin ta wuce wajen Larai suna fira, Mumy tace ta tsaya taci abinci, tace aa zata ci wajen Larai, Zainab ta tsargu da kallon da taga Hashim nayi mata, kamar baiji da'din ganin ta gidan ba.




Mumy ma duk bata ji da'din yanda taga Hashim din na kallon Zainab ba, tayi mamaki don Hashim bai da hakan komi yasa shine bata sani ba, labari sukeyi suna ta dariya, Hashim yace Mumy yaranki fa sun girma, naga ko gyaran dakin nawa an gyara min da kyau ba kamar wancen zuwan nawa ba, Zara tace yaya Ummin Mumy ce ta gyara ma, Hashim ya matsae fuska yace Mumy bana son ' 'stranger's' na shiga min daki, Mumy murmushi tayi tace Ummina ba bak'uwa ce ba, ita ce yarinyar da nake fa'da maka a waya, Hashim yace Mumy yarinyar nan baki san gidan su, baki san uwayen ta ba, baa san asalin ta ba, duniya nan ba gaskiya kega mutane ba, Mumy ha'de fuska tayi.




Cikin jin haushin abun da Hashim yace tace, Ummina marainiya ce, nayi niyar taimaka mata, zan taimaketa saboda Allah, komai bazai faru ba insha Allah, Hashim shiru yayi, bai san dalili ba, haka nan yaji haushin yarinyar yake ji, bayan sun k'are cin abincin ya fitar ma su Zara da tsaraba su, jallabiyar da ya siyo ma Zainab boyewa yayi, don Mumy tace ya siyo mata, Mumy cikin tsarabar su Zara ta bata jallabiya Hashim duk baiji da'di ba, Zainab sai da suka k'are tazo zata gyara wajen, Hashim tun da ta shigo ya dauke kan sa.




Zainab gyara wajen tayi tsab Mumy sai sannu take mata, Hashim duk haushi ya cika shi, sai kace wadda tayi wani aikin ana mata sannu, an dauka yarinya ko asalin ta baa sani ba, Zainab bayan ta k'are dakinta tawuce, lokaci daya taji ta tsanin Hashim tana Lura da shi yana harara ta, ko ka'dan baiyi halin Mahaifiyarsa da k'anen sa ba, ana cewa mai kirki ne,bata ga kirkin sa ba.




Kwanciyar tayi dakin ta, duk hayaniyar da sukeyi bata fito ba, damuwarta Magaji tana son Magana da shi, gobe zata yiwa Mumy magana, ta kira Magaji, sai karfe goma suka kwanta, lokacin Zainab ta dade dayin bacci.


**** ****


Mamee ranar assabar sammako sukayi zuwa Abuja, Mamee cike da murnar Maryam zata dawo gida, ba ma tunanin wane irin hali Maryam din ta jefa kanta ciki, damuwar ta Hajiya Rabi bata san yanda zata dauki abun ba, kudi sosai ta barwa Hajjo kakar ta, zaa yi mata aiki sosai kan Abba.




Har danginsa tace a ha'da ba tunanin komai, ba tunanin HAK'K'IN da suke kwasarwa kan su, sai yammah suka isa Abuja, tun a hanya take kiran Hajiya Rabi ta ki 'dagawa, Mamee ta shiga damuwa sosai, a daren taje gidan Hajiya Rabi, Mamee rantsuwa ta yita ma Hajiya Rabi cewan bata san Maryam zatayi hakan ba, da kyar Hajiya Rabin

Please Login or Register in order to submit comment