You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dubu daya ta bata Uwar Audu ta amsa ta wuce, sai da ta fita gidan tace wanan farawa ce Delu, HAK'K'IN maraya wasa ne, Uwar Audu tace duk abuna bazan ci HAK'K'IN wani ba, HAK'K'IN wani babban Abu.

**** ****




Hashim sosai yake jin tausayin Zainab cikin kwana biyu komai take yi yana saka mata idanu, wani zubin in sun ha'da idanu sai zainab ta kauda kanta, ita haushin sa take ji, duk lokacin da yake son a gyara masa daki ita yake sawa.




Da yammah zasu fita shan ice cream da su Zara, yacewa Zara tace Zainab tazo su tafi Zainab tace su tafi, zatayi aiki, Mumy tace ta shirya taje, in ta dawo sai tayi aikin, Zainab tana jin nauyin Mumy, shiryawa tayi cikin jallabiya da Mumy ta bata tsarabar Hashim din, tayi kyau sosai, red an black, Zainab tayi fresh tayi jiki gwanin sha'awa, ta k'ara haske, ainihin chocolate collar dinta ya fito, a wajen motar Zara da Lailah sai rigima suke wanan tace ita zata shiga gaban mota, wanan tace ita zata shiga, Hashim yace Zainab ta shiga, su shiga baya.





Zainab a dare ta shiga motar Hashim sai kallon ta yake yi, mamaki yake yi, bata son masa magana, in kaji doguwar firata da Larai ko su Zara, kallon ta yayi yace Mumy tace zata je diba Magaji kina zuwa? Zainab da tayi dariya tace zanje yaya yaushe zamu je, Hashim yayi murmushi yace yaushe kike so tace ko gobe.




Yace zan fa'dawa Mumy in tace, sai muje goben Zainab sai murna take yi, Hashim a ransa yace duk kaga dariyar ta ance Magaji, ya matsu yaga Magajin nan, siyaya sosai yayi masu har Zainab godiya sosai tayi masa.

**** ****





Khalifa Abun nasa yayi nisa shaye -shaye har giya sha yake yi, neman maza yan uwan sa yama fi Marwan don Marwan yana hadawa da Mata, yanda sukeso haka sukeyi, Mamee sai murna takeyi don duk sukayi waya da Khalifa zai ce karatu yayi zafi.




Maryam gidan Zero tayi kwana biyu tacewa Mamee zasuje excotion a makaranta, lokacin Abba yayi tafiya, tsawon kwana biyu Maryam Sam sun mance da maganar maganin daukar ciki sai shagali sukeyi, ranar da suka tuno Zero yace tasha biyu komai bazai faru ba, tasha sai ranar kwana ukku ta koma gida.




Farida da Fadila wata k'awar su ta fara koya masu amfani da painter wanan allura da yan kwayya keyi, ranar bacci sukayi sosai a gidan Hajiya Rabi, duk abun dake faruwa Hajiya Rabi bata sani don tace baa matsawa yaro suna dakin su, har dare basu tashi ba, sai cen goma ta wuce suka falka, Farida ta kira Mamee tace gidan Hajiya Rabi zata kwana.




Mamee komai bata ji ba, tace ai duk gida ne, Farida kwana ta biyu gidan su Fadila shaye -shaye sukeyi, daya ke Abba baya gari Mamee ba ruwan ta tsarin ta tsarin Hajiya Rabi baa takurawa yara.




Cikin kwana biyu sosai Auwal ya saba da Ummi komai tare sukeyi abinci sallah ma duk abun tayi zaiyi, Baba Ladidi wani lokacin in ta kalle su har kuka takeyi.




Alhaji Muhamud yasa a nemowa Ummi admission a wani day school private ne mai tsada,Islamiya a nan kusa ga gidan aka nema mata, har lesson teacher zaa nemo, dayake ana hutu yace kamin hutu ya kare.





Ummi ta kira Anty tana fa'di mata, Anty tayi murna sosai, hankalin Anty ya k'ara kwantawa, damuwar ta daya kar Auwal din ya samu lafiya yak'i Ummin.


Ummu Asma'u(Sa'adatu)

08182654508.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'IN NE😭😭
*NEMESIS*


Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.


*Bismillahirahamanirrahim*


*Wanan shafin naku ne Hawanccy, Mummy, Ummu Hafsat, comments dinku na burgeni na gode*

*Page* 43πŸŽ—44


Bayan sati daya Mubina ta koma misau, Fatima 'yar ya Maryam ta koma gida, hutu ya k'are Ummi ta fara zuwa makaranta, a ss3 aka dauke ta, cen misau ss2 ta k'are, mota Alhaji Muhamud ya siya don kai Ummi makaranta, yace ranar da ba makaranta sai ta fara fita koyo, Ummi tayi murna sosai, Baba Ladidi sai dariya take mata, girkin abincin Ummi keyi, yar aikin Baba Ladidi tayi wanke-wanke da share-share




Ranar da Ummi ta fara zuwa makaranta yak'i akayi da Auwal yace zaije, da kyar Baba Ladidi ta lalafa ya zauna a gida, duk ya koma wani iri ba Ummi, Baba Ladidi har tana mamakin shak'uwar su, Ummi ko yaushe cikin waya take da Anty Amina Ummi tayi fresh abunta komai takeso zata samu, sosai take girmama Baba Ladidi da Alhaji Muhamud.



Hajiya Rabi da Mamee sunzo kano, Mamee ke cewa Ummi an kashe maki rayuwa an ha'da ki da Mahaukaci, Ummi shiru tayi tana kallon su, suka Karachi surutun komai bata ce ba, suka wuce, da suka fito Mamee ke cewa Hajiya Rabi, in Auwal din ya samu lafiya yaso Ummin fa?. Komai na Alhaji Muhamud zai dawo hannun sa, Hajiya Rabi tayi ashar tace ai zai tabbata haka ne muddin ina raye lafiya sai dai a wasu.



Mamee tayi dariya tace Ummin Amina ta tabbata matar Mahaukaci kenen, bak'in cikin Amina bazai tafa k'arewa ba, Mamee tace kisan jiya ta kira Abba Lawal yayi ta rejecting karshe ya kashe wayar, ina kallon sa, Hajiya Rabi tayi dariya tace Amina ita da babu ai duk daya shegiya da fari kamar aljanna, dariya suka kwashe da shi, suka wuce suna ta dariya abin su.




Ranar Ummi ta dawo makaranta, Auwal ya 'dauko sirinji a cikin magungun sa, yace Ummi tazo yayi mata allura, ya iya allura, Baba Ladidi da Ummi cike da mamaki suke kallon sa, ya ajiye sirinji ya hau yin game. Baba Ladidi Alhaji Muhamud ta kira ya kira Dr ya fa'di masa Dr yace alama ce mai kyau, in ya fara tuno rayuwar shi suci gaba da addu'a komai zai dai-dai.




Ranar har sadaka sukayi, Ummi ta kira Anty Amina ta fa'da mata, Anty Amina tayi murna sosai, tace Ummi ta rik'a karanta masa, ayoyin Qur'ani a ruwa tana bashi ko ruwan zam-zam.

**** ****




Maryam sun rubuta exams din su na karshe, ta nemi Zero bata ganshi ba, ta kira wayarsa rufe, gidansa ta wuce, maigadin gidan yace mata bayanan, ganin motar a cikin gidan ta wuce bata tsaya sauraren maigadin ba, falon ba kowa ta wuce cikin bedroom din sa, Zero ta gani kwance da wata, Maryam cikin tashin hankali ta kira sunan shi, Zero ko a jikin sa yace lafiya zaki shigo min daki ba sallama?



Maryam cikin takaici tace an shigo din, in zaka ci amanata, Zero yayi murmushi yace cin amana ke matata ce? an daura min aure dake? kin isa kice bazan kula wata ba, fice min daga gida idiot, Maryam cikin mamaki take kallon Zero, kin fita tayi tace yazo ya fitar da ita, Zero yazo ya fara ingiza Maryam waje, Maryam ta turesa ta wuce ta shak'o wuyan yarinyar dake tare da Zero.



Zero cikin zafin nama ya dibe hannun Maryam, ya wanke ta da mari, ya fara jibgarta yana tura waje har get ya kai ya rufe gidan, yacewa Maigadin duk ya bari Maryam ta k'ara shigo masa gida bakin aikin sa. Maryam ta dade a mota tana kuka, gida ta wuce ta rufe daki kuka sosai tayi, nan zazafi ya rufeta ta fara amai, har dare bata bude dakin ba.



Bayan Mamee ta dawo, bata ganta ba taje tana buga dakin, Maryam ta bude kofar duk idanta sun kumbura Mamee cikin tashin hankali tace lafiya? Maryam ta kwashe duk abun Zero yayi mata ta fa'dawa Mamee, Mamee tace ki k'yleshi mana, mutun nawa ke sonki, ko jiya wani senator yayiwa Hajiya Rabi maganar ki.




Tun farko kika lek'e sai wanan yaron, Mamee ba tunanin me yakai Maryam gidan saurayi, damuwar ta bacin ran Maryam din, Maryam kuka ta fashe da shi Mamee sai lalamin ta takeyi, amai ne ya tasowa Maryam, Mamee ta fara fada kin sawa kan ki damuwa har da zazafi kan Zeron banza, Maryam toilet ta wuce tana zuba amai, Mamee duk hankalin ya tashi, Family Dr ta kira ya zo ya diba mata yarinya ba lafiya.



Bayan likitan yazo yayi ya dibi jini ayi mata blood test tak'i tace ya bata drugs, bata so allura, drugs din ya bata ya wuce, tasha maganin ta kwanta, cen tsaka dare ciwon mara ya dame ta, tana tunanin ko period zatayi, tunanin ta fara yi yakai wata biyu batayi period ba me kenen?

**** ****



Bayan Uwar Audu ta wuce Baba Delu ta kira Gaje tace Uwar Audu tayi alkwali, tazo ta kawo kudin wata, da yake Gaje ta bar gari ta koma Azare wajen yaronta, Abu ne ya fito sai rangwa'da yake yi wai shi mace, Baba Delu kallo daya tayi masa ta kauda kanta, yaro dan shekaru goma shabiyar da Daudu, Malan Bello yayi sallama ya shigo gidan, Ido ya bi Abu da shi yana kallo ikon Allah.



Cikin takaici yace Daudu ka koma, wallahi in bakaje ka cire kayanan ba ranka zai baci, Abu wani fari yayi da Ido, yace infa banason sa Ido, Malan Bello yace fitar min da gida, Baba Delu cikin takaici da jin haushin Malan Bello tace in ya fita ina zaije, mutun da gidan Ubansa.



Malan Bello cikin daki ya wuce, ransa bace Abu bai tsoron sa yanda yaga dama haka yake fa'da masa magana, Abu yacewa Baba Delu a bashi nasa kason kudin aikin Zainab don ya gani, jiki na rawa ta dauko dubu biyu ta bashi tace ya bar Daudu komai yakeso zatayi masa, ko kallon ta baiyi ya fara tafiya yana rangwa'da.



Baba Delu zama tayi k'asa tana zuba da hawaye, wanan abin takaici har ina, duk inda ta fita sai an nunata ga Uwar dan daudu, bazata k'yale Magaji haka ba, ko shi sai ta illata masa rayuwa gobe zata koma gurin Boka, in an gama mata aikin matar dake dumunta, a sake masa wanin wacen baiyi ba.



Har tunanin dare takeyi, data kwanta zata fara mafalkin matar, mutane a hanya sai kallon Abu sukeyi, tafiya yake yi yana jijga jiki shi mace, duk wanda yasan tarihin Baba Delu zaice HAK'K'I ne ke bibiyar Abu daga sata sai daudu.



Mumy sosai tayi farinciki da siyayar da Hashim yayiwa Uminta Zainab sai albarka take saka mashi, Hashim yayiwa Mumy maganar zuwa jama'are gurin Magaji, Mumy tace tsoron takeyi suje da Zainab Baba Delu ta ganta.




Hashim yayi shiru yace gaskiya ki Mumy, tunanin ta Zainab na wajen siyar da abinci, Hashim yace zai tafi shi 'daya Mumy tace yaje, ya nemi Muktar suje tare, Hashim yace zaije, ya rasa dalilin son farantawa Zainab rai, sosai yake son ganin ta cikin farinciki, murmushi yayi, dazun shigarta ya birgesa, Mumy na magana Hashim na murmushi, baima san tana yi ba.


Ummu Asma'u (Sa'adatu)

08182654508.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*


Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.

*Bismillahirahamanirrahim*


*Page* 45πŸŽ—46


Hashim ya rasa yanda zai fa'di ma Zainab, shi 'daya zai tafi Jama'are sosai yasan tasa ranta a tafiyar, wajen Mumy ya koma, yace Mumy ko muje da Zainab ta saka nik'af, ai kinga ba wanda zai ganeta in ba yaga fuskar ta, Mumy ki barta taje pls, Mumy tace ba komai ta shirya kuje da su Zara, Gwaggon ku, Fatima tace zata zo, da ko in zan biku muje tare.



Hashim wucewa yayi baice komai ba, Mumy tayi murmushi, tace a in bansan yanda zaa yi wanan abun ba, Hajiya Fatima ta kasa ganewa Hashim bayason auren 'yarta duk lokacin da akace zasu in yazo, zai bar gidan, Mumy tace Allah ka zafa masa alhairi. Zainab Hashim yace ta shirya da su Zara su wuce, Zainab farinciki baa magana, tana shiryawa tana kuka duk murnar ganin Magaji ce.



Nik'af suka samowa Zainab, in sunje tasaka, Zainab tasha gayun ta, tayi kyau sosai, baza ganta lokaci daya kace itace Zainab din da Baba Delu ke ganawa azaba, Hashim sai da ya shiga kasuwa yace Zainab ta zafi kaya dai-dai Magaji, Zainab taji da'di sosai, sai godiya take yiwa Hashim.



Suna fita Hajiya Fatima ta shigo ita da yan Matan ta, Hajiya Fatima 'yar uwar Mahaifin su Hashim ce, tobasai ne, da Mahaifin Hajiya Fatima da kakar su Hashim, Mahaifiyar Mahaifin su, uwar su daya uban su daya, tun Mahaifin su Hashim din nada rai, take masa maganar su ha'da yara aure sai yace in suna son juna.



Hajiya Fatima mijinta mai kudi ne sosai duk yaran ta matane, su ukku ne Zaituni ce babba sai Walida sai Rufaida, tun Zaituni na secondary takeson Hashim, tayi nuna masa yak'i kullata, lokacin da Hajiya Fatima ta fahimci 'yarta nason Hashim taje da kanta tayiwa Mumy magana, Mumy tayi biyar Hashim yace Zaituni bata tsarin matan da yake so.



Hajiya Fatima ta sagarta yaran ta sosai, komai suke so shi ake masu, Mahaifin su nada kudi ba abun da suka nema suka rasa, Zaituni har ta shiga jami'a ko ruwan zafi bata iya dorawa a wuta ba, komai yi masu ake yi, Mumy tasha fa'dawa Hajiya Fatima wanan ba gata bane, mata ne gidan wani zasuje, sai tace aiko aure sukayi zaa ha'dasu da yan aiki, ta gaji tasa mata idanu



Bayan sun gaisa Hajiya Fatima tace, Mairo yarona ya dawo baki fa'da mun ba, Mumy tace na kira wayar ki baya zuwa na zaci kinje dubai ne, har ina cewa baki fa'da mun ba, muje tare, Hajiya Fatima tace munyi tafiya da Abban su Zaituni ne, Mumy tace ina tsaraba uwar gidan Abba su Zaituni, Hajiya Fatima tace sai kinzo, nazo maganar yaran, dazun munyi magana da Hajiya Dada (kakar su Hashim, tanada ranta).



Mumy shiru tayi, bata ji da'din sako Hajiya a wanan maganar ba, bata son a matsawa Hashim, ko mace akayiwa auren dole akwai matsala, balle namiji, Hajiya Fatima tace, zata zo anjima tayi magana da Hashim din, ko yaje cen gidanta, Mumy tace to yaje Jama'are in ya dawo, su Zaituni na kan table suna cin abinci, tun da suka gaisa da Mumy tace ga abinci suka fara ci, sai santi suke yi girki yayi da'di, komai gidan su yan aiki keyi.



Bayan sun wuce Mumy abun duk ya dameta, tasan halin Hajiya Dada tana iya sa masu kuka kan auren ko, tasawa kanta tunani gata da hawan jini, Mumy duk ta matsu Hashim din ya dawo zata zauna da shi ya amince da auren Zaituni din, ko ta samu lafiya, tasan duk baa yi auren ba, dangin Mahaifin sa zasu tsane ta, har Hajiya Dada, tana ganin girman ta sosai tamkar Mahaifiya haka ta dauke ta.



Lokacin da Hashim suka isa Jama'are, Muktar ya kira, a hanya suka ha'du, suka wuce gidan Mamman Sadiya, Zainab sai kallon k'ofar gidan su take yi, tana addu'ar Magaji ya fito ko Mahaifin su, Muktar ko sai kallon Zainab yake yi, yana tunanin ita ce Hajiya Mairo ke cewa Ummina sister Magaji don yasan su Zara.



Suna parking k'ofar su Maman Sadiya, Zainab tasa nik'af suka fito, Abu ne ya fito cikin gidan su, yasha k'waliyya, har da su jan baki, Zainab kallon Abu takeyi cike da mamaki, me ya ha'dasa da kayan mata kar dai Dan daudu ya koma, tsaye tayi tana kallon sa, har ya wuce, Laila ce ta jayo hannun ta, Muktar ya kira Baba Sadiya yanada num sa.



Baban Sadiya yace su shigo, har cikin gidan suka shiga, cikin sa'a suka sami Magaji a tsakiyar gidan yana cin abinci da babban yaron Maman Sadiya tsaran Magajin ne, Zainab da sauri ta debi nik'af din tace 'Magajin Inna' Magaji cikin mamaki yace Adda Zainab.



Da sauri ya tashi yaje ya rungumeta, hawaye na zuba a idanun su, su Hashim yan kallo suka zama, Maman Sadiya tace Zainab sannun ku da zuwa, yanzu kuke tafe, zama suka aka gaisa, Magaji na gefen Zainab ya rik'e mata hannu, Hashim yayi murmushi yace Magaji zo mu gaisa, Magaji yaje kusa ga Hashim ya zauna, fira sosai sukeyi, Hashim yacewa Baban Sadiya yana son ganin Mahaifin su Magaji.



Baban Sadiya ya kira Malan Bello baa dauki lokaci yazo, har cikin gidan ya shigo, bayan sun gaisa Hashim yayi masa bayanin komai, Malan Bello yayi godiya sosai yace zaizo har Bauchi yaga Mumy, su taimaka su bar Zainab wajen su, zaifi masa kwanciyar hankali, Hashim yace babu matsala wanan, in ya samu lokaci yazo yaga inda Zainab din take, adirishin Hashim ya bashi.


Yace kar ya fa'dawa Baba Delu zuwan su, Malan Bello yace bazataji komai ba, yanzun ma tun safe ta fita, baisan inda taje ba, Muktar yayi masu sallama yace zai koma gun aikin sa, godiya sosai Hashim yayi masa, Muktar yace duk abun da kenan kan makaranta Magaji zaiji, don Hashim yace ya nemo masa makaranta mai sauki kudi a cenzawa Magaji, bayan Muktar ya wuce kayan da Hashim ya siyo Magaji ya bashi Magaji yaji da'di sosai, Hashim yacewa Malan Bello sunyi magana da Muktar zaa cenzawa Magaji makaranta.


Yasa Muktar din ya nemo masa makarantar kudi mai sauk'i a cenza masa, Zainab ido ta zubowa Hashim, Hashim kallon ta yayi, murmushi yayi Zainab da Malan Bello sai godiya sukeyi, Malan Bello yace, Babar ta su dai keda matsala, Hashim yace Muktar zaiyi komai, Hashim sai mamaki yakeyi, mutum har mutum ace bayada ikon a gidan sa, Malan Bello bayada talaucin da zaa kai masa yarinya aikatau, wannan Baba Delu yana jimata rana da HAK'K'IN mijinta da marayun nan zai kamata.



Sai bayan azahar suka fito zasu wuce godiya sosai Hashim yayiwa Baban Sadiya, ya basu kudi, ya basu kudin Magaji Malan Bello ma ya bashi, Magaji kuka sosai yayi sai da Hashim ya lalafa shi yace yayi hankuri zasu zauna da Addar sa, yayi masa alk'awalin hakan, Magaji yaji da'di sosai, suka wuce, bayan sun wuce almajiran Maman Sadiya suka taya Magaji ya k'are aikin sa, sai yammah Baba Delu ta dawo ta karfo aikin da bokanta yayi mata, na matar dake damunta, dana Magaji duk ta amso Abu bashi aikin ya bar Daudu sai bayan kwana biyu zaa ha'da mata.

**** ****


Maryam da safe ta shirya, taje wani private hospital, pregnancy test tace ayi mata, result din ya fito positive, Maryam kuka ta fashe da shi ta shiga ukku Abba Lawal kasheta zaiyi, office din Baban likitan taje, d tace tana son tayi abortion, private ce ba ruwan su Indai zaka bada kudi, yace akwai tsada fa tace ba matsala Indai cikin zai fita, kudin ya fa'da mata tayi masa transfer, Ultra sound, ya fara yi mata.



Ya fa'da mata cikin bazai wahalar fita k'arami ne, wasu allurai yayi mata ya bata maganin yace bayan kwana biyu ta dawo Maryam tayi masa godiya ta wuce gida, bayan ta isa gida tafara bleeding, daki ta shige, ta kira Dr yace zai bari cikin ne ke fita, Mumy tun safe ta fita ita da Hajiya Rabi, Abba yaje wajen aiki duk hidimar da akeyi basu da labari.


Fadila da Farida Abun nasu sai a hankali ko yaushe cikin shaye -shaye suke, Mumy da Hajiya Rabi basu gane ba, basa zama gida sai yawon busines, Abba 10m yaba Mamee ta bude shago, Dubai sukaje da Hajiya Rabi suka saro kaya aka zuba a shago.



Anty Amina tun da aka wuce da Ummi, Abba bai k'ara zuwa misau ba, kudin da ya bar mata sun k'are, sosai ta shiga damuwa, tana ta tunanin ya zatayi, Ummi ta kirata, tace zata turo mata kudi a acct din Nasir yaron Dan iya ne ya kawo mata, Anty Amina tace ina ki samu kudi, Ummi tayi mata, bayanin kudin da Alhaji Muhamud ke bata ne, an buda mata acct akwai dubu dari biyu zata turo mata dubu dari.


Anty tace sunyi yawa Ummi tace bata komai dasu, tasan wani lokacin Abba na da'dewa bai zo ba, ranar Ummi ta tura mata kudin, Anty ta godewa Allah, tayi duk cefanen ta, ko a waya tace bazata kira Abba Lawal ba, Mubina tun tana kewar Ummi har ta saba, bayan kwana biyu Anty Amina ta tashi da zazafi mai zafin gaske, asibiti ta je, test din farko suka tabbatar mata tana dauke da ciki wata biyu.



Anty Amina shiru tayi tana tunani, lokacin da aka zo auren Maryam sun tara da Abba Lawal, ashe rabon cikin ne, gida ta koma bayan sun bata magani, tace kowa bazata fa'dawa in ya fito su gani, koda ta koma gida ta isko matar Dan iya tazo sako ne Dan iya ya aiko mata na kudi yace tacigaba da addu'a tayi hankuri komai zai wuce, lokacin da duk Dan iya yaga Abba ya dade baizo zai aikowa Anty Amina sako haka Chiroma yana aiko mata.



Godiya tayi sosai, suka shiga Babban gida tare, za ta gaishe su, duk wanda yaga Anty Amina zaice tayi k'iba, ta debi damuwar Abba a ranta Ummin ta ma tasan batada matsala, damuwar ta daya kar Auwal ya samu lafiya yak'i Ummin.


Wata Jumma'a Baba Ladidi tace suje gidan su Hajiya Maryam, Ummi ta kira Gwaggo Maryam din tace gasu nan zuwa, suna hanya zasu je, wani mai napep ya bugi motar su, Auwal da Ummi suna baya, Baba Ladidi da driver ne gaba, jin k'ara bugun motar, Auwal yayi k'ara mai firgitawa ya suma.


Ummu Asma'u (Sa'adatu)

08182654508.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*


πŸ–ŠUmmu Asma'u(Sa'adatu)


Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.


*wanan shafin naku ne, yan Unguwar su Mumyn Gombe, na gode sosai Allah ya bar zumunci, godiya mai yawa Mameen Fadeel, Mamman Abba baby Radeetu comments din ku na burgeni*



*Bismillahirahamanirrahim*


*Page* 47πŸŽ—48



Cikin tashin hankali Baba Ladidi ta fashe da kuka tana kiran sunan Auwal, Ummi kuka takeyi sosai, Baba Ladidi sai fadin takeyi Manu mu wuce asibiti na shiga ukku na rasa Auwal, Manu ma a rude yake, parking motar yayi gafen hanya, ya dauko ruwan Pure water ya yayyafawa Auwal.



Ajiyar zuciya Auwal din yayi, a hankali ya bude idanunsa, Baba Ladidi ya tsurawa idanu, yace Gwaggo lafiya naga kina kuka, Baba Ladidi sunan Allah ta fara kira tana sallati, wanin kukan ta fashe da shi tace Allah na gode maka Auwalu ya samu lafiya. Auwal baki ya bude yana kallon ta, me ya same shi lafiya me ya samu? idanunsa ya sauke kan Ummi wacece wanan?.



Baba Ladidi ya Kalla yace Gwaggo wacece wanan? Baba Ladidi tace muje gida, Ummi yar kallo ta koma jin Auwal na tambayar wacece ita, gaban ta ya fa'di, gida suka koma, Baba Ladidi ta kira Alhaji Muhamud tana basa labari tana kuka, tace yaya yau Auwal ya kirani da Gwaggo, Alhaji Muhamud kabbara yayi yace Auwal ya sami lafiya Allah na gode maka, cen farko lokacin Auwal na yaro Baba Ladidi suke kiranta, da Auwal din ya k'ara girma yake kiranta Gwaggo, wani lokacin yace Baba, yanda yaran Hajiya Rabi ke kiranta mata.



Ya Maryam ta kira Ummi lafiya basu zo ba, Ummin tayi mata bayanin abun da ya faru, ya Maryam tayi farinciki sosai, tace zasu zo diba sa, tun da suka koma gida Auwal ke tambayar Baba Ladidi waye Ummi? ko yar uwar su ce bai santa ba.


Baba Ladidi tace yar uwar sa ce, Alhaji Muhamud ya kira likitan yace su hadu kano, likitan yace kar suyi masa maganar komai da ya faru lokacin da baya cikin hankalin sa, abi komai a hankali, Ummi jikin ta yayi sanyi sosai, kicin ta wuce ta fara girki, Baba Ladidi suna falo da Auwal suna labari.



Bayan Ummi ta k'are girkin kololin abinci ta dauko tana shigowa Falon Auwal ke fa'dawa Baba Ladidi, akwai wata yarinyar da suka ha'du England har sunyi alkawalin zasuyi aure, Mahaifin ta shine ambassador Nigeria to England ita ma likita ce, sunan ta Khadija Amma ake kiran ta sunan Mahaifiyar Abban tace.



Ummi wani irin juwa taji ya kasheta, sa'ar ta isa ga table din ta ajiye abincin, Baba Ladidi da sauri ta tashi ta rik'o Ummi tace zo ki zauna, Ummi zama tayi kan kujera, Auwal zaiyi magana Baba Ladidi tace Auwal anjima zamuyi maganar, shiru yayi, ya tashi zuwa cikin bedroom din sai mamaki yake yi, wanan gyaran kamar dakin mace.




A daren ranar Alhaji Muhamud ya iso tare da likitan, ya diba Auwal sosai yace komai normal yanzun, bayan likitan ya wuce Alhaji Muhamud ya fa'dawa Baba Ladidi gara su fa'dawa Auwal Ummi matarsa ce yafi su boye masa, Ummi na daki kwance, tana tunanin me zai faru, ta kasa kiran

Please Login or Register in order to submit comment