You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Anty ta fa'da mata, tsoron Anty kenan kar ya warke yak'i ta, gashi har yanada wadda yake so.



Alhaji Muhamud ne zaune, Auwal da Baba Ladidi na gefen sa, Alhaji Muhamud ya kwashe duk abun da ya faru bayan ha'darin Auwal din har shawara da likita ya basu na yi masa aure da aura masa Ummin, Alhaji Muhamud ya yi masa bayanin Ummi yar DC Abba Lawal ce, 'diyar matar sa dake misau.



Auwal cikin tashin hankali yake kallon Mahaifin sa, Alhaji Muhamud yace Auwal in har na isa kayi min biyayya, ina son ka rik'e Ummi amana, kayi min alkawalin ko bayan rai na, bazaka wulak'anta Ummi ba.



Baba Ladidi tace Maryam aka shirya aura maka da farko ta gudu, aka ce Farida, tace bazata aureka ba, Ummi da Mahaifiyar ta suka amince da auren ka, zaman Ummi gidanan ku shak'u sosai da ita, Auwal na rok'e ka kar ka wulak'anta Ummi, yanda tayiwa Mahaifanta biyayya kaima kayiwa naka nasan da yardar Allah zaka ga alfanon haka gaba.



Auwal yayi shiru, yace Abba naji insha Allahu zan zauna da Ummi, ina rok'on alfarma k'ara wani auren, akwai wadda nake so, Alhaji Muhamud zaiyi magana Baba Ladidi tace zaka iya auren wadda kake so Auwal rok'on mu daya kar ka wulak'anta Ummi don Allah.



Auwal yayi shiru sosai abun yayi masa ciwo ya zasu aura masa wanan k'aramar yarinyar wanan ai child abuse ne" yasha yiwa abokanin sa dariya masu auren k'ananen yara yanzun da wane Ido zai kalle su.



Baba Ladidi duk ta damu tasan Auwal ya amsa ne, ba don yana so ba, tasan halin sa sosai, Auwal da Alhaji Muhamud sun jima suna fira, Auwal sai tambayar Mumy yake yi Hajiya Rabi da su Farida, Alhaji Muhamud yace zasu so eh.



Auwal yace zaije Abuja tare da Alhaji Muhamud, Baba Ladidi tace ya bari ka k'ara jin sauk'i ko ka'dan hankalin ta bai kwanta da zuwanan Abuja ba, taji yana fadin zaije wani course a England garama ya tafin yafi zuwa Abuja, sai karfe goma suka watse fira, Auwal na zaune baida niyar tashi, Baba Ladidi tace kaje ka kwanta dare yayi, tashi yayi ya wuce dakin Ummi.



Ummi wanka ta shiga tana fitowa Auwal na shigowa dakin, tsaye tayi waje daya, ta kasa matsawa daure take da towel iya cinyoyin ta, batayi tsamanin Auwal din zai shigo dakin ba, Auwal wani irin faduwar gaba yaji da sauri ya fita dakin, cike da mamakin wanan wane irin fari gareta, yaga fararen turawa kala-kala bai tafa gani fari mai kyau irin na me ma sunan yarinyar?



Falo ya dawo ya kwanta, yana kwance tunanin kala-kala yakeyi, jin motsin Baba Ladidi da sauri ya tashi ya wuce dakin Ummi, tana zaune kan sallaya tana karatun Qur'ani, Auwal kayan sa ya dauka na bacci toilet ya shiga yayi wanka ya shirya ya fito, komai bace mata ya kwanta gefen gadon.



Ummi karatun ta cigaba da yi, Auwal na kwance yana sauraren ta, har bacci ya dauke sa, Ummi kan sallaya tayi bacci.

**** ****




Hajiya Rabi duk abun da akeyi bata sani ba, Alhaji Muhamud cemata dai yayi zaije kano bai fa'da mata kan Auwal ne ba, bayan ya wuce tana zaune falo ta fara jin kuwar Fadila da sauri ta wuce dakin su, Fadila da Farida sunyi shaye-shaye sai kuwa sukeyi, Hajiya Rabi cikin mamaki tace lafiya kuke, sai surutu sukeyi kamar mahaukata.



Cikin tashin hankali ta kira Mamee, Mamee tace gata nan zuwa, koda Mamee tazo Hajiya Rabi ta rufe daki don Farida sai tsirara ta koma, Mamee da Hajiya Rabi hankalin su ya tashi sosai, likitan gidan Alhaji Muhamud suka kira, bayan bincika ya fa'da masu sunyi -shaye-shaye ne, kwayar tayi masu karfi har dai Farida jinin Fadila yafi karfi.



Mamee da Hajiya Rabi k'asa suka zube suna kuka, wasu allurai likitan yayi masu yace zasu dawo hayacin su bayan awa ashirin da hudu zasuyi bacci yanzu, yace su kulla sosai, duk suka cigaba da shan irin wanan k'wayar kwakwalwar su zaa ta tabu ko su hauka ce, baa dauki lokaci sukayi bacci, Mamee da Hajiya Rabi kuka suke yi sosai, Hajiya Rabi tace zasu je wajen Malamin su neman taimaka, Mamee na gidan Abba ya kirata.



Cikin tashin hankali tace lafiya, yace tazo gida ba lafiya, gidan Hajiya Rabi ta bar Farida don batason Abba Lawal ya gane halin da Faridar take ciki, koda ta isa gida a tsakiyar falo ta samu Abba, hannun sa rik'e da takarda sai kai da komowa yake yi, cikin tsoro tasa inda yake, takardar ya mik'a mata.



Hannun ta na rawa ta amsa, bakin na rawa tace takardar meye ce? Abba cikin wata irin Murya da bata fita yace Khalifa da Marwan aka kama da hodar iblis a Uk, kisan hukuncin wanda aka kama da hodar iblis, tun farko abun da nayiwa gudu kika matsa sai yaje.


Mamee zaman yan bori tayi tace na shiga ukku in Balkisu wanan bala'in yayi min yawa da me Zan ji? wayake son ganin bayana? Abba wucewa yayi gidan su Marwan, Senator Bubu ya kira shi, su shirya zuwa Uk din, Mamee ta kira Hajiya Rabi, Hajiya Rabi ma hankalin ta ya tashi sosai.



Maryam dawowar ta daga asibiti, ta koma wajen likitan yace cikin ya zube, ta tarada Mamee na kuka jin abun da ya faru Maryam ma kuka ta fara, Hajiya Rabi gidan Abba ta wuce, tana ta kiran wayar Lailah bata zuwa tun safe ta fita bata dawo gida ba, Hajiya Rabi sai tunani take wanan masifar lokaci daya, ko wani ke masu asiri ne, inko nace asiri ko HAK'K'I ba.

**** ****




Sai bayan la'asar su Hashim suka isa Bauchi, koda suka isa Hajiya Dada tazo, sosai taji da'di ganin yan jikokin ta, kallon Zainab tayi tace Mairo bak'uwa kika samu, Mumy tace ai daga Jama'are tazo, Zainab ta duk'a tana gaida Hajiya Dada, Zainab ciki ta wuce ta basu waje.



Hajiya ta fa'da Hashim tafiyar tasa ce, tazo ne kan maganar sa da Zaituni, Hashim matse fuska yayi yace baya son ta, Hajiya Dada kuka ta fashe da shi tacewa Mumy, Mairo kina gani danki na wulak'anta in don Mahaifin sa baida rayuwa ban isa da yaran sa ba, Mumy shiru tayi ranta ya baci.



Hashim zai tashi Mumy ta buga masa tsawa tace Hajiyar warinka ce tana magana zaka tashi, tunda Hajiya tace dole zaka auri Zaituni, in na isa gareka, Hashim idanunsa sa sunyi ja sosai, ransa ya baci, ya kalli Hajiya Mairo yace Mumy zanyi yanda kika ce, zanyi maki biyayya kin san bana son zaituni, kin San irin tarbiyar su, inada wadda nake so, Hashim ya tashi yawuce dakin sa cikin tashin hankali da danisanin zuwansa hutun.



Hajiya Dada tace to ko kai fa, daman Mahaifanta yace ranar jumma'a sai a daura auren, Mumy tace wace Jumma'a Hajiya Dada tace jibi mana me zaa jira? in zan wuce gida, Mumy ta rako ta har wajen mota ta wuce.



Ummu Asma'u( Sa'adatu)

08182654508
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*

🖊Ummu Asma'u Sa'adatu)


Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.

*Wanan shafin naku ne, Mummy Abdallah, Alhamdulilahi, Maryam, Mmn Abdul, comments dinku na burgeni, godiya gare ku yan Taskar Asma'u Baffa, Fancy Honey, Umi, Hadeeza Muktar, yar Katibi, Jannat*


*Bismillahirahamanirrahim*


*Page* 49🎗50


Bayan Mumy ta dawo da rakiyar Hajiya Dada, dakin Hashim ta wuce, kwance ta same sa kan gado yana jin k'ira'a sudese, idanunsa sunyi jawur, kallon sa tayi tace Hashim! zaune ya tashi bai ce komai ba, Mumy tace Hashim ina rok'on ka kayi biyayya ga Hajiya, mu rabu lafiya da ita, rashin yi mata biyayya duniya zata zage in ace don Mahaifin ku bashi da rayuwa ne, Hashim yace Mumy na amince, sai dai inada wadda nake so in muka fahimci juna zan k'ara aure, damuwata daya auren mace biyu baya cikin tsari na.



Mumy shiru tayi tana sauraren sa, ita kanta bata son yayi aure biyu a yanzu, duk ta hana sa auren zafinsa ta cutar da shi, Allah ya zafa masa alhairi, Mumy ta fa'dawa Hashim jibi zaa
daura aure yace duk yanda suka yi, baida zafi, nan da sati biyu zai wuce, Mumy tace nan zaa kawo Amarya gefen Mahaifin ku.



In an kammalla ginin ka sai ka koma gidan ko ya kagani Hashim yace yayi Mumy, ginin zaa kara wani part tunda akwai fili gefen mace biyu zaa yi yanzun, Mumy tace ka barshi a haka gefen ka sai ka ba wadda zaka auri da bayan, in ance ayi wani gefen baza'a samu wadatacen filin gida ba, Hashim yace yanda kika ce zaa yi, Mumy hamdala tayi ta samu yaro mai biyayya, duk da tasan an cutar da shi, don yaran Hajiya Fatima ba tarbiya.


Zaituni ma bawani girme mata yayi sosai ba, duk bai wuce ya bata shekaru ukku, Hajiya Fatima ta biyewa yan barikin k'awayen ta b'ata rayuwar ta da ta yaran ta, kanta dai ta sani sai yaranta, da asiri ne ko meye, duk abun da tace Alhaji Kabiru yayi shi yake yi maigidanta, duk dangin sa bamai jin da'din ta, ko Mahaifiyar sa tana raye bata jin da'din danta tafi tunanin HAK'K'IN dangin Alhaji Kabiru ne.



Ke bibiyar Hajiya Fatima, tasha lurada ita bataji, yara har sun gindemi cikin gida ba miji, har ga Allah bata son auren Hashim da Zaituni don abun yafi karfin tane, yanda ta rabu da Mahaifin su Hashim din tana son rabuwa da Mahaifiyar sa lafiya, cikin gida Mumy ta wuce ranta ba da'di. Zainab na falo tana goge -goge Mumy ta shigo ganin yanayin Mumy tasan akwai matsala.



Sama Mumy ta wuce Zainab jikinta duk yayi sanyi lafiya ko? ya Hashim ma taga ya shige daki bai fito ba, Zara ce ta sauko k'asa, Zainab tace Zara lafiya Mumy take naga kamar bata jin da'di, Zara tayi tsuki tace Gwaggo mu ce sai ya Hashim ya auri 'diyar ta, shiko baya son ta, kin ga yaran sam basada tarbiya su, Zainab wani faduwar gaba taji ko meye sa? Hashim aure? tace Allah ya zafa masa alhairi.



Zainab na 'dagowa suka ha'da Ido da Hashim ya fito dakin sa zaije masallaci, Hashim murmushi yayi mata, Zainab din ma murmushi tayi, cikin tsokana yace Adda Zainab yanda Magaji kece mata, Zainab dariya tayi tana fadin kai ya Hashim, Hashim masallaci ya wuce, wani irin son Zainab yake ji a ransa, bai san ina zai fara ba.



Sosai yake son tarbiyar yarinyar batada hayaniya ko kadan, ga natsuwa irin yarinyar da yake mafalkin aure, auren sa da ita zai cikawa Magaji alk'awalin da yayi masa, zasu zauna da Addar sa waje daya, bayan Hashim ya dawo masallaci, harabar gidan ya zauna, saman kujerun dake wajen, Zara ya kira yace ta fa'dawa Zainab ta dafa mashi indomie yana waje.



Indomie Zainab ta dafa masa, sai da ta fa'dawa Mumy ta fita wajen, ajiye plate din ya dawo da Hashim tunanin da yake yi, Zainab zata juya ta koma cikin gidan yace ta zauna, zama tayi duk sukayi shiru, Hashim yace shekarun ki nawa, Zainab tayi murmushi tace sha shidda, Hashim murmushi yayi yace kinyi girma js3 kiyi kok'ari zanwa Mumy magana ayi jumping dinki, su Zara ka'dan suka girme har sun kusa k'are secondary, Zainab tace Allah ya Hashim zan yi, Hashim yace kin matsu ki k'are secondary kiyi aure ko?, Zainab ido ta zaro tace aure, makaranta nakeson yi.



Hashim Ido ya zuba mata, yace ance an maki miji ko, Zainab cikin mamaki tace in aa, ba wanda yace yana so na, cikin yarinta tayi maganar, Hashim murmushi yayi yace na yi maki miji, Zainab duk'ar da kanta tayi, Hashim yace kina son sa? Zainab tace duk abun da kake so ina so ya Hashim kayi min komai kai da Mumy, tana magana idon ta na cika da hawaye.


Hashim yace zamu bata in kina min kuka, Zainab share hawayen tayi tana fa'di na bari ya Hashim, Hashim yace kiyi min alkawalin bazaki Kula kowa har sai na dawo, Zainab ta d'ago da sauri tace komawa zakayi? Hashim yayi murmushi yace bakison in koma kanta ta 'daga masa, k'asan mak'oshin sa ya furta kina sona Addar Magaji? Zainab tace sosai ya Hashim banada kamar ku yanzun.


Hashim yayi dariya mai cike da farinciki, Zainab tace Kaci abincin zai yi sanyi, yana cin abincin suna fira yawan fira duk ta Magaji ce, Hashim ya fahimci in kanason Zainab ta saurareka ayi firan Magaji, su Lailah ne suka fito suka zauna fira suke yi suna dariya, Hashim yacewa Zainab gobe za muje a siyo maki waya, Lailah tace ya Hashim a cenza mana namu.



Mumy ce ta k'araso wajen tana fadin yaushe aka cenza maku waya, Ummina dai zaa siya ma, gobe zaku rakani a hado lefe, goben zaa fara gyaran gefen Abban ku, Hashim tashi yayi yace zai shiga ciki, nan ya barsu ya wuce ciki, yana jin son Zainab a zuciyar shi, duk ya tuna maganar Zaituni sai yaji kamar yayi kuwa kan haushi, zai fa'dawa Mumy, Zainab yake so gudun matsala gaba.

**** ****


Mamee kwana tayi tana kuka, Hajiya Rabi ma kuka ta kwana yi, tayi ta kiran num Lailah bata shiga gasu Fadila kwance kamar gawa, bayan gari ya waye su Abba da Mahaifin Marwan suka wuce Uk, tafiya ce mai cike da tashin hankali Abba cikin dare gudu duk ya fa'da, Senator Bubu ma jininsa ya hau sosai, don ya matsa ne sai yaje, asibiti sunce ya kwanta ya huta.


Alhaji Muhamud na kano Abba Lawal ya kira sa ya fa'da masa abun da ya faru, Alhaji Muhamud hankalin sa ya tashi sosai, yace yaje kano Auwal ya sami lafiya, Abba yayi murna yace in sun dawo zai zo, su Abba sun isa, duk inda ya kama su shiga sun shiga, magana daya ce dokar k'asar duk aka kama mutum da hodar iblis, shekaru ashirin da biyar ne gidan yari, Senator Bubu hankalin sa ya tashi ya kira shugaban k'asa Nigeria ya taimaka masu.



Maganar dai itace sai sunyi "25yrs in prison" dole su Abba suka dawo gida da kyar aka bar su, suka ga su Khalifa, Abba kuka Khalifa kuka, Abba ya rasa abun da zai fa'dawa Mamee ganin ba mafita ya fa'da mata, Mamee suma tayi, aka wuce da ita asibiti jinin ta ya hau sosai. Maryam ta kira Hajjo kakar Mamee tana kuka ta fa'dawa Hajjo Abun da ya faru, Hajjo kuka takeyi tana cewa shirin matar ubanki ce, wallahi bazamu k'yale ta ba, duk abun nan mutanen sun kasa gane HAK'K'I NE ke bibiyar su.



Hajiya Rabi dole ta kira Alhaji Muhamud tace Lailah bata dawo gida tun jiya, Alhaji Muhamud cikin tsananin mamaki yace Lailah bata dawo gida har aka kwana baki fa'da mun ba, fa'da sosai yayi yace gashi nan shigowa Abuja, sai da aka kwana su Fadila suka tashi, sai Zara Ido sukeyi, Farida gida ta wuce, Fadila Hajiya Rabi kuka tasa mata tace, kashe in kuke son kuyi ne, ga Lailah tun jiya bata dawo gida ba, Fadila komai bata tace ba ta shige toilet don ganin takeyi duk Mumyn ta dame ta.



Maryam ke tare da Mamee asibiti, Maryam ta rasa me ke damun ta, duk bata jin da'din jikin ta, ko fever ce tunda likitan ya fa'da mata cikin ya zube, kwana Mamee biyu asibiti ta dawo gida duk ta rame, Hajjo ta iso daga misau, ta fa'dawa Mamee, Anty Amina ce tayiwa yaran ta aiki suka lalace, Mamee ta share hawayen da suka zubo tace wallahi bazata yarda ba, sai ta dauki fansa.



Hafsa tana shigo dakin jin abun da Mamee ke fa'di ta gaida Mamee ta fita, cikin takaici tace yaushe Mamee zata gane, Anty Amina boyar Allah ce, HAK'K'IN ma bazai barki ba Mamee, duk cikin yaran Mamee Hafsat ce daban ita ce k'arama har Uwar ta fita tunani, Abba bayan an sallami Mamee haka yaji yana son zuwa misau, shiryawa yayi ya wuce, Mamee ma a waya ya kira ta, sosai abun yayi mata ciwo, nan ta k'ara haukacewa acewan Anty Amina tayi masu asiri.


Ranar Monday tun asuba Ummi ta shirya abincin break fast ta shirya zuwa makaranta, ranar zasu fara ssce, Auwal koda ya tashi ta wuce, wanka yayi ya shirya,ya fito abinci yaci yana cewa Baba Ladidi girki nan yayi da'di, Baba Ladidi tace aikin Ummi ne, shiru yayi bai ce komai ba, bai ma Lura bata gidan ba.


Baba Ladidi tace ya kamata ka shirya kuje Misau ka gaida Mahaifiyar Ummi, Auwal ha'de fuska yayi yace inda ke shirin tafiya, Baba Ladidi tace Abbanka yace sai Ummi ta k'are jarrabawa ku wuce tare, Auwal zaiyi magana ta 'daga masa hannu, shiru yayi sosai yaji ya k'ara jin haushin Ummi, yarinya ta zame masa bala'e rayuwar sa, aiko duk ta bishi zata ga takaici, tashi yayi ya fita waje yana waje Ummi ta dawo, morning paper ce tun karfe bakwai suka fara, Auwal na ganin ta ya bata rai.



Ashe ko secondary bata k'are ba, ji wani k'aramin hijab da tasa kamar ba matar aure ba, tsuki yayi don me zai damu da shigarta ta, Ummi ganin yanda ya dauke kai murmushi tayi ta isa wajen da yake tsaye, tace ya Auwal barka da kwana, Auwal a ciki yace lafiya lau sai mamaki yakeyi duk dauke mata kan da yayi har inda yake tazo ta gaida shi.



Ummi wanka tayi ta cenza kaya zuwa bak'ar jallabiya, gyalen rigar ta daura, ta gyara fuskar tayi ta fito wajen Baba Ladidi, suna fira da Baba Ladidi Alhaji Muhamud ya kira Baba Ladidi yana fa'da mata abun da ya samu Khalifa, Baba Ladidi sai salati takeyi, tace Abba Lawal fa? Alhaji Muhamud yace ya wuce Misau bayan sun dawo.



Bayan sun k'are waya Baba Ladidi ta rasa yanda zata fa'dawa Ummi, Ummi sai kallon takeyi taji ance Abban su, Baba Ladidi daki ta shiga ta kira Anty, Anty Amina da kukan ta da Dan iya ya fa'di mata don Abba ya kira su, Anty Amina tacewa Baba Ladidi zata kira Ummi ta fa'da mata, ta kira Ummi ta fa'da mata, Ummi kuka tayi sosai sosai abun ya dameta, Auwal ma a yaji ciwon abun, Baba Ladidi tace gobe in Ummi ta k'are jarrabawa zasu je Misau suyiwa Abba jaje.



Auwal ba yanda zaiyi, da safe suka wuce driver yaja motar don likitan yace kar Auwal yayi driving, Abba Lawal Anty Amina kwatsam ta gashi, abinci ta shirya masa yace baya iya ci, gefen shi ta zauna, tayi ta bashi magana tace yasa ayi ta addu'a babu abun da yafi karfin addu'a, in Allah ya yarda komai zaiyi dai-dai.


Abba Lawal abinci yaci, yayi wanka, ya dan ji natsuwa rabon sa da abincin tun shekara jiya, kwantawa yayi kan kujera yayi bacci, Anty rufe masa kofa tayi ta barshi yayi bacci, Anty Amina tana zaune falo sai tunani takeyi ta tausayawa Mamee, Allah ya kawo sauk'i, wayar ta janyo ta kira Mamee ta da'de tana ringin cen Mamee ta dauka.



Bayan su gaisa Anty Amina tace wani abun ya faru Allah ya, bata k'arasa ba Mamee tace gurin ki ya cika Amina, ki sani naki bak'in cikin na nen tafe, sai yafi nawa, me kika ra kiji munafuka duk shairin ki kanki zai koma, mu zuba da n,i kukeyi, Anty Amina imani ne yayi mata yawa anya kan Balkisu lafiya lau yake, ko dai Abun da ya samu Khalifa ya taf'i kanta.



Ita take zargi da abun da ya samu Khalifa, Anty Amina ya Maryam ta kira tana fa'da mata, ya Maryam tace k'yale sakarya mutuniyar banza, in bakiyiwa yaranta asiri ba, mugun abunta ya koma mata, HAK'K'I NE ke bibiyar ta, wallahi wanan ma ka'dan ne komai bata ganin ba, ba zalunci ta sawa gaba ba, zata gani, ya Maryam tace ya Abban ance yazo Misau, Anty Amina tace yayi bacci yasa damuwa a ransa, ya Maryam tace sai addu'a.



Bayan Ummi ta k'are exams suka wuce Misau, tanada intervals na 3dys, Auwal duk fira da sukeyi komai bace ba,yana gaba da driver suna baya, suna tafiya Ummi tace ruwa take so, Auwal yace driven in yakai inda ake sayarda ruwa, a gefen hanya suka tsaya, Auwal din yaje ya siyo masu ruwa da drinks, Baba Ladidi ya mik'awa ruwan ko kallon Ummi baiyi ba, Baba Ladidi amsa tayi tana mamakin Auwal din.




A misau sosai Anty Amina ta tarbe su har Abba, sun jajanta masa akan Khalifa, Ummi da Auwal sun shiga cikin babban gida ya gaida su, Auwal guest part din gidan aka sauke shi, Baba Ladidi tace Ummi taje cen ta kwanta, kayan ta, ta dauka ta wuce, Auwal na zaune falo yana kallon news ta shigo, cikin mamaki yace lafiya? Ummi duk taji kunya da takaici, bata ce masa komai ta wuce cikin dakin toilet ta shiga tayi wanka ta sanya night gown ta kwanta, koda Auwal ya shigo tayi bacci tsuki yayi ya shirin kwanci yace yarinyar sai shegen naci

*** ****


Muktar police school ya samowa Magaji, kudin su ba yawa Makaranta nada kyau, yazo da headmaster su Magaji yacewa Baba Delu gwabnati ce ta dauki nauyin karatun Magajin Baba Delu ganin Muktar tasan ma'aikaci ne tayi shiru, tayi bak'in ciki sosai Magaji sai cigaba yakeyi Abu na tasha wajen *Daudu* duk ya shigo gidan yaga yan kayanta zai dauke.



Anyi mata aiki kan Magaji shiru sauk'i ma tabar ganin matar nan a mafalkin, tashin hankalin ta yanzu kasuwar dillanci bata ci, tana zaune ta zuba tagumi Abu ya shigo yau relaxer yasa gashin shi har sallon yaje, yasha Jan baki sai rangwa'da yakeyi, Baba Delu kallo daya tayi masa ta kauda kai, Akuyar dake daure ya fara kwance daurin ta, Baba Delu cikin Mamaki tace ina zaka jemin da Akuya, Abu yace biki gare mu gidan Magajiya banida kudin biki.



Baba Delu tashi tayi tace ajiye min Akuya ba inda zaka jemun da Akuya, Abu yace Baba meyasa kike min bak'in ciki ne, Akuyar nan ko mutuwa kika yi gadona ce, in bani son bak'in ciki, yar bak'in ciki Kawai Baba Delu tsaye tayi tana kallon Abu har ya kwance Akuya ko kallon ta baiyi ya wuce abun sa, Baba Delu zama tayi tana kuka.


Ummu Asma'u(Sa'adatu)

08182654508
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*

🖊Ummu Asma'u(Sa'adatu)

Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.


*Wanan shafin naku ne, Mumy Best, Fauziya Toles, Mummy Musadiqq*


*Bismillahirahamanirrahim*


Page 51🎗52


Baba Delu najin k'ara machine din Malan Bello ta fara masifa, bazata yarda sai an biyata Akuyar ta, ta dawo gida ba Akuya, tasan aikin Magaji ne, sata a jinin su take, Malan Bello yana jin abun da take fa'da yasan ba yanda zaa yi Magaji ya daukar mata Akuya, bai ce mata komai ya wuce cikin daki, Baba Delu ta jayo rigarsa jikinta sai rawa yake yi, tace kai kurma ne, baka jin ina magana b'arawon danka ya sace min Akuya.



Wallahi ko a biyani ko inyi k'arasa, Malan Bello cikin takaici yace naji zan biyaki sakar min riga, wucewa yayi cikin dakin zuciyarsa nayi masa zafi wanan masifar ta ishe shi, ana haka Magaji ya dawo makaranta, Malan Bello ya fito yace meya kai ka daukar Akuyar Delu? Magaji cikin mamaki yace wace Akuyar? wallahi in Ban dauki Akuyar ta ba, Baba Delu ta zaburo tace wazai dauka in ba kai ba, b'arawo anyi gadon sata uwar ku har ta bar duniya sata take yi.


Malan Bello cikin takaici ya ajiye mata dubu ukku ya fita waje, Magaji dakin su ya wuce idon sa na zubar da hawaye, cikin kuka yace Allah ka saka min, yana cire uniform din sa Baba Delu ta kwalla masa kira tace duk bai zo ya k'are mata aiki bazai je Islamiya ba, Magaji da sauri ya fito ya fara wanke -wanke yayi shara, yana kare ya fara wanki, koda ya k'are hudu tayi da sauri yayi wanka ya wuce makaranta, a hanya ya sayi kosai yaci kudin da Maman Sadiya ta bashi, bai kashe ba.



Da safe kamin ya wuce makaranta ta bashi abinci, Baba Delu kudin ta dauko tace gara hakan, lak'awa Magajin na samu kudin Akuyar, ta shirya zuwa dillanci ta, ta biyo hanyar gidan Magajiyar karuwai duk yan Daudu ne da karuwai sai goge ake yi ana biki, Abu ta hango yana shan taba, Baba Delu sauri tayi ta wuce idanunta na zubar da hawaye,

Please Login or Register in order to submit comment