You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta rasa me ke damun Abu, kudin ta dai take kaiwa Malan ko yaushe abun gaba yake yi, ta mance HAKKI biya yake yi.

**** ****


Auwal ya motsa yaga Ummi na sallah, tashi yayi ya yi arwala ya fara sallah, lokacin sallar subahin yayi kusa, bayan sun k'are kowanan su da abun da yake rok'o, Ummi na addu'ar Allah ya dai-dai tsananin Anty da Abba, Allah ya dai-dai tsananin ta da Auwal Allah ya bata sa'ar karatun ta, Auwal na addu'ar Allah yasa Khadijasa bata manta da shi ba.


Ummi sai da tayi wanka ta shirya, tayi k'waliyya gwanin sha'awa, gefen Anty ta wuce tasan tana kicin, a kicin din ta sameta har Mubina, k'aidan Anty duk safiya in yaranta basa zuwa makaranta tare suke girki, Ummi ta sanya hannu suka ha'da abincin, sinasir ce da miyar ganye favorite din Abba Lawal, suka ha'da soyayen dankali da kwai, ruwan zafi sun sha kayan kamshi.


A falon Abba Mubina ta jera abincin Abba yace duk su hadu falon sa a karya, har Baba Ladidi, Abba Lawal yace sun zama daya, Auwal yayi wanka ya shirya cikin kaftan din wani ha'daden yadi milky collar, yana dadana wayarsa, Ummi tayi sallama ta shigo, tace barka da kwana, bai d'ago ba yace barka mu, Ummi tsaye tayi, Auwal bai d'ago ba yace ya dai, Ummi tace kazo Abba na kiranka.


Sai lokacin ya d'ago kansa, suka ha'da Ido da Ummi, kauda kansa yayi gefe, gaban sa na faduwa ya rasa dalilin duk ya kalli Ummi sai yaji faduwar gaba, falon suka wuce, Auwal ya gaida Abba da Anty ya zauna suka fara cin abinci, bayan sun k'are suka fara shirin tafiya, Anty Amina tace tana son magana da Auwal a falon ya sameta, tana kan kujera ya zauna kan cafet, Anty Amina tace Baba Ladidi ta fa'da min in visa ya fito zaku wuce ka ida course dinka, Allah ya kaiku lafiya.


Allah yasa a dace, kayi hankuri da Ummi yarinya ce akwai kurciya sosai tare da ita, nasan an aura ma ita ba bisa ra'ayin ka ba, in tayi ba dai-dai ka tsawa ta mata, ka rik'e Ummi amana Auwal, Auwal jikin sa yayi sanyi sosai, sosai yake ganin girman Anty Amina, yana tausayawa mata, duk labarin ta, Baba Ladidi ta fa'da masa, Auwal jiki sanyaye yace Anty zan rik'e Ummi amana insha Allahu.


Anty Amina godiya sai tayiwa Auwal, suka wuce, Auwal sai tunani yake yi, Anty Amina tayi masa wayo manya, yayi niyar in yaje England zai sawak'a ma Ummi ya rok'i gaffara Mahaifin sa, yanzun yayiwa Anty Amina alkawalin zama da Ummin, bai masan ta ina zai fara ba, har suka je kano baice komai ba, Baba Ladidi sai addu'a takeyi Allah yasa dubara nata yayi don ita tace Anty Amina tayiwa Auwal din magana, tasan Auwal din nace mata Anty Amina tausai take bashi labarin da ta bashi nata.



Bayan sun isa Ummi kicin ta wuce ta dora abinci, Auwal wanka yayi ya kwanta, duk kano ta ishe shi yana son zuwa Abuja Baba Ladidi ta hana, ko me hakan ke nufi bai sani ba?.

**** ****

Duk abun da ake cikin Hajiya Rabi batasan Auwal ya sami lafiya ba, Baba Ladidi tacewa Alhaji Muhamud kar ya fa'dawa kowa, har yan uwan su, matsalar Khalifa sai hankalin sa ya dauke, ga rashin ganin Lailah, ranar da ya koma Abuja aka shiga neman Lailah har dare ba labari, Hajiya Rabi kamar tayi hauka.


Har akayi kwana ukku ba labarin Lailah, sai rana ta hudu yan sanda suka tsinci gawar Lailah gefen hanya, an debe mata idanu da nono,
Alhaji Muhamud suka kira, cikin tashin hankali ya isa police station, gawar suka nuna masa yace Lailah ce, sun fa'da masa zaa je asibiti ayi gwajin kan gawar kamin su bashi ita.



Alhaji Muhamud yace shi musulmai ne baya son wani dogon bincike tunda ba dawowa zatayi ba, duk wanda yayi mata haka shi da Allah, gawar ya dauka suka wuce gida, Hajiya Rabi na daki kwance cikin damuwa duk ta rame cikin kwana biyu fuskar tayi k'ozai k'ozai rashin kwalliya ga man blicin duk ya bata mata fuska, gawar Lailah aka ajiye tsakiyar falon Alhaji Muhamud ya kirata Hajiya Rabi tazo, koda ta shigo falon gawar taci k'aro da ita cikin tashin hankali ta zube k'asa tana kuka da ihu.



Alhaji Muhamud yanuwansa ya kira, ya kira Abba Lawal ya fa'da masa, ya kira su Baba Ladidi, duk mutuwar ta tafa su, waya yiwa Lailah wanan aikin, abun da basu sani Lailah batada aiki sai bin masu kudi Alhazawa kudi sosai suke bata suyi lalata da ita, wasu ma ta baya suke amfani da ita, duk halin da take ciki Maryam dai tasani don Lailah mutuniyar tace, cikin rashin sani ta hadu da Don suka k'ulla, Don dan k'ungiya asiri ne yayi amfani da body parts dinta wajen tsafi bayan sun k'are suka yadda ita gefen hanya.


Maryam lokacin da labarin rasuwar Lailah ya sameta kuka tayi sosai, tace Don ne tasan ranar da Lailah ta bace sunyi waya tace mata zasu hadu da Don,har Maryam din ta fa'da mata cikin da ta zubar Lailah tace ke kika fara yanzun in na zubar da ukku duk Mumy bata gane ba, Maryam kuka tayi sosai.



Ranar su Auwal, Ummi Baba Ladidi suka isa Abuja, Hajiya Rabi bata san sunzo tana daki anyi mata allura baci don abun kamar hauka ya zama mata, Farida ma kuka takeyi sosai na rashin yar Uwar ta, Auwal ma mutuwar ta tafa shi, dakin Auwal Baba Ladidi tace Ummi ta sauka yana da daki a Abuja, su Baba Ladidi gefen bak'i suka sauka da wasu dangin Alhaji Muhamud, sai dare aka rufe Lailah.



Mamee tayi kuka har idanta sun kumbura sai tunani take yi meke faruwa ne? ganin Anty Amina da Abba Lawal sunzo tare, Mamee abun yayi mata ciwo lele Anty Amina ta samu guri amman zata daidaita mata zama har akayi kwana ukku kullun sai anyi Hajiya Rabi allura bacci.



Ranar da akayi kwana hudu taga Auwal da Ummi kuka ta fashe da shi, Auwal ya samu lafiya ta rasa Lailah, Farida sai shaye -shaye takeyi, bazata yarda ba, kuka sosai take yi, dayawan mutane sun zaci rashin 'diyar tane ke damun, ranar su Auwal suka juya, duk nacin sai an barshi Abuja Baba Ladidi tak'i tace wani satin in Ummi ta k'are exams zasu wuce an samu visa su, Alhaji Muhamud ma yace hankalin sa yafi kwanciya Auwal din na kano domin gani yake yi kamar wasu ke masa shairi kan yaransa.


Ummi duk abu ya dameta Auwal baya kulata ko tayi masa magana sai yaga dama zai amsa, su kwanta waje daya bai ce mata komai damuwar ba wanda zata iya fa'dawa, bata boyewa Anty Amina komai, amman wanan bazata iya fa'da mata ba ko ta fa'dawa Gwaggo Maryam ta bata shawara yanda zatayi?

**** ****



Mumy ta hado lefe dai-dai karfin su akai kai gidan su Zaituni, an gyara gefen Abban su Hashim din duk da Hajiya Fatima ba haka taso ba, sun so Hashim ya amshi gidan da Mahaifin Zaituni ya bashi yace baya so, akayi yak'i dole suka hank'ura.


Shak'uwace sosai tsananin Hashim da Zainab, ya siyo mata waya kullun suna magana da Magaji ya fa'da mata zancen Akuya tace yayi hankuri, Zainab ta samu natsuwa sosai.


Ranar Jumma'a aka daura auren Zaituni da Hashim, Hashim ko daurin aure bai jeba, ranar Jama'are yaje wajen Magaji Zainab sai kiranta yayi ya bata Magaji, sun Jima suna fira da Malan Bello ya fa'dawa Malan Bello Zainab yake so Malan Bello yace ya bashi, Hashim farin ciki baa magana sai magarib ya dawo Bauchi, Mumy tayi ta masa fa'da ya zaa yi a daura aure baya nan, baice komi ya wuce dakin sa.


Bayan isha'e aka kawo Amarya, Hashim fita yayi cen bayan layin su ya kira Zainab cen ta samesa, gidan cike da yan kawo Amarya, Hashim bude mata gaban mota yayi ta zauna, ya fa'da mata Malan Bello ya bashi auren ta, Zainab ido ta bude tace Zaituni fa? Hashim ha'de fuska yayi yace ba ruwan ta, Zainab sai mamaki takeyi daman shine ke sonta ita duk tunanin ta wani zai aura mata, anya wanin abun zai yuyu tana masu aiki, ko Mumy ai bazata yardar ba, sai dai har ga Allah tana son Hashim yana cikin tsarin mazan da takeso gashi da illimi addini sosai.


Ummu Asma'u Sa'adatu)

08182654508.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*

Ummu Asma'u( Sa'adatu)


Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama


*Bismillahirahamanirrahim*


*Page* 53πŸŽ—54


Hashim kwantar da sit din motar yayi ya kwanta, jin yake yi su tabbata haka ko ka'dan baya son rabuwa da Zainab yana son Zainab sosai yana tausayawa rayuwar su, yana burin dawo masu da duk gatan da suka rasa rayuwar su, Zainab duk ta takura gida take so zuwa bata son Mumy ta gane bata gidan, cikin fuskar damuwa tace yaya muje gida kar Mumy ta neme in batasan na fito ba.


Hashim shiru yayi yana sauraren ta, Zainab tace yaya pls, Hashim gyara sit din yayi yaja motar, koda sukaje gidan duk yan kawo Amarya sun watse, har abokanin Amarya sunyi jiran ango sayen baki, basu ganshi ba sun wuce, Zainab yana parking da sauri ta bude k'ofar motar ta zuba cikin gida da gudu, Hashim dariya ma abun ya bashi, k'urciyar ta na daya daga cikin abun da ke birgesa.


Su Mumy na zaune falo Zainab ta shigo sai hak'i takeyi Mumy tace Ummina lafiya? Ina kika je? Zainab tace ya Hashim ya aike in, Mumy tace kuzo ku gyara falon ina su Zara, Hashim ne ya shigo, yana fadin Mumy akwai abinci yunwa nake ji, Mumy hararasa tayi, duk da tasan bayason auren Zaituni abun yayi bai kyauta ba.


Kan table ya zauna ya fara cin abinci sai aikin kallon Zainab yakeyi dake tattara plates din da aka ci abinci, Mumy na lura da Hashim kar dai Zainab yake so, har ga Allah da tayi farinciki, da safe zata bincike sa, in har Zainab yake so bazata yi shiru ba, don Zaituni, tasan baiyi mata, yarinyar sam ba tarbiya, ko yanzun da aka kawo ko yar kunyar nan ta Amare babu.


Mumy tacewa Hashim in ka k'are cin abinci zamu rufe gefen mu, Hashim murmushi yayi yasan korasa takeyi, bayan ya k'are dakin sa ya shiga yayi wanka, ya cenza kaya zuwa jallabiya, kayansa ya hado cikin trolley yaba Zara yace takai masa gefensa, Zainab na gyara dining table ya fito falon, Zainab kallon sa tayi ta kauda kai, haka nan taji duk bata ji da'di ba, Hashim zama yayi kan kujera yana kallon ta, bayan ta k'are tace Mumy tace a rufe k'ofar falo, Hashim yace korata kukeyi, zo ki rakani.


Zainab kicin ta wuce, Hashim ya bita yace in bazaki raka bazan je ba, juyowa tayi suka fito tare, har gefen ta raka shi, tajuya tace sai da safe yaya da gudu ta wuce ta rufe k'ofar fdlon, Hashim murmushi yayi ya wuce ciki, ta falon ya shiga, gyara sosai aka yiwa gidan, an kashe kudi sosai, Hashim dakin dake cikin falon ya wuce, Zaituni na dayan dakin tana jin shigowar shi, ta fito.


A dakin ta same shi, yana tsaye yana kallon gefen Mumy ta window, Zaituni ba sallama ta fado dakin rumgumo Hashim tayi ta bayansa, da sauri ya janye jikin cikin takaici yace baki iya sallama ne ba? zaki shigo min daki ba sallama, in bazaki yi sallama fitar min da daki.


Zaituni cikin jin haushi ta fita, sallama tayi ta shigo, kok'arin rungomo Hashim takeyi ya wuce toilet, arwala yayi ya fito, sallah ya fara yi, tun Zaituni na tsaye har ta zauna, bayan yayi sallama, zai tada wata tace, nazo a bani hakki na, Hashim cikin mamaki yace hakki lailai yarinyar nan batada kunya, cikin takaici yace zo muyi sallah in baki hakkin ki, Zaituni dakin ta koma ta dauro zani kan night din ta sanyo wani k'aramin hijab.


Hashim na sallah ta shigo, bayan ya sallame kallon ta yayi yace wanan hijab din, tace shi ke gareta, Hashim yace ta dauko zane ta dora sama hijab din, sallah raka'a biyu yaja su, Zaituni duk ta matsue a sallame, yaja dogayen ayoyi k'afafun sunyi mata sanyi, sosai buk'ace take kayan matan da ta dirka.


Bayan sun sallame sallah Hashim addu'a yayi sosai, ya fara zuba mata tambayoyi kan farilan sallah, sunnoni mustahabi, duk bawanda ta fa'di dai-dai, yace ta karanta masa abun da ya sawak'a a Qur'an nan ma sai a hankali Hashim ranshi ya bacci da wannan jahila zaiyi rayuwa.


Cikin jin haushi yace ta fara shirin komawa Islamiya, Zaituni jinsa dai takeyi, kan gado ya kwanta cikin takaici, Zaituni ta kwanta bayansa ta rugumeshi, Hashim dif yayi, Zaituni cikin kissa tafa shafa jikin sa, Hashim jayota yayi zuwa jikin sa, ko ka'dan baiji sha'awar ta ba, zaiyi kokari ya bata hakkin ta, hular dake kanta ya debi, ga mamakin sa kitsion attachment ya zuba, cikin takaici yace meye? wallahi wanan baa cikin gidan nan ba, in kinason kanki cire shi, Zaituni tace zan cire pls, don ita dora ta da yayi jikin shi, duk wani yanayi takeji, Hashim ya daure ya kusanci Zaituni sai dai me wajen a bude duk irin gyaran da tasha, Hashim gefe ya koma ya kwanta, idanunsa sa na zubar da hawaye, duk irin tsare kansa da yake, ya buge da auren watsatsiya, wanan kaddarasa ce ya amshe ta hanunu biyu yana rok'on Allah ya bashi ikon cinye ta.



Yana da illimi sosai akan mace, duk gyaran da akayiwa Zaituni ya gane ta gama wattsewa a waje sam baiyi mamaki ba, tashi yayi cikin fushi ya shak'o wuyan Zaituni, yace fa'da min wa kika tara dashi kamin in aure ki, Zaituni kuka ta fara tana fadin don baka sona zakayi mun shairi, Hashim cikin tsananin fushi ya dauke ta mari yace kar ki rainan min wayo, fa'da mun, Zaituni taji tsoro sosai don Hashim iya karfin sa ya shak'o ta, idanunta duk sun fito, cikin wahala tace lokacin ina makaranta da wani course mate dina yace zai aure in.



Hashim sakin ta yayi yace Gwaggo ta sani? tace aa, yace bayan shi fa, ina ina ta fara, Hashim cikin sanyi jiki ya wuce toilet yayi wanka yayi arwala ya fito, sallah ya fara yana sallah yana kuka, Zaituni dakin ta koma sosai hankalin ta ya tashi, Hashim sai da yayi asuba ya kwanta, Mumy da safe ta aiko masu breakfast har shabiyu Hashim bai fito, Mumy duk ta damu lafiya, bai zo ba ya gaishe ta, su Zara sunje Zaituni tace bacci yake yi, Mumy ta kira wayarsa rufe.


Sai da yayi sallar azahar ya fito, idansa duk sunyi ja sun kumbura, Azumi ya tashi da shi, jin hayaniyar yan uwan Zaituni ya fita k'ofar baya, Mumy ta tsorata da Hashim yazo gaidata tace lafiya yace ba komai, da ta matsa yace Zainab yake so ta nema mashi auren ta, Mumy shiru tayi tace jiya aka kawo ma mata fa, yace Zainab yake so, idanunsa sun ciko da hawaye, Mumy tace yaje ya samu Hajiya Dada ya fa'da mata.


Hashim gidan Hajiya Dada yaje,bayan sun gaisa ya fa'da mata, fa'da ta fara yi masa, Hashim cikin takaici yace wallahi bazan zauna da wanan watsatsiyar ba, ko ki yarda nayi aure ko na sakota yau wallahi, Hajiya Dada sosai ta tsorata kar ya bar masu abun kunya ankai Amarya jiya an sakota dangin Mahaifin Hashim din ta kira su shirya suje Bauchi neman aure.


Hashim ya kira Baban Sadiya, ya fa'dawa Malan Bello, Malan Bello ya rok'i Baban Sadiya aje gidan mai unguwa ayi komai cikin Siri bayason Baba Delu taji, Baban Sadiya yayi murna daman tunanin sa baisan yanda zaiyiwa Malan Bello maganar ba, bayan gari ya waye, k'anin Mahaifin Hashim biyu sukaje neman aure, num Baban Sadiya Hashim ya basu, suka kira ya kai su gidan mai unguwa, Malan Bello yaje da k'aninsa biyu.


Bayan an k'are sun tambaya an basu ansa sadaki, Malan Bello yace yanason a daura aure yanzun, Baban Sadiya ma yace haka yafi, Malan Bello yace yanason su kira masa Mumy, sun kira Mumy an fa'da mata, yace ta bashi Zainab, ya fita waje, yace Zainab kinason yaron da kike gidan su? Zainab tayi shiru, yace kiyi magana, tace ina son Baba, yace Masha Allah zan kira Hajiya Mairo anjima.



Sai da aka daura auren Zainab da Hashim suka dawo an biya sadaki dubu goma don Malan Bello yace bayason komai, ya rok'i mai unguwa kar ya fa'dawa kowa har lokacin da zata tare, mai unguwa yace kowa bazai ji ba, sun San irin zaman da yaran keyi da Baba Delu, a Bauchi Hashim duk ya matsue su dawo yaji in an bashi Zainab, bai san an dura masa Zainab ba.

**** ****

Mamee da Hajiya Rabi bayan an k'are kwana bakwai na rasuwar Lailah, suka shiga Malamai, Mamee matsalar ta Khalifa, Anty Amina Ummi aiki sosai zaa yi mata Auwal yak'i Ummi, har kan su Farida da anyi masu aikin, rayuwar su mai Ban tausayi komai bazasu rok'i Allah sai dai ayi masu, Malamin da suka je kan maganar su Farida yace a kawo su akwai aikin da zai masu.


Yace kar akai su rana daya kowa da ranar da zaa yi masa aiki, Hajiya Rabi tacewa Mamee a fara kai Farida, ranar da aka kai Farida, yace suje su dawo, wata powder ya shak'a mata tayi bacci mai baiyi, ya tara da Farida, da yake baa cikin hayacin take ba, batasan yayi ba, da farko bata hul'da da maza da shaye -shaye yayi yawa ta fara bin maza, Malamin ya dade kan Farida yana shek'e ayar sa.


Koda su Mamee suka dawo ya fito yana tsiyayar zufa yace aiki ne aka yi mata ya karya shi, godiya suka yi masa suka dauki Farida don har lokacin bata farfado( duk wanda ya taka dokar Allah sai ta taka shi, Nabeety zango) Hakkin wasu, yaja masu sun lalata rayuwar 'yar 'yar 'yar su, 'diyan wasu basu lalace nasun sun lalace.


Ranar da akayiwa Farida aikin, ranar ta shawo k'ayar ta Alhaji Muhamud na falo da bak'i taje tayi ta masu hauka, da k'yar aka fiddata falon, Alhaji Muhamud zubewa yayi jinin sa ya hau sosai, sai da aka kira likitan sa, duk da haka Hajiya Rabi duk aikin da akayi masu sai da suka binne, bak'aken bunsuru biyu aka yanka.


Aikin su Auwal wani amintacen ta aika kano, ranar da aka je binne Layan ranar suka tashi zuwa England, bayan Ummi ta k'are exams din ta, Ummi tayi kuka sosai duk fuskar ta kumbura, Anty Amina tazo kano har airport suka raka su da Baba Ladidi, Anty Amina gefe ta kira Ummi tayi mata nasiha sosai tace kar tayi wasa da turarunka da ta bata, sunda amfani sosai.


A cikin jirgin Auwal ko kallon Ummi baiyi ba, ga sit din sa ga anata, addu'ar shi 'daya ya isko Khadija shi bata mance da shi, Ummi duk'ar da kanta tayi tana kuka, ya zaman su da Auwal zai kasance?, ko zata bi shawara Gwaggo Maryam ta siyo mata k'ananen kaya, tayi kokari ta janyo hankalin Auwal gareta.


Anty Amina sosai ta damu, ta fahimci kamar Auwal din bai damu da Ummin ba, taga ko airport duk kukan da takeyi bai bi kanta ba, cikin ta taji ya motsa, cikin da kowa bai san da shi Abba Lawal bai san Anty Amina nada cikin ba.


Ummu Asma'u Sa'adatu)
08182654508
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*

Ummu Asma'u(Sa'adatu)


Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 55πŸŽ—56


Da safiyar jumma'a su Auwal suka sauka, taxi Auwal ya nema masu ta dauke su zuwa gida, hayar gida Alhaji Muhamud yasa aka daukar masu a wata unguwa, gidajen masu ban sha'awa, Ummi tun a k'ofar gidan, gidan ya birgeta, mai kula da gidan ya bude masu gidan.Babban falo ne da dakin bacci daya, kicin, toilet da back yard, anyi foolishing gidan, sosai tsarin yayiwa Ummi kyau, Auwal yaji haushin dakin bacci daya, yaso tanada dakin ta.


Ummi cikin dakin ta wuce ta ajiye kayanta, tayi arwala ta fara ramuwar salolin ta, Auwal ma wanka yayi ya fita, sosai yasan garin don nan yayi karatun dgree sa, yanzu consultant yake son zama, bangaren mata, fita yayi ya ha'da layin k'asar ya kira Baba Ladidi da Alhaji Muhamud, Baba Ladidi tace ya kira Anty Amina, ya ha'dawa Ummi layin ta rik'a magana da yanuwanta yace zaiyi.


Take away yayiwa Ummi bai shiga ba yaba mai kula da gidan ya bata yawuce, gidan su Khadija yaje, masu gadi ya isko suka ce masa sunyi tafiya Dubai jiya, Auwal ya tambayi dayan maigadin don ya sanshi, ya Khadija maigadin yace lafiya lau take sunyi tafiya in sun dawo zasu wuce Nigeria zaa yi aure Auwal yace wazai yi aure, Maigadin yace yaran gidan ne.


Auwal sosai gaban sa ya fa'di, an kira Maigadin yaso ya k'ara tambayar sa, haka ya wuce gida jiki sanyaye, wani layin ya siyawa Ummi yayi shopping kayan abinci, a hanya ya kira Anty Amina sun gaisa yace Ummi na gida zata kirata in ya koma, Anty Amina tayi masa godiya sosai tace ya rik'e Ummi amana in tayi ba dai-dai ya tsawata mata.


Auwal yayi shiru yana jinjina kirkin Anty Amina, gida ya wuce Ummi na zaune falo tana kallo ta k'ara gyara gidan tasa boner da turaren wuta, sai kamshi ke tashi, Auwal tun a harabar gidan ya fara jiyo kamshi, kamshin yayi masa, ciki ya wuce Ummi tayi masa sannu da zuwa yaron da ke kula da gidan ya fara shigowa da shopping din, Ummi ta dauki kayan kowane ta ajiye shi a muhalin da ya kamata a ajiye, wayar ta Auwal ya dauka ya ha'da mata layin ya kira Anty Amina, Ummi tayi tsale tace na gode yaya, Auwal kallon ta yayi ya wuce ciki.

Anty Amina ta k'ara jawa Ummi kunne ta kula da Auwal sosai, ta kyautata masa, kamin ya fita ta tabbata ta bashi abinci ya karya, Ummi tace zatayi hakan, Ummi bayan ta k'are kicin ta wuce, wasu kayan girkin sunzo da su daga gida, frid rice an chicken ta ha'da masa, sai kamshi ke tashi.


Auwal yana daki kwance abun duniya ya dameshi wa zaiyi aure gidan su Khadija kadai Khadijar shi ce, duk ya matsu gobe ya shiga makaranta yasan zai iya samun num ta hannun friends din ta, bayan ya dawo masallaci sallar isha'e, Ummi ta jera abinci kan table wanka ta shiga, sai da tayi sallar isha'e, ta zauna ta tsara k'waliyya sosai, zaune tayi tana tunanin kayan da zata saka, kayan da Gwaggo Maryam ta kawo mata ta dauko, Mini skirt ne, da three-quarter wando, sai body hug's, Ummi three-quarter wando ta dauko.


Red collar da Black top sosai suka amshi jikin ta, red hula tasa tayi kyau sosai, falon ta fito ta fara kallo, Auwal bayan ya sallami mai masu hidima, aikin sa iya yini ne, da sallama ya shigo falon, idon sa suka sauka kan Ummi, numfashin yaji yana fita ba dai-dai ba, tsaye yayi yana kallon ta, Ummi tashi tayi ta taka wajen da yake tsaye tace yaya sannu da zuwa.


Auwal da wata irin Murya yace sannu, Ummi tace yaya ga abinci a table, Auwal kamar Wawa ya bita suka zauna Ummi ta zuba mashi abinci, ci yakeyi yana satar kallon ta, Ummi dariya ma abun ya bata, bayan sun k'are ta kwashe kayan ta gyara table din, bacci take ji ta wuce daki, Auwal yana falo yana aiki kan system din shi.


Ummi wanka ta sake tasa night gown ta kwanta, Auwal koda yazo dakin Ummi tayi bacci, gefenta ya kwanta, da k'yar bacci ya dauke sa sai juyi yakeyi a gado, duk wani iri yakeji a jikin sa, to me kenan? Ummi tun asuba ta tashi, sai da ta gyara ko ina gidan ta wuce kicin abin Kari ta ha'da masa, bayan ta k'are tayi wanka, tana fitowa toilet Auwal ya tashi.

Ummi ta rusuna tace yaya barka da kwana, Auwal hannu ya 'daga mata ya wuce toilet, Ummi shiryawa tayi ta wuce falo, yau ma tight wando tasa da top Auwal ya fito cikin shiri tace ga abinci, ka'dan yaci duk sauri yake yi yake makaranta.


Bayan yaje department din su ya k'are duk wani cike cike

Please Login or Register in order to submit comment