You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fara neman abokanin Khadija, da Lisa suka hadu, cikin mamaki take kallon Auwal tace shine ko mafalkin takeyi, Auwal yayi dariya tace ina Khadija duk da halshen turanci suke magana, tace tayi tafiya, yace ta bashi num ta bashi tace masa Khadija zatayi aure, don ta sami labarin shima yayi aure.


Auwal cikin tashin hankali yace wazata aura, Lisa tace a Nigeria yake, Auwal cikin tashin hankali ya kira Khadija ta dauka, jin murya Auwal tace Auwal kai ne, Auwal yace abunda zakiyi min kenan Lisa tace zakiyi aure duk tsawon lokaci nan kina raina, Khadija cikin fushi tace kai ka fara auren naji labari ha kake son in zauna.


Auwal ya fa'da mata duk yanda akayi auren sa da Ummi, Khadija tace yayi hankuri Dubai din da sukaje kayan aure zasu siyo zata auri tobashin tane, Auwal cikin k'araji yace karya kike yi Khadija duk son da Nike maki, Khadija kashe wayar ta tayi, Auwal yayi ta kira baya samu.


Auwal cikin fushi ya wuce gida a falo ya sami Ummi ba sallama haka ya shiga falon Ummi tana gaishe shi ko kallon ta baiyi ya wuce daki, Ummi dakin ta bishi tana shiga tace ya, ya daka mata tsawa cikin fushi yace get out, duk kanki na rasa farinciki na, ina zama na aka dora min ke, Ummi hawaye ne suka fara zubo mata, cikin kuka ta fita dakin.

**** ****

Hashim da ya gaji da jira ya wuce gidan Hajiya Dada, yana zaune k'anin Mahaifin sa suka dawo, sun fa'dawa Hajiya Dada an daura aure, Hajiya Dada tace yafi da ya sauko masu Zaituni ita kanta tasan su Zaituni basu da tarbiya wani lokacin har fa'da takewa Hajiya Fatima.


Hashim kamar a mafalki yaji an daura masa aure da Zainab din sa, cikin mamaki yace Baba an daura suka mik'a masa goro, Hashim hawaye suka zubo masa, Hajiya Dada cikin mamaki tace Hashim mace kakewa kuka? Hashim tashi yayi ya wuce gidan Mumy, Hajiya Mairo na zaune Hashim ya shigo rungume Mumy yayi yana kuka.


Mumy dariya tayi tace Malan Bello ya kirani yayi min bayani, su Zara naji suka fara ihu suna jin da'din, Mumy ma murna tayi mata yawa, ko ba komai Hashim ya samu yarinya ta gari abun da yake so kuma, Zainab na daki tayi wanka don sunsha aikin bak'i, Maman Sadiya ta kirata tace Malan Bello keson magana da ita, bayan sun gaisa ya fa'da mata ya daura mata aure da Hashim, Zainab tayi shiru, yace zai rok'i Hajiya Mairo alfarma su barta tayi karatu yasan Tano son karatu, Zainab tayi farinciki damuwar ta karatun ta.


Ita batada zafi ko ba Hashim kowa zaa aura mata Indai zasu fita bala'in Baba Delu zata zauna, ta gode Allah bata tafa tunanin zata samu miji irin Hashim ba, Malan Bello yace zaizo Bauchi yana son ganin inda take Zainab murna ta shiga yi, bayan ta k'are wayar duk taji kunyar fitowa wajen su Mumy take ji, Hashim yayi kira tak'i dauka, Mumy ce da kanta ta haura sama Zainab naji Mumy ta bude, Malan Bello ya kira Mumy, Mumy ta sauki da Zainab lokacin Hashim ya wuce gefensa, Sam ya mance Azumi yake yi ko yanwa baji kan farinciki.


A falo ya samu Zaituni tasha kwalliya ga Amarya baice mata komai ya wuce dakin sa, wanka yayi ya shirya sai kamshi yake yi, falo ya fito yace ta shirya masa abun shan ruwa azumi yake yi, kan kujera ya kwanta, Zaituni shiru tayi tace kanta ke ciwo ya amso wajen Mumy Hashim cikin takaici yace jiya kince in baki hakkin ki inma nawa hakkin nakeson inada hakkni kiyi min girki, daman yasan komai bata iya ba, dariya yayi yace jakkar banza, wanan auren har ga Allah ba aure ne, mace tagama watsewa ba ma istibra'e a aura min ita.


Lokaci zaizo da zasu raba auren da kansu, in Zainab ta isheni rayuwa, murmushi yayi ya shafa kansa, Mumy ya kira yace Mumy Azumi nakeyi, Zaituni tace kanta ke ciyo, Mumy tace Allah ya sawak'a, Zainab tace taje ta dafawa mijin ta abun shan ruwa, Zainab na zaune kin tashi tayi duk kunya ta cika, Mumy murmushi tayi tace kaga 'diyar kwarai irin albarka, Mumy sama ta haura, Zainab ta wuce kicin.


Sai mamaki takeyi ina Amarya sa, abinci ta ha'da masa, tana cikin ha'da abincin Hajiya Fatima tayi sallama, sai zage zage take, tana tambayar Mumy, Mumy ta sauko, Hajiya Fatima tayi ta zuba mata masifa, ita zaa yi wulak'anci jiya a kawo yarinya yau a aura masa yar aiki ai anci baya tunda yar aiki ce, har takare Mumy bata ce mata komai ba.

Zainab na kicin tak'i fitowa, Zaituni ce ta shigo tana kuka don Hajiya Fatima ta kirata ta fa'da mata, Hajiya Fatima jan Zaituni tayi suka wuce gefen su, Hashim na kwance ta fado falon, shima masifa tayi ta masa komai baice ba, zata fita tace da in kukeyi, Hashim a ransa yace Allah ya fiki Gwaggo in garesa na dogara, Zainab ma nasan komi bazaki iya yi mata ba.


Hashim sai addu'ar yakeyi ta wuce da Zaituni gida a mamakin sa ta wuce Zaituni ta wuce daki Hashim tsuki yayi ya wuce gefen Mumy, cikin farin ciki, zai je yaga Zainab din sa.

**** ****


Amina cikin ta nata girma ba wanda ya lura doguwar mace Mara jiki tun kan su Ummi sai cikin ta ya tsufa yake fitowa, zaman su da Abba ba laifi yana kiranta, tun lokacin dai bai koma Misau ba, Anty Amina na yawan bashi shawara ya rik'a tashin dare ko kan matsalar yaran ya fahimci Farida shaye takeyi, ranar da ya fa'dawa Anty Amina kuka tayi sosai, duk tunanin Abba Maryam da Hafsa ne masu daman.


Fadila tayi daman shaye -shaye Hajiya Rabi nata murna sai Malamin duk aka kai mai Fadila zai shek'e ayar sa, wani rubutun yaba Hajiya Rabi a rik'a ba Fadila tunda ta fara shan rubutun cikin hankalinta yake tarawa da ita, mugun son Malamin take wani lokacin da kanta take zuwa.


Mamee tayi biyar Farida tak'i zuwa sosai Mamee ta damu, su Khalifa shiru anyi shige shige ba labari Mamee hawan jini ya kama, ko yaushe cikin shan magani take, Abban ma yanzu ba wani jin tsoron ta yakeyi kamar da ba, Maryam wani lokacin sai taji kamar motsi a marata ganin batajin ciwon komai ta share, tayi ta neman num Zero bata samu, da ta bincika ace ya wuce London yin masters.


Hajiya Rabi ranar da taji su Auwal sun wuce har kuka tayi duk kudin da ta kashe sunje a banza wajen Malamin ta koma yace zai masu turen bak'aken aljanunu kudi sosai ta bashi na aikin.

**** ****

Baba Delu na kwana tayi mafalkin matar nan cikin tsoro ta tashi, hankalinta ya tashi matar bazata barta ba, Abu abin baa cewa komai ya zama rik'aken Dan daudu, komai na daudu ya iya, sallah sai anga dama,Malan Bello abun ya dame sa duk inda ya wuce yara har ce masa sukeyi Baban Yar Abu.


Baba Delu bata zuwa taron biki sai an nunata, Magaji karatun yake yi lafiya lau, matsalar sa bauta Baba Delu.

Ummu Asma'u Sa'adatu

08182654508
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*

Ummu Asma'u( Sa'adatu)

Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 57πŸŽ—58


Abun duniya duk ya damu Baba Delu ba damar tayi bacci zatayi mafalkin matar na bibiyar ta, in ta fita waje yara su fara kiranta Uwar yar Abu, sosai ta shiga damuwa, daddare Baba Delu na bacci tayi mafalkin matar nan tazo, ta bude fuskar ta, cikin mamaki taga Baba Jummai ce Mahaifiyar su Zainab, Baba Delu cikin tsananin firgita ta falka tana ihu, Malan Bello ya falka yace lafiya? Baba Delu ta tsorata sosai ta kasa cewa komai.


Malan Bello sai tambayar yake yi lafiya? Baba Delu jikin ta rawa dai yake yi, Malan Bello kwanciya yayi abun sa ya k'yale ta, har gari ya waye Baba Delu bata koma bacci ba, sosai ta shiga damuwa me kenan Baba Jummai ke bibiyar ta, kar dai maganar Malamin da yace in tana da hannu cikin mutuwar ta bazata huta ba.


Magaji na aikin sa Baba Delu ta fito, yana gaishe ta bata amsa batayi masa bala'en da ta saba yayi mamaki sosai, aikin sa ya k'are ya wuce makaranta, Baba Delu na zaune tasaka kunun koko gaba ta kasa sha, Abu ne ya shiga, ko kallon ta baiyi ya wuce daki, bincike ya fara yi mata yana neman kudi, duk ya yamutse dakin baiga kudin ba, cikin takaici ya fito waje.


Baba Delu kallon sa tayi tace me kake nema? baka damu da halin da inke ciki ba, ka shigo kana neman abun da baka ajiye ba, Abu harara Baba Delu yayi yace kar ki dame in,tun shigowata gidan kinga na kulaki, meyasa kike da sa Ido, in ba Magaji ne ba, da kike zaluntar su, damuwa matsalar kice, ko HAK'K'I su Magaji ai dole ki shiga damuwa, duk garin nan maganar irin zalunci da kike masu ake yi, muguwa yayi tsuki ya wuce Baba Delu ido ta bude tana mamakin Abu ne? ko iska ne ya hau kansa.


Hawaye masu zafi suka zubo masa, 'daga kan da zatayi taga Babar su Magaji tsaye da fararen kaya, cikin wani irin ihu Baba Delu tayi waje, gidan su Maman Sadiya ta fa'da , Maman Sadiya cikin mamaki tace Babar Abu lafiya kike? Baba Delu ta kasa magana jikin ta sai rawa yakeyi da Maman Sadiya ta matsa tace aljanunu ta gani, Maman Sadiya tayi dariya tace muje, da k'yar Baba Delu ta yarda zataje, koda sukaje ba komai.


Baba Delu zauren gidan ta zauna kamar taf'afa bata iya zama gidan ita daya, da ta shiga sai taga Inna Jummai tsaye, har Magaji ya dawo, lokacin ta shiga gidan Magaji aikin sa yayi ya shirya zuwa Islamiya, Baba Delu ma shiryawa tayi ta fita, bata iya zama ita daya, Magaji sai mamaki yakeyi meke damun ta, yau ba masifa.


Baba Delu na tafiya taga Inna Jummai na biyar ta, da gudu ta zuba, mutane sai
kallon ta suke yi, gudu takeyi tana ganin Inna Jummai, ranar haka ta koma kamar mahaukaciya, yara sai biyar ta suke yi.

**** ****


Abinci sosai Zainab ta ha'da Hashim, kan table ta jera ta wuce sama, ana magrib Hashim ya shigo gefen Mumy, ba kowa falon zama yayi yasha ruwa,yana cin abincin Mumy ta sauko, zama tayi, tacewa Hashim duk abun da Gwaggo sa Mahaifiyar Zaituni zatayi yayi hankuri, Hashim yace zaiyi yadda tace, ta gyara zama tace maganar Zainab, zata cigaba da karatu anan sai ta k'are secondary bazata bika ba, Hashim cikin tashin hankali yake kallon Mumy.


Mumy tace eh, nayiwa Mahaifin ta alkawalin zatayi karatu, yanzun tunda tanada kokari zaayi jumping dinta tayi SS3 tayi exams in yaso sai ta bika Madina taci gaba da karatun ta, kabar Zainab har gaba, banason muyi abunda zamu cutar da ita, Hashim yace ba komai Mumy, Mumy tace kaje da Zaituni mana, in ina son ta shiryu sanadin ka, Hashim shiru yayi meye amfani zuwanta yasan ruwan zafi bazata iya dora masa ba.


Mumy kamar ta fahimce shi, tace kaje da ita, dole zatayi maka girki ai, Hashim shiru yayi bayason yiwa Mahaifiyar sa garddama, Mumy tace zataje wajen Hajiya Dada ta aiko kiranta, shiryawa sukayi suka fita dasu Zara, Zainab taso zuwa Hashim yace bazataje ba, Mumy tace ta tsaya, tacewa Hashim Ummina yar amana ce, Hashim sunkuyar da kansa yayi, duk yaji kunya.


Hashim zama yayi yace Zainab tazo ta zauna, nesa dashi ta zauna, tashi yayi ya zauna kusa gareta, Zainab jikinta sai rawa yakeyi, ranar farko da ta zauna kusa ga namiji, Hashim jayo ta yayi ya kwantar da ita jikin shi, Zainab tana ta kok'arin kwancewa ta kasa, Hashim a kunne ya ra'da mata in mijinki ne, Zainab duk'ar da kanta tayi duk kunya ta cika ta.

Hashim zauna da ita yayi ya koma dayan kujera, don ya lura akwai kurciya da rashin Sabo, bayason matsa mata yafi son su saba, kallon ta yayi yace dazun nayi magana da Magaji, Zainab tace Allah yaya, murmushi yayi yace Allah Addar Magaji, Zainab tayi dariya, Hashim yace Zainab ta d'ago tana kallon sa, yace Mumy ta fa'da maki an daura mana aure tayi shiru yace ko Malan ya fa'da maki tace eh.


Malan yana nufin Baban su Zainab, Hashim yace yanzun me kikeso, Zainab cikin sauri tace yaya karatu nakeso, Hashim yayi murmushi yace zakiyi karatu Zainab, Mumy tace anan zaa barki ki k'are secondary, Zainab cikin jin da'di tace eh, Hashim sosai yaji farinciki, zai tsaya mata karatun tunda tana so, fira sosai sukayi, Zainab naji motar su Mumy ta gudu sama.


Hashim ya fito yayi masu sai da safe ya wuce gefen su, a falo ya samu Zaituni kwance tasha matsatun kaya, baice komai ya wuce dakin sa, yana tunanin yanda zai zauna da wanan karuwar a Madina, zaije da ita zaiyi maganin ta don cen baa iya shege, dole zata zauna waje daya.


Yana dakin ta shigo, Hashim ko kallon ta baiyi yace ta bada passport din zaa yi visa wani satin zasu wuce, Zaituni da'di sosai taji ta zata da Zainab zaije, wanka yayi ya kwanta, Zaituni taje dakin ta, koda ta dawo ya rufe kofa, tayi ta bugawa yak'i budewa.



Da safe Hashim wanka yayi ya wuce gefen Mumy ya karya, su Zainab sun wuce school, Zaituni ba kunya tazo gaida Mumy tace Mumy yunwa nakeji, Hashim zaiyi magana Mumy tace ga abinci a table, zama tayi taci sosai, Hashim haushi yaji ya fita, wajen neman visa Zaituni.


Cikin sati aka samu visa suka shirya zasu wuce, ranar da zasu wuce Hashim a daki ya samu Zainab, rungumeta yayi jikin sa, yace bazai Jima zai dawo tayi karatu, ya bar komai na Magaji hanun Muktar da Baban Sadiya, Mumy ma zata rik'a aika masa, duk abun da takeso ta fa'dawa Mumy kar taji kunya, Zainab tace to, Hashim ya riko hannun ta har waje Zaituni sai harara su takeyi, Mumy wayayar mace yi tayi kamar bata gan su ba.


Ta kano suka tashi, Zaituni sun sha zuwa saudiya ko waje bata wani damu ba, a jirgi ita da Hashim kowa harkasa yake yi, bayan sun sauka wani friend din Hashim ya dauke su airport, Balarabe ne Mansur sai kallon Zaituni yakeyi, yana mamaki, duk da Hashim din ya fa'da masa yanda aka yi aure.



Unguwar su daya da Mansur, gida Mansur ya ajiye su, yaje ya kawo masu abinci, a falo suka zauna suna labari da Hashim cikin halshen larabci, Zaituni abinci taci ta wuce daki bacci ta hau ba sallah ba sallati.Bayan Masur ya wuce Hashim yazo ya tasheta, yasan batayi sallah ba, fita yayi yayi recharge layinsa ya kira Mumy, sun gaisa ya kira Zainab, suna sha fira Zainab sai dariya takeyi.


Tun zuwan su Zaituni Madina bata da aiki sai bacci, abinci sai take away, ranar Hashim yace dole ta girka ta dora abinci bacci ya dauke ta, yana shigowa gidan yaji k'auri da sauri ya wuce kicin ya kashe gas din, a daki ya sameta tana bacci, tsaye yayi cikin takaici yace wanan baccin bana lafiya ne ba, dole yakai ta asibiti a binciketa, ko baccin meye Zaituni? friend dinsa ya kira likita ne ya fa'da masa, yace ya kawo ta ayi mata test, zaa gane me ke sakata yawan baccin, Hashim da yammah yace Zaituni ta shirya su fita, jallabiya ya ajiye mata.


Yace matan nan garin shigar su kenan tana tunzurin baki ta shirya suka fito, hospital din suka wuce Zaituni komai bata Fahimta don duk rubutun larabci ne, sai da suka je office din Dr ya rubuta test har biyar lab suka wuce sai lokacin Zaituni ta fahimci abunda kenan cikin masifa tace ciyon me ke gare ta da zaa yi mata test, Hashim gudun ta tara masa mutane yace Medical certificate zaa basu, zaiyi tafiya ne, Zaituni tace yanzu naji zance, ta yarda aka dibi jininta.


**** ****


Ranar Jumma'a Abba ya shirya zuwa Misau, Mamee na zaune dakinta ya sameta yace zaije gida, cikin mamaki tace lafiya ko ana wani abun ne, kallon ta yayi sakarce yace sai akwai wani abun zan je gida,bani da wasu iyalin cen ne, hutu na zai fara zai yuyu inyi sati biyu ko daya cen, Mamee cikin mamaki take kallon Abba Lawal, ita yau Abba ke fa'dawa haka.


Abba kudi ya ajiye mata ya wuce don duk ATM din sa dake hannun ta ya amsa, Abba zai fita dakin Farida ta shigo, a buge take abun ta, tana tafiya kamar zata bangaji Abba Lawal, Abba cikin tsananin bak'in ciki, ya fara fada yana zagin ta, yace saukin abun ba kudai ke gare in ba, Mamee najin haka ta taso masa daman taji ciwon yanda yace zai tafi Misau din, Abba Lawal tsawa ya daka mata.


Cikin fushi yace kar ki maidani sakarai, duk waya bata yaran bake ba, ke yar bariki, ai ga bariki nan kina gani, komai yara sukayi kice baa matsawa yaranki, kar ki mance ba naki dai ke gare in ba, ya wuce abun sa.


Mamee kuka ta fashe da shi cikin tsananin tashin hankali meke faruwa, Hafsat ce ta fado dakin da gudu tace Mamee tazo Maryam ta fa'di bata motsi cikin tashin hankali ta wuce dakin su, daukar Maryam sukayi da masu aiki, asibiti suka wuce emergency, Abba Lawal Mamee ta kira kamar kar ya dauka ganin kiran yayi yawa ya dauka.



Ta fa'da masa suna asibiti, Abba Lawal na isowa asibiti likitan ya fito yace ina mijinta, Abba Lawal cikin mamaki yace miji? ga Mahaifin ta, likita yace ya biyo sa office.


Auwal gidan su Khadija ya koma cikin sa'a ya samu sun dawo, Mamanta tace a shigo da shi cikin gidan, bayan sun gaisa tayi masa bayani Khadija zatayi aure sati biyu masu zuwa, yay hankuri Khadija tayi mata bayanin abun da kenen, Auwal yace ba komai sallama yayi masu, zuciyarsa cike da damuwa ya fito gidan, Khadija ta rako sa har waje suka yi sallama.


Auwal gefen hanya yayi parking wasu hawaye masu zafi yaji sun zubo masa, yaso Khadija kamar ransa, ya hank'ura Allah yasa haka ya zame masa alhairi zai je gida ya koya ma kansa son Ummi, gida Auwal ya wuce abun mamaki ya nemi Ummi gidan bai ganta ba, cikin tashin hankali ya tambayi yaron dake masu hidima yace yaga ta fita da jikkar kayanta, Auwal cikin masifa yace ka bari meye amfani ka? wallahi duk Matata ta bace sai na kasheka, Auwal cikin tashin hankali ya fita neman Ummi.



Ummu Asma'u( Sa'adatu)

08182654508
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*

πŸ–ŠUmmu Asma'u (Sa'adatu)

Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 59πŸŽ—60


*Kuyi min uziri da typing errors*πŸ™

Auwal yayi neman Ummi har yammah bai ganta ba, duk Unguwar ya zagaye bai ganta ba, kuka ya zauna yanayi da hawayen sa, tabbas ya zama butulu, duk hallarcin da yarinyar nan tayi masa butulcin fa zai mata kenen, yasa duk abun da ya samu yarinyar mutane, Abban sa bazai yafe masa ba, Gwaggo Ladidi ma bazata yafe masa, kuka yakeyi sosai, Herry yaron da ke masu hidima ma hankalin sa ya tashi, da ya sani bazai barta ta fita ba.


Kiran Alhaji Muhamud ne ya shigo wayar Auwal yakasa daukar wayar Abban don bai san me zai ce masa ba, text ne ya shigo na Alhaji Muhamud, yana fa'da masa, an samarwa Ummi admission anan University dayake sun bata medicine, zata fara kamin certificate din ta na SSCE ya fito, Auwal kuka ya k'ara fashewa ya shiga ukku, karshe Abban yace zaizo jibi ya gansu ya k'are komai na makarantar Ummin, Auwal zama ya yi yana kuka.


Har dare ba Ummi, dole Auwal yace yayi reporting wajen police, passport din Ummi sukace ya kawo, sai lokacin ya tuna gidan suka je passport din nan inda ya ajiye police din sun tabbata mai bata fita county bazai yuyu ta fita ba passport ba, CCV CAMERA din Unguwar aka diba ba inda ta fito, Auwal tsaye yayi to ina Ummi ta tafi, yan sanda sun bashi shawara ya koma Unguwar ya diba, zasu tafi da photon zaa saka wanted duk wanda ya ganta.

Auwal gida ya koma, tun safe rabon sa da abinci yunwar ma bayaji, wani irin son Ummi da tausayinta yakeji a ransa, yasan so dai ne yakewa Khadija but Ummin sa tafi ta komai ga k'urciya, kwance yayi tsakiyar falon yana kuka, me zai cewa Anty Amina, yasan Ummi, Mubina suna farinciki, yaci amanar Anty Amina, ta rok'e sa ya rik'e mata amana ya kasa, wata irin k'ara Auwal yayi ya zube k'asa, Herry cikin tashin hankali ya isa falon, don Herry ya kira Maman sa tace ya tsaya tare da Auwal din har aga Ummin.


Herry Emergency line ya kira cikin mintuna suka iso gidan, taimakon gaggawa suka fara ba Auwal, likita aka kira yace damuwa ce, bayan minti talatin Auwal ya farfado, Ummi yake kira ta dawo wallahi yana sonta, Herry sosai ya tausayawa Auwal, Auwal tashi yayi suka k'ara fita Unguwar basu ga Ummi ba har dare ya fara yi,bayan sun dawo Auwal ya wuce bayan gidan, inda keda suke suke, kamar nishi yaji, cikin sauri ya wuce, Ummi ce kwance tayi ammai sai nishi take yi.


Auwal k'ara yayi yana kiran Ummi, Herry da sauri ya iso wajen, Auwal duk ya rude, Herry ne yace masa su kaita hospital din dake bayan layin, cikin tashin hankali Auwal ya dauke ta, sai surutai yakeyi wallahi Ummi ina sonki, Ummi ko motsi lokacin batayi, da sauri aka wuce da ita Emergency Auwal sai kuka yakeyi kamar mace, shi ya mance likita ne,Dr ne ya fito yace damuwa da yunwa ne suka bugeta lokaci daya, an saka mata drip zuwa gobe zata dawo dai-dai, Auwal sallama Herry yayi yace yaje gida, Herry yace zai tsaya gidan su sai gobe in sun dawo.


Auwal rik'e yake da hannun Ummi kamar zaa k'wace masa, runtse bai runtsa ba, sai kusan biyar nasafe ta falka, Auwal ta Kalla ta dauke kanta, Auwal yayi mata sannu tayi shiru komai bata ce ba, nurse ce ta kawo masu abinci, nurse din ce taba Ummi, Ummi taci sosai don yunwa takeji wani irin haushin Auwal take ji, yaci amanar su, duk hallarcin da suka yi masa.


Dr yazo ya diba Ummi yace suna iya tafiya gida, Auwal ma jininsa ya auna yace ya hau ya kula da cin abinci ya rage damuwa, gida suka wuce har lokacin Ummi bata ce komai ba, Herry ya gyara gidan sosai, Ummi boner tasa turare ta shiga wanka, tana fitowa Alhaji Muhamud ya kirata yace Auwal ya fa'da an samu admission dinta, Ummi tace eh, godiya tayi sosai, Ummi murna ta shiga yi, zata tsaya tayi karatu in ta k'are zata rabu da Auwal don baya sonta.


Bayan ta shirya Auwal ya shigo wanka yayi ya shirya, kusa ga Ummi ya zauna, ya rik'e hannun ta, yace Khadija kiyi hankuri ki yafe min wallahi ina sonki, Ummi kauda kanta tayi tun da ya fara magana idon ta ke cika da hawaye, tasan zai yuyu bai samu Khadijan shi bane ya dawo mata, taso Auwal tun ranar farko da ta ganshi, yanzun tsanar sa ce kwance cikin ranta.


Auwal yayi Ummi tak'i cewa komai, yace ta tashi suje makaranta, tashi tayi ta dora abaya sama, Auwal sai kallon ta yake tayi kyau sosai, yana son rugumar ta yana jin tsoro, shi yanzun ma shakkar ta yayi.



School sukaje yayi printing admission letter da duk documents din Alhaji Muhamud ya turo masa, aka bude mata file, gefe daya suke da hospital din da Auwal ke consultancy services din sa, Auwal cikin ya wuce, duk ya ha'du da friends dinsa zaiyi introducing Ummi as his wife, Ummi duk takaici ya cika ta.


Office dinsa ya kai ta, yace sunada operation zai tafi, har ya juya Ummi batayi magana ba, dawowa yayi yace Khadija na, bazakiyi min addu'ar samun nasara ba, Ummi tsuki tayi ciki-ciki, Auwal yayi murmushi yace Khadija in kikewa tsaki, rungumeta yayi ta baya ajiyar zuciya ya sauke, ya juya ya wuce.


Bayan ya fita, Ummi ta kira Anty Amina cikin murna take fa'dawa Anty, Abban Auwal ya nema mata admission yanzu haka tana cikin makaranta, Ummi tace Anty medicine aka bani, Anty a England zanyi karatu, sai kuka Anty dariya tasa

Please Login or Register in order to submit comment