You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yardar, sun ajeye zasu bi wata hanyar har Mamee nacewa wanan yakin Hajiya ba naki ne ke daya ba.




Bayan Mamee ta koma gida tun a get take jin haniya da sauri ta wuce gidan, Khalifa ne da Farida suke ta fa'da yace ta ara masa mota tace bazata bada duk ya lalata nashi wajen shaye-shayen sa, shine suka fara fada yan aikin suyi rabasu sunk'i, Mamee jiki na rawa ta shiga gidan, Mamee sai da tayi masu kuka suka bari duk sun farfasa wasu kayan Falon Khalifa cikin kwayarsa yake duk abun ya dauko jefawa Farida yake yi, Mamee zaune tayi tana kuka.




Matsalar yaran ya fara damun ta Sam basa jin maganar ta, Abba ne suke dan tsoro duk cikin su Hafsat ce kejin maganar ta, ita ce k'arama su. Mamee ta mance Allah bayason zaluncin, ta mance Hakki bibiya yake yi, ranar Mamee kwana tayi tunanin duk abun dauniya ya dameta, tsoron ta in ba Anty Amina ce keyiwa yaran asiri ba.






Maryam sammako sukayi zuwa Abuja, sai da tayiwa Zero alk'awalin zasu rik'a zuwa gidan sa ko hotel suka rabu bayan ya bata maganin da ya siyo na hana daukar ciki, tasha ya tafi da sauran sai sun k'ara haduwa, nesa da gidan ya ajiyeta ta hau taxi zuwa gida, Maryam hankali kwance ta shiga gidan, Mamee da su Farida ihu sukeyi Maryam ta dawo, Mamee ba fa'da ba komai, damuwar ta Maryam ta dawo ta dawon ko ina kikaje bata tambaye ta ba.




Ranar Abba Lawal ya dawo komai bai cewa Maryam ba na barin gidan ko tashen maganar, Mamee murna tayi sosai ta kira Hajjo tana fa'da mata, Hajjo tayi dariya tace ki kwantar da hankalin ki, aikin da ake maki babba ne.




An ajiye bayan sati daya zaa kai Fatima, a kano zaa ajiye ta, zasu zauna tare da Baba Ladidi, Anty Amina cikin kwana biyu har rama tayi, sosai ta damu da halin da Ummin zata shiga tsoron ta daya kar Auwal din ya samu lafiya yak'i Ummin, yanzun ma batasan wane irin zama zasu yi ba, duk yanda taso magana da Abba bata samu daman hakan ba tun safe ya wuce Abuja, kudin cefanan su ma dan Lami yaba ya bata, ta rasa me Abba Lawal ya maida ta, tun zaman da sukayi da su Anty Maryam bai k'ara ce mata komai ba.




Komai na siyayen da zaa yiwa Ummin, ya Maryam tayi masa magana yace a Abuja zaa siya karshe tasan Mamee zai ba, hawaye ne masu zafi suka zubowa Anty Amina yaushe kukan ta zai k'are? da anan misau ya aurada Ummin hankalinta zaifi kwanciya, Ummi ce ta shigo dakin Anty Amina kallon Anty tayi ganin kamar kuka take yi, Ummi zama tayi gefen Anty ta rik'e hannun ta.




Cikin damuwa tace Anty ki kwantar da hankalin ki duk abun da kika ga ya samu Bawa tun farko mukaddarine daga Allah, tashin hankalin ki shine damuwata, nayi imani da wanan kaddara, Anty Amina Ido ta zubowa Ummin hankalinta da tunanin ta sun fi karfin shekarun ta, Anty Amina sosai taji natsuwa a ranta.




Ta kalli Ummi tace Abbanku yace wani satin zaa kai ki kano, Ummi tace ba komai Anty, kinga ko cen zan cigaba da zuwa makarantar shine damuwa karatun, har islamiya zan cigaba Abba yace, Anty murmushi tayi tace komai kikeso Alhaji Muhamud zai baki, Ummi murmushi tayi tace Anty kizo ana firm mai kyau a arewa dole Anty ta fito Falon.




Ummi dakin su ta wuce, ta shiga toilet hawaye suka zubo mata, ko kadan bata son ganin Mahaifiyarsu cikin damuwa shine take boye nata damuwar, farin cikin Mahaifiyarsu shine farinciki ta, tasan irin wulak'ancin da Mahaifiyarsu ke gani, in ta bar Mahaifiyarsu cikin damuwa abun zai mata yawa, shine take boye nata damuwar wanan wane irin aure ne? Wanke fuskar ta tayi ta fito, kwalli tasa ta fito falo, tana cewa Mubina me akayi a firm din, Anty kallo ta bita dashi kamar ta fahimci damuwa a fuskar Ummi sai Ummin ta kama tsokanar Mubina, suna ta dariya suna wasa.





Magaji har ya Saba da wahalar Baba Delu, tun asuba in ya tashi zai fara aiki, in lokacin makaranta yayi ya wuce in ya dawo yaci gaba, wanki har na Abu yi yake yi, Malan Bello abun na damun shi baya iya magana, ko Zainab tun da ta tafi bai k'ara kiran ko sunen taba an debe masa ita cikin rai, duk abun da ya samo Babe Delu zai kawowa, tanemi magani da saura, sauran a kashewa Abu ko ya sace




Abu sata ko b'eran masallaci albarka sata sai in bai gani ba, in yace uwar ta bashi abu in tak'i yayi ta zagi yana jifar ta, Maman Sadiya suna taimaka Magaji sosai, Baba Delu taje wajen Malamin da take zuwa ta fa'da masa Abu sata yake yi, tana sane shi keyi ta lak'awa Magaji, yace zai mata aiki kan Abu, tace tana son ay aiki kan Magaji ance yanada k'okari makarantar su, tana son aikin da komai aka koya masa bazai gane ba, yace taje bayan kwana biyu ta dawo, gida ta wuce, bata tunanin HAK'K'IN marayun Allah da take daukawa kan ta, ba tunanin mutuwa ba tunanin kwanciyar kabari.



Ummu Asma'u Sa'adatu)

08182654508
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*

Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.

*Bismillahirahamanirrahim*


*Page* 37πŸŽ—38



Bayan kwana biyu Delu ta koma wajen Malamin ta, rubutu ya bata yace tasaka masa a abinci duk yaci batare da yayi bismillah ba duk abun da aka koya masa ko aka fa'da masa zai mance shi, bazai gane komai ba, Baba Delu tayi murna sosai, wajen yawon dillancin ta, ta wuce, ta zuba rubutun a k'arama gora gudun kar ya zube tasa jikka.





Tana tafe tana murnar gurin ta, zai cika zata tarwatsa zuri'ar Jummai, Uwar Audu ta kira tace ya Zainab, Uwar Audu tace kar ta damu tanen wajen siyar da abinci a bakin titi, taga ma kwanan bata da aiki sai wasa da maza, Delu tayi shewa tace kice cikin shege yazo kenan, da kinga tayi ciki turo ta gida, kowa yaga shegiya da cikin shege, Uwar Audu tace ba damuwa zata dawo da ita in tayi cikin, Baba Delu tace wata fa ya fara tafiya da an biya kudin aiki ina jira, Uwar Audu tayi dariya tace Delu naira da an biya zaki ganin.




Bayan sunyi Salam Uwar Audu shiru tayi tana mamakin Delu duk bala'in ta bazata iya mugun abun da Delu keyi ba, wanan wane irin bak'in zalunci ne haka, bata ma tunanin HAK'K'IN yaranan ta kashe masu Mahaifiyarsu duk bai isheta ba, zata sha mamaki in taga Zainab gaba, bak'ar muguwa.




Sai kusan magarib Baba Delu ta koma gida, Magaji duk ya k'are mata aikin ta ya dafa abinci, Abu tun safe da ya fita bai dawo ba, Malan Bello baya gida, sobo ta siyo a hanya ta juye rubutun ciki, duk kok'arin Magaji bata gani ba, haushi ma taji da ta same sa zaune, abincin ka'dan ta bashi, ta bashi goran sobon da ta zuba rubutun amsa yayi yace ya gode, zama yayi ya fara cin abincin, Baba Delu sai kallon sa takeyi duk ta matsue ya sha zobon, tsoronta kar yayi bismillah, aikin ta zai lalace

**** ****



Zainab tun da tayi sallah bata koma ba bacci ba, k'asa ta sauko ta fara share -share da goge-goge, tsab ta gyara gidan, dakunan bacci take jiran su tashi ta gyara, kicin ta wuce jin sallamar Larai mai aiki, masar da suka ha'da suka fara suyawa Larai sosai ta iya abinci, tana koyawa Zainab duk da Zainab din ta dan iya, wanda Baba Delu ke sata, da lokacin Mahaifiyarsu na nan tana koya mata.




Koda Mumy ta fito sun k'are masar har an jera a table Zainab ta gyara kicin din, Larai ma ta gyara kicin din waje inda ake sa itace, sun wanke komai tas Zainab ta gaida Mumy ta wuce sama ta gyara dakin Mumy, su Zara sun tashi sun gyara nasu don Mumy ta hana Zainab gyara masu, wanka duk sukayi suka sauko k'asa zasu karya, Hashim ma ya fito yayi wanka ya shirya cikin kaftan na boyel dark blue, yayi kyau sosai.




Zainab ma tayi wanka ta shirya cikin riga da siket na atamfa kayan su Zara da Mumy ta bata, tayi k'waliyya ta dai-dai, duk tayi wanka batayi k'waliyya ba, Mumy fa'da take yi mata, tace mace yar k'waliyya ce, Mumy da shekarunan ko yaushe tsab take, saukowa tayi k'asa, zata wuce kicin ganin Hashim wajen ta matsa tace yaya Hashim barka da kwana.




Bai juyo ba yace barka kade, Zainab ta wuce kicin tafi son zama tare da Larai, bayan sun k'are cin abinci, Zainab tacewa Larai tana son Magana da Magaji tana jin nauyin Mumy, Larai tace kiyi mata magana Hajiya batada matsala, Zainab Falon ta wuce da tunanin Hashim ya tashi, zaune ta same sa yana kallon Al-Jazira, Mumy tace zo nan Ummina akwai magana a bakin ki.




Zainab murmushi tayi tace Mumy,Mumy tace Magaji Zainab tace 'daga kai, Hashim na sauraren su, zakayi tunanin kallo yakeyi hankalin sa na kan su, yarinya ta samu waje sai sagarci takeyi, waye Magaji kuma? tsuki yayi har ya fito, Zainab kallon sa tayi suka ha'da ido harara ta yayi.




Zainab taji haushi kamar ta rama ta kauda kanta, Mumy ta kira Maman Sadiya, ta aika a kira Magaji, Zainab tana jin Murya Magaji tayi ajiyar zuciya, Magaji kuka yasa ya fa'da mata dukan da Baba Delu tayi masa ta lak'a masa sata Zainab kuka Magaji kuka, Hashim sai mamaki yakeyi, me take ma kuka haka? Mumy ta fara fa'dan in don ta rik'a tada hankalin Magaji baza k'ara kira mata shi ba.




Zainab ta share hawaye, ta rarashi Magaji, ta fara basa labarin ban dariya sai gasu suna ta dariya, tace ya rik'a addu'a sosai komai zaiyi yayi addu'a yace yanayi, sunyi sallama cike da kewar juna bayan sun k'are Zainab ta fa'da Mumy abun da Magaji ya fa'da mata Mumy tace ta kwantar da hankalin komai yayi farko karshen sa na zuwa, Hashim sosai yaji tausayin Magaji, yaji yana son sanin labarin Magajin.




**** ****




Tun lokacin Maryam duk ta fita makaranta zasu hadu da Zero, su shak'e ayar su son rai ta dawo gida, karatu basuda Matsala suna ba malamai kudi, wanda yak'i yarda su nemi wani hanyar duk abun da Maryam ke ciki Mamee bata gane ba, in sun fita gida sai kusan magarib duk da sunan Makaranta.




Farida tana shan kwaya a boye, ba ruwan ta da maza, a watsa kwaya aje party, Khalifa abun nasa ya girma ba karatu sai shaye -shaye tun Abba bai gane ba har ya gane, wani abokin Khalifa G dog nick name dinsa ainihin sunan Marwan Baban sa senator ne, abokin Abba Lawal ne tare aka kai su waje karatu, tare aka kore su makaranta, Baban yaron yace zai mayar dashi waje a cenza masa 'country' yaron yacewa Mahaifin zai tsaya yayi karatu.





Senator Buba ya kira Abba Lawal ya fa'di masa zai mayar da Marwan UK ya cigaba da karatun sa, cen farko Malaysia aka kai su, Abba Lawal yace zaiyi shawara da Mamee, bayan ya koma gida ya fa'dawa Mamee sosai taji da'di tace gara a kaisu cen ko zasu tsaya suyi karatun, Abba Lawal yace zai k'ara dubawa don hankalin sa bai kwanta da UK nan ba, in suka kama mutun da laifi ba ruwan su hukunci suke yi bisa dokar k'asar su, Mamee tace ba komai da zai faru, haka Abba ya fara nemawa Khaifa visa.




Khaifa sosai yaji da'di, Marwan yacewa Khalifa su rage abun da sukeyi har su fita, cen suyi rayuwar su ba takurawa, Khaifa yaje ya aske sumar da ya bari ya nemo jallabiya yana sakawa Mamee sai murna takeyi, Khalifa n ta ya fara natsuwa.





Abba ya bawa Mamee kudi yace tayiwa Ummi siyaye kayan kici zuwa kayan daki, Hajiya Rabi ta kira, Hajiya Rabi tace ta siyawa mata kayan gefen hanya, gadaje biyu da set din kujeru biyu ta siya duk na road side a photo ta nunawa Abba Lawal tace kayan Dubai ne yace sunyi kyau, kayan kici duk na china ta siya mata.




Ko rabin kudin da ya bata bata kashe ba, duk abun da ake ciki, Anty Amina bata sani ba, ya Maryam da tayiwa Abba magana cewa yayi baya son shishigi, ranar ya Maryam har kuka tayi, komai Mamee da Hajiya Rabi keyi, Hajiya Rabi kudin Lefe da Alhaji Muhamud ya bata duk k'ananen kaya ta siya, wacen lefen yace a barwa Maryam, dariya suka tayi ko ba komai sun k'unsawa Anty da danginta bak'in ciki, ba tunanin HAK'K'IN ko ka'dan.




Anty duk juriyar ta, sosai ta rame har saura kwana biyu a kai Ummi batasan komai ake shiryawa ba, abun yazo ba shiri, bata tunanin auren Ummi yanzun, sauk'in yayun ta sun ha'da mata kudi sosai ya Maryam tace a bari aga abun da su Mameen sukayi don tasan komai ita zatayi.


Ummu Asma'u Sa'adatu

08182654508.
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE 😭😭
*NEMESIS*


Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.


*Bismillahirahamanirrahim*


*Page* 39πŸŽ—40



Sai saura kwana daya, akai Amarya Ummi kano Abba Lawal ya zo misau, su ya Maryam Gwaggonin Amarya duk sunzo misau, ya Maryam ta fa'da Umman su yanda sukayi da Abba zancen kayan da aka siyawa Ummi, Umman tace ba laifi don yaba Mamee tayi siyayar, ya Maryam shiru tayi tana jijina lamarin a ranta Umman bata ganin laifin Mamee ko meyasa?





Anty Amina tun zuwan Abba gaisa dai sukayi ya fita, sai dare ya shigo gidan, idan yazo misau mutane na cika gidan sosai, gefen sa ta same sa ya k'are cin abincin yana kallon news, tana shiga ya ha'de fuska, yace ya gaji bacci yake ji, Anty baki bude take kallon sa, Abun da Anty Amina bata sani ba an cirewa Abba sha'awar ta cikin ransa, baya son ganin ta har ita har yaran ta, cikin aikin da Hajjo kakar Mamee tayi kenan.




Anty Amina zaune ta kasa tashi, sai mamaki takeyi tun da aka daura auren Ummi ya koma Abuja ko a waya bai kira ta ba, yanzun, ya saurareta yak'i yana fa'din yagaji, tashi yayi ya wuce bedroom din sa, yana tafiya yana fa'di mata gobe karfe bakwai na safe zaa wuce da Ummi, har ya shige dakin Anty bata motsa da inda take ba, ta dade zaune, ta tashi ta kwashe kayan da yaci abinci ta wuce gefen ta, kicin ta ajiye kayan ta wuce dakin ta, duk bak'in da suka zo a Babbangida suka sauka.




Kayan Ummi da take shiryawa ta cigaba da shirya mata, lefe Abba yace a bari in taje cen a bata kar yawon yayi yawa, ya Maryam tayi mata sababin dinkuna a kano, Anty Amina tana ha'da kayan tana kuka, su Ummi suna gidan Dan iya cen aka yi wankin Amarya, aka yi sai walima gidan Chiroma, Mamee bata zo tace wa Abba bata jin dadin jikinta.




Bayan ta k'are ha'da kayan arwala tayi ta fara sallah a sujadar karshe ta rok'i Allah ya kawo mata saukin halin da take ciki, auren na Ummi Allah yasa ya zame mata alhairi, fitinar dake cikin sa Allah ya nisantar da ita, ta dade tana addu'o, a kan sallaya bacci ya dauke ta.




Da safe su ya Maryam suka kawo Ummi wajen Anty, fita sukayi dakin, Anty tayiwa Ummi nasiha sosai, tace ta rik'e addu'a Allah ya zai tsare ta, Ummi kuka takeyi sosai, Abba ma yayi mata nasiha, suka wuce kano, tare zasuje da Mubina zatayi sati wajen Ummi, bayan sun wuce Abba ya wuce Abuja.




Anty Amina sosai ta damu, duk da ya Maryam ta kwantar mata da hankali zata Kula da Ummi suna gari daya, tasan Baba Ladidi ma zata Kula da ita, Baba Ladidi ta kira Anty Amina, Anty tace mata suna hanya sun taso, Baba Ladidi tace ta kwantar da hankalin zasu rik'e Ummi tamkar yar su, insha Allahu ko Auwal ya samu lafiya zai rik'e Ummi amana Anty Amina godiya tayi sosai, Baba Ladidi tace zata kirata in sun iso.




Anty Amina sosai taji natsuwa, sai bayan azahar suka isa kano, gidan cike da dangin Alhaji Muhamud, sun tarbi su ya Maryam sosai abinci kala-kala ya Maryam ce rik'e da Ummi suka wuce gefen da aka gyara mata, nan gefen da Baba Ladidi ke zama da aka gyara masu, daki ukku ne da falo kichi da store, Baba Ladidi daki daya, daki biyu da Falo aka gyarawa Ummi, ya Maryam taji haushin kayan da Mamee ta siyawa Ummi, tasan kudi sosai Abba ya bata.




Baba Ladidi tace ba komai, ba kayan daki ne aure ba, fata Allah yaba Auwal Lafiya su fahimci juna, Mubina da Fatima yarinyar ya Maryam aka bari wajen Ummi sauran mutanen suka wuce gidan ya Maryam, duk hayaniyar da akeyi Auwal na gefen Alhaji Muhamud ya na bacci, allurorin da ake masa bacci suke sawa, likitan yace duk yana samun bacci sosai tunaninsa zai iya dawowa.



Sai bayan sallar isha'e Alhaji Muhamud ya shigo gidan lokacin Auwal ya tashi, gefen Maryam suka shiga Baba Ladidi ta kira su Maryam su gaida Alhaji Muhamud, har k'asa suka zube suna gaishe shi sosai ya yaba tarbiyar yaran sai jansu yake da fira, Auwal na gefe yana kallon su, Baba Ladidi ta nuna masa Ummi tace ga matar ka nan zata zauna damu, murmushi yayi yace zatayi wasa dani Baba Ladidi tace sosai, tashi yayi yaje ya zauna kusa ga Ummi yana mata murmushi.




Ummi ma murmushi tayi, Alhaji Muhamud yayi da'di sosai, Baba Ladidi hawayen suka zubo mata ta share, tana addu'ar Allah ya ba Auwal Lafiya, jan Ummi Auwal yayi dole ta tashi suka je wajen kayan wasan sa, yace suyi wasa, duk kayan ya fitar suka fara ha'da gida irin na wasan yara, Mubina da Fatima na tayasu, abin gwanin tausayi, cikiken likita ya koma kamar yaro Dan shekara bakwai.




Mamee gurin ta ya cika an samu visa su Khalifa sun wuce Uk, su Maryam da Farida suna best university in twon, ba abun da Mamee keso irin yaran ta su sami abun da ba kowane yaro ke samu ba, tafison ace nata yafi na kowa, ko yanzun ta nunawa duniya ita da Anty Amina ba daya ne ba, Abba Lawal mijin tane ita daya, su Mubina da Ummi bisa kaddara suka zo duniya, yanda ta mayar da uwarsu abin kwatance haka zata mayar da yaran.



Tagama da Ummi saura Mubina, ta godewa Allah auren Maryam da Auwal baiyi ba sai yanzun ta yarda da maganar Hajjo kakar ta, don tun farko Hajjo tace kar ta yarda Maryam ta auri mahaukaci, Mamee tayi nisa duniya ce gaban ido rufe Sam bata tsoron ranar da HAK'K'IN Anty Amina da yaran ta zai waiwaye ta.




Maryam duk suka k'are watsewar su da Zero sai ya bata maganin hana daukar ciki tasha Maryam tayi nisa sosai ko Zero bai nemeta zata neme shi, in tayi masa maganar suyi aure sai yace ta bari su k'are makaranta saura ka'dan su k'are, su Khalifa tun da suka je Uk ba wani karatu shek'e ayar su dai suke yi, shaye -shaye abin har yafi da, cen suka hadu da wani bature ya fara koya masu neman maza yan uwan su, a biyasu ayi lalata da su, idanun suka k'ara budewa.


**** ****


Hashim sosai maganar Magaji ta tsaya masa a rai, bayan su Zainab su wuce Islamiya yake tambayar Mumy waye Magaji, Mumy ta kwashe duk labarin Zainab da k'anin ta Magaji ta fa'da masa, Hashim yayi shiru yana jinjina rashin imanin Delu abun kamar a firm, anya mutane na tsoron HAK'K'IN wanda aka zallunta.




Hashim yacewa Mumy shima zai bada nasa guduwa wajen taimakawa marayun Allah, zai tafi har jama'are ya diba Magaji Mumy taji da'di sosai tace ita ma zataje, Hashim yace Mumy Mahaifin su fa? Mumy tace a yanda Maman Sadiya ke fada mata Mahaifin nasu matarsa tayi masa asiri sosai yanda takeso haka akeyi, Hashim yayi shiru yana tunanin tabbas wasu Matan basa da imani, ya kuddurta a ransa zai tsayawa rayuwar Magaji.



Magaji sai da yayi bismillah ya fara cin abincin, Baba Delu sai murna takeyi jin bata ji yace bismillahi ba, hankali kwance yasha zobon sa, Baba Delu tace yaje ya huta yayi aiki ya gaji, Magaji sai mamaki yake yi, tsakar dare Baba Delu na bacci tayi mafalkin wata mata da faren kaya ta rufe fuskar ta, tana ta bibiyar ta duk inda taje, cikin tsanin firgita ta falka.



Ummu Asma'u (Sa'adatu)

08182654508
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*


Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama.


*Bismillahirahamanirrahim*


*Page* 41πŸŽ—42


Tun daga ranar da Baba Delu tayi mafalkin mata da fararen kaya ta rufe fuskar ta, tana bibiyar ta, duk lokacin da ta kwanta bacci zatayi mafalki mata, haka zatayi ta gudu matar na biyar ta, tayi ta kuwa, koda zata falka tayi zufa har muryar ta ta shak'e duk kuwar da zatayi ko Malan Bello da suke kwanciya waje daya baya jin ta, sosai abun ya dameta har bata son dare yayi .






Dole ta fa'dawa Malan Bello yace ta rik'a addu'a in zata kwanta bacci, addu'ar ba wani iyawa tayi ba zamanta ne da Malan Bello yake dan koya mata yayi ta koma Islamiya tak'i, haka ta cigaba da ganin matar, ranar taje wajen bokan da take zuwa,wasu yan layu ya bata yace tasa a daki, tayi yanda t
yace abun baiyi ba, wata dillaliya da suke dillancin tare ta fa'dawa matar tace taje wajen wani Malamin limamin masallaci ne yanada sanin addinin sosai.




Tare suka je, Baba Delu tayi masa duk bayani tun ranar da ta fara mafalkin matar, Malamin yayi shiru yana nazari, bayan ta k'are masa bayani, yace irin haka tana faru in kanada HAK'K'IN aka mutuwar wani, wanan mutun din zai rik'a damunka yana bibiyarka, wasu mutanen in sun mutuwa wayyanda Allah yaba zasu iya zo ma wani a mafalki su ida sak'o, wasu in kana HAK'K'IN aka wani Abu da ya same su, to zaka rik'a ganin su a mafalki.




Wani ko in baka yi masa addu'a zaka rik'a yawan mafalki kin sa, Baba Delu sai zare ido takeyi kar dai Jummai ce Babar su Magaji ke bibiyar ta, cikin tashin hankali tace Malan in banida HAK'K'IN kowa a kai na, yace taje ta yawaita addu'a zata daina ganin ko meye ne, Baba Delu ta tashi jiki sanyaye suka fita, bayan sun rabu da dillaliyar gidan bokan da take zuwa ta wuce, ta fa'da masa yanda sukayi da Malamin yace taje bayan kwana biyu ta dawo aiki sosai zaa yi mata, zata bar ganin ta.




Bayan ta koma gida ta samu Magaji har ya k'are aikin sa yana zaune yana home work din da aka bashi, fada ta fara yi masa, ya zauna bai k'are mata aikin ta, Magaji yace duk aikin da kika bari nayi Baba, cikin jin haushi ta wuce cikin daki, Abu ne ya shigo gidan, daure da dank'walin lace saman kansa, ya daura zanen atamfa ya zuk'e k'ugu da wani zane Magaji cike da mamaki yake kallon Abu.



Me kenen? Wanan shigar ta yan daudu ce, Abu sai harara Magaji yake yi, k'afafun Abu Magaji ya kalla sanye da takalmin mata, Magaji karatun sa ya cigaba da yayi, Baba Delu na fitowa taga Abu yana tafiya yana karkace k'ugu wai shi mace cikin tsoro take kallon Abu tace Abu *Dan Daudu* ka koma na shiga ukku in Delu, Magaji tashi yayi ya wuce dakin su, yace ba dole ya zama dan daudu ko yaushe yana tasha cikin yan daudu.




Uwar Audu ce tayi sallama, Baba Delu ta amsa jiki sanyaye, Uwar Audu tace dillaliya Delu Manya mata, Delu tayi murmushi wanda iya fuskar ta, Uwar Audu tace wai lafiyar ki, Delu tace da dama ta fa'da mata Abu ya zama dan daudu, Uwar Audu tace Ashsha, sai addu'a kudin Zainab na wata da Hajiya Mairo ta aiko ta bata, dubu goma ne, Hajiya Mairo ta dibewa Zainab dubu hudu ta bada dubu shidda.




Baba Delu taji da'di sosai duk da bata jin da'din rayuwar ta, Uwar Audu tace zata wuce ayi ta addu'a, Delu

Please Login or Register in order to submit comment