You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata, tace godiya zakiyiwa Allah ba kuka zakiyi, ki kira Abba Muhamud din da Abbanku, Ummi tace to Anty ina Mubina ki fa'da mata Ummin ta a waje zatayi karatu.


Bayan sunyi sallama, Anty Amina hawayen farinciki taji sun zubo mata, godiya sosai tayiwa Allah, ta kalli cikin ta da ya fara fitowa, wanan cikin tayi mamaki ya fito ba kamar sauran da sai in zata haihu suke fitowa ba.

**** ****


Abba Lawal zaune office din likita yaba jiran bayanin Dr, likitan ya nisa yace Alhaji yarinyar ka tana dauke da ciki na wattani biyar, Abba Ido ya zubowa Likitan, Likitan yaci gaba da fadin babba matsalar tana dauke da cutar HIV shine yasa ta suma, Abba k'ara yayi ya fa'di k'asa, Mamee dake tsaye bakin k'ofar ta zube k'asa, likitan ihu yakeyi yana kira nurses, drip suka daura masu dukkan su.


Abba Lawal sai da aka saka masa oxygen don numfashin daukewa ya fara yi, likitan cikin tashin hankali ya diba calls din Abba, da Anty Amina sukayi waya karshe, likitan ya kirata ya fa'da ma, Anty cikin tashin hankali tace zasu zo, Chiroma ta kira da Dan iya, kano suka wuce ya Maryam na jiransu a jirgi suka isa Abuja.


Koda sukaje Mamee ta farfado, sai dai ta samu strok, barin jikin ta daya ya daina aiki, Abba Lawal dai ne abun sai a hankali numfashin sa yak'i komawa dai -dai, su Chiroma hankalin su ya tashi sosai, Anty Amina da ya Maryam kuka sukeyi, Chiroma Dan iya dasu Anty likitan ya kira yace suyiwa Abba Lawal addu'a in numfashin ya koma dai-dai suna San ran bazai samu strok kamar matar sa ba.


Jinin sa ya fara sauka, shine ma sauk'i, Chiroma yace Dr meye dalilin lokaci daya suka samu wanan matsalar, likitan sai lokacin ya tuna da Maryam, allura bacci sukayi mata, nan ya fa'da masu matsalar Maryam, duk dauriyar maza sai da su Chiroma sukayi kuka, wanan bala'in yayiwa Abba Lawal yawa, Chiroma cikin damuwa yace ba abun dake wahala da Balkisu da yaranta sai HAK'K'I Amina.


Wajen Maryam sukaje ta falka batasan Mike faruwa ga, ganin su Chiroma tasan akwai matsala, Dr ne ya shigo yace Abba ya falka da sauri suka wuce Abba na kuka da hawaye, Chiroma fa'da ya fara yi masa, yana fadin bambamci musulmai da kafiri yarda da kaddara, wannan yana cikin kaddara ka rok'i ya baka ikon cinye wanan jarrabawa, Abba tashi yayi yace gida zaitafi, likitan yace ya bari har gobe yace gida zaije, gidan suka wuce, suka bar Mamee da Hafsa na kula da ita, Mamee baki ya juye bata iya magana sai hawaye ke zuba.


Hafsa ma kuka sosai takeyi, don uwa na uwa ce amman tasan Mamee bata kaico abun da ta kulla ne take girbewa yanzun wa gari ya waya, Anty Amina an wayi gari gata cikin Abuja tare da Abba har ciki gashi jikin ta, Mamee kuwa a gadon asibiti duk yara sun lalace mata.


Anty Amina Maryam ta jayo don likitan ya sallame ta yace zata rik'a zuwa karfa magana kamin lokacin haihuwar ta, Abba yana ganin Maryam ya kauda kan sa, gida suka wuce Abba yak'i shiga mota daya da Maryam, Anty daki daya aka gyara mata, sosai take kula da Maryam su Chiroma sun zaunar da Maryam ta fa'di ko yi mata ciki tace Zero ne.



Bayan kwana biyu su Chiroma suka wuce Anty Amina ce tsaye kan komai gidan duk safiya sai taje gurin Mamee kakar tazo da Misau, ranar da aka sallami Mamee ta dawo gida, a ranar Abba ya tara Mamee da Maryam, Farida, yace Anty Amina tazo, Mamee cikin wheelchair ake turata.



Abba ya dibi Anty Amina yace Amina ina neman afuwarki ga duk abun da nayi maki wanda na sani da wanda ban sani ba, idon Abba na zubar da hawaye, Anty tace ta yafe masa bai mata komai ba, Abba yace nasan Amina HAK'K'I kine da yaranki ke bibiyar mu ki yafe min na fifita Balki kan ki, na fifita yaran Balki kan naki, Anty tace ta yafe masa, Mamee sai kuka takeyi tana son magana bata iyawa.


Abba Lawal ya kalli Maryam da cikin ya fito yace ban sa uwayena kuka ba, ku kun sani kuje gaku ga duniya,nayi iya kokari na wajen baku tarbiya kun watse tarbiyar da nayi maku, ko yaushe Mahaifiyar ku na nuna maku bariki yau ga karshen bariki nan, wanan ta kwaso cikin har da HIV, wanan tazama yar k'waya, Khalifa nacen wata uwa duniya an yanke masa shekaru ashirin da biyar gidan yari, Abba tari ya fara yi sai da Anty Amina ta rik'e shi.


Sai lokacin ya lura da cikinta da har ya fito, hawaye ne suka zubo masa, rik'e Anty yayi yana kuka yana fadin ki yafe min Amina, Mamee ma kuka takeyi sosai bata iya magana, Abba kallon su yayi yace yanzun zai yanke hukuncin da yake ganin zaiji saukin wanan bala'in da yake ciki.


Maryam tunda taji maganar HIV numshi ya fara yi ba dai-dai duk basu lura ba, ganin dai sukayi ta zube k'asa, kanta sukayi aka kasheta zuwa asibiti, sosai numfashin keyi sama yayi k'asa, Anty Amina kuka takeyi sosai, Abba Lawal kwantawa yayi kan kujera yana sallati.


Farida fira tayi sosai jikinta ke rawa k'waya takeson sha babu, wani saurayinta ta kira yace tazo ga wata mai zafin an samu cen ta wuce jikinta sai rawa yake yi, Allah ka tsare mana zuri'ar mu.

**** ****


Hashim Dr ya kira ya bashi results din Zaituni ciki ne wata ukku ke gareta, Hashim tsoro da tashin hankali suka shige shi, yayi bak'in cikin tarawa da Zaituni likitan yace yayi masa HIV anyi masa negative gida suka koma komai bai cewa Zaituni ba.



Sai da gari ya waye yace ta shirya zasu tafi Nigeria tayi biyarsa yace ba komai, a kano suka sauka, ya dauki mota suka wuce Bauchi har k'ofar gidan su ya ajiye ta ya bata result din cikinta yace daman ba aure tsananin mu, don baa aure da ciki, like na sake ki, Zaituni ihu ta k'urma da gudu tayi cikin gidan.


Hashim gidan su ya wuce, Mumy na falon k'asa tana kallo, Zainab na sama tayi wanka tayi k'waliyya har su Zara nayi mata tsiya k'waliyya me takeyi mijinta bayan nan tace masu taji a jikin ta Hashim zaizo, dariya suka sa mata sukace bata da lafiya Hashim dake wata uwa duniya, sallatin da Mumy keyi ne suka sako k'asa Hashim din suke kallo cike da mamaki, korasu yayi ya fa'dawa Mumy abunda yasa ya dawo, Mumy results din ta amsa din coppy biyu aka yi masa, Mumy hawaye ne suka zubo mata.


Cikin takaici tace Hajiya Fatima ko HAK'K'I mijinta da dangin sa bazai barta ba, mutane suna hallaka kansu kan duniya yanzu wa gari ya waya, ta tsare daga ita sai yaranta, mijin ta sai abunda tace yake yi, yanzun riba me taci, wanan abun kunyar har ina, in Hajiya Dada ma nake Jima kar jininta ya hau.


Hashim yacewa Mumy zaije ayiwa Zainab passport wanan k'aro tare zasu je, Mumy shiru tayi, fita sukayi har su Zara suka wuce wajen yiwa Zainab passport.

**** ****

Magaji yanzun baida matsala da Baba Delu don abun nata ya koma kamar tafin hankali, bata ma na Magaji zai gyara gidan yayi abinci, Malan Bello ma yanzun baya shakkar Baba Delu, akwai lokacin da ta tashi tana kuwa da dare, marin ta yayi tace tayi masa shiru jahillar banza.


Dole ta kwanta tayi, bacci ya dauke tayi mafalkin Baba Jummai tace taje ta fa'dawa mutane ita ta kashe zata bar bibiyar ta, Baba Delu kika ta tashi tanayi da gari yawaye Magaji ya wuce Makaranta, Malan Bello ya fita, Baba Delu na cikin gida taga Inna Jummai da gudu ta fito, daga ita sai daurin kirji.



Tana ta kuwa, Malan Bello aka kira, yana zuwa yasa aka daure ta, asibiti aka wuce da ita don ta fa'di tajimu a kafa, asibiti sukace a wuce da ita asibiti mahaukata case din su ne, Baba Delu sai dariya takeyi tana cewa in na kashe Jummai, mutane wasu suna ganin hauka ce, wasu suna cewa zata iya HAK'K'I NE, Abu na gidan Magajiyar karuwai, Magaji ya same shi yace yazo Baba bata da lafiya, Abu ya kallesa yace kai bakasan ciwon kanka duk zaluncin da muguwar matan tayi maku, wallahi ba inda zanje.


Magaji cikin takaici ya wuce, Abu tashi yayi ya fara taka rawar bori da keyi.


Hajiya Rabi jininta ya hau sosai Fadila bata da lafiya, Alhaji Muhamud sai shirin zuwa wajen su Auwal yake yi, abun duniya ya dameta, yanzu tsoron Alhaji Muhamud takeyi, don har cewa yayi in ta matsa zai sake ta.


Asibiti suka wuce da Fadila bugun farko tana dauke da ciki, liver ta samu matsala shaye -shaye da tayi Hajiya Rabi faduwa tayi tana kuka sosai.


Ummu Asma'u Sa'adatu)

08182654508
[5/5, 4:06 PM] Nabila Lady: 😭😭HAK'K'I NE😭😭
*NEMESIS*

🖊Ummu Asma'u Sa'adatu)

Sadaukarwa Ga Mahaifana Allah yayi maku Rahama

*Bismillahirahamanirrahim*

*Page* 61🎗62



*LAST PAGE*



Hajiya Rabi ta tashi ta shak'o wuyan Fadila tace don ubanki waye yayi maki ciki? Likita ne da Alhaji Muhamud suka shigo dakin, Alhaji Muhamud cikin tsananin mamaki yace kasheta zaki yi, Hajiya Rabi sai tambayar Fadila take nace waye yayi maki ciki, Fadila cikin azaba ciwo da shak'ar da akayi mata, tace Mumy Malamin da kike kaini wajen shi, shi yayi min ciki, duk lokacin da yace zaiyi min aiki tarawa yake yi dani.


Mumy kinci amanar mu, ki bata mana rayuwa duk halin da muka shiga kece sanadin haka, kin haife mu, baki bamu tarbiyar kwarai ba, kinyi wa Mahaifin mu asiri, ya Auwal kinyi kok'arin kashe shi Allah bai baki iko ba, Mumy bazamu yafe maki bata mana rayuwa da kikayi ba har Lailah, wani irin tari Fadila tayi, jinin ya fito cikin hancin ta.


Cikin jin jiki ta cigaba Mumy HAK'K'I Dady da ya Auwal ma bazai barki ba, kiyiwa Daddy asiri kinyiwa ya Auwal, Fadila ta maido kallon ta ga Alhaji Muhamud cikin jin jiki tace Daddy ka yafe mana, kar kayi muna baki ba abun da ke wahala da mu sai HAK'K'IN mutanen da Mumy ta zalunta, Mumy azzaluma ce, duk rayuwar ta akan zalunci ta ginata, ka yafe min Abba nasan tawa ta k'are.


Alhaji Muhamud matsowa yayi wajen gadon yana karantawa Fadila Kalmar Shahada, saboda ya lura tayi nisa jini ke fitowa ta hancin ta, yana karanta yana zubar da hawaye, har Fadila ta cika ga hannun sa,gawar ta ya amsa ya kira dangin sa, kano ya wuce da ita cikin ambulance don Abuja ta fita ransa, Hajiya Rabi suma tayi a asibiti ya barta ya wuce.


Bayan ta dawo hayacin ta suka wuce da driver sai dare ta isa, koda taje an rufe Fadila, ranar da akayi sadakan ukku ranar ya tara dukkan yan uwansa bai boye masu komai, Baba Ladidi tace ita batayi mamaki ba, fiye da haka Hajiya Rabi zatayi.


Alhaji Muhamud gaban yan uwansa yace ya saki Hajiya Rabi saki ukku, ko lafira baya addu'ar Allah ya ha'da su, Hajiya kuka ta fashe dashi, excort dinsa ya kira yace suje da ita Abuja ta kwashe kayanta, motar sa ko daya kar ta dauka, haka suka saka Hajiya Rabi suka wuce, cikin motar prinson ta daukar b'arayi, Allah ka rabamu da zalunci, sunyi *MUGUN ZALUNCI* sun ga abun su, Hajiya Rabi haukacewa tayi karshe, ko yaushe tana baki bola tana tsice tsince.

Baba Ladidi ta kira Auwal komai ta kwashe ta fa'da masa, Auwal kuka sosai yayi yace Allah ya saka masa ta zalunce shi, Auwal ya fa'dawa Baba Ladidi halin da yake ciki da Ummi, Baba Ladidi fa'da sosai tayi masa, tace zata kira Ummi.


Ummi na makarantar call din Baba Ladidi ya shigo sun gaisa, Baba Ladidi tace tayi hankuri ta yafewa Auwal Ummi tace ya wuce,nan Baba Ladidi ta fa'da mata rasuwar Fadila Ummi sosai abun ya tafa ta, sun kira Alhaji Muhamud sunyi masa gaisuwa.


Bayan sun koma gida, Auwal yaje daki Ummi na zaune ya duk'a a guwayun sa yace Khadija ki yafe min wallahi ina sonki, Ummi shiru tayi yace ki yafe min, Ummi tace Allah ya yafe mana.


Auwal tsalle yayi ya rumgumo Ummi, sunne kanta tayi a kirjin shi, ranar tare sukayi girki, bayan sun k'are suka fita shopping, sai magrib suka dawo, bayan sallar isha'e suna kwane falo, Auwal yace suje su kwanta, daukar Ummi yayi kamar baby suka wuce daki tun a hanya kidin ya cenza, Arwala sukayi sukayi sallah, inajin Ummi na kiran Anty na fito waje.


Zama ne na Fahimta tsananin Ummi da Auwal, sosai Auwal ke son Ummi, tun tana dari dari har ta sake, soyayya sosai, duk zasu je makaranta tare, Auwal shekara daya zaiyi ya k'are, yace zaiyi aiki dasu kamin Ummi ta k'are, Ummi ya saka driven school ta koyi mota, in kaga Ummi baza ce ita ce ba.


**** ****

Koda su Anty Amina suka isa asibiti Maryam bata da rayuwa, Anty Amina ta kasa kiran Abba su Chiroma ta kira Chiroma ranar sai da jinin sa ya hau, Umman Abba Lawal kuka tasa, tana tsinewa Mamee da yi mata Allah ya isa.


Abba da aka fa'da masa Maryam ta rasu baiyi kuka, sallati ya fara yi yana kiran sunan Allah, andawo da gawan Maryam zaa yi mata sutura, an shirya Maryam zaa fita aka shigo da Farida ba alamun rayuwa, wasu suka yadata a mota, Abba faduwa yayi jinisa ya k'ara hawa


Duk asibiti aka wuce dasu, Farida anyi lalata da ita har kasanta na fitar da jini, kwayar da tasha tayi mata karfi, saurayinta da ya bata k'waya shi da abokanin sa sukayi lalata da ita, Farida coma ta shiga, numfashin nan amman ko motsi batayi.


Kwana biyu asibiti Farida ta cika, Abba ranar kuka yayi sosai, bayan an dawo rufe Farida ya samu Mamee a daki tana kuka, tana sonyi magana ba baki, Abba yace ya saketa saki biyu, Mamee faduwa tayi k'asa Abba ko juyowa baiyi ya fita dakin su Hajjo ne suka fito neman masu taimaka masu ranar asibiti ta kwana da cen yace su wuce da ita Misau.


Hafsa tak'i binsu tace wajen Anty Amina zata zauna, Anty Amina cikinta ya tsufa, duk sun tataro kayan su sun dawo Abuja, Mubina da Hafsa aka sasu makaranta daya. Bayan wata daya Anty Amina ta tashi da nak'uda Abba sosai hankalin sa ya tashi, kar ya rasa matarsa, tsoro yake ji tun mutuwar su Farida ganin yakeyi kowa aka kai asibiti mutuwa zaiyi, likitan yace ayi mata CS don dadewar da tayi bata haihu ba, CS aka yi ma aka cire tagwaye duk maza,jajir dasu.


Ranar suna duk zuri'ar Dan iya da Chiroma ta sauka Abuja, yara suka ci sunan Dan Iya da Chiroma Misau, Muhmmadu da Abubukar, shureim da sudesss, anyi shagali sosai naira tayi kuka.

Anty Amina ta zama babba mace juya naira takeyi son ranta, yaranta nata girma abin su,sosai Abba ya sawa Hafsa Ido gudun matsala, Anty Amina ko yaushe ce masa takeyi yayi ta addu'a Allah ke shiryawa.

**** ****


Malan Bello asibitin mahaukata yaje suzo su dauki Baba Delu, sun daure ta aka fito da ita, duk mutanen layin sun taru sai kallon ta suke, sai fadin takeyi in na kashe Jummai, cikin yan gidan mahaukata ke tambayar waye Jummai, Malan Bello yace matarsa ce Margayiya.


Zaunar da Baba Delu suka ga duk yan unguwa mai unguwa ma yazo, sukace ta fa'di abun da tayiwa Jummai nan ta kwashe duk abun da ya faru na maganin da ta bata har ta mutu ta fa'di da duk asirin da tayiwa Malan Bello, Magaji na gefe zaune yana Vedio, Hashim ya siya masa Babar waya, mutanen shiya sai dauka suke yi.


Malan Bello yana kuka da hawaye yace ya saki Delu saki ukku, nan Malaman asibiti suka ce lafiyar ta lau depression ne, yanzu kotu shari'ar musulunci zaa kaita ayanke mata hukuncin dai-dai laifin ta, daman duk wanda ya kashe a kashe shi, maiunguwa yayi masu godiya yace zasu kira police suzo su tsare kamin a kai ta kotu.


An kira yansandan kamin suzo, mutane suka ga Baba Delu na wani irin k'ugi, tana shure shure, an nade mata k'afafun an juye hannu, limamin Unguwar aka kira yace shairin shaidanun aljannu ne, suke haka, kamin yakai ga yi mata addu'a tayi mik'a ta cika, yace sun shanye mata jini.



Nan yakewa mutane bayanin, dogara ga Allah yafi, yanzun gashi aljan sun shanye mata jini zai yuyu wani alkawalin tayi bata cika ba, daman duk inada mugun Abu yake cen shaidani aljannu suke basa zama sai cikin k'azamta kamar bola ko hanyar ruwa masu k'azamta, mutane duk watsewar su sukayi.


Malan Bello ma yace ba ruwan sa ya sake ta, Jan Magaji yayi suka yi gida, Abu da aka fa'da masa yazo da yan Daudu suka dauke Baba Delu suka yi mata sallah suka rufe ta, sallar dai anyi don basu San yanda ake yi ba, Allah kasa mufi karfin zukatan mu.


Hajiya Mairo ta kira Malan Bello ta fa'da masa Hashim yazo zai wuce da matarsa, dan Malan Bello ya fa'da mata abun da ya faru, tace zata kira sa, Hashim ta fa'dawa, yace Mumy me zai hana Malan din ya dawo nan ya zauna nan tunda wasu yan uwansa ana Bauchi suke Mumy tace inma tunanin da nayi kenen.



Hashim yace gidan sa dake tudun Wada, ya bashi kyauta, cikin gadon Mahaifin sa, Mumy tace ka kyauta, daman yan hayan sun fita ana gyara, daki biyu ne da falo, sai kicin, ko wanan daki akwai toilet,kaga Magaji sai ya dawo nan da karatu.


Mumy ta kira Malan Bello yace anyi haka tace ba komai, tace ya siyarda gidansa ko yasa haya yace zai saisuwan yafi daman yayi ritaya sai ya fara kasuwanci, Zainab ya kira Zainab da kukan ta, tace Abba Abu fa, yace kuyi masa addu'ar shiryawa in ya shiryu zai neme mu.


Sai da suka koma Bauchi su Magaji da Mahaifin su, Zainab suka wuce Madina, Zainab tace batason bikin komai bidi'ace don Mumy taso ayi biki kamun su wuce.


Hajiya Fatima mijinta har sakinta yayi kan cikin Zaituni da k'yar ya mayar da ita, sai da ya k'ara aure wata bazauriya, Zaituni ta haihu baby bai zo da rai ba.


*BAYAN SHEKARU GOMA*


A wata babba asibiti, Auwal ne da Ummi keta famar aiki, Ummi har takai matsatun consultant da yara ukku masu ban sha'awa, asibitin hadin gwuiwa Alhaji Muhamud da Abba Lawal, babba asibiti ce sosai, anyiwa Hafsa aure tana aiki bank da yaranta da maigidanta duk a nan Abuja.


Anty Amina twins sun girma har sunje college, Mubina ma Medicine take karantawa tana shekara karshe, Abba bayada magana sai Anty Amina, Uk sun aikowa Abba yazo Khaifa ba lafiya Abba yaje da kwana ya rasu cen aka rufesa, Mamee Balki yau ciyo gobe lafiya ita bata mutu ita bata rayuwa, Hajjo tsufa ya kama bata iya kula da ita sosai, Uwa uwa ce Hafsa ke biya ana jinyar ta.


Wani lokaci su Anty Amina sunje Misau sukaje diba Mamee don duk fa'dan da Abba keyi Anty zuwa take yi, Mamee na gani su shuirem ta fashe da kuka kamar su daya da Khalifa, har kasa suka duka suna gayar da Mamee, kuka takeyi sosai gashi bata iya magana, yaran sun birgeta ga tarbiya.


Hashim da Zainab sunada yara biyu, Hashim ya samu kudi sosai, sai dai su shigo Nigeria su fita, Magaji ya koma Madina wajen su, Malan Bello yayi aure wata yar Uwar Mumyn su Hashim, kasuwancin sa yake yi sosai suna zumunci sosai da su Baban Sadiya, Abu an neme shi an rasa wasu suce ya mutu wasu suce ya gudu.


Baba Ladidi gidan su Auwal ta koma Abuja, Alhaji Muhamud ya auri wata datijjuwa sosai take kula da yaran Ummi rabin zaman su duk gidan kakani ne.


*Kyakyawan Hadisin Manzon Allah SAW) Hadisi na ashirin da hudu arba'u Hadisi, Allah yace ya haramta zalunci a kansa, yace ya ku bayuna kada kuyi zalunci, Allah yace zai yafewa mutun komai girman laifin da kayi masa bazai yafe ma laifin da kayiwa wani ba, in har ba wanda kayiwa laifin yace ya yafe ma ba, HAK'K'IN wani babban Abu ne Allah ya nisantar da mu ga HAKKIN wani*


*Alhamdulilahi*

*Allah na gode maka daka nunamin karshen wanan littafinmai suna HAK'K'I NE, kurakuren da nayi Allah ka yafe mani, ina mik'a godiya ga Ummu Asma'u novels, Nabeety Lady novels, Fahimta novels Zuwairat novels, Kainuwa fans, sai mun hadu a Sabon littafina, MUGUN ZALUNCI Allah ya bamu alhairi dake cikin watanan na Ramadan da zamu shiga, Allah yasaka mu cikin yantatun bayun sa*

Ummu Asma'u Sa'adatu)

08182654508

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment