You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng [5/21, 13:03] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


*Bissimillahir Rahmanir Rahim....*
_Dasunan Allah mai Rahama mai jink'ai nake farawa_
_Ina mik'a d'umbin godiyata ga d'aukacin masoyana Na yanda suka nunan soyayyarsu gareni akan novel d'in_ *ZAMAN MARINA* _naji dad'i sosai har ckn raina Allah yasa wannan ma yasamu karb'uwa agareku ya fad'akar daku ya nishad'antar daku_
_haka wannan littafin shima k'irkirarsa nayi bawai satar fasahaba inwata taga yai kama da labarinta to arashine_



~pg 1....~


Da safiyar Allah ta,ala kukan jaririyar yakad'e bayan asibitin Na Khadija clinic a gindin wata bishiyar mangwaro wata matashir mace ce azaune da jariri a nad'e ahannunta tana jijjigata tana goge hawayen idonta akwai damuwa atattare da ita

Ta dire jaririyar ak'asa tana kuka takawo Yr envelop ta ajiye ajikinta ta mik'e tsaye tana share hawaye tana kallonta ta juya zata tafi dasauri tajuyo tak'ara kallon jaririyar ta bud'eta tashafi fuskarta tace"ko yafeni babyna balaifina bane walh inasonki har raina mahaifinkine baya k'aunarki keba shegiya bace "yar sunnah ce da gatanki gaba da baya,babu yanda zanyi " yata dole ce,oh! Ni Salma waiyau nice zan yarda "yata ta cikina sbd infarantawa mijina rai ya Allah kana kallona biyayya zanyi sbd inason Aurena Allah ka karemin " yata kasakata ahannu nagari,kiyafeni babyna zantafi nabarki sai wata rana.

Tana gama fad'in haka tai saurin juyawa tana kuka ahankali jaririyar ta callara wani mugun kuka tamkar anmintsineta a take mahaifiyarta ta rintse ido tai saurin waigowa tai mata kallon k'arshe tajuya dasauri tai gaba tabar "yar Na kuka ackn tsumma.


*shin wacece Salma?*
***********************
Salma nitsattsiyar yarinya ce me matuk'ar biyayya ga iyayanta Wanda suka tashi a ckn k'uncin talauci d'akyar tagama secondry d'in gwamnati yayanta mus,ab shima yana matakin k'arshe Na Jami,a mahaifinta malam Musa sana,arsa shine kasa kayan miya ak'ofar gida kayan gwari yake saidawa akan tebur a " yar rumfarsa yake kafa bencin yaxauna agefe guda,Allah yakan saka masa nasibi domin da wannan sana,ar dayakeyi yake rufawa kansa asiri yake yiwa yaransa biyu da Allah yabashi hidimar yau da kullum duk da mus,ab yakanyo "yan buga buga a tasha ko dako a singa duk ranar da bashida lecture mahaifiyarsu inna halima tana saida gasara da safe harma takan soya wainar gero akanzo asiya

Salma yarinyace kyakkyawa ajin k'arshe batada rawar kai ko kadan danko k'awaye basu dametaba balle Tara samari harta gama makaranta saurayinta d'aya Wanda takeso yake sonta wato kamal d'an kwalisa Wanda yake matukar sonta saidai shidin karatu yake marayane Amma yayarsa datake Auran me kud'i ta tsaya masa akan harkan karatunsa

Alokacin da Salma ta shekara dagama karatu sai babanta yace mata tafuto da miji Aure zai mata

Tasami kamal da batun sai kamal yace shikam yanxu Aure baya gabansa harsaiya gama karatu Yakama aiki yafison yadogara dakansa intaga zata jirashi to inko baxata jirashiba to intasami miji tayi Aure shikam bayanxuba

Tun dagananma saiya d'auke k'afarsa da zuwa gunta har Allah yakawo ranar Tashin su daga gidan domin dama haya sukeyi Allah kuma yataimaka mallam Musa yasami Aikin gadi a gidan wani hamshak'in me kud'in gaske wato Alh Bashir tekun kud'i


A boysquater suka sami matsuguni inda nan Allah ya hutarsu domin baba Musa yadaina sana,ar gwari inna ta daina saida gasara da tuyar waina shikuma mus,ab yadaina yin dako rayuwarsu tadaidaita adadalin yanda Alh bashir yake yi musu abin arxik'i domin salary metsoka yake biyan mahaifin Salma haka yana yawan kyautata musu duk adalilin son dayakewa "yar tahalikar Allah Salma Wanda bai tab'a nunawaba tana ganin girmansa tasha ganinsa sugaisa inta dawo daga islamiyya sukan had'u afarfajiyar gidan ko inya fito a mota zai futa takan durk'usa har k'asa tagaidashi

Yakan yaba da d'abiunta gashi tayi masa ta koina tanada tarbiya da girmama nagaba da ita,

Aranar da yai k'undun bala yagayawa malam Musa zancen yatsammaci baxai amince masaba Amma saiyaga sab'anin hakan domin murna ma yai da abin har yai masa albishir dacewa yabashi ita

Dayajewa inna da labarin itama taji dad'i sosai tasawa abin Albarka domin dama kullum addu,arta Allah yafito wa da " yarta miji nagari to sunyaba kuma da halayyar Alhajin yana da kyautatawa mutane gashi da tausayin talakawa da taimako yatara kud'i saidai magada

Alh bashir tekun kud'i shekararsa hamsin babban mutum ne baida uwa baida d'a ko "ya sai " yan uwansa guda biyu aduniya da suke ciki d'aya Alh mansur shine k'aninsa yana london da zama tareda iyalansa saikuma k'anwarsa mesuna Haj maryam wacce take Auran v.chairman itama kamarshi Allah bai t'aba bata haihuwaba tana R/zaki da zama.

Magana tai k'arfi tsakanin Alh da Salma domin itama tai amanna dashi batai ja da iyayantaba, yaya mus, ab shima abin yai masa dad'i domin yasan Hutu yaxo musu kwata kwata rashin haihuwar Alh bata damesuba har Akai Auran agidansa dake Zoo road ta tare wannan kuma yabarwa iyayanta

Matar dasuke tare da Alh alokacin dama yagaji da zama da ita sbd yasha kamata da laifuka yana hkr da ita domin yasan ba Dan Allah take zaune dashiba sbd kudinsa ne dama irin yn duniyar nan ne tanada shekaru babbace. Har yawon siyasa take dama a haka ya Aureta ansha Kawo masa tsegumin tana bin maza yn duniya tana shek'e ayarta aboye baitab'a yarda saida yagani da idonsa yakamata da tsohon megadin gidansa k'iri kiri a ckn gidansa awannan dalili yasa yakoreta tareda takardar sakinta sannan yakori megadin nasa yasa anemo masa wani wannan shine dalilin dayasa Aka nemo masa mallam Musa ashe rabon Allah zaisa ya Auri "yarsa ne......


~Auntyn sayyada~πŸ’˜
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


_Sak'on ta,aziyya gareki Aunty Nafee Anka_
_Na rashin "yar yayarta datayi ubangiji Allah ya jik'anta yasa mutuwa tazama Hutu agareta_
_Allah yakai Rahama kabarinki_ *Fauziyya Anka*


~*pg 2...*~
A watan da Salma ta tare agidan Alh bashir Allah yanuna k'udurarsa akanta tasami ciki

Huuu! Fad'ar irin farin cikin da Alh yakasance b'ata bakine mutane yaringa fadawa abokansa da " yan uwa suntayashi murna sosai k'anwar Alh hajiya maryam taringaji aranta itama nan gaba zata iya samu Dan haka bxata fitar da raiba itama,

Tabbas Salma taga soyayya ta miji sosai yake nuna mata yafi son cikin jikinta da komai dake ckn duniya yakance da Allah zai karb'i dukiyarsa yabarshi da d'ansa ko "yarsa dazata haifa ms su zauna ckn talauci shihakan zaifi masa domin rashin haihuwa akwai d'aci arai

Salma tasha kyautuka agunsa domin yabata filaye guda biyar tafka tafka kyauta amatsayin gudunmawa motar kuwa da take hawa tazarce tasa yayantama hadaddiya aka bashi ayanxu mus,ab kam bashida matsala afannin rayuwa harkar karatunsa komai yana tfy normal saidaima ya taimakawa abokansa.

Yabiyawa inna da mallam Musa kujerar zuwa hajji sukaje suka sauke farali itako ance saita haihu

Da cikin yai kwari ya isa haihuwa saiyace ba,a Nigeria zata haihuwa gara yafuta da ita k'asar waje tahaihu acan kulawar da zasu bata yafi Na nan.

London yakaita gidan wansa Alh mansur yabarta acan yadawo gida saita haihu zaikoma,matar Alh mansur Aunty Lubna mekirki tanunawa Salma qauna itake kaita awo duk alokacin zuwa inyaxo,Alokacin ita yaranta biyu twins maxa farare kyawawa ita " yar meduguri ce acan ya Aurota yakaita k'asar London d'in don acan yake Aiki babban likitane shikuma tunda Allah yabashi haihuwa a farkon Auransu Na yn biyu basu sake samuba

Alhamdulillah Allah ya sauketa lfy ta haifi d'anta sankacece k'ato fari tas tamkar d'an bature Alh murna tamkar yai tsintsu yaganshi acan aranar da aka gaya masa sai aranar yabi jirgi domin zuwa ganin magajinsa d'an baiwa.

Kamar ya lasheshi yaringaji yayi masa hotuna sosai basu baro k'asarba saida tayi sati biyu likitoci suna bata magungunan k'arin lfy tasha wuya wajen haihuwarsa tubar kalla k'atone Allah yasotama da ba aiki akai mataba tayi k'okari suma sunyaba mata tayi juriya sosae

Taron suna akayi sosai dasuka dawo gd Nigeria yakashe kud'i tamkar baisan amfaninsuba Hjy maryam taringa jin d'an tamkar subatashi k'aunar haihuwa take sosai itama ga d'an da shiga rai jama,a kowa sai yabon kyansa suke saida mallam yasa akai masa rubutun baki aka ringa bashi yanasha bayan suna.

Komai Na Alh sunan d'ansa yake sakawa *Saifuddeen*

Tundaga sunayen kamfanoninsa da sunayen gidajen mansa komai nasa saifudden, kaunar dayake yw deen sai Allah yaron Allah yabashi farin jini gashi yataso da wani irin farin jini kowa sonsa yake yayo kama da Alh sosai yanada jiki,d'an kubul kub'ul dashi ga kuzari da Allah yabashi shekara d'aya yana gudunsa ko ina

Yaya mus, ab yana kaunar saif yakan yawaita zw gidan k'anwar tasa sbd saif

Allahu Akbar!rabon d'a rabon agana dai Alh kwanansa yakare aduniya ciwon ciki kawai ya turnik'eshi aranar da saif yacika shekara biyu anata bajet d'in za,ai masa birthday asatin Ashe babu rabon ayidai

Salma tasha kuka domin Alh yatafi yabarta da soyayyarsa aranta ga tausayin saif da taringaji zaitaso maraya mutuwa tai mata shigar sauri Shikenan saidai avaiwa saif labarin mahaifinsa.

Mutane sunji mutuwar bawan Allahn nan mutum me tawakkali da hkr ga kyauta da iya mu,amula soyayyar sugar dady akwai tsayewa arai don yajiyar da ita dad'i

Aranar da akai sadakar bakwai hajy maryam tanemi abata deen yadawo gunta da zama Amma sai yayanta Alh mansur yahana yace tayi hkr kada tayiwa Salma fami dame zataji daga yin rasuwa ai insuka mata haka da gaggawa akwai kwara gara dai abari idan nan gaba ta tashi yin Aure saisu karb'eshi.

Dole tahakura badan taso hakanba tana qaunar deen bawai Dan mugunta ko son zcy tashirya hakanba

Allah ya sakawa Salma hkr da Dangana gameda rashin Alh aranta

Taci gaba da rainon d'anta agunta alokacin daya shekara uku tana zaune agida sai yayanta yabata shawarar akan ta koma karatu kawai shiyafi kafin Allah yakawo mata miji

Hakan kuwa akai tafara karatunta a Sa,Adatu rimi NCE abinta tana karantar mass communication

tana NCE2 Yaya mus,ab yafito da matar dazai Aura saudat akasaka ranar Aure a filayenta tabashi d'aya a d'an agundi dayake har account tabude masa nanta tayashi ginin gidan akayishi mekyau naburgewa,sannan tabiya musu kud'in kujerar makka ita dashi hajji.

Alokacin saif yana gurin inna sunyi sabo sosai tunda ita ba wuni take agidaba

Saida suka dawo daga hajji akai bikin Yaya Musab,Amarya tatare agidansa alokacin bikinne Allah yasake had'ata da kamal d'inta ya sake zama handsome a gurin dinner suka had'u abokansa suka gayyaceshi baizaci bikin nasu Salma bane

Yasha mamakin yanda tazama babbar yarinya aranar yataso mata da mikin kaunarsa aranta basu rabuba saida yakaita gida amotarsa

Soyayya mekarfi tasake k'ulluwa atsakanin Salma da kamal Wanda take masa mugun so haryafi nasa yaje turai yai karatu har ya kama aiki shine manaja awani kamfani alokacin data gama karatunta ne tayi masa zancen Aure yace yanxu kam ashirye yake dayi saidai yanada wani ra,ayi guda Na rashin son Tara Tara totally ma bayaso ta haihu agidansa daga Aure yafison siyi rayuwar jin dad'i inyaso daga baya sai su haihu insun kwarari shekaru soyayyar kamal ta rufewa Salma ido ta Amince har a rubuce sukayi babu Wanda yasani

Dazatayi Aure Hjy maryam tazo takanas tatafi da deen yakoma gurin ta d'ungurugun da zama ab'angaren dukiyarsa wasu kulawarsu nahannun mijinta wasu kuma Alh mansur Amma kamfaninsa uncle mus,ab aka nad'a akai yake kula da komai

Anyi Aure Salma da kamal d'an kwalisa domin kwalisarsa dad'uwa tayima saboda yana warwasawa yana samun kud'i ga matarsa Salma datake sakar masa dukiyarta itama domin ta tashi da kadara da mak'udan kud'i a tumulin takabarta

Salma tana bin kamal Sauda kafa tsantsar biyayya tanayi masa komai yace shitake Ni batason b'acin ransa yana bata kwayoyin family planning tana d'irka sosai bata masa muna muna

Saidaga baya da sukai shekaru biyar taga abin nasa bana k'are bane saitayiwa kanta fada taga cewar gara tadaina sha kada yai mata illa a mahaifa

Alokacin data dainasha Ashe rabone zai shiga domin awatan tasamu ciki,bata tashi saniba saida yai wata tfy zuwa k'asar Canada zaiyi wata uku,aiko ta shiga wani hali Na tunani gashi sunyi alqawari inhar ta munafurceshi zai rabu da ita saboda shi kaifi d'ayane baya munafurci baya kuma son a munafurceshi


Aiko dai alokacin daya dawo ciki yafito a ranar yaganota tasha zazzaga kuwa sukaita kai ruwa rana shi alallai inbata zubdaba saidai surabu taxaci abin wasane saida taga sunyi wata baya kulata kana tayi masa dabara cewa Yy hkr inhar tahaihu zata kai Dan gidan marayu kota yar tayarda ta zauna dashi

To sai asannan taga yadawo mata kamal d'inta datake masifaffen so shidin ya iya luv namba dayane awajan nan


Salma ta tafka babban kuskure babu Wanda ta tunkara da halin da suke ck ko yayarsa da take mugun sonta, harta haihu tabiyewa son namiji dason zama dashi Wanda wasuma nema suke Amma ita aranar data haifi d'iyarta zankad'ed'iya sonkowa taje tayarda ita taxabi zama da namiji.....

_muje zuwa_

~*Auntyn sayyada*~
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


~*page 3...*~
Yanayi ake ciki nasanyi rana bata fitowa da wuri har hazone ya baibaye koina nagarin, har k'arfe takwas nasafiyar babyn nan tana kwance agurin gindin bishiyar nan tana tsaluma kuka dayake gurin yakasance babu yawan jama,a kuma masu tfyr k'afama basu cika bintaba saimasu motoci suma tsilli tsilli sukan wuce awani sa ilin toyau abin kamar almara babu wanda Allah yakawo yabi tagurin kodon ranar anyi sanyi sosai

Tunda uwarta tayarda ita misalin k'arfe shida nasafe sai k'arfe takwas Na safiyar Allah yajefo wata mota odessy bak'a zata wuce ta gurin da sauri matuk'in motar yataka burki Allah yajiyar dashi wannan kuka datake babu k'akkautawa matarsa dake gefensa taisaurin kallonsa tace"dady lfy wannan cin burki haka ko mantuwa kayi a cikin asibitin?

Yayi shiru yana sauraro daga waje yad'an lek'a kansa yace mata"momy bakiji kukaba kamar najariri?

Tagyad'a kanta tareda rungume nata jaririn dake hannunta tace"naji mana dady,to menene natsayawar idan tare yake da uwarsafa menene amfanin tsayawar tamu kuma?

Yakalleta yace"kefa macece keya kamata kifara fahimtar wani Abu akai bani namijiba,yanxu idan ba uwarsΓ  agurinfa? Idan muka kai masa taimakon gaggawa ai kinga munyi jahadi ko?

Tajuyar dakanta tace"kaga dady walh ba inda zanje a sanyin sfyr nan injema ko aljanine,nifa gara mutafi kawai Dan harnaji tsoro yafara kamani ma asassafen nan munbiyo guri tsit kace zaka tsaya damu haba

Yai murmushi yace"momy kiyi hkr bari naje Nagano nahango kamar acan ne gindin bishiyar kamar abune agun,yi addu,a kfn nadawo.

Yana gama fad'in haka ya fuce dasauri

Tayatsina fuska tace"kanada taurin kai dady saikaje ai bana iya da jaye jayenkaba

Yana zuwa gurin kuwa yaga abinda zcyrsa take zato dafarko yaji tsoro Amma sai kyakykywar zcyrsa tadake yakaranto addu,a yadurk'usa ya d'auka yana mik'ewa da ita aiko yaga doguwar Envelope ta fad'o yasake tsugunnawa yad'auka hajiya yanufi motarsa

K'ura masa ido tayi da mamaki kan fuskarsa tace "subhanallah dady me nake gani ahannunka?

Yace" jaririyace momy kinga zatona ya tabbata yanzu haka wata uwarce tayo cikinta awaje shine Dan rashin imani ta haifeta tayarda ita.

Ta d'an bud'e fuskar "yar takalleta take taji tanason baynn Dan hartafi ta hannunta kyau.

Tace" to yanxu me kake nufi zamuyi da ita kenan?

Yace"tafiya da ita muhad'a biyu inmunje gida mu nunawa mutane cewar "yan biyu kk Haifa koya kika gani?

Tace" anya kuwa dady za,a yarda kagafa basui kamaba ko kusa tamu chaculet ce wannan fara,Ni walh damun hakura koka maidata kokuma mukaita gidan marayu'

Ya girgixa kai yace"walh tunda Na d'auketa da hannuna ba inda zan kaita insha Allahu nixan sami ladanta babu wani gdn marayu dazan mik'ata zanhad'ata da tawa narik'e shekara da shekaru muna nema yanxu Allah yabamu harma da k'ari tawata hanyar sai ink'i karb'a ina! Bansan me Allah kenufi da hakanba garama kiy shiru kibi abinda natsara tunwuri Dan kinfi kowa sanin halina da yanda nake akan mgn.

Tai shiru tareda karb'ar "yar ta had'a da tata tai musu rik'on gefe da gefe a cinyarta d'aya Na cnyr hagu d'aya na ta dama alokacin kuma abin mamaki Jaririyar ta daina kukan tayi shiru idonta biyu tamkar tana jinsu ita kuma tasu sai baccinta take


*______________________*koda sukaje gida a d'akin momy suka kwantar da jariran akan gadonta Alh yaxauna ya d'auki babyn da suka tsinta yace" gata masha Allah momy,gaskiya tashiga raina Dan Allah kitaimaka kibani goyon baya akan rik'onta kada kik'i koki watsan k'asa a idona matata kinunawa duniya cewar "yanbiyu kk haifa Dan Allah badan niba.....ta katseshi" haba dady meye nasaika rok'eni akan abinda nima zan sami ladan kuma nima ai riba biyu nasamu shekara nawa nayi ina nema Allah baibaniba sai yanxu kuma yabani wata ajiyarsa daban inbijire aibazai yiyuba,insha Allahu zan rik'e Dan haka wane suna zakai musu huduba kasan dai yanda nakeso nasaka sunan mahaifiyata danhaka inaso kasaka sunan atawa Dana Haifa da cikina

Yayi murmushi yace"wannan babu matsala ita wannan saita amsa sunan mahaifiyata Fatima ita kuma tamun saita amsa mahaifiyarki Safeena d'in

Tayi murmushi tace"kaga sai inringa kiransu da teemah da feenah kokuwa?

Yagyada kai yace"yayi sosaima,

Nan yai musu hud'uba kamar yanda suka tsara yaringa yiwa mutane waya yana sanar musu matarsa ta haifi "yan biyu duk mata akaita yi masa barka ana tayashi murna itanma duk Wanda tayiwa waya hakan take sanarwa cewar yau tahaihu twns duk mata.

Harzai futa yaga wannan takardar akan babyn yai saurin cirowa ya yaga saiga k'udade " yan dubu dubu sunzubo kan gadon Hjy maryam tayi saurin tattare su guri d'aya yafarke Yr takardar daya gaani aciki anyi d'an note kamar haka:- _Dan Allah duk Wanda ya tsinci wannan yarinya yataimaka yasaka mata suna Fatima sunan kakarta Knn ba shegiya bace tahanyar suna Na haifeta a wannan asibitin Na Khadija clinic misalin biyar nasafiyar yau Talata abisa wata lalura yasa dole zan rabu da ita bawai Dan bamasontaba k'addarace da jarabta ta Allah sunan mahaifinta kamal nikuma mahaifiyarta Sunana Salma_

Yana gama karΓ ntawΓ  yamikawa momy itama takaranta nan jikinta yai sanyi tad'auki wasu zobuna Na azurfa da gwal manya ackn envelope d'in tahau juyawa ahannunta tace"Dady kaga ikon Allah ko? Ashema sunan daka bata shine nata lallai Allah ya ajiye wata k'udira akanta tunda ba shegiya bace akwai k'addarar data afka mata"

Dady yagyada kai yace"hakane momy danayi tunaninma ko iyayanta talakawane futuk basuda yanda zasui shiyasa suka zab'i yarda ita akan zama da itan.

Momy tace"hhhmmm wannan da alamar iyayanta masu haline dady kalli wannan uban zobuna masu tsada kawai dai murufa zancen haka kada "yan barka sufara zuwa inka dawo mak'arasa.

Yamike yana fadin" hakane yisauri had'e kudaden da zobunan ki adana inmun sami lokaci ma kirga muga nawane,yafuta tayi masa adawo lfy tayi saurin adana zuba kud'aden da zobunan acikin zanin babyn ta Adana a ckn akwatinta.

Ta d'auko waya tayi dialing wata namba takara wayar akunne tace"hello Aunty Lubna kinyi twins duk mata fa'

Daga can b'angaren Hjy Lubna tace"kai haba Alhamdulillah kema kingado d'an,uwanki kenan?

Tayi dry tace"walh kuwa Ku ai maxane mukuma mata Allah yabamu.

Hjy Lubna tace"kinga lamarin ubangiji Knn,ko hkrnku yayi rana gashi yabaku biyu alokaci d'aya,

Hjy maryam tace"walh kuwa'

"To Allah ya raya saimunxo kafin suna

Hjy maryam tace" ina d'ana Deen?

Hjy Lubna tace"yana tare dasu hassan a falo,
"To atahon da d'ana dai hutunsu zai k'are asatin nan,

Hjy Lubna tace" insha Allahu dashi zan taho su Hussain ne dai baxanzo dasuba akwai skul bahutu sukeba,

Anan sukai sallama nandanan kafin awa guda gidan Hjy maryam ya d'inke da jama, a "yan barka anata murnan ganin twins Amma kowa yakance hassanar tafi kyau(teemah) murmushi kawai take tace" dandai kunganta farane Amma ai hussaina tafita kyau.


Aranar suna manyan Raguna Alh Lurwan ya yanka akai walima taro yayi shima sosai natayashi murnar samun twins dayai,

"Yan biyu sun sami kaya tamkar k'ofar wambai aka baje dama Abu yasami meyi gashi v.chairman harda wadanda sukai Dan Neman suna.

Hjy maryam tasami kud'i da atamfofi sosai lallai haihuwa tai mata rana atamfofi tamkar alefeb wata " yar gatan


Teemah da feenah suka taso gwanin sha,awa kowa sonsu yake haka Hjy taci gaba da rikonsu bata nuna bambanci tsakaninsu d'anta datake rik'ewa Deen yana pri aji biyar alokacin shekararsa goma sukuma suna one year gudu koina suke "yan dagwai dagwai gwanin sha,awa alokacin data yayesu shikuma deen yakoma gun k'anin ubansa London domin yayi secondary da jami'arsa a can

Bayan shekaru gomasha biyar abubuwa suka fara sauyawa agidan Alh lurwanu ta b'angaren Hjy maryam taringajin haushin dady akan yanda yafi nuna kulawarsa akan Teemah

Yarinyar tanada shiga rai ga nutsuwa ga ilimi tanada son karatun addini sosai bata fashin zuwa islamiyya itako feenah bata qaunar zuwa har bokonma bata bada himma akai

Teemah ansha zuwa da ita competition kokuma takan d'auki Na d'aya kona biyu a class gashi tayi nisa a krtn alqur,ani
Duk wadannan abubuwan su sukaja mata qauna a zcyr dadynta gashi yana bata wani matsayi aransa nasunan mahaifiyarsa dataci

Duk ayyukan gidan yawanci ita takeyi Yr Aiki shara takeyi da wanke wanke Amma teemah ke girki Amma duk abinnan datake bata gani tafi nunawa feenah kulawa batason laifinta ga feenah akwai surutu da tsiwa itako teemah surutu bai dametaba tanada hakuri....


~*Auntyn Sayyada..*~
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


~*pg 4...*~
Alokacin dasu feenah da teemah sukai candy dady waya yasai musu Amma ta feenah k'aramace ta teemah kuma Babba ce touch kuma dama yafada musu duk wacce tayi kokari tazo ta d'aya kota biyu ita zaisiyawa babbar waya

Tana karb'ar wayar ta zumb'uri baki tahaye sama gurin momy tasameta akwance akan gado tafara bacci tatasheta da shagwab'a tace"momy ki tashi kiga abinda dady yaimin...

Firgigit ta bud'e idonta tace da feenah"me dadyn yai miki?

Nan feenah tamik'a mata wayar tana hawaye tanacewa "Dan Allah ki kalli sankai niyabani tech no me madannai ita kuma yabata Techno touching, walh baxan rik'eba gara inbaiwa almajiri ita wannan ai abin kunyane aguna k'awayena suna rik'e babbar harka nikuma Na rik'e rigwagwa burin d'an garuwa.

Hjy maryam ta janyota ajikinta tace" yi hkr Uwata nikaina inajin ciwon yanda dady yake nuna muku nasonkai atsakaninku sbd yaga hassanrki sunan babarsane da ita, sha kuruminki inasonki fiye da ita indai wayace zansai miki sabuwa wacce tafita ma saiki had'a biyu ba shikenanba.

Nan tahau murmushi tamik'e tanaiwa momy godiya ranta yai fari tas itama zata fantama.

A satin suke saka ran dawowar kamaludden gida yakammala da karatunsa a k'asar waje zai dawo gidan momy

D'okin da feenah take yafi Na teemah domin ita feenah sonsa take har ckn ranta itako soyayyar "yan uwan taka take masa yana yawan yo waya gidan duk sugaisa Amma yafison yaji muryar teemah shikansa yafi yabawa da hankalinta

Aranar da zai diro teemah bata zauna ba tanata aiyukan gida itace gyaran d'akinsa itace yi masa " yan toye-toye da abinci kala kala ga lemuna data tsara masa Amma feenah ko hannu batasaka mata ta tayataba

Dadyne ya d'aukoshi a Airport dukkansu suna daining table suna dinner deen yakalli feenah yace"k'anwata naji kunyi candy yanxu kuma wacce sch kk sha awar zuwa?

Tayi fari tace"aini Yaya walh banida ra,ayin yin wani karatun saina huta dayawa ko zanyima sainaga dama walh karatu akwai wahala.

Yace"aiko dai baki isaba karatu shine gatanki ayanxu tunda ba Mijin Aure kk fito dashiba.Amma babu wani Hutu da zakiyi,hutun jaki dakaya Knn,nikaina banda inaso naxauna nakula da kampani Na da karatun zan dad'a dorawa inyi digree Na biyu Amma sainaga yadda yanayin Aikin dazan kama yake

Dady ya girgixa kai yace"gaya mata dai Deen wannan k'anwar taka batason karatu kwata kwata batada k'okari...momy takatseshi"aiko dai dady feenah tana ja,kadaina aibata kwakwalwarta insha Allahu gaba saimunyi alfahari da ita

Dady yai murmushi yace"Allah yasa aini hakan nakeso"

Deen yakalli teemah datake kurb'ar lemo tanata doka murmushi yace"yadai k'anwata teemah kefa wacce skul kk so kiyi kokema ra,ayinku d'aya da Yr,uwarki?

Ta girgixa kai tana kallonsa tace"aini Yaya da yardar Allah karatu zanyi babu kama hannun yaro,kai nake jirama kazab'amin sch d'in da zanje domin b'angaren science nake.

Yatafa hannu yace"gud girl Allah yataimaka zangoya mk baya d'ari bisa d'ari zantsaya mk harsai naga kingama lfy sch of nursing yakamata Na nema miki.

Dady yace"masha Allahu, Allah yataimaka yabada Sa,a

Teemah tace"Amin,

Itako feenah ranta ab'ace yake sosai batayi full tank bama Dan bakin cikin abinda yafaru ta tashi fuuu tayi d'akinsu take momy tabi bayanta domin ta rarrasota

Watansa d'aya da dawowa mahaifarsa yakai wa mahaifiyarsa ziyara kafin nan yaje yagaida kakanninsa inna da mllm Musa

Uncle Mus,ab shiya nunnuna masa komai dake tfy a kamfanin nasa aka bud'e masa babban ofishin da dama yana kulle yana jiransa,

Yafara aiki a kamfaninsa gidajen mansa guda biyu sunan ana kula dasu

Tabbas Deen bashida matsala ta rayuwa arxik'i ya gama samunsa tun aduniya a kullum yakanyiwa mahaifinsa daya rasu addu,a


************
Ranar wata laraba yana kwance ad'akinsa baifuta aikiba yana hutawa Dan ba kullum yake zuwaba koma yaje d'in dawuri yake dawowa

Kamar anjefota

Please Login or Register in order to submit comment