You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

falo suna kallon wani Indian film marriage again, sunata hira akan yanda film din gudana kowacce tana fad'ar tauraronta da tauruwarta ackn film d'in

Suko su hassan da Hussain suna tare da deen a d'akin Sa sunata shan hira ta yaushe gamo sunsaka wani american film basu suka kwanta ba sai d'ayan dare


Washe gari teemah ce tashiga kicin don had'a abin Karin kumallo Nabeehat ta tayata sukai soye soyensu feenah tazo ta d'an tayasu don ba kwarewa tayi aharkar girkiba shayi kawai ta dafa ta tayasu kaiwa dinning table

Sai goma aka had'u a dinning d'in feenah tana kusada Hussain yamballs sukeci suna kurbar shayi suna ayyakawa da junansu sak'onni tabbas Hussain yaga canji sosai agun feenarsa yanxu kam yayarda tana sonsa kamar yadda take fad'a masa a network

Teemah nakusa da deen tanacin buredi da bota atsakiya shiko tana kurb'ar shayi hadin murtuku hankalinta kwance

Shiko deen dankali yakeci su Nabeehat ma abinda suke ra,ayin ci shi suke ci agun

Su momy da dady suna azzumi Monday ce basu fitoba,

Hussain kyakkykyawane dogo kamarsu d'aya da hassan saidai shi hussain yanada wani d'igon bak'i akusada kunnensa kamar tusar jaki ta inda wasu keganesu knn farare ne sunada saje akewaye da fuskarsu halinsu ya bambanta danshi hassan bayada fad'a baida zafi yanayin maganarsa akwai sanyi ck

Shiko Hussain bayada hkr inka tab'oshi yanada zafi ga saurin fushi

Hassan Aikin banki yake acan shiko Hussain barista ne basu dad'e dafara aikinba Dan saida suka had'a digree bibbiyu.

*_____________________*
Da yamma dukkansu suka futa ababbar jeep d'in deen mecin mutane kusan bakwai uku gaba hudu baya

Haka aka had'u anata shan hira ackn motar

Kowacce ta tsala kwalliya shope rite yakaisu kowacce tad'auki abinda takeso deen yabiya suka fito ya zazzagaya gari dasu basu suka dawoba sai ana sallar magriba

Hassan dai dole yahak'urewa son Teemah tunda ya fahimci tana son deen sosai koya fad'a matama babu amfani Dan HK saiya ja bakinsa yai shiru domin yanda yafahimta wannan soyayyar tasu sai Allah

Haka itama Nabeehat tunda ta lura deen yanaiwa Teemah muguwar soyayya tasan tabbas ta makaro dukda yasan da tana sonsa baxata iya yi musu tsaikoba dole tasawa ranta salama dontana son Teemah tana kaunarta sun shak'u ayanxu bazataso taga ta tarwatsa farin cikin taba......


~*Auntyn Sayyada da shahida*~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘


*KADUNA....*


~*Pg 15-16*~

Yaya Mukhtar yana tsaye yakurawa Aisha datake bacci ido zcyrsa fal da takaicin abinda tajanyo musu Na abin kunya jiyake kamar yashaketa ta mutu ahuta,

Yakalli Aminatu yace"Aisha bata kyautawa kantaba meyasa tajanyo mana wannan abin kunyar,tanaso ta tozarta iyayanmu ne Ashe duk irin tsayawa tsayin daka da aka Baku tarbiya saita baiwa iyayanmu kunya walh yau da agida muke babu mehanani inmata mugun duka yanxun ma Dan bacci takene walh da saina lallasata ko ckn yaxube,Dan walh baxata reni shege agidanmuba,

Aminatu ta rintse idonta hawaye yana surnano mata ranta yana mata suya tabbas Aisha tacucesu ta suci kanta

Yaya Mukhtar ransa ab'ace yace "tashi maxa Ummie mutafi gida babu me zama agunta yanda inna ta tafi muma tafiyar yakamata muyi Dan banga amfanin zama agun wannan" Yr iskarba,kud'in da aka cajeni nagado da ruwa da akasa matama nayi Dana sanin biya a aljihuna Wanda yai mata ckn yakamata yabiya baniba,yana gama fad'in haka ya juya yai hanyar futa

Aminatu takatseshi "Dan Allah Yaya kayi hkr kada mutafi mubarta ahalin da take ck,kome tayi dai mune dolen ta,baxan iya tfy nabarta awannan halin ba Yaya...ya d'aga mata hannu ckn fushi yace" toshikenan aisaiki zauna Mara tunani da kishin kanta inke kina sonta to ita ba sonki takeba bakuma k'aunar iyayenki takeba,yaba gama fad'a mata hakan yafice abinsa

Aminatu takifa kanta akan gadon da Aishan ke kwance ta fashe da kuka


***** ***** *****

Acan gida kuwa da isar inna gida tun ak'ofar gida ta aika am kira mallam

Suna zaune jugum itada inna halima donta gaya mata komai sunyi tagumi kowacce rantaba dad'i suna sak'awa da kuncewa mallam ya shigo yanemi guri ya zauna yana fad'in"ince dai lfy ko?

Inna A'i tashare kwallar data zubo mata tace"inafa lfy mallam Aisha ta janyo mana abin fad'a ackn unguwa ta ja mana magana da terere saidai Allah ya sawwak'a donta gama cutarmu ta tona mana asiri wai cikine da ita...

Mallam yace"ciki? Wanne irin ciki kuma ana zaune qalau?

Inna A'i tace"ciki dai Na d'an mutum Wanda ake cewa ckn shege shitake dashi Aisha ta cucemu ta cuci kanta.

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,haka Aisha tayi,Amma dai ta b'ata wayonta tayi girman banza girman kobo,ba komai kanta ta cuta zanyi maganinta kada kusa wannan aranku yaxo ya dameku abanxa nasan mexanyi,ina zuwa yashura takalmansa yafice

*_____________________*
Sai dare ta farfad'o ta dawo hayyacinta ta warware taji k'arfin jikinta aka bata sallama tun a asibitin Aminatu ta gaya mata komai Na abinda yafaru da ita Na abin kunyar data janyo musu,

Kuka sosai Aisha take da idonta hankalinta yai mugun tashi lallai Ashe zargin da Aminatu take akanta yazama gaskiya tayarda aminatun tafita kaifin basira ko ita dayake jikinta bata ganoba bata tab'a tunanin zatai cikiba balle takare kanta

Aminatu dan sahu ta tare musu drop har gida ackn adaidaita d'inma Aisha ba abinda take sai kuka hawayenta sai zarya yake akan kumatunta cknta ya d'uri ruwa tana tunanin shin wane hukunci zata fuskanta daga iyayenta.

Har k'ofar gida me d'an sahu ya saukesu Aminatu tashiga gida takarb'o kud'i gun inna A'i tabashi

Atare suka shiga ckn gidan jikin Aisha asanyaye sallamr Aminatu suka amsa su innar suna zaune akan tabarma duk sunyi jigun² kamar wad'anda akaiwa rasuwa yau

Aisha ganin basu kalletaba ma balle sukulata mahakan yasa tai sunsum tashige d'akinsu

Aminatu kuwa Alwala ta d'auro donta bada faralin sallar magriba gakuma ishsha,I ya doso,

Ashe mallam aranar yaiwa "yan makaranta da suke semester k'arshe waya su yaya baffa da Yaya suraj cewar lallai lallai duk yanda zasuyi subaro makaranta sutaho gida agobe Dan akwai babbar maganar data taso agidan haka yaiwa Kawu Ibrahim waya shima yasanar masa yaxo goben yanason ganinsa da gaggawa akan wata muhimmiyar mgn

Aranar mallam da bakin ckn abin yakwana yaci alwashin yanda Aisha ta b'ata musu rai itama nata ran saiyafi nasu b'aci don saiya had'ata Aure da d'aya daga ckn Almajiransa kotak'i ko taso dolenta ta Amince,kuma dolenta ta fad'i kowaye yai mata ckn domin anemoshi abashi kayanshi inta haihu domin baxa a d'au zunubin zubda ciki ackn gidansaba.......


_muje zuwa_

~*Auntyn Sayyada da shahida*~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘


~*Pg 17-18*~

Washe gari da k'arfe 1:30 pm Aminatu ta dawo daga makaranta agajiye sunyi jarabawar biology dukda taxo musu da sauk'i bakamar yadda suka zataba Amma tilis tashigo gidan asakamakon kwalleliyar ranar da akeyi ga yunwar da take cknta

Tana shigowa kicin ta nufa dama tayi sallah a sch ta zubo abinci a plet shinkafa da miyane tadora cokali akai tafuto tanufi d'akin inna A'i

Tatarar innar tana sallah tazauna akan kujerar innar 2siter tafara cin abincinta anutse

Inna ta idar da sallar takalli Aminatu tace "a,a Autar mallam har kun taso?

Aminatu tace" walh mundawo inna da yunwa yau nadawo bantsaya yin Karin kirkiba shiyasa yunwa takwak'uleni dayawa

Inna tagyad'a kanta tace"dafatan jarabawar batai wuyaba ko?.

Aminatu ta girgixa kai tana murmushi tace"inafa wuya inna walh taxo da sauk'i anwatso mana simple questions munkuma amsa suka sai fatan samun Sa,a

Inna tace"to ubangiji Allah yabada Sa,a

"Amin,inna yanaga motocin su Yaya ak'ofar gida kuma ba week End ba, badai sune suka dawoba?

Inna tace" sune mana ba dole ki gansuba mallam ne yai musu waya kan abinda Aishar tayi zama za,ayi yau akanta yanxu haka ma suna masallaci sai kawunku ya iso zasu shigo gidan

Aminatu tace"hhhmmm koma dai menene Aunty ita tajanyowa kanta nasan mallam baxai mata ta dadiba,walh inna tun farko nake gayawa Aunty Aisha akan sabuwar d'abi,ar data tsiro nafutar dare intaga bakwa tsakar gidan bata dawowafa sai kusan anrufe gida saitakai shadaya awaje nasha yi mata magana akai nanuna mata rashin kyan hakannai mat nasiha Amma bata d'auka saidai ma ta hayayyak'o mini tun daga rana takarshe datayimin kashedin nakyaleta kada nasake yi mata magana akan hakan Shikenan nai gum nazuba mata ido,kuma Ni ina zargin akwai wani danaji tana waya dashi waishi Adam watakil shine yai mata ckn nan Dan gunsa take futa

Inna tace "babu musu a zancenki Ummie don nima sau 2 ina kamata da futar nan datake Aisha tanada kunnen k'ashi yanxu gashinan kwabarta tayi ruwa Dan mallam ya rantse cewar baza,a zubar da cikin nanba k'auye zaikaita gun danginsa ta haihu acan inyaso saita dawo yad'aura mata Aure da Almajirinsa abinda ta haifa kuma amik'ashi gun ubansa.

Aminatu tayi ajiyar zcy tace"Allah yakyauta to yanxu wannan wa gari ya waya,karatun da taketa kulafuci zatayima baxata samuyiba Knn,

Inna tanisa tace" to aidama koba wannan abin datayi mallam yahanata yace bayada ra,ayin barin "ya mace agabansa tayi dogon karatu gara inkunje can gaban mazajenku kwayi insun bari.

Aminatu tace" ummm dama Ni inna ban zurfafaba domin wanna ma Dana samu nagode wa Allah Yaya ma baya son inci gaba yace sana,a zanyi acikin gidansa

Inna tace"hakan yayi Allah yataimaka Aikin iya d'inki da sak'ar kayan sanyi duk sai a sai miki komai kitafi dashi

Aminatu akullum Hankalinki k'aruwa yake halayyarki tana burgeni Allah yai miki albarka

Aminatu tace"Amin inna,

Ta mike tafuta dontaje d'akinsu ta cire uniform sauransu jarabawa 1 danm suna saka interval atsakani da tuni sungama

Aminatu ta tarar da Aisha a zaune tayi tagumi ta zauna kusa da ita takalleta kawai awani b'angaren tana bata haushi wani b'angaren kuma tausai take bata bayama dataji irin hukuncin da mallam zai yanke mata ayau

Aisha ta janye tagumin datayi tace"Ummie ina ckn damuwar wannan abin danayi walh nayi matukar nadama da danasani gashi ina fargabar zubar da ckn nan domin ance anashan wuya wajen zubda ciki kokuma ka rasa ranka nagayawa Adam yace zubarshi za ayi...

Aminatu takatseta"zubar da ciki kuma Aunty?

"Kema kinsan mallam baxai yardaba gara tun wuri kidaina tunanin xubarshi don mallam yace saikin haifeshi abaiwa meshi...

Hawaye suka zubowa Aisha tasa bayan hannunta tagoge tana fad'in" nashiga uku Na lalace walh baxan bari nahaihuba gara.....sallamar inna takatseta"tokuzo maxa yanxu d'akin mallam kowa ya hallara Ku ake jira.

Gaban Aisha saida ya fad'i cknta ya d'uri ruwa yau tasan Allah ne zai kwaceta takalli Aminatu tace"Dan Allah Ummie kibani addu ar addu,ar da zanyi kona samu nutsuwa ckn raina.

Aminatu tace"kiringa fad'in innalillahi wa inna ilaihir rajiun dakuma lahaula wala quwwata illah billahi alaihil azim,

Nan Aisha tayi caraf tahauyi Aminatu tarigata yin gaba harta shige d'akin itako tunda tajiyo muryar Kawu daga ckn d'akin saigabanta ya tsananta faduwa domin tasan shine farkon yin cuta agareta shiya fara keta mata haddi koma meye dai shine sila tabbas ayau inhar suka matsa mata zata b'allo masa ruwa domin zata futo fili tagaya musu cewar kawun ne yai mata cikin aibai isa ya musaba tunda yasan shiya fara cutarta yarabata da budurcinta.....


~*Auntyn Sayyada da shahida*~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_👉🏼 *Nabilancy Luv* ©💘


~*Pg 19-20*~

Asanyaye zuciyarta Na dukan uku-uku ta d'aga labulen d'akin mallam d'in da sallama abakinta tashiga kanta a k'asa bata d'aga kai ta kallesuba ta rab'a kusada Aminatu datake ak'asa gab da kofa ta zauna

Suma yayun nata ak'asan suke a zaune sai wurga mata kallo suke

Inna A'i da inna halima suma suna gefe guda ak'asan a zaune

Kawu yana kan kujera one siter mallam ma akan kujerar yake

Gyaran murya mallam yayi kana yace"to kamar yadda nafad'a muku irin cin zarafin da Aisha ta janyo min Na cikin shege agidana to nikuma natarukune domin kuji irin hukuncin Dana yanake akanta sbd baxan d'auki reniba tunda tazama mekunnen k'ashi itace ta fara b'atan gida tanaso sunana ya b'aci a unguwa Dan haka Na yanke hukuncin ta tafi can k'auye gun "yan,uwa ta zauna harta haihu inyaso saita dawo gida anemi uban abinda ta Haifa abashi sai ind'aura mata Aure da Ashiru Almajirina ko kuma ta zab'i barmin gida tashiga duniya ta nemi wasu dangin ta zauna gunsu tayi duk watsewar da zatayi acan ko Yaya kuka gani?


kowa yai shiru a d'akin ita Aisha zcyrta ke bugawa kamar ta tarwatse yama za,ai ta Auri wani Almajiri kuma ma Ashiru datasan k'azantarsa tab walh bazata iyaba

Shiko Yaya baffa tausayi tabashi dukda yanajin haushin abinda takeyi agidan shiya fara magana yace" Amma mallam yakamata arangwanta mata akan Auren Ashiru Dan Allah ina tayata Neman Alfarma domin mutane zasu iya farga suso jin dalilin hakan,Dan haka ina ganin kamata yayi ace shi Wanda yai mata cikin za,a nemo inta haihun aimusu Auren kokuwa ya kuka gani?

Yafad'a yana kallon su Mukhtar

Yaya suraj da zcyrsa ta d'au zafi ya harxuk'o yakalleta yace"ke Dan ubanki wane d'an iskanne yai miki cikin ko waye saimun dank'oshi dole ya Aureki inkuma ba hakaba inyak'i saiki hkr ki Auri ashirin.

Kan Aisha a kife akan cinyarta tana kuka batace k'alaba

K'afa Yaya suraj ya Kawo zai maka mata Kawu yai saurin dakatarshi"barta suraj kada kai mata lahani azo ayi biyu babu bari tafad'a a hankali

Yakalleta yace"Aisha kifadi ko waye za,a nemoshi anitse zamu bishi da lallami ko yak'i Auren naki zan bashi makudan kud'i sbd baki dace da Almajiriba...."walh Kawu yace saidai in zubda cikin za,ayi shine zai Aureni sbd iyayansa manyan mutane ne yace bayaso suji balle kuma nahaihu akai ms d'an baxai yardaba....

"Walh baza,a zubar da cikinba dole ki haihu akai masa d'ansa Dan uwarshi wato mu namu asirin yatonu knn," cewar Yaya Mukhtar


Mallam yace"kudakata Ni bance atsaya jayayyaba tunda har sai an zubarda ciki zai Aureki karya yake yi baxan d'auki zunubin zubda ciki agidanaba yaxo daga baya ma ya gujeki kokuma ki rasa ranki gun zubda cikin gara kawai ayi abinda nace tun farko Ashiru yanada nutsuwa aduk Almajiraina yafisu hankali da kwazon nema Na dad'e da yayeshi saidai ma yakoyar da wasu kuma yana zuwa yayi dako akasuwa danhaka zab'in Dana bakima nakansile dolene Aure da Ashiru kokuma kicanxa uba.


Ta dad'a fashewa da kuka Aminatu tana gefe tsuru batada ta cewa don mallam yagama magana haka iyayanta mata sunyi shiru agefe su aganinsuma mallam daidai yayi

Kawu yakalli Aisha yace"Aisha kiyi shiru ki karb'i zab'in mallam insha Allahu zan tsaya miki akan zamanku da Ashiru zansai gida kuzauna ciki har sai Allah yabashi nashi zan bashi jari metsoka yayi sana,a kema kuma zantsaya kiyi karatu agidansa sannan motarki zata dawo hannunki haka yayi miki?

Ta d'ago kai takura masa ido tana k'issima wani Abu aranta harsaida yaji fad'uwar gaba yakanne yace"toya kk gani ko hakan baiyi mikiba?

Ta girgixa kanta tace"yayi Na amince Kawu

Tana gama fad'in haka ta mik'e ta fuce da kukanta

Mallam yace"to magana ta k'are Dan haka kai Mukhtar xaka kaita k'auye da kanka saika mikata ahannunsu zaka taho

Kawu yace"ba saiya kaitaba ma nahutacceshi nizankaita dakaina

Anan taro ya watse kowa yafuce aka bar Kawu da mallam suna tattaunawa mallam yadubi Kawu yace"inaso dama muzauna tuntuni akan zancen zamanka haka ba Aure banajin dad'i walh kamanyanta ga arxik'i kana samu ba mutuncinki bane zama kai d'aya a katon gida ba mace gara kanemo mace ka Aura ko cikin "yan uwane ko kuwa?

Kawu ya gyara zama yace" insha Allahu kafin musauka zanyi Aure yanxuma akwai k'anwar abokina da mijinta ya rasu takaba take yine munyi magana dashi inta gama takabar zanyi maganar Aurenta

Mallam yayi murmushi"to harnaji dad'i Allah yataimaka

Da Kawu zaitafi dubu hamsin yabaiwa mallam sbd hidimar saukar Aminatu samarin maxan kuma yabisu da dubu ashirin ashirin su inna kuma dubu goma goma yabaiwa su Aminatu biyar biyar

Dama haka yake musu kokowada tasa kyautar inyazo samarin kuwa duk wata yake tura musu da kud'i ta account


Aisha abin duniya yai mata yawa bata iya bacci ba aranar har cikin dare tanata tunanin mafita domin harga Allah baxata iya Auren Ashiruba gashi mummuna gashi Almajiri lallai k'awayenta zasui mata dariya itada take da Auren saurayi mekyau metashen kud'i kamar Adam saikuma suji ta b'ige da Auren k'olo tab A'i walh dole tabi abinda Adam yagaya mata nata zubda cikin tabiyoshi sugudu kano suzauna yanada gida acan

Lallai dole tayi hakan domin baxata iya aikata abinda mallam yaceba aici bayane sosai agunta waima hartayi watanni ak'auye tabdijan! Aisaidai suga bata gidan dama ta nuna ta amince ne kawai dansu kyaleta

Tajuya takalli k'anwar ta Aminatu datake ta baccinta cikin nutsuwa hankali kwance batada damuwa saitaji inama itace Aminatun......


~*Auntyn Sayyada da shahida*~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘


~*Pg 21-22*~

Ana gobe saukar su Teemah ranar Asabar Knn su hajy Lubna da mijinta Alh mansur suka sauka a Nigeria d'aki guda aka ware musu domin zasu dad'e sai sunyi wata kafin sukoma Dan hutun aiki ya d'auka sbd ya dad'e rabon shi da Nigeria yanaso yazaga "yanuwansa

Gida yafara cika da baki " yan taya murnar saukar karatu "yan uwan momy sun zozxo domin zasu tayata Aikin abinci da abin rabo su snacks agobe Sunday

Yaya deen zunzurutun kud'i ya k'arawa momy domin yaga irin hidimar data shirya natarar baki sbd za,ayi walima bayan andawo daga Na islamiyyar


Da yamma su Teemah suka shirya ckn kwalliya zasuje yin lalle da gyaran kai gun madam Linda datake a unguwar sabon gari ta iya saloon da kitso iri iri inda gashinka kk so zata mk koda attach


Teemah tana gaban motar Yaya deen yana janta suna tafe suna tad'insu ckn jin dad'i suna nishadi motarsa ce agaba sai motar dady da Hussain yakeja feenah tana kusa dashi su hassan da Nabeehat suna baya

Har k'ofar shagon me saloon suka diresu sannan suka tafi sukuma yawon bud'e ido abinsu kafin su dawo d'aukarsu

Teemah tanada gashi bayan tashiga saloon aka yaryara mata kitso k'anana har gadon baya ya zubo yai mata

Itako feenah gwanar " yan saka gashin doki anyi mata kitso dashi da ja da bak'i Ne yai kyau yaxo mata har gadon baya cikas d'aya daba gashin ta bane Amma dake tasaba sawa yai mata kyau

Nabeehat kuwa gyaran gashin kawai aka mata tagaban goshin aka tsagashi ya kwanta yai lup sai shek'i yake itama ba laifi akwai shi

Sunci k'unshi ja da bak'i yafi yiwa Teemah kyau domin farace tafi Nabeehat fari dukda Nabeehat d'inma tanada haske

Sai k'arfe shida suka dawo d'aukarsu

Acikin mota Yaya deen sai yaba k'unshin Teemah yake"wannan rana inajinta tamkar ta Auren mu my Teemah ga wannan k'unshi da kk yi tamkar Amarya gaskiya kinyi kyau sai kyalli kk.

Tayi murmushi tace "nagode"

Yace"wannan kitson yayi kyaufa dafatan da zallan gashinmu akai mana ba mis.

Takad'a idanu tace"lallai Yaya nizan bari asamin gashin dokine,haba da hankalina nasan baya sallah da iya nawa nayi,

Ya gyada kansa yace"gud naji dad'i inmunje gida zanbada kud'in kitson". Tace"duk Wanda kabada jiya"

"Eh A'i k'arawa zanyi sbd an gwangwajeni da yawa,

Tayi dry shima dryr yayi

Itako feenah dasukaje gida suka keb'e a balcony itada Hussain suna zaune kan fararen kujeru suna hirarsu suna raha yakalli k'unshin yace" walh inason inga mace tayi wannan zanen ahannunta gashi yai matuk'ar yi miki kyau yaukam a Amarya nake kallonki..

Tayi fari tana murmushi tace"da gaske my only? Kai Amma naji dad'i,to kitson fa ko baiyi kyauba?

Yakalli kanta data zame d'an gyalen data yafa yace"hhhmmm shikad'aine yai cikas sbd naga anyi algus anhad'a da isgar doki nikuma bana son inga mace da gashinta tanasaka gashin dokin nan walh kobakida gashi gara kiyi da naki saikinfi burgeni Amma kamar bakida ilimi zaki tsaya Joni,a,a Sam indai kinasona dole adaina Joni Dan bazamu shirya ba

Tun kafin yayi shiru ta had'e rai ta juya fuskarta gefe taji haushin kalamansa matuk'a aiko bai isaba Dan ita ba,a mata dole

Yace"yadaga magana za,a canxan fuska Alhalin gaskiya nafad'a kuma tsarina Knn,

Tace"to aikaine daga kwalliya da attach saikace min wani banda ilimi Alhalin ba dawwama dashi zanyi akainaba,nariga kuma nasaba baxan iya dainawa ba gaskiya banji dad'in abinda kaiminba,

Tafad'a ranta ab'ace ta had'a girar dama data k'asa

Shima sai ransa ya b'ace lallai dole sai yayi da gaske akan feenah don a"yan kwanakin nan yafara gano halayyarta

Yace"gaskiya ce nafad'a mk kuma dole kiji ki d'auka amatsayina Na Wanda zai Aureki inbaki tankwasu tun ananba sai a ina, inhar kina sona dole kibi abinda duk nace inba hakaba kowa Yakama gabansa(yasan tana sonsa yanzu shiyasa yagwadata yafadi hakan)

Ta zumb'ura baki tace"aiko dai walh nariga nasaba babu mehanani nayi kwalliya dashi bazakamin doleba garama kasani tun yanxu Ni ba,amin dole tana gama fad'ar haka ta mik'e tabashi guri

Yak'ura mata ido yana kallonta ta tafi bai tsaida taba don shima yad'au zafi yanda tad'auka tabbas dole yatsaya tsayin daka yai da gaske akanta don baxai d'auki raini ba.


***** **** ***** *****

Ranar sauka a islamiyyarsu Teemah ancika mak'il da masu sarauta da manyan masu kud'i da manyan "yan kasuwa da manyan lauyoyi ciki harda Hajiya Salma datazo da tata gudunmawar donta rabawa " yan sauka

"Yan sauka Na zaune acan gefe guda cikin tasu rumfar kowacce tasha hijab har k'asa wasu sun saka nik'ab afuska wasu kuma basu sakaba

Mata goma sha biyarne zasui saukar kowacce iyayanta SDA " yan Uwata suna gurin iyayan Teemah da yanuwa kowa yana gun ckn farin ciki bayama momy da take alfahari da wannan ranar domin Allah yasako mata wata muguwar k'aunar Teemah ayau tana alfahari da ita tabbas Teemah kyautar Allah ce agunsu gashi tafiye musu Yr cikin su tazama Yr baiwa wacce za ai fahari da ita Dan bakowa kesamun wannan baiwarba sai Wanda Allah yaso sauka ta biyu dantafarko ba ai taroba sai yanxu da sukai saukar hadda

Ankira kowacce d'aliba tafuto tayi karatu Na bak'ara takoma Teemah itace mace ta farko da aka fara kira agun taringa rera karatun alqur,ani me girma ckn murya me dad'in gaske bayama gurin da kowa yai shiru tsikar jiki taringa tashi kowa yana kallonta cikin so da qauna hajiya Salma taringa jin wani Abu yana mata yawo aka tarin ga jin faduwar gaba haka kurum takurawa Teemah ido tana kallonta qaunar yarinyar taringa tsarga mata saitake ganin kamanninta da mai gidanta har lotsawar dimple d'in tabbas ayau saitaji inama "yarta tananan ace itace agun saukar nan itama ko datayi alfahari kamar yanda iyayanta yarannan sukai ayau

Hawaye ya surnano mata tayi saurin gogewa sbd kada abokan aikinta sugani ga k'awarta babbar lauya kusa da ita Hjy zulaihat zata iya tuhumarta damuwarta itako wannan sirrine dako iyayanta basu saniba domin tasan ta tafka babban kuskure Wanda har ila yau suke nadamar shi har Allah ya jarabcesu da rashin haihuwa akan hakan mijinta yafita nadamar abinda sukayi abaya


Da akaxo rabon kyaututtuka Na alqur,ani me girma sai 2Teemah nafitowa karb'a haka hadisai tasamu kyautarsa itace taxo ta 1 a d'alibai masu kaifin basira da tsafta haka da akaxo bada rabon kyautar da hajiya Salma takawo aka fara kiran *Fateema Lurwan*

Hjy Salma da kanta zata raba musu Dan haka tad'auko ta mik'awa Teemah kenan hannun da Teemah ta mik'o domin karb'a aiko idon Hjy Salma yaci karo da zob'en dake Teemah tai tsai da atamfar bata bataba tana kallon zoben ba shakka babu musu wannan zoben d'an uwan zoben dake hannun mijin tane duk yadda akai wannan yarinyar " yar tace tabbas jini ya nuna tunda taxo dama take kallonta gabanta Na bugawa akanta jikinta ya bata banu Tantama duk inda fateema ta fito to itace d'iyarta data yar shekara da shekaru......



_Muje zuwa_

~*Auntyn Sayyada da shahida*~💘
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘


~*Pg 23-24*~

Saida Teemah tayi gyaran murya kana Hjy Salma tadawo daga d'an tunanin data tafi Na sakanni murmushi tasakarwa Teemah sannan ta mik'a mata atamfar takarba da gdy ta juya tabita da kallon k'auna tana ayyana wani Abu a ckn ranta kana aka kira d'aliba ta gaba da zata zo takarb'i tata kyautar

Sam Teemah bata San Hjy salmace mahaifiyar Yaya deenba don ko a hoto bata tab'a ganintaba

Haka Hjy salman batasan da cewar Teemah ce surukartaba Yr Hjy maryam dake rik'e da d'anta saif

Shiko deen dake zaune agefe dad'i ne yacikashi ganin mahaifiyarsa taxiyarci gurin saukar masoyiyarsa harma tana raba musu kyautuka

Koda Teemah takoma taxauna tunanine fal acknta da mamaki naganin wannnan matar data basu atamfa kyauta ta tsaya kallonta k'ura mata idon datayine yabata mamaki hardayi mata murmushi gashi taga bahaka tayiwa sauran dasukaje karb'ar atamfarba toko tasan tane? tokoma dai meye akwai haduwar jini itama taji son matar ackn ranta taji inama akwai dangantaka atsakaninsu

K'arfe biyar da Rabi aka tashi Wanda aka farashi k'arfe hudu

Babbar d'alibar da akeji da ita Fateema Lurwan wacce ta bud'e taron da addu,a hakama yanxu

Please Login or Register in order to submit comment