You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wuri

Aminatu k'anwace agunta tsiransu shekaru uku Amma tafita tunani da hangen nesa haka zakuga tasaka yayarta agaba tanΓ  mata fad'a akan tarage abinda takeyi Sauda yawa indare yayi inna A,i takanxo dubata d'akin taga ko tananan sai Aminatu takareta tace tana band'aki ko tacetafuta zance yanxu zata dawo sbd innarce meyi mata fad'a kuma tafi shakkar inna A,i akan inna halimar sbd inna halima takanyi mata karar faranci.

Wannan hali Na Aisha yanaciwa Aminatu rai tana shiga damuwa sosai akan haka ita gudunta kada " yan unguwar sugano yanda take yyawon dare tana zuwa gun namiji yana futa da ita kokuma tad'aukowa mallam abin kunya....

Tabdijan! Wannan shi ake kirada d'an mallam yak'i halin mallam!(Allah ya kiyaye)


~*Auntyn Sayyada*~πŸ’˜
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜



~*Pg 8...*~

Alokacin da Aminatu ta shiga SS2 sai furifofin SS3 suka matsa mata lamba domin surama abinda yayarta tai musu dasunga tahowarta zasu rufe gate sufara kamen latti akanta insunkai sugoma ko fi haka za,a shata musu guri meyawan gaske ace su share haka zatayi ita kad'ai Dan sauran guduwa suke ko ace suyi picking k'arshe itake tsincenta abokan lattinta suzame subarta dayake kuma ita d'in dai akeson azabtarwa basayiwa wad'ancan komai

Ayyukan wahala dai iriΒ² Itace har wankin toilet Amma bata tab'a yi musu gardamaba domin inta gamama zuwa take tasamesu tace"Aunty nagama saime kuma zanyi muku?

Masu imanin ciki tausayin ta suka hauji dole dai suka d'aga mata k'afa domin tana basu girmansu duk inda zatagansu saita gaishesu dole tasa suka dawo lelenta

Tasami shiga SS3 suna tsaka da rubuta waec aka tsaida musu lokacin dazasuyi sauka taxo daidai da candynsu

Wata WeekEnd da yamma tasami Yaya baffa ad'akinsa yana zaune akan kujera yana danna laptop yana ganinta ya turar da lap d'in gefe yana murmushi yace mata"Aminatu Autar mata,Aminatu Autar mallam,akwai magana me dad'i Knn naga kina fara,a

Tasami guri tazauna tana murmushi tace"barka da hutawa yayana"

Yace"yawwa Sayyada Aminatu uwar "yayana"

Tayi murmushi akaro nabiyu tace"Yaya naxo ingaya maka antsayar mana da ranar saukar mu daidai da ranar candynmu bakwai ga watan july Dan haka naxo mushirya Tsare tsaren abinda za,ayi agun walima.


.yanisa yace"Nafi kowa murna da wannan ranar Aminatu tabbas nayi dace dasamun uwar "Yaya metarin ilimin addini Dana bokonma walh ke " yar baiwace kinyi sauka gashi zaki sake wata saukar ta hadda tabbas dolene Na bud'e bakin aljihu nahidimta miki Aminatu,

Bayan kundawo dg walimar makaranta za,ayi wata a k'ofar gidan nan sannan za,a gayyaci manyan malamai da attajirai za,ayi karatun alqur,ani me girma za,ayi sitaka da memo zakuma ayo calanda da key holders narabo...."haba Yaya abin yayi yawa ai,duk nikad'ai?

Yace'kwarai kuwa Aikin cancanci haka koma fin haka,barima nasanarwa Kawu tun wuri yasani sbd shima yayo nasa gayyar da gudunmawar,

Tayi dry tace"kai gand'oki"

"Ainafi gand'okima ba dole nayiba saukar matatafa za,ayi maxama jeki shiryo muje inkaiki ayi miki hotunan da za,ayi abubuwan rabon Dana lissafo

Ta mik'e tana fad'in" to bari naje Na fad'owa su inna.

Hotuna kala goma akai mata kowanne yayi kyau suna tsaye aka wanke aka basu saidai sunsha kud'i duk daya d'ari uku Haka ya lale yabiya suka dawo gida saida yacake kud'in da za,a bud'a masa guda biyu

Dasuka dawo Aisha tana tsakar gidan tabisu da wata muguwar harara ana kallon hotuna su inna ana yabawa taja tsaki takoma d'aki

Aranar tasami mallam yana d'akinsa yanacin abinci inna A,i nakusa dashi tanemi guri tazauna bayan tagaidashi tayi shiru

Yace"yadai Aishatun nabiyyi akwai wani abunne?

Ta d'aga kanta tace"akwai mallam "

Yace"inajinki to fad'i "

Ta muskuta tace"dama mallam Akan zancen karatuna ne naxo neman alfarma inaso inci gaba dakaratu kona shekara biyune nasami diploma.

Mallam ya girgixa kai yace"kiyi hkr Aisha baxaki sami wannan alfarmar agunaba domin banida ra,ayin barin "ya mace agabana ta xurfafa karatu,balle ked'innan inasane da duk abinda kikeyi addu,a nake binki dashi ana zuwa ana fadamin komai jira nake nagani da kaina shiyasa nayi shiru naxuba mk ido,adalilin haka Na hanaki Jan motar da kawunki yabaki sbd naga har yanxu hankali baigama binjikin kiba har k'anwarki tafiki nutsuwa da kamun kai ko daga irin shigar da kk ga ilimin addini data fiki hakan baxaisa kiyiwa kanki fad'aba ko gyara kfn agaya mk,

To walh kisani lokaci nabaki zuwa nanda lokacin da " yar,uwarki Ummie zata kammala karatunta wata biyu kawai zan d'eba miki kifito da miji inyi auranku arana d'aya tunda ita naga sundaidaita da baffa Dan haka kisani inhar baki Kawo mijiba to walh zanbaki komawane a ckn manyan almajiraina tunda kuma narantse babu d'agun k'afa maxa kitashi ficen ad'aki Mara aiki da lissafi

Tunda mallam yafara wannan mgnr hawaye kawai take xubdawa takalleshi idonta jajir tace"walh mallam inaso inyi karatu kayi hkr innagama nafuto da Mijin...

"Yimin shiru anan ja,ira dama nasan kinaso mana tunda gashi kinxomin da zancen har muna ja,inja dake,ahakama baki kama mutuncinki ba kinaso kinunawa duniya cewar kingagareni inaga nabarki kina futa karatu, kinga alokacin wuyanki ya isa yanka Knn?

Inna A,i tace" mallam kayi hkr ka sassauta....ya d'aga mata hannu kurum tayi tsit bata k'arasaba

Aisha ta mik'e fuuu! Tai waje tana kuka inna A'i ta mik'e tabi bayanta

Tasameta a d'aki tana gunshek'en kuka alokacin Aminatu tana kan sallayarta tana rahazar karatun ta

Inna tace"Aisha kindaiji abinda mallam yace Dan haka Ni abinda zan shawarce anan shine ko gaggauta fito da Mijin Aure ko hakura da zancen wani karatu in Allah Yy zakiyi kyayi a gdn mijinki inajiye mk tunda mallam yai alwashin baki miji ckn almajiransa to walh inhar kk wuce lokacin daya d'eba mk babu mehanashi ya zartar da mk Aure da almajirin nasa... "Walh inna baxan Auri almajirin mallam ba kowaye inko ba hakaba saidai nagudu nabar gidan bayan duniya da fad'i

Inna takai mata duka ta goce tace" Ni zaki duba kice zaki gudu to Dan Allah ga hanya nan karki fasa, Dan kinga anabin kanki tokije daga yau nikuma nacire hannunta akanki xan zuba mk ido tunda HK kika fiso,kuma indai duniya da fad'i kije kishigeta itace dama me koyawa mutane hankali kuma dad'inta dai bake kad'ai bace "yar da zata faranta mana.tana gama fad'ar haka tafuce ranta ab'ace

Aminatu ta girgixa kanta kawai itama yanxu lamarin Na yayarta sai kallo agunta

Ana saura sati d'aya saukarsu Aminatu yarage sauransu jarabawa biyu biology da chemistry kai yad'au zafi danma tanada kwakwalwa kuma tana karatu

Tana lura asatin yanayin yayarta ya sauya kullum bacci ga amai datake yi a d'akin Aminatuce me gyara wa bata tab'a nuna damuwa da hakanba ko gajiyawa Allah sarki " yar,uwa Rabin jiki....


~*Auntyn Sayyada*~πŸ’˜
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


~*Pg 9...*~
Dafarko Aisha taso ta tusa yayar tata agaba ta tambayeta taji meke damunta Amma saita tuna yadda suka k'are akwanakin baya gargadin datayi mata natadaina shiga sabgarta Dan haka saita zuba mata ido kawai

Amma dake tanada wata irin zcy me rauni taringajin tausayin Auntyn tata ganin kwana biyu tana zazzab'i ga yawan amai datakeyi

Aranar datayi kwana uku tana ckn wannan halinne inna A,i takawo mata magani tasha Aminatu taxubo mata abinci dafadukan shinkafa takawo mata dakyar ta iyaci Dan bata iyakai komai bakinta saidai tasha koko ko farauΒ²


Ko gama cin abincin batayiba taji zcyrta natashi kfn ta mik'e amai yataho mata bayanda zatayi tatsunna a k'asan ledar taringa kelayashi

Aminatu tana gefe da littafin biology note Buk ahannunta ta kalleta ckn tausayawa tayi mata sannu sannan ta mik'e tagyara gurin dataga tagama tadawo kusa da ita tana cewa"Aunty wai meke damunkine Wanda bakiso insani,dole dai nice yakamata Nafi kowa jin matsalarki tunda ba zuwa zanyi waje ina terere dakeba,Dan Allah kifad'amin abinda ke damunki domin ina zargin wani Abu akanki

Aisha tace"walh bansan meke damunaba Ummie Dana sani Dana gaya miki,Dan Allah kije ki kiramin mallam akaini asibiti ko akiramin Dr beenat taxo gida tayimin allura ko tasamin ruwa ko zanji sauk'i

Aisha tace"to aunty zanje Amma kafin nan intambayeki mana"

Aisha takalleta kawai bata iya cewa komaiba

"Aunty yaushe rabonki da ganin al,adarki"

Aisha taji gabanta ya fad'i data tunoda kusan wata 2 ma rabonta da yin period

Takalli Aisha tace"meyasa kk yimin wannan tambayar Ummie?

Aminatu tace"sbd ina wani zargi akanki Wanda kuma bana fatan ya tabbata

Aisha ta mirgina kanta tareda dafewa tace"abar wannan zancen Ummie tashi kije Dan Allah Ni nasan yadda nakeji.

Aminatu ta mike tace"to bari naje.

Dasaurinta tafuce daga d'akin hartana tuntub'e ak'ofar d'akin wajen saka takalminta sukai kicib'us da inna halima tafito daga kicin takalli Aminatu tace"Auta ina zakije haka kk sauri?

Amina tace"walh zanje gurin mallam inna insanar dashi yanda jikin Aunty Aisha yamatsa ko za,a kaita asibiti sai amai take yi yau.

Ckn rashin nuna kulawa akan zancen innar tai gaba tana fad'in"Allah ya sawwak'a" (karace irin nafarin nan take nunawa akan Aisha )

Aisha tasami mallam a makaranta ckn Almajiransa yana hangota yataso da sauri yana fad'in"yadai Autar mallam meya faru a gdn?

Tace"walh mallam Aunty Aisha ce jikin nata yau ya matsa mata shine naxo ingaya maka ko za,a kaita asibiti?..

Mallam yace"ashsha Allah ya sauwak'e bari nakira yayanku muntari yaimaxa yaxo akaita asibitin, yana gama fad'ar haka yasa hannunsa a aljihu yad'auko wayarsa yakira Mukhtar yasanar masa


Aisha takoma gida tashiga d'akin inna A'i tatarar sunacin abinci atare tazauna akusa dasu inna A'i tace"ya jikin waccen uwar taurin kan?

Aminatu tace"jikinta yafi Na kullum rikicewa inna yanxuma mallam yace asibiti za,a kaita yakira yaya mukhtar yagaya masa yanxu xaixo Dan Allah kishirya muje.

Inna ta mike tana fad'in"to bari nashirya muje.

Inna halima abincinta kawai takeci hankalinta akwance itako inna A'i jikin ta har b'ari yake Dan rud'ewa

Yaya Mukhtar naxuwa Aminatu tafito mata da kaya tacanxa mata tasaka mata hijab sannan suka kamata suka fito da ita tfyrma kasawa tayi don jikinta yagama macewa sai Aminarce ta kamata inna takamata suka futa da ita suka shiga mota tana jikin su tana faman nishi jikinta zafi rau

Wani prvt hospital mafi kusa sukaje likita yabata gado akasamata ruwa Dan tagalabaita sannan aka shiga yi mata gwajeΒ²

Likitan yabuk'aci ganin inna da Yaya Mukhtar domin yashaida musu sakamakon da suka gani

Matukar bakin ciki inna tashigeshi jin sakamakon yanuna Aisha nad'auke da ciki wata 2 har hawaye ta xubda Dan bata koma takantaba ma tayi waje ta tari d'an sahu takoma gida sbd baxata iya kallon Aisha da bakin cikin dataja musuba Yaya Mukhtar baisan gida ta tafiba shima yaji matukar bakin ciki ransa yaita suya yasami Aminatu ya rattaba mata wannan k'azamin labarin

Itama tashiga rud'u da tashin hankali tak'urawa Aisha ido datake ta baccinta taji tamkar tashak'eta ta mutu kowa ya huta tabbas biri Yy kama da mutum.......


~*Auntyn Sayyada*~πŸ’˜
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_ πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv* Β©πŸ’˜


*KANO...*


~*Pg 10..*~


Da misalin k'arfe takwas Na dare dady yana zaune afalonsa yana kallon tashar *CNN* Hjy maryam ta shigo da sallmarta bayanta teemah da feenah ne ya amsa musu sallamar suka durk'usa kusa gabansa suna masa barka da hutawa yakalli teemah yace"Uwata dama akan maganar saukar kine dazakuyi shiyasa na aika akiraki naji ko antsaida ranar sbd nasan irin shiryeΒ² daxanyi miki.

Teemah tace"k'arshen watan nan ne dady lahadin k'arshen watan anfito mana da ankon shadda purple sai kuma hijab da akace muyi pink colour hark'asa sai kud'in allon zayyana da kud'in walima akace mukai dubu dubu goma shabiyar saikuma abin sadaka da sukace mufadawa iyayanmu duk abinda kayi niyyar yi musu dady suna bukata

Dady yagyara xama tareda rage volume d'in TV yace"yayi kyau duk za,ayi miki abinda kk fad'a insha Allahu agobe ma zansiyo mk shaddar sbd kisamu kibada dinkinta da wuri sannan zansayi saniya nakai musu sadaka fisabilillah haka yayi? Yatambayeta

Tayi murmushi taji dad'i har ckn ranta tagyad'a kanta tace"yayi dady Allah yabiya Allah yasaka da Alkairi,

Itako feenah wani malolo ne yatsaye mata dama sbd teemah akai kiransu aka katse mata chart d'in datakeyi data sanima bataxoba takalli momynta taga itama fuskarta ba annuri

Dady yakalli Hjy maryam ckn fara,a yace"ke momy banji kinfad'i irin taki gudummawar da zakiyiwa "yartakiba Dan nasan tunda macece " yarfari zaki fini bajinta ko? Yafada yana tsattsareta da ido

Ta murmusa tace"sosaima kuwa domin zan d'auki nauyin duk wata cima da za,ayi ackn gidannan Dan dole nima Na shirya mata walima agida kuma akwai wata babbar kyauta Dana tanadar mata wacce bakowane zaijiba harsaina bata ahannunta,tafada tana dry

Shima dryr yayi yana fad'in "a,a toshikenan muma bazamu matsa dole sai munjiba ko feenah,yafada yana kallon feenah tayi murmushi kawai

Dady ya bud'e wata jaka kusa dashi yaciro bandir d'in kud'i yn Dari biyarΒ² yafara mikawa teemah dubu ashirin ne yace" gashi wannan aje ayi siyayyar kayan kwalliya dannasan turare da hoda sunyi low,

Takarb'a tana godiya yamik'awa feenah ma yanda yabaiwa teemah itama takarba tana yin godiya fuskarta fal fara,a ranta yai k'al

Anan suka tashi suka barsu momy afalon suka koma d'akunansu


*********

Washe gari ahanyar zuwnta sch tana ckn motar Yaya deen yana tuk'i yanashan kid'an wakar celindion yana bin wakar itakuma tajingina kanta ajikinta kujera tayi shiru sbd ita music bai dametaba yarage volemu yakalleta yace"ya akaine my teemah?

Tace masa"bakomai menene?

Yace"naga kinyi shiru kina tunani "
Tagirgiza kanta tace"batunani nakeba "

Yace"OK yau saura kwana nawa saukar taku?

Tace "k'arshen watane"

Yace "OK to yakamata fa inkaiki ki gaida Ummana before tym d'in domin tayimin waya lokacin muna London ta taho gidanmu donsu gaisa da momy sundade basu haduba tace nataho nasata ahanyar gidan shine nace mata bama gari donhaka kishirya nakaiki kigaisheta dantasan da zancenki nafison kafin tazo gidan kifara kaimata gaisuwarki kokuwa?

Yafada yana murmushi yana d'aga mata gira

Tayi murmushi tace" yanxu har zancen soyayyar mu yakai kunnenta Dan Allah bakaji kunyar fad'a mataba haba kana Dan fari"

Yayi murmushi yace"Dan fari kuma d'aya tilo ba,tunda banda wa ko k'ani don agidan Mijin natama har yanxu bata haihu dashiba,

Teemah tace"kai aini naxaci kamar momy tace tataba yi mata waya cewar ta haihu d'anba rai,

Yace'to aiku mata inkuna aiki bason Tara yara kukeba maybe itama tana bin wannan tsarin ne

Tace"kada kai mata wannan zargin may be Allah ne baikawo matanba,

Yace "yanxu ke Dan ina d'an fari sai Inji kunyar fadawa Uwata nasami wacce nakeso zan Aura tab,to duk irin son da nake miki saida nazayyane mata

Teemah takama baki tace" wuuu! Lallai aikodai kunyar ta nakeji anya zan iya zuwa kuwa?

Yace"dolema kuwa danhaka a week End dinnanma zamuje asabar ko lahadi tunda bana xw aiki kekuma ba sch saiki shirya dab zuwanki wajib ne

Tace"to Allah yakaimu"
Yace"amin,


*___________________*


Da daddare teemah nakwance ad'akinta kan k'aton gadonta dayasha luntsumemiyar katifarta metaushi saijuyi take ckn jin dad'i tana chart da Yy deen da kuma Yr uwa Rabin jiki Nabeehat sai zuba murmushi take daganinta ackn nishad'i take momy tayi sallama tashigo d'akin nata

Dasauri Teemah ta ajiye wayar gefe tareda Amsa sallamar momyn

Hjy maryam tace"Teemah Yr gatan dady ga shaddarki nan harya Kawo miki gexna ce ta dubunnan kudad'e yace kikai d'inki ayi miki kona dubu nawane dadynki dai yanaso kifita daban ckn "yan sauka

Teemah takarb'i shaddar tana murmushi tace" kai Amma tayi kyau momy naji dad'i kitayani yin godiya ga dady Amma fa ya iya zab'e kamar tare kukaje

Hjy maryam tace"to nima gatawa gudunmawar"

Tamik'awa teemah zoben gwal Dana azurfa (tun Wanda suka tsinci teeman dashi ne)

Teemah ckn jin dad'i takarba tasaka atsanta tana murna sunyi mata cif,

"Kai momy naji dad'i nagode Allah yakara bud'i"

Hjy maryam tayi murmushi tace"to amin,yayanku deen yacemin ranar Asabar zaikaiki gidan Hjy Salma tonace masa harda feenah zakuje itama taje ta gaisheta tunda babu Wanda tasani cknku

Teemah tace "to momy Allah yakaimu"

"Amin, tace tareda futa daga d'akin tabar teemah tanata juya hannunta tana kallon zoben bawai Na gwal d'in ne yad'au hankalintaba Na zurfar ne Dan nagwal tanadashi Momyn ta tab'a sai musu itada feenah Amma baikai wannan tsadar da girma tun suna secondry

Ajikin axurfar ansaka harafin *SK* wannan sunan ne yad'auki hankalinta domin batasan me hakan ke nufiba sbd tasan dai farkon sunan iyayanta babu wannan harafin haka natama

Tarasa gane me wannan harafin kenufi dole tahakura tabar tunanin Neman ba,asin sanin sunan domin batada Wanda zata Tambaya don ita batada yawan tambayeΒ² don magana ma ba damunta tayiba.....


~*Auntyn Sayyada da Shahida*~πŸ’˜
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_ πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


~*Pg 11-12*~

Aranar Asabar kamar yadda aka tsara tfy gidan Hjy Salma wajen 11:am suka gama shirinsu

Kamar had'in baki teemah shadda tasaka ruwan Zuma haka shima deen shaddarsa ruwan zuman ce saidai tasa light ce tata kuma dark colour ce, doguwar rigace shaf d'in rigar yakamata sosai yafito da cake din breast d'inta cif,Aikin rigar har k'asa aka kawo shi kalar ruwan madara gyalen datasaka ma ruwan madarar ne flat shoe ne ak"'afarta donbata saka me tsini d'an kunnen tama Yr barimace me stone din farar danja

Kwalliyar datayi simple ce bata tsaya k'ak'aleΒ² ba Dan farar hoda tasakama sai weat lips batayi jagiraba domin gashin girarta bak'ine sid'ik cikakke saidai ta tajeshi ya kwanta luf kanfatar yai kyau,

Tayi kyau sosai dukda batayi make up sosaiba domin tana ganin zata gun suruka bai kamata tacika fuskarta da kwalliyaba kartaga tafiye gwalli donbashine da itanba

Turare kala 2 tafesa da _you and me_ da kuma _one Luv_ turarenta kenan ko yaushe sunada matukar k'amshi mesanyin gaske

Itako feenah fuskarnan kamar za,a saketa sai shek'i take anci pondetion dasu eye-shadow da eye liner da jagirarnan da ake yayi janbakin nan anrabaja shi bajau fakistan tasaka sky blue da kwalliyar stone agaban rigar

Riga da wandone rigar har guiwa take me shape a saman k'irji da d'an gyalen rigar ta ratayashi a kafad'a hancinta ta manna barima kamar a indiya dama itama ga hanci dogo kamar biro balaifi tayi kyau sosai Amma bata kai Teemah ba

Teemah tafuto falon ta tarar da feenah zaune ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tasaka ear peace akunnenta tanashan kid'a tanata latseΒ² awayr takalli teemah kallo 1 tad'auke kanta

Itako teemah murmushi tayi tazauna ahannun kujerar da feenar take tace" _wow my sister ur dress is fine_

Bata kalletaba tace atak'aice _tank u_

Teemah tace mata "Yaya fa kobai gama shirin nasaba?

Still dai bata kalle tanba ckn rashin kulawar tace mata " kije kigano"



Teemah tace"basainaje ba bari natab'o shi awaya
Tai dialin d'in wayrsa bugu d'aya yad'aga "kungama shirin nakune?

Tace " eh kana d'akine?

"A,a gani a wajen motata iliya yana wankemin ita kufito yama gama muwuce kawai"

Tace"to"
Tana kace wayar takalli feenah tace"yana waje yace mufito mutafi'

Momyce tafuto da wasanta tace"ymmatan momy kunyi kyaufa"

Dukansu suka dara Hjy maryam tace"inkuje kugaisarmin da ita kuce ina nan tafe nima nan gaba zansa deen yakaini mugaisa tunda ita tayardani"

Suka mike suna fad'in to zataji" suka fita

A cikin mota zcyr feenah tamkar tafashe Dan haushi da tuk'ik'in kishi naganin irin ankon da Yaya deen da teemah sukai gani tayima kamar da gayya sukayi dantaji haushi taji inama bata amsawa momy cewar zata bisunba dabataga wannan takaicinba

Suna gaban mota sunata hirarsu ta masoya deen yanata yaba kwalliyar da teeman tayi

Itako feenah tana gdn baya tasan duk Dan taji haushi Yy deen ke mata hakan tunda yasan har yanxun tana sonsa takasa cireshi aranta dukda Hussain ya nace kullum yana koro mata kalaman soyayya da k'ok'on bararsa ta waya yanxuma dashi suke chart yana gaya mata yakusa zuwa Nigeria sbd ita

Yy deen ya waigo takalleta ckn zolaya yace"yadai "yar k'anwat yana jiki shiru ko ciwon hak'ori kk?

Ta watsa masa wani kallo tace" mekakeso nace bawani ciwon hako'ri danake hankalina yana nan ina chart da masoyinta Hussain yana online "

Deen yace"ah! Lallai abin naku yayi nisa Knn aimu haka muke so gara da kuka k'ulle kinga in antashi biki sai ahad'a danamu ko my queen teemah? Ya fad'a yana kallon teemah da taketa zuba murmushi

Itako feenah banxa tayi dashi domin k'ara k'ularta Yy

A k'ofar gidan Hjy Salma ya faka motar babban gidane mekyau yamatsa hon megadin yabud'e Yalek'o da kansa ganin deen ne yasa yataho da saurinsa suka gaisa yace"saidai hajiyar batanan yanxun nan tafuta"

Deen yace"tafuta kuma? Tafa San da zuwanmu toya akai haka bata kiraniba"

Bala megadin yace"eh to gaskiya naga kamar saurima take da alama ko futar ta gaggawa ce ko gun Aikin aka nemeta,

Deen yace"OK bari nakirata" yaciro wayarsa yakira umman tasa saida yai mata 2missed call bata d'agaba can kuma yn sakanni saiga kiranta yashigo yad'aga suka gaisa tace"Saif harkunxo?

Deen yace"gamu a bakin gate ma baba me gadi yace kin fita yanxu"

Tace"eh walh futar dole ce wani case aka turo daga Abuja babban case ne ahannuna aka dank'ashi shine akaimin waya naxo yanxu akansa za,a zauna kabaiwa surukar tawa hkr kada natsaida Ku Dan banajin zamu tashi da wuri sai wjn yamma zanxo gidan naku nima

Yace"kada ki zamu Umma munyi miki uziri bari nakaisu gidansu inna sugaisa momy ma tace zataxo madawo latter kawai

Tace"yawwa to Shikenan ma" sukai sallama yakashe

Nan yake gaya musu yanda sukai da Hjy salman teemah ta gyada kanta dukda taso sugaisa da umman Amma ba yanda zatayi dole su hakura sai wataran d'in

Yakaisu gidansu inna tsoffin arxik'i suka ringa nan nan da teemah sunga matar da jika zai aura inna tabata tsaraba tace takaiwa momynta basu dadeba sukai musu sallama ya daukesu donya maidasu gida....


~*Auntyn Sayyada da Shahida*~πŸ’˜
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


_ina mai baiwa masoyana hkr asakamakon jina shiru banyi type ba wayarce takawon matsala_ _adalilin haka har wata tana bina prvt tana gayamin bak'ar magana akan tace naturo mata da novel d'ina wai nashareta Dan haka insani bani kad'aice marubuciya a Nigeria ba danma nasamu ana son nvl d'ina_ _wasu mutanen basa yiwa "yanuwansu musulmai uxuri d'an Adam fa ajizine_......


~*Pg 13-14*~

Bayan Sati guda daxuwansu gdn Hjy Salma momy kuma tasake saka musu ranar da za,a koma har itan.

Da kanta takira Hjy salman ta jaddada mata zuwansu Dan kar asamu sab'ani

Da ranar zuwan nasu taxo kowa ya shirya za ,a tafi sai teemah ce suka jita shiru bata fitoba momy dakanta tashiga d'akin nata ta tararta dafe da Mara tana juyi agado

Hjy maryam ta tsaya akanta tana tambayarta ko lfy taganta haka

Teemah tace" walh momy marata kemin ciwo tun dazu,

Hjy maryam tace"to basaiki fad'aba kyayi shiru ad'aki mu munacan munata jiranki kitashi kisha magani inyaso saiki daure muje karmu barki ke d'aya agidan

Teemah tace"momy kuje kawai baxan iya zuwaba kugaisar min da Umman nasha magani d'azu inba bacci nasamuba baxai lafaba nasaba duk wata inyi wannan wahalar dama

"Hala period d'inne"?

Gyada kai teeman tayi kawai

" kinada always ko in d'auko miki ?

"Akwai momy"

Hjy maryam tajuya tafara tfy tana fad'in "tomun tafi Allah yasauwaka," amin,adawo lfy"


Bayan futar momy bacci yakwashe teemah saida tafarka tad'au wayarta taga kiran da deen yai mata hr 3 missed call

Tayi murmushi tasan dole zaikira dama,takirashi saida takatse sannan yakirata tad'aga muryarta a sanyaye tai masa sallama

Ya amsa yana fad'in"nakikkiraki naji baki d'agaba ko duk zafin ciwon ne?

Tace"walh bansan ka kirabama baccine yakwasheni saiyanxun Na farka "toya jikin?"

Ta lumshe ido tace"da sauk'i sosai ina Umman tamu ya kuka sameta?

Yace"ga Umma tanata tambayarki nagaya mata ciwon mata kk"

Tayi dry harda rufe idonta kamar yana gun"kai Yaya Amma dai dawasa kake yi ko?
Yace"kamar Yaya da wasa?

Tace"Dan Allah da gaske kafad'i hakan?

Yace"gata ai zanbaki ita kugaisa"
Tace"Ni walh kunyarta nakeji balle kagaya mata haka"

Yace "tosaime itafa Yr uwar kice mace,Ni meyasa bakiji kunyataba?

Tace" aibani nagaya makaba nasan abakin momy kaji,

Yace"OK to bari naje Na mik'awa Umman gasucan afalo da momy suna zuba hira futowa nayi nabarsu muma yanxu zamu taho sbd munbarki ke d'aya agida baxanso adad'eba,

Tayi murmushi tace"to Allah ya dawo daku lfy,kawai kagaidamin Umman ba saika bani itanba Allah Yy da gaske inajin nauyinta,

Yace"da wasa fa nake mk bangaya mata komaiba,

Tana rik'e da wayr yaje yakaiwa Hjy Salma takarba takara akunneta suka gaisa duk akunyace teeman take ita kuwa dayake wayayyiyace saihira taja teeman dashi"Teemah kinxo munyi sab'ani yau kuma Allah baiyi zakizo muganaba naji momynki tace bakida lfy' toya jikin?

Ckn jin kunya teemah tace"da sauk'i Ummah ya Aiki?

Hjy Salma tace"Alhamdulillah ai insha Allahu zanzo walimar saukarku Dan shugaban makarantar taku dan,uwan Alkalin mune kuma tunda har anfada min dake aciki kodanke zanzo d'iyata

Teemah tace"to Ummah Allah yabada ikon Zuwa ngd"

Sukai sallama yakarba yace"kikula da kanki kafin mudawo"

Tace"to Allah yadawo daku lfy,

Sukai sallama yakashe

**********************

Ana saura sati d'aya saukar su teemah "yan London suka dira agidan twins ne da Nabeehat kawai banda iyayansu su sai ana gobe sauka zasu diro,

Nabeehat a d'akin mutuniyarta teemah tasauka sunata murnar ganin juna balaifi feenah ta shiga cikin su tasake bakamar daba datake ad'arere tana sha musu k'amshi kamar wata bare acknsu

Adarenma suna tare a

Please Login or Register in order to submit comment