You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zayyanewa mallam komai harkawowar abinda yaiwa Aishar da motar
Daya bata ta alkawarin abinda yai mata.

Sosai mallam ya shiga firgici da wanga zance lallai duniya abin tsoro

Yakalli kawu yace"yanxu duk kai kayi wannan tabargazar da hamkalinka da komai? Haba Ibrahim amma baka kyauta was kankaba,Ashe Kaine silar lalacewar Aisha tabbas kayiwa Allah laifi dolene ya tuhumeka gashinan ai tun ba,aje koinaba kaga abinda ka aikata da idonka kayi gaggawar kadaita da Allah kanefi yafiyarsa ka kasance a kullum kana Neman tuba gun Allah nidai nayafe maka tunda babu yanda zanyi aikin gama ya gama saifatan Allah yadawo min da "yata gida zansaka Almajirai suringa tayani addu,a akanta akan Allah ya juyomin Hankalinta ta dawo gida

Mallam ya dafe kansa yace" kai wannan duniya cike take da *cakwakiyar zamani* yanxu ace k'anin uba ya Tara da "yar yayansa? Hodijan Allah kasa mu dace...

******* *******
Anata hidindimun biki angawaye sun gama lefe domin kowannensu Yakama aikinsa yana samun nakansa daidai gwargwado

Yaya baffa yana Abuja kullum yana manne da Aminatunsa ta waya tana zuba masa shagwab'a ita lallai tagaji yadawo tayi missing dinsa

Shikuwa lallab'ata kawai yake Dan jiyake da ita kamar kwai.

Asatin bikin ya d'auki hutun Aiki saigashi ya diro Kaduna baisanar da itaba Yaya suraj kawai da Mukhtar yasanarwa suma aranar sukai masa waya amotarsa ya dawo Aminatu murna kamar me!
Harsaida inna A,i tace da ita" ke d'okin mazallak'o kiyi ahankali kada yagano kinmatsu da son ganinsa mana kodai mubashi ke yatafi dake,

Kamar tace mata 'eh inna,Amma saita dake don tanada kunya taringa murmushi bata tankawa innarba

Sun dad'e tare ana hirar yaushe gamo ta masoya saiyaga Aminatun tak'ara wani kyau sai shek'i take kodon tayi gyaran jiki

Ana saura kwana biyu d'aurin Aure baffa da Aminatu suna tsakar gida kan tabarma suna hira wajen takwas da rabi Na dare saijin sallamar Mace sukayi tashigo gidan tana rab'ewa Aisha ce!

Zabura Aminatu tayita tafi aguje kamar zata fad'i tarumgumeta tana fadin"Aunty Aisha kece"?

Baffa kallonta kawai yake yana mamakin ta lallai Aisha duniya ta koyarta Knn.


Matan gidan suka fito da sauri suga wacce Aishan

Inna halima ta nuna mata hanyar waje "maza ki fita kada ki tunkaromu kinemi wasu iyayan munyafeki

Aisha tasa kuma" inna kuyafemin nayi nadama natuba bazan sakeba

Inna A'i. Taje takamo hannunta takaita d'akin mallam yana kwance yaji shigowarsu yatashi zaune yak'ura mata idanu tanata goge hawayenta ta durkusa agabansa tana kuka tana Neman yafiya

Murmushi mallam yayi yaji dadin dawowarta lallai addu,a bata fad'uwa k'asa banxa yace"daina kuka tunda Allah yadawo dake kingane kuranki nayafe mk Allah Ya yafemiu gaba d'aya tashi kuje saida safe za,a zauna akanki inkowa yazo,

Ta mike tana matsar kwallah ta futa

××××× ××××× ××××××

Da safe kowa ya hallara har kawu mallam yace"ga Aisha ta dawo tace ta tuba tayi nadama nikuma nayafe mata akan wani b'oyayyen dalili Dan Allah yana yafiya agaremu

Sannan kuma inaso Ku yafe mata

Inna halima tace"shikenan mallam nayafe mata Amma yatayi da cikin jikn nata?

Aisha tace"hatsari mukayi nida Adam yarasu nikuma cikn ya zube nayi jinya ne nasha wahala sosai

Kawu yace"Allah ya kiyaye gaba Aisha munyafe mk muma kiyafe mana,

Tagane nufinsa wato shima yayi nadama Knn,

Ta durk'usa agaban mallam tace"mallam Na amince Na mik'a wuya ka Auramin Ashiru zanyi zaman Aure dashi da zcy d'aya,

Murmushi mllm yayi yace"toshikenan Amma kin faranta min rai sai ahada da nasu baffa jibi A d'aura allah ya sanya Alheri.

Dukkansu sukace Amin!'"


Muma muce Amin!!!!

👏🏼👏🏼🙌🏼bissalam

Saimun had'u asabon Nvl dina inda ranmu da lfy bayan sallah


~*Auntyn Sayyada da shahidah*~💘
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_👉🏼 *Nabilancy Luv*©💘


~*pg 40-41*~
A can gdn Aunty Amina kuwa Da isarsu ta taresu da murnarta tasa me aikinta ta Kawo musu abin motsa baki

Taita kallon Teemah kamar tayi magana dai amma saitayi shiru teemah ma dai kallonta take taji aunty Aminar ta burgeta don ta iya karb'ar bak'i gata da raha

Bayan angaggaisa Hjy salma tace da ita"Aunty munxo mk da wata magana me karfi wacce muka b'oye mk ita tun a farko

Aunty Amina ta gyara zama tana saurare

Alh kamal shiya fara koro mata jawabin yadda abin yake kana Hjy salma ta cafe ta k'arasa

Aiko dai Aunty Amina tasha mamaki takasa magana ta kurawa teemah idanu tana hango tsantsar kama da take da d'an,uwanta itakanta tasha jinin jikinta don tayi kama da d'iyarta da take boarding sch Nana faty,"yar shaekara 18 tana year d'inta ta k'arshe

"Allah Almusawwiru Ashe haka abin yake? Amma dai naga laifinki Salma da baki iya gaya min halin da kk cikiba,kk biyewa soyayyar miji kk sab'awa zcyrki sannan da ace kinshiga wani halin kumafa ya zakiyi? Yanxu da ta Auri d'an uwan natafa? Da walh laifunku zasu gani yaran,

Ta juyo kan d'anuwanta gaskiya baka kyautaba ka cutar da " yar mutane banda Allah ya jik'anku da Kaine ka kwan aciki,

Alh kamal yace"yanxu dai Aunty tunda komai ya wuce ba fad'a zakiyiba,saimu godewa Allah gabaki d'ayanmu kawai

Tace"to mungodewa Allah amma gaskiya anan zaku tafi kubar min ita takwanar min inyaso gobe sai indawo muku da ita

Takalli teemah"Mamana zaki kwanan anan?

Teemah tace"zan kwana mana Aunty,

Aunty Amina tayi murmushi tace"yawwa Uwata so nake Anjima Alhaji ya dawo kugaisa awace skul kike?

Teemah tace" sch of Nursing"

Ta gyad'a kanta yayi kyau my dotah,takalli Meenal tace"Meenal anga "yar uwa ko"?

Dariya Meenal tayi kawai don itanma bame surutu bace.

*********************

Sati d'aya ya rage ayi bikin amare Teemah,feenah,Nabeehat,angwaye suka bugo iv,Teemah " yar gatan Aunty Amina da Yaya mus,ab dukansu sunyi mata kayan furnitures. "Yan ubansun haka Alh kamal kuma yabiyawa mazajen sadaki shiko Alh Lurwan gida ya dank'awa hassan kyauta a d'an agundi babban gidane mekyau da tsari har Wanda zai ringa musu gadi aka tanada nan mahaifinsa daya koma can London d'in yahau nemar masa transfer Na aiki,

Dama Alh mansur yayo lefe akwatuna set bibbiyu nakowacce acknsu masu kyau da tsada 'yan London d'in angwaye sunji dadinsu

Gidan da Deen ya k'era inkungani saikun kama baki.

Yayi filoti biyar harda bene gaskiya ankashe nera(ai dole Dan shid'in me kudin kansane Yaya saifudden ba)

" ya mata anata gyaran jiki Nabeehat tana gidan momy dan Hjy lubna komawa tayi tabi mijinta kfn sud'au hutun aiki


Ango hassan sai waya yake yi da feenarsa yana zak'ak'a mata zafafan kalaman soyayya Dan yaga takamu sosai yanxu takwantar da kanta agunsa duk abinda yace da ita tanabi su saka atattach an daina tanata rawar kai za,a kaita turai ta xauna zaman Aure gata ga iyayen miji Na kwarai

Sosai akai gayya awannan hamshak'in biki da za,ai gidajen redio ya d'auka bayama a Arewa redio kullum ayi sanarwar bikin nan yakai goma bare in Aunty Nabila mukhtar uba nakan duty.(Alherin Allah yakai inda kk my namesake)

Amare ansha gyara dukansu Aunty Amina ta taresu agidanta tana banka musu maganin mata nasha da madara ga kaji da tsimi datake basu ta tanadar musu "yar Sudan da zatayi musu kunshi itace me musu dilka da halawa

Feenah datake bak'a saida ta haska fatarnan sai shek'i take

Hassan gwanin iya soyayya duk ckn mintina yakira Teemah harsaida Aunty Amina takwace wayar tace dashi" surukina zako kabari agyaramin "yar nan tawa? Kaki bari ayi mata gyaranta anitse"

Awasan dare tafad'a shima dariyar yayi yace"sorry my Aunty nabarta in angama nakira,dry Aunty Amina tayi takashe wayar Dan tafiso agyara mata d'iya tafito fess da ita

Ana jibi d'aurin Aure angwaye su hassan da Hussain da iyayaensu harma da "yan zuwa bikinsu suka diro Nigeria


Biki yayi biki kam don Ankashe kud'i abin ba,a cewa komai.

Ranar lahadi aka d'aura Auren Na " yammatan uku da maxajensu

Aranar akayi partyn lauyoyi da suka had'a a Royal don suyi mata kara Hussain yaji dadin wannan party don dama abokansa lauyoyi sunxo anci ansha amare sunyi kyau haka angwaye ma

Hjy salma tayi kyau ackn kayan lauyoyi saida za,a tashine ma tasaka ankon atamfar datayi musu su hud'u england ce babba itada Hjy maryam,Hjy lubna,Aunty Amina,duk d'inki iri d'aya

Hatta kayan Amare da angwaye ita tayi musu

Awashe gari kuma a tahir aka shirya partyn banda manya Saifudden ne yayiwa mutane ankon haka amaren ma shiyayi musu sannan yai musu odar tsadaddiyar bak'ar kot suka saka anci ansha anyi lik'in daloli

Mawak'a shidane suka baje wak'arsu ta bikin

Nura m inuwa,Ali jita,sabon zuwa Na bori,ado gwanja namai dawayya,sai Naxir ahmad,Ibrahim Ibrahim,

Tabbas sunkwashi kudi don basu tab'a zuwa bikin da suka sami neroriba irin wannan babban biki

A can kan kujera nahango marubuta novel ana cin kaza ana korawa da lemo,

Mama hassy princia,da Aunty Nafee anka,da Zee Autar Hjy,da Khadija candy,Ummu Affan Nabila Mmn Khalil,Safiyya Mrs sadeeq,Nabilancy Luv,Anisa didi, Amnoor,Party bb,maman shakur khalisat haidar,Ummi aysha ,Aysha garkuwa,kai wasu ma namanta sunayensu harda sunzo taya murna da kwadayi

Dan nahango Maman aleesha Kawata anasaka lemo ajaka....
😂😂


~*Auntyn Sayyada da shahidah*~💘

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment