You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan nan su baxama Neman ta"

Kai tsaye inna d'akinsu Yaya baffa ta nufa ta buga musu tana sallama duka nsu suna ciki,jin innar suce yasa suka fito a gaggauce suna tambayarta ko lfy?

Nan ta zayyane musu abinda ke wakana

Duk sunyi mamaki ainun abinda basu tab'a jiba.

Atsakar gida duk sukai cirko cirko inna halima da mallam ma sunfito kowa yana jimanta abin aransa Yaya suraj da Yaya Mukhtar "yan zafin rai sun k'ufula sunci burin sai sunyi maganinta inta dawo

Yaya baffa yana tsaye yai tagumi abin ya tsaye masa arai tabbas Aisha tanada matsala. Shikam yagodewa Allah daba masoyiyarsa ce me wannan halin ba.

Mallam ya janye tagumin dayai yace" Na fahimci Aisha so take tasaka min mugun ciwo araina to insha Allahu daga yau najanye hannuna akanta domin kuwa hanyar data d'auko ba hanya me kyau bace Sam muna mata tarbiyane tana rushewa taje can ta karata inma guduwa tayi baxan damuba A'i duniya ce'"yana gama fad'in haka ya juya yakoma d'akinsa

Inna halima ma barin gurin tayi batace k'ala ba dama domin batada tacewa dukda itama lamarin Na Aisha yana qona mata rai.

Inna A'i takallesu tace"maxa Ku koma Ku kwanta abinku abarwa safiya komai insha Allahu zata dawo daga duk inda ta tafi"

Dukansu suka koma d'akinsu itama Aminatu d'akin takoma tana jin ranta ba dad'i Allah yasa kada zarginta ya tabbata akan yayar tata

Mubeena me nauyin bacci batasan ma me ake cikiba sai baccinta take hankali kwance

Aminatu kasa bacci tayi tana kallon mubeena Na juyi agado ta ayyana inama itace wacce ayau batada damuwa domin tanajin gobe babbar ranace agunta Amma gashi yayarta tanaso tai mata tsaikon farin ciki.

Saida tayi sallar nafila k'arfe d'aya da Rabi Na dare tayi addu,o,inta kana takwanta ckn Sa,a baccin yadauk'eta


Da safe hankalinta ya tashi Dan daga sallar asuba bata komaba tanata "yan laziminta akan sallaya itama mubeenah tayi sallarta Amma ita takoma bacci danta saba komawa baccin bayan asubahi


Hankalin Aminatu yai mugun tashi data farga da akwatin Aisha baya kan saman sif d'insu tabbas zatonta ya zama gaskiya Aisha guduwa tayi

Lallai Aisha tayi girman banxa tabbas kowa yabar gida, gida yabarshi tasan zatayi nadama nan gaba Amma bataso tayi hakaba tana qaunar " yar uwarta Amma gashi tayi mata nisa batasan uwa duniyar data cillaba yanxu yazatayi Knn?

Koda mallam dasu inna suka ji cewar Aisha da kayanta ta tafi sai sukace tafi ruwa gudu ai duniya tafi bagaruwa iya jima,suka nuna kamar basu damuba ammafa can k'asan zcyr mallam wani abune ya tokare masa yak'i tafiya saida ya rubuta ayar Allah yasha sannan yaji sauk'i aransa,

Itako inna halima Har kuka tayi ad'akinta taji inama Aisha ba "yar cknta bace da bata ringa kurb'ar wannan bakin cikin ba


Su Yaya Mukhtar kamar su hadiyi zcy Dan haushi da bakin ciki tabbas duk randa Aisha ta dawo inta shiga hannunsu sunci alwashin saita gane shayi ruwane.....


~*Auntyn Sayyada da shahidah*~πŸ’˜
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


*KANO...*


~*pg 32-33*~

Tun Ahanyarsu ta zuwa gidan Umman deen Hjy salman ta kira megidan nata kamal yana d'agawa tace"Ranka ya d'ade kana ina? Yace mata"ina gida ban fitaba banajin dad'in jikina ya akayi?

Tace"bakomai ganinan da bak'inka"

Yace"bak'i Na kuma? To daga ina amma basuyimin wayaba?

Tace"saidai munxo kawai,

Tana kashewa takalli Teemah dake gefen ta tai mata murmushi tace"my dotah yau zakiga mahaifinki yau Abbanki zaiyi farin ciki Wanda bai tab'a yiba,Dan Allah kisaki jiki damu domin saikin yi mana biyayya sannan zaki samu aljannah,bazamu rabaki da momy da dadyn kiba amma mune dolenki kinji,

Teemah tayi murmushi itama tagyad'a kanta itanma ai a ckn farin ckn take

Sunyi fakin d'in motocinsu a a parking space bayan sun shishshigo da motocinsu uku ta Hjy Salma ta hudun,

Alh kamal kasa zama yayi Dan gabansa keta faman faduwa yanata tunanin wane bakine wadandan da sukaje gun matarsa kafin sugaya masa zasuzo?

Saida takaisu sitting Room kana ta nufi d'akin Mijin nata kicib'us sukai a korido Dan shima saurin yake ya fito sbd yaji shigowar motocin

Yakalleta yaga tana murmushi yace"yadai my madam akwai news ne?

Tagyad'a kanta tace"sosai ma kuwa,yau kukanka ya k'are yau ka xama baba Allah ya amshi tubanka ya amsa maka rokonka mijina

Yace"bangane nufinkiba"ciki kk samu ne?

Ta kama hannunsa tace muje d'akin bak'i kaga wani Abu

Yabita zagwai zagwai

Da sallama tashiga suka amsa masa .idonsa akan deen shikadai ya gane kawai yanemi guri ya zauna sukuma kallonsa kurum suke domin sungano tsantsar kamarsa da Teemah,

Itama teemahn kallon mahaifinta take cikin so da k'auna tabbas ta d'aukoshi idonsa sak nata gashi yanada haske

Bayan ya zauna aka gaggaisa samari da "yammata suka gaidashi

Hjy Salma ta kalli Teemah tace" my dotah dawo kusa da Abbanki,

Tsam Teemah ta mik'e ta dawo kusada Alh kamal ta zauna yak'ura mata ido yanajin wani Abu akanta baigane nufin matar tasaba kwataΒ² yadaiyi shiru yana saurarenta amma zcyrsa harbawa kawai take

Hjy Salma takalleshi tace"dafarko inaso kafara da godewa Allah subhanahu wata,ala domin ayau kukanka ya k'are Allah ya baiyana mana "yarmu da muka rabu da ita tun tana jaririya....


Tayi shiru ta nuna masa Teemah tace" kagan tanan fatimah sunanta Wanda Allah ya baiwa Iyayen rik'on saif ita domin sune suka tsinceta,saigashi k'udira ta Allah data girma kuma sai Allah yasaka soyayya atsakaninta da Saif.......


~*Auntyn Sayyada da shahidah*~πŸ’˜
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

Mutuwar zaune Alh kamal Yy saida matarsa Hjy Salma ta taso ta dafashi ya dawo hayyacinsa hawaye yaji yana biyowa kan kuncinsa hajy Salma tace"bakuka zakayiba Abban Teemah kayi murna ka godewa Allah daya bayyana "yarka kaganta da idanka pls kadaina zubda hawaye akwai yara agun,

Yakama hannun teemah ya rik'e gam tamkar Za,a kwace masa ita yakura mata idanuwansa masu kama da nata yace" kiyafeni my dotah munyi nisa dake baki shak'u damuba nasan kinji cewar duk laifi nane walh nayi matukar nadama nayi Dana sani me hali irin nawama ina masa fatan shiriya ina sonki Mamana,

Teemah batace komaiba saima hawaye dataji suna kwaranyo mata duk Na tausayin mahafin natane tabbas tasakanin iyaye da "Yaya sai Allah taji tana k'aunar Abbanta tasan kuma komai daga Allah ne shiya rubuto mata komai dazai faru arayuwarta

Tasa hannu ta goge hawayensa tana masa murmushi

Hjy Salma tace" Abban Teemah kagodewa iyayen goyon Saif domin sun mana komai arayuwa sunbaiwa diyarmu tarbiyya mekyau sun tsaya tsayin daka akan iliminta Na addini Dana boko tabbas bamuda abinda zamu saka muku dashi saidai muce Allah yabiyaku da gdn Aljanna.

Alh kamal yakalli Alh Lurwan yace"hakika yau ranar farin ciki ce agareni nagodewa Allah kuma ina matukar godiya agareku domin kunmin komai Allah yasaka da alkairi yabiyaku da kairan naji dad'i sosai

Alh Lurwan yayi murmushi yace"babu komai Alh kamal komai muk'addarine daga Allah shiya tsara faruwar hakan tabbas naga kamanninka da Teemah ga kuma irin zoben dake hannunta ahannunka hakika Na Dada yarda da Fatima yarkace

Hjy maryam tacire tagumi data rafka tace"nidama tun a farkon zancen da Hjy Salma taxo mana dashi nayarda da batunta domin baxata xomana da zancen k'aryaba saikuma gashi naga irin zoben hannun Teemah ahannunka Alh kamal


Hjy Lubna tace"to masha Allahu muma munaiwa Allah godiya dabai zartar da Aure atsakanin wadannan yanuwaba Allah yabaina mana gaskiyar lamarin da wuri Dama tun farko da laifinmu mata dabama zumunci ajunanmu datuni hakan bata faruba da tuntuni mungano da wuri Amma yanxu ai saimu rik'e zumunci

Hjy maryam tace"ai dole ne yanxu kam mu rik'e zumunci saidai kuma zanyi kewarki "yata Teemah ,tafad'a tana share kwalla taeemahn ma kwallar take gogewa tabbas sabo turken wawa ne

Hjy Salma tace" kwantar da hankalinki Momyn saif insha Allahu Baku rabu a "yarkiba kamar kuna tare ne Dan inhar kullum take son taganki Abu me sauk'i ne da kaina ma zanringa kawota gidan ki

Alh mansur yai gyaran murya yace" to Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya Kawo mana wannan Al, amari ckn sauk'i Dan haka inada magana me muhimmanci dafatan zaku karb'eta hannu bibbiyu "

Alh kamal yace"insha Allahu zamu karb'eta fad'i muji,

Alh Mansur yace"to gameda yaran nan ne inaganin mexai hana mu had'a Fateemah da hassan Aure Nabeehat kuma da deen inyaso sai ayi tare dana su Hussain da Feenah ko kuwa?

Yafad'a yana kallon Dadyn Feenah yana murmushi Alh Lurwan yayi murmushi yace"a mezai hana hakan yayi walh naji dad'i sosai saidai ko yaran Allah yasa kada musami tangard'a daga gunku,

Dukkansu murmushi sukai Dan suma hakan yayi musu bayama hassan da dama bai Dana son Teemah ba yaji anfaranta masa rai teeman ma taji ddn hakan don Yaya hassan mijine Na nunawa Sa,a yanada mutunci gashi ba ruwansa taji sonsa yashigeta one tym Dan dama ita batasan yana dakon sontaba

Shiko deen kallon Nabeehat yaringa yi yana murmusawa don Nabeehat tayi masa koba komai tanada kyawun hali irin Na Teemah gata kyakykyawa me kunya ayanxunma sunne kai tayi dataga irin kallon dayake mata

Feenah da Hussain sunji dad'i gashi suma za,ayi nasu Auren Knn kwana kusa

Nan iyayansu Nasu suka farga da halin da "yayannasu nasu shiga najin dad'i suma sai sukai farin ck lallai Abu yayi knn.

Abban Teemah yace" to masha Allah naji dad'i nima zanbiyawa "yayana sadaki konawane insha Allah naji dad'in wannan had'in natuwona maina kunga zumunci zaik'arfafa Knn,Allah yasanya Alkairi acki"

Dadyn feenah yace"amin,Dan haka nixan saka ranar Aure nan da wata d'aya,

Dadyn Nabeehat yayi murmushi yace"to Shikenan Ai kacancanta nikuma tawa gudunmawar zanyiwa "yayana mata kayan d'aki " yan waje.

AbbanFeenah yace" saidai kuma banaso "yata Teemah tatafi har k'asarku don tayiw maahaifanta nisa natabbata zasu bukaceta akusa dasu dansu kara shakuwa Dan haka hassan inaso kanemi transfer d'in aikinka yadawo Nigeria zan saimaka gida kuxauna,

Hassan yace" to dady godiya nake,

Iyaye mata nan aka hau murna ana saka albarka a Auren....


_nima albarkar nasaka kema me karatu saiki saka taki albarkar_


~*Auntyn Sayyada da shahidah*~πŸ’˜
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


*KADUNA...*


~*Pg 36-37*~


To acan Kaduna ko kuwa a b'angaren gidan mallam bak'in ckn Abinda Aisha tayine yakwantar dashi yakamu da hawan jini kullum cikin b'acin ran guduwarta yake yana ganin wannan abin datayi tafi tozarta tashi akan Na farkon tabbas yasan yanzu kowa yafahimta tunda sati biyu Knn da barinta gidan anyi taron saukar Aminatu babu ita ack

Aminatu kuwa abin yana damunta harta fara rama Yaya baffa yasakata agaba yana mata fad'a"haba Ummie Na wannan wane irin abune kullum zanyi mk mgn akan kibar tunanin nan kink'iya itadai Aisha tana can hankalinta nasan akwance may be ma tamanta damu zakije ki kashe kanki abanxa kimin asara gashi bikinmu yarage sati uku ga mallam akwance duk kunsawa kanku tunanin wata banxa can...

"Haba Yaya kaima kasan abin akwai tsayawa arai kayi min uzuri ina k'aunar Auntyna walh nitunanina akullum shine makomarta domin ta d'auki zunubai kuma tana kan d'auka ma ga alhakin iyayanta data d'auka

Yaya baffa yace" to naji kina k'aunarta Dan Allah kisawa ranki salama ki fidda tunanin ta aranki,nimafa "yaruwatace daku nashaku banida wani Dan,uwa ko yr,uwa sama daku Dan haka inaso mutaru nidake akullum muringa mata addu,a akan Allah yashiryata yadawo da ita gida,bawai muita tunani aranmuba,

Anan tayi d'an murmushi har wushiryarta ta fito datake k'ara mata kyau tace" to Yaya nadaina zanyi addu,ar da kace"

"Yawwa kokefa my wifey "

Tayi murmushi akaro Na biyu tace"saidai Yaya ina tunanin tafiyarka har Abuja Aiki gaskiya Ni saidai ka tafi dani in An d'aura bazaka barniba,

Ta mak'e nafad'a kamar wata baby

Yayi dariya yace"to ya zanyi Ummie Na acan Kawu yasamarmin Aikin dole Na amince naje kinga sunkusa sauka kada nayi wasa da damata bandama munada hanya nidasu Yaya suraj d'in kina gani daga gama karatu zamu samu aikine inba munsha wuyaba ko munkashe kud'i Ai hanya tayi,

Aminatu tace"kaga shi Yaya suraj yayi Sa,a anan yasamu aikinsa matarsa Nabila ta huta gata ga mijinta,

Yy dry yace"kece Knn baki hutaba?

Batace komaiba,

Yace"kwantar da hankalinki my wife nima Kawu yace baifi Nai wata hud'u acanba zaisa aimin transfer Na dawo kadunaba,yanxu baga Mukhtar ba shi kinga anan zariya yasamu nasa Aikin kuma matarsa can zai zauna da ita,

Aminatu tace"ita ai batada damuwa tunda tanada "yan uwa acan kuma gata ga angonta.

Baffa yai murmushi yace" inaso kigane wani Abu Ummie Na kinga abujan nan bamuda gida acan kuma haya tsadane da ita acan d'in wata hud'u kamar yaune,zan ringa zuwa duk k'arshen month ina ganin amaryata ko hakan bai yi miki ba?

Yafad'a yana mata wani had'add'en kallo me motsa zcy tayi murmushi k'arfin hali tace"yayi yayana,saidai Ni kawai abarni agida gunsu inna yafimin sauk'i,

Yace"a,a banyardaba inkuma nadawo ganinki kumafa aibaxan sakeba,kiyi hkr zamu zauna agidan mu da Kawu yabamu bagaki ga matar Yaya suraj ba kuna tare a unguwa d'aya saiki ringa zuwa kullum kuna hirarku ko?

Ta gyad'a kanta tace"to Allah ya tabbatar mana da Alkairi,

Yace"yawwa Amin, amaryata ko kefa.....


~*Auntyn Sayyada da shahidah*~πŸ’˜
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


*dis my novel 4rm 1st to end I dedicated to my luvly dotah Pharty b.b*






_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


~*pg 42-23*~
Biki yayi biki kam domin koina ka zaga zancen wannan bikin "yan gatan akeyi kowa kaji kaji yace zashi bikin Auren dangi"

Party kala biyar akayi Na k'arshe ranar talata aka k'areshi feenah ce ta shiryashi Hussain yabiye mata yanarkar mata da nera iya "yammata ne don k'awayenta Na jami,a tayishi ankon partyn k'ananan kayane dogon wando bak'i ko sket hark'asa baki d'amamme da Riga body hog,pink inkaga dama kasaka d'an mayafi ko hula sunan wanan pharty *berver Q,*

Anyi shagali sosai mawak'an mu Na Hausa matan sunbaje hajarsu ta wakar bikin da sukayo musu sunkuwa kwashi naira Faty nijar ce da Murja baba da fantimoti,

Amare sun cashe don babu maxa agun dogayen riguna suka saka har k'asa masu dogon hannu farare masu adon kwalliya Na stone me shek'i da fulawowi.

Sai goma aka tashi a phartyn nan a can nahango " yan lek'en asiri marubutan mu Na novel sunje d'aukar news sunata shirin shiga mota da saurina Na tafi gunsu natari maman Aleesha nace"kewai amara kowanne pharty dake? Wannan ai gayyar sod'ine...

Da tsiwarta ta katseni dacewa"wani irin gayyar sod'i to inma baki saniba kisani feenah ce ta gayyaceni nikuma nagayyato mata mutane 20 gasunan nakama bakina nace "me ? Da gaske kk ko kuwa ? Keda kk matar Aure zakizo phartyn " "yammata"

Tai murmushi tace'"kalli bayanki kiga matan Auren yanda suka d'ora After dress akan shigar tasu ,

Najuya bayan nawa kuwa nakai kallona kan mata sunata shiga mota wasu sun d'ora gyale akan shigar dasukayi wasu kuma sun d'ora after d'in nace lallai "yan ganin kwal uwar daka sauranku kai amarya,

Tayi dariya tace" ai wannan dolene ko baki fad'a ba zamuje raka Aunty Teemah gidan Angonta hassan,

Nace"dafatan Baban Aleesha yasan kinzo ko?
.tace"ai bana satar futa da amincewarsa Na xo nan"muje inraka ki kugaisa da '"yan uwa marubuta online novel,

Nabi bayanta muka k'arasa gun zugar matan dake shirin shiga mota wasu kuma suna tatstsaye ajikin motar

Lallai marubuta online suna da had'in kai da kara gasu da mutuncin da sanin darajar mutum mungaggaisa dasu ckn mutunci one by one muka gaisa Dan agane juna,ta farkonsu itace


*jiddah Aliyu,Faty Azland ,meesha Luv,lilmeerahcute,Ruky sadau,billy giro,muhmeelat,k.Candy,Aisha wakili,miss neerat,summyn bash,miss xoxo,ummiey agos,basmar er lele,Asiya bashir,Asmy b Aliyu,queen mermue,beebie isah,futha Luv,khausar luv,Anisa didi, zee yabour,Nuceey Luv,Ummi hambali,Amnoor,Nabila Mmn Khalil,ummu Affan,mummeetie,Aisha A,muhd,Ayusher,kdeey,Fiddausi.sodangi,ummu sabreenah* kai wasuma bazan iya rik'e sunan suba


Saidai muce Allah yamaida kowa gida lfy πŸ‘πŸΌπŸ˜‚

*===============*

Ranar laraba da dare motocin kai amarya teemah sukai jerin gwano domin kaita d'akin angonta hassan

Antsara idan su feenah da Nabeehat suka rakata d'akinta sukuma washe gari sai atafi kaishu a jirgi

Teemah ansha kuma MNA rabuwa da iyaye tana jikin momy ackn motar tana shafa kanta tana tausarta da kalami mai ddi, "kiyi shiru Teemah kowa d'an hakane keda kk akusa damu ma meye Na kukan sukuma " yanuwanki suyi Yaya?

Dama suna ckn motar abaya basai suka hau kukaba Aunty Amina tana tsakiyarsu ta janyosu jikinta tana rarrashinsu"haba daga fadin haka saikuyi kuka kamar anturaku,tokuma ai kamar akusan kuke Dan zamu ringa ziyartarku akai akai kunji,

Nan taita aikin rarrashi sudai sunaji ne kawai

β„…β„…β„…β„…β„…

Bayan "yankai amarya sun watse aka bar teemah a zaune kan gado lillib'e da gyale har kanta ta rufe fuska tana kuka

Ango kuwa bashi ya shigoba ma sai goman dare

Shikad'ai ya shigo gdnsa babu " yan rakiya Dan yanxu anwaye

Ganin tana kuka yashiga wani hali yaringa nan nan daita yana rawar jiki akanta yaita aikin rarrashi hartai shiru ya hada mata ruwa ta watsa dantace masa zafi takeji

Yasa sukai sallar nafila ta godiya ga ubangiji sannan yakawo mata yoghout d'in daya shigo mata dashi da nama taci kad'an ta ture

Saida yai da gaske ta iya saka wasu k'ayatattun sleeping dress masu hautsina zcy

Hassan dakyar ya saita kansa yajata zuwa gadon baccinsu yakashe musu fitila....


Ganin duhu adakin yasa nafito da gudu nayo waje

Bazan iya daukar muku wannan rahotanba yafi k'arfina

Asuba ta gari Teeman hassan....


βœ‹πŸΌβœ‹πŸΌβœ‹πŸΌπŸ™ŒπŸΌ


~*Auntyn sayyada da shahidah*~πŸ’˜
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_ πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


~*pg 38-39*~

Da daddare Hjy Salma tana zaune itada me gidanta Alh kamal da d'iyarsu Teemah sun sakata agaba suna mata tambayoyi akan duk abinda take so da Wanda bataso tamkar wata "yar gold

Murmushi kawai teemah take xubawa tabbas yau taxama " yar gata duk da ada canma tana kallon kanta a "yar gatan dady to amma wannan tana ganin ba irin wancan bane lallai mahaifinta yana sonta Dan motsi kad'an tun bayan tafiyarsu dady da momy inya kalleta saiya zubda hawaye

Alh kamal Yakama hannunta yace" my teemah Uwata takaina my kk so aduniyar nan inyi mk ? Ki fadi ko mene ne xansai mk gida ko mota ko kujerar makka kafin Aurenki insiya inbaki?

Murmushi tasakeyi sannan tace" Abbana niku kawai nake so ayanxu tunda Allah yabani Ku,gani ina tare daku banison duk wani k'awar duniya fatana ubangiji Allah yabarminku....

Hjy salma ta katseta"amin,naji dadi sosai teemah mungodewa Allah daya bamu "ya me hankali da fahimta sannan inaso ki fad'a mana gaskiyarki kada ki kwari kanki kina son hassan har zcyrki ko kuwa gara ki fad'a kada ko alkunya kk yimana.

Teemah ta girgiza kanta tace'" ko d'aya Umma inason Sa zanyi zaman Aure dashi domin Yaya hassan yanada kyawawan halaye irin Na yayana deen,

Hjy salma ta gyad'a kanta ckn jin dadi tace "to Alhamdulillah Allah yabaku zaman lfy ki zama me biyayya gun mijinki inaso ki gado halin me sunanki Nana fadima d'iyar manzan Allah

Teemah tace" insha Allahu zanyi kema Ummah ai me biyayyarce ko hali irin naki Na d'auko ai Na more tunda biyayyar ce takaiki shiga halin rashina,

Abbanta ya gyada kansa yace"kwarai kuwa zancenki daidai yake Uwata domin ina alfahari da Ummanki tunda nake da ita bata tab'a yimin musuba,baxan tab'a samun macen da zatayimin abinda tayiminba,gata nan tanada rik'e sirrin miji sosai Na jinjina mata,ko wani nata bata tab'a fad'awa halin data shigaba balle nawa ayanxu ma Ni tunani nake Na abinda zamuce dasu akanki.

Hjy salma tace"gaskiya zamu fad'awa kowa Na tabbata za,a yarda damu kobamu da shaida tunda kamarka da "yarka ta nuna,

Ya gyad'a kansa yace" hakane,gobe saimu fara zuwa gasu inna zanyiwa Yaya Mus,ab waya yasamemu agidan daganan saimu wuce gidan "yar Uwata .
" Allah yakaimu goben,

Yace"amin,yakalli teemah yace"Uwata tashi kije ki kwanta dare yayi kiyi baccinki kinji,

Hjy salma ta kama hannunta tace"tare zamu kwana Abban teemah yau dole kayi hkr bamu tab'a raba d'aki ba Dan bazan iya nisa da itaba har sai in tayi Aure,

Dry yayi yace"Au abin hakane? To Shikenan ai dole dai zata tafi gidanta tabarmu tare adawo d'akin nawa

Yafad'a yana dyr itama dryr take teemah ko murmushi takeyi ita iyayan nata ma burgeta sukeyi ko don"yan bokone baruwansu sunada wasa da dariya ga wayewa abinsu

Da asuba kamar yadda tasaba ta kira deen Awaya yana d'auka da sallama saida taji wani abun ya tsarga mata tai saurin kawar da abinda ke ranta tace"Yaya dafatan ka tashi yin sallah baka makaraba ko?

Yayi murmushi yanadaga kwance yace"k'anwata yanxu dai kk tasheni nagode ina Ummanmu?

Tace"Umma tana sallah,

Yace"to kigaidamin ita da Abba nagode my sister zanyiwa Nabeehat wannan kyakykyawar hudubar taringa tashina bacci awaya domin hakan yanada kyau ga d'iya mace rik'e ibada kici gaba dayi k'anwata har gidan Aurenki kinji"

Ta gyad'a kanta taji dadin hakan tace"naji nad'auka xancigaba dayi insha Allahu kagaidamin kowa da kowa insun tashi

Nan sukai sallama ta kashe tana murmushi"Allah sarki yayana ya zama Na Nabeehat"ikon Allah Knn,

Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—Γ— Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—Γ— Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—

Saida suka gama shirinsu Na tafiya gidan tsoffin hjy Salma kana Abban Teemah yakira yayan Hjy salman Yaya mus,ab d'in yasanar masa cewar yanason ganinsa yanzu agidan inna.

K'arfe sha d'aya a can gdn tai musu suntarar da Yaya mus,ab d'in a can harda "yayansa ya taho macen budurwarsa sunan Meenal sai maxan da suke sama da ita Musa, Mesunan mallam ake cemasa Sai kuma k'aninsa Ahmad Sudais sunan mahaifin matar musab d'in Knn duk Jami,a suke zuwa

Bayan angaggaisa suna zaune Hjy salma ta kasa musu bayanin Dan batasan ta inda zata fara bama

Sai Alh kamal ne yai musu bayanin yanda zasu fahimta ckn sauk'i baib'oye musu komaiba Dan baxai yi k'arya ackba

Aiko dai sunsha mamaki sosai inna takama baki tace" ikon Allah taho nan jikallena fad'ama Bintu shiyasa tunda kuka shigo nake jinki ajikina Allah wahidun ahadun Ashe ked'in jininace bamu saniba kikazo gaidamu Allah mungoma da Aure bai gifta tsakaninki da saifu ba.

Shima mallam abin mamaki yaita bashi Yakama hannunta yace"sannunki Fatima kinji haka Allah ya k'addara zaki nesanta da iyayaenki to amma mungode Allah daya kaiki hannun Arxiki kuma gida,

Yaya mus,ab yace"lallai wannan Abu akwai *cakwakiya* acknsa tabdijan Amma kema kema kinyi ganganci da kk biyewa mijinki salma saidai tunda HK Allah ya rubuta dole ya faru Alhamdulilah muna godiya da Allah daya bayyana muku ita awannan lokacin Allah ya nuna mana bikin nata,

Hjy salma tace "Amin Yaya,zansa Hassan d'in yazo ya gaidaku tareda k'anwar tasa da zata Auri Saif d'in kugansu ,

Inna tace " to aishikenan hakan yayi ma,Allah yasa ayi damu.

Dukansu sukace "amin,

Dazasu tafi gdn Aunty Amina yayar Alh kamal Ai Meenal cewa tayi saita bisu domin itakam taga k'awa kuma " yaruwa Teemah dama kusan Sa,annine

Teemah Ranta Fe's yauu gata ga kakanninta Na gaskiya masu sonta da qaunarta....


~*Auntyn Sayyada da shahidah*~πŸ’˜
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

*End...*

_Sak'on gaysuwata ga wad'annan manyan grps d'in masu matuk'ar muhimmanci agareni..._

*Hikima writers Nvsl*
*Cooks Yumms Nvls*
*Mar,atus'Saliha Nvsl*
*Sahafs Nvls*
*Dandalin Autar Hjy Nvls*
*Rumbun Asiya b.Aliyu Nvls*
*Pharty B.B. Nvls*
*Crazy buddies Nvls*
*Khadijah Candy Nvls*
*Novella's lodge Nvls*
*Fabulous ladies Nvls*
*macen gaban goshi Nvls*



_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


*KADUNA...*



~*pg 44-45*~

Kawu ne a ckn falonsa yanata zurga-zurga shik'adai sai gumi yake hankalinsa atashe abin duniya yai masa yawa

Yakai yakawo saikuma ya zauna ya rafka tagumi yana zancen Zuci"wannan Abu daya sameni natabbata ixina ce Allah ya nuna akaina dakuma Alhakin Aisha tabbas kuskuren Dana tafka ne tun a farko yanxu nk gani..

"To yanxu ya zanyi,ya Allah ka yafemin abinda nayi Na sab'onka danai wajen Neman duniya akan inaso nasami mulki nai sab'o agareka Na cuci " yar d'an uwana Astagfirullah ya Allah,

Ya mik'e zumbur ya d'auki mukullin motarsa sai gidan d'an uwansa mallam

Karfe shida Na yamma a masallaci yasameshi don ankusa kiran sallah baya fitowa sai yayi sallah

Sun keb'e dagashi saishi ya rasa ta ina zai faro masa wannan bayani domin ayau dai kome d'an uwansa zai masa saiya gaya masa gaskiyar lamari ya nemi yafiyar abinda yaiwa "yarsa

" kayi shiru ka kasa cewa komai,inji mallam

Kawu ya sharce gumi kansa ak'asa yace"ka garfarceni Yaya nayi maka ba daidaiba naci amanar "yanuwantaka natafka sab'on Allah duk ni kad'ai duk akan son zcy Wanda abokina ya runjayeni akan hakan... Yai shiru yakasa ci gaba

Mallam yace" banganeba meya sakoni ackn lamarinka dahar ka cuceni bansaniba. Mekayi min...

Kawu ya sharce gumi kan goshinsa yace"karayar arxik'ice tasameni Na mak'udan kudadena har kada rorina Dana samesu ta hanyar matsayin danake kai sun dulmiye narasa su mallam gashi saura sati guda musauka akan kujera natabbatar hakkin Aisha da abinda naiwa ubangiji ke bina...

Mallam yace "wai mekayi ne ?me kuma kaiwa Aishan..?

Kawu yafara zubda kwallah ya zayyanewa mallam komai tunda ga ranar dasukaje gurin boka yanunawa boka cewar yanason yahau kujerar chairman kota halin k'aka konawa zaibawa boka inyai masa aiki yasamu

Boka kuma yace" yakawo sperm d'in yarinya budurwa wacce suke da kusanci da ita yakusanceta yakawo sperm dinsa danata za,ayi aiki mekarfi.kud'in Aikin ma saiyahau zai bashi

Kawu yana kuka yagama

Please Login or Register in order to submit comment