You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashigo masa saida tazo tsakiyar d'akin nasa kana tayi masa sallama dagashi sai gajeran wando da Yr bes yai saurin tashi zaune yana kallonta

Feenace tasaka wani matsatstsen siket mejikin roba,rigarta body hug kanta tasha kitson attach

Ya girgixa kansa yaja tsaki yace"feenah wannan ba d'a,a bace kishigo ba sallama kuma saikinzo hr tsakiyarr d'aki kana zakiyi sallama inkin tarar ba kaya ajikina ba kumafa?

Ta yatsina fuska tace"tosaime Yaya Dan naganka ba kaya nifa Yr uwarkace akwai Wanda zanje nafadawa ne?

Kawai dai danka tsanenine shiyasa zakaimin fad'a

Tahau goge hawaye,tajuya zata futa yakirata tadawo yace"zauna,yanuna mata guri kusa dashi yace"feenah baikamata kice Na tsane kiba, awane dalili zan tsani Yr Uwata tajini kawai dai bakyason fad'ane yanxu kiduba kiga yanayin shigarkima bata daceba kalli kanki kinsaka isgar gashi...

Tashafa kanta tace"to ai kwalliyace kuma birthday d'inmu za,ayi shiyasa,nasaka

Yace"to Amma teemah tayi hakan?

Ta yatsina fuska tareda zob'aro baki tace "ina ruwana datayi ko bataiba wai ita ustaziyya nace taje aimata takiya"

Yace"gud taburgeni sosai gara kada tayi don babu kyau Karin gashi kinafa zuwa islamiyya ko...tace"inhar bakaso zangyara Amma saikaimin Alqawari guda d'aya.

Yace"yes inajinki '

Tayi fari (al a,adar tace yin hakan)"Yaya zaka Aureni?

Yace "me?

Tace" Aure nace ko baka sona? Walh Yaya tun kafin kadawo gida naketa d'awainiya da soyayyar ka Dan Allah kaji tausayina kada kawatsan k'asa a ido,

Yai murmushi ya girgixa kansa yace"feenah baxan b'oye mikiba bakuma zan yaudarekiba zancen gaskiya akwai wacce zuciyata keso wacce kema inkinjita zakiso hakan zakuma kiyarda kibar mata Ni har abada.

Hawaye suka zubo mata"wacece haka Yaya?

Yace"zakiji ko WACECE anan gaba Amma ba yanxuma

Tatashi afusace tana kuka tabar d'akin sukai kicib'us da teemah ak'ofar d'akin Wanda duk taji abinda suke cewa,

Tashigo a nitse da sallamarta

Ya amsa yana kallonta yana murmushi tasami guri nesa kadan dashi tazauna tace"Yaya sannu da hutawa'

Yace"yawwa teemah andawo daga islamiyyar ?

Tace"walh nadawo, meyasa Yaya kayiwa "yar Uwata haka ?

Yai murmushi yace" mekike nagaya mata nai mata k'arya ko Yaya,har raina zcyta ba ita take soba.

Tace"to wa zcyrka take so d'in?'
Ya nunata yana d'an murmushi dayake k'arawa fuskarsa kyau

Dasauri ta nuna kanta tana fad'in"nikuma Yaya? Banganeba"

Yace"yau zaki gane ai teemah walh Nike zuciyata take qauna,tun inacan nake da muradinki sbd akwai hotunanku keda feenah a wayata ba tab'a jintaba araina saike ingaya miki ma d'iyar Aunty Lubna wato Nabihat k'anwar su hassan kinga Yr,uwatace itama ta nunamin tana sona Amma ban munafurce taba nabata hkr dukda bata hkr ba,

Kinga itama Nabihat tanada kyawawan halayya kamar taki Amma naki amsar tayinta sbd ke zuciyata takeso

Teemah ta rasa bakin mgn tayi shiru zcyrta Na hrbawa duk saitaji ta takura kamar tahak'a rami tabuya"wai ita Yaya deen yakeso!


Yakatseta da fad'in "teemah ko banyi mikibane,kada ki b'oyemin inbakya sona Dan Allah

Takalleshi tasadda kanta k'asa tace" inasonka Yaya Deen Amma ina tunanin halin da Yr Uwata zata shiga,

Yace"kada ki damu zata hakura tabar miki itama tasan dake nadace teemah.

Nan tayi murmushi ta mik'e zata futa yace"teemah!

Hartakai k'ofar d'akin tajuyo takalleshi itama shidin take kallo yace"ya batun birthday d'inku yaushe za,a fara partyn?

Tace"jibine Yaya Amma Ni gaskiya baya gabana sbd baxan iya fashin zuwa islamiyyaba aranar munkusa yin sauka kullum hadda muke bayarwa.

Yaji dad'in hakan teemah tana burgeshi yace"yayi kyau Allah yataimaka.

*_____________________*
Aranar da za,ai birthday tayi shirin fita makarantar tahfeez d'inta tana d'akin tana zura hijab d'inta dogo hr k'asa momy tashigo tasameta tace"yanxu nan Allah dagaske baxaki kansile makarantar yau d'ayaba?

Teemah tace" aimomy hadda muke kuma banaso karatun ya wucemu,

Momy tace"aishikenan kekijiyo ga wannan doguwar rigar dadynku ne yasai muku saiki jibge taki aloka tunda bazata sami sakuwa ayau ba.

Takarba ta ajiye kawai rigar tayi kyau gown ce
Fara hark'asa tayi mata kyau Amma ita kyale kyalen duniya bay gabanta karatun qur,aninta yafiye mata wannan hidimar da yahudu yakawo mana.....


~*Auntyn sayyada*~πŸ’˜
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


_dis page dedicated to mu lovly dear_ *Ummu Affan* ( _marubuciyar Dr khareemah_)


~*Pg 5...*~
Da taimakon Allah da taimakon dady da Yaya Saif teemah tasami shiga sch of nursing tafara karantar medicine ckn kwanciyar hankali take karatunta bata fasa zw islamiyyartaba kullum da yamma domin watanni ya rage suyi saukar karatun alqur,ani


Ita kuwa feenah saida dady yadage mata tasamu tafara zuwa FCE yakashe kud'i akanta Dan takardarta bawani kyau tayiba pass yafi credit yawa hardasu fail aciki bata bada himma a karatu

Soyayya sark'e atsakanin Deen da teemah tun tana jin nauyinsa hardai tadawo tasaki jiki dashi itama tana nuna masa soyayyar kullum shike kaita sch yad'aukota teemah kuwa driver kekaita don lectures d'inta Na rana ne kullum sai 12:00pm take futa ta dawo six islamiyyarma ta kansile babu lokacin xuwanta agunta

Aranar da feenah tagano akwai soyayya atsakanin teemah da Yaya Deen bak'amin tashin hankali tashigaba ranta yai mugun dugun Zuma Ashe dama akan teemah yai mata wulak'anci

Tana kuka tajewa momy da zancen momy tace"kk kwantar da hankalinki Uwata zanyi yanda zanyi yadawo gareki domin dake yadace dama nasha yimiki sha,awar Auran Deen sbd banaso yatafi waje ya Auro mana wacce bamusan Asalintaba sbd yanada arxik'in dako dadynku bayidashi kinga aidole mujanyoshi jikinmu da ace baki fara nuna masa soyayyarki bama da sai kibarwa "yar uwarki to Amma kinrigata dole tahakura taci girma yi shiru share hawayenki zansami dadaynku da zancen yau.

Aikodai aranar da daddare momy takalli dady tace" dady akwai wata magana danake so muyi akan yarannan Allah yasa kabani goyon baya

Dady yace " fad'i ina sauraranki"

Ta muskuta tana murmushi tace"dama akan feenah ne ta dad'e tanason d'an uwnta saifu tun kafin yadawo to Ashe said yadawo shikuma saiyace mata tayi hkr Yr,uwarta yake so' to nikuma naga baikamata mubari ayi hakaba sbd feenah yadace ya Aura ba teemah ba domin feenah itace jininsa kuma da mubawa Na dawa ya k'oshi aigara mufara baiwa Na gida ya....

"Ya isa haka maryam! Ransa ab'ace yafurta hakan ya nunata d yatsa " ki iya bakinki akan yarana banaso kifara Kawo mana matsala tun yanxu naga alamar kezaki fara tona asirinmu akan teemah Wanda kuma inbaki mantaba alk'awari ne mukai dake cewar insha Allahu baxaki tab'a bari kowa yagane bake kika haifi teemah ba to sai gashi akan son zcy zaki ganar da mutane su fahimta banaso ki Kawo tsaiko akan rayuwar teemah inaso kiyi duba da yanayinta bawai sonkai nakeba nibana nuna banbamci ko wani abin kk ga nayiwa teemah banyiwa feenah ba walh nayi hakane saboda taji haushi tadage tabada k'aimi tayi k'okarin kanta Amma ke naga a kullum burinki shine kiringa nuna musu bambanci to walh banyardaba kibar wannan maganarma yanda mukayita anan kirufeta anan

Kibarsu Suyi Soyayyrsu kada kiraba tunda shiyanuna teemar yakeso aishikenan ita feenar ta hkr dama munyi magana da Alh mansur akan Hussain yagaya masa yanason ita feenar naji dad'i matuka nanuna masa Na amince to kinga tun wuri kigaya mata ma gawanda zanbata tasawa ranta salama tafitar da Saifudden aranta


Hjy ta k'ule ta furzar da iska daga bakinta tasan halin mijinta sarai akan inyai magana baya canxawa tana kuma shakkarsa dole yanxu ta samu hanyar da zata rarrashi d'iyarta tunda yai mata nisa dady yak'iya

Tace"zanbata hkr kamar yadda kace Amma gaskiya banso wannan had'in nata da Hussain ba dama dai hassan ne don walh Hussain yanada zafin zuciya banjin zama zai iya d'orewa atsakaninsu tunda itama feenar ba kanwar lasa bace...

Yakatseta "tun wuri gara kigyara yrki tazama me iya saka dangana aranta kada kinuna mata wata d'abiar ta rashin kirki Aure kuma tunda muka shirya za,ai da Hussain ba canji intaga zata kwantar dakanta in anyi amatsayinta Na miji agunta tai biyayya ita tajiyo

Ta mik'e ranta ab'ace tabar masa falon yakalleta ya girgixa kansa yai tsaki kawai

Data sami feenah tagaya mata yanda sukai da dady bak'aramin dad'a turata sukaiba domin kuka taitayi tana cewa ita batason Hussain walh ko hassan dinne bataso

Taringa tumami momy nabata hkr awashegari ma ko sch batajeba da dady ya nemi dalilin HK saitace zazzabi take kwana biyu tana gida ba fita komai a kasalance take yinsa ciwon kai taringayi sosai damuwa ce takawo hkn

Teemah tasameta ad'aki akwance tahawo gadon tadafata tace" wuu! Sister jikinki zafi yakamata akaiki asibiti fa,sannu bari dady yadawo nafad'a masa,kinsha magani ko inkawo miki kisha?

Tai mata banxa teemah tace"ko kinada damuwane sister ko fad'amin kozan iya share mk kukanki.
"Sonake kibarmin Yaya deen sbd sonsane yasakani awannan halin...abinda yakamata tace mata kenan Amma saita galla mata harara

Teemah tayi mamaki sosai to metayiwa feenah? Ko wani ne yai mata laifi zata huce akanta? Abinda baitab'a faruwa atsakaninsuba,anya kuwa kamar wacce aljanu suka shigeta.

Da sanyin jiki tafuta tabarta Amma ranta yacushe datarin tambayoyi danbabu me amsa mata sune.

Tofa tun daganan feenah tashiga takun sak'a da teemah har rashin kunya take yi mata dukda sunkasance twins Amma ance musu teemah aka fara Haifa itace hasana tunda anhaifeta biyar Na asuba itakuma bakwai nasafe tabiyo bayanta tsiransu awa biyu

Ak'arshen shekara duka suna Hutu dady yashirya musu tfy k'asar London domin suyi ziyara

Aranar da suka dira Nabihat tafi kowa murnar ganinsu domin dama tanason itama taje Nigeria sbd kawai taga Yaya Deen Wanda sonsa ke d'awainiya da ita,tare suke kwana da teemah tasu tazo d'aya sosai itako feenah Yr baruwana da kowace bata saki jiki da itaba ad'akin da aka sauki momyn tama take kwana (d'akin Hjy Lubna)

Shiko Alh mansur suna tare da dady

Shiko Yaya saif yana tare dasu hassan da Hussain kullum suna futa zaga gari ana gobe zasu dawone ma suka futa da "yammatan k'annan nasu amota dansuma suga gari sunje wani hamshak'in guri Na hutawa suna zazzaune akan kujeru sunashan ice cream Hussain yace da Deen" my Broz wannan "yar k'anwar taka tafiya shan k'amshi taki sakar min fuska daga cewa inasonta Shikenan tayi blocked d'ina a whsApp da fcbk bansan daliliba Dan Allah my Broz katayani ban hkr inhar akwai laifin danayi bansaniba.


Feenah ta zub'ura baki taharareshi hassan dayake shi miskiline Na gaske yai murmushi kawai yadad'e yana son teemah Amma dayake yanada zurfin ciki baiyi gigin gaya mataba balle yabari taganema don yana gudun kada tayi masa abinda feenah taiwa d'an uwansa

Deen yakalli feenah yace" barni da ita saimunje gida zantambayeta anutse koma meye aixaki fad'amin ko my sister?

Ta yatsina fuska hardayin fari tace" _may be I will tell u_

Nabihat da teemah suka kwashe da dry takallesu tahad'a rai kawai taci gaba dashan ice cream d'inta.

Satinsu d'aya acan sukai musu sallama suka barosu da kewarsu Dan Asatin nabihat taji son datakewa Deen yadawo sabo taji tamkar tabiyosu sutaho saidai sch bayanda zatayi....


~*Auntyn Sayyada*~πŸ’˜
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐



_by_ πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


*KADUNA...*


~*Pg 6 ...*~
K'arfe goma da rabi Na dare tatura k'ofar gidan ta shiga da sand'arta ahankali tarufe ta tokare da turmi kamar yadda tagani takalli d'akin samarin gidan taganshi arufe dayake baxafi akeba bakuma mugun sanyi akeba dasauri tasanya kanta ckn gidan motsi taji a band'aki tayi saurin shigewa d'akinsu dankada Wanda yake ciki yafuto yaganta asirin ta yatonu

Tana shiga d'akin ta tararda k'anwar ta Aminatu(ummie) a zaune tarafka uban tagumi tana gyangyad'i tanajin motsin shigowarta tai saurin tashi tsaye tace"yawwa Aunty Aisha kinshigo walh hankalina yak'i kwanciya tun d'axu danaga futarki Dan Allah Aunty kidaina wannan futar Daren ba mutuncinki bane ace kina zuwa gun namiji amaimakon shiyaxo gunki Dan bada kai saidai ke kije yanzu kuma insu Yaya ko mallam yaganoki ? Mexaki fad'a masa nima fa kullum kinasawa ina k'arya don inkareki in anxo nemanki haba Aunty yakamata kiji tsoron Allah a ckn lamarinki....

"Ke " yarsa ido ya isheni haka,dama bakiyi bacciba knn ,kina jiran shigowata dankiyimin wa,azin k'alallahu ta,ala to walh tun wuri ki kiyayeni kafin Nayi maganinki banxa kawai.

"Yanxu Aunty kan nayi miki mgn akan kina futa bin maxa shine zaki cemin haka? Harma kicemin " yarsa ido Alhalin ina yruwarki ta jini da dole abin yaimin ciwo araina daga gyara kayanka kuma...

"Rufemin baki ya isheni haka uwar yn shishshigi kid'auke idonki akaina inba hakaba walh wataran saina fasa miki d'an mitsitsin bakin nan naki mekama Dana jarirai ko inxubar mk da hak'ora banxa kawai Yr rainin wayo harni zaki dubi idona kicemin ina bin maxa,watoma iskanci kk zargin nake zuwa?

Aminatu tace" aibama zarginki nakeba aunty shid'in kk zuw....duka Aisha takawowa Aminatu ita kuma tayi saurin kaucewa aiko Aisha ta girgixa kai taciji yatsa tai tsaki tace"da mana kitsaya kiga yanda ake futarda jini a baka, karamar Mara kunya.

Aminatu tai kwafa tace"aishikenan insha Allahu nakyaleki daga yau zansaka mk ido Allah ya shiryaki kigane. Tana gama fad'in haka takoma takwanta akan gado itama Aisha tahaye gadon tajuyawa k'anwar tata baya Kowa najin haushin kowa


***********
Malam zakariyya shine mahaifinsu babban mutum ne Wanda ake ganin mutumcinsa ackn unguwar domin shike limantar sallah a masallacin unguwar yanada almajirai dayake koyardasu domin yanada sani akan ilimin addini yayi xurfi a b'angaren nan baiyi bokoba d'anuwansa da suke ciki d'ayane yai boko mesuna Ibrahim Wanda "Yayan mallam suke kiransa da Kawu

Kawu Ibrahim yai Aure Amma matarsa ta rasu wajen haihuwa ta haifi d'a namiji kyakykyawa dashi tabarshi aduniya Wanda rik'onsa yadawo hannun matan yayansa Amma yana hannun Amaryar mallam d'in Dan Alokacin bata tab'a haihuwaba Akasaka masa suna Abubakar sunan mahaifinsu mallam Knn Amma sai suke kiransa da baffa

Inna halima mace mekirki ita take rik'e da baffa rik'on gaskiya da amana alokacin madara aka ringa bashi mekyau da tsada Wanda mahaifinsa Kawu kejigilar kawowa aikinsa yake a makarantar gwamnati yake koyarwa

uwargidan mallam inna A'i tanada yara biyu duk maxa don asannanma itama jego take d'anta Na fari suraj shekararsa hud'u sai Wanda take goyo Sa,an baffan wato Mukhtar

Matan mallam Kansu ahad'e yake hakan nema yasa alokacin da inna Halima ta haihu akasawa " yarta sunan inna A'i wato Aisha wasu sukance da ita humaira ammafa anfi gaya mata Aishan ta

Inna taji dad'in wannan kara da mallam yai mata hakama tasan Dan inna haliman nasone shiyasa haryasa d'in lallai dad'in zama ba abinda bayasawa anayi don ita alokacin azatontama tazaci sunan mahaifiyarsa zaisaka Amina saitaji akasin haka Ashe Takwarar tatace

Saida Aisha ta shekara uku sannan akai mata k'anwa zankad'ediya chakulet kala mekyau da ita dantafi Aisha kyau dukda Aishan farace ranar suna mallam yarad'a mata suna Amina sai suke kiranta da Ummie Amma wasu suna fad'a mata Aminatunta...

Tunda inna ta haifi Aminatu sai baffa yaringa rawar k'afa akanta kullum yana manne da ita inya d'auketa tamkar karya bada ita sosai yake k'aunarta har ransa baya iya nisa da ita adole yake iya tfy makaranta yabarta agida ko kud'in break aka bashi saiya raba biyu yasai wani abin yaxo mata dashi gida yace inna ta ajiyewa Ummiensa

Inna takanyi dariya tace"baffa kodai inyi maka tanadin Ummie ne inyi tuwona maina?

Inna A'i takanyi mata dry kawai tace"abine dai nayarinta Amma ai wannan shirmene daya girma zai iya watsarwa "

Hatta wankin Aminatu baffa taya inna yake suyi tare sannan abinci data fara ci baya cin nasa saida ita

Yasha samun Kawu yace yanaso yasaiwa Aminatu kayan wasa"

Kawu inya tashi kawo wa har Aisha yake had'owa yakance baxai nuna bambanciba domin Aisha babban sunane agunsa me muhimmanci don sunan mahaifiyar baffa ne da ita yanason duk wani mesunan

Wata muguwar shak'uwace tashiga tsakaninsu domin dataga baffa taita d'aga masa hannu Knn ya d'auketa taganeshi Knn harsaiya d'auketa sukuwa sauran yayunta su Yaya Mukhtar k'iwa take musu bata yarda dasu ko kad'an daxarar wani cknsu ya d'auketa taita tsaluma kuka Knn harsai in baffa yakarb'eta take shiru

Kawu ibrahim yana taimakawa mallam sosai akan harkar ckn gidansa da karatun yaransa domin duk su uku maxan a private sch yasakasu yaringa biya musu kud'in makaranta harsuka gama da suka zo shiga jami,a ma shine yad'auki nauyin yimusu reg, suraj da baffa yasama musu ABU Zaria suke zuwa a hostel suke zaune Amma suna zuwa gida kafin suyi hutuma insunso hakan shi kuwa mukhtar management yake zuwa

Alokacin su Aisha ana secondary sch Aisha tana SS3 itakuma Aminatu tana SS1 kowa ackn makarantar yasan Aisha karancy sunanta yai k'aurin suna hargun malamai

Aisha akwai fad'in rai da tak'ama da jijji da kai ga karyar tsiya tana kashewa k'awaye kud'i don neman suna banda kud'in da mallam yake bata takanje gurin Kawu tasameshi hargida yabata nera d'ari kullum wataranma d'ari biyu yake bata yace tabaiwa Yr,uwarta d'arin Amma saita hana ko kallonta batayima insukaje makarantar Aisha itace head girl a sch d'in shiyasa take taka d'alibai son ranta irin muguntar da take yine yasa dayawa d'alibai sukaci alwashin ramuwa akan k'anwar ta in tafuta futa asch d'in

Itako Aisha baiwar Allah ko k'awar arxik'i batada ita maganama bata dametaba balle tasami abokin fad'a gashi malamai sukan yaba da haxak'ar ta bata wuce ta biyar a aji


Shekarar Kawu ashirin da biyar yana teachin yaga babu ci gaba saikawai yai sha,awar yafad'a siyasa nan yafuto takarar chairman aiko "yan local grvmnt suka amince dashi to Amma babu kud'i ak'asa yaxowa da mallam shawarar ko gdnsa zai saida yasaka kud'in ackn hrkr ko Allah zaisa yahaye aifa nan mallam yahana yace kada yafara kudinsa zasu iya lumewa yaxo baiciba shikuma ba hanya ko wasu manya gareshi a ckn siyasarba balle ayi murd'iya abashi

Babban amininsa shike dad'a zugashi akai yad'aukeshi yakaishi gurin wani boka akan sunxo Neman taimako boka yace musu zaici zab'e za,a zab'eshi zaisami kujera zaiyi kud'i Wanda za,ai kwatance dashi to Amma harsai in yakawo maniyyin mace matashiya budurwa wacce d'a namiji baitab'a sanin taba ayi amfani dashi wajen Aikin samo masa Sa,a

Aiko dai Kawu Ibrahim yagigita da jin wannan zancen domin kwakwalwar Sa cushewa tayi da tunani shin wa zai tunkara yasami spearm ajikinta? taya zai iya wannan aiki me wahalar yiwuwa? Yacewa boka yabashi lokaci zai sake dawowa

Koda yaje gida baiyi bacci ba yaji gara yahakura Dan wannan Abu bamai yiyuwa bane

Cak! tunaninsa yatsaya akan Aisha " Yr yayansa tabbas ita yadace yasamu agunta Amma ta wacce hanyar ?

Yasanta tanada son kud,i indai ba dabara zaiyi yai amfani da kudiba wajen yaudararta haryasamu yacinma burinsa to ammafa dole saiya kusanceta shin anya zai iya....?


~*Auntyn Sayyada...*~πŸ’˜
[5/21, 13:04] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_ πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*πŸ’˜Β©



~*Pg 7...*~
Aminatu yarinyace me nutsuwa ga hankali akwaita da girmama nagaba da ita tanada sanyi gata da alkunya tamkar bafulatana

Aminatu ba fara bace bakuma bak'a k'irinba zamu iya kallonta a wankan tarwad'a kyakykyawa ce tanada doguwar fuska ga hanci harbaka,ga dara daran idanu da d'an bakinta d'an mitsitsi tanada gashi har gadon baya kitso baidame taba tafiyin kalba kotayi farkin d'anshi

Tunda Aminatu ta taso taga yanda Yaya baffa ke mata d'awainiya yake nuna mata gata fiye da yayarya Shikenan zcyrta takwanta akansa Allah ya d'ora mata k'aunarsa Amma bata tab'a tunanin tayi gigin gaya masaba sbd tasan ba mutuncin mace bane fara nuna tayinta akan namiji babu mutunci kwataΒ² ace mace tafara fad'awa namiji cewar tanasonsa Dan haka saitabar abin a ckn ranta taita renon soyayyarsa har zuwa ranar da Allah ya yanke mata yafurta mata shima

Yaya baffa yaso Aminatu tun tana k'aramarta soyayyar da yake mata ta dabance ya Adana ne sbd yaga tanada k'uruciya saida yaga tamallaki hankalin kanta alokacin ta shiga SS one sannan ya furta mata tofa tundaganan suka fara gudanar da tsaftatacciyar soyayyar su

A kullum inta dawo daga makaranta saita shiga tagyara d'akin yayun nata tashare ta goge tas ta wanke toilet dukda Yaya baffa ba,a kadunan yake da zamaba Amma baya ganin Nisan zariya da Kd,Dan haka duk weekEnd yana gida sbd Aminatun Sa shikuwa Yaya suraj sai anyi Hutu yake dawowa gida ko wani abin yake buk'ata baffa ke karb'o masa yakai masa

Kowa yasan da wannan soyayya ta baffa da Ummien nasa mallam yaji dad'i sosai haka iyayansu mata sunsawa abin albarka

Itako Aisha dama ba shiri take da baffanba sbd yawan fad'an dayake mata intayi laifi a ckn gidan gayanda take Tara samari indare yayi tayi zancen da wancen me motar tayi da wancen me mashin d'in danma Mukhtar yana taka mata burki tunda shi kullum yana gida tana d'an shayinsa Amma Aisha kar take zcyrta a k'ekashe take batada mugun tsoro nawasu "yammatan zamanin


Alokacin da Aisha tazoyin candy saita rabawa k'awayenta iv akan zatai party

Tasami mallam da zancen anan ya fattataketa yace ba,a gidansaba wannan rashin mutuncinsa ana ganin girmansa a unguwa yasan indai akace party to sai maxa sunzo gurin anyi bad'ala

Taringa kuka tana d'ora hannu aka kamar wacce akaiwa rasuwa tashiga uku itakam antsaneta agidan aranar Mukhtar yakusa bugunta danta gudune dayayo kanta aiko dai taringa masa gunguni tana cewa ina ruwansa da ita"

Har gida tasami kawunta tashaida masa tana kuka aifa Kawu ya bata hkr yace zaixo yasami mallam anjima

Da Kawu yaxo yaringa rarrashin mallam akan yabarta ai babu maxa matane sallah zasuyi a ckn makarantar ake irin wannan partyn candyn to anan nefa mallam yabari


Dubu ashirin kawun yabata har Alqawarin sai mata sbwr waya yayi nangaba(duk sbd qudirin dake ransane)

Ranar da Aisha zatai prtyn batayi a ckn makarantaba guri takama Na musamman tagudanar da taronta kuma harda maxan Dan k'awayenta sunxo da samarinsu anan ma wani had'add'en gaye daya rako saurayin k'awarta ya k'yasa da ita yanuna yana sonta dayake taga yanayin shigarsa ba k'arya yad'au wanka motarsa tana shek'i tuni ba musu ta amsa masa yakarb'i nambarta Dan aranarma shiya kaita gida Amma bata yarda yak'arasa da ita hark'ofar gdnba anesa tasauka tanuna masa gidan,

tofa tundaga wannn ranar suka k'ulle da Adam Vila Wanda basa haduwa sai agidansu wata k'awarta ya d'auketa ya yawata da ita yadawo da ita gdn su k'awar yana bata kud'i tasaki jiki dashi

Aranar da Kawu yai mata Alqawarin siya mata waya bata mantaba taje tasameshi har gida da magariba ranar wata laraba yana falo azaune yana ganinta yai ajiyar zcy don aranar yaci burin ya aikata abinda bokansa yasakashi Yy.

Sabuwar wayar android yabata fara sai d'aukan ido take dubu ashirin yasiyeta taringa murna yakawo lemo me d'aukeda sinarin kashe jiki yabata batai gardamaba ta karb'a takurb'e tana ayyanawa aranta lallai kawunta yana qaunarta ita d'in "yar gatace agunsa

Tana gamasha da sakanni taji jikinta ya mutu murus idonta yana limshewa alamar bacci takeji menauyi ga wata muguwar sha,awa data kamata

Nanyaga abin yafara kamata babu alamar kunya atare dashi yaja ta zuwa bedroom d'insa yakwantarta agado yasille mata kayan jikinta yafara aikaΒ² da ita saida yagama biyan bukatarsa da ita yasami abinda akasakashi samu ajikinta sannan yadawo yaji dad'i aransa yanata xufa yana kallonta nan kuma yaji nadama tashigeshi yiyanxu mexaice da ita?

Take k'azamar zcyrsa ta ringa bujiro masa da hoton irin arxikin da zaiyi nangaba saikuma ransa yai fari yahau murmushi

Koda ta dawo hayyacinta tafurgita matuk'a gaya taringa kuka data fahimci abinda yaimata aiko masoyinta Adam bata yarda dashiba saidai suyi romance kawai dukda d'an Luv ne Amma bata yarje masa sunyi making Luv ba saigashi kawunta da take ganin girmansa ya haik'e mata batasan dalilin saba

Nan yaringa lallashinta yana bata baki yace mata" kiyi hkr Aisha walh sharrin shaid'an ne baxan sake mk ba Dan Allah kada Ni fad'a kowa kinji nayi mk Alqawarin zansai mk mota in nasami kujerar chairman kinji?

Tofa nan zcyrta ta girgixa wai! Ace tamallaki mota ai zata fantama zatayi garari gata dama ta dad'e dasanin ta zata dace da mota kowacce irice...
Yakatse mata tunani da fad'in" inhar kk rufamin asiri to walh mota sai wacce kikeso zaki hau dakanki zaki zab'a Aisha kuma metsadar gaske zansai miki,

Tayi murmushi tace"to Kawu baxan fad'a wa kowaba ya wuce,,
Ta mik'e tasaka kayanta yakawo kud'i dubu goma yabata yace tasaka kati

Tofa tunda yakashe bakin tsanya Shikenan bakinta gum babu Wanda yagane abinda suke ciki itada kawunta

Abin Allah sai Allah ya ara musu lokaci da xab'e yaxo Kawu Ibrahim yalashe k'uri,a yasami kujerar chairman kowa yatayashi murna har walima aka tsara su suraj da baffa suka dawo gida akayi walimar dasu yatara manyan malamai yasa sukai masa saukar karatu yabasu sadaka

Cikin "yan watanni da hawansa arxik'arxik'i ya fara bunk'asa yabiyawa yayansa da matansa kujerar hajji sukaje yasaiwa yaran maxa mota anan yafake yasaiwa Aisha yacika mata alqawarinta to Amma sai mallam yahanata hawa yace yafiso yaga tafito da miji tayi Aure inyaso tahau a gdn mijinta

Ab'oye Aisha suke had'uwa da Adam tunda tasan kawunta yakarb'e mata budurci Shikenan tasakarwa Adam shima yake gurxa

Aisha tana fantamawa su inna sukanyi mata fad'a akan yawan futar da takeyi saitace musu gidajen k'awayenta take zuwa sada zumunci

Saitaga mallam yana masallaci take fucewa Dan inya futa sallar magriba baya dawowa gida

Please Login or Register in order to submit comment