You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da aka tashi again ita malaminsu mallam Abdulhadi ya kirata donta rufe taro da addu,a

Ta taso da nutsuwarta tatsaya gaban dubban jama,a taringa kwararo zafafan addu,o,i suna amsawa da amin tana shafawa al,ummar annabi nagun kowa ya shafa wasu harda yin kabbar

Hjy Salma harda hawayenta gani take sosai Teemah diyar cikin tace tabbas zcyrta tayi mata amanna dolene tabi yrnyr gidansu domin tajiyo gaskiya kada ta tafi tayi sake da wannan damar a kullum dama bata fidda rai da ganin yrta sbd tasha mafarkin sun had'u to yau tana fatan Allah yasa wahalarsu taxo k'arshe Allah kuma yasa zatonta ya tabbata baxata yi saurin kiran mijintaba don yanxu saiya baxamo yaxo gun sbd yafita shiga damuwa gara saita tabbatar tukunna yaji komai

Takalli k'awarta Hjy zulai tace"nifa saidai nai miki sallama zantafi wani guri ba tare zamu tafiba zanje gurin mahaifiyar saif ne zan lalubota acikin taronnan mugaisa don akwai yrta ackn "yan saukar zanmata murna.

Hjy zulaihat tace" to ba damuwa saimun had'u.

Hjy Salma ta tashi tabar gurin kamar yadda aka fara watsew a sai gurin yacushe k'ura taringa tashi Na sawayen dubban mutane

Ta kira d'anta deen awaya tana tambayarsa yana ina yagaya mata suna bakin motarsu yai mata kwatancen inda suka ajiye dayake tagane gun saita nufi gurin gabanta yanata faduwa taringa addu,a danbatasan mezai faru ba bata tab'a jin irin wannan faduwar gaban ba.


Da inda tayi parking motarta babu nisa da inda suma sukai parking tasu motocin guda uku.

Tun kafin ta isa garesu deen yai saurin tarota yana fad'in"oyoyo Ummana naga kinyi mana baxata kinzo harkin raba kyaututtuka Munji dad'i dafatan kinga Teemah tayi miki?

Yafada yana fara,a itako gabantane yabada dum! Badai fateemah Lurwan d'in datake jinta aranta tana ganin itace "yarta teemahn ba?

Takalli deen tace" wacce ce Teemah aciki,badai Fatima Lurwan ba?

Ya d'aga kansa yana fad'in "itace Umma itama tafara karb'ar kyautarta itace kuma tafara bud'e taro da addu,a kuma itace wacce ta rufe taro da addu,ar gatacan amota ma muje kiganta,yana gama fad'ar haka yai gaba zuwa gun motar gabanta yaci gaba da faduwa

Su hassan suna zuba kyautukan da Teemah tasamu a ckn but suka gaidata har k'asa deen yace" Umma gasu hassan da Hussain fa'

Hjy Salma tace"lallai su hassan kungirma nasan kunmanta ko? kunyi Aure ne?

Dukansu sukai murmushi deen yacafe da cewa"ba Wanda yai Aure suna dai nema gwaurayene kamarni anan "

Hjy maryam tafito taxo suka gaisa tace"Hjy Salma kincika alqawari kinxo munji dad'i sosai harda kyaututtuka Allah yakara budi,

Hjy Salma tace"amin,yau naga teemah surukata ina alfahari da ita naji dad'i anata yabon kwaxonta agurin deen yacemin itace Fatima Lurwan data rufe taro da addu,a,"

Momy tayi murmushi taji dad'i har ranta nayabon Teemah da akayi tace"kwarai itace yau Allah Yy kunga muna bari inkirata kugaisa ,

Ta leka ckn motar dasu teemahn suke tagaya mata taxo sugaisa da Umman deen Akunyace tafuto tai mamakin ganin wannan kyakykyawar matar data raba musu atamfofi lallai Ashe akwai danganta Knn,Ashe surukar tace toko taganeta ko deen ya tab'a nuna mata hoton ta shiyasa taringa mata murmushi? Da walakin dai....sun gaisa da Umman takoma ckn mota da sauri tanajin nauyinta su feenah da nabeehat ma suka fito suma suka gaidata Hjy Salma taleka motarsa Alh Lurwan suka gaisa Hjy Lubna takama baki tace"a,a lallai Hjy Salma rai kanga rai Ashe zamu had'u? Hjy Salma da fara,arta tace"gashi Allah yakawo dalilin haduwar, kinyadani kota waya bama gaisawa wato saidai kuyi zumuncinku da Hjy maryam sbd deen yana gunta?

Murmushi Hjy Salma tayi tace"ba haka bane sha,anin aikine yake boyeni itama hjy maryam din mundade sosai bamu haduba tun atsohon gidanta kema yanxu ai tunda Allah yahadamu saimu karb'i nambar juna ko Allah zaisa wataran naje muku ,

Hjy Lubna tace "toshikenan ba matsala ,wane Aiki kikeyine?

Hjy Salma tace" Lauya ce ni yanxuma tare mukaxo da ma,aikatan mu don shugaban makarantar nan d'anuwan alqalin mune shimuka zowa kara,
" kunyi anko da d'anki Hussain shima a kotu yake Aiki saidai shi bai dad'e dafarawaba"


Hjy maryam takalli Hjy salma tace"to Amma zamuje gidan dake ko tfy zakiyi?"

Hjy Salma tace"zanje mana inaso ingano gidan domin akwai wata magana danake muyi dake "

Hjy maryam tace"toshikenan biyomu muje"

Hjy Salma tana binsu abaya ckn motarta har sukaje gidan megadin yabud'e musu sukai parking a can parking space suka fito suka shiga ciki da jama,a agidan sbd za,ayi kwaryaΒ²r walima agidan

A sitting room suka zazzauna hajy maryam da Hjy Lubna sai Hjy salman sai dady da Alh mansur dadyn su hassan

Hjy maryam tace"bari nasa akawo mk kayan motsa baki"

Hjy Salma tace"kafin nan Dan Allah kitaho da Teemah domin ta naxo akanta nakeso muyi maganar"

Hjy maryam tace"to! Ikon Allah! bari naturota

Momy ad'aki ta tarar da Teemah tana latse latsen waya jikinta duk asanyaye yau ranar farin cikin tane Amma kuma gabanta yanata faduwa batasan daliliba sai addua taringayi azcyrta

Hjy maryam tasanar mata kiran da Hjy salman ke mata nan gabanta ya k'ara faduwa Allah dai yasa lfy tanajin nauyin surukar nan tata Amma ita taga wayayyi yace bata jin komai

Dasallama tashiga suka amsa mata tasami guri ak'asa tazauna kanta ak'asa itako Hjy Salma murmushi kawai take tana kallonta tana addu,ar Allah yasa zatonta yazama gaskiya

Hjy maryam tashigo tazauna tana fad'in"to Hjy Salma ga teemahn wace magana ce zakiyi?

Dady yace"toko mufuta mubaku guri kwafi sakewa?

Hjy Salma tayi saurin girgixa kanta tace"a,a Alh basai kunfita ba maganar me muhimmancice kuma yakamata ace kuna gurin"

Hjy maryam tace"to Allah yasa ta Alkairice"

Hjy lubna tace"Amin"

Hjy Salma tagyara zamanta tace"to dafarko Alh Kaine namiji watakila zakafi fahimta ta akan zancen danaxo muku dashi ina fatan zakuyimin kyakykyawar fahimta akai Dan Allah kugarceni domin zcyta ce takemin shakku akan Teemah domin ina ganin kamar itace "yata data b'ace shekara 20 da suka wuce tun tana tsumma,


Hjy maryam tayi saurin mik'ewa tsaye takalli Hjy Salma kallo Na rashin fahimta tace"wannan wane banxan zancen mekike nufi?

Hjy Salma tace" Dan Allah kizauna magana ce zamuyi ta fahimtar juna kitaimaka kigaya min shin awane asibitin kk haifi yrki Teemah dakuma wace rana...?

"Dakata Hjy Salma banason tambayar rainin hankali ke a asibiti kk rasa Yr taki koya? Kuma keya kamata naiwa wannan tambayar bawai nizakiyiwa ba

Sannan alokacin Dana haifi Teemah su biyu sukaxo duniya mijina shedane yana ckn asibitin nahaihu haka duniya ma shaidace kodon kinga basuyi kamaba,sannan alokacin Dana haihu nabuga wayarki nagaya mk haihuwar saikikace baxaki sami damar zuwar minba don kema kinhaihu Amma " yar taxo barai ko bamui hakaba? Tafada tana tsatstsare Hjy Salma da ido ammafa gabanta ba abinda yake sai faduwa tabbas bata fatan abinda Hjy salma taxo dashi yatabbata domin tana qaunar Teemah baxata iya rabuwa da itaba

Hjy Salma hawaye yazubo mata takalli Teemah data zubo musu ido cknta ya d'uri ruwa yaume takeji?

Alhaji Lurwan shima ya firgita da wannan batu Na Hjy Salma Alh mansur yakalli Hjy salma yace"toke awane dalilin kk yarda d'an mutum sukutun ko sace miki ita akai?


Girgizakai Hjy Salma tayi tana goge hawaye idonta yakada yai ja tace"walh har kullum ina nadamar biyewa zcy danayi akan inbi ra,ayin mijina dukda alokacin akwai yarinta... Hjy Lubna tace"kina nufin da kk haihu sai mijinki yace kiyar bayaso?


Dady yakatsesu"kudakata kada mu tsaya wani tambayeΒ² Hjy Salma bamu labarin duk abinda yafaru dake abaya da dalilin ki nacewa Teemah "yarkice.....


_muje zuwa_...

~*Auntyn Sayyada da Shahida*~πŸ’˜
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


~*Pg 25-26*~

Hjy Salma tagyara zama takallesu d'aya bayan d'aya sannan ta fara basu labarin kamar haka:-


Γ—Γ—Γ—Γ—Γ— Γ—Γ—Γ—Γ—Γ— Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—
Alokacin Dana Auri mijina kamal akwai soyayya me k'arfi atsakaninmu Wanda atun farko kafin Na Auri mahaifin deen shinaso Na Aura Allah baiyiba Na Auri kamal yana sona ina sonsa saidai son da nake masa yaxarta nasa ina masa tsananin biyayya ina shakkarsa

Kamal d'an gayune d'an boko aturai yai karatunsa dan hakanema yakwaso wasu daga ckn d'abiunsu Na rashin son haihuwa da wuri kokuma rashin son Tara "Yaya dasukeyi

Tun kafin muyi Aure dashi mukai yanunamin cewar inhar mukai Aure bayaso nahaihu da wuri at less yanaso Nafi shekara goma kuma kozan haihun kada muwuce " Yaya 2 ko 3

Ba musu ba jayayya Na amince masa

Haka ko akai Dan da mukai Aure kamal maganin FML planning yaringa kawomin inasha bana munafurtarsa tsakanina da Allah nakesha har Na shekara uku bandamuba saboda nima alokacin karatu nake Na low

Alokacin Dana tafi digree Na Na biyu saina canxa planning nadawo yin allura ita kuma shekara biyu nayita Amma saita ramar Ni tasa nake yawan bleeding saina masa complain saiyakaini asibiti aka canza wani tsarin akasamin inplan a hannu Na shekara uku

Alokacin Dana gama karatuna kafin nasami Aiki ina zaune agida nid'aya kwal sai nake kewar yara naita sha,awar ace nima Na haihu ga shekaruna suna tafiya hatta Yaya mus,ab yayana da mukai Aure kusan tare yaransa uku maza biyu da mace d'aya

Yayar mijina tasha zuwa tasani agaba taringa min tambayoyin ko dai planning nake nakance mata a,a Allah nedai bai kawoba takance inma planning d'in nake sbd karatu nake boye mata to yanzu aina gama gaskiya intaji shirun yaiyawa zamuje asibiti dukanmu aduba mu tanaso taga jinin kaninta danshi d'aya kwal gareta

Natsorata da kalamanta nasameshi da zancen nace gara tun wuri muhakura kawai kada aganomu kotasa yai Aure

Kamal yanuna b'acin ransa akan wannan yr magana tawa waishi in haihuwa nakeso tomu rabu naje nahaihu da wani mana in "yayane ba inada d'a ba meye Na damuwa kuma batun Aure baiga Wanda zaisashi ya k'ara ba danvayada ra ayin k'arawa

Naso Na hakura nabi tsarinsa Amma saina kasa daurewa naje aka ciremin in plan

Aiko nacireshi da wata uku nasami ciki

Tabbas Dana gano inada cikin sai hankalina yakwanta Amma awani b'angaren Na zcyta tana fargabar hln da zamu k'are da kamal

Aiko dai Bai fargaba saida ciki ya fito

Cikin yashiga wata takwas yadawo daga wata tafiya Dan wata uku yai acan wani cos ne da aka k'ara masa girma daya dawo


Yasha mamaki daya ganni da cikin yatambayeni meyake gani nace cikine Allah yabani Dan in haihu

Yatambayeni da ixinin wa nadaina planning d'in?

Cikin dakiya nace" da yardar Allah da ixininsa"

Yakufula yace"aiko ko a zubarshi ko inje innema masa uba murabu kwataΒ²

Naringa kuka koyaji tausaina Amma kamar Wanda aka yiwa asiri akan k'in "Yaya ya dake yama daina nunan kulawarsa akaina yaraba d'aki dani kallo ban isheshiba Aiki ma danake nema yahana yace ba agidansaba

Niko inaso inyi Aiki nasameshi da zancen meyakeso daga gareni Wanda innayi zan faranta masa ?

Saiyace " zubda ciki"

Nace dashi"Ai ciki baxai xububa Dan yashiga watan haihuwarsa in akace za,a cireshi saidai arasamu gabaki d'aya

Kamal yanuna shifa yananan akan bakansa saidai ko inna Amince inhar Na haihu to insan yarda zanyi da abinda nahaifa ko inya ko inkai gdn marayu

Walh har raina Na amince sbd son kwanciyar hankalinsa da shairrin shaid'an

Aiko ganin Na amince da abinda yatsara tuni ya yarjemin nayi Aiki Dan dakansama yafara nemarmin.....


~*Auntyn Sayyada da Shahida*~πŸ’˜
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_ πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


~*Pg 27-28*~

Ganin Na Amincewa kamal cewar idan nahaihu zan rabu da abinda Na Haifa d'in nazauna dashi nacigaba da planning din sai kamal yasake dani ba kmr da ba daya juyan baya saiya dawo sakarmin fuska

Munyi abinmu a sirrince duk da bana tona asirin mijina balle wannan danasan babban abune Dan haka saina boyeshi ckn raina saidai abin yana nuk'urkusata nabi duk Na rame sai k'aton ciki ajikina sai k'ashin wuya dasuka fitomin akwai jindadi dai atattare dani tunda ackn arxik'i nake nagodewa Allah


Yayar kamal Aunty Amina tunda taga inada ciki sai hankalinta ya kwanta saidai tana yawan Kawo k'afarta gidana wai nan kulawa take nunamin komai tasiyo takawomin dake mijinta me haline siyayyar haihuwa kuwa tunda nace mata nashiga EDD d'ina ta jubgo kayan babies wai babu abinda bazataiwa jinin kamal ba domin ciki d'aya yafi k'arfin wasa shi d'aya kwal gareta kuma ahannunta yatashi

Tasami kamal da maganar wai tanaso inkoma gidanta dazama har inhaihu domin zata bani kulawa sosai

Kamal bae b'oye mataba donba "yar kunya suke da itaba yafito fili yace mata bae amince ba ko gidanmu bai yarda najeba

Haka Aunty Amina ta hakura Amma bataji dad'i ba saima ta d'auke k'afarta nasan fushi tayi shiko yayi hakane sbd yasan shirinsa akaina

Kulawar da kamal yake bani ba kamar dai daba zai kwana a d'akin danake Amma baya kusantata zamuyi hira Amma ba kamar daba kafin nasami ckn Toni hakan ma yafimin lokacin daya shareni don nasan inna haihu narabu da ckn da abinda ke ckn cikin zamu dawo normal dashi

Aranar da nak'uda takamani kamal baya gari yaje Aiki Kaduna banbuga wayarsaba dama kayana suna kammale Na haihuwa Na d'ebi kud'i natafi asibitin *Khadija clinic* Wanda tunda nashiga da magriba bani Na haihuba sai k'arfe biyar Na asuba mace nahaifo mekama da ubanta kunji k'udira ta Allah ba , baxan tab'a mantabawa ranar talace aranar.


wata Norse data karb'i haihuwata Na nemi data bani takarda da Biro zanyi rubutu haka ko ta nemomin takawomin narubuta bayani akan " yar nabayyanawa duk Wanda ya tsinceta cewar wannan yrnyr ba shegiya ba da ubanta ta hanyar sunnah Na haifeta babban daliline yasa rabuwarmu Na fad'i sunana Dana mahaifinta tareda zabar sunan daza,a saka mata Fatima domin sunan mahaifiyar megidanace,

Bayan nagama wannan rubutu nalinke wasika nasakata acikin envelop d'in Dana zuba mata kud'i naira dubu d'ari da hamsin

Da sassafe ko bakwai banbari tayiba nabaro asibitin nan bantsaya ako inaba sai a bayan wannan asibiti Dana haihu Na ajiye "yar agindin wata bishiya ina kuka raina nasuya nabarota badan nasoba cikin tsumman zani tana kuka nabarta natafi ina cwn rai najin kukanta hr ckn raina

Koda naje gida sainayiwa kamal waya nasanar masa duk abinda yafaru abin mamaki murna yayi kamar wani susutacce harda yimin kalaman soyayya Wanda ya dad'e baeminba

Aranar yadawo yaiwa " yan uwansa danawa waya kan cewa nahaihu Amma "yar batazo da raiba.

Ahaka muka bunne kowa akaita tausayamin

Bayama Aunty Amina kwananta uku agidana tana gasani tabbas tana qaunata matarnan data tafima duk kwana biyu tana zuwa ganina ta tayani Aiki

Tofa soyayya sabuwa nida kamal tamkar sabuwar Amarya haka yaringa d'okina yaringa nunan qauna tamkar yacinyeni akwai wata tafiya dayai sarin kaya zuwa k'asar Togo watansa d'aya yazomin da zoben azurfa mekyau guda biyu daya nasa d'aya nawa Wanda yace wannan zoben alkawarine atsakaninmu babu rabuwa babu batun yin kishiya harafin sunansa danawane a jikin zoben anyi zanen harafin da ruwan kalar goldin taciki.

Bayan wata biyu da haihuwa aikina yafito nafara Aiki a kotu cikin kwanciyar hankali domin kuwa inajin dad'in k'aunar da mijina yake nunamin domin kamal d'an soyayya ne ga iya sace zcy sannan gashi yaimin alqawura nabaxaimin kishiyaba Ni d'aya Na isheshi yana nan nan dani shike kaini yadaukoni amotarsa duk dankar nasha wuya

Saidai fa planning ana cigaba da yinsa domin bana k'etare dokarsa shikansa yana fad'a yanajin dad'in irin biyayyar danake masa yasan babu macen da xata iya abinda nai masa

Intak'aice muku bayan shekara d'aya da haihu wata sai Allah ya bujurowa kamal k'aunar son " Yaya dakansa yazomin da zancen yakamata inbaryin planning kada mahaifata ta lalace yau yaji illar yin dogon planning barema macen dabata tab'a haihuwaba aranarfa yaringa nadamar sani dolen daya ringa yi Ashe wasa farin girki domin koda nadaina Allah baibada abinda akesoba ciki shiru yak'i zuwa ada nafishi damuwa Amma saigashi damuwarsa ta linka tawa barema dayaga girma yaxo masa kuma yasami matsala shima daga yimasa Aiki a ciki za,a cire k'aba Shikenan aka gano masa cewar bazai tab'a haihuwaba asakamakon wani Abu dake da mahad'a da kwan haihuwarsa yasami matsala

Yayi magungunan har angaji yajejje asibitoci yafi biyar ko inadai zancen d'aya ne

Duk yabi ya rabe yashiga damuwa kullum saiyayi nadama bayama ganin Ni inada Wanda zankalla naji dad'i aduniya kogani yayi saif yaxo gaisheni aranar sainaga canjin yanayinsa harkuka yake da idanunsa Nike tausarsa

Tabbas dama duk abinda kayi nasab'on ubangiji saikaga ba daidaiba arayuwarka

Nikaina nasha mafarkin Allah yahad'ani da "yata cikin kyakykyawar shiga da kamala nakanji dad'i inkasance ckn farin ciki kullum kamal yana addu,ar Allah yabaiyana mana " yarmu inda rabon zamuga juna domin bamu tab'a fudda raiba naganinta sbd addu,a bata faduwa k'asa banxa

To wannan shine labarina da dalilin dayasa nace muku Teemah "yatace ta cikina Ni Salma.....
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv*Β©πŸ’˜


~*Pg 29-30*~

Jikin Hjy maryam yai sanyi hawaye taji yana zarya kan kuncinta tabbas tayarda da zancen Hjy Salma itace ta haifi Teemah ba jayayya shedu sun nuna domin duk abinda ke ckn wasikar da suka gani haka Hjy Salma ta fad'a tabbas itace ta rubuta

Dady kuwa axcyrsa yahau fad'in"lahaula walaquwwata illah billah...tabbas basuda tsimi basuda dabara akan wannan sark'ak'akk'en labarin yana ganin ma gara d Allah ya bayyana Hjy salman domin da bata gano teeman ba da anyi babbar katob'ara wa ya Auri k'anwarsa ciki d'aya

Allah Lurwan (dady) cikin sanyin jiki yakalli Hjy Salma yace"Tabbas Hjy Salma babu musu azancenki munyarda kece kk haifi Teemah domin kuwa tsintar ta mukai.....

Dasauri Teeman ta mik'e tazaro ido da mamaki tanuna kanta tace"dady niba "yarka bace dama? Hawaye ya zubo kan kuncinta me d'umi

Hjy maryam ta janyota jikinta tace" kwantar da hankalinki Teemah kada kisa damuwa aranki kigodewa Allah dakika zamo "yar sunnah kuma iyayanki Na Raye, sannan muma dole mui godiya ga Allah da hakan ma ya kasance da wuri domin yayanki deen muharramin kine Ashe kinga babu Aure atsakaninku tunda kunsha nono d'aya dashi.

Alh mansur da Hjy Lubna dasuke zaune mamakin abun ya cikasu sunkasa cewa komai domin tabbas basu tsammaci zancen Na Hjy Salma zai xama gaskiya ba kamar a ckn shirin film suke kallon abun,

Alh mansur shiya fara magantuwa dacewa" Amma wannan zancen yabani mamaki Alhaji domin babu Wanda zaiyi tsammanin fateemah Yr tsintuwa CE a ckn gidannan tabbas kunyi k'okari Na yimata kyakykyawan rik'o tabbas tasami tarbiyar dako "yar cikinku bata sameshiba,gashi kuma abin Allah sunan da kuka rad'a Na mahaifiyarka shine sunan da mahaifiyarta tazab'a sunan Kakar tace tabbas Fatima kinxama " yar baiwa kigodewa Allah tunda har haka takasance gareki da wuri ba,akai da daura muku Aure da saif ba,

Hjy Lubna tace"to yakamata wannan zancen ayishi agaban deen domin yasan halin da ake ciki

Hjy maryam tace"bari nakirashi ta mik'e ta futa

Itakuma Teemah kallon Hjy Salma kawai take tana jinjina abun a ckn ranta gani take kamar a mafarki kokuma zasu dawo suce mata da wasa suke bada gaske sukeba

Ashe son dataji tana yiwa Umman ganin farko datayi mata Ashe soyayya ce ta uwa da d'a Knn? Lallai dole ne taji ajikinta itama tana sonta tawani b'angaren dad'i taji aranta domin koba komai Hjy Salma uwace da za,asota tayaba dakyan halayenta duk da taji dad'in su dady samun irinsu sai an tona tabbas zataji ba dad'i rabuwa da momy da dady

Yanxu Shikenan Yaya deen ya tashi daga masoyinta ya dawo d'an uwanta Na jini? Yanxu Shikenan babu Aure atsakaninsu Ashe irin yanda take jinsa aranta take masa muguwar k'auna shima hakan yatafi abanxa dama Ashe d'anuwantane Na jini tabbas wannan ikon Na Allah akwai ban mamaki ciki..

Hajy maryam tashigo da sallama abayanta deen ne da Feenah da Nabeehat suma suka shigo da sallamarsu

Suka zazzauna ak'asa

Alh Lurwan yakalli yayaa deen yacea"Saifuddeen yau zakaji labari me ban mamaki akanka da kan "yar uwarka Teemah Wanda bak'a zata ba, akace ranar wanka ba,a b'oyen cibi labari zanbaka Wanda muka b'oyeshi aranmu nida momynku domin rufuwar asirin Fateema

Yanisa kana yaci gaba " wato shekaru ashirin da suka wuce alokacin da momy ta haihu a asibiti ta haifi feenah bayan ansallamomu munfito ahanyarmu muna tfy ta wajen jen bayan asibitin naji kukan jaririya Nafaka nagacewa Hjy bari naje naji komeye,to alokacin tsoro hajy taji Dan da ace nabiye ta tata da baxan jeba

Amma dayake Allah yarubuta komai saida naje naga jaririyar ayashe agindin baishiya cikin tsumma tasha kayan sanyi sai kuka take nayi k'arfin hali nadauketa nakawo ta ckn mota nadankawa Hjy maryam ita nace Allah ne yabamu ita

Alokacin Hjy maryam k'in ta tawa tayi tace saidai mukaita gdn marayu nikuma nak'i ta tata nanuna mata cewar mundad'e muna nema yau Allah yabamu harda ajiyarsa baikamata muk'i karbata dataga cewar raina yanason rik'on jaririyar dole ta amince anan muka shirya yanda zamu gayawa mutane cewar "yan biyu ta Haifa

Acikin zanin da muka tsinci jaririyar munga zoben azurfa samfur Na daban sannan akwai kud'i sai wasika da akayi bayani kan cewa ita ba shegiya bace an fad'i sunan ubanta kamal mahaifiyarta Salma bakuma kowa bane wadannan iyayan nata sai Wannan hajiya salman dake zaune gabanka deen!

Alh Lurwan yaci gaba" hajiya Salma mahaifiyarka itace mahaifiyar Teemah ayau Allah yaganar damu...deen ya mik'e tsaye da sauri kansa nasarawa yanuna Ummansa yace"Ummana itace ta haifi Teemah? _for what reason_?
Dady Kana nufin kacemin baku kuka haifi Teemah ba? Dama tsintarta kukai

Dady yace"kwarai kuwa domin tunda muka sameta Allah yabamu ita mukai Alqawarin rik'e amanarta bamuda nufin mugayawa kowa wannan zancen to Amma ayau Allah yabayyana mana kosu waye iyayanta mungode Allah domin hakan yazama taimako daga indallah tunda da bamu gane hakan da wuri ba har kukai Aure aikaga da anyi aika aika domin cikinku d'aya...

Deen yakalli mahaifiyarsa yace"Umma idan har dagaske ke mahaifiyace ga Teemah taya akai kuka rabu shin awane dalili kika yarda ita,ko sace ta akayi alokacin?


Hjy Salma ta kalli deen tace"zauna tukunna sai inbaka labarin komai Amma inaso kayiwa zancen kyakykyawan fahimta domin idan Allah ya aiko da komai tabbas saiya faru kadauki wannan abun tamkar kaddarace domin rubutaccene daga Allah.

Nanta zayyane masa komai kamar yadda ta fadawa su Hjy maryam

Ya dad'e kansa akife akan cinya tunani ya cika masa kwakwalwa saida yayi hawaye itama Teeman hawaye take futarwa

Su hassan da Hussain da Nabeehat da feenah sun tausaya musu,bayama Teemah da saida tayi kuka hawaye kashinb'ar akuncinta kenan zasu rabu da "yar,uwarta Teemah duk saitaji ranta ba dad'i Ashe ba cikin su d'ayaba?

Dady yace" yanxu abinda yakamata tashi zamuyi mutafi gidan ki Hjy Salma domin muyi
Surprise d'in Mijin ki muyi bayanin komai agabansa koba hakaba ?

Alh mansur yace"wannan haka yake"

Dukansu suka mik'e domin tafiya gidan Hjy Salma.....


~*Auntyn Sayyada da Shahida*~πŸ’˜
[5/21, 13:05] Nabilancy Luv: 🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*CAKWAKIYAR ZAMANI*
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


_by_ πŸ‘‰πŸΌ *Nabilancy Luv* Β©πŸ’˜


*KADUNA...*


~*Pg 31-32*~

A B'angaren Aisha kuwa abin duniya yayi mata yawa ita kanta ba qaunar cikin dake jikinta takeba gashi yajanyo mata tsana gun "yan gidansu hatta Aminatu da tafi kula da ita yanxu bata fiye kulataba saitaga dama take mata magana

Abin yadameta ainun ga Adam da kullum yake damunta da zancen ta gudo gunsa sugudu kano suyi kyakykyawar Rayuwarsu a acan babu takura babu kyara balle suyi Abu a d'ari-d'ari

Sharrin shaid'an da kuma sharrin zcy suka rinjayeta ta amince masa ta ringa shirinta a b'oye tak'udura aranta inhar tabar gidan nan tabarshi Knn(kunji wauta da shashanci ko? Hhhmmm duniya budurwar wawa...)

Ranar Laraba aka tsaida yin saukarsu Aminatu a islamiyyarsu anata shirye Β²n walima gidan yasami bak'i Na " yan uwa ana gobe saukar talata Knn Allah ya arawa Aisha dama tazille tabar gidan babu Wanda ya farga

Aminatu ce tafara fahimtar Aisha bata ckn gidan domin har goman dare tajita shiru bata dawoba don azatonta tafuta taje gun Adam d'inne kamar yadda tasaba zuwa

Mubeena itace "yar yayar Inna halima taxo gidan zata kwana sbd ayi walimar da ita, a tudun wada take budurwa ce Sa,ar Aminatun ce suna kwance kan gado suna hira har bacci yakwashe mubeenar itako Aminatu hankalinta baya kwanciya harsai taga shigowar Auntyn ta

Har bacci yakwasheta Na mintina ta farka firgigit ta duba agogon bangon d'akin yanda ya buga k'arfe sha d'ayan dare haka k'irjinta ya buga lokaci guda domin Aisha bata wuce sha d'ayan bata shigo gidanba

Ta tashi tsam taje ta lek'o d'akin inna A'i ko can zata kwana aranar sbd takan kwana acan in innar ba itace da girkiba

Aminatu Na shiga taga innar ita kad'ai tana baccinta tashiga mamaki aranta to shin INA Aunty Aisha tashiga haka?

Ta juya zata futa Knn taji innar Na fad'in" ya akayi Ummie? Wani abun ne?

Dayake akwai hasken wutar lantarki Aminatu takalli innar tace"inna ba lfy ba walh hankali Na yak'i kwanciya domin Aunty Aisha bata ckn gidannan"

"Bata nan? To ina taje?

Aminatu tace " nikaina mamakin danake yi Knn nazacima kotana nan d'akin nema shiyasa naxo dubawa

Inna tace"to fa ai bacci baikama muba maxa muje intaso maxan

Please Login or Register in order to submit comment