You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yatashi,
Tabbas wata kawar ta tabata labarin Ameena tana akasa dukda tasan soyayyar ta da Abdul acan baya amma batayi tsammanin haka ba,
Hankalinta yaci gaba da tashi yayinda ta dinga cin karo da wasu sakonni wadanda suka fi na farkon, Dan kuwa wannan Number mai matsayi ce da tasamu Kalmar Heart Beat!
Nanda nan itama tata zuciyar tashiga kara bugawa.
🙆🙆🙆YACUCENI🙆🙆🙆
The book
Of

Queen Mermue

©
HIKIMA writers
Association

Edit by
ANaM Dorayi
Page2⃣2⃣

My lovly Fans Ina matuk'ar jin dad'in yadda kukemin uzurin kasancewar bakwa samun yadda yakamata, ina yawan jin korafe korafenku, ina mai Dada baku hakuri harwa yau ku kasance masu yawan YAKANA! Insha Allah zan qara qoqari, nagode muke, 😍😘


Saida wayar tayi kara tayi k'ugi har ta gaji kamar baza,a daga wayar ba can kuma sai aka d'aga,
Abin har yaso yabawa Ameena haushi amma ganin ya daga wayar yasa tadawo dai dai,
Sallama tayi acikin kalar muryarta ta larabawa, wanda jin muryar kawai yasa yagano mai magana,
Cikin fara,a ya amsa sallamar, kana yace,
"Manyan mata masu Nigeria,"
Cikin sanyin murya wadda tuni wata guguwar son shi taqara qaruwa a zuciyar ta,
"Hmm Abdul kenan, mune manya ko kuma ku,
Ya gajiya ya 'ya'yana,"
"Lafiya kalau muke,"
Bayan doguwar gaisuwar da sukayi sai kuma shiru ya biyo baya kamar bazata dago zancen ba can taja doguwar ajiyar zuciya tace,
"Abdul ya zancen mu ya kwana duk da nasan ni mai dinbin laifice a wurin ka amma nasan kai mai Hak'uri ne da rik'on alk'awari, ina ce baka manta alk'awarin da kayimun ba,"
Ajiyar zuciya yayi yayinda wani haushi ya tokare makoshin sa, can ya daure yace,
"Eh Ameena ban manta da alk'awarin da nayi maki ba, amma ki sani na riga da nayi aure a yanzu kuma ina son mata ta haka kuma idan nace zan aureki a yanzu ba k'aramar fama zansha a wurin iyayena da can nayi doguwar jayyaya dasu ne abisa kuskure da kurciya amma yanzu ki sani ba abinda zai sa nak'ara wani tashin hankali akan na aureki, a gaskiya kiyi Hak'uri,"
Wani murmushin cin nasara tayi,
"Yanzu dai idan na fahince ka iyayenka ne matsalar ka?"
Kai tsaye yace
"Eh"
Dan yana tunanin itace hanya mafi sauk'i da zai sallameta batare da wani bacin rai ba, duk da yasan dimbin irin alk'awarin da yayi tayimata,
"Idan iyayenka suka amince kenan babu matsala?"
"Eh ina tunanin hakan,"
"OK shukran laka, saida safe"
Kashe wayar tayi, tare da yin lamo akan gadon ta, tana hango irin rayuwar masoyar da zasuyi, lalle duk wani tanadi na soyyaya shi tayima shi,
Kamar wadda aka mintsila ta mik'e zaune,
Gabanta yafadi tuno da Abbakar wannan mutumin ya takura mata a rayuwa,
Tsaki tayi,
"Bak'in kaud'i harda wata 'yarshi zai kawomin,"
Sai kuma tayi murmushi koba komai danginsa suna daraja ta, dukda yanda yasu suke mata daukar tana muguwar hark'alla da manyan k'asa,
"Kutttt su acciki"
Text tashiga turawa Abdul dan kuwa gobe tana son sukai komai a k'arshe,

Zaune take bakin gado tana saka maballin rigar bacci, wayar Abdul tayi k'ara alamun text yashigo, kamar kar ta duba sai kuma wata zuciyar tace ta duba, dama kwana biyu tanada tuhume tuhume a kanshi, dan haka sai kawai tadauka,
Number ce wadda ba,ayi save ba gabanta yafara fad'uwa daganin irin kalamain da tafara cin karo dasu kamar haka,
" Assalamu alaikum, Abdul nasan har yanzu kaunata tana tare da kai, yayinda nake maka albishir da cewa nima har yanzu ina kaunar ka fiye da yadda na soka abaya Dan kuwa yanzu koma me namallaka zan iya sadaukar dashi wa soyayyar ka, nasan bazamu samu matsala ba, dan haka gobe inason mu tattauna, a gidana zan turo maka da adireshi,
Nice mai kaunarka dai Ameena Abi Turab "
Har rawa hannun Baseera yadinga yi nan take ira izzan bala,in ta yatashi,
Tabbas wata kawar ta tabata labarin Ameena tana akasa dukda tasan soyayyar ta da Abdul acan baya amma batayi tsammanin haka ba,
Hankalinta yaci gaba da tashi yayinda ta dinga cin karo da wasu sakonni wadanda suka fi na farkon, Dan kuwa wannan Number mai matsayi ce da tasamu Kalmar Heart Beat!
Nanda nan itama tata zuciyar tashiga kara bugawa.
🙆🙆🙆YACUCENI🙆🙆🙆

The book
Of
Queen Mermue

©
HIKIMA Writers
Association

Edit by
ANaM Dorayi

Page2⃣3⃣

Ankerlicious🤸‍♀📣📣📣📣📣📣📣📣
Rabon Wani!
Rabon Wani!
Rabon Wani!

Tab ina masoyan Nafeesat Anker shin kunada labarin ta garzayo ta tankad'o ta hankad'o da bankad'o, ta kara tinkowa da iya HIKIMA da baseerar ta domin ta faranta maku?
Zakaran da Allah yanufa da cara ko ana shaho ana mazuru sai ya cara,
Ta had'a gumi da Anker ta suburbud'o muna da wani k'aya taccen buk mai d'adi da karantar wa,

Toh!!! Kowa yaje yanemi rabon sa nidai harda Rabon Wani zan had'o😂


Jin alamun zai fito daga wanka yasa ta kofi numbobin duka biyu,ta bar dakin,

Da yafito daga wanka bayan yayi shirin kwanciya, ya dauko wayar Sam bai kula da wani text sai lokacin da yashiga dumin turawa gimbiyar tashi saida safe da yake yau basuyi waya da yawa ba,
A lokacin ne yagan sakon Ameena Turab, tabe baki yana mai mamakin son kai irin na Ameena, lallai yayi mata son hauka amma yanzu babu shi a zuciyar sa dukda har yanzu da burbushinsa amma wannan bazai sa ya aure ta ba, dad'in abin a wurin shi yasa irin tsinuwar da iyayensa suka yiwa Ameena sanadiyar mugun halin da dansu yashiga bayan tafiyar ta saida yai tsawon wata biyu a asibiti yana fama da ciwon zuciya, daga bayane Allah yasan ya mishi dangana,
bayan ya kammala digirinsa ne Baseera wadda ta Dade tana fama da sonshi aka had'a su aure da yake da Baban ta da Baban Abdul kakansu d'aya, dan haka 'yar uwarshi ce, Baseera mace ce mai mugun kishi akan abinda take so dan kuwa ko abokan aikin Abdul mata bata yarda dasu ba, dukda tasan da son da yayiwa Ameena, sati biyu kenan da wata kawar ta take bata labarin akwai wadda mijin ta yake neman auren ta ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, musamman yadda tasan kannenshi basu cika dogon shiri dasu ba, haka ma yayunshi da yake Basee akwai walak'anci sosai shiyasa basa cika kula ta,
Yanzun ma tun lokacin da taga sak'onnin ta kideme abin ya daure mata kai kardai ace Abdul yafara bidar mata, gudun kar yasan ta duba message din yasa ta koma d'akin ta dukda cewa tanada bala,i amma tana bala,in shakkar Abdul ta tsani abinda zai sa yaga laifinta, wannan yasamo asali ne daga mugun sonshi da take Sam bata son yaga laifinta, tana matuk'ar kyautata masa kasancewar tasan ba wani sonta yake yiba Hak'uri ne yakeyi dukda ta mallaki duk wani abu da 'ya mace take buk'ata, Basee kyakkyawar mace ce ajin farko ga ilmi ga kud'i iya kudi tin daga iyayenta har ita kanta, mahaukaciya ce akan abinda take so, tin tana secondary take mahaukacin son Abdul jin labarin son da yayiwa Ameena ya bala,in kuntata mata, bayan tagama makaranta kirikiri ta shaidawa iyayenta Abdul take so dukda irin dimbin masu sonta amma Sam taki aminta da kowa hakan yasa aka had'a su aure, gwargwado yana jin dad'in zama da ita dan haka basuda wata matsa sai irin nakasar da take yiwa mutane.


K'arfe shabiyun rana bak'in Kaduna suka iso wato Abbakar Omar Tanko, tare da 'yarshi tilo Yasmeen, duka gidan muka fito domin yimusu sannu da zuwa, Matashin Namiji mai kimanin shekaru talatin da bakwai, kyaukkyawa ajin farko Wanda tin daga suturarshi zaka ga kud'i ilmi gogewa ta kowanne fanni, sai k'aramar yarsa wadda bazata wuce sa,anin Jeedda ba, da murmushi yafito daga motar hakan Ameena haka kawai yau taji ya burgeta duk dacewa Abbakar yakai iya Namijin da kowace 'ya mace zata so, shekara biyar kenan da yake binta amma ita tanada nata buri bai gaji ba dai har yanzu da yake kaf danginsu na kusa kowa yasan da Ameena, Matarshi ta rasu wato mahaifiyar Yesmeen tin bayan haihuwar Yasmeen tin lokacin bai sake aure ba, dan asalin garin Kaduna ne aiki ne yake kawo shi a kano.
🙆🙆🙆YACUCENI🙆🙆🙆
The book
Of
Queen Mermue

©
HIKIMA Writers
Association

Edit by
ANaM Dorayi

Page 2⃣4⃣

My swt little sis Beebie, na gaisheki da k'oqari Allah yayi miki jagora, wannan page naki ne da Fan's naki💔



Babban lauya ne, Abbakar yana matuk'ar son Ameena dukda
yasan da Abdul a rayuwarta shi acewarsa matar mutum kabarinsa,

A babban parlourn k'asa suka zauna cin abinci,
Sai hira da akeyi yayinda su kande da Aisha suka shiga jera abinci kala kala,
Bayan sun zauna akan teburin ne aka fara Sabin dinsu, saidai su duka ukun suka ture abinda aka samusu a faranti, Ameena ta ajiye cokalin da yake a hannunta ta kalle Anee da Abbakar harda Yesmeen tace
"Ya dai ko abincin baiyi bane?"
Anee ta kalle Ameena tace
"Anty kin manta bana cin wake,"
Abbakar yace
"Mu mafa haka dagani har Yesmeen bama ci,"
Ameena tace
"Ikon Allah, to ai ba abinci daya bane ga kuloli nan sai Ku nemi Wanda kuke so"
Abin yak'ara bawa Ameena mamaki ganin su ukun basa iyaci da spoon dukda tasan Anee bataci hakama Abbakar Ashe harda 'yar tashi,
Ameena ta kalli Yesmeen tace,
"Au kema duk abinda Dadynki yayi shi kikeyi?"
Yesmeen tayi dariya tace,
"Au Mumy haka muke harda grandpa da kowa sai grandma tayi tafada wai bamacin wake kema Anty Anee idan tagani sai tayi maki fada"

Dariya sukayi gaba d'aya,,

Falon bak'i aka sauke shi yayinda Yesmeen tashiga ciki tare dasu Jeedda, ai tuni Jeedda ta barke da murna har tarasa wane yaren zata yiwa Yesmeen a wurin gaisuwa, dayake yaran basu bar yaren mahaifiyar su ba suna larabtawa Daidai gwargwado,
Aneesa ma taji yarinyar ta kwanta mata sosai hakama take jin Abdul din bazai fi Abbakar da komai ba dukda shi bata ganshi ba,

A falon bak'i kuwa Abbakar ne zaune a kan kujera bayan ya kammala cin abinci, Ameena akan kujerar dake gefen shi, doguwar Riga ce bak'a sanye da ita sai zanen atamfa da za,a iya tsinka, da alama dai atamfar ce tasa tare da aza bak'ar rigar asama,sai d'ankwalin rigar bak'a da tayane kanta dashi, tsarki ya tabbata da mahallicin da yayi wannan hallitta, Abinda yake fad'a a ransa,
Bayan sun kara gaisawa yake kara dada mata cewa har yanzu fa yana akan bakarshi,
Har wa yau dai Hak'uri tabashi duk da tasan itama tana kaunar shi amma son Abdul da kwadayin kyautata masa yafi k'arfin ta barshi, tabbas tasan Abbakar yafi dacewa da rayuwarta amma tafi son Abdul akan shi
Haka dai yatashi yabar gidan da yake sai wani sati
Zai koma week end a Kaduna anan yabar Yesmeen dama nan zatayi satin ta,
Haka Ameena ta koma aciki tana jiran zuwan Abdul, ganin har ukku bai zoba yasata ta kirashi,
Ya shaida mata zai zo tare da niyar idan yazo zai gayamata bazai aure ta ba koda kowa iyayensa sun amince,
Adireshin gidan da ta turo mishi yabashi mamaki, haka dai yabi ta adireshin har ya iso gidan cikin mamaki, ya kirata nan take tayi masa iso zuwa ciki,
Wani irin farin ciki ya cikata nan take ta shaidawa Aneesa da zata kira ta tazo tagaisa da Abdul, Anee cikin murna tace,
"Kai Anty wannan wanka haka kamar yau ne ranar,"
"Gidanku Anee gaban 'ya'yan nawa,"
Cikin dariya ta wuce falon da akayi masa iso, bayan an jere masa kayan taba ka lasa,
Wayar Anee tayi k'ara ganin Bawan Allah ne yasa ta saurin dauka, saidai tana d'agawa kiran Ameena yana shigowa dan haka kafin yace wani abu ta shaida masa Anty ta kirata zata kirashi daga baya,

Ganin kamar waya zaiyi yasa Ameena daukar wayarta dan takira Anee tana dagawa tace mata tazo ta gaida Abdul,

Hijab dinta kawai tasaka ta sauka a k'asa, bangaren bak'i ta nufa ta bud'e kofar falon tare da sallama,
Ameena zaune akan kujerar dake kallon kofar yayinda shi kuma yake a kujerar dake kallon ta Ameenar wato dai yaba wa k'ofa baya,
Rassss! Gabansa yafad'i jin sallamar wadda yake ko kwanton,
Duk'awa tayi har k'asa tare da fad'in
"Yaya Abdul barka da...."
Sauran maganar ya mak'ale a bakinta yayinda ta mik'e a tsaye.
🙆🙆🙆YACUCENI🙆🙆🙆
The Book
Of

Queen Mermue

©
HIKIMA writers
Association

Edit By
ANaM Dorayi

Page2⃣5⃣

Tab! Banida bakin gode muku fa, gaskiya kawayen Ameena Abi Turab da kuma kawayen Aneesa nagode sosae Allah yabar kawancenku😂



Juyowa tayi ta kalli Anty Ameena,cikin .matuk'ar mamaki,
Sai kuma tayi zaton cewa ko tsokana ne Anty takeyi,
"Anty wannan ne Abdul dinki"?
Ta fad'a cikin matuk'ar mamaki,
Ameena Turab tayi murmushi tace,
" eh Anee ko kunsan juna dama?"
Girgiza kai tayi ta k'ara duk'awa hankali tashe tace,
"Yaya Abdul barka da zuwa"
Tana kai nan ta tashi ta fita da sauri,

Shikam mutuwar zaune yayi yana mamakin Wannan rikitaccen al,amari da yake shirin faruwa,
Ameena ma abun ya daure mata matuk'a dan haka ta kalli Abdul cikin damuwa tace,
"Abdul Hameed, me yake faruwa ne? Dama kunsan juna ne?"
Abdul ya mik'e tsaye ya har yakai k'ofar fita kuma sai ya juyo,
"Ameena dama kece kika taimaki Anee?"
Ameena ta ware ido
"Allah Allah ni kuyi min bayani ban gane ba, wai meke shirin faruwa ne"?
Abdul ya bud'e kofar fita bai juyo ba yayinda Ameena ta mik'e ta tare shi, tare da rik'e k'ofar,
Kallon ta yayi ya kauda kai
" nasan dole zaki san Bawan Allahn Aneesa, to ba kowa bane sai ni, kuma kin Riga da kinsan shirye shiryen mu na aure,"
Yana kai nan ya fuce yaja motar shi a guje dan saura kad'an yahada da mai bud'e get din,
Ameena kowa zama tayi a wurin, ita Sam bata fahimce me suke nufi ba,
Shin Abdul din da gaske shine Bawan Allah, Wanda tasha alwashin zata karar da komai nata Dan ta aure shi?
Kuma shine Bawan Allah dinda tayi alk'awarin ko ana ha maza ha mata sai ta aurawa Anee shi?
Lalle wannan rikitaccen alamari ne ?
Nikam naci kuka iya k'arfi na, koba a fad'a ba nasan narasa Bawan Allah har gaba da abada,
Duk wasu plan nawa cikin sakanni kad'an suka rushe,
Domin kuwa nasan kowaye ubana a Nigeria na rasa Bawan Allah,
Kan gado na koma na dauki waya ta tare da shiga wurin sak'onni sakonnin Bawan Allah ne burjik, masu nuni da cewa ya tsunduma acikin kogin so na, tabbas ko ba,a fad'a ba nasan Bawan Allah da gaske yana sona ga 'yan uwanshi da suke sona babu kamar Abdul Hakeem, da k'anwar sa Sadiya dan tuni mun kulla zumunci a yanar gizo,
Yesmeen suka shigo d'aki na a guje su ukkun,
Suka fad'a kaina,
Jeedda ce take cewa
"Anty boye mu kar Mumy ta dokemu, d'akin ta muka shiga ta koromu,"
Sai sannan suka bar duban su daga bakin k'ofar da suke zaton biyosu zatayi suka kalleni, nan take nashiga share hawayen da yake fuska ta tare da kirkiro murmushin k'arfin hali,
Yesmeen ta kalleni,
"Anty Anee meyasameki?"
Suka fad'a a tare,
Cikin murmushi nace,
"Kaina ne yake mun ciwo,"
Jeedda ta mik'e bari inje na fad'a wa Habeebaty,"
Saurin kamo hannun ta nayi nace,
"Ai tasani har nasha magani, yanzu kuje koyi shirin islamiyya naji kande tana kiran ku,"
"Anty nima na bisu"?
Cewar Yesmeen,
Daga mata kai nayi sa,anna suka fice.


Pls follow this link to like my face book page
https://www.facebook.com/o436431613362583/
🙆🙆🙆YACUCENI🙆🙆🙆

The book
Of

Queen Mermue

HIKIMA
Writers
Association

Edit by

ANaM Dorayi

Page 2⃣8⃣

Give thanks to the LORD in all things. Thank You LORD for giving me life and giving me a chance to live with purpose.


Farkawar da zanyi Sai naga mutane akaina, da sauri na mik'e zaune ina son na tonu shin ko mafarki ne nayi,
Cikin rudewa na kalli Anty na juyo na kalli Abdul dake a zaune yana min sannu,
"Anty ashe mafarki nayi Abdul bai mutu ba"
Ameena tayi murmushi,
"Ba mafarki bane kwana ne dai basu k'are ba,Ashe driver shine a motar shi a jirgi yazo dama,
Har yashiga motar yaji kansa yana ciwo shine sai yabar kayan sa aciki yanufi filin jirgi dan yabi jirgi yazo sai yabawa driver shine yayi hatsari kwanansa suka kare, mukuma aka kiramu da wayar d'aya da yabari a motar d'ayar kuma yakashe a jirgi,"
"Alhamdulillahi"
Ba fad'a,

Tsawon sati d'aya kenan ko Anty yar boyo mukeyi Sam bana bari wani abu yahada ni da ita, hakama wayata aka she bana waya da Abdul kuma shima yadaina nemana a wayar Anty
yau ma bayan munci abinci, da yake jiya su Yesmeen suka wuce,
Anty ta kalleni tace,
"Anee zaki iya auren Abdul bayan ya aureni, ina nufin dukan mu biyu ya aure mu?"
Gabana ya bala,in faduwa, na dago idanuna na kalleta,da kyar nayi wani gutun yake Wanda yafi kuka ciwo nace
"Hmm Anty dai, ai koda ace na aure Abdul ne daga baya Nagano shine Abdul dinki, to dole ne nafito ke ko aure shi, dan dake yafi dacewa,
Nikam ke kamar uwace a wurina ko kuma yaya ta jini d'aya, dan haka had'a kishi dake haramun ne a wurina,"
Ameena ta girgiza kai tana jin k'arfin hali irin na Anee, bata kara cewa komai ba muka ci gaba da hirar mu,

Gidan shirye shirye kawai akeyi, wannan satin sai bak'i maza da mukeyi da alamu da anzo tambaya wa Abdul Auren Ameena ne dan har a sokoto suka je wajen daginta, haka naga tana bawa su Hajja Falmi sako izuwa Dubai,
Hankali na yatashi matuk'ar gaske da Anty ke shaidamun dauran auren ta a wani sati,
D'aki na koma nayi kuka har na k'oshi,
Shirin bidirin biki akeyi hai kam, biki na kece raini,
Nima har dinkuna anmin iri d'aya da Jeedda har kala goma, nikam hankali na baya ajiki na, mussaman idan natuna Angon Anty Abdul,
Babu wani event da aka shirya duka sai bayan an daura aure,
Daren yau na had'a kayana kasan cewar gobe dauran aure, bazan iya ganin abinda za,ayi ba, nafiso naje nakoma wani gari nacigaba da rayuwa ta acan, dankuwa anan dole na dauwama a bak'in ciki,
Ina son Abdul fiye da yadda nazata zan soshi, amma nafi son ya auri Ameena.

Daga can sama nake hango mai gadi daidai lokacin da yake arwalla subahin dan haka na silalo na fita, a hankali.
Saidai ko unguwar ban bari ba aka dinga dannamin horn
A Dole na tsaya kasancewar nasan Ameena ce,
Banso takamani ba, dan haka duk sai naji kunyar ta,
Motar na bud'e nashigo na fara kuka
Ko kala batace dani ba har muka shiga gidan,
Saida ma bud'e motar zanfita najiyo tana cewa,
"Karki kara tunanin barin wannan gidan ko kuma idan nak'ara kamaki nayi maki hukunci tsatstsaura,"
Daga haka tayi ciki tabarni tsaye ina kuka,


👑Queen Mermue👑:

Dear God, I wanna take a minute, not to ask for anything from you. But simply to say THANK YOU, for all that you gave me.
🙆🙆🙆YACUCENI🙆🙆🙆
The book
Of

Queen Mermue

©
HIKIMA writers
Association.

Edit by
ANaM Dorayi
Page 2⃣6⃣



Toh nikam babu abinda zance daga masu supporting din Turab har Anee,
Sai dai mu duka muzura ido muga mezai faru, dan nimafa ba sani nayi da masu bina pc suna tambaya ta,
Harwa yau dai
Ameena Abi Turab
Ko
Aneesa?

Muje zuwa maji............


Waya ta tayi k'ugi har tagaji ban kula ta ba, haka akaci gaba da kira naki na daga dan nasan me kiran.
Banko k'ofar akayi da karfi,
Nayi saurin tashi zaune,
Ameena ce tsaye bakin k'ofar d'akin, gashin kan ta duk ya murje, idanun nan nata duk sun kumbura,
"Anee dama Abdul shine Bawan Allah Wanda ya taimake ki, Wanda kike so kamar rayuwarki,? Nikuma Abdul dina wadan yafi k'arfin komai yafi karfi kowa a wurina?"
Ta tako har ta iso a wurina,
"Anee meyasa kika bar hakan ya faru? Yakike so nayi a yanzu?"
Kuka na a yanzu ya tsanan ta,
" Anty meyasa zaki tsareni da wad'an nan tambayoyi bayan kinsan Wannan shirin

Please Login or Register in order to submit comment