You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da gwalagwalan yasiyamuna gida a goran dutse, dasu nan zamusa masu haya a gidan da zamu bari,
Sauran kud'i kuwa ya bud'e shago a unguwar Dorayi,
Naji dad'in haka matuka,
Bayan daura aure muka tare a gidan mu na unguwar Goran dutse,

Kamar kowace amarya ranar farkon da tayi gari taganta a gidan ta a ranar farko farinciki nishad'i da walwala sune zasu taru su k'ara mata kaunar angone nata, haka nima yakasance ce a wurina,
ganin har k'arfe shad'aya na rana banga angon nawa ya dawo ba yasani tashi na nufi kitchen ko ruwan Lipton nasamu nasha
"Assalamu alaikum"
Sallamar da aka rangad'a abakin k'ofa ne yasani tsayawa daga kitchen din da nayi hararamar shiga dan kuwa muryar k'aramin yaro naji, kafin na karba sallamar sai naji ana cewa,
"Alhaji Iro ya aikoni"
"To ganinan zuwa" mayafi na nadauko daga kan kujera nafita,
Leda bak'a ce ya mik'omin,
"Gashi yace abaki yace kuma da rana kar kisa abinci dashi sai dare zai dawo,"
"A ina kaganshi dan Allah?"
"Yanzu yawuce akan mashin yace nabaki"
"To jeka nagode,"
Koda nakoma nashiga kitchen din ledar d'anyen kifi ne a ciki sai taliya macaroni d'aya da kullin magi da mai sai tarugu da tattasai, naji dad'in ganin cefanen duk da cewa nasan kowa ce Amarya abinci ta na farko a gidan mijinta bai dace yakasance kayan kwalama ba, sai dai kash!mukan bamuda wannan gata,
Dayake anguwar bansan kowa ba haka yasa nayi zama na a d'aki ina yan karance karancena dama ni kad'ai ci ba abu sabo bane a wurina,
Kamar yanda tafaru jiya haka ma ayau din Iro sai K'arfe d'ayan dare yadawo haka ma daya dawon bai nemeni ba d'akin da ya kwana ajiya ko yau acan ya kwana, abin yabani mamaki sai dai nima bacci na nayi, tun k'arfe hud'u da rabi ya kwankwasamun k'ofar d'aki natashi nabude mishi, ya shigo ya zauna akan kujera da mamaki nabishi da kallo, sai kuma nace,
"Iro ko lafiya?"
"Lafiya kalau dama kud'in zaki bayar dan inajin yau zanga mutuminnan sai nabashi inyaso ko gobe kayan suka kai sai nafara shiga kasuwa a jibi,"
"Amma kuma ai kasan an tab'a kud'in yanzu tunda komai fa na wannan auren aciki mukayishi kuma jifa ka amshi wasu, ni ina ganin da kabarsu a wurina inyaso bayan kwana biyu idan nasaba da anguwar nan sai nafara dauko kaya ko a shago musaka yafi wannan kasuwanci da kaje so ayi na manyan masu kud'i ne"
Ran shi ya bala,in b'aci ya tashi a hasale,
"To kije kiyi yanda kika ga dama tunda munshirya abu yanzu kuma kin canza tunda baki yarda dani ba sai kije kiyi,"
Yatashi fuuuuu yafice daga gidan gaba d'aya.
Anan na zauna ina tunanin hali irin na Iro muda mukayi aure jiya jiya sai kawai yazo da wani tashin hankali,
Kusan sati d'aya kenan da auren mu da Iro amma sai sai naga ficewarshi da asuba Dan kuwa bazai dawo ba sai d'ayan dare, nasan bakomai bane illa fushin da yakeyi danine,
Shiyasa yau na yanke shawarar bashi kud'in ko zan samu yabani kulawa irin ta ango da amarya,
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆. YACUCENI
The book
Of
Queen Mermue

©
HIKIMA Writer's
Association.

Edit By

ANaM Dorayi.

Page 🔟


Yee! Yeeeee yeeeee! Kukan da yarinyar tashigo tana yi ne ya katse Malam Damma daga shiga bayin da yayi niya, ajiye butar hannun sa yayi ya juyo Zuma gareta,"'yar Baba meya faru kike kuka haka inace yanzu kika fita daga nan waya tab'a ki?"
Wadda aka kira da "yar Babar ta share hawayenta sai faman cikowa takeyi,
Malam Damma yak'ara fadin "" yar Baba ko bada ke nake magana ba,?"
Wai wai Ukashan Lami ya mareni wai dan Iron mu ya yayi fad'a dashi"
Iron da yake a cikin d'aki tin shigowarta ya ajiye furar da yake sha, jin ta ambaci sunan shi yasa shi saurin fitowa hasale,"kan Uba wallahi sai na halaka.."
Saukar marin da Malam damma yayi mishi ne yahana shi k'arasa mugun nufin da yake shirin yi,"kul naji ka k'ara taba shi sai na cimaka mutumci,yaron banza kawai gashi akan banza kajazamata Mari fita kabani wuri" Iro kam yacika ya batse dan kuwa ba Ukasha kadai ba har ita wadda tasa aka mareshi ya yi damarar dan k'aramata duka, a hasale ya fita yabar gidan,"
Zo nan 'yar Baba duk lokacin da kika ga wani zai dokeki akan banza ki gudu kar ki wani tsaya dan wannan d'an uwan naki komai zai iya jazamiki,
Malam damma yana shiga bayi tabi bayan iron Hak'uri ta dinga bashi akan kar yayi fushi da ita,

Wannan 'yar Babar bakowa bace face ni,
Wannan kuma Baban nawa bakowa bane marik'i nane
Iron kuma d'an shi ne tilo,

Tin ina k'ara Allah yasa min son wannan iron da na daukeshi kamar yaya na najini,banida tashin hankali irin ace yau yana fushi dani dukda cewa ya girmeni sosai,
Hakama Baban nawa nadaukeshi shine Wanda ya haifeni,
Mun taso cikin talauci sosai, amma dukda hakan bai hana mu samun ilmi daidai gwargwado ba,
Iro baya son makaranta ko kad'an idan aka tura mu sai ya labe idan nadawo gida kuma bazan ce baije ba,
Gidan da muke Baba ya shaidamun gida nane halak malak,
Tin ina 'yar shekara goma yake sanar dani bashi ya haifeni ba,tsintuwa ta sukayi alokacin da yake zama jeji da matar shi,
Sun tsinceni ne da mak'udan kud'i acikin kwalin da aka ajiyeni a ciki da sark'ar gold har guda ukku,tare da sunana a takarda da kuma ranar haihuwa ta,
Ranar da zasu bar jejin da safe suka sameni a bakin k'ofar d'akin nan ne Malam habu yake gayawa matarshi tabbas jiya yaji kukan karnuka a dajin,
Basu kai wurin 'yan sanda ba dayake kinsan Fulani da tsoro,
Sai suka bar ni a hannun su suka hadani da dansu dan kimanin shekara shida suka rik'e,
Saida mukayi shekara,
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
YACUCENI

The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi
Page 1⃣3⃣
Ameena ta numfasa tace, "To bayan kin hada harda gwala gwalankikuma to kudin me zaki bashi?"
"Eh innada sarka guda daya wadda tafi saura girma akalla kudin ta zai kai dari biyu, banso saida itaba amma ganin yayi fushi dani yasa na yanke shawarar bashi,"
Kwafa Ameena tayi tace, "Lallai ke kam idan nice saidai ya sakeni amma bazan bashi ba,"
Aneesa tayi murmushin takaici tace,
"Anty kenan, kin manta Abdul kudinsa yake rabawa biyu yabiya miki haya da sauran lalurarki,?Koda yake bakisan meye soba shiyasa kike cewa haka,"
Ameena tayi dariya tace,
"Au hakama kikace, lallai Aneesa, to bari naji inda guguwar son takai ki."
Aneesa tayi murmushi ta gyara zamanta tacigaba da cewa,
"Banyi barciba har k'arfe d'aya, can naji shigowar shi, da sauri na fito na tareshi a tsakar gida, har saida ya dan tsorata, ya kalleni yace,
" meye haka zaki tsorata ni,"Nan nashiga kame kame , da kyar nace,
"Dama cewa nayi gobe ka shirya sai muje mu saida sarkar,nabaka kudin,"
Wani murmushi yasakar min, sannan yakama hannuna, yace, "Yawwa Mata ta ko kefa, nafiso komai zakiyi karkiyi tunanin zan cuceki, kinga bakida kowa a duniya tin da ke 'yar tsintuwa ce, ni kadai ne naki a duniya, ko ba haka ba?"
Wadannan kalaman nasa bamasu dad'i bane amma dukda haka sai naji kamar ansani aljanna ne.
Ranar kam nasan mecen so dan kuwa nasha shi, yasamarmin farin ciki sosai.
Dukda Iro irin mazan nanne masu kama da sakarkaru, jikin Fulani ne dashi, ga rashin k'arfi dan kuwa abinda zan dauka mai nauyi bazai iya daukarshiba, wani irin malalacine sosai,
amma nikam sai naji da dai za'a tara matan duniya to ina ganin nafi kowa dace da jarumin namiji.
Sati biyu muna shan soyayya dukda na fahimci cewa ko kad'an Iro baya sona dan ma ana cikin amarci ne.
Wata d'aya da aurenmu na tada mishi da maganar gidan na dake a tsohuwar unguwarmu kan maganar hayar da zamu sa dan ina son idan aka fara registration na makaranta koda polyne na shiga amma sai ya hauni da masifa wai nacika rigima, idan so nake ya had'a kayana yabani basai naci mashi mutumciba.
Hankali na ya tashi da jin irin fassarar da yayimin dan haka nashiga bashi hakuri,da kyar nashawo kansa muka daidaita.
Wata biyu da aurenmu nashiga laulayi, muka je asibiti aka tabbatar mana cikine dani, murna a wurina kamar me, Naji dad'i sosai zan zama uwa saidai muna dawowa gida Iro yahau bala'i; wai daga aure har na kwashi ciki sai kace akuya... Jin yanata zantuka maras dad'i yasa murna ta takoma ciki.
Bayan kwana biyu yace nashirya muje asibiti za'a zubar da cikin. Nayi kuka har nagode wa Allah, nayi rok'on har nagaji amma fafur yace sai munje.
Da mukaje asibiti likitan da muka samu yace tinda cikin bashida wata matsala bazasu zubarba,
Cikin bak'in ciki, muka dawo gida nikam murna nakeyi cikin raina........
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
YACUCENI

The Book
of
Queen Mermue
©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi
Page 1⃣1⃣

Hausa novels
ANaM Dorayi fan's,
Na gaishe ku sarakunan surutu😂
Wallahi ina sonku da yawa,

Lyk
my Frnd,Teeman Abba,
Sayyeeda
Saheeba
Husnat
Hafsat
AA Alkali dinnan😏
Batalo
Shureim
Bebeji
Abdusallam
And others,

Oho kai bakina zaiyi ciwo ANaM katara family dayawa😂




Said a mukayi shekara, shida a wani dajin ne Allah yayiwa Mairo rasuwa,wato mahaifiyar Iro,
Bayan nan ne muka kaura izuwa garin sakkwato,
Wata unguwa muka zauna wadda tafi kama da unguwar 'yan gudun hijira,
Babu abinda ke cikin shiyar mafi yawa sai gidajen kwano, wasunsu 'yan Niger ne wasu yarbawa, wasu zabarmawa Fulani, ke babu yaren da babu a unguwar,
Yaran unguwar kuwa daga dan daba sai barayi, dan haka Sam unguwar bata zaman lafiya,
Anan aka samu a makaranta ni aji d'aya Iro dan shekara sha ukku, aji hud'u aka sakashi kasan cewar yayi girma da yawa,
Zaman mu a unguwar ba dad'i iro tuni yafara bin yaran banza,
Satar kaza satar zakara,
Shanun da Malam damma yake kiwo kuwa kullum ido biyu yake kwana,
Wata rana alokacin ina Aji shida na faramari, ranar unguwar ta rikice domin kuwa yaran unguwar suka kaiwa mak'otansu farmaki, har suka datsa wani daga cikin dan Wannan yanki,
K'arfe goma sha biyun dare aka fara k'one k'one,
Kowa akasamu a bige, duk gidan da aka shiga sai anyi sata kuma a k'one gidan,
Malam damma kuwa duk shanunsa da komai aka kwace, haka ya suntume akwati ta wadda take dauke da dukiya ta yaja hannuna da iro,muka tsere,

Ameena ta kalli Aneesa tace,
"Dama a sokoto akwai irin wadannan anguwanni,?"
"Kwarai ma kuwa ai Anty duk wata jaha da kike gani dole ne zata had'a taron zaka zani,Dan haka dole adinga samun matsala,"
"Bayan mun samu mun tsira a tasha muka k'arasa kwana, k'arfe shida muka kama hanyar Kano,
Bayan mun isa Kano, bamuda masauki dan haka Baba yanemi izinina da yataba kud'i na zai sayamuna k'aramin gida in yaso idan yasamu kud'i sai yasiye nashi,
A garin kano muka zauna nan naci gaba da karatu Iro kam ya ajiye karatu dan kuwa mugun malalaci ne,ba aikin da yake iyayi,
Nikuma duniya babu Wanda nake tausayi sama dashi, dayawa idan Baba yabani kudin tara, akan hanya zai tareni ya karba kuma bazan gayawa Baba ba,
Haka muka ci gaba da zama komai rintsi Baba baya tab'a kud'i na,

Iro yazama saurayi Dan shekara a shirin da ukku,
Ba aikin da yakeyi sai zaman kashe wando dukda cewa yanzu yadaina tab'a kayan mutane,
Baba yayi fad'a har ya gaji, gashi yanzu Baba bashida k'arfin da zai nemo, uwa uba yana fama da ciwon hawan jini,
Ina aji shida a makaranta
Wata rana ina zaune a d'aki na Iro yashi go fuskar sa a daure, daganin shi nasan da akwai abinda yake nema dan kuwa yasan ina tsabar tsoron shi,
Kallo na yayi kana yacemun
Annee, kinsan meyasa kika ganni anan?
Cikin tsoro nace a,a,
Yayi murmushi yace,
"Ina so kicewa Baba yabaki dukiyar a hannu, kinga yanzu tunda kin girma nizan taimaka miki muyi sana,a a tare, Wannan talaucin yayi muna yawa,

Abinki da halina nan da nan nayarda da zancensa, saidai yayimin gargadi kar na she dawa Baba shi yabani wannan shawarar,
Da daddare kuwa da Baba yashigo nasameshi nafada mishi, kallo d'aya yayimun yace,
" Annee wai har yaushe zaki daina biyewa zancen yaron nan, toh bazan bada ba kibari idan kika fidda miji nida kaina zan mallaka miki dukiyarki ki,
🙆🙆🙆 YACUCENI 🙆🙆🙆
The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi

Page1⃣5⃣
A tsakar gida na durkushe ina kuka dan ni larin mamaki yake bani, haka na rarrafa na koma a d'ayan d'akin dake a kusa da k'ofar fita daga gidan,nan na samu jakar kayana, sai wata k'aramar katifa da filo,
Saida bayan kusan awa d'aya yafito daga d'akin,ya leko yasameni ina rawar dari,dan kuwa nayi kuka har ya saukarmi zazzabi sai rawar Dari nakeyi. Tsawa ya daka min har saida na mik'e zaune. yakalleni a wulak'ance,yace,
"Ke wannan da kike gani yayar kice, kina Asibiti aka daura aurenmu, Asama ce wadda nake baki labarin tin a gida,"
Na dafe k'irji nace, "Asama fa kace Iro?ko ba Asama mai shinkafa ba?"
"Eh itace dama kinsan da alk'awarin aure tsakanin mu,"
"Iro, kana sane da Baba ya hanaka ka aureta ko bayan ranshi shine kuma yanzu ka aureta kuma sabida tsabar walak'anci bazaka ajiyetata a ko inba sai d'aki na kuma gida na."
Nan danan ya kara tanke fuska kamar wani bak'in kumurci,
"Au rainamin hankali zakiyi dan yana gidanki, to idan bazaki iya zama anan ba sai ki had'a naki ya naki kibar gidan, daga na rufa maki asiri kefa shegiyace, marar asali, wallahi idan idan naji kinyimata rashin kunya sai na lahira yafiki jin dadi, jaka kawai mai fuskar mutanen da...."
Tsaf yaci min mutumci ya tafiya, anan na kwanta lamo ina tunanin wannan abun.
Asama fitsarariyar yarinyace, dukda ban taba ganintaba amma tayi kaurin suna a saida abinci, nasan ita ce budurwa Iro, wadda yake mutuwar so, Lokacin da labari yasami Baba ne yasaka shi a gaba sai ya rabu da ita,to tun alokacin ya daina zancenta ashe basu rabu ba,

da rana tayi ina jin yunwa na fito, nashiga kitchen dan nasamu abinda zansaka a cikina, inna kofa kitchen Asama tafito daga ita sai wando guntu da breziya,tsira mata ido nayi dan nagano shin ita fuskar ta ta zamani ce,ko yaya, tunda naji yace ni fuskar tawa anbar yayinta, lalle kam da alama irin fuskar ta ake yayi dan kuwa radau a goshin ta aka rubuta bleaching, kana kallonta kasan tasha man Dari da hamsin, wato irin Jel dinnan da ake saida wa, Dan ko kallonta mutum bazai so yayi ba tayi jawur, ga wani k'aton baki da take fama dashi, kace an bud'e Masai,
Sai da takawo gab dani ta hura cingum dinda take ci, tai wani jujjuya idanu sannana tacemin, "Malama bana son naga kina shigar min madafa bansani ba ko a wurin bokayen aka fito, koda yake mijina yace cikin shege kika je aka cire miki, bakya iya yawo, kije akwai kayana ki wanke min dama ke nafito inkira,"
Har ta juya sai kuma ta kara dawowa,
"Am akwai zanin gadon da muka kwanta a daren farko, nasan baza a rasa inda ya lalaceba ki wanke sosai, karfa kiga laifina nacewa mijina akai wanki, yace ke kikeyimasa wanki."
Daga haka tayi tafiyarta.
Nikam abinyi ma narasa, lallai da sake, dan banji zan iya yiwa wata jaka wanki ba.........
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
YACUCENI

The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi
Page 1⃣4⃣
Muna shiga naga ya rufe k'ofar gidan, d'aki na muka shiga, muna shiga ya rungumeni ta baya,
Yan bud'e zip din riga ta,
Daga ni sai 'yar bes a jiki, na juyo na rungume shi,
A dole ni soyayyar India,"
Ameena ta kwashe da dariya, harda rik'e ciki,
Aneesa ma dariyar takeyi,
Amina tace,
"Ya sauko kenan, nazata zai kaiki wani Asibitinne,"
Aneesa tai dariya tace,
" uhm ai da asibiti yakaini a ka cire cikin da zaifi, kinsan meyafaru acikin soyayyar indiyar tamu,?"
Ameena ta k'ara feshewa da dariya, tace,
"Aneesa da abun dariya kike, meyafaru?"
Ta cije lebenta na k'asa tace,
"Ubana yaci! Belt din wandon shi yasa yayi min mugun duka, takai yasa kafarshi yakai min mugun duka a ciki, Hanci baki ke duk wata hanya ta jiki na jini take fitar wa, ni tuni na fita daga hanya cina,
Sai farkawa nayi naganni a asibiti kwance, da natambayi ma'aikaciyar asibitin meyafaru dani, sai take gayamin wai nayi barin yaron ciki ne, akan dukan da nasha da nayi sata awani gida,"
"Sata kuma?"
Ameena ta fada tare da dafe k'irji,
Taci gaba da cewa,.
"Amma Aneesa kinyi tsinannen miji wannan zaluncin har ina haka,"
Aneesa ta goge hawayen da suka biyo kuncinta sannan tacigaba da cewa Saida nayi sati d'aya a Asibiti aka sallameni.
Wani tashin hankali shine koda nakoma d'aki na sai nasa meshi dauke da kayan d'aki na zamani, dayake ajiyeni kawai yayi abakin kofar gidan ya juya,
Abin yabani mamaki matuk'ar gaske,
Tabe baki nayi, ai dole zai canja min kayan d'aki tunda YACUCENI. Jin tsayuwar mashin dinsa yasani ajiye gyalena kan kujera na shiga d'aki ina karewa d'akin nawa kallo."
Ameena tace
"Mugu ai dole zai canza miki kayan d'aki tinda ya halaka ki,"
Aneesa tayi murmushin takaici tace,
"Ai aure ne yayi"
Ameena ta mik'e tsaye cikin razana, ta dafe k'irji,
"Aure kika ce Aneesa, amma wannan munafikin Allah ne, gaskiya YACUCEki."
Ameena tayi murmushi tacigaba da cewa,
"Ina cikin dakin zaune akan gado ina jiran yashigo, kwatsam sai naga yashigo tare da wata rungume a jikinsa, fad'a wa sukayi kan gado tare, kasancewar da duhuwa a d'akin, nayi sauri nasauka tare da fad'in a'uzubillahi, Iro menake shirin gani?"
Da sauri ya saketa naga tana mishi wani mugun kallo,
"Ke ubanwa yabaki iznin shigo min d'aki?
Cikin rashin fahimta nace mata ina ne dakin ki,
Nan take ta kwasheni da mari, shi kuwa gogan sai hak'uri yake bata, ya jani ya hankada ni waje........
🙆🙆🙆 YACUCENI 🙆🙆🙆
The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi

Page 1⃣6⃣
"Wanki fa kikace?" Ameena ta fada tana da zare idanu.
Anee tayi dariya tace
"Eh Anty wankinace"
"Lallai, amma gaskiya kin burgeni da bakiyiba dan ba shegiyar da zata kwanta da wani k'ato dan rainin hankali tace na wanke mata bedsheet."
Aneesa ta gyara zama tacigaba da cewa, "Anty kefa Boss Lady mind set ne dake, kinsan 'yancinki dan koba komai kinfini wayewa da ilimi nasan da kece bazakiyiba, nikaina da yanzune da bazan yiba, amma kinsan Hausawa suna cewa; inda k'aton banza gwara ta fika. Watao duk aikin da kadawo kana inda nasani aikin banzane gwara kace, gwara danayi kaza kaza,
Banyi niyar yin wankin ba dan kuwa d'aki na koma saidai yana dawowa tasashi d'aki ko fad'a ta mishi koma meye, oho nidai yasameni a d'aki ya tambayeni ko inajin yunwa nace mishi,
Inaji,
Fita yayi bai dade ba sai gashi ya dawo da take away, da alama anci an raga ne,
Ya zauna a kusa dani, yace mun
"Annee tashi kici sai kisha maganin ki,"
Abin yabani mamaki,
Dukda bana jin k'arfin jiki na sai na daure naci dan har acikin raina inajin dad'in naga ya kulani,
Bayan naci nasha magani zan kwanta sai naji yace,

"Am.. dan Allah tknda kin samu sauk'i kije ki wanke mata kaya kinji,"

Ga mamakina naga ban iya masa musj ba natashi naje na fara wankin.

Bayan na wanke na koma d'aki ina kuka dan tsananin bacin rai....
Inna ta zuba ido naji anyi maganar raba girki amma shiru,
Kusan satin Amarya uku kullum can yake kwana har takai ga abin ya isheni dan banji zanci gaba da zaman gidan ba, gashi

Please Login or Register in order to submit comment