You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
YACUCENI

The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi
Page 1⃣
Sadaukarwa zuwa gareki
Nafeesat Anker


Alhamdulillahi masoyana yauma Allah yak'ara had'a mu acikin sabon Littafinmu wanda ke kunshe da darasin, Allah yabamu ikon fahimtar abinda ya kunsa.
K'irk'irane, Idan had kamceceniya ta afku tsakani halayya kokuma ta Kowane bangare akasine! Fatanmu anfani da kunshin darasin ta hanulyar k'ok'arin gyara kurakuran da kuka samu kamanceceniya...


Hajijiyar da ta kwasheni ne yasa na afkawa motar da take faman yimin horn a kunne, aguje wadda ke cikin motar ta fito duk da cewa tasan ba kad'eni tayi ba.....Daga nan farkawa nayi najini akan wata katifa mai dad'i, dai dai lokacin da nake k'ok'arin tinano abinda ya faru naji antura k'ofa anshigo ,wata matashiyar mace ce sanye da doguwar Riga bak'a sai yane kanta da tayi da bak'in d'ankwali shigarta irin ta larabawa hakama fuskar ta kamar balarabiya ko bafulatana, sai k'aramin yaro da ke rik'e a hannun ta, murmushi tayi sannan ta karaso ta zauna a gefen gadon da nake kwance,
"Baiwar Allah ya jiki"?
Hakan yasani kallon hannu na danaji yayi min nauyi, sai alokacin nafahimci cewa ruwa ne a mak'ale a hannu na, da alamu dai a asibiti nake,
" da sauk'i" nafada a tak'aice kafin na tsura mata ido da alamun tambayoyi a bakina. Bisa alamu ta fahimci hakan shiyasa tayi saurin da katar dani,
"Am yanzu bari drip din yak'arasa sai muwuce gida in yaso idan kika dan huta sai na kaiki gidan ku amma idan kinada number wani dan gidanku kibani nakira dan kar anemeki,"
Girgizamata kai nayi da alamun dai babu,
"OK ba komai"
Komawa tayi tazauna a gefe har ruwan ya k'are tazo ta ciremin.
"Dan Allah ya akayi nazo nan?"
Ta dago daga kallon takardar datake ta kalleni tayi murmushi,
"Am sorry Sunana Amina Abi Turab, dazu na sameki akan hanya tsautsayi ya ritsa saura kiris na kade ki, dukda hakan bai faru ba amma koda nafito daga motar kin tsorata kin suma shine nakawo ki nan ganin cewa kina buk'atar taimako, idan badamuwa yanzu muje gidana idan kika huta sai na kaiki gidanku,"
Daga kai nayi alamar na amince,
Wayarta tadauko takira wani nan take sai gashi yashigo cikin girmamawa yagaishe ta,
"Am Dahir jeka ka karbomin wadanna maganin yanzu kasameni a mota"
Cikin hanzari ya karba yafita,
"To baiwar Allah tashi muje ko?"
Ya gulallen hijabina na jawo nasaka na mik'e sai gani a tsaye daram ba inda yake min ciwo.
Hannun yaron ta takama muka fita muka nufi wata galleliyar mota,tana shiga tayi mata key sannan ta bud'e mun baya nashiga, yaronta ya shiga gaba,Wani irin k'amshi ya ziyarci hancina tare da wani sanyi mai ratsa jiki, daidai nan yaron da ta aika yadawo dauke da ledar maganin….
Bazan iya tamtance wace unguwa muka shigaba saidai tacika shiru sannan yawanci manyan gidajen benene sukafiyawa.
Daidai wani k'aton get muka tsaya tayi horn, nanda nan aka wangale k'ofar gidan,
Gidan ya tsaru, ban k'ara fahimtar kyau da tsarin gidanba har saida muka shiga ciki a wani falo muka zauna, falon ya tsaru harb bazan iya fasaltashiba.. Wata mata tazo ta gaishe damu taja hannun yaron tashiga dashi ciki.
Amina takalleni tace,
"Baiwar Allah ya sunan ki?"
"Aneesa. " Nafada da sauri,
"Masha Allah shiga ciki…" tana maganr ta danna wani abun latsawa dake a hannun kujerar da take zaun.
Wata mata tashigo da saurin ta tazo ,
"Hajiya barka da zuwa"
"Yawwa kande, kikai wannan a d'aki tayi wanka abata abinci, idan ta kammala ki kaita a falo na,"
Daga haka ta mik'e ta hau sama, nikam binta kawai nake da kallo.
Wacce aka kira da Kande, ta kalleni tace
"Tashi muje"
Bayanta nabi mukabi wani corridor sannan muka shiga wani d'aki wanda babu ce kawai babu aciki. Sai da ta had'a min ruwan wanka nashig, bayan nayi wanka na dauro alwala.
Koda nafito wasu kaya nagani a kan gado, banyi k'ok'arin tabasu ba najanyo nawa ina k'ok'arin sakawa kande tashigo dauke da k'aton tire… "a’a ga kayanan Hajiya tace kisa,"
ta miko min, zanine da riga da d'ankwali sai hijab.
Sai da nayi sallar azahar sannan nazauna naci abinci, koda na kammala ana kiran la’asar dan haka nayi sallar, inna idarwa sai ga kande ta kara shigowa,
"Idan kin kammala Hajiya tana jiranki"
"To " nace nabita a baya, muna fitowa matar da nagani da farko ita nakuma gani rik'e da yaron yayi shirin islamiyya, sai ga wata kyakkyawar yarinya wadda da alama itace Yayar yaron,
"Nanny," tafada daga can saman benen
"a ina aka ajiye min hijab?"
Wadda aka kira da Nanny ta juyo tace, "Au baki ganshi a kan gadonki ba,"?
Ta kwabe fuska tafara bubbuga kafafuwanta a k'asa,
" kai ni bashi nake so ba gaskiya bazan sa shi ba, Ina wannan pink din da nasaka a dazu"
Wannan karon ba Nanny tayi magana ba Kande e tace,
"Kai ranki shi dadkumainsashi dazu yanzuma shi zaki k'ara sakawa?"
"Eh ina ruwan ki ke kuma."
Daga haka tayi sama, Nanny ta bita,
Kande ta juyo takalleni tana dariya, tita, "Muje kar Hajiya tayita jira indai wannance kullum sai anyi rigima da ita.
Benen muma mhka hau; Sai dai ba ta inda naga yarinyar sunbi ba, wani kawataccen falo muka shiga wanda ya had'a komai na kayan alatu, ga luntsuma luntsuman kujeru irin na alfarma...........Kubiyoni
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆 🙆 🙆
YACUCENI

The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi
Page 2⃣

ZUZU UNA😘
Wannan page naki ne ke kadai!

Benen muna muka hau, Sai dai ba ta inda naga yarinyar sunbi ba, wani makeken falo muka shiga wanda ya had'a komai na kayan alatu, ga luntsuma luntsuman kujeru irin na alfarma.
Zaune take akan kujera wata 'yar budurwa zaune a k'asa tana rubutu a littafi,da alama wani list sukeyi.
Bayan munyi sallama mun shiga na zauna a gefen kujera, nan take tayimin nuni da nazauna akan kujerar, ba musu na mik'e na zauna,
Kande kuwa juyawa tayi tafita.
Saida sukayi kusan mintuna goma suna magana sa'annan yarinyar ta tashi, har k'asa ta gaidani sannan ta fita.
Amina Abu Turab, ta juyo ta kalleni, na k'ara gaisheta.
Cikin nutsuwa tace, "Aneesa ya jikin yanzu? da akwai inda yake maki ciwo?"
Girgiza kai nayi nace,
"Babu, yanzu sai godiya,"
"Alhamdulillahi" tafada a bayyane, sannan taci gaba da cewa,
" fitazanyi dama yanzu sai na wuce dake zuwa gidanku nayiwa iyayenki bayani dan kar ayi miki fad'a"
"Toh"
Nafada tare da k'ara makure jikina dan kuwa sanyin d'akin yafara tabani.
Wani d'aki naga tashiga, batadadeba tafito sanye da mayafi sai jaka da ta dauko muka fito, abinda yabani mamaki shine ganin taci gayu amma takalminta sam basu dace da shigar taba dan kuwa sunyi kama da irin takalmin nan da ake tsintuwa acikin zanen gado.
A babban falonnan na k'asa muka hadu da Kande yayinda ta nado kayana ta rik'emin, har muka kai bakin k'ofar falon ina mamakin takalmin ta, tsayawar da naga tayi ne yasa na dago kai na kalleta..
Wata durowace na gani a gefen k'ofa gaba d'ayanta gilashi ce,sai jerin hadaddun takalma kala kala.
Nan take Kande ta bud'e ta jawo wasu flat Shoes masu shige da tsadaddiyar atamfar da tasa...
Motar da muka hau dazu ba ita nagani ba wata ce ta daban yanzu kuma; Lallai masu abu ke ci da rana, abinda nafada a raina kenan,
Acikin motar ne ta kalleni tace,
"Aneesa wace unguwa zan kaiki?"
" Goran dutse " Na fad'a, ni kaina banyi niyar cewa can ba dan kuwa bansan bala'in da zan tarar a can ba.
Bayan mun isa nake mata kwatance har muka kawo bakin kofar wani gida.
Anan nace ta tsaya yayinda duk na dabarbarce, fita nayi itama ta rufe motar tabiyo bayana.
Bayan tashigo nayi mata iso acikin kangon d'akina wanda babu komai aciki face tabarma sai filo,
Bayan tazauna tanemi da nayi mata iso ga iyayena. Tsakar gida na fito na tsaya, kamar naje kamar na fasa, sai kawai na wuce nashiga ainahin cikin gidan.
Daidai lokacin da natura k'ofar ne nayi karo da Asama, tana ganina ta kece da wata mahaukaciyar dariya,
ban kalletaba na wuce d'akin shi daga shi sai k'aramin wando, yana ganina ya turbune fuska, tin kafin nace komai ya katseni da cewa
"Ke dan ubanki waya dawo dake a gidan nan?"
Cikin tsoro nace
"Dama am am dama"
Wani wawan mari ya daukeni dashi,
Kafin nayi yink'urin gudu ya rufeni da wawan duka, ihun da nakeyine yasa Amina ta fito domin taga me yake faruwa,
Daidai tsakar gida muka hadu da ita, na fad'a jikinta inna ihu.Ganinta bai hanashi jawoni yaci gaba da jibgaba.
Ganin yana Neman illatani yasa Amina ta yi mishi tsawa tare da k'ok'arin jawoni jikin ta.
Tsayawa yayi yana kallonta,
"Haba Malam Dan Allah kayi Hak'uri wallahi ba laifinta bane"
Wani kallon banza yayi mata,
"Oh kece uwar da take daure mata gindi ko"?
Yaci gaba da jibgarta,
Cikin harzuk'a tace,
"Kai wane irin mahaukaci ne, yazaka kama yarinya kana jibga kamar wata jaka, batare da ka tsaya kaji me ya tsaida ita ba?"
Cikin fushi take maganar, shi kuwa
Kallonta yayi sama da k'asa dukda bai ga kalar raini ba...
"Malama meyasa bakin ki aciki?
Ko kasheta nayi meye ruwan ki aciki? nagaya mata idan tak'ara dawowa gidan nan sai na lahira yafita jin dad'i, Karya kawai marar galihu dabbba jaka shegiya,"
Amina ta hasala ainun dan haka
ta kalleni, Cikin fushi tace,
"Aneesa nan ne gidanku?"
"Eh"
"Ina mahaifanki"?
Girgiza kai nayi nafashe da wani matsanacin waje, Hannuna taja mukayi waje.....
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
YACUCENI

The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi
Page 3⃣

A matuk'ar hasale Amina Abu Turab take Jan motar yayinda nikuma nake faman azababben kuka. Jin alamun ta tsaya ne yasa na sassauta kukan tare da dago kaina. A wani wuri ta tsaya da alama mutane basu cika shawagiba. Munfi k'arfin minti goma sanna ta kalleni,
"Aneesa"
Ta kira sunana a raunane fuskarta dauke da alamun tsananin bacin rai da tausayi..
"Waye wannan da yayi maki dukan rashin imani?"
"Mijina ne"
Na fad'a acikin wani yanayi yayinda naji kalaman sun zomin da wani daci a maqoshi.
Karo na farko kenan da naga alamun mamaki zahiri a fuskar ta,
"Mijinkifa kikace? dama kina da aure a haka?"
Ta nunani da yatsa,
"Eh inada aure wata, biyu kenan da auren amma kuma sati d'aya kenan da yasake ni."
Bud'e baki tayi wanda ke nuni da alamun tsananin mamakin da tayi na sakin yafi wanda tayi alokacin da taji ni mai aure ce.
Cikin rashin fahimta tace,
"Mijinki ya sakeki tsawon sati biyu to me yamaidake gidan sa, ke inane gidan naku?"

Wani kuka tsananin yazomin mai dauke da kalolin bak'in ciki,
Nan take kuwa na darje abina,
Abinda yayimin dad'i shine, sam bata hanani kukan ba, k'arshe ma wayar ta ta dauko taci gaba da sha'aninta, sai da naci na k'oshi sannan tajuyo tace,
"Ina ne gidanku ina so na koma Office a kwai abubuwan da zanyi,wace unguwa kike,"
"A inda kika kaini d'azun canne gidanmu,banida wani gida da yawuce can,amma ki ajiyeni ko anan sai ki wuce abinki nagode da taimakon ki a gareni Allah yasaka maki da alkhairi,"
K'asan hijabina nasa ina goge hawayen da yake rige-rigen kwaranya a kan kumatuna.
Bata ko uffanba ina k'ok'arin bud'e motar naji tayiwa motar key dan haka nayi shiru nasanya idanu innaganin ko gidan mijin zata maidani.
Gidan da mukazo dazu yanzuma nan naga tana horn, yayinda mai gadin gidan ya bud'e gidan tare da kwasar gaisuwa.
Muna shiga daga ciki wasu mata na gani sun nufomu kowacce daga cikin mini dress,
"Weldon madam,"
Suka fad'a harda dukawa kasa,
"Weldon"
Tamaidar musu,
Nan tashiga gaba muna take mata baya, saida tashiga falon ta canza takalmi sai yanzu na gane manufar takalmin da tasaka a dazu kenan idan ana cikin gida irinsu ake sawa.
Anan falon k'asa ta zauna, haka ma sauranan suka zauna, wasu takardu suka mika mata suka juya harshe, suna faman turance juna.
ina danbjin me suke fada, bisa alamu zancen kasuwanci ne sukeyi.
Wani abun dannawa a gefen kujerar da take zaune naga ta dannan ba'a fi sakon goma ba sai ga wata matashiyar budurwa tazo, nan take tayimata umarni da tashiga dani, dakin da aka kaini dazu yanzuma can aka ajiyeni, da alamu dai d'akin wannan matashiyarne.
Da yake gab ake da sallar magrib yasa na wuce bayi na dauro alwalla,
danafito nasamu kwayoyin magani tare da kofin ruwa a saman madubin d'akin. Wannan matashiyar ce ta turo k'ofa tashigo,
Saida ta kalleni tayi murmushi sannan tace,
"Ga magani can Anty tace kisha sannan kiyi salla,"
"Toh"
Nace na dauko maganin nasha nayi salla, ban tashi daga kan sallayarba saida akayi sallar isha,i.
Nan aka kawomin abinci naci, nayi wanka nafito, nan take naji wani irin nishad'i yana zomin wanda na dade rabona da naji irinsa, dukda dinbin damuwa da bakin cikin da nake dauke dasu........
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆 YACUCENI

The book
Of
Queen Mermue

©
HIKIMA writers
Association

Edit by
ANaM Dorayi.

Page 4⃣

Hikima writers association.

Amina Abu Turab bata nemeni ba har tsawon kwana uku,
Zama na a gidan zaman jindadi ne,dan kuwa banida damuwa, duk safe na kanje na gaishe ta daga nan kuma ba k'ara ganinta zanyi ba sai dai naji shigenta ko fitar ta,
Duk bayan sallar isha,akwai wadda take zuwa tana muna lecture, wata wayayyiwar mace ce,
Aisha kande inno Hasiya zaina,sai kuma ni,mune acikin gidan su hasiya da inno su suke kula da abincin gidan sai zaina da Aisha tsabtar gidan suke dubawa yayinda kande take kula da Jeedda da Jayyid, wato 'ya'yan Amina Abu Turab,
Abinda ya daure mun kai shine tin zuwa na a gidan bayan mai gadi bantaba ganin ganin wani namiji a gidan ba,hakama kaf gidan bantaba jin wanda yayi zance gameda mijin Anty ba,kamar yadda akafi kiranta,
Yau Alhamis ce tun k'arfe bakwai Anty tafita yayinda naga anata faman gyaran gida, gaba d'aya ko ina sai faman shara da goge goge akeyi hakama harda su kande duk ake aikin haka yasa nima naje domin nataya su,amma fur suka hanani,nayi nayi na taya su koda gugar takalmin Anty ne, amma suka ce ita tace kar nayi komai hakan yasa nakoma na zauna ina kallon su,
Suna aiki yayinda nake taya su hira,Aisha da kande ne kawai a k'asan sauran sunyi sama domin su gyara can,
Can na kalli Aisha nace,
"Yau kam kunsha aiki hala maigidan zai dawo a yau ne,"
Kamar hadin bakin sukace,
"Mai gida kuma"?
Aisha taci gaba da cewa,
" shekara biyar kenan muna aiki a gidan nan amma ba wani namiji da ya tab'a shigowa acikin gidan nan idan ba wadanda suka
Kama dole ba,ke in tak'aice miki ko dan uwan Anty indai namiji ne to ban tab'a ganin shi a gidan nan ba"

Cikin mamaki nace,
"Au dama batada aure to ina Baban su jayyid?"
Wannan karo kande ce tace,
Ai ina ganin ya rasu dukda abakin jeedda naji"

Haka mukayi ta hira suna gayamin tsarin gidan da irin yanda Hajiyar gidan ke tafiyar da rayuwar ta dukda ita mai tarin dukiyace Wanda dole kayi mamaki irin karamar mace da ita da irin dukiya ta hamshak'an mazajen da ake fafatawa dasu a Nigeria,




****************

Labulen tagar d'akin ta yaye, yayinda ta rungume hannayenta a k'irji tafara turn and fro, abubuwa suna dawo mata sabbi a rayuwa iya tunanin ta bataga matsalar da zata hanata kwana a yanzu ba amma ina,sai gashi wani k'aramin alhaki yana so yasha mata kai,lalle dole tasan yadda zatayi ta shawo kan wannan al,amari,domin kuwa yanda tayi tunanin abin yazo da sauk'i sai taga akasin hakan, gashi kuwa dole ne tayi nasara akan wannan lamarin,
Agogon dake manne a bangon d'akin ta kalla k'arfe ukku daidai dan haka takoma tabi lafiyar gado dan kuwa akwai gagarumin aiki a gabanta.

**************
Yau Aneesa tacika sati d'aya a gidan Amina dan haka yau k'arfe uku Amina ta aiko a tafi da Aneesa a gadinar da ke a bayan gidan,
Tana tafe tare da Aisha sai Jeedda dake rik'e a hannun Aneesa dayake Allah ya had'a jininta da yaran gidan wato Jeedda da Jayyid,

Can ciki take zaune acikin wata rumfa irin mai kama da bukka, sai kayan marmari dake a gaban ta jarida take karatu mace cikakkiyar mace mai k'ananan shekaru sam bazakace ta haifi 'yar shekara sha d'aya ba
Bayan mun gaishe ta ne Aisha ta juya ta wuce Jeedda ta koma can saman kafufuwan mamarta ta zauna,
Cikin shagwaba tace,
"Mummy yau fa kikace zaki fara koyamun driving amma kuma kin zo nan kin zauna,"
Mumyn ta kalleta tayi dariya tace,
"Jeedda kin cika rigima yanzu inake ina koyan mota kibari nan gaba sai ki koya yanzu jeki kande ta shirya ki lokacin islamiyya yayi,"
Kafin ma Mamar ta k'arasa Jeedda tafuce a guje harda jamin hijab wai kar tayi latti ayimata bulala,

Kafin Amina tayi magana wayarta ta hau k'ara tana neman taimako, kamar bazata daga ba sai kuma ta tadauki wayar,
Abinda yabani mamaki shine ganin yanda ta canja yare izuwa yaren k'asar larabawa da alama Wanda take maganar dashi yaren da yake ji kenan.
Kusan mintuna goma tana wayar bayan ta kashe ne ta kalleni da kyau, tace,
"Aneesa kamar yadda kika sani bansan komai dangane da rayuwar ki bayan sunan ki danasani,
Amma nadauko ki nakawoki acikin gida na acikin iyalina,
Tun lokacin da na hadu dake naji kin kwanta min naji kaunarki kamar yadda ki kasan yaya zata kaunaci k'anwar ta,
Yanzun dakike gani nakiraki ne na baki labarin rayuwa ta dukda kece mace ta farko da zan taba fadawa sirrina,
Kamar yadda kika sani sunana Amina Abu Turab,
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆. YACUCENI
The book
Of
Queen Mermue

©
HIKIMA Writers
Association

Edit by

ANaM Dorayi

Page5⃣




Taci gaba dacewa,
Aneesa a rayuwa ba bakar wahalar da bangani ba,
Mahaifi na dan nan Nigeria ne, jihar sokoto, yayinda mahaifiyata kuwa mutumniyar k'asar Cairo ce, mahaifina dan kasuwa ne Wanda har kasuwanci ya zaunar dashi acan na tsawon shekaru,
Ba kad'an mahaifiyata take sonshi ba, Wanda har yakawo mata matsala a wurin danginta dayake tuni mahifanta sun rasu tana zaune a wurin k'anen mahaifinta,
Bayan soyayyar su tayi nisa ne yayinda sukayi wa juna alkawarin aure kota halin k'ak'a,
Dangi mahaifiyata Sam suka ki amincewa da auren dukda cewa sun matsu da su aurar da ita, dan haka aka had'a ta da dan k'anen mahaifinta alokacin tanada shekaru ashirin,
Saura kwana daya a daura auren aka nemeta aka rasa, sai daga baya akaji labarin cewa guduwa sukayi, anan garin kano suka samu wasu malamai suka daura aurensu domin kuwa Sam bai barta tasan danginshi ba saidai kullum yayi mata karyar suna gaida ita idan tayi maganar zuwa yace zasuje,
Mahaifiyata Allah ya dauromata wani irin son mahaifina,
Shekara d'aya da auren su ta haifi ne, Amina,
Sam mahaifina baya kaunata yayi ta aniyar halakar dani tsarin Allah ne kawai,
gashi akwai shi da yawan tafiye tafuye tin sa,adda suka haifeni yakai mahaifiyata aka juye mata mahaifa,
Dukda tanajin ciwon abinda yake yimin amma sai ta daure akan kaunar da take masa yayinda nikuma nataso da tsoro da tsanarshi,
Ina aji shida a primary ne muka nemeshi tsawon wata ukku muka rasa hankalin ummi yatashi ainun nikam ko ajikina dan kuwa idan baya nan nafi sakewa,
Ummina taje ta dauko ni daga makaranta koda muka dawo sai kayan mu kawai mukaga ana futarwa daga gidan mu cikin tashin hankali ummina tashiga tambayarsu ko lafiya?, anan ake shaida mata ai mai gidan ya saida gidan kuma dama wata biyu aka bashi ya kwashe kayanshi sai gashi Allah yayimasa Rasuwa, cikin gidima ummina ta fadi anan,somammiya, kwanan mu biyu asibiti aka sallanemu daga nan ummi ta had'a mana kayan mu da aka rabe a makota muka wuce jihar sokoto, dukda tasan unguwarsu

Please Login or Register in order to submit comment