You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

duk wani aiki ni nakeyi a gidan, Sabida tsabar RASHIN GATA yasa koma tamkar 'yar aiki, ga bak'in zagi nakesha daga garesu baki daya, kuskure kad'an zatasashi yayi ta jibgata kamar jaka.
ABINDA AKE GUDU kenan, nayi gudun gara na fadawa zago.
Yau kam abin ya isheni dan kuwa dukan tsiya nasha jiya cikin dare, akan Asama ta fita unguwa ta sani gyaran d'akinta, yana dawo wa tacemasa yaje ya karbo mata kud'in ta a wurina ta ajiye goma akan gado bataganiba, dayazo ya tambayeni nace ban daukaba shine ya hauni da duk har yake cewa, duk yadda akayi uwata barauniyar karuwace da safe kuwa inna tashi na sameshi naimasa maganar gidan da muka taso tinda ba'asa 'yan hayar ba ya barni na koma na zauna acan, sannan kuma shagon dake Dorayi a saida shi abani kud'i n innaso zancigaba da Karatu.
Nan da nan yashiga kame kame,
Ganin na tsareshi da idanu danson jin abinda zaice sai kawai ya fara kwasar karan mahaukaciya,
"Au so kike na baki kije kina karuwanci ko, dama ku 'ya'yan shegu idan ba karuwanci kukayiba bazakuji dad'i ba."
Asama dake a labe, tafito tana cin cingum ta kalle shi ta watsamai wata harara.. "Dan kana munafiki shine kake wani boye mata, to idan bazaka fad'a mata gaskiyaba ni zan fad'a mata,"
Ta maida kallonta a gareni,
"Ke bawasu kud'i da kike dasu yanzu, gidanki ya saida ya biya sadakina da lefe, kud'in shago kuma tsohon saurayina da zan aura ya biya kud'in shi, sauran kudin kuma sune muke cin abinci a yanzu, idan kinji bazaki iya zama ba ki tashi ki bar gidan kikoma asalin gadonki na karuwanci."
Cikin k'arfin hali da bak'in ciki, na kalle su nace,"Ni ba karuwa bace kuma sai Allah yasakamin, kai kuma kasani DAGA K'IN GASKIYA sai fad'awa halaka, Gida kuma wannan nawane, dan haka inaso abani gidana." Nakuma kudiri aniyar nunamata RAMUWAR GAYYA tafi gayya zafi......
Wani gigitaccen mari ya daukeni dashi wanda yasani ganin taurari a idanuna yayinda sukuma naga sun koma su hud'u.
Nuna ni yayi da dan yatsa, "Keeeee duk iskancinki ya tsaya a kaina amma idan kika k'ara sanya Asama saina illataki, kuma gida da kike magana inaki saniba kisani duk kotun da zakije a duniya ba a isa a karbar miki shiba, dan suna nane radau a takardun, dan haka ki canja shawara,"
Asama ta katse shi da cewa,
"Iro kodai ni ko Annee a gidan nan wallahi bazan zauna da itaba dole ka saketa a yau tinda har ta iya kallon mu ta furta irin wad'annan maganganu, ina so ka saketa sakina walak'anci."
Cikin rashin Imani ya koma ya dauko biro da 'yar takarda ya mika ma Asama,
"Asama ki saketa iya yanda kike so"
Cikin wani irin kuka na fadi na rik'e k'afafunshi,
"Iro banida kowa idan ba kaiba dan Allah kar ka sakeni,"
Hannuwansa biyu yasa ya tun kudani gefe,
Ya karbi ta kardar daga hannun Asama yace,
"Saki nawa ne?"
"Uku"
Ta fad'a tana murmushi,
Jefamun yayi,
"Kije ko sana'ar karuwanci kiyi na sakeki saki uku, kuma tashi kibar gidannan ko wallahi na halakar dake,"
Cikin kidima na jawo hijab dina, na rugo a guje dana nasan halin Iro irin mak'etatan fulanin nanne,
Dan haka nafito kafin na k'arasa bakin k'ofa Asama ta rufe k'ofar tarike kugu.
"Iro wallahi kafito dan bazata bar gidan nan ba har sai tafuta daga hankalinta.......
Pls fellow this link to like my face book page
https://www.facebook.com/Queen-Mermue-Novels-Fans-436431613362583/
🙆🙆🙆 YACUCENI 🙆🙆🙆
The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi

Page1⃣7⃣
Sai dasukayimin mugun duka sannan suka bud'e k'ofar, dana fito ko gani banayi sosai gefen idona daya kumbura,
Layin baya nabi ba wuce, nikaina bansan inda zani ba,
Cikin tsautsayi na hau titi zan tsallaka wata mota ta k'ade ni," Abu Turab ta dafe k'irji tace, "Innalillahi Allah yasa baki mutu ba"
Aneesa ta kwashe da dariya tace, "Kai Anty wai ban mutu ba to dana mutu ne wazai baki wannan labarin?"
Sukayi dariya gaba daya, wannan tace, "Ke aini tsabar rudewa ce wannan wahalar har ina, waye ya kad'ekine?"
Annee tayi dariya kad'an kana tace,
"Hmm Anty wani bawan Allahne mai kirki, kyakkyawa dashi, bayan yakaini Asibiti aka nemi yimin k'arin jini, nan take yaje aka auna jininsa akayi sa'a zai iya bani aka duba lafiyarsa sannan aka diba aka karamin.
Sai bayan kwana d'aya saannan na farka. Wannan bawan Allah shine mutum na farko a dunkya ya yataba nunamin gata da darajar dan Adam bayan Malam Damma,yanemi yasan gidanmu, banb'oye masa komai dangane dani ba kasan cewar takardar sakina ma tana hannunsa tin lokacin da yakadeni. Ya tausayamin matuk'a, haka ya dauki nurse din da ko toilet zanje sai tarakani, kullum zaizo da safe ya kawomin breakfast, sannan kuma zai dawo k'arfe d'ayan rana wani sa'in kuma k'aninshi yake turowa.
Haka k'arfe takwas na dare zaizo sai sha d'aya zai bar Asibitin. Mutum ne mai raha da tausayi.
Abinci kuwa sai wanda nakeso. hakama k'anenshi yanada kirki sosai, shima yacika abin dariya, zamu iya yin sa'anni. Cikin kwanaki goma na shak'u dasu sosai, saidai abinda yabiyo baya shine, jinake bayan iro a duniya babu wani d'a namiji da naji ina so kamar bawan Allahn, idan yashigo sai nayita kallonsa, fahimtar irin kallon da nake mishine yasa ya dena zuwa, saidai k'aninshi, kwana biyu baizoba hakan yasa hankalina ya tashi sosai..
Abdul Hakeem sunan k'anin nasa, shine yake zama a wurina da daddare idan na tambayeshi bawan Allah sai yacemun yana gida..
Ranar da aka sallameni Abdul Hakeem ne yazo daukata, na tambayeshi ina zai kaini, sai yace gidan Yayarsu,
Na tambayeshi sunan Yayanshi na gaske sai yayi dariya yace, "Bawan Allah."
Muna kaiwa a bakin wani shago yatsaya zaiyi sayayya na bud'e mota na fito dan bansan abinda zai faru ba idan nabi Abdul Hakeem,
Wata k'ila danginsa basa daraja dan Adam,
Watak'ila yayanshi da nakejin sonshi a raina yanada mata,
Kinga kywa zanyi zaman bak'in ciki, tinda nasan zaiyi wuya mutum yaji tarihina bai gujeni ba, wannan daliline yasa tension yayimin yawa a ranar na afka miki a mota."

Ameena tayi ajiyar zuciya,
Tace, "Lallai Annee kema kinga rayuwa, gashi kin gamu da son maso wani, ni a ganina da kinbishi kinje gidansu wata k'ila shima yana sonki."
Ameena tayi dariya tace, "Kai Anty nifa Bazawarace yanzu haka ban kammala iddaba,dan haka duk wani batun So duk baya gabana karatu nake so nayi dan nasamu abin k'are hakkina."
"Annee labarinki ya matuk'ar bani tausayi, kina neman soyayya yayinda nikuma nayi fatali da nawa masoyin na gaskiya, lallai kowa yasami Abdul a rayuwa yaji dad'i,yanzu shine buri d'aya da yaragemin a rayuwa, wato ya aure ni,ke kuma zan taimakamiki wajen neman bawan Allah har inga yasoki ya nuna miki gata zankuma kasance yaya a gareki, makaranta kuma zakiyita zan koya miki yanda zaki zama me 'yanci a wurin da namiji."
Aneesa ta share hawayen dake kwaranya a idanunta tace, "Anty ko yanzu kinmin komai a rayuwa kin bani abinci kin bani wurin kwana kin bani sutara sannan kin bani labarin rayuwarki nagode Allah yabiyaki."
Ameena ta duba Agogon dake manne a falon Wanda ya nuna k'arfe d'aya da rabi na dare, ta kalli Annee tace,
" Ashe dare yayi haka, tashi kije ki kwanta gobe k'arfe shida zan fita ki shirya zamu fita tare."
Aneesa ta mik'e tana hamma tace
"Toh Anty Allah ya tashemu lafiya"
Tafita......

Asuba tagari
Annee Ameena,

Bawan Allah
Abdul Hameed.

Page 1⃣8⃣
This page is for yku my Hanny😘much love Fadeematu Bature,

Lallai kam nasamu kyakykyawar kulawa da gata gurin Aunty Amina, cikin dan kankanin lokaci tasamamin gurbi a jami'ar Bayero, zamana a gidan zaman 'yancine dan tamaidani tamkar kanwarta ta jini, babu abinda zan nema na rasa a gidan, hakama abinci tare da iyalanta nakeci, duk wata hark'allar kasuwancinta nasani dan tini tafara nunamin dabarun kasuwanci.
Macece mai tausayi da jinkai saidai akwai nuna isa, da son girma. Yaranta kuwa sun kasance kamar kanne a gareni dan tinima nakoma da zama a saman bene nabaro kasamu inda duk masu hidimarta suke.

A yanzu babu abinda Aunty tasa agaba sai kasuwancita, tana harkalla da manyan k'asa sannan kuma tana yawaita neman Abdul duk da cewa bata san asalin garinsu ba.
Yau kimanin watana shida a gidan har nagama iddata.
Yau ta kasance Asabar ba school haka ma Aunty Ameenama tana gida, nashiga falon da sallama sai najiyota a d'akin karatu tana amsamin sallama, nasameta a ciki tana cike wasu forms, "Kai Anty yaufa Asabar amma kintashi tunda safe haka,?"
Dago kai tayi tana murmushi tajawo kofin dayake a gefenta ta kurba, kana tace,
"Anee ai gwara da kikazo kema kizo kitayani, kwangilace gwamnoni suka bada Kaduna Katsina da kano, shine nakeso tazo hannuna dan kuwa akwai samu,"
Anee tayi dariya tace
"Ai naga alama Anty dan naga kin dage"
"Ai dole nadage dan kuwa zata iya kubcewa dukda cewa bawai zanyi kwangilar neba inasone kawai tafito ta hannuna akwai wasu da zanbawa,kwangilar kimanin biliyan ashirince,nikuma zan bada ta a kimanin bilayan goma sha tara, kinngan natashi da biliyan d'aya, su kuma wadanda zan bawa zasu fini samu dan kuwa akalla bazasu kashe biliyan goma sha shida ba, kingan zasu samu suma, idan tashigo din tsakanin Alhaji Ja'afar da Alhaji Ayuba bansan wa yadace nabawa ba, dan dukansu mutanen kirkine, naso na had'a su duka suyi a tare amma shi Alhaji Ja'afar ya nunamin d'ansa yake so yasa aciki, shi kuma Alhaji Ayuba akwai wasu 'yan kwangila a kasan sa, Ranar litinin kishirya kirakani meeting din dan idan nagansu duka sai na rasa wa yadace na bawa idan tashigo."
Aneesa ta nisa tace,
"Anty kwangilar menene haka da kud'i dayawa?"
"kanfanonine za'ayi a kowace jaha na sarrafa shinkafa, sai wasu motoci da za'ashigo dasu daga kamfanina na Jayyid motor's...." Karar da wayarta tayine yasa tayi shiru,
ta number....kamar bazata dauka ba, sai kuma sai ta daga tare dayin sallama.... Tayi tsawon mintuna goma tana wayar wani sa'in tayi murmushi wani sa'in dariya sosai,
Daga k'arshe naji tana cewa,
"Ba komai sai tazo"
Banji me akace daga daya bangarenba naji ta kara cewa
"Ohk bye"
tare da katse wayar.
Bayan data katse wayar ta jima tana juyata daga bisani ta kalleni tace,
"Anee gobe inaso kirakani Abuja,dan haka idan kinje islamiyya a yau ki fadawa malaminku bazaki je gobeba,"
Ta k'are maganar ne da alamun damuwa a fuskar ta,
Cikin ladabi nace
"Toh" tare da mik'ewa,
"Anty bari nashiga d'akin Jeedda zamuyi wasa"
Na fada da sigar dariya dan banaso naga tana shiga irin yanayin wanda ya zamemata jiki a 'yan kwanakinnan,
Na yi sa'a kuwa d'an dariya tayi tace,
"Anee Allah ya shirya yanzu haka zan wankewa bawan Allah ke kina wasan yara?"
Nashige da sauri tare da rufe fuska itama tarama zolayar.
"Jeedda, Jeedda, shine kika share ni ko? to bari nafita naje wajen Jayyid,"
Har nakai bakin k'ofa tazo gudu ta rungumeni ta baya,
"Anty Anee karki tafi, bakyaleki nayiba addu'a nakeyi kinsan kince nayi addu'a zanci exams dina, Pls dawo ki zauna,"
Na juyo ina dariya nace, "Oh hakan nada kyau, amma kizo nayi miki kitson yanzu dan kuwa gobe fita zamuyi, idan bahaka ba kande ta kaiki ayimaki,"
Nan da nan ta turbune fuska dan kuwa bata son kitso ko kad'an Aneesa ce kawai take zaunawa tayi mata kitso ba tare da tayi kukaba, yarinyar tanada dogon gashi ga yawa,
"Kai Sis Anee kibarni Dan Allah sai na d:aure kan kawai naje school haka nan,"
"To shi kenan idan akayi maki bulala kar kizo mana da kuka,"
"A,a to muje kiyimin amma name zafiba,"
"Toh tashi muje,"
Suna fita Jayyid yana fitowa,
"Sis Anee gud morning,"
"Yawwa Jayyid how are u?"
"Fyn, sis Jeedda mrng,"
"Morning too"
Jeedda ta fad'a fuska a turbune,
"Sis Anee kitso zakiyimata naga ta daure fuska,"
tafada da alamar tsokana,
Anee ta kalleshi,
"Ba ruwana idan tayi maka duka,"
Ai kowa tana kallo shi yayi mata gwalo ya shek'a d'akin Mummy, Anee kam dariya tayi tace,
"Muje garden idan ya biyomu muyi mishi duka,"
Nan da nan Jeedda tasaki fuska dan taji yanda zata rama.....
Pls fellow this link to like my face book page
https://www.facebook.com/Queen-Mermue-Novels-Fans-436431613362583/
20

Dago kai nayi na kalleshi zuciya ta tana dukan uku uku,
Kodai yasan ina sonshi ne?
Tambayar da nayiwa zuciya ta kafin nak'ara cewa komai yaci gaba da cewa,
"Aneesa tsakanina da ke ba wani boye boye, bazan tilastaki ba idan kinji bazaki iyaba amma kisani zuciya ta takamu da cutar kaunarki fiye da yadda zata warku,
Aneesa ni ba k'aramin yaro bane da zance bansan meyeso ba ina da mata shekarar mu shida da aure kenen Allah bai bata haihuwa ba dukda yar uwa tace ta gefen mahaifina auren hadi akayi muna kuma muna zaune lafiya mahaifiya tana matuk'ar son na kara aure ko Allah zaisa adace, "
Ya juyo ya kalleni da fuskar tasauyi,
"Aneesa kitaimaka mun kar kice bakya sona,"
Hankali na atashe ga samu ga rashi,
Domin kuwa abu mai wuyane iyayensa su amince da aurena,
Kamar yasan abinda nake tunani a zuciya ta katse ni da,
"Aneesa iyayena bazasu hanani auren ki ba koda kowa ke kika fi kowa rashin asali, sunada ilmi sosai basa hana mutum yin abinda yake so matuk'ar bai sabawa addini ba, dan haka kada kikawo wannan tunani a zuciyar ki,"
Cikin sanyi jiki na bud'e baki na dakyar nace,
"Babu komai nagode sosae amma yanzu bazan baka amsa ba har sai Anty Ameena ta dawo idan na gayamata komai muka yanke shawara zakaji,"
Ya kalleni tare da kanne ido,
"Pls ataimaka Bawan Allah kar agujeshi,"
Murmushi nayi muka dan tab'a hira daga nan mukayi sallama nashiga ciki,
Ko baccin kirki banyi a yau ba sai faman juyi da nakeyi akan gado ganin al,amarin nakeyi kamar a mafalki,
Allah maji rokon bawa,
Allah yasa Bawan Allah ne zai sheremin kuka na,
Da safe jirginsu Anty ya iso bayanTa huta ne takirani a d'akin ta,
Nan nashaida mata yanda mukayi da Bawan Allah, harda rawa ta tashi ta taka sai faman murna takeyi,

"Anee Allah yana karbar addu,ar bayi a wani gefe ta inda bazasu yi tsammaniba,
Kamar yadda nake gaya miki matsalar da zan samu a wurin Abdul itace mahaifiyar shi,insha Allah yanzu zan kauda wannan matsala,"
"Da gaske Anty? Tayaya?"
"Wani kamfani ne mahaifiyarshi ta bud'e Wanda muka saka hannun jari na kaso hamsin aciki dani da Hajja Fati matar gwamna, yayinda kaso a talatin da biyar na sauran mutane ita kuma tanada kaso goma shabiyar aciki,
Amma kamfanin a karkashinta yake
Tafiyar da kikaga nayi tare da matar gwamna muka je domin duk akan maganar ne, idan muka cire kason mu a ciki kamfanin bazai je ko,ina ba zai durkushe,
Hajiya Zaino wato mahaifiyar Abdul tasan ni tin alokacin da Abdul yayi zama a asibiti amma yanzu da muka hud'u Sam bata ganeni ba,sai mamaki ma tayi a lokacin da taji cewa nice Turab ita a tunanita ni babbar mace ce,yanda take jin sunana,
Yanzun nasamu hanyar kusanci da ita kuma nasan zan samu me nake buk'ata gobe zamu hadu da Abdul,
Tsawon shekara goma kenan ban sashi a idona ba,"
Anee tayi ajiyar zuciya tace
"Allah yasa alkhairi Anty,"
"Ameen my Anee, yanzu ki fad'a wa Bawan Allah kin amince zaki aureshi amma zai barki kici gaba da karatu Dan bazan yarda ya hanaki karatu ba,"
"Toh Anty bari na kirashi tin dazu naga call dinshi,"
"Toh jeki, amm kicewa kande tazo ina son ganinta,"
"Toh"
Daga haka tafice bayan ta she dawa kande kiran Anty ta wuce d'akin ta ta soma neman layinshi,
Yaji dad'i sosai da tasanar dashi ta amince cikin murna ya kira Mumyn shi yasanar da ita tare da Anty kultum babbar yayarsu,
Dukan su sunsan da zancen Aneesa dan haka suma sunyi murna sosai ba kamar Mumy da tayi tasamishi albarka,

Abdul yana zaune a office dinshi ya jingina bayanshi asaman kujerar da yake zaune akanta tare da runtse idanunshi yana jiran shigowar bakuwar da sakatariyarshi tasanar dashi yayi,
Sallamar da tayi ne yasashi bud'e idanunshi tare da karba sallamar,
Ras! Gabanshi ya fadi,
Ganin matar da ko zai shekara dubu bai gan taba bazai manta da fuskar ta ba,
Murmushi Ameena Abi Turab tayi tare da zauna akan d'ayar kujerar dake a gaban teburin,
"Sannu Abdul ko baka ganeni ba?"
Gyara zaman shi yayi tare da maida mata murmushin da tayi,
"Naganeki mana dama zan manta dake ne?"
"Toh ai naga shekaru sunja nadauka ko kamanta ni dukda nasa bakada mantuwa,"
"Lallai kam kinsan da haka,
To yakike ya gida"
"Alhamdulillahi sai godiya,"
"Yaushe aka shigo k'asar ne?"
"Hmm ai najima a k'asar sai da ban sameka ba har abujan naje akace kuntashi,"
"Hakane Ameena mun jima da barin gidan da yake yanzu ma anan kano ni nake zaune,"
"Masha Allah ya iyali ko kana nufin bakayi auren ba?"
Dariya yayi kana yace,
"Nayi aure mana kema ba kinyi ba"
"Waya gaya maka nayi aure ne,"
Tafada tare da juya ido,
"Ameena ai nasan ba zaki zauna har yanzu ace bakiyi aure ba,"
"Hakane kam nayi harda 'ya'ya biyu,"
"Masha Allah, Allah yarasu to ya Baban su anan Nigeria kenan,"
Murmushi tayi kana tace
"Baban su yarasu shekara tin da jimawa bayan rasuwarshi ne nadawo anan Nigeria,"
"Eyyah Allah ya gafarta,"
"Ameen"
Haka dai suka tab'a daga bisani ta karbi number wayar shi ta wuce,
Yanzu kam hakan ta zai cimma ruwa dan tuni Hajja Aisha wato Matar gwamna ta k'enkesawa Hajiya zaino labarin wacece Amina Turab, tsaf Hajiya zaino ta tuna ta dan tasan irin sonda dan nata yayiwa matar hakan yasashi zama kamar wani tababbe,
Da farko Sam kin yarda tayi Aisha ta nuna mata Kamfanin da take takama dashifa sune rik'e dashi, dan haka tuni ta gano kuskurenta ta shaida musu karsu damu Ameenar kawai ta sasanta da Abdul din ita batada matsala saidai matarshi da take basu labarin ita ta like masa har akayi auren,
🙆🙆🙆 YACUCENI 🙆🙆🙆
The Book
of

Please Login or Register in order to submit comment