You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

amma da kyar muka gane gidan, bayan an tabbatarmuna da ya yayi hatsari akan hanyarshi ta dawowa daga kano kuma Allah yayimashi rasuwa tsawon wata uku kenan, nan ummi ta nuna ni a matsayin 'Yarsa da suka haihafa ita kuwa a matsayin matar sa, nan take hayaniya tatashi, nan suka nuna mana matarshi da 'ya'yanshi goma, dukan tsiya suka tashi yimuna Allah yataimake mu,wani k'anen mahaifina yashigo nan take ya gane mu dan kuwa lokacin da aka kai mahaifina a asibiti ya bashi labarin komai sannan ya danka masa takardar sakin da yayiwa mahaifiyata,
Tashin hankali ba,a cewa komai, dukda ni alokacin bawata damuwa ce dani ba sai dai yanda naga ummi na kuka shi yake daga min hankali lalle mahaifina YACUCE ta,
Wannan k"anen mahaifin nawa ne yabamu dubu dari biyu mukara muyi na jirgi dan mukoma k'asar mu,
Sarkar gold din ta tasiyar muka kama hanya,
Ban taba zuwa Cairo ba sai a wannan karo da yake shekara goma kenan rabon ta da can,
Da kyar muka gane gidan k'anen mahaifinta, a yayinda suka yi muna.
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
YACUCENI

The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi
Page 6⃣

A yayinda sukayi muna mugun walak'anci,
Ba irin Hak'urin da ummina bata basu ba amma fur suka k'i karbarmu, a lokacin raina ya bala,in baci bako kad'an ba,
Saida makota suka sa baki aka bamu d'akin da zamu zauna, da yake suma talakawa ne sosai dan haka kowa ci da kanshi yakeyi,
Bayan canjin da muka zo dasu ya k'are Ummi tashiga damuwa domin kuwa dangin nata sun shirya da ita, sai dai ni suke bala,in kyama,

Tunda ta fara Aneesa k'asa take kallo sai yanzu ta dago ta kalleta, cikin mamaki,
Amina tayi murmushin takaici tace,
"Aneesa kina mamaki dan nace suna kyamata ko?
To bakomai ne ya jawomin ba sai launin fata!
Kamar yanda kika ganni bak'a to su ba abun tsana a wurin su kamar bak'in mutum, musamman nida suke tunanin shegiya ce,

Aneesa ta maida kanta k'asa tana mamaki dan kuwa Amina baza,a sata a jerin bakake ba saida masu kama da kopi, sai yanzu ma tak'ara gane cewa tana da zubi da larabawa dan kuwa yanayinta irin nasu ne shiyasa da fari tayi tunanin ko Fulani ce,

Amina tace gaba,
" sak fuskar ummina na biyo, to amma laifi na anan,meyasa nabi fatar k'asa ta,
Bana wasa da 'ya'yansu bana shiga gidajensu,
Dangin Ummi suka dage akan sai tayi aure dan haka, akwai wani tsohon malami da yake sonta akayi musu aure tare,
Wannan bawan Allah shi yataimaka mun nashiga secondary, dukda ba wani hali ne dashi ba, ina aji ukku a secondary a lokacin nafara sanin kaina, mijin mahaifiyata da Ummi sukayi accident!

Innalillahi wa,inna alaihir raji'un,
Aneesa ta fada tare da dafe k'irji,
Amina ta share hawayen da ke a fuskar ta ta kalle Aneesa tayi wani murmushi wanda yafi yak'e da yafi kuka ciwo,
"Ai shi kadai ya mutu saidai Ummi nakasa tayi domin kuwa k'afarta d'aya ta cire,
Tashin hankali ba,asamishi rana, gadon wannan mutumin akaba mahaifiyata, nayi nayi muje asibiti koda kafar roba ce asamata amma Sam tanuna tafi son haka, danginta kowa ba mai wani hali da zai taimaka,
Kullum ni nake hidimar Ummi, makaranta har aka fara karatun aji hud'u nabar zuwa, wata rana, Ummi takirani, take gayamun ya kamata naje k'asar mu Nigeria,
Fur nace ba inda zani dan bansan kowa ba,
Tayi lallaba har ta gaji naki amincewa, aka samu nafara zuwa makaranta, ina ajin k'arshe wata ciwon Ummi ya matsa, gashi ina fama da jarabawar k'arshe,
Ranar da muka k'are jarabawar k'arshe ranar na dawo na tarar da dandazon jama,a abakin layin gidan mu,

Ameena tasa hannayenta ta toshe bakin ta tana wani irin kuka na tuna bakin ciki,
Aneesa ma kukan takeyi,
Ameena ta dago ta kalli Aneesa tace,
" Aneesa Ummina ce,
Ummina nace,"ta k'ara fashewa da kuka,
Aneesa da itama kukan yaci k'arfin ta ta rarrafo izuwa inda Ameena take ta rik'e hannayenta,
Aneesa bata hana Amina kuka ba saida tayi ta k'oshi, sannan taci gaba da cewa,
"Rasuwar Ummina ta hauka tani dan kuwa kad'an ban kuwata ba, saida nazama kamar zautacciya,
Bayan sati d'aya aka tattaro komai na mahaifiyata aka bani, bayan kwana biyu danginta sukayi cuku cuku, suka had'a nawa da nawa suka sani a jirgin Nigeria,
Shekara ta shida rabona da Nigeria gashi bansan kowa ba, dan haka, dana fito daga air port, taxi na Tara dayake naji ance Abuja ne muka sauka,
Ina dauke da makudan kud'i a jikina, damukayi yawo Dan taxi ya gaji ya ajiyeni,
Gashi magrib ta doso,
Wani gefen gida nasamu na tsaya anan ina famar kuka,
Wani matashin yaro yazo akan babur da alama gidansu ne har ya wuce sai kuma ya dawo,

Aneesa tace,
" Allah yasa ya taimake ki Anty,"
Ameena tayi dariya tace,
"Daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki?"
Suka yi dariya duka.
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
YACUCENI

The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi
Page 7⃣

Amina Omar zamau,
Na gaishe ki Antyna Maman Deedat da Eman,

Allah yabar muna ke😘ko Dan amalekum😂

Amina cikin murmushi taci gaba da cewa,
"Wannan bawan Allah ya tambayeni meyafaru dani nake kuka dole na yasa na fad'a mishi tafiya nayi daga Cairo kuma bansan inda zaki a yanzu ba,
shi yashiga dani gidan su, saidai hankali na ya tashi ganin ba kowa a gidan,
Wani d'aki yakai ni nayi wanka nashirya, sannan na kwaso kaya na nafito lokacin har an k'are sallar isha,
A falo na hadu dashi, rik'e da take away na abinci yabani naci,
Nan yake gayamun ba kowa agidan iyayenshi sunyi tafiya, ya tambayeni labari na, ban boye mishi komai ba, ganin shi yaro ne sa,a ta ko zai girmeni saida shekara d'aya,
Anan gidan na kwana sai da safe nace zan tafi, yayi yayi na zauna har iyayenshi su dawo nace a,a,
Ya shaidamun shi a kano yake karatu yanzu sune zasu shiga level na biyu,
Gashi gobe zai koma,
Jin ya ambaci kano yasa nace nima kano zanje a can zan zaun,
A gidan su na zauna har tsawon kwana biyu sannan muka shirya muka wuce kano,
Yaro k'arami yaro mai kirki yaro kyakkyawa,
Abdul Hameed kenan,
Dakin haya yakama mun a wani gida na 'yan makaranta, yayinda yayi alk'awarin taimakamun, haka yace idan wata shekara ta zagayo zai sani a jami,ar bayaro,
Ci da sha sutura ta duk shine dauke dasu, duk ranar da baida karatu a makaranta, anan gidan mu yake zuwa muyi hira sosai,
Duk duniya banda kamar Abdul Hameed alokacin,
Idan gidansu aka bashi kud'i na siyen abinci, zai raba biyu yabani koda bazasu isheshi ba,
Saidai abinda na hanga shine Abdul ba tausayi na kawai yakeyi ba harda so na yafara, Wanda kuwa nikuma alokacin banida buri irin naga nakasance wata, ni a rayuwa banida burin da ya wuce nayi kud'i, dan haka sam soyayya bata gabana,
Wata na biyar ina zama da Abdul abu yaci tura domin kuwa ya shaidamun Yana sona kuma aure na yake so yayi kafin wata shekara, dayaje wa iyayenshi da maganar aure ba irin bala,in da mahaifiyarshi batayi mishi ba, alokacin yanada shekara a shirin,
Ni kaina nasan tashin balaga ne kawai yake damun sa,
Wani irin masifar sona Abdul yakeyi, amma ni banji koda wasa zan iya auren shi ba,Dan kuwa ba shida kudin da zai rik'e mu,
Koda munyi auren karkashin iyayenshi zamu zauna wanda nikuma a rayuwa ta tagaba banji zan iya zama akarkashin kulawar wani ba,

Ameen takaalli Aneesa tace
"Aneesa while some gals a searching for a rich husband to ni gaba d'aya I'm focusing of being a rich wife,
Iyayen Abdul ganin zaiyi hauka tuburan, shiyasa suka amince masa da ya kawo wadda yake so, zasu aura mishi tunda ko karatun ya ajiye gefe, cikin farin ciki ya gayamun, nan da wata d'aya yake so muyi aure,saida ya k'are surutun sa natashi na juya mishi baya, nan da nan hankali sa yatashi,
Abdul bazan aure kaba,abinda nafada masa, juyin duniya yayi, nace bazan aure shi ba,
Ke in tak'aice miki saida ya kwanta asibiti sabida tsananin bugawar da zuciyar sa takeyi,
Iyayenshi sun rok'eni da na aure shi komai nake so zasu bani,
Ganin da gaske Abdul zai iya rasa ranshi yasa na amince zan aureahi,bayan yasami sauqi Dan haka nikuma nace mishi zanje Cairo nasanar da 'yan uwan mahaifiyata, baiso hakan ba yaso ya fadawa iyayenshi gaskiya amma na hana,
Ya
yi yayi muje tare, nace yabari sati d'aya zanyi kawai kuma ai zamu dinga yin waya,
Kafin na wuce saida na nuna masa ina sonshi kamar yadda yake sona,
Kud'i na tin na gadon mahaifiya ta ko kwandala ban taba ba, ga tarin kudin da nake samu a wurin Abdul, na had'a su duka na rik'e, koda naje wurin dangin

Amina cikin murmushi taci gaba da cewa,
"Wannan bawan Allah yazo ya tambayeni ko lafiya nake kuka anan, ganin idan bashi ba ba Wanda yanemi yaji meyafaru dani yasa na gayamishi ni bakuwa ce kuma bansan inda zanje ba,
shi yashiga dani gidan su, saidai hankali na ya tashi ganin ba kowa a gidan,
Wani d'aki yakai ni nayi wanka nashirya, sannan na kwaso kaya na nafito lokacin har an k'are sallar isha,
A falo na hadu dashi, rik'e da take away na abinci yabani naci,
Nan yake gayamun ba kowa agidan iyayenshi sunyi tafiya, ya tambayeni labari na, ban boye mishi komai ba, ganin shi yaro ne sa,a ta ko zai girmeni saida shekara d'aya,
Anan gidan na kwana sai da safe nace zan tafi, yayi yayi na zauna har iyayenshi su dawo nace a,a,
Ya shaidamun shi a kano yake karatu yanzu sune zasu shiga level na biyu,
Gashi gobe zai koma,
Jin ya ambaci kano yasa nace nima kano zanje a can zan zaun,
A gidan su na zauna har tsawon kwana biyu sannan muka shirya muka wuce kano,
Yaro k'arami yaro mai kirki yaro kyakkyawa,
Abdul Hameed kenan,
Dakin haya yakama mun a wani gida na 'yan makaranta, yayinda yayi alk'awarin taimakamun, haka yace idan wata shekara ta zagayo zai sani a jami,ar bayaro,
Ci da sha sutura ta duk shine dauke dasu, duk ranar da baida karatu a makaranta, anan gidan mu yake zuwa muyi hira sosai,
Duk duniya banda kamar Abdul Hameed alokacin,
Idan gidansu aka bashi kud'i na siyen abinci, zai raba biyu yabani koda bazasu isheshi ba,
Saidai abinda na hanga shine Abdul ba tausayi na kawai yakeyi ba harda so na yafara, Wanda kuwa nikuma alokacin banida buri irin naga nakasance wata, ni a rayuwa banida burin da ya wuce nayi kud'i, dan haka sam soyayya bata gabana,
Wata na biyar ina zama da Abdul abu yaci tura domin kuwa ya shaidamun Yana sona kuma aure na yake so yayi kafin wata shekara, dayaje wa iyayenshi da maganar aure ba irin bala,in da mahaifiyarshi batayi mishi ba, alokacin yanada shekara a shirin,
Ni kaina nasan tashin balaga ne kawai yake damun sa,
Wani irin masifar sona Abdul yakeyi, amma ni banji koda wasa zan iya auren shi ba,Dan kuwa ba shida kudin da zai rik'e mu,
Koda munyi auren karkashin iyayenshi zamu zauna wanda nikuma a rayuwa ta tagaba banji zan iya zama akarkashin kulawar wani ba,

Ameen takaalli Aneesa tace
"Aneesa while some gals a searching for a rich husband to ni gaba d'aya I'm focusing of being a rich wife,
Iyayen Abdul ganin zaiyi hauka tuburan, shiyasa suka amince masa da ya kawo wadda yake so, zasu aura mishi tunda ko karatun ya ajiye gefe, cikin farin ciki ya gayamun, nan da wata d'aya yake so muyi aure,saida ya k'are surutun sa natashi na juya mishi baya, nan da nan hankali sa yatashi,
Abdul bazan aure kaba,abinda nafada masa, juyin duniya yayi, nace bazan aure shi ba,
Ke in tak'aice miki saida ya kwanta asibiti sabida tsananin bugawar da zuciyar sa takeyi,
Iyayenshi sun rok'eni da na aure shi komai nake so zasu bani,
Ganin da gaske Abdul zai iya rasa ranshi yasa na amince zan aureahi,bayan yasami sauqi Dan haka nikuma nace mishi zanje Cairo nasanar da 'yan uwan mahaifiyata, baiso hakan ba yaso ya fadawa iyayenshi gaskiya amma na hana,
Yayi yayi muje tare, nace yabari sati d'aya zanyi kawai kuma ai zamu dinga yin waya,
Kafin na wuce saida na nuna masa ina sonshi kamar yadda yake sona,
Kud'i na tin na gadon mahaifiya ta ko kwandala ban taba ba, ga tarin kudin da nake samu a wurin Abdul, na had'a su duka na rik'e, koda naje wurin dangin mahaifiya ta kakana ya rasu wato k'anen mahaifin Ummi matarshi ce kawai anan,
A wurin ta na zauna, ganin ina da kud'i yasa bawani walak'anci da ake mun,
Kwana na biyu ina shawara akan nakoma Nigeria ko kar na koma,
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
YACUCENI

The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi
Page 8⃣

Nafeesat Ankerh Fans,
It's Mss MJAY fans
Anee Luv, Ayman Fans
Rookie Sadau Fan's.

Na gaisheku shi isa nabaku wannan page,
Allah yabar kauna tsakaninmu da ku,
Au kunga na manta da nawa Fan's🙈
Love u all Guy's😘

Aneesa ta kalli Ameena tace,
"Kai Anty Allah yasa dai kin dawo Nigeria, dan kuwa samun mai sonki kamar Abdul sai an tona,"
Ameena tayi yake tace,
"Aneesa ai kaddara tariga fata, dukda nasan Abdul ya soni,kuma nima alokacin ba zance bana son shi ba saidai nafi fita burina akan sonshi,"
Aneesa tace,
"Anty a rayuwa ai ba,ason dogon buri dan kuwa yana kai mutum a ma halaka,
Dashi kika aura da zaifi burinki,
Toh amma Waye mahaifin,Jayyid da Jeedda?"
"Yawwa kin zo tambayar da nake so,
Ahmad ibn jawwa, shine mahaifin Jeedda da Jayyid,
Bayan Ummi na da Abdul ba Wanda yasoni a duniya kamar shi,
Balaraben k'asar Sudan ne,
Ahmad mazaunin kasashe ukku, Saudiya, Sudan Cairo,
Sana,arsa shine saida gwala gwalai,saidai kash mashayine matuka,
dangin mahaifiya ta ganin har nasamu mai sona basu San asalinshi ba suka daura min aure dashi amma kuma da amincewa ta,
domin kuwa ya shaidamun zai barni nayi karatu, koma me nake so,
Ba laifi yana sona, a Sudan yamaidani, alokacin na fahimci cewa shi mai kud'i ne sosai amma kuma bashida dangi ko yan uwa,
African university nashiga, ina aji daya nayi haihuwar fari,
Wato Jeedda,
Business nakaran ta, shekar da na k'are na haifi Jayyid,
Ahmad shaye shayenshi sai karuwa yakeyi,duk wani abu da yamallaka yana hannu na har ya kasance ina shige da fice a harkar kasuwancinsa,
Jayyid yanada wata bakwai,Allah yayiwa mahaifin su rasuwa,
Yabar tarin dukiya mai yawa,
Gashi ba wani nashi dan haka nida 'ya ya na mukaci gadonshi, naci gaba da tafiya da kasuwanci sa,
A haka na tattara na dawo Nigeria,
Buri na yacika nazama hamshakiyar mai kud'i dan kuwa samun Irina 'yar talakawa mai shekara talatin da dukiyar irin haka abu ne mai wuya,
Saidai wani da baki sani ba shine har yanzun
maki, ina dauke da wani kurji a zuciya ba komai bane kuma face son Abdul,"
Aneesa tayi ajiyar zuciya tace
"Lalle Anty kinga rayuwa, toh amma tunda ga lokacin baki kara samun labarin Abdul ba?"

Amina tayi dariya tace,
"Abdul kuma ina zan samu labarin sa,nida na guje shi?
Saidai ko mutuwa aka cemun yayi ba zanyi musu ba dan nasan irin kurciyarsa.
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆 YACUCENI

The book
Of
Queen Mermue

©

HIKIMA writer's
Association.

Edit by
ANaM Dorayi

9⃣

"Aneesa tun lokacin da Abdul ya rakani a filin jirgi har yanzu ina tuna kalmar sa ta k'arshe a gareni,cewa duk rintsi zan jira dawowarki,koda kowa zanyi jira izuwa karshen rayuwa ta,"
Ameena ta saki wani wani murmushi,
Kana ta kalle Aneesa,
Aneesa tace,
"Kai Anty meyasa da kika dawo baki nemeshi ba, tinda kinsan gidan su a Abuja wata k'ila har yanzu yana jiranki,"
"Aneesa kenan, kin manta wannan abun da yafaru shekara goma kenan da faruwar sa?, nasani ko da Abdul zaiyi aure zai jirani kuma yanzu ne Daidai lokacin da ya dace na nemeshi domin kuwa duk wani buri nawa yacika saura d'aya, shine Hameed,"
Aneesa ta girgiza kai tace,
"A ganina da tun lokacin da kika dawo Nigeria kika nemeshi da yanzu bakida damuwa,"
"Bazan nemeshi ba alokacin domin kuwa alokacin ban kai matsayin da buga k'irji naja da duk wani mai tak'ama da kud'i na Nigeria ba, amma yanzu ba Nigeria ba har kewayenta zan iya fafatawa,"
Aneesa ta numfasa kana tace,
"Nikam Anty inaga soyayya tafi kud'i, ko wani buri,danice nasamu wannan dama taki da soyayyar zan dauka nabar duk wani buri nawa,"
Amina tayi murmushi tace,
"Yanzu dai gashi ana kiran magrib dan haka tashi mu shiga daga ciki in yaso idan mukayi salla sai kibani labarin ki, tinda kinji nawa,"
Aneesa ta mik'e,
Suka fita tare,
Lalle Ameena taga rayuwa, nanda nan taji soyayyar Ameena har acikin zuciyar ta,
Haka yakasance a wurin Ameena dukda bataji labarin Aneesa ba, yarinyar ta kwanta mata ita yarinya ta farko da tajita kamar k'anwar ta ta jini,
Bayan da mukayi salla,
Har sama Ameena tasa aka kaini, tagayyaceni cin abincin dare,
Wani dinning Area ne, wanda acikin dakin akwai na,urori da litattafai, da alama tana zama da 'ya'yanta anan su yi karatu,
Bayan mun k'ara gaisawa na zauna a d'aya daga cikin kujerin a kusa da Jeedda wadda ke ta famar gardama da Jayyid,
Ameena tayi gyaran murya ta kalli yaran nata tace,
"Habibi Habibati, let pray an remain quite, let's start d dinner,"
Nan da nan yaran suka natsu, akayi addu,a kana su fara cin abinci,
Ameena ta juyo ta kalleni ganin ni ban fara ba tace,
"Yadai Aneesa bismilla mana,"
Na kalleta nace,
"Am zan wanke hannu na,"
Tayi murmushi tace,
"Au bakya cin abinci da spoon ne, naga ba tuwo bane,"
"Eh bana iya rik'a spoon da hannun dama sai a hagu kuma kinga ba kyau cin abinci da hannun hagu,"
Tayi dariya tace,
"Oh lalle to ga fanfo can kije ki wanke,
A hankali naje na wanko na dawo,
Bayan na bud'e farantin dake gabana,
Sai nayi kicibis da abinda bana iya ci, wato wake aciki,
Shinkafa ce shaleliya dahuwar jelop tasha wake da kifi aciki,
Rufe farantin nayi na ture daga gabana,
Ameena ta tsaida cin abincin da take, tace,
" idan bai miki ba ga birabisko nan sai kici,
Ko shinkafarce bakyaci?"
"A,a dama ni bana cin wake shiyasa kuma naga ansa aciki,"
"Hakane nikam kinga ina son wake, haka ma Ummi na da Abba gidan mu muna yawan cinsa,"
Nan dai na jawo birabisko da miyar hanta na fara ci,
Bayan mun kammala ne,
Jayyid da Jeedda da gaba d'aya masu hidimar gidan suka wuce lecture din da ake masu,
Nikuma muka koma a falo domin cigaba da labarin mu,
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆
YACUCENI

The Book
of
Queen Mermue

©

HIKIMA Writters
Association

Edit by
ANaM Dorayi
Page 1⃣2⃣

Gaskiya Fans dina inajin dadin yadda kuke supporting dina,
Hakan zai bani kwarin guiwa, nagode sosai Allah yabar zumunci,
U guyz u are so amazing
Love you All😘😘

Saida nayi fushi da Baba na tsawon sati d'aya amma yafita batuna,
Domin kuwa yasan duk shirin iro ne,
Da dai muka gaji yasharemu, dole nacewa Iro da muhakura kawai idan yaso in natashi aure sai nabashi dukiyar ya juya muna,
Akan haka ranar ya yimun dukan jaki,saida na gaza tashi,
Da Baba yadawo yaga fuska ta a kumbure da ya tambayeni sai nace a makaranta mukayi laifi,
Kusan sati ina rok'on Iro da yayi Hak'uri sannan ya Hak'ura ya daina fushi dani,
Bamu Dade da k'are jarabawar k'arshe ba ciwon Baba yatashi sosai akan haka ya matsamun da sai na fitar da miji,
Da iro yaji labari sai yasameni, yacemun mai zai hana nacewa Baba shi nake so tunda yafi kowa sanin asalina yafi kowa iya zama dani,
Dukda akwai wani Jameel dayake nacin sona kuma ni naso na aura amma sai nakasa yiwa Iro musu,
Baba akwance baida lafiya fur yaki yarda da cewa Iro zan aura,
Da kyar ya yarda, da yaga muna shirin guduwa,
Bayan Baba yabar wasicci a masallaci ranar jum,a yana so a aura auremu,
Acikin satin Allah yayiwa Baba rasuwa,

Aneesa ta share hawayen takaici daga fuskar ta taci gaba da cewa,
Nayi kuka har nafitar arziki, banida kowa kenan da ya wuce Iro,
Dan haka nak'ara jin kaunarsa, kudin sadaki dubu goma Iro bashi da su ni nadauka acikin kud'i na na bashi,
Haka ya lallabani ya karbi kud'i dayawa a hannuna har yagama

Please Login or Register in order to submit comment