You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi

Page1⃣9⃣

Tsaye nake bakin titi na taso daga makaranta, taxi nake jira sabida yau direban su Jayyid Anty ta aike shi kebbi dan bisa al'ada shine yake kaini ya dakkoni, kusan mintuna talatin ina jiran taxi ban samuba akan yasa nafara takawa a k'asa, inna shirin tsallaka titi wata mota bak'a ta tsaya kusa dani,
Sauke gilashin motar akayi a hankali wanda yayi sanadiyar fad'uwar gaba na,
"Bawan Allah"
Na fad'a tare da sakin wani murmushi, najin dad'i
Shima murmushin yayi tare da cewa,
"Humm malama Aneesa, dama da rabon ganin ki,"
Ya bud'e kofar motar,
"Shigo daga ciki kin ga bakin hanya ne ko wani kike jira?"
Girgiza kai nayi ba musu nashiga dan ninasan waye bawan Allah,
Mungaisa sosai saida yafara tafiya kana ya kalleni yayi murmushin da yake tadamun da kurjin da yake kasan zuciyata, a duk lokacin da natina dashi nakan shiga damuwa domin kuwa yakasan ce kaikayin haushi Wanda bazan iya sosawa ba.
"Aneesa manya yanzu dai kingama idda kenan tunda naga kin goge kinyi kyau haka,"
dariya nayi nace,
"Eh! Harma nasamu admission nafara zuwa makaranta,"
"Ikon Allah yanzu ina kike da zama,?"
"Anan GRA a gidan wata Antyna, ita tadaukeni tin daga lokacin da nabar asibitin, bayan iro ya koranine ta kadeni da mota shine har yanzu nake zaune da ita,"
Bawan Allah ya dan bata fuska yace,
"Ai Iro anyi shegen namiji wai me zai hana a had'a shi da hukuma?"
"Hmm hukuma shine zai hadu da ubangiji ni ba wani Abu da nake buk'ata daga wurinsa yanzu,"
"Hakane kuma Allah zaimiki sakayya, bari na ajeki a gidan sai naga gidan nima,"
Kafin nabashi amsa wayata tadau ruri,
Antyce, a hankali na daga wayar tare dayin sallama,
"Am Aneesa idan kin taso daga makaranta ki biyo tanan gidan Hajiya Falmi sai muwuce tare dan ina gidan,"
"To ganinan zuwa"
Na katse wayar, bawan Allah na kalla wanda tin lokacin da na fara waya ya maida hankalin shi kan tukin da yakeyi, dan haka nayi mashi bayanin gidan Hajiya Falmi, har muka isa munata hira, nayi mamaki sosai ganin har mun rabu bai yimin maganar dalilin da yasani tafiya ta batare da yasani ba.
Bayan yasaukeni ya karbi number wayana mukayi sallama cikin nishad'i nashiga ciki.
Saida mukayi magrib a gidan muka fito. Anty na tukin motar ta kalleni tace, "My Anee bani labari dan tinda kika shigo naga kina ta fara'a ko an samamin suruki ne?" Tana maganar dauke da dariya a fusakarta, nima dariyar nayi,
"Kai Anty bakida magana sai suriki ai sai kinyi aure sannan nima zanyi,"
"Anee kenan nima ai na kusa nayi auren dan haka fai naji."
Kara gyara zama nayi a motar
"Anty yau na hadu da Bawan Allah,"
Ameena ta juyo tare da bud'e ido, hakan yasa nasa hannuwana na rufe fuskata ina dariya,
"Anee da gaske? kinji dad'in da naji kuwa?"
"Wallahi Anty shima ya saukeni a gidan Hajja Falmi,"
"Amma naji dad'in hakan insha Allah abinda muke fata zai faru hop kin bashi number wayarki, nima yanzu nasamu labari mai dad'i a wurin Falmi, ansamamin addireshin Abdul a wurin tsohon mai gadinsu na Abuja,"
Harda wani ihun dad'i nasaka,
"Kai Anty mezai hana muje yanzu?"
Ta kalleni da harara,
"To idan munje kice me?"
"Au kice kece Amina wadda yayiwa alk'awarin aurenki komai rintsi ko mai tsawon lokaci,"
tayi dariya,
"Ai Aneesa abu a sannu ake binshi nafison nafara samun labarinshi kafin na jemishi dukda nasan bazan samu matsala a wurinshi ba saida ko mahaifan,"
"Hakane Anty to Allah yasa alkhairi,"
" Ameen 'yar kanwata matar bawan Allah insha Allah, "
Haka muka cigaba da hira har muka isa gida cike da farin ciki.
Bawan Allah yakasa barci sai yawo da yakeyi a d'akin, tabbas bazai bar wannan damar ta wuce shiba, dan yanzu ne daidai lokacin da yadace yajewa Aneesa da buk'atar shi. Juyowa yayi ya kalli matarshi Baseera,
Ita kadai ce matsalar shi, duk da yana jin sonta a yanzu amma son da yakeyiwa Aneesa na dabanne dan shi kanshi baisan lokacin da yakamu da sonta hakaba, bai taba yiwa wata 'ya mace a duniya irinsa ba.
Yau kwana ukku kenan da haduwarsu da Aneesa amma kullum yana kiranta fiye da sau biyar, yau kam dakewa yayi yanemi ganin ta, tayi mishi kwatancen gidan yagane,
Da yake Ameena tayi tafiya zuwa Dubai hakan yasa na kirata nasanar da ita.
Bayan isha yakirani ya shaidamun ya iso gidan.
Cikin wata dakakkiyar shadda yake yayi kyau sosai sai k'amshi dadadan turare yakeyi.
Bayan mungaisa sosai ya kalleni tsawon mintuna baice komai ba daga bisani yafara da,
"Aneesa tsawon wata bakwai kenan kullum kina raina, a kullum ina rokon Allah da had'a ni dake naji ko wani laifin nayi maki kika gujeni a daidai lokacin da zuciya ta take da buk'atar taimaka miki, hankalina yatashi sosai lokacin da Abdul yajemin da zance ya nemeki ya rasa, har Asibitin muka koma, amma bake ba labarinki, wani tashin hankali shine tafiyarki ta haddasamin wani sabon al'amari, dukda tin lokacin da nafara ganinki acikin mawuyacin hali nake jin so da kaunarki amma hakan baisa nasanar dake ba kasancewar nasan kina cikin idda, tsawon kwanakin da kikaga nadaina zuwa asibitin abinne yaci karfina domin kuwa shed'an yana ingiza zuciyata da nasar dake wanda nasan hakan zan haramta ma kainake."
Yadan ja numfashi tare ajiyar zuciya, sannan yacigaba da cewa, "Aneesa ina kaunarki ina sonki fiye da yadda nazata zan soki, ina fatan wani bai riganiba ataimaka a karbi kokon barata......
Pls fellow this link to like my face book page
https://www.facebook.com/Queen-Mermue-Novels-Fans-436431613362583/
🙆🙆🙆YACUCENI🙆🙆🙆

The book
Of

Queen Mermue



Dago kai nayi na kalleshi zuciya ta tana dukan uku uku,
Kodai yasan ina sonshi ne?
Tambayar da nayiwa zuciya ta kafin nak'ara cewa komai yaci gaba da cewa,
"Aneesa tsakanina da ke ba wani boye boye, bazan tilastaki ba idan kinji bazaki iyaba amma kisani zuciya ta takamu da cutar kaunarki fiye da yadda zata warku,
Aneesa ni ba k'aramin yaro bane da zance bansan meyeso ba ina da mata shekarar mu shida da aure kenen Allah bai bata haihuwa ba dukda yar uwa tace ta gefen mahaifina auren hadi akayi muna kuma muna zaune lafiya mahaifiya tana matuk'ar son na kara aure ko Allah zaisa adace, "
Ya juyo ya kalleni da fuskar tasauyi,
"Aneesa kitaimaka mun kar kice bakya sona,"
Hankali na atashe ga samu ga rashi,
Domin kuwa abu mai wuyane iyayensa su amince da aurena,
Kamar yasan abinda nake tunani a zuciya ta katse ni da,
"Aneesa iyayena bazasu hanani auren ki ba koda kowa ke kika fi kowa rashin asali, sunada ilmi sosai basa hana mutum yin abinda yake so matuk'ar bai sabawa addini ba, dan haka kada kikawo wannan tunani a zuciyar ki,"
Cikin sanyi jiki na bud'e baki na dakyar nace,
"Babu komai nagode sosae amma yanzu bazan baka amsa ba har sai Anty Ameena ta dawo idan na gayamata komai muka yanke shawara zakaji,"
Ya kalleni tare da kanne ido,
"Pls ataimaka Bawan Allah kar agujeshi,"
Murmushi nayi muka dan tab'a hira daga nan mukayi sallama nashiga ciki,
Ko baccin kirki banyi a yau ba sai faman juyi da nakeyi akan gado ganin al,amarin nakeyi kamar a mafalki,
Allah maji rokon bawa,
Allah yasa Bawan Allah ne zai sheremin kuka na,
Da safe jirginsu Anty ya iso bayanTa huta ne takirani a d'akin ta,
Nan nashaida mata yanda mukayi da Bawan Allah, harda rawa ta tashi ta taka sai faman murna takeyi,

"Anee Allah yana karbar addu,ar bayi a wani gefe ta inda bazasu yi tsammaniba,
Kamar yadda nake gaya miki matsalar da zan samu a wurin Abdul itace mahaifiyar shi,insha Allah yanzu zan kauda wannan matsala,"
"Da gaske Anty? Tayaya?"
"Wani kamfani ne mahaifiyarshi ta bud'e Wanda muka saka hannun jari na kaso hamsin aciki dani da Hajja Fati matar gwamna, yayinda kaso a talatin da biyar na sauran mutane ita kuma tanada kaso goma shabiyar aciki,
Amma kamfanin a karkashinta yake
Tafiyar da kikaga nayi tare da matar gwamna muka je domin duk akan maganar ne, idan muka cire kason mu a ciki kamfanin bazai je ko,ina ba zai durkushe,
Hajiya Zaino wato mahaifiyar Abdul tasan ni tin alokacin da Abdul yayi zama a asibiti amma yanzu da muka hud'u Sam bata ganeni ba,sai mamaki ma tayi a lokacin da taji cewa nice Turab ita a tunanita ni babbar mace ce,yanda take jin sunana,
Yanzun nasamu hanyar kusanci da ita kuma nasan zan samu me nake buk'ata gobe zamu hadu da Abdul,
Tsawon shekara goma kenan ban sashi a idona ba,"
Anee tayi ajiyar zuciya tace
"Allah yasa alkhairi Anty,"
"Ameen my Anee, yanzu ki fad'a wa Bawan Allah kin amince zaki aureshi amma zai barki kici gaba da karatu Dan bazan yarda ya hanaki karatu ba,"
"Toh Anty bari na kirashi tin dazu naga call dinshi,"
"Toh jeki, amm kicewa kande tazo ina son ganinta,"
"Toh"
Daga haka tafice bayan ta she dawa kande kiran Anty ta wuce d'akin ta ta soma neman layinshi,
Yaji dad'i sosai da tasanar dashi ta amince cikin murna ya kira Mumyn shi yasanar da ita tare da Anty kultum babbar yayarsu,
Dukan su sunsan da zancen Aneesa dan haka suma sunyi murna sosai ba kamar Mumy da tayi tasamishi albarka,

Abdul yana zaune a office dinshi ya jingina bayanshi asaman kujerar da yake zaune akanta tare da runtse idanunshi yana jiran shigowar bakuwar da sakatariyarshi tasanar dashi yayi,
Sallamar da tayi ne yasashi bud'e idanunshi tare da karba sallamar,
Ras! Gabanshi ya fadi,
Ganin matar da ko zai shekara dubu bai gan taba bazai manta da fuskar ta ba,
Murmushi Ameena Abi Turab tayi tare da zauna akan d'ayar kujerar dake a gaban teburin,
"Sannu Abdul ko baka ganeni ba?"
Gyara zaman shi yayi tare da maida mata murmushin da tayi,
"Naganeki mana dama zan manta dake ne?"
"Toh ai naga shekaru sunja nadauka ko kamanta ni dukda nasa bakada mantuwa,"
"Lallai kam kinsan da haka,
To yakike ya gida"
"Alhamdulillahi sai godiya,"
"Yaushe aka shigo k'asar ne?"
"Hmm ai najima a k'asar sai da ban sameka ba har abujan naje akace kuntashi,"
"Hakane Ameena mun jima da barin gidan da yake yanzu ma anan kano ni nake zaune,"
"Masha Allah ya iyali ko kana nufin bakayi auren ba?"
Dariya yayi kana yace,
"Nayi aure mana kema ba kinyi ba"
"Waya gaya maka nayi aure ne,"
Tafada tare da juya ido,
"Ameena ai nasan ba zaki zauna har yanzu ace bakiyi aure ba,"
"Hakane kam nayi harda 'ya'ya biyu,"
"Masha Allah, Allah yarasu to ya Baban su anan Nigeria kenan,"
Murmushi tayi kana tace
"Baban su yarasu shekara tin da jimawa bayan rasuwarshi ne nadawo anan Nigeria,"
"Eyyah Allah ya gafarta,"
"Ameen"
Haka dai suka tab'a daga bisani ta karbi number wayar shi ta wuce,
Yanzu kam hakan ta zai cimma ruwa dan tuni Hajja Aisha wato Matar gwamna ta k'enkesawa Hajiya zaino labarin wacece Amina Turab, tsaf Hajiya zaino ta tuna ta dan tasan irin sonda dan nata yayiwa matar hakan yasashi zama kamar wani tababbe,
Da farko Sam kin yarda tayi Aisha ta nuna mata Kamfanin da take takama dashifa sune rik'e dashi, dan haka tuni ta gano kuskurenta ta shaida musu karsu damu Ameenar kawai ta sasanta da Abdul din ita batada matsala saidai matarshi da take basu labarin ita ta like masa har akayi auren,
🙆🙆🙆 YACUCENI 🙆🙆🙆
The Book
of
Queen Mermue

©
Hikima Writters
Assotiation

Edit by
ANaM Dorayi

Page2⃣1⃣
👑Queen MERMUE👑
wish to use dis opportunity to Thanks all dos wished gud to me u r really amazing😍
Wollah mugun sonku nakeyi😘


💃Awesome feeling when someone is making an effort to make you smile.☺😍

I'm so glad wit u ppls
thanks for all ur gud wishes to me u really make me to enjoyed my day❤💃😘




K'arfe takwas na dare lokacin sun kammala cin abinci dare suna zaune a falo, Ameena ta kalli Aneesa tace,
"Aneesa kin gayama Bawan Allah yanda mukayi kuwa,"?
Aneesa tayi murmushi tace,
" Anty yayi murna sosai yace kuma makarantar tawa ba matsala yanzu ma so yake ya ganki nace ya barshi har weekend sai yazo,"
Ameena wadda tin fara zancen Anee take murmushi tace,
"Oh Aneesa kinyi zurfi acikin son wannan mutumin wai to dashi da iro wakikafi jin sonshi a ranki?"
Yanzu kam fuskar Anee ta canja daga murmushin da yake shimfede fuskar ta zuwa alamun damuwa..
"Anty Iro daban yake a rayuwata, zanfi tsammanin shakuwa dashi shine kaso mafi yawa fiye da son da nake mashi, sabanin Bawan Allah da nan take zuciyata ta kamu da sonshi, yanzun ma da yanuna yana sona sai nake tausaya ma kaina kar azo asamu sabani, dan kuwa inajin bazan iya jure rashin sa a rayuwa taba, Anty ni inada raunin zuciya a fagen so nanda nan na kamu da son mutum rabakuwa yakanyimin wahala, Anty wallahi ina son Bawan Allah sosai shine wanda nake ganin zai share min kukan masoyi yayinda ke kuma kika share min kukan mahaifiya."
Tini idanun Aneesa sun kawo ruwa,
Ameena ma cikin alamun tausayi tace,
"Aneesa insha Allah babu abinda zai rabaki da Bawan Allah, ni zan zamemiki dangi zan zamemiki kowa ke koda k'arfin iko ko da k'arfin dukiya ne sai kin auri Bawan Allah wannan alk'awarine da zancika miki muddin ina numfashi a doron k'asa,"
Cikin jin dadi Anee ta taso ta rungume Ameena yayinda Ameena tashiga sharemata hawayen da suka wanke fuskar ta,
Ameena ta kalli Aneesa tace,
" gobe zamuyi bakuwa zatayi sati d'aya anan idan kin sauka k'asa ki cewa kande ta gyara d'akin daie kusa da naki,sannan kicewa saura ashirya abincin baki,"
"Toh Anty"
"Bari nashiga daga ciki zamuyi waya da Abdul zanji yadda zancen mu ya kwana,"
Anee tayi dariya tace
"Anty ko shine tafe a goben?"
"A,a wani ne zaizo tare da k'anwar shi wai ta matsa mishi tana son ta ganni, shine yayanta zai kawo ta wurina anan yake aiki amma dan Kaduna ne, shine Abbakar dinda kikaji muna maganar shi da Falmi,"
"Ohk shine wanda yake sonki, kai gaskiya Antyta matar Abdul ce insha Allah,"
Ameena ta mike tsaye tana dariya tace,
"Allah yasa,"
"Ameen" tace kana ta bi hanyar fita daga benen anan taci karo dasu Jayyid sun dawo daga d'akin kallo,
"Kai Anty Anee baki zoba har mun k'arasa kallon bakiga yanda aka kashe boss din ba,"
Jayyid ne mai maganar
Jeedda ta lakuce masa hanci,
"Toh bai mayi kyauba shirme kawai,"
"Oh Jeedda ina ruwanki zakice baiyi kyau ba ,? Jayyid dina bari gobe ma zasu maimaita sai na kalla, ke kuma Jeedda sai nasa an miki repeating kin dawo jss 1 kiyi ta zama har Jayyid ya sameki,"
Ai nan take ya dau tsalle yana murna, sai da yakai bakin k'ofa yayi wa Jeedda gwalo,
"Woo naje nagawa Habeebaty".....

Pls fellow this link to like my face book page
https://www.facebook.com/Queen-Mermue-Novels-Fans-436431613362583/
22
My lovly Fans Ina matuk'ar jin dad'in yadda kukemin uzurin kasancewar bakwa samun yadda yakamata, ina yawan jin korafe korafenku, ina mai Dada baku hakuri harwa yau ku kasance masu yawan YAKANA! Insha Allah zan qara qoqari, nagode muke, 😍😘


Saida wayar tayi kara tayi k'ugi har ta gaji kamar baza,a daga wayar ba can kuma sai aka d'aga,
Abin har yaso yabawa Ameena haushi amma ganin ya daga wayar yasa tadawo dai dai,
Sallama tayi acikin kalar muryarta ta larabawa, wanda jin muryar kawai yasa yagano mai magana,
Cikin fara,a ya amsa sallamar, kana yace,
"Manyan mata masu Nigeria,"
Cikin sanyin murya wadda tuni wata guguwar son shi taqara qaruwa a zuciyar ta,
"Hmm Abdul kenan, mune manya ko kuma ku,
Ya gajiya ya 'ya'yana,"
"Lafiya kalau muke,"
Bayan doguwar gaisuwar da sukayi sai kuma shiru ya biyo baya kamar bazata dago zancen ba can taja doguwar ajiyar zuciya tace,
"Abdul ya zancen mu ya kwana duk da nasan ni mai dinbin laifice a wurin ka amma nasan kai mai Hak'uri ne da rik'on alk'awari, ina ce baka manta alk'awarin da kayimun ba,"
Ajiyar zuciya yayi yayinda wani haushi ya tokare makoshin sa, can ya daure yace,
"Eh Ameena ban manta da alk'awarin da nayi maki ba, amma ki sani na riga da nayi aure a yanzu kuma ina son mata ta haka kuma idan nace zan aureki a yanzu ba k'aramar fama zansha a wurin iyayena da can nayi doguwar jayyaya dasu ne abisa kuskure da kurciya amma yanzu ki sani ba abinda zai sa nak'ara wani tashin hankali akan na aureki, a gaskiya kiyi Hak'uri,"
Wani murmushin cin nasara tayi,
"Yanzu dai idan na fahince ka iyayenka ne matsalar ka?"
Kai tsaye yace
"Eh"
Dan yana tunanin itace hanya mafi sauk'i da zai sallameta batare da wani bacin rai ba, duk da yasan dimbin irin alk'awarin da yayi tayimata,
"Idan iyayenka suka amince kenan babu matsala?"
"Eh ina tunanin hakan,"
"OK shukran laka, saida safe"
Kashe wayar tayi, tare da yin lamo akan gadon ta, tana hango irin rayuwar masoyar da zasuyi, lalle duk wani tanadi na soyyaya shi tayima shi,
Kamar wadda aka mintsila ta mik'e zaune,
Gabanta yafadi tuno da Abbakar wannan mutumin ya takura mata a rayuwa,
Tsaki tayi,
"Bak'in kaud'i harda wata 'yarshi zai kawomin,"
Sai kuma tayi murmushi koba komai danginsa suna daraja ta, dukda yanda yasu suke mata daukar tana muguwar hark'alla da manyan k'asa,
"Kutttt su acciki"
Text tashiga turawa Abdul dan kuwa gobe tana son sukai komai a k'arshe,

Zaune take bakin gado tana saka maballin rigar bacci, wayar Abdul tayi k'ara alamun text yashigo, kamar kar ta duba sai kuma wata zuciyar tace ta duba, dama kwana biyu tanada tuhume tuhume a kanshi, dan haka sai kawai tadauka,
Number ce wadda ba,ayi save ba gabanta yafara fad'uwa daganin irin kalamain da tafara cin karo dasu kamar haka,
" Assalamu alaikum, Abdul nasan har yanzu kaunata tana tare da kai, yayinda nake maka albishir da cewa nima har yanzu ina kaunar ka fiye da yadda na soka abaya Dan kuwa yanzu koma me namallaka zan iya sadaukar dashi wa soyayyar ka, nasan bazamu samu matsala ba, dan haka gobe inason mu tattauna, a gidana zan turo maka da adireshi,
Nice mai kaunarka dai Ameena Abi Turab "
Har rawa hannun Baseera yadinga yi nan take ira izzan bala,in ta yatashi,
Tabbas wata kawar ta tabata labarin Ameena tana akasa dukda tasan soyayyar ta da Abdul acan baya amma batayi tsammanin haka ba,
Hankalinta yaci gaba da tashi yayinda ta dinga cin karo da wasu sakonni wadanda suka fi na farkon, Dan kuwa wannan Number mai matsayi ce da tasamu Kalmar Heart Beat!
Nanda nan itama tata zuciyar tashiga kara bugawa.
🙆🙆🙆YACUCENI🙆🙆🙆
The book
Of

Queen Mermue

©
HIKIMA writers
Association

Edit by
ANaM Dorayi
Page2⃣2⃣

My lovly Fans Ina matuk'ar jin dad'in yadda kukemin uzurin kasancewar bakwa samun yadda yakamata, ina yawan jin korafe korafenku, ina mai Dada baku hakuri harwa yau ku kasance masu yawan YAKANA! Insha Allah zan qara qoqari, nagode muke, 😍😘


Saida wayar tayi kara tayi k'ugi har ta gaji kamar baza,a daga wayar ba can kuma sai aka d'aga,
Abin har yaso yabawa Ameena haushi amma ganin ya daga wayar yasa tadawo dai dai,
Sallama tayi acikin kalar muryarta ta larabawa, wanda jin muryar kawai yasa yagano mai magana,
Cikin fara,a ya amsa sallamar, kana yace,
"Manyan mata masu Nigeria,"
Cikin sanyin murya wadda tuni wata guguwar son shi taqara qaruwa a zuciyar ta,
"Hmm Abdul kenan, mune manya ko kuma ku,
Ya gajiya ya 'ya'yana,"
"Lafiya kalau muke,"
Bayan doguwar gaisuwar da sukayi sai kuma shiru ya biyo baya kamar bazata dago zancen ba can taja doguwar ajiyar zuciya tace,
"Abdul ya zancen mu ya kwana duk da nasan ni mai dinbin laifice a wurin ka amma nasan kai mai Hak'uri ne da rik'on alk'awari, ina ce baka manta alk'awarin da kayimun ba,"
Ajiyar zuciya yayi yayinda wani haushi ya tokare makoshin sa, can ya daure yace,
"Eh Ameena ban manta da alk'awarin da nayi maki ba, amma ki sani na riga da nayi aure a yanzu kuma ina son mata ta haka kuma idan nace zan aureki a yanzu ba k'aramar fama zansha a wurin iyayena da can nayi doguwar jayyaya dasu ne abisa kuskure da kurciya amma yanzu ki sani ba abinda zai sa nak'ara wani tashin hankali akan na aureki, a gaskiya kiyi Hak'uri,"
Wani murmushin cin nasara tayi,
"Yanzu dai idan na fahince ka iyayenka ne matsalar ka?"
Kai tsaye yace
"Eh"
Dan yana tunanin itace hanya mafi sauk'i da zai sallameta batare da wani bacin rai ba, duk da yasan dimbin irin alk'awarin da yayi tayimata,
"Idan iyayenka suka amince kenan babu matsala?"
"Eh ina tunanin hakan,"
"OK shukran laka, saida safe"
Kashe wayar tayi, tare da yin lamo akan gadon ta, tana hango irin rayuwar masoyar da zasuyi, lalle duk wani tanadi na soyyaya shi tayima shi,
Kamar wadda aka mintsila ta mik'e zaune,
Gabanta yafadi tuno da Abbakar wannan mutumin ya takura mata a rayuwa,
Tsaki tayi,
"Bak'in kaud'i harda wata 'yarshi zai kawomin,"
Sai kuma tayi murmushi koba komai danginsa suna daraja ta, dukda yanda yasu suke mata daukar tana muguwar hark'alla da manyan k'asa,
"Kutttt su acciki"
Text tashiga turawa Abdul dan kuwa gobe tana son sukai komai a k'arshe,

Zaune take bakin gado tana saka maballin rigar bacci, wayar Abdul tayi k'ara alamun text yashigo, kamar kar ta duba sai kuma wata zuciyar tace ta duba, dama kwana biyu tanada tuhume tuhume a kanshi, dan haka sai kawai tadauka,
Number ce wadda ba,ayi save ba gabanta yafara fad'uwa daganin irin kalamain da tafara cin karo dasu kamar haka,
" Assalamu alaikum, Abdul nasan har yanzu kaunata tana tare da kai, yayinda nake maka albishir da cewa nima har yanzu ina kaunar ka fiye da yadda na soka abaya Dan kuwa yanzu koma me namallaka zan iya sadaukar dashi wa soyayyar ka, nasan bazamu samu matsala ba, dan haka gobe inason mu tattauna, a gidana zan turo maka da adireshi,
Nice mai kaunarka dai Ameena Abi Turab "
Har rawa hannun Baseera yadinga yi nan take ira izzan bala,in ta

Please Login or Register in order to submit comment