You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suke bai qara kallaba ya dauke Kai fuskarsa na sake fitar musu da annuri ya nufi qofa zai fice zarah tayi saurin ajiye wuqa da gwaibar hannunta tana miqewa ta nufesa tana cikin kulawa tace"


Fita zakayine gashi har an jere maka komai na breakfast a dining,
Ko zaka daure kaci ko ka.....


Zanyi a office idan naje I'm late already excuse me"
Rabata yayi ya wuce Yana daukar wayarsa datai ringin batareda yasake waiwayartaba ya fice.


Shiru tayi agurin tareda bin qofar daya fice din da kallo jikinta a matuqar sanyaye sbd a zaman aure kulawa da lokacinsa ne tasan bazai taba Bata ba gashi abin Yana damunta matuqa musamman idan a gaban mutane ne.


Qaqalo murmushi tayi tareda boye damuwarta ta juyo tadawo gefen amatun ta zauna tana kawo wani labarin daban sbd wancan datake Bata na farko ta manta Abinda take cewa.


Tsura Mata ido amatu tayi tana kallon hannunwanta dake yanka gwaibar duk sai taji bataji dadiba
Sbd me zai dizga anty zarah din bayan ita kulawa ta nuna Masa¿


Dafa hannunta tayi tareda karban wuqar da gwaibar ta aje cikin plate dake Kan table tana qoqarin kawar Mata da damuwa ta saki murmushi tana cewa"


Anty zarah gwaibar Nan ta isheni haka babyb harya Fara zama qato daga zuwanmu jiya sbd ciye ciyen da kike basa.


Sai alokacin tasaki fuskarta sosai cikin Jin dadin Abinda amatun ta kalla tace"


Ai dama so nakeyi yayi qatoto cikin qoshin lfy ta yanda iyayensa da kakanninsa zasu bani lambar yabo ta musamman.


Hmm anty zarah waye zai baki lambar yabo acikinsu Dan kin kula da renon cikinda ba'a so?
Dr ne kawai ke sonmu sai ke Dan haka Kona haihu ke zanbarwa babyn har sai kema kinsamu nai.


Dariya sosai anty zarah tayi tana cewa''


Waye yake kyautar ciki tun baa haifesaba amatu,
Kuma ki daina cewa ba'a son abin dake cikinki sbd idan har ana maganar gata to na tabbata abin dazaki Haifa gata yagama yimasa yawa,
MD ZABEERA Dr ne Wanda yafi kowa qauna fiyeda komai da duk abin daya mallaka Dan haka Ina tabbatar Miki da Babu wani uba bayan Dr dazaifi MD qaunar abindake cikinki musamman sbd ni ba haihuwar nakeba Kinga kuwa Dole zai qaunaci 'dan Dan uwansa uwa uba Kuma Dr khalil shi yanzu ai bashida kamarku keda cikin Dan hakama ki daina cewa ba'a sonku mu Muna sonku Andi ma Yana sonku hakama Modibbo.


Gyada Kai kawai tayi tana daukar sauran fruits din dake gabanta tana cinyewa tana lumshe ido Dan dai tunda tazo idanba da daddare data kwanta ba bakinta bai zauna a rufeba komaima cin cire haushi take Masa sbd ganinsa kamar ba kudi aka saka aka siyoba komai akwai kamar a banza.




******
Zaune take tana sauraren 'yar guntuwar da nasiha tareda lallashi da 'yarta juwairiyya ke Mata cikin kulawa da tausasa harshe Amma ita Sam hankalinta baya kanta tayi nisa gurin tunanin abindake damunta,


Ganin hankalinta baya kanta yasa juwairiyya yin shiru tareda miqewa tana cewa"


Umme tafiya zanyi ga dadynsu Fatima na kirana Kuma gobene tafiyarmu Lagos sai gaf da azumi zamu dawo Inshallah.


Dagowa tayi ahankali ta kalleta batareda tace komaiba ta gyada Mata Kai tana shafa Kan Ahmad 'dan qaramin 'danta tace"


Allah yakaiku lfy.


Amin tace suka shiga bedroom din umme suna qarasa dauko sauran kayansu suka fice.


Shiru tacigaba dayi tana saqa da warwara,
Yarinya qarama kamar amatu itace tayi Wasa da tunaninta tasakata cikin wannan tunani da halin na baqin ciki har ana cewa itace Zara raini cikinda Babu ubanda yayishi,
Wlh bazata yarda ba tunda shirinta ya lalace na kowama saiya lalace Dan kuwa sai ansan wa aka taba,


Idanma MD ne ya ninkawa wannan makwadaiciyar kudi datake iya komai akan kudi ta kuwa kowa sai yaji ajikinsa wlh,


Amatu cikin dayayi sanadin baki Jin Dadi da gata acikin zabeera shine zaizama mugun sanadin barinki zabeera da mummunan hukunci tareda wulaqancin da sai Yan jarida sun buga,
Zanga yanda za'a haifi cikin da Babu.


Shigowar Haj maryam ce tasata kallon qofa tana sake ajiyar zuciya ganin yanda itama haj Maryam din duk ta hargitse sbd burinsu na shekara da shekaru ya lalace cikin mintuna goma a hannun yarinya qarama.


Zama tayi ummen nace mata'Â Yaya nuratu?


Nuratu na can haryanxu kuka takeyi
Wlh Nima aishatu nakasa yadda da khalil wata yake aure ba nuratu ba,
Yarinyar Nan fiyeda shekara goma take fama da son Khalil sai yanxu da ake maganar aure kwatsam wannan mugun labarin ya fada,
Labarin da mune muka qirqiresa Amma sai asamu wani juyin Masa a zancen
Ni dai wlh Kam wannan Abu ban amince dashi ba nabawa nuratu wuqa da nama nace ta qetare duk wata iyaka ta qwato Khalil dinta mukuma maji da sauran.


Cikin quluwa itama ummen tace"


Dukkansu zasu raina kansu ne harshi Khalil din saiyaga bacin raina.






***Da Rana lafiyyan faten dankali da Naman kaza da carrot akayi sbd ita kawai
Haka ta zauna tacinye Wanda aka kawo Mata tas ta kora da ruwan roba masu sanyi Danma lemu masu sanyi taso Sha anty zarah din ta hanata da cewa saidai Tasha fruits drinks ba lallai su bawa baby lafiya ba
Haka ta hkr badan taso ba Dan ita wannan cikin badan Shiba da duk abindake gidan saita ringa cinsa ba kakkautawa.


Baccin Rana tayi bayan tayi sallah sai yamma sosai ta tashi bayan tayi la'asar suka Fara waya da USI Nan yake fada Mata Dr yazo gida yafadawa su kawo shine 'dan wadda ta daukeki aiki Kuma zai ringa zuwa Yana dubamu kafin kidawo hakama ya tafi dashi anyi cike ciken makarantar dazashi har ilorin.


Saidatayi sallar magrib tukuna ta fito Palo ya zauna tareda miqe qafafu hafsatu na matsa Mata tana kallo cikin ranta tana cewa"


Amatu kinfa zamo hajiya
Irin wannan Jin Dadi haka


Gashi dama ba wani ciwo da qafafunta keyi tsaban son Jin Dadi da wuce wurine yasa take cewa ciwo suke Mata Dan a matsa Mata.


Wata tashar turawa take kallo ana wani film na adventure sai washe baki takeyi tana cin cake din data sa anty zarah tasa hafsatu tayi mata na inibi me laushi yaji butter sai ci take tana lumshe ido tana kallo tana Jan hafsatu da labari itama hafsatun na tayata fassarar qanxon kurege na turancin da akeyi Dan itama ba wani iyawa tayiba Amma ta dage tana fassara Mata.


Anty zarah ce ta fito daga dakinta ta nufosu cikin ado da kwalliya me kyau sai qamshi me Dadi take fitarwa amatu tabita da kallo cikin farin ciki tace''


Anty zarah kinyi kyau sosai
Amma meyasa zakiyi kwalliya yanxu da dare tunda kwantawa zakiyi?


Zama tayi kusa da ita tana murmushi tace"


Amatu MD na hanyar dawowa shiyasa.


Ohhh ohhh nagane anty zarah"
Taqarasa fada tana dariya.


Miqa Mata plate din cake din tayi tana cewa''
Anty zarah kici kiji yayi Dadi sosai.


Har takai hannu zata dauka saita fasa tana cewa"


Idan naji cikina zai cika bazan iya cin wani abincin ba kada MD yadawo nakasa tayasa cin abinci a dining.


Kallonta tana cewa' kici ko kadan anty zarah tunda kinaso.


Girgiza Kai tayi tana gyarawa amatun pillon data jingina dashi tana jawo Mata wani labarin take amatun tahau dariyar labarin datake Bata anty zaran na tayata sunyi nisa sunata nishadinsu saiga bude qofar palon aka shigo Dr ne hannunsa daukeda qatuwar ledoji da amatu ta ajiye plate din cake din hannunta ta taso kenan saigashi a bayansa Shima ya shigo fuskarsa kawai ta kalla ta janye daga gefen Takoma gefen Dr ta tsaya tana Masa murmushi zatai Magana yace"


Baki gaida MD ba amatu.


Kallonsa tayi kafin ta kalli inda MD din yake Yana qarasa shigowa palon tayi qasa da murya tace"


Ina wuni sannu da dawowa.


Hannu kawai ya daga Mata ya nufi hanyar samansa anty zarah dake zaune ta miqe itama tana Masa sannu da dawowa to ita ya bude baki ya amsa Mata tareda Dan tsayawa ya kalleta kafin ya dauke Kai Yana cewa'


Karki jirani dinner nariga nayi dinner agurin Modibbo.


Kallonsa tayi Yana qoqarin wucewa tace"


Akawo maka ko fruits ne?


No thank you.


Wucewa yayi ya barta a tsaye tana binsa da kallo fuskarta na 'dan canzawa Amma Jin duk idanuwansu akanta yasa ta washe fuska tareda juyowa tadawo inda suke tana cewa"


Dr ko zakayi dinner tareda mu ne to?


Kallonta duk su duka sukeyi girmanta na qaruwa a idon Dr
Tausayinta da qaunarta na shiga a zuciyar amatu tareda takaicin MD din ta yanda anty zarah ta Hana kanta cin komai sai yadawo Amma ya take hakan ya wucewarsa ko kwalliyar datayi danshi bai tsaya yayi Mata kallon ko mintu biyu ba ko me ya dauki kansa Dan ma yasamu mace me kirki da kyau kamar anty zarah tana sonsa wlh da itace koya Masa hankali zatayi taga qarshen kyau da Jan ajin banzansa.


Kamo hannun anty zarah din tayi suna zama palon tace"


Anty zarah Zo kici cake din Nan kiji Allah yayi Dadi sosai.


Ledojin hannunsa Dr ya miqawa amatu Yana cewa"


Nima a gajiye nake kamar MD shima yau a gajiye yake sosai Nima tunda muka hadu baicemin ko qala ba sbd gajiyar dayake tareda ita zanje na kwanta Saida safenku
Amatu ki kula ok?¿


Gyada Masa Kai tayi tana cewa''


Nagode Saida safe.


Yana fita zarah tasaki murmushi tana cewa"


Dr kayaushe kanason gyara Abinda MD yakeyi Dan kada aga laifinsa
Kadaina damuwa Dan Nima Babu ranar dazanga laifin nasa.


Takaicin MD din yasake Kama amatun tasake dagewa Saida anty zarah din taci cake din sosai Tasha apple drink suka cigaba da firarsu
Ganin hankalin zarah din na Kan hanyar sama yasa amatu sakin tsaki qarami tana miqewa tace"


Bacci zanyi Saida safe anty zarah.


Tana shigewa zaran tasa hafsatu ta kashe komai itama tashige
Suna shigewa taje dakinta ta shirya ta nufi dakin MD.




Ahankali amatu tasaba da zarah da hafsatu sosai kamar sunyi shekaru atare,
Kulawar dasuke Bata da gatan datake samu daga garesu yasa hankalinta ya kwanta sosai acikinsu musamman ma da kullum tana waya dasu kawu dasuketa sawa Dr khalil albarkar yanda yake kula dasu sosai Dan yanzu ranakun matsuwarsu sun qare ga USI anata shirye shiryen zuwa makaranta,
A duniya yanzu mutanen datake so a rayuwarta fiyeda komai da kowa sune USI,kawu,iyami,Dr da anty zarah sbd sune mutanenda tasan tabbas qaunarta sukeyi Babu wani qyama ko munafurci.


Dr ya Gina qaunarsa cikin ranta danasu kawu sbd Suma shine mutum daya qwal daya fito ya tsaya musu a rayuwa yake qaunarsu batareda qyama ba ko buqatan wani Abu daga garesu shiyasa dukkaninsu kowannensu ya bude baki Dr ne abakinsa sai anty zarah dinta.


Qaunar data kewa anty zarah din yasa take Jin tsanar MD matuqa cikin ranta sbd yanda tagama lurada Sam baya damuwa da alamarin zarah din kullum shine damuwarta shine kukanta shine jimaminta ko tausaya Mata bayayi da yanda take matuqar qaunarsa/sonsa da ganin girmansa,


Duk yanda zarah din take qoqarin boyewa hakan baya boyuwa ga Wanda yake zama taredasu shiyasama Sam ta tsani ko ganinsa matuqar Yana gida Bata fitowa sbd kar wataran tayi amsa zagin maguzawa akan Abinda yakewa antyn saidai duk Abinda zai faru yafaru ba ruwanta.


A bangaren Jin Dadi kuwa zatace itakam gwara da akayi Dan kuwa rayuwa ta sauya Mata sosai Dan ko jikinta da fatarta sum nuna suna cikin hutu sbd lafiyayyar rayuwar datake ciki,
Banza ta Fadi" kaman yanda take fada
Dadinta takeci ba qaqqautawa duk wani Abu me Dadi cewa takeyi tanaso ba Bata lokaci kuwa Zarah zatasa akawo Mata shi,


Hafsatu kanta ta qararda 'yar ta'addace a gidan Dan kuwa tunda amatu tazo Bata zaman awa biyu batai aikin hada mata wani abuba,
Itace ayi Mata gullisuwa,
Tuwon Madara,
Kwakwameti,
Cake,
Dambun nama,
Dambun kaza,
Furar Madara da Milo
Komaima ci takeyi ita Bata taba ganin me ciki irin wannan na amatu ba da baya tadar komai
Komai ci takeyi hadda Wanda masu ciki baya shafa musu lafiya
Gashi ko ciwon Kan Nan na banza da masu ciki keyi ita batayi kullum daram dam take
Ga Dr ya Hana asa kowane likita ya duba matarsa yace shine zai ringa dubata musamman da kwanakin umme tasaka fitinar sai Modibbo yasa anyi scanning Dan asan ranar haihuwar cikin su Fara shiri.


Hankalinta bai wani tashiba sbd tasan Dr na Nan shine zaisan yanda za'ayi da Maganar scanning din itadai damuwarta 'dayace shine anty zarah data Fara maganar cikin baya girma sbd ta shanye kusan wata biyu a gidan gashi Koda tazo tace ciki wata biyu wata hudu kenan Amma Babu alamar tasowar cikin shine anty zaran ta daga hankalinta cewar cikin baida lafiya itama tanason ayi scanning.
##mamuh##








ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA
safiyya huguma


MIN QALB
mamuhgee


YANKAN BAYA
billyn Abdul


KIBIYAR AJALI
Miss xoxo


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA
hafsat rano


Pay @09033181070
Or 09032345899
6/17/21, 8:02 AM - ': *_MQ 16_*


Zaune take gaban madubin dakin daya zama Mata tana kallon fuskarta datayi haske sosai tareda duka fatar jikinta har wani qyallin samun hutu da kayan gyara masu tsada da mutunci zuwa qirjinta daya ciko shima yayi daram dam sabanin dah banbancinsa da shafe idan tasaka brazier ne push up.


Mayarda kallonta tayi Kan cikinta tana miqewa tsaye ta Dan matse rigarta tana shafa cikin sai tasamu kanta da sakin murmushi karon farko datai shaawar dama ace cikin gasken ne da ita da zaiyi mata kyau Kuma da duk wahala da dawainiyar anty zarah baza taje a banxa ba,


Dan sake dafe cikin tayi tana cewa''


To idan ace cikin gske ne to waye zai zama babansa?


Dr??


Girgiza Kai tayi tana cewa''


Ummen sa bazata Bari ba.


Amma dai duk da haka shine zaifi iya bawa babyna kulawa Amma dai kamanninsa kuwa anty zarah nakeson ya dauko sak sai Kuma......


Shiru tayi takasa qarasawa


Daga bayanta taji ance' sai Kuma me maman bby?


Juyowa tayi tana kallon ZARAH din kafin ta juya ta qurawa cikinta ido ta cikin madubin ahankali tace'


Sai Kuma inason ya dauko hancin MD.


Zarah dake qoqarin zama bakin gado tsayawa tayi ta kalli amatun tana karban zancen a baibai saidai kawai tasan duk irin shirme shirmen Amatun sai kawai tasaki murmushi tana janye Amatun daga gaban madubi tana cewa"


Zoki zauna zaki gaji da tsayuwa gashi yau zamuje scanning anjima kadan
MD nake jira ya kirani na sanar Masa zamu fita nayita Kira baya dauka tun safe bayan fitarsa.


Ki qyalesa anty zarah mu tafiyarmu kawai tunda Dr na can Yana jiranmu a asibitin tun dazu yake Kira bamu fitoba.


Bazaki gane bane Amatu dokar MD ce baya barina fita Babu wani babban dalili me qarfi sbd shi mutum ne me buqatar sirrintacciyar rayuwa Mara hayaniya shiyasa bayason ko iyalinsa ace kowa ya sansu a haka dai zance MD mutum ne me tsananin kishi.


Dibar zancen na anty zarah tayi ta watsar da baki tana cewa"


Anty zarah to nidai gskia muje karki tsaya jira tunda yaga Kiran naki fa na tabbata,
Kuma nidai bazan Bari Dr yayita jiraba tunda Modibbo da Andi sunsan da zancen fitar muje kawai Dan Allah.


Miqewa anty zarah tayi tana nufar qofa tana cewa'


Amatun 6acin ran MD ba kyau bazan iya take dokarsaba
Zan iya fita yanxu wani Abu yafaru wlh bazan iya daukar fushinsaba kiyi hkr Bari nasake gwada kiransa kozai dauka....


Takaici yasa Amatun dafe ciki ta durqushe tana cewa''


Wayyo Allah anty zarah cikina marata ciwo sosai
Dan Allah anty ki taimakeni kada cikina ya samu matsala Ina sonsa banason ya zube.....


Da gudu anty zarah ta dawo tana Kiran sunanta cikin tashin hankali tana riqota
Ita kuwa Amatu sai wani murqususu takeyi tana sako hawayen qarya tana Daman cewa''


Anty ki taimakeni banaso cikina ya zube.


Tsabar tashin hankali da firgici tareda tausayin Amatun me tsanani ZARAH batasan lokacin data fashe da kuka ba tana kamota jikinta tana qoqarin muqar da ita tana kwalawa hafsatu Kira Dan tazo su kamata suyi asibiti.


Kamata sukayi suka saka mota a gigice anty zarah ta yafo gyalen jallabiyar dake jikinta ta fada motar ta jasu suka fice tana cewa hafsatu"


Hafsatu maza Yi sauri ki Kira Dr khalil ki sanar Masa Abinda yake faruwa gamunan zuwa.


Shiru Amatu tayi daga kukan qaryan datakeyi jikinta na yin sanyi da yanda anty zarah ta daga hankalinta sai hawaye takeyi tana Mata sannu Amma Babu yanda ta iyane itama sbd Dr yace Mata komai zatayi ta tabbatarda sunxo asibitin sbd yabasu scanning din daya shirya Dan ita din idan basuxo asibitin ba to tabbas wani likita ummensa zatasa akawo har zabeera din Dan kawai ayi komai yafito fili
A bangare daya Kuma ga USI da shima zasu hadu duk a asibitin shiyasa tayi hakan,


Ahankali ta kamo hannun anty zarah din bayan har sun iso asibiti Khalil ya karbeta sun shige yayi duk yanda zaiyi ya hado scanning din aka kwantar da ita office dinsa tareda 'yan magungunan vitamins sai alokacin hankalin zarah yadawo jikinta ganin Amatun tadawo daidai ciwon ya daina.


tana kallon anty zarah din bayan ta riqe hannunta ganin har lokacin da sauran damuwa a fuskarta itama cikin sanyin murya furta"


Nagode anty zarah,
Nagode da matsayin da Kika bani na qanwa tamkar wadda kuka fito ciki daya,
Anty zarah wlh kece mutum ta uku da Kika taba qaunata tsakani da Allah ba qyamata ko wulaqantawa Dan haka kinada babban matsayi a zuciyata da har abada bazan mantaki ba.


Kasa cewa komai anty zarah tayi sbd har lokacin Bata Gama fitowa cikin shock din halinda Amatun tashigaba
Dan wato da ace wani Abu yasamu cikin bazata taba yafewa kanta ba.


Shigowar Dr da USI a bayansa yasata miqewa zaune da sauri tana washe dukkanin haqoranta cikin tsananin farin ciki takira sunansa tana qoqarin saukowa gadon Dr khalil yayi Mata gyara murya Yana kallonta
Take ta kallesa tana dawowa nutsuwarta saita waske ta hanyar cewa"


Anty zarah ga qanina usman.


Kallonta anty zarah tayi irin da gasken Nan kike?


Daga Mata Kai tayi murnarta na sake bayyanuwa ta jawo Usman din gaban anty zarah tana cewa"


Usi ka gaida anty zarah.


Da sauri cikin girmamawa yace"


Anty mun wuni lafiya?
Ya gida Yakuma qoqari?
Mungode sosai sosai fa anty
Allah ya saka Miki da alheri
Ya biya Miki buqatunki na alkairi.




Murmushi anty zarah tayi tana kallon yanda jikinsa har mazari yakeyi gurin gaidata Yana fiddo dukkanin girmamawar dayake ji akanta sbd duk yanda take qaunar Amatunsa tafada Masa shiyasa shima tun baigantaba yake Jin qaunar halayenta da ganin girmanta.


Kallon Amatu dake cikin dokin ganin usman din tayi tana cewa''


Amatu me Kika fada Masa yaketa wannan addua haka?
Usman karka ji komai ba komai Amatu tamkar qanwar da kuka fito ciki daya nake jinta
Saidai kayi Mata nasiha ko zataji Amatu Bata zama kurum kodan halin datake ciki gashi yauma sbd tasa damuwar fitowa Dole yasa akaso samun matsala har muka qare kwance a asibiti.


Anty zarah ki ringa doketa kokuma ki Fara hanata kayan Dadi zata dawo hankalinta.


Dariya sosai anty zarah tareda Dr suka saki harda ita Amatun tana kaiwa usi mugun duka a baya tace"


Ni zakayiwa baqin ciki usi?
Zakasan dawa kayi sai nasa kawu ya aura maka qanwar maman junior data maqale maka.


Cab wannan ai koni tafi iya sanin yanda ake sanfewa Dan wlh koke duk qwarewarki saita sanfeki
Kisa ranarda aka kawota ta sanfe Dan cinikin iyami da kawu kejin yanzu yafara zamowa sahun masu abun Kai kawu ya kwana ya debewa auren albarka.


Dariya suka saki gaba dayansu hadda anty zarah da batasan meye sanfewarba dagasu sai Dr ne kawai suka sani shima sbd yayi bincike sosai akansu ne Kuma sun zauna dashi su kawu da USI din Basu boye Masa komaiba gameba rayuwarsu sbd sunriga sun daukesa kamar jininsu.


Ta Dan saci kallon Dr da ita yake kallo shima zuciyarsa na samun nutsuwa da yanda yake ganinsu cikin nishadi zuciyarsa na sake samun nutsuwa
Ta juya ta harari usi tareda take Masa qafa da qarfi har Saida ya zabura tayi saurin dafesa Dan kada anty zarah tagane qasa qasa tace"


A gaban Dr baban babyn nawa kake tayarda maganar qwarewata a sata ka shirya kwanciya a asibitin Nan Dan saina fasa maka baki da haqora idan anty zarah ta fita.


Kallon Dr yayi da Ido Yana cewa''


Ka ceceni matarka zata fasa bakina Wai.


Kamar zaiyi Magana sai ya fasa Yana sakar Mata murmushi sbd idanun data zuba Masa tana jiran jin Abinda zai ce ta mayarda rigimar kansa.


Ikon Allah anty zarah tayita kallo a tsakaninsu sunata raha da nishadinsu cikin tsananin qaunar junansu ga Dr da tuni dama yazama 'daya daga cikinsu gabanta harsu iyami aka Kira da kawu a wayar Dr Nan aka Dora wata sabuwar hayaniyar sbd labarin fadanda kawu yayi dasu maman basiru ya dauko motar yan sanda biyu aka kwashe gidan kaf harda alhaji mande daya iya shigar sani infika.


Dariya sukeyi sosai musamman da iyami ke fadawa Amatu kawunta ya zabure yanzu tunda yaga ya 'dan tsayu hakama insfector Garba na Nan Yana bibiyar kawun akan maganar aurenta.


Nishadi sosai suke saka anty zarah tayi zugum tana kallonsu suna burgeta hakanan taji inama acikinsu take itama data samu farin ciki kamarsu,
Abu daya tasani shine Koda take cikin wadata ta taso cikin tun tana gidansu Basu San wani Abu Wai sakewa cikin nishadi kayi rayuwarka ba,
Tun a gida sun Saba bin umarni ne kawai da oda suka sani
Iyayensu basa jansu ajiki Wai da sunan tarbiya da kadasu lalace
Shiyasa yawancinsu Basu wani cikin walwala saidai kawai suyi rayuwa cikin daular Amma Babu wani walwala saigashi wainnan bayin Allan sunada duk wani nishadi da walwala suna rayuwarsu hankali kwance,
Tabbas shi nishadi da farin ciki ba siyansa akeyiba Allah ne yake baka
Gashi ayau duk da tarin daular datake ciki rayuwar wainnan talakawan tana burgeta harma tanajin inama acikinsu take.


Anan sukai kusan Rabin yinin sai yamma suka fito gabaki dayansa tana Jin kewar usi dasu kawu tun Usin be tafi Amma hakanan suka rabu shida Dr suke tafi a motar Dr sbd yakaisa gida itakuma suka tafi a motar anty zarah da hafsatu.


Suna tafe suna tana kallon titi cikin nishadi sbd tunda tashiga zabeera tsawon wata biyu sai yau tafito,
Gskia dai ma Ashe wani lokacin masu kudin rayuwar takura kawai sukeyi kullum a killace Wai sbd kar mutane su dameka,
Ita Sam batason akoma gidan yanzu yawo takeso tadan sakata ta Wala.


Qaramin tsoki taja a fili Wanda yasa anty zarah kallonta tana cewa''


Yaya dai Amatu?


Bata fuska tayi tana yamutsawa tace"


Anty zarah Dan Allah muje blue fox na taba yin aiki acan
Muje kibiya madam dinmu kudi yau da kanta zata wanke min Kai da qafafu tasan Nima bayan ta koreni aiki nayi gaba ba bataba.


Murmushi tayi tana cewa''


Amatu ba dama.


A blue fox wani shaqiyanci ta dinga yiwa madam bell din tana cewa ga Abinda da Abinda takeso
Haka dai suka ringa yimata Abinda tace sbd ganin wadda sukazo tareda ita din she's from zabeeras.


Gyaran Kai akai musu itada anty zarah din tareda kyan qafa da gyaran fuska take suka koma tamkar wasu amare musamman amatun da Bata taba irin wannan gyaran ba take suka hau wani irin sheqi.


Daga nan restaurant din blue fox din ta matsawa anty zarah suka shiga Nan tayi odar kayan dadin dataci harta Bar saura sbd sunfi qarfin cikinta suka fito nanma matsawa anty zarah tayi suka nufi wani qatoton shopping mall datace tanada kwadayin son shigarsa.


Suna shiga mall din me hawa biyu batasan lokacin data saki tsallen murna ba tana rarraba idanu cikin gurin farin cikinta a bayyane.


Sama suka hau gurin kayan babies antyn na cewa kayan baby kawai zasu siya
Nan anty zarah tadan zaba kayan babies suka sauko Amatun nata zare Ido tarasa abin dauka sbd duk kayan Dadi da maqulashen dake gurin akwaisa a gida hakama sutura Bata buqata sbd Dr kusan kullum cikin kawo Mata su yake hakama anty zarah
Idan turarukane duk tanadasu a gidan hakama takalma,
Ita Kam da a dah ne tazo wannan gurin da saita sace kusan kayan dubu dark saidai suje station
Amma ko yanxu ba damuwa Dan saita yiwa Dr tsarabar dazai ringa tunata.


Wani tsadadden agogon Rolex tagani Yana qyalli take ta hango kyanda zaiyi a hannun Dr
tasaki murmushi tana kallon anty zarah dake qoqarin Ciro card dinta tabayar gurin payment ta faki idanuwansu ta zaresa tareda sakawa cikin aljihun doguwar English gown din dake jikinta tana waskewa tahau 'yan juye juye tana latsa wayar anty zarah dake hannunta.


Suna Gama payment din suka fito har zasu shiga mota aka tsayar dasu da sauri ana cewa su dawo ciki anason ganinsu.


Tsayawa anty zarah tayi tana kallonsu cikin mamaki kafin ta kalli time har anfara Kiran sallar magrib tace"


Lafiya?
Sauri mukeyi munyi dare fa.


Dayan ne me sanyeda suit kamar ma shine babbnsu yace"


Haj wani Abu mukeson kugani da idanuwanku kafin muyi mgn please.


Qaramin tsoki tasaki tana cewa''


Amatu ku jira a mota Ina zuwa.


Aa hajiya da ita zakuzo duka muke buqatar ganinku.


Ba musu suka koma ciki har office din managern gurin suka zauna take aka kunna musu Abinda footage na CCTV camera
Mutuwar zaune anty zarah tayi cikin mamaki da kunya
Amatun ma cikeda kunyar anty zarah ta dago ta kalleta kafin

Please Login or Register in order to submit comment