You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rayuwa kafin daganan Andi yayiwa Amatun kyautar aure ta sabuwar mota fil sak irinta zarah datake hawa banbancin kalane kawai dayace Tata Ash ce ta zarah farace.


Godiya sosai sukayi suka fito umme na riqeda hannun ta saka Mata wani acikin hannun dayake rufe cikin qaramar kwalbar roba suna shiga mota tace"


Shanye kiban roba.


Kallon ummen tayi tana sake kallon abun ta Dan 6ata fuska zatai mgn tace"


Bansan Jin komai hanzarta kishanye kiban.


Marairaice fuska tayi tana kallon abun.
Anty salamatu dake sit din gaba ta juyo ta kwace kwalbar ta bude tareda Dora Mata abaki tana cewa''


Dallah shanye da abin dadine da yanzu kinfara maganar qari to wannan dadinsa saikin fi kowa.....


Rufe Mata baki Amatun tayi da sauri tana zaro Ido kunyar umme kamar ta nitse ta saci kallonta tace"


Haba anty salamatu nidai karki fara zancenki Dan Allah.


Itama anty salamatu kunya taji sbd mantawa tayi da umme da iyami dasuke taredasu sbd sun Saba zantukansu na banza dasu maman junior shiyasa.


Shanyewa tayi ta miqawa umme kwalbar daidai isowarsu qofar part dinta motar har qofar palonta ta faka suka fito umme na riqeda hannunta tana fada maganganu qasa qasa na rikita miji wainda sukafi qarfin duk rawar Kan Amatun kunya kamar ta qwace hannunta ta zura da gudu Amma ummen ba ruwanta fada Mata takeyi har suka shiga suka zauna palon tana sake zayyano Mata zantuka masu qarfi wainda wasune suka samu damar shiga kanta wasu kuwa nauyinsu yasa suna kasa shigewa Kan nata.


Turaruka ummen ta fitar cikin jakar hannunta ta fesawa Amatun ko Ina jikin masu wani irin sanyin qamshi dagaji tasan bazasu wuce ouds ba masu tsananin tsada take qamshinta ya qaru tana fitarda wani qamshi me ni'imtaccen sanyin dadi suka Fara qoqarin tafiya anty salamatu tace"


Zarah ko lafiya Naga banganta ba na dauka ma zamu sameta anan gashi har zamu tafi.
Umme tace'


Eh Kam gashi dai Nima duk yau banganta ba Nima nai zatan zamu sameta anan din tana jiran isowarmu.


Iyami data miqe tsaye tana gyara zaman mayafinta yace"


Mezaisa zarah tazo ta zauna anan tana jiranmu karku manta bafa kamar da bane yanzu ana Magana akan Amatu tazama matar mijintane Dole wani abun zata Kama kanta ba kamar da ba da Amatun take matsayin qanwarta yanzu kishiyarta ce Dole akwai radadi ko yayane aranta.


Tsit Amatu tayi tana saurarensu sbd duk lokacinda akai Mata tunin kishiya saitaji kamar hankalinta nason tashi saidai girma da nauyin anty zarah da haryanxu take gani da ji atareda ita yana danne kishin datakeji shiyasa take sauke zafin kishinta agun MAHMOUD sbd bazata iya kallon fuskar anty zarah tayi fitinar kishi da ita ba duk zafin kishinsa kuwa sbd Abu daya data fahimta takuma lurarwa kanta MAHMOUD da kansa zai iya kiranta butulu akan zarah idan bata nutsu ta iya zama acikinsu ba yanzu Kam akwai aiki agabansu su dukan na iya zama da juna.


Bayan tafiyarsu iyami kasa tashi tayi daga Inda take zaune tashiga tunani daban daban akan rayuwarta da Kuma ranar farko da aka Fara kawota cikin part dinnan amatsayin matar KHALIL DAHEER ZABEERA yanzu Kuma gashi ankuma kawota amatsayin matar Dan uwansa MAHMOUD DAHEER ZABEERA,
Duk da ansauya sashen gabaki daya Babu inda zaka iya gane shine wancan din Amma dai memories diinsa suna cikin zuciyarta.
Hawayene suka ciko idanuwanta suna qoqarin gangarowa taji bude qofa
Bata dagoba Amma qamshin daya shiga cikin hancinta da motsinsa da baya qarfi yasa ta fahimci waye yashigo ta rufe idanuwanta ta bude ahankali batareda ta dago ta kallesa ba saima sake lumshe idanuwanta datai.


Qarasowa yayi cikin nutsuwarsa da kamalarsa ya zauna kusada ita sosai qamshinta ya Shiga hancinsa yanl dago fararen idanuwansa dasuka Gama gabalaituwa a sonta ya zuba Mata tareda riqo hannuwanta ya sarqe da nasa ya sauke ajiyar zuciya wadda itama ta sauke tata a boye cikin cikinta.
Kasa Magana yayi sbd bayajin yin maganar ya kwantarda kansa Kan kafadarta Yana sake sarqe hannuwansu ya lumshe idanuwansa sukai shiru ahakan sai numfashi da qamshin juna dasuke shaqa nutsuwa na shigarsu duk da Babu Wanda yafito yagfada Amma numfashinsu dake fita ya bayyanarda hakan.
Sun jima ahakan Babu wani motsi Saida yagama samun dukkanin nutsuwar daya rasa kafin ya sauke numfashi tareda dagowa ya kalli fuskarta suka hada idanu ta sauke nata tana qoqarin rufesu ya Kai hannu ya juyo da fuskar tata Yana kallon halittar da ita kadai ke iya rikita MD ZABEERA baisan lokacinda ya saki wani irin murmushi ba yana kallon bakinta daya iya fidda Magana ta arziki data tsiya.
Fuskarsa yakai dab da tata Yana kallon cikin idonta yabawa bakinta light kiss Yana sake sakin murmushi cikin taushin muryar data sanyata dago idanuwanta cikin rashin yadda ta zuba Masa yace"


I can't live without you Mrs MD ZABEERA so kada ki sake tunanin barina sbd komai zakiyi bazaki iya barin rayuwa Dani ba.


Miqewa yayi tsaye hannunta cikin nasa har lokacin ya miqar da ita Yana cewa''


Let's have dinner zarah is waiting.


Ba musu tabiyosa suka fito hannunsa na riqe da nata itama saiyi takeyi tana kallonsa duk da tasan so yake azauna lfy Amma dai mamakinsa bai daina kamata ba sbd ganin yanda ya sauya din dama ita batada niyar zama da miji Babu shaquwa Babu Wasa da dariya Babu hayaniya Babu muguwan wasan gudu gudu idan ma takama to Ina dadin rayuwar auren take tanason morewa sauran kuruciyarta a tareda mijin aurenta Dan haka Babu wani daga mulki sai oda a Shirin zamanta dashi.


Suna shiga anty zarah na fitowa daga bedroom dinta cikin adon riga da skirt na lace maroon tayi Yar simple makeup ga qaramin cikinta daya Dan fito tayi kyau itama sai qamshi take saidai suna qarasa shigowa qamshin dake fita cikin Amatun saita ji ta daina Jin natan ta qurawa Amatun idanuwanta dake son raunana da irin dacewa da kyan dasukai tareda juna ta kalli hannuwansu dake sarqe tafara Kiran sunayen Allah tana kore shedan daga zuciyarta ta saki murmushi tana kallonsu tace"


Sannu da zuwa Amatu.


Murmushi Amatun ta saki tana kallonsa da shima ita yake kallo tace"


Thank you anty.


Kallon MD din zarah tayi tana dauke idonta daga Kan hannunsa dake riqe Dana Amatu tace"


Dinner is ready fa.


Dining suka nufa su dukkansu suka zauna zarah ce ke zaune kusada MAHMOUD din sukaci abinci itadai Amatu drink kawai Tasha sai spoon biyu datai ta miqe tace ta qoshi.


Shima ba wata yunwa yakeji ba Amma ya zauna yaci abincin sosai tareda zarah haryana yaba abincin sosai sbd Fara sanin halin Mata dayayi ya fahimci sunfi son ko yaushe ka nuna musu yabawa da kulawa.
Aikuwa hakan ya faranta ran zarah musamman daya nuna Jin dadin abincin a fili saitaji damuwarta ta ragu sosai suka baro dining din itama Yana riqeda hannunta suka iso ya zaunar da ita Kan kujera ya zauna gefenta Yana kallon Amatu data matsu tawuce yafara musu bayani da nasiha tareda roqon Dan Allah a zauna lfy plus respecting juna duk da yasan suna ganin qimar junansu sosai kafin ya sanar dasu 2days ne kwanan daga haka aka tashi Amatu tafara wucewarta shikuma zarah yabi Dan sake lallasarta Abinda Baya faruwa a zamansu mamakinsa da Jin dadin hakan ya sanyaya zuciyarta sosai harta cemasa yatafi gurin Amatu tana jiransa.
Bedroom dinsa ya nufa yashiga wanka Yana fitowa Saida ya tsaya wata waya kafin ya fice.


Bedroom 'dinda ta tabbatarda shine nata tashiga data dawo daga sashen na zarah ta ajiye wayarta ka bedside drawer ta warware lafayarta ta nade takai wardrobe
tana budewa ta tsaya kallo cikin mamakin ganin Kaya a shaqe maqil da hadda wainda aka dinka da wainda ba'a dinkq ba ga qananun Kaya da jallabiyas ire iren wainda yasan tana sanyawa.
Murmushi ne yaso subuce Mata data Kai hannunta Kan tarin qananun kayan dake jere Wanda taga bumshorts ne sukafi yawa abin data lura yafiso kenen wato shigarta zata fiddo cinyoyinta duka a waje.


Rungumeta taji anyi tayi saurin juyowa sbd bataji motsin shigowarsa ba,
Kallon fuskarsatayi cikin basarwa ta zame daga jikin nasa ta jefa lafayar ta rufe wardrobe din ta bar gurin ta nufi toilet ta jima ciki Babu Abinda zatayi tana saqa da warwara kafin dai ta wanke hannuwanta tayi alwala kawai ta fito tana goge fuskarta da qaramin towel sai ganin lafayarta tayi ya miqo mata Yana cewa''


Ki mayar inason nizan cire miki inason sake ganinki cikinta you look innocent acikinta.
Batareda ta kallesaba ta karba ta nufi gaban mirror tana nadawa ya zauna Kan sofa Yana kallonta hannuwansa nade da qirjinsa.


Tana gamawa ta juyo ta kallesata ta gefen Ido ya taso Yana murmushi ya Kama hannunta suka nufi bedroom dinsa suna shiga wani sanyin qamshi ya doki hancinta sbd kalar turarukansa ba Arabians bane nasa designers Eglh perfumes yake amfani dasu,
As she expected komai na dakin fari ne da milk sbd sune colours dinsa.
Daddumar sallah ya Ciro itama milk color ce ya shimfada Yana kallonta yace"


Kinyi alwala right?


Saida ta dauke Kai kafin tabude Baki daqyar tace"
Yes.


Yanda taketa daure Masa din Yana sake burgesane Bata saniba sbd shi fushin ma nata Yana Masa kallon wani sabon feeling.
Sallah sukayi ta nafila rakaa biyu kafin ya juyo ya riqo hannuwanta duka biyun Yana kallon fuskarta ahankali ya furta"


Sorry.


Qin juyowa tayi ta kallesa ta zame hannuwanta zata miqe ya matse hannun Kai tsaye yace"


I love you..


Cak ta tsaya daga qwace hannun dazatayi zuciyarta ta Fara tsananta bugu takasa motsawa hakama takasa juyowa ta kallesa.


Ya lumshe idanuwansa yasake budewa ya Dora akan hannuwanta dayake riqe dasu cikin murya me taushi yasake cewa''


I love you AMATULLAH K SALEH and I am saying sorry so please wannan fushin yakamata ya sauka please.


Juyowa tayi tana kallon fuskarsa zuciyarta na qarasa bugawa da qarfi ta kasa yadda da Abinda taji idan MAHMOUD ZABEERA dinda tasani ne yake furtasu saidai zumudin zuciya dakeson kamata gudun bada kanta yasa ta miqe ahankali tana zare hannuwanta ya dawo da ita jikinsa ta hanyar fixgota ta Fado qirjinsa ya Bata kyakkyawar runguma Yana fada Mata Magana cikin kunnenta data sanyata saurin zaro Ido waje tana kallonsa takaici da muguwar kunya suka dabaibayeta batasan lokacinda ta Fara mintsinansa ba ta bude baki Dole tana cewa''


Wlh ni sharri ne wannan kakemin, Allah bazan yaddaba....


Dariya yakeyi Mara sauti da hayaniya wadda yaune karonta ba farko ganin dariyarsa ba murmushi ba.
Ganin ta kunnu sosai da Abinda ya fada din yasashi miqewa Yana Sosa inda ta mintsinesa Yana cewa''


Zaki fasamin fatane da wannan mintsinin naki..
Biyosa tayi tana sake kunnuwa har lokacin kunyar zancen bai saketa ba ta nufesa tana cewa''


Saika janye wannan sharrin dakamin bazan yadda ba..
Tana isowa gurinsa ya riqe hannuwan tareda shigar da ita jikinsa ya Kai fuskarsa Kai tsaye ya hade da Tata ya hade bakinsa da nata yana Bata wani ni'imtaccen kiss daya kashe jikinta harya warware Mata lifayar jikinta Bata saniba Saida ya cirata gabaki daya zuwa Kan qaton gadonsa Yana rage musu hasken dakin ta makunnin gefen gadonsa.
##Mamuh#


*_Thank you 4 d prayers_*🥰🙏




ZAFAFA BIYAR
NA KUDI NE:::


Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,


Guda hudu 4 Kuma 500,


Guda uku 3 Kuma 450,


Guda biyu 2 Kuma 400,


Guda daya akan 300.


Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


*+234 903 234 5899*


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇


*09033181070*


Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO


TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
6/17/21, 8:09 AM - ': *_MQ 47_*




_INA MASU SHA'AWA DA QAUNAR KARANTA LITTAFIN DAZAI SANYASU CIKIN NISHADI DA DAWWAMÀMMIYAR NISHADI TO GA DAMA TA SAMU KU NEMI LITTAFIN_ _*WASA DA ZUCIYA*_ _NA ZINNEE SMART WANDA TSARUWAR RUBUTUNSA DA TSAFTARSA TAREDA DADINSA SAIZA KU KAMU DA QAUNAR RUBUTUNTA A KARATUN LAYIN FARKO DAN SAMUN WANNAN QAYATACCEN LABARIN NATA ME SANYAYA ZUCIYAR ME KARATU
TA WANNAN NUMBERN_
👇👇👇
08080840567




*******
.


Tana Isa gidansu Kai tsaye dakin ummanta ta wuce ta zube Kan gado sai alokacin wani gigitaccen kuka ya 6arke Mata me ciwo.


Umman data fito toilet taganta tana kukan sai kawai ta barta tayi me isarta kafin tabar gefenta Takoma Kan kujerar dakin ta zauna tana kallonta tace"


Wannan kukan dakikeyi ki Dena zarah sbd Abinda yake taredake Wanda baya buqatan irin wannan tashin hankalin tunda kinfi kowa sanin yanda cikin baida qwari.


Tashi zaune tayi tana share hawayenta ta zare hijabin jikinta ta dago ta kalli umman dake Mata kallon jiran jin dalilin wannan kukan.


Bude baki tayi ta korowa umman bayanin komai zata Dora da wata maganar umman ta daga Mata hannu cikin takaicin ZARAn da cewa''


Zarah kinada matsala babba idan har Baki dawo hayyacinki ba,
Shi so da zaman aure duk ba hauka bane,
Ta Yaya Zaki maida kanki doluwar qarshe akan gudun zuciyar namiji,
Shin meye amfanin rayuwar aurenda babu fahimtar tunani ko Babu so ana zaman aure me Dadi idan kowa yasan mutunci da darajar kansa data abokin zamansa,
Matsalarki zarah itace kin kasa bawa kanki darajarda shima abokin zaman naki zai baki,
MAHMOUD ya zauna dake cikin girmamawa da mutuntawa tsawon shekaru masu tsayi batareda ya taba complain ko nuna muzantawa garekiba duk da kece Kika kasa kawo sauyi da shaquwa acikin auren naku sbd kece mace kinada hanyoyi da damarmaki da Zaki sauya MAHMOUD tun kafin wata tashigo rayuwarku Amma Kika kasa yanzu abin yazo a biyu na farko koki yarda ko karki yarda MAHMOUD son mararsa AMATULLAH yake so me tsanani musamman tunda yanzu gatanan tana bude Masa hanyoyin sanin zamantakewar aure sannan akwai fadanda ko sunyi abunsu na tsakanin ma'aurata ba huruminkineba Shiga gashinan yanzu kin qare zuwa bikon kishiya Wanda idan dai baki koyi sanin darajar kankiba data Kama kanki akan Abinda Babu ruwanki har ruwan wanka kina Kan hanyar daukarwa kishiya Dan haka kada kiga laifin mijinki laifinkine
Da Zaki farka ki nuna Masa kinsan darajar kanki data aurenki da zamanki matarsa tsaf zakiga yazo yazauna daku anbawa kowacce haqqinta anzauna lafiya.
Bance kinyi baya ba sbd wannan halindakike ciki Allah na gani Kuma Yana sane wlh zakiga irin tanadin sakamon da Kika samu agaba Amma gskia zarah ki farka Babu Wanda zai qwaceki a cikin wannan yanayin sai kanki da kanki Zaki qwaci kanki ki tashi kije bikon naki dakika daure kanki da zakiyi Danni bana cikin wannan mutuwar zuciyar.


Mutuwa jikinta yayi ta miqe ta wanko fuskarta tadawo ta dauki keys ta fice batace qala ba ta shiga mota ta nufi gidansu Amatu.
Tana Isa tayi parking ta fito tana daidaita kanta da nutsuwarta ta nufi ciki ta Isa qofar Palo tashiga da sallama
Su iyami dake zaune palon duk suka juyo suna kallonta
Saiga Amatu ta fito daga kicin daukeda indomie data dafo tana ganinta itama ta tsaya cak tana kallonta.


Anty salamatu ce tayi saurin miqewa tana cewa''


Zarah kece da yamman Nan sannu da zuwa.
Iyami ma cewa take"
Qaraso ki zauna zarah kinji sannu da zuwa fitar yamma.


Murmushin qarfin hali tasaki tana qarasowa ta zauna tana kallon Amatu dake kallonta tana Mata sannu da zuwa itama.


Murmushi tasaki tana cewa''


Amatu idonki kenan.


Indomin ta ajiye tana murmushi tace"


Anty zarah kedai karkice komai nakira wayarki Allah harso biyu bana samu.


Zobo anty salamatu takawo Mata suna qara gaisawa zarah tace"


Iyami wannan 'yar Taki zaneta zamu farayi sbd tashin jinta yanzu kiduba kiga yanda takasa aje fushin datakeyi damu shiyasa nazo da kaina nabata hkr tunda taqi sauraron mijinta to gani nazo Dan yau bazan fita gidan nanba saida ita.


Kallonta Amatu tayi cikeda mamaki tace"


Anty zarah.


Tsit antyn tayi sbd tsawon lokaci sai yau takirata anty zarah complete.


Juyowa tayi ta kalleta zuciyarta na rauni da damuwar datake ciki Amma tana daurewa kada ta gasa ta bude baki zatayi mgn sukaji sallamarsa dukkaninsu suka juya.


Iyami na ganinsa gaisawa kawai sukayi ta miqe ta bar gurin hakama anty salamatu.
Kallonsa zarah tayi harya qaraso gabanta baice komaiba ya kamata hannunta ya miqar da ita yace"


Let's go.


Kallonsa tayi da idanuwanta dake son cikowa ya sakar Mata murmushin dake nuna banhaqurinsa Yana girgiza Mata Kai yace"


Ita tariga ta taho gidansu ke dakike taredani bazan Bari ki barni ba,
Bazaki bawa kowa hkr ba sbd selfishness ba.


Wani irin sanyin Dadine yake kwaranya cikin zuciyarta haryana bayyanuwa Kan fuskarta tasaki wani yalwataccen murmushi tana girgiza Kai tace tunda nazo zankoma da ita idan har da akwai mutunci da ganin girma a tsakaninmu.


Gyaran muryar kawu sukaji daga bayansu suka juya Banda Amatu da abun duniya ke neman shawa Kai.
Palonsa suka nufa aka zazzauna Nan ya rufe Ido duk su dukan yayi musu fada tareda sanarwa da kowa laifinsa Kuma ya buga rantsuwar yau Amatun a gidanta zata kwana da daddare iyami da salamatu zasu kawota.


Godiyar da MAHMOUD din yaringa yiwa kawun yasa su iyami Jin wani iri sbd zarah din.
Bayan tafiyarsu Amatu Tasha kuka harta gaji iyami ta kalleta tana cewa''


Amatu kiji tsoron Allah kobaki zauna da mijinki lfy Dan Allah ba Kya zauna dashi lafiya kodan baiwar Allan Nan tasamu nutsuwa gidan aurenta,
Karki manta shifa aure hkr ne cikinsa kusan gabaki daya,
Bakiyi rayuwar zaman aureba da Khalil ya rasu sai yanxune zakiyi rayuwa Kuma wlh duk Kika dagawa MAHMOUD hankali har hakan yasa aka Shiga haqqin zarah Allah bazai barki ba,
Matar Nan koba komai wlh duk Wanda yasameta abokiyar zama ya huta a rayuwa sbd matardake danne kishin Mijinta Dan kawai a zauna lfy ai itace abarso da tattali Banda shi so yake wani dabam,
Dan haka Amatu Dan Allah ki dauke Ido ki koyi hakuri Kuma ki zauna da Matarnan tsakani da Allah kamar yanda kuke ada ni wlh tausayi take bani Kuma Ina tsananin ganin girmanta.
Itadai Amatun Banda hawaye Babu Abinda takeyi sbd hukuncin da kawu ya yanke akanta ta wani bangaren Kuma yanzunema zasu Fara tsara zaman auren dakuma kishin tunda yanxune za'a hadesu araba musu kwanan aure da komaima.


Daki Takoma anty salamatu na hada Mata sauran kayan Sha da iyamin ke hada Mata kullum tun ranarda aka Fara maganar tarewarta.


Har dare Basu Gama Shiri ba sai Bayan ishai tayi wanka ta shirya cikin wata farar lafaya da wani lace me taushi aka bita da turaruka masu sanyin qamshi suka fito bayan kawu yaqara tashi nasihar.
Andi ne dakansa ya aiko drivern dayazo daukarsu suka nufo zabeera inda ake jiran isowarsu.
##Mamuh#
6/17/21, 8:09 AM - ': *_MQ 49_*






*_THE FLAVORLAND BY ACEEY_*
Ina ma’abotan son ingataccen yaji, Different Flavors that complements each other, Yajin da ke daidaituwa da duk sinadaran abinci na al’adance da zamanance, Muna muka albishir da sanardaku cewa nesa tazo kusa domin @the_flavorland by Aceey yakawomuku duk nau’ukan yajinda kuke iya buqata Saboda yajin ya hada da:
Daddawa Yaji, Waton yajin daudawa
Garlic Yaji, waton yajin tafarnuwa da kuma
Beef Yaji, wato yajin Nama kuma me hade da nama
Domin ayukkanku da yau da kullum wanda ya hada da:
Dahuwar abinci/nau’uka na miyoyi DA
Gashe gashe da soye soye kamar su
Kaza
Kifi
Nama
Doya
Dankalin turawa/hausa
Awara
Danwake
Gurasa
Kwado da dai sauransu....
Ba Mu tsaya anan ba—â€?
The_flavorland ya hada da kayan tande tande da lashe lashe da suka hada da
Hoppers wato Fara
Milky candies wato alawar madara da kuma
Milky balls wato Gullisuwa da de sauran abunda rai ke buqata...
Zaku iya tuntubar mu a kafofin sada zumunta kamar haka
IG: @the_flavorland
Whatsapp:08104673847
Sending Some treats your way.... l


Let us satisfy your cravings:
We Deliver anywhere and everywhere.






************
Ahankali ta bude idanuwanta dake cikeda nauyin baccin dabai Gama isarta ba sbd sai Bayan sallar asuba ne tasamesa tana Gama budesu da kyakkyawar fuskarsa tafara cin karo daf da tata numfashinsu na sarquwa cikin na juna,ta kalli idanuwansa dake lumshe ta gangaro da idanuwanta Kan lips dinsa wani gajeran murmushin samun nutsuwa ya subuto Mata ta motsa hannuwanta dake sarqe cikin nasa taji yasake matsesu ta maida kallonta Kan fuskarsa da mamakin da alama idanuwansa biyu kenan?
Hancinsa taji akan nata ya hade fuskarsu ya Dora mata ta Kai idanuwanta Kan idonsa daidai Yana budesu cikin kasalar baccin dabai Gama sakinsa ba ta dauke idanuwanta ahankali daga nasa zata sake zamewa yasake qin Bata damar motsawa.


Ahankali ta bude bakinta dake daidai kunnensa cikin qaramin sautin daya qarasa kashe jikinsa da saukar Masa da kasalar tace"


Yunwa.


Daqyar ya iya bude idanuwansa dasukai laushi da yanayin yanda dumin numfashin bakinta ke shiga cikin kunnensa ta maganar datai Masa.
A kasalance ya saketa ta tashi zaune ta sauka daga Kan gadon ta nufi toilet ta Shiga.
Wanka tayo tana fitowa daureda towel brown ta nufi closet dinsa ta dauko wani sabon towel din qarami Tana sake goge kanta ta nufi gaban mirror Yana duba dryer Amma Babu a dakin ta waiwaya ta kallesa taga idanuwansa qyam akanta Yana binta dasu kamar wani mayen qarfe saita fasa tambayarsa sbd ganin hadda miskilancinsa daya hanasa tashi bare Magana sai binta yake da idanuwa ta nufi qofa ta fice zuwa bedroom dinta sbd akwai acan taganta jiya gaban mirror.


Tana Isa dakin ta zauna gaban madubin ta jonata ta kunna ta hau busarda gashin tana kallon fuskarta dake wani irin blushing da qyalli ta cikin madubi,
Tana gamawa ta gyara Kan ta daure ta shafa Neutrogena oil sai bodymist dasu spray ta qara da humra me sanyin qamshi ta miqe takoma jikin wardrobe ta bude Bata wani tsaya zabe ba ta dauko wani plain drylace peach ta saka riga da skirt ne saita fito Palo tana qoqarin nufar kicin akai Knocking ta nufi qofar ta bude,
Cikin sa'a kuwa abinci ne anty zarah ta aiko musu Dan haka saita fasa aikin ta ajiye a dining ta Kama hanyar zuwa tadoshi aka Kuma knocking taje ta bude wani abincin ne daga umme itama ta karba duk ta hada ta ajiye a dining tana juyowa da nufin zuwa tadosa saigashi yafito shirye tsaf cikin wani milk yadi me tsananin taushin daya bayyanarda tsadarsa fili ya nufota Yana kallon kwalliyarta tareda nuna yabawarsa a fili Yana Mata kallon qasa qasa daya sanyata Jin kunya me tsanani sbd kallon ya qunshi yagama da saninta cikinta da wajenta ga sauke Kai daga kallonsa tana juyawa ya riqota ya dawo da ita gefensa suka nufi dining din Yana kallonta qasa qasa da wani irin murmushi harsai data gaji cikin muryar shagwaba tace"


Dady Allah zantashi na tafi.


Qaramar Daria Mara sauti ko kadan yadan saki Yana sauya kallonsa daga kanta yace"


Ok sorry sorry na daina Zo Nan lemme feed you.


Akan cinyarsa taci abincin tana bashi Yana Bata sai sake kashe Masa jiki takeyi da rashin zamanta guri daya ajikinsa daqyar dai aka gama cin abincin ya dauketa suka koma daki tana wani zille zillen daya qarasa juyar dashi daga MD ZABEERA.




Qarfe goma sha daya harda kusan rabi suka fito tana riqeda hannunsa ta sauya wasu kayan sbd wani wankan datayi tayi simple makeup da wani irin hot red lipstick daya zauna daram Kan lips dinta dayaketa saukar hankalinsa Amma Dole ya dauke Kai suna shiga palon zarah ya saki hannunta ya nufi sama inda hafsatu tace musu tana can yatafi yabarta tana kallon hannunta daya saki domin zuwa ga wata wani rashin Jin Dadi ya taso ya rufe zuciyarta ta zauna Kan kujerun dake palon Ahankali tana Kiran sunayen Allah tareda kore shedan daga cikin Kai da tunaninta taji motsin saukowarsu ta daga Kai tana kallonsu hannuwansa duka biyun riqeda zarah din suna saukowa yanajin kamar ya daukota gaba dayanta ya sauko da ita sbd ganin yanda take tafiyar sbd tace Masa da ciwon qafafu ta kwana.


Har Kan kujerar yakaita ta zauna Rana kallonsa cikin farin cikin kulawarsa gareta tace"


Thank you MD.


Murmushi me sanyi ya sakar Mata Yana zama kusada ita yace"


Akwai godiya tsakanin miji da Mata ne?


Dariya tayi tana kallon Amatu dake qaqalo murmushi tace"


Amatu Yana tambaya tayani bashi amsa sbd zaifi ganewama idan Kika fada Masa Dan Naga yafi gane yarenki.


Maganar ta daki zuciyarsu daga Amatun har shi Musamman shi ya tsura Mata idanuwansa yanajin wani irin yanayi me nauyi na rashin Jin Dadi wato tariga da ta amincewa kanta yafi son Amatu kokuwa yafi daukar Amatun da mahimmanci akanta ko me?


Amatu ma Jin tayi nauyi da rashin Jin Dadi ya dabaibayeta take sbd maganar antyn Magana ce data fito dauke da raunin da zuciyarta ke ciki batareda tasani saitakejin sabon mutuncin antyn na sake shigarta koba komai haryanxu anty mutum ce me tsananin mutunci da ganin qimar Dan Adam duk wannan auren na bazata da akaiwa mijinta da qanwar data ke yiwa kallon uwa daya uba daya bai canzata zuwa wata daban hakama vai sauya kyawawan halayenta ba.


Kallonta tayi taga cikin Yar dariya tai maganar bakin gskiyarta batasan tayi mgnar da wata manufa Abinda yake gskia ta fada Dan haka sai itama ta qirqiro murmushi cikin batar da zancen tace"


Anty baya buqatan amsa yasan akwai godiya tsakani ma'aurata musamam ma keda kikeji da Rabin

Please Login or Register in order to submit comment