You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanakine agaba ba......


Kasa barin ya qarasa zancensa iyami tayi ta katsesa cikin tsananin mamaki da fargabar maganarsa da cewa''


Mijin Zarah fa kuke maganar aurawa Amatu idan dai MAHMOUD din Dana sani kuke Magana akai.


Wani kallo kawun yayi Mata cikin rashin fahimta yace"


Eh shifa mijin Zarah din ake Magana wani abin ne?


Ta Yaya kuke tunanin hada zarah da Amatu kishi fisabillah bayan kunsan yanda suke matuqar qaunar juna ga kishi mugun Abu ne Dan Allah ku sauya shawarar Nan idan basaso Amatun tabar zabeera gaba daya Baga Salman Nan ba sai ahadasu Amma Dan Allah Ina Amatu Ina auren mijin Zarah......


Kallon mamaki da shashanci yake yimata cikin 'yar hasala yace"


Meya kawo maganar kishi da rashin yuyiwa?
Shine yafi kowa cancantar ya riqe iyalin Dan uwansa dakuma zamowa uban Muhammadu Khalil mu shi muka duba bawai kishi ko wani tunaninku na Mata daban ba,
Yanda suke qaunar junan nasu ai shikenan sunsamu damar zama tare har abada Kuma bawai anyi ne Dan cin zarafin ita zarah din ba anyi ne sbd ganin hakan ne ya kamata,
Shi MAHMOUD tun ranar farko da akayi zancen gabansa akayi Kuma bai musaba Dan haka ni me 'ya mace bazai yiyu ace ansamu tangarda ta gurina ba Dan gaka ki aje maganar kishi da rashin yakamata a gefe tun kafin Amatun taji ta samu qarfin ji daga gareki,
Sannan Banda abinki shin ba abin farin cikinmu bane da Jin Dadi tareda kwanciyar hankali ace mun aurar da yarinyar Nan ba adaidai irin yanxu datafi buqatan Wanda zata jingina dashi amatsayin Miji Kuma uban danta,
Kina tunanin duk yanda zabeera suke qaunarta da Bata kulawa idan tana gida zaune wata ran sai ta fuskanci juyin rayuwa wani Kai tsaye zai sheganta danta,wani akan 'dan sai afasa aurenta shin kin manta irin rayuwar data fito ne bayan tsanani da jajircewar Dr khalil aka samu ta watsar da komai shine yanxu zamu vari me tadawo zaman banza Wanda bama fata amma komai zai iya faruwa.,
Ki aje maganar shaquwarsu da yakamatanki mu fuskanci ci gaban yarmu Dan kuwa aure gareta yanzu shine babban rufin asiri.


Numfashi ta sauke me nauyi kafin tace"
Dukkanin bayaninka naji amma bana saka ran wannan auren Abune da Amatun zata karba Dan kuwa Ayanda nasan tanajin zarah to zata gwammaci mutuwa ba aure data auri mijin Zarah.


Wace irin maganace wannan iyami kike fada?


Wlh maganar gskia kenan nake fada maka
Amatu bazata yarda da auren mijin antyntaba nake fada maka
Tun wuri kafin Azo aji kunya kayi Magana da ita kaji Dan Nafi kowa sanin ba amincewa zatayiba
Ai ana barin wani halak din ko Dan kunya,
Amatu tafison koba soyayya tsakaninta da salmanu ta auresa idan anyi Mata tilas dadai ta auri MAHMOUD.


Shiru kawu yayi zancen iyami na sanyasa nazari,
Idan Amatu ta bijire ta dage tabbas zasuji kunya Kuma dai Allah yasani yafi buqatar tayi aure ayanxu data zauna zaman zawarci Kuma,
Gskia bazai Bari hakan yafaru ba zai tabbatarda ta amshi wannan auren hannu bibbiyu Amma kafin Nan bazai sanar da ita komaiba sai andaura auren Inshallah ta yanda kotaqi kotaso bazata iya kubucewa aurenba.


Kallon iyami yayi Yana tattaro dukkanin hankalinsa yace"


Kada ki sanar da ita komai dangane da hakan yanxu sai Bayan auren
Kin fahimta ko?


Da mamaki tace"


Meyasa??


Sbd kada asamu damuwa.


Shiru tayi ta danyi nazari kafin ta jinjina Kai tana cewa''


To shikenan Amma dai dakun sanar da ita tukuna zaifi..


Zan aurar da ita amatsayina na ubanta Bayan auren Zan Sanar da ita alokacin danaga ya dace Dan haka na rufe zancen daga Nan.






Washe gari kamar yanda Andi yace da yamma sun aiko da kudin aure tareda sadakinsu da katin daurin auren Wanda aka bugo da safen sun karba tareda adduar zaman lfy me dorewa ga auren.


Take maganar Daurin aure ta Bazu koina sbd fitar katikan Daurin auren ga Kuma sanarwa agidanjen radio da talabijin musamman daya kasance auren mutum me suna kamar MD ZABEERA guda,


Take abokanan hurdarsa manyan mutane suka Fara Kira suna tayasa murna tareda saka zuwa Daurin auren cikin mahimman aiyukansu na washe gari.,


Umman zarah ce tafara Jin wannan mugun labarin Wanda ya sanyata cikin tashin hankali da rashin nutsuwa saidata Kira zarah din wadda daga bakin umman tata itama tafara Jin wannan mummunan labarin daya sanya qafafunta qasa daukarta ganinta ya dauke ta sulale agurin ta Fadi zaune tana qoqarin Kiran sunayen Allah Amma suna bace Mata sbd tashin hankali daqyar ta iya cafko sunan Allah daya ta furta tana lalubar wayarta tareda shiga social media take kuwa ta ringa cin karo da hotunan katikan Daurin AUREN dakuma masu cewa zasu sako hoton macen datai sa'ar shiga rayuwar MD ZABEERA akaro na biyu bayan matarsa ta farko wadda haryanxu duniya batasantaba.


*MAHMOUD DAHEER ZABEERA* da *AMATULLAH K SALEH* sune sunayen datake ta maimaitawa akan hoton Daurin auren idanuwanta nason kawo ruwa Amma tashin hankali da tsoro yaqi Bari.


Sama ta nufa dakin MAHMOUD din Wanda tun rana daya dawo ya shige bai fito ba Ashe sbd yasan fitinar daya dauko ne,


Babu bugawa yau Kai tsaye ta bude kofar palonsa ta shigo ta nufi bedroom dinsa ta tura ta shige zuciyarta na wani irin harbawa da sauri sbd gaf kwanyarta take da zautuwa,
Bayani kawai takeso daga MAHMOUD din kokuma Amatun sbd wata zuciyarta takasa yadda da wannan Abinda saitana kallon abin tamkar a mafarki Sam takasa gasgatawa.


Kwance yake Kan gadonsa ya qure AC idanuwansa a rufe daga gani ba bacci yakeyiba saidai Kuma batada tabbacin idonsa biyu,
Farin wando da farar rigace Mara hannu ajikinsa sai fararen qafafunwa dayau bai sakawa safa ba sunyi fari tas dasu tafin qafar kamar Baya taka qasa fuskarsa sai annurin kwarjini yake fitarwa take taji hankalinta yasake tashi da kishinsa duk da tasan bama Abune me yiyuwaba mijinta yaso Amatu sbd halayensu sunyi gabas da yamma sam Babu Abinda zaisa ma ya iya kula Amatun amatsayin Mata.


Qarasowa kansa tayi ta tsaya zatayi Magana sai kawai kuka ya kufce Mata Mai Dan qarfi batasan lokacinda ta durqushe agurinba tana rufe fuskarta kukan na qara tsanantuwa.


Bude idanuwansa yayi dasukai jajir sbd pressure dayashiga shima akan wannan auren Wanda yayi Magana dasu Modibbon sun nuna babu fashi kawai yaje yayi Shiri,
Bai iya hayaniyaba bare gardama da manyansa shiyasa kawai ya taho sbd bazai iya tsayawa hayaniyar gardama ba dasu Modibbo musamman da Andi yafara daukar zafi kamar zai Dora laifin akan Modibbo shiyasa kawai ya taho yabarsu suyi yanda suka dama din,
Yaso yayiwa zarah bayani Amma sbd Koda yashigo yaganta cikin walwala saiya share da nufin idan yadawo tafiya zaifada Mata idan Kuma taji shikenan saisuyi mgnar.


Tashi zaune yayi ahankali tareda miqewa tsaye Yana zuba Mata idanuwansa dasukai jajir ahankali yaringa nazarinta sautin kukanta na fita ahankali Yana shigarsa sai kawai yaji zuciyarsa da jikinsa sunyi sanyi tausayinta na sake kashe jikinsa ahankali ya durqusa ya kamota ya dagota tareda sanyata cikin jikinsa ya rungumeta sosai Yana Dan bubbuga bayanta batareda ya iya cewa komaiba.


Kusan mintuna da dama suka shanye a tsayen Yana sake Bata kyakkyawar runguma harsaida kukanta ya rage Takoma ajiyar zuciya tana sake shegewa cikin jikin nasa.


Zaunawa yayi bakin gado tareda zaunar da ita Kan cinyarsa ya kwantar da kanta Kan kafadarsa Yana hade hannuwansu cikin na juna suka damqe ya dago ya kalli cikin idanuwanta da itama shi take kallo ya sakar Mata wani kyakkyawan murmushin daya saka jikinta mutuwa ya bude baki ahankali yace"


Zarah kada ki taba tunanin bana son ki sbd irin rayuwar zaman damuke,
All my life Babu abin Dana sani Bayan kadaici,
Bansaba rayuwa da kowaba,
Bansan ta Yaya Zan sake cikin mutaneba nayi rayuwar walwala ba acikinsu,
Mutanen waje sune wainda na Dan Saba dasu sbd sune mutanen dasuka Saba Jana ajikinsu batun yanzuba shiyasa su nake iya sakewa acikinsu,


Khalil was the only family dana dauka inadashi sai Modibbo Wanda shima tsakanina dashi umarni ne kawai da bada oda,
Khalil shine kawai Dan uwana Dana sani Wanda yake tsananin qaunata da damuwa Dani tun Muna Yara harya rasu yabarni ni kadai nasake komawa tamkar banida kowa again,


Shigiwarki rayuwana da farko na dauka kamar takurawane Amma daga nabawa alaqar dama da mahimmanci saidai daga gareki ke bakya min kallon miji abokin rayuwar dazamu sake kamar kowane normal couples kina min kallon abin tsoro,
Abin shakka dakuma son muyi rayuwa kamar yanda kowannenmu ke buqata wato ta rashin shiga takurawa kowa Wanda yasani Barin muyi irin rayuwar da Kika zaba Mana wato kowa yayi nasa since you don't want to give it a chance.,


Zarah kadaki dauki wannan auren cin Amana ko cin zarafi daga garemu mu duka sbd you know me Sam Banda sha'awar wani Tara Mata,
Dagani har ita yarinyar ma Babu Wanda akai Magana dashi wannan umarninsu Modibbo ne and na amince da umarninsu sbd Inada raayin cigaba da kula da yarinyar da Muhammad so please kadaki ga laifin kowa akan maganar Nan ki mu duka muyi accepting sabon canjin dazamu samu banason doguwar damuwar dazata kawo hayaniya anan,
Idan kin kwantarda hankalinki is nothing compared to ace wani labarin ne na daban kiyi sbd kanki kiyi sbd ni Kuma kiyi sbd ita me zuwan sbd kowa ya zauna lafiya,
Kinsaba zama da ita ai so Kinga ba sabon Abu bane.


Wani qaton Abune yazo ya tsaya a maqoshi kamar zai toshe numfashinta idanuwanta dasuka Fara kumbura sukai jajir ta qurawa fuskarsa Ido tanajin da ace da Hali data cire sonsa aranta ta huta da Abinda takeji kamar zata shide,
Sai dai kamar yanda yace kowa ya dauki dangana sbd azauna lfy bazata tayarda hayaniyaba saidai tana buqatar kasancewa ita kadai yanzu sbd tunanin Abinda yakamaceta Dan kuwa idan har Amatu ce za'a aurawa MD din tanajin kamar bazata iya daukaba gwara a aura Masa kowama Banda Amatu bazata iya kishi da Amatu ba zuciyarta bugawa zatayi.


Sakinsa tayi ahankali tareda zare hannunta tana kallon cikin idonsa dashima ita din yake kallo kamar bashine yayi dogayen maganganuba yanzu din,
Sakinta yayi shima ta miqe tana share hawayenta dasuka kasa tsayuwa ta bude baki zatayi Magana saikuma ta kasa tayi saurin juya Masa baya ta tattaro jarumta ahankali ta iya bude baki ya furta"


Inshallah bazaka samu damuwaba akan hakan ta gefena saidai ka tayani da adduar cigaba da jurewa hakan.


Da sauri ta fice ta sauko da gudu ta nufi dakinta tana Shiga ta zauna tsakiyar dakin tareda fashewa da wani irin kukan tsananin baqin ciki tana rufe bakinta sbd kada ya sauko yajita.




Amatu kuwa kawu da kansa yasameta har daki cikin Daren ya zauna Kan daddumar dakin Yana kallonta da kyau cikin sauti Me nuna matuqar mahimmancin zancensa a natse yakira sunanta ta dago ta kallesa dakyau tana amsawa gabanta na tsananin faduwa..


Amatu bani na haifekiba Amma wallahi inajinki tamkar 'yar Dana Haifa ta jinina,
Kisani duk Abinda Zan iya zartarwa akan 'dan dazan Haifa Zan iya zartarwa akanku ku biyun sbd irin qauna danake muku keda Usman,
Ni ubane da bazanso ace 'yata tadawo gabanaba tana zaman jiran wani yazo gareta,
Kinyi aure cikin zuriar dasuke tsananin qaunarki da ganin mutuncinki tareda matuqar qaunar 'danki Wanda har suka kasa hakurin jure tafiyarki ki barsu,
Amatu amatsayin na na uba gareki kamar yanda na dauki kaina na zarce hukunci akanki batareda na nema shawarar kiba sbd tunanin ke din Zaki karbi duk wani hukuncina da Isa dazan nuna akanki.
Mahaifan Khalil sunzo nemawa 'dansu aurenki sun roka alfarma nakuma amince musu gashi min yanke shawarar tunda tafiya zakuyi gwara adaura auren sbd samun nutsuwar kowa duk da bataredashi zakuyi tafiyarba goben.....


Kalmarsa ta qarshe tasanyata sauke wata qaqqarfan ajiyar zuciyar da saura kadan zuciyar Tata ta buga Jin yace batare zasuyi tafiyarba kenan ba MAHMOUD bane kamar yanda ta zata da farkon zancen na kawu Wanda saura qiri ta zunduma ihun dabata shiryaba Dan tuni zuciyarta tafara harbawa ashe bashi yake nufiba
SALMAN""zuciyarta ta ayyana Mata take tayi saurin rintse ido saidai kalmomin da kawu yayi amfani dasu da farko na ikonsa akanta yasa ta sauke ajiyar zuciya Kai tsaye Dan gajarta zancen tace"


Shikenan kawu duk Abinda ka yanke akaina wallahi na amince maka Kuma Dan Allah kadaina cewa bakai ka haifemu ba sbd mu bamuda Wanda yahaifemu agurinmu idan bakaiba,
Ni yarkace zaka iya yanke kowane hukunci akaina batareda ka tambayeniba,
Tunda Dr khalil ya rasu walh Banda raayi gameda zaben miji sbd ra'ayina ya rasu tareda Mijina Dan haka Banda zabi sai Wanda kayi.


Da zallar mamaki iyami da kawun ke kallonta saidai tunda ta gajarta zancen ta amince Babu amfanin dogon bayani Bari abar zancen ahaka har zuwa bayan Daurin aure agani.


A daran kukan rashin Dr Khalil yadawo Mata sabo tayi kuka kamar mutuwarsa na sabuwa,
Ayau itace zata auri Salman mutumin data dauka aboki Kuma Dan uwa ta Yaya zatai rayuwar aure da wanin Dr dinta,
Wayarta ta janyo ta Kira anty zarah ki zataji sanyi Amma Bata daukaba kusan Kira bakwai no answer
Miqewa tayi tayo alwala tazo tahau nafila tana jaddada adduar ta ga ubangiji akan yabata juriya da hkr na rashin Dr tareda sanyawa wannan auren dazatayi dawwamà mmiyar albarka.




Koda gari ya waye anata Shirin Daurin aure itakuma da anty salamatu sunata Shirin tafiya sbd jirgin qarfe biyu zasubi Daurin auren Kuma daya da rabi ne after jumaat.


Ba wani dogon noqe noqe iyami ta hakura hakanan ta babbata wasu Yan magungunan masu kyau da qarfi tareda yimata gyaran jikin gaggawa Wanda Sam duk basa gaban Amatun hardai qarfe daya tayi aka wuce gurin Daurin auren daya Tara dubban JAMA'A aka shaida akan sadaki naira dubu hamsin kacal.


Koda Yan Daurin auren suka dawo su Amatun sungama Shirin komai na tafiyarsu sbd qarfe biyu zasu tashi shiyasa Koda kowa yadawo Dan kada asamu Yan kanzaki akayi airport dasu cikin shirinta na doguwar rigar jallabiyar Kuwait datai mugun yimata kyau Muhammad khalil na hannun anty salamatu suka fito cikin mota a airport din wayarta tayi ringin saiga sunan Dr salman zabeera ajikin wayar take taji jikinta yayi sanyi waifa yanzu mijinta ne ta sauke ajiyar zuciya tareda daukar wayar zatai magana ya rigata da cewa''


Congrats Mrs MAHMOUD DAHEER ZABEERA.


Ciro wayar tayi daga kunnenta ta kalli sunan Wanda suke wayar takuma mayarwa kunnenta tana cewa''


Salman ne??


Eh Mana nine kokina jiran Kiran mijinkine MD ZABEERA yanzu yabar zabeera Yana hanyar airport yafasa zuwa daga baya tare zasu tafi.....


Salman me Keke cewa yimin bayanin dazan fahimta waye aka daura aurena dashi kaine kokuwa sbd banason boye boye fadamin.....


Mezaisa adaura Miki aure Dani Kuma?
Da MAHMOUD ZABEERA dai aka daura muku aure........


Juwace ta dibeta tayi baya gabaki daya jikinta asaki taji antarota jikin babbar rigarsa Fara qal dabai cireba ta Daurin aure.
##Mamuh#
6/17/21, 8:07 AM - ': *_MQ 38_*






Anty salamatu da umme dake qoqarin fitowa mota jikinta duk a sanyaye itama da wannan auren Dan ganin yau anwayi gari wani ya aure iyalin Khalil dinta,
Yarinyar da Khalil dinta yafiso fiyeda komai wadda ya yarda yarabu da kowa da komai akanta yau tazama mallakin wani
Wani abin sai mutuwa Dan kuwa da Babu Abinda zai raba Khalil da Amatu idan ba mutuwarba,
Amma tunda har MAHMOUD ne ya aureta damuwarta qalilance sbd MAHMOUD dinma mutum ne me matuqar mahimmanci da girma a rayuwar Khalil Dan haka take musu fatan farin ciki me darewa a wannan auren.
Fitowa motar taqarasa Yi itada anty salamatu sukai gaba.


Qoqarin dawowa tunanin ta takeyi ga bude Ido ta rufe taga tabbas shi din ne take cikin jikinsa da qarfi ta yunqura ta qwaci jikinta tana sake kallon kyakkyawar fuskarsa dayaqi kallonta ya juya Yana cewa Mal Umar ya fiddo Masa luggages dinsa daga mota.


Sake tariyo maganar datayi da Salman tayi cikin kanta tana Dan girgiza Kai tana qoqarin yakice zancen cikin kanta sbd bama zai yiyuba ace anyi tunanin hadata aure da MAHMOUD ZABEERA Rabin ran Anty zarah,
Sam bazaima yiyuba wannan hadin Bayan ansan tsakaninta da antynta Sam Sam......


Wayarta ta daga hannuwanta na rawa sbd tashin hankali da tsoron Abinda zataji ta lalubo numbern iyami ta Danna Kira tayita ringin no answer
Da sauri ta lalubo ta kawun tayita kira shima bai daga ba kasa hakuri tayi cikin tashin hankali ta nufi su umme dasukai gaba sosai ganin Bata sauri yasa ta Fara gudu tana kiran sunan umme cikin ficewar hayyaci Dan gabaki daya kanta ya kunce gabaki daya so kawai take a qaryata Mata zancen salman zabeera a tabbatar Mata daba mijin anty zarah aka daura Mata aure dashi ba.....


Hannunta aka damqo tareda birkitota tadawo baya gaba daya cikin jikinsa akaro na biyu wannan karon cikin tsananin masifa ta juyo zatai magana idanuwanta suka Shiga cikin nasa daya zuba Mata Wanda ke bayyanar da seriousness dinsa ya bude baki bayan ya Dan kalli mutanen dake wucewa suna kallonta yanda tafara keta gudu ga jallabiyarta very attractive sbd irin me shape dinnan ce Kuma gyalen jallabiyar kawai ne tayi rolling dashi sai handbag dake hannunta...
Murya a daqile yace"


Nan ba gurin Wasa bane kokuma Zabeera you better behave yourself....


Kasa hadiye Abinda ya tsaya Mata a maqoshi tayi ta kallesa cikin masifar da batamasan tanayiba tace"


Hakama rayuwata ba abin Wasa bace kokuma Zabeera dazaka shigo batareda sani ko damata ba,
Nafasa tamabayar kowama kaga agabana Kai Zan tambaya tunda mune abin yashafa inason tabbatarda da cewan da waye aka daura aurena ayau din?


Sakinta yayi batareda ya kalletaba ya wuce Yana cewa''


She's crazy.


Biyo bayansa tayi tana sake nanata tambayar Amma ko inda take baida alamun kalla saima agogon hannunsa daya kalla yaga time yayi ya wuce Kai tsaye su umme ma tuni suka shige.,


Ganin zata Tara Masa attention na mutune dasuka Fara Binsu da kallo suna Magana qasa qasa gashi wasu sunfara ganesa Kuma da alama akwai 'yan Media agurin yasan good days dinshi sunzo qarshe dama tunda aka daura Masa aure da wannan crazy yarinyar gashi ranar farko ma zata Bata sunansa a idon mutane...,


Juyowa yayi ya fizgota da qarfi tareda kallon fuskarta Yana Kai bakinsa daf da kunnenta cikin bacin Rai Mai tsanani yace"


I swear idan baki nutsu kindawo hankalinkiba Zan tabbatarda kinyi nadamar sanin zabeera sbd right this moment Zan rabaki da Muhammad ki koma gida keda ganinsa saina tabbatarda baimasan kece mahaifiyarsa ba..


Cikowa idanuwanta sukai da wasu irin kwallar baqin ciki cikin rawar murya tace"


Bakada Imani Rabin ran Anty zarah.


Sakinta yayi tareda dagowa ya juya ya kalli yanda mutane ke kallonsu suna washe baki sbd sun burgesu sun dauka soyayya sukeyi yayi gaba batareda ya tsaya ya kalleta ba jiki amace zuciya na tafasa tabi bayansa tana ayyana irin tashin hankalin dazai biyo baya sbd har abada Babu maganar aure tsakaninta da mijin Zarah.


Acikin jirgi seat dinta ne gefen na umme sbd shi Yana first class
Tana zama ta rufe fuskarta wani irin azababben kuka ya kufce Mata ta rufe baki tahauyi zuciyarta na wani irin quna da qarfi.
Umme tasan ayi hakan shiyasa ma batai yunqurin rarrashinta ba sbd tana buqatan kukan ko taji sanyin Abinda akai matan Dan kuwa da tsananin ciwo da kunya Mara iyaka tareda nauyi a aura maka mijin Wanda ya yarda dakai tareda baka qauna Mara iyaka,
Duk su dukan Kam sai hkr Amma zarah ce tafi kowa cancantar ban hkr sbd kishiya ba Dadi musamman irin wannan ta bazata Kuma da wadda baka taba kawowaba
Gashi Amatu mace ce daba kowane namiji zaisamu ya iya Bari ba sbd ita kanta shaida ce tagani akan Khalil dinta tanadai fatar Allah yabasu rayuwa me albarka acikin wannan zaman nasu.


Ganin kukan yaqi qarewa gashi lokaci yaja tafiya tayi nisa yasa umme dafa kanta cikin kulawa da taushin murya tace,


Amatu wannan kukan dakikeyi Babu sauki ko mafitar dazai kawo Miki acikin wannan alamarin,
Aure dai anriga andaura Kuma banajin akwai abindazai warware hakan Dan haka amatsayina na tamkar uwa agareki Ina baki shawara da umarnin ki daina wannan kukan da duk wata masifa ki aje gefe neman lafiyar danki mukazo ki maida hankali mu dage muga munsamu Abinda mukazo nema,
Ki aje komai muyi Abinda yakawo mu idan yaso Bayan munyi nasara idan ankoma gida sai ayi maganar auren kinji.


Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya me qarfi akai akai sbd qarfin kukan datasha Wanda har lokacin zuciyarta Bata daina Mata zafi da ciwo ba tunanin anty zarah da halin datake ciki da irin kallon datake Mata sun kasa barinta sukuni saidai kamar yanda ummen tace su maida hankali Kan Abinda yakawosu neman lafiyar Muhammad khalil idan sun koma za'a yi Yanda za'a yi a warware auren kokuma tun anan zatasan yanda zatayi ya sawwaqe Mata tun anan suna komawa gida kowa yakama hanyarsa.


Share hawayenta tayi ahankali tareda dago idanuwanta dasukai jajir suka kumbura sbd tsananin kuka ta kalli anty salamatu taga bataga Muhammad din a hannunta ba ta bude maki cikeda mamaki zatai magana antyn ta rigata da cewa''


Yana gurin MAHMOUD.


Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda mayarda kanta ta jinginar tana rufe idanuwanta tana tuno zancensa na cewa zai rabata da Muhammad take taji kamar tsoro yanason kamata saidai Kuma ita ba anty zarah bace batajin tsoronsa tafison daganan har qasar sin tabisa akan 'danta duk inda yakaisa.


Bacci ne ya Dan dauketa sbd ciwon Kai me tsanani daya saukar Mata sbd kukan datasha har jikinta sai daya dauki zafi Wanda da wuya idan ba zazzabi bane ya damqeta ga tashin hankali,ga kuka,ga pressure,ga fargaba da tsoro duk sun hadu sun dabaibayeta Dole zazzabi ya damqeta me qarfi kuwa.


Koda jirginsu ya sauka saidai anty salamatu ta riqota suka fito sbd jiri jiri take gani.,


Basusan Yaya akaiba sai ganin wata white jaguar XK120 tayi parking gabansu yanayin motar kawai yasa umme gane MAHMOUD din ne sbd kusan duk Wanda yayi Masa farin sani yasan irin motocin dayake hawa ko a Nigeria ko aqasashen waje.


Zagayawa tayi tabude gaban motar tacewa salamatu" Zo sakata anan salamatu.


Qwacewa tafara qoqarin yi Jin ance zata shiga gaban motar umme ta kalleta ba Wasa a fuskanta tace"


Salamatu zoki shiga mutafi tunda ita Bata tashi tafiyarba.


Jin kamar ran ummen yafara baci yasa ta shiga gaban motar ahankali tareda rufewa tana jinginar da kanta tana kallo gefe zuciyarta na sake cunkushewa.


Shiru dukkaninsu Babu me Magana har suka isa wani kyakkyawan building din dake jerin wasu Athens self-contained flats.


Parking yayi acikin qatuwar harabar kafin suka firfito shine yafara wucewa gaba kansa na juyawa sbd baisan ta Yaya zai zauna da mutane acikin gidansa ba Sam baya iya zama da mutane musamman ana inda yake sakewa yayi rayuwarsa gashi harda umme.


Forth floor ne nashi Dan haka suna fitowa lift din forth floor da sunansa baro Baro dake rubuce akan qofar shiga sukaci karo *_MD ZABEERA_*


da security password yabude qofar yafara shiga tareda kunna fuse na wutar gidan take komai ya kawo haske anty salamatu ta bude Ido da baki tana kallon aljannar duniya tashigo tana kallon sama idanuwanta kaman zasu fado,
Haduwarsu da familyn ZABEERA yasa idonsu suka Dan bude da ganin rayuwar masu kudi da Kuma ganin daular masu kudi Amma anan Kam taga Abinda duk kyau da tsari tareda dukiyar zabeera Bata gani acan ba.


Umme ma data Saba da yawon qasashe Saida Nan din ha burgeta sosai ta yaba saidai flat din 2 bedrooms ne bayan master bedroom dake Dan daga gefe saman qananun stairs Wanda aka zagaye da glass door.


Sauran 2 bedrooms din Kuma sune suke kallon juna daga gefen hanyar dining can umme tace su nufa sbd ganin can ne masaukinsu danshi tuni yayi hanyar master bedroom dinsa yashige qofar glass din kafin ya nufi qofar asalin bedroom din.


Umme ce tashiga dayan bedroom din Amatu da salamatu suka Shiga daya bayan salamatu ta kwantar da Muhammad toilet tafada da sauri sbd fitsarin datake ji tun acikin jirgi Amma tsoro ya hanata ko motsawa bare tayi Magana.


Amatu kuwa bakin gado ya zauna tareda rafka tagumi tana dafe kanta dake tsananin Mata ciwo ga tunanin duniya daya kasa barinta.




Dayake dare ne Babu Wanda yadamu da wani abinci salloli kawai sukai bayan wanka suka kwanta.
Dadin AC da qamshi me sanyaya zuciya tareda gajiyar dake taredasu yasasu samun bacci me Dadi da nutsuwa.




Qarfe takwas na safe qarar doorbell yasasu fitowa kowanne a shirye sbd zuwa asibiti.
Breakfast ne umme tayi odar daga wani restaurant data bincika online Dan haka Babu Bata lokaci sukaci Wanda suka iyaci Amatu da salamatu suda Basu taba fita waje ba.


Bayan sungama anty salamatu batareda kowa ya sataba ta tashi tahau gyaran koina tana gamawa me gidan na fitowa sanye cikin qananan Kaya hannunsa daukeda key din mota da wayarsa sai zuba qamshinsa yakeyi ba kowa a palon sai anty salamatun Dan haka suna gaisawa yace ta sanarwa Amatu Yana mota tafito da Muhammad.


Yana ficewa tayi daki ta tararda ita zaune tana hawaye bayan Gama wayarta dasu kawu da iyami da

Please Login or Register in order to submit comment