You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ÿþ"[7/12, 5:29 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU

PART A

MARUBUCI:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- Abubakar Saleh AlQuyraemey

Note:- Comments da likes da share ya zama wajibi ga duk masu bibiyar wannan littafi bayan haka

"Kuma Ina yiwa kowa barka da sallah. Muna adduar Allah yasa ibadarmu karbabbiya ce, Amin "

Marubucin yaci gaba da cewa...

"Cikin sulusainin dare ne, yayinda kwanakin wata suka cika goma Sha biyu. Duk da cewa tsakiyar dare ne"

"Amma gari yayi haske fau sakamakon hasken farin wata. Gaba daya garin yayi tsit ba a Jin motsin komai sai tsirarun kukan karnuka da na Kananan kwari. Wata irin sassanyar iska ta fara busowa. A dai-dai wannan lokaci ne yayi juyi bisa gadonsa don Jin dadin barci. Babu komai a jikinsa sai wani gajeran wando, wannan wando yafi shekara Ashirin yana Amfani da shi, don tun Yana Neman auren matarsa Zuhura."

"Kallo daya mutum zayyi masa ya tabbatar da cewa barcin yayi Masa dadi. Saboda iskar da ke shiga dakin da cikin 'yar Karamar tagar dakin. Rabon da RUZYAL ya samu isasshen barci irin na yau, tun kafin hatsabibin dansa ya sace KUNDIN TSATSUBA. Tun bayan tafiyar JAFARU hankalin RUZYAL ya tashi, ya Kasa zaune ko tsaye Walau da rana ko da dare. Musamman idan RUZYAL ya tuno da Aljanin nan da yazo Masa da Batun KUNDIN TSATSUBA. Tun a sannan barci ya kaurace Masa. Abinci ya gagara shiga bakinsa"

"har tsawon kwanaki arba'in, Amma shiru Aljanin Bai dawo gareshi ba."

A bisa wannan dalili ne RUZYAL yayi shiri ya tafi izuwa ga Bokaye don Neman kubuta. Sai da ya ziyarci

"Bokaye hamsin da tara, duk Wanda ya fadawa matsalarsa sai ya koreshi yace Kar ya shafa Masa kashin Kaji. Domin Ala'marin KUNDIN TSATSUBA yafi karfinsa. Yayinda RUZYAL ya riski Bokan karshe wato na sittin, wani kasurgumin Boka ne da ke zaune a birnin kisra ana kiransa HAJARUL MUNKURUS sai ya bushe da dariya ya ce kwantar da hankalinka ya Abul-hikima. Ka sani cewa ka kawo kuka inda za'a share"

maka hawaye. Ni zan baka maganin da indai ka barbada shi a zagayen gidanka babu wani Aljani da ya Isa

ya sake bayyana a zagayen gidanka. Koda Jin wannan batu sai farin ciki ya baibaye RUZYAL ya kawo

"dukiya mai yawa ya baiwa Boka HAJARUL MUNKURUS, shi ko ya dauko wani garin magani ya bashi."

"Nan take sukayi sallama, RUZYAL ya kama hanya ya koma gida. Koda RUZYAL ya Isa gidansa ko shiga"

"gidan bayyi ba, ya fito da garin maganin nan ya barbada shi a zagayen gidansa. Don kada ma iska ta watsa shi, sai ya rinka tona Kasa da hannunsa yana binneshi. Daga wannan rana RUZYAL ya saki ransa ya cigaba da harkokinsa ya manta da batun KUNDIN TSATSUBA."

"Ba zato ba tsammani sai gidan ya kama girgiza tamkar zai bar doron Kasa, Kai kace bishiya ake son"

"jijjigowa tare da jijiyoyinta. Wata irin Kara Mai ban tsoro ta cika dakin da RUZYAL ke kwana. RUZYAL ya Farka firgigit zaune, idanuwansa suka zazzaro sukayi kwala-kwala kamar Wanda aka shake. Gaba dayan jikinsa ya kama kyarma. Ai kuwa take yayi arba da wani murgujejen mummunan Aljani Wanda ko a labari Bai taba Jin Aljani Mai muninsa ba. Take RUZYAL ya fadi Kasa sumamme. Koda ganin haka sai mummunan Aljanin ya takarkare ya bushe da bahaguwar dariya. Kawai sai ya Suri RUZYAL da yatsa guda ya aza shi bisa gadon bayansa. Cikin abinda Bai wuce dakika guda ba, Aljanin ya luluka dashi kololuwar"

sama suka bace a cikin gajimare.

Shi dai wannan Aljani da ya sace RUZYAL sunansa RAB-DA-KAGU. Yana da fuka-fukai dubu dari

"hannayensa kuwa guda dari shida ne haka ma kafafunsa. RAB-DA-KAGU na iya yin tafiyar shekara guda a cikin dakika dari. Yayinda RAB-DA-KAGU ya samu dan dogon yana tafiya a cikin gajimare sai asubahi ta riskeshi. Nan fa mugun sanyi ya kada. Ala'marin da ya janyo farfadowar RUZYAL kenan. Koda ya Bude Ido sai yaji iska Mai karfi na kadawa. Sai ya leko Kasa Nan ma sai yaga Yana hango duwatsu bishiyoyi da tekuna 'yan mini-mini tamkar 'yayan tsakuwowi, kawai sai ya kwala ihu. Sa'adda Aljani RAB-DA-KAGU yaji wannan ihu na RUZYAL sai ya mayar Masa da martanin dariya. Batare da yace da shi komai ba, sai RAB-DA-KAGU ya zura 'yan yatsunsa biyu cikin kunnensa ya zaro Boka HAJARUL MUNKURUS daga ciki yana wutsil-wutsil da kafafu. Ya Dora shi a kusa da RUZYAL sannan ya ce, shin ba wannan ne abun dogaronka ba? Shin ba wannan ne ya baka maganin mu ba? To da Kai da shi karyarku ta sha karya."

"Tabbas kowa ya tabamu zai San cewa ya tabo bala'i. Yakai Abul-hikima idan baka manta ba, a wancan karon mun turo maka wani hadiminmu ya Shiryar da Kai hanyar da za'a ajiye KUNDIN TSATSUBA cikin kyakkyawan tsaro. Wannan hadimi sunansa KARIZUL MARGUS. ka nemi ka San sunansa da na mai- gidansa Amma Bai sanar da Kai ba. Harma yace dakai ba zaka sanshi ba sai ranar da danka ya samu nasarar dauko kubar miftahuzzarbil, sannan ya Bude littafin kundin tsatsuba. To ka sani cewa wannan rana ta zo saura na mai-gidansa. Tabbas danka ya janyo maka masifar da sai ka gwammace baka kirkiri littafin KUNDIN TSATSUBA ba. Ina tabbatar maka da cewa Nanda rabin sa'a zan Isa da ku izuwa fadar shugabana Kuma Shugaban KAZIRUR MARGUS, Wanda a halin yanzu ya dade da mutuwa. Ba wani ne ya kasheshi ba sai Shugabana. Koda Jin haka sai jikin RUZYAL ya cigaba da karkarwa sannan ya dubi Aljanin cikin shakakkiyar murya yace, na rokeka da ka kasheni yanzu na huta da fargaba, domin bansan yadda zan kasance ba idan nayi arba da megidanka. Wai shin wanene Shugaban naku? Yayinda Aljani RAB-DA-"

KAGU yaji haka sai ya sake bushewa da dariya sannan ya ce me kake ci ne na baka ba zuba? Ka Kara

hakuri nan gaba kadan zaka hadu da Shugabana inyaso Kaji sunansa Kasan ance Waka a bakin me ita tafi

dadi. Daga wannan maganar RAB-DA-KAGU yayi shiru bai Kara cewa komai ba.

RUZYAL da Boka HAJARUL MUNKURUS kuwa Banda hararar juna babu abinda sukeyi. Daga can sai ruzyal

"ya ce Amma ka cika tsohon banza makaryaci. Nikam kaine ka cuceni ka jefani a cikin masifa. Meyasa ka bani maganin banza kace zai kareni daga sharrin kowane Aljani ? Maimakon Boka HAJARUL MUNKURUS yace wani Abu sai idanunsa suka cicciko da kwalla, sannan ya ce ai ba ni ne na cu-ce-ka ba Kai ne ka cuceni da har ka kirkira kundin tsatsuba. Tabbas yanzu na gano hannun Wanda muka fada. Bari na fada maka Gaskiya, idan zaka iya kashe kanka yanzu ka gaggauta yin hakan domin yin arba da Wanda ya turo a kama mu, ba karamar masifa bace. RUZYAL ya ce wanene shi? Maza ka sanar da ni. Nikam dama ai aikina kenan bincike akan abubuwan Al'ajabi. Ba zan mutu ba har sai naga ko wanene wannan takadarin Aljani da yasa ayi tsaron KUNDIN TSATSUBA. Kuma naji dalilinsa nayi hakan. Yayinda RUZYAL yazo nan a zancensa sai Boka HAJARUL MUNKURUS yace Nikam ba zakaji wannan a bakina ba. Ai gani ya Kori ji. Da gama fadin hakan sai Aljani RAB-DA-KAGU ya kyalkyale da dariyar mugunta yayita yin dariyar kamar ba zai dena ba. Bayan shafe tafiyar rabin sa'a RAB-DA-KAGU ya sauko Kasan wani gabjejen tsubiri Mai ababen Al'ajabi. Saukarsu ke da wuya RUZYAL da Boka HAJARUL MUNKURUS suka zama cikakkun 'yan kauye Banda kalle-kalle babu abinda sukeyi. A wannan waje sukaga bishiyoyi da duwatsu masu siffofin bil'adama Kuma rayayyu suna harkokinsu, kamar yadda sauran mutane ke yi. RAB-DA-KAGU ya dakawa su RUZYAL tsawa ya umarcesu dasu sauko Kasa daga Kansa. Cikin rawar jiki sukabi Umarni. Faruwar hakan keda wuya sai suka ga wani Katon dutse da ke gabansu ya bambare Kansa kamar yadda kwai ke farfashewa. Kawai sai ga wani Katon kyakkyawan gida ya bayyana daga cikin 6ararren dutsen. Girman"

gidan ya Kai wani girman wani garin. Gaba dayan gidan an ginashi da karfen Zinari.

"Wata hamshakiyar kofa ta bude, wadda Koda ita kadai mutum ya mallaka a duniya ya zama Sarkin"

attajirai. Kofar na gama budewa wasu Aljanu masu siffar Aljani RAMDAKAGU suka yi sahu-sahu suka jejjeru har inda su RUZYAL ke tsaye.

Bambancin wadannan Aljanu da RAMDAKAGU shi ne sun ninkashi girma sau goma. Kai da gani Kasan shi

ne Dan Autan su. A tsakiyar wadannan Aljanu wani siririn Aljani ne dogo zarkalele ya ratso ta cikin ta

"cikinsu yana tafiyar takama, fuskarsa cike da murmushi har ya iso gaban ruzyar da Boka HAJARUL MUNKURUS."

"A wannan lokaci aljanun duka sun kame Kam Kai kace gumaka ne saboda tsananin biyayya, Shima Aljani"

RAMDAKAGU haka ya kasance. Siririn Aljanin yayi shiga irinta sarakan bil'adama akansa akwai farin rawani. Jikinsa gaba daya lullube yake da jar alkyabba da farin rawani. Hakika shigar tayi Masa kyau. Koda yazo dab dasu RUZYAL sai ya bushe da dariya sannan ya ce lale marhabun da babban bako Abul- hikima tare da wawan Boka HAJARUL MUNKURUS. Ina Mai barka da zuwa tsubirin BAHARZUS. Ku sani

cewa daga nan zuwa duniyarku tafiya ce ta shekara dubu. Ni ne Sarki SHAMHARU Aljanin da yafi kowane

Aljani a doron Kasa sanin sirrin tsafi. Ku biyoni cikin fadata don kuji dalilin da yasa na aika Azo da ku da

"Kuma dukkanin shirina akan KUNDIN TSATSUBA. Kai tsaye SHAMHARU ya juya izuwa cikin gidan, batare da fargabar komai ba RUZYAL da HAJARUL MUNKURUS suka bi bayansa. Su ko Aljanun Nan Basu motsa ba, har sai bayan su SHAMHARU sun kule a cikin gidan sannan suma sukabi bayansu. RAMDAKAGU ne ya take masu baya, kofar ta kulle kanta. Kofar na kullewa sai 6ararren dutsen nan ya koma ya hade Kansa."

"Ma'ana gidan gaba daya ya koma cikin dutsen, Kai kace tun fil-azal gidan bai taba wanzuwa ba."

Sa'adda RUZYAL da Boka HAJARUL MUNKURUS suka tsinci kansu a cikin wannan fada sai suka dimauce

"saboda ganin irin tsananin kawar da ke ciki. Kuyangi ko da barorin da ke cikin wannan fada, kyawunsa ya Isa Kai kace su sukayi kansu. Sarki SHAMHARU yayiwa su RUZYAL nuni da wasu kujeru na alfarma. Kafin suyi wani yunkuri tuni wata irin iska ta zuke su ta zaunar da su akan kujerar. Nan fa kuyangi suka kawo masu ababen ci da Sha. Koda ganin haka sai suka yunkura da niyyar suci su Sha, Amma bisa mamaki sai sukaji cikinsu ya cika fam har sun koshi. Koda suka duba abincin da aka kawo masu sai sukaga ya ragu."

"Ala'marin da yayi matukar firgita su kenan suka kamu da tsananin mamaki. Yaushe mukaci abincin nan? Ya akayi muka koshi? Boka HAJARUL MUNKURUS ne yayi wannan tambaya ga ruzyal. RUZYAL ya ce wannan wace irin tambaya ce? Da ni da Kai fa duk tare abun ya same mu. Yadda Kaji ka gani, haka Nima naji Kuma na gani. Koda Jin haka sai Sarki SHAMHARU ya kece da wata siririyar dariya Kai kace wani tsuntsu ne yake rera Waka. A lokaci guda yayi shiru yace ya ku wadannan baki nawa, inason ku sani cewa duk abinda kuka ga ya faru yanzu kadanne daga cikin irin sihirina na tsafi. Yana gama fadin hakan sai ya tafi izuwa wata kasaitacciyar karagar mulki ya zauna. Take kuyangin nan da barori suka tsaitsaya"

kikam babu Mai alamar yin numfashi cikinsu.

Sarki SHAMHARU ya sake kyalkyalewa da dariya a karo na biyu sannan ya shiga yiwa Kansa kirari kamar

haka:-

Ni ne SHAMHARU uban takadarai. Mutum da Aljan ba su Kaini ba a sihirai. Duniyata daban da ta kowa.

"Babu me irin tawa rayuwar. Babu Wanda yasan sirrina, ni kadai nasan tsatsube-tsatsubena. Koda SHAMHARU yaxo nan a zancensa sai Kuma ya fashe da kuka harda hawaye. Lokaci guda ya dago Kai ya dubi RUZYAL sannan ya nuna RUZYAL da yatsa yace, Kai takadarin tsoho Kai kadai ne ka binciko abinda zai bayyana sirrina ga duniya. Ka sani cewa ka samu shekaru tamanin kana rubuta abubuwan Al'ajabi. To ka sani duk manyan abubuwan Al'ajabin da ka rubuta ni ne sanadinsu. Duk aikin da kake Muna biye da Kai. Bamuyi tsammanin zaka iya binciko gaba dayan sirrikanmu ba, har sai da mukaga ka rubuce su duka guda dubu Daya. A bisa wannan dalili ne mukaga ya dace mu tserar da rubutun naka mu adana shi ta yadda babu Wanda ya Isa ya Karanta shi. Saboda haka ne muka wakilta Aljani KARIZUL MARGUS akan yaje yayiwa littafinka lakani da kundin tsatsuba. Kuma ya kulleshi da kubar nan ta Miftahuzzarbil. Haka Kuma muka umarceshi da ya raba kubar izuwa sassa uku, Kuma ya kaisu karshen bangwayen duniya guda uku. Duk da hakan Kuma muka bashi Umarnin tabbatar da tsaro akan wannan kuba Amma saboda sakaci irin nasa sai ya sha'afa ya kwanta barci bisa gajiyar aikin da yayi. Kuma sai hatsabibin danka"

JAFARU da fitananniyar yarinya YALISA sukaje suka fito da Aljani MARKAHUSSABUS sukaje suka turashi

"ya dauko masu sassan kubar nan ya kawo masu, su ko suka hada kubar suka Bude kundin tsatsuba. A"

halin yanzu sun karance shafuka hudu saura shafi dari Tara da casa'in da shida. Zasu iya karance littafin nan daga zuwa shekaru Ashirin masu zuwa. Amma lallai inaso ka dakatar da su. Domin idan na kuskura na bari suka kammala Karanta shi zasu samu irin sirrin da nake takama dashi. Ni ko bani da burin da yafi ace nafi kowa nayiwa kowa Nisa. Ya zamana babu Mai taka matsayi irin nawa har abada. Domin naci

gaba da juya duniya kamar yadda ake juya waina a kaskon suya.

A halin yanzu kaf duniyar nan ni ke juya ta. Abu biyu ne kawai yake Neman kawo min miskila. Ba komai

"bane wadannan Abu biyu face musulunci da musulmai. Na yarda cewa Ubangijin musulunci yafi karfina, to Amma ba zan bishi ba Kuma bazan Bauta Masa ba. Nayi rantsuwa da uban bijirarru da takadarai wato shedan cewa komai daren dadewa sai na zama sanadin yakar musulunci da musulmai a doron Kasa. Ba zan samu nasarar yin hakan ba, har sai idan wani mahaluki Bai karance littafin KUNDIN TSATSUBA ba."

"Koda Sarki SHAMHARU yazo nan a zancensa sai ya Mike tsaye ya dubi RUZYAL da HAJARUL MUNKURUS yace ku biyoni a baya. Kai tsaye ya wuce izuwa wani dogon daki, su ko suka bishi a baya. Da shigarsu sai suka iske wadansu dogayen akwatunan gilashi rufaffu guda dari tara da casa'in da tara. A cikin kowane gilashi gangar jikin wani mutum ce. Kuma kamannin mutumin iri dayace da gaba dayan duka na sauran gilasan dari taran da casa'in da tara. Wannan gangari jiki a kame take ko motsi batayi sai guda daya ce Mai motsi. Daya Kuma ta kone tayi baki-kirin. Wadda ke motsin a bude take, a cikin akwatun gilashi har ma tana iya yin duk abinda rayayyun mutane keyi. Sarki SHAMHARU ya dubi su RUZYAL yace kunga wadannan gangunan jikin ba mutane bane ruhi ne guda dari tara da casa'in da tara. Daga cikinsu guda Daya ne na Gaskiya sauran tsafaffu ne. Wancan dake cikin budadden gilashin shi ne na gaskiyar. Kunga dai gaba dayansu siffa dayane kamanni daya. Ba siffar kowa bane face na Sarki a duniya da ake kira"

LU'UMANU na birnin TEHRAN.

A halin yanzu yayi yaki da wani makiyinmu wai shi Hubairu bn mas'ud. Shi Hubairu ya samu nasarar

"kashe LU'UMANU. To Amma abinda be sani ba shine, ba LU'UMANU ya kashe ba tsafaffen ruhinsa ya kashe. Kuyi duba izuwa wancan konannen jikin. Shi ne Ruhin da aka kashe din. Cikin sauri RUZYAL da HAJARUL MUNKURUS suka waiga suka dubi konannen jikin. Cikin matukar Al'ajabi Sarki SHAMHARU ya kyalkyale da dariya sannan ya tafi izuwa ga wannan ruhi Mai motsi ya tsaya dab dashi suka fuskanci juna sannan ya ce , ya Kai LU'UMANU kayi sani cewa ruhinka ne anan Amma Gangar jikin ka na can birnin TEHRAN. Haka Kuma kambun tsafi na nan tare dakai a damtsen hannunka. Yanzu zan sake aikawa da Kai domin Ruhin ya shiga Gangar jikinka. Domin ka karbi kasarka Kuma ka kashe babban makiyinka jarumi Hubairu bn mas'ud. Ka sani cewa a halin yanzu Gimbiya sima na tare da Aljani MARKAHUSSABUS har ya tafi da ita izuwa garinsu don a Daura masu aure. Ya zama wajibi ka dakatar da wannan daurin aure."

Kuma ka sake kamo MARKAHUSSABUS ka tsare shi a wannan kurkuku naka.

Bamu da bukatar ka kasheshi domin akwai aikin da zayyi mana nan gaba.

"Yayinda SHAMHARU ya zo nan a zancensa sai ruhi Mai motsi ya numfasa ya ce, ya Sarkin duniya me zai"

"hana ka bani Umarni na kashe dukkannin musulman duniya? Tunda su ne masu kawo mana cikas a Ala'marin mu. Kaga Nima sai na tafi izuwa ga Gangar jikina naci gaba da Jin dadin rayuwata. Yayinda SHAMHARU yaji wannan Batu sai ya bushe da dariya sannan ya turbune Fuska ya ce yakai LU'UMANU ai ba zamu samu damar hallakar da musulman duniya ba, har sai idan an rufe KUNDIN TSATSUBA wato an dena Karanta shi. Wannan shi ne dalilin dayasa na tura Azo min da wadannan mutanen biyu wato RUZYAL da HAJARUL MUNKURUS. Idan har munaso a dakatar da karatun kundin tsatsuba, dole sai an koma da baya an sake rubuta duk abubuwan Al'ajabin da aka rubuta a wancan littafin na kundin tsatsuba. Ma'ana dole ne ayi wani kundin tsatsuba na biyu. Shima Kuma ayi Masa kuba ta miftahuzzarbil. To da wannan kuba ta biyu ne za'a kulle wancan KUNDIN da ke hannunsu JAFARU. Har a kamo su Azo dasu nan na yanke masu hukunci bisa laifin da sukayi mana. Koda Jin haka sai RUZYAL yayi zumbur yace haba-haba ya ma haka zata yiwu? Shin ka manta ne cewa sai da na shekara tamanin Ina yawo kasa-kasa wurin tajirai da matsafa suna bani labarurruka Ina rubutawa? Tabbas yanzu dayawa daga cikin irin mutanen sun mutu babu damar samun irin wadannan labaran. Sa'adda RUZYAL yazo nan a zancensa sai SHAMHARU ya daka Masa tsawa yace Kai karamin me basira saurara Kaji, tarihi baya tsufa Kuma baya mutuwa. Sai dai masanansa su mutu ko su tsufa. Duk jama'ar da ka ziyarta akwai 'yayansu idan babu 'yayansu akwai jikokinsu. Indai labarin ya shafesu ko Basu sani ba, mu zamu iya sa wa su tuno da shi su"

fada Kai Kuma ka rubuta.

SHAMHARU ya sake juyowa ga ruhi Mai motsi ya dafa kafadarsa yace yakai LU'UMANU ka sani cewa

"kaine wakilinmu a bangaren masu mulkin bil'adama. Nasan cewa ba karamar gwagwarmaya zaka Sha ba. Shiyasa na baka kariya da ruhi guda dubu Daya. Saboda haka yanzu kana da sauran ruhi dari Tara da casa'in da takwas, ba zaka koma kasarka ba har sai munga bayan makiyanmu Koda kuwa duka"

wadannan ruhinan zasu kare.

Yanzun nan zan tura ruhi na biyu yaje ya shiga cikin Gangar jikinka. SHAMHARU na gama fadin hakan sai

yaje ya shafi akwatun gilashi ta biyu. Kawai sai Ruhin ciki ya ratso ta cikin gilashin sannan ya zama haske ya bace.....

Mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na BIYU part B don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen

labari Mai dadi da debe kewa

"[7/12, 5:29 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU 2

PART B

NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- Abubakar Saleh Aliyu

Note:- Comments da likes da share ya zama wajibi ga duk masu bibiyar wannan labari...

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...

"Faruwar hakan keda Sarki SHAMHARU ya bushe da dariya, Shima ruhin Mai motsi ya tayashi. Bayan"

"sunyi dariya sun more sai SHAMHARU ya kira RAMDAKAGU yace na umarceka da ka dauki Abul-hikima tare da wannan Bokan ku tafi izuwa ga mutanen nan da ya fara ziyarta a wannan lokaci. Idan basa nan, ku Nemo zuri'arsu domin su Baku labarin kuna rubutawa. Kai HAJARUL MUNKURUS amfaninka a cikin wannan tafiya shi ne, kayi Amfani da sihirinka na tsafi wajen kare ku daga sharrin hadarin Kan hanya. Kai ko RAMDAKAGU ka kasance ka gajarce maku tafiyar shekara tamanin izuwa kwana arba'in. RUZYAL Kai Kuma ka tabbatar ka rubuta dukkanin labaran da suka Baku dai-dai, batare da kayi Kari ko ragi ba. Duk Wanda yayi kuskure akan aikinsa, sakamakonsa mutuwa ne. Don haka na sallameku, ko akwai me tambaya? RUZYAL yayi gyaran murya yace yakai Sarkin duniya, meyasa kace da Boka HAJARUL MUNKURUS ya bamu kariya a yayin tafiyarmu alhalin karfin sihirinku yafi namu? SHAMHARU yayi murmushi ya ce wannan Kuma wani sirri ne daga cikin sirrikana. Kai dai kawai kubi Umarni tambaya da"

bincike ba naku bane.

"SHAMHARU na gama fadin hakan ya shige cikin wani daki, kafin RUZYAL da HAJARUL MUNKURUS suyi"

wani yunkuri tuni Aljani RAMDAKAGU ya sure su ya tashi dasu sama.

Wannan shi ne abinda ya faru ga RUZYAL ma'abocin hikima bayan an sacesu daga birnin Sin an kaishi

tsubirin BAHARZUS. Wajen da tsakaninsa da duniya tafiya ce ta shekara dubu ga JARUMIN bil'adama.

Ala'marin MARKAHUSSABUS kuwa Koda yaga ya mallaki Gimbiya sima sai zuciyarsa ta cika makil da farin

"ciki. Nan fa ya Kara kaimi a cikin tafiyarsa don ya Isa gida domin burinsa ya kusa cika. Haka dai MARKAHUSSABUS ya wanzu Yana ta sauri cikin wannan tafiya Amma sai da ya shafe kwana goma Sha uku sannan ya iso garinsu. Samaratu na kwance a cikin turakarta tanayin barci sai ga wata baiwarta me suna LUSHIZA ta rugo da gudu cikin murna. Da zuwa ta zube gabanta tace ranki ya dade yau kina da babban bako, ga danki can MARKAHUSSABUS ya dawo gida tare da abinda ya tafi nema. Koda Jin haka sai samaratu ta daka tsalle ta Mike tsaye ta dubi LUSHIZA tace lallai kinzo min da babban albishir don haka daga yau na 'yantaki. Nanfa murna ta kama LUSHIZA tayi ta godiya. Ita ko samaratu sai ta ruga"

farfajiyar gidan inda ta iske MARKAHUSSABUS dauke da Gimbiya sima tamkar Wanda ya dauko gawa.

Cikin farin ciki ta ruga gareshi suka rungume juna. Bayan tsawon lokaci ta janye jikinta daga nasa suka

"dubi, sannan ta ce ya Kai dana hakika ka cika gwarzo kuma jarumi uban jarumai. Yaya akayi kayi arba da Sarki LU'UMANU da matarsa FATISA?"

"MARKAHUSSABUS ya numfasa sannan ya ce yake Ummina ai wannan ba FATISA bace, tuni FATISA ta"

"mutu don tare aka kullemu a cikin wannan kurkukun dake karkashin Kasa na Sarki LU'UMANU. Cikin mamaki samaratu ta ce Kai dana, don me zakayi kin karya? A iya sanina babu wani mahaluki da ya taba shiga kurkukun Sarki LU'UMANU ya fito da Rai. Yaya akayi ka fito a Raye? Ita Kuma wannan kyakkyawar da ka dauko a Ina ka samo ta? MARKAHUSSABUS yayi murmushi sannan ya ce ai labari ne me tsawo."

"Yanzu dai muje ciki mu zauna, inason ki taimaka min ki tashe ta daga barci na rasa yadda zanyi na tashe"

ta.

"Samaratu ta Kara hancinta dai-dai na Gimbiya sima taji tana numfashi, sannan ta Dora tafin hannuwanta"

"akan kirjinta, kawai sai ta jijjiga Kai cikin alamun damuwa tace ai wannan barcin ba na Ka'ida bane. Sihirtaccen barci ne, idan anaso ta Farka sai anyi gagarumin aiki. Koda Jin haka sai hankalin MARKAHUSSABUS ya dugunzuma ya ce yake Ummina inaso ki sani cewa komai wahalar aikin zanyishi"

domin ta farfado a Daura mana aure da ita.

"Yanzu dai sai muje cikin turakarki mu zauna don na baki labarin tafiyata, da yadda akayi na mallaki"

"wannan kyakkyawar budurwa. Samaratu tace na yarda da batunka. Take ta juya ta nufi cikin turakar MARKAHUSSABUS na biye da ita dauke da Gimbiya sima. Bayan sun zauna a cikin turakar ne ta karbi Gimbiya sima ta je ta kwantar da ita akan gado, sannan tazo ta zauna kusa da MARKAHUSSABUS suka fuskanci juna. Batare da Bata lokaci ba MARKAHUSSABUS ya Bata labarin duk abinda ya faru a tsakaninsa da su JAFARU. Tun lokacin da suka mallaki battar karfen da yake ciki kawo yanzu. Koda ya kare sai ta numfasa ta ce hakika na yarda da masu iya magana da suka ce sai ansha wuya ake Shan dadi, Kuma"

kowa kaga ya zama wane ba banza ba.

"SAMARATU ta dubi Dan nata cikin alamun tausayawa tace, kasha wahala dana. Lallai ko zan tsaya tsayin"

"daka don ganin bukatarka ta biya. Kamar yadda ka sani cewa mahaifinka ya mutu shekaru da dama baya, Kai ya kamata ace ka gaji sarautarsa. Amma saboda Neman duniya bamu samu damar zama ba. Tabbas ko yau ka sanar da Sarki kanason sarautar mahaifinka zai nada maka rawani, ya tumbuke Wanda ke Kai yanzu. MARKAHUSSABUS yayi murmushi ya ce na San da haka Ummina. Yanzu dai kibar wannan magana"

mu dawo Kan Abar begena. Yaya za'ayi ki tashe ta daga wannan barcin me nauyi?

"SAMARATU ta numfasa tace ba zan iya yin komai ba, har sai nayi bincike. Nan take

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment