You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ina da tabbacin dana zai zo da wadannan kifaye yadda ake bukata. Da Jin wannan batu sai Sarki"

ABULHIYANU ya ce naji Kuma na amince.

Nan take Sarki yasa aka kira Sarkin yaki JAMJUS Kuma ya bashi Umarnin lallai ya Shirya Dakaru wadanda

zasu yiwa IMNAS rakiya izuwa kogin BAHARJALLUS don debo wadannan kifaye.

"Batare da Bata lokaci ba Sarkin yaki ya cika Umarni, sannan HAMZUR ya ware IMNAS gefe sukayi kus-kus,"

"Wanda ya kwantar wa da IMNAS hankali. Nan dai sukayi sallama suka fice daga cikin birnin suka nausa cikin daji. Tafiya suke ba ji ba gani suka keta koramai da dazuzzuka suna wucewa. A cikin kwanaki bakwai sai da suka yada zango sau uku. Kuma duk Inda suka yada zango sai IMNAS ya roki Sarkin yaki JAMJUS akan ya Koya masa yaki domin kare kanshi daga Muggan halittu. Shi ko JAMJUS bayyi gardamar komai ba, ya rinka koyawa IMNAS fada da dabarun yaki. Abun mamaki cikin kankanin lokaci IMNAS ya zama"

wani gawurtaccen SADAUKI na gaban kwatance Wanda har sadaukantar shi tafi na Sarkin yaki JAMJUS.

Haka dai suka ci gaba da tafiya har suka iso wani surkukin daji Mai yawan duhuwar bishiyoyi. Da shigar

"su wannan daji sai sukaji ana masu ruwan kibau, kafin su ankara tuni an kashe masu dakaru dubu biyu harda dawakansu. Cikin tsananin zafin nama JAMJUS da IMNAS suka zare takubbansu suna sare bishiyoyin dajin, kafin a jima sai ga su sun bayyana karara. Ba wasu bane face murtuka-murtukan MARIDAI. Koda sukayi arba da juna sai suka ruguntsume da azababben yaki. Nanfa wuri ya yamutse suka rinka kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama, jini ya rinka Malala tamkar magudanar ruwa ta balle. Sai da aka shafe rabin sa'a ana gumurzu Amma ko maridi daya ba a kashe ba. Duk gawarwakin da ke wajen na dakaru ne. A wannan rana sunci kayan ciki sun more. In ka dauke IMNAS JAMJUS da wasu zaratan jarumai su goma, babu wadanda ke iya agaza komai akan wadannan MARIDAI. Su ma din daf suke da gazawa. A kowane lokaci IMNAS na kusa da mahaifinsa HAMZUR Yana ta kokarin kare shi daga harin maridan Nan. Shi ko Boka HALKAMU Bai yadda ya sauko Kasa ba, Yana can sararin samaniya Yana yakarsu da sihirin tsafi Amma a banza don sihirin yaki aiki a kansu. Ana cikin wannan gumurzu ne SADAUKI JAMJUS ya lura da cewa ba karamar barna wadannan dodanni sukayi ba, domin sun kashe masu dakaru dayawa. Haka Kuma sai ya tuno da lagon maridan cewa basa Jin Sara a ko'ina sai a tsakiyar kansu. Cikin zafin nama JAMJUS yayi tsalle gami da daga takobinsa sama ya dankarawa wani dodo a"

tsakiyar ka. Take Kan ya rabe gida biyu ya fadi Kasa matacce.

Nan fa JAMJUS ya zamo tamkar tsuntsu wato ya rinka taka kawunansu da kafafunsa Yana saran tsakiyar

"kansu. Koda IMNAS yaga abinda JAMJUS keyi sai Shima yayi koyi da shi. Kafin wani dogon lokacin sun kashe sama da dubu goma. Koda dodannin nan sukaga haka sai duk suka runtuma a cikin jeji. Suka bar gawarwakin 'yan uwansu a wajen. A sannan ne Kura ta lafa su IMNAS suka tsaya suna kallon gawarwakin da ke kwance a wajen. JAMJUS ya shiga kirga gawarwakin dakarunsa, karshe ya samu adadin Dakaru dubu biyu. JAMJUS ya hada lissafi da sauran Dakarun da aka kashe Mai a baya yaga cewa an kashe mashi Dakaru dubu dubu takwas da Dari biyar, a halin yanzu ragowar dakarunsa Basu wuce dubu daya da dari da hamsin ba. Nan fa JAMJUS ya dafe Kansa sannan ya kwarara ihu Yana Mai cewa Ina ku ke matsiyatan maridai inkun Isa ku dawo filin daga. Na rantse da kaifin takobi sai mun Karar da ku komai yawanku."

"Haka dai JAMJUS yayi ta surutai har ya gaji Amma basu dawo ba, shiru kakeji kamar maye yaci shirwa. Su ko Dakarun da suka rage sai suka kama kuka saboda ganin irin kisan wulakancin da aka yiwa 'yan uwansu. A dai-dai wannan lokaci ne Boka HALKAMU ya sauko Kasa bisa tsuntsun sa. Koda suka hada Ido da JAMJUS sai JAMJUS ya harareshi yace Ina ka tafi ka barmu da wadannan dodanni har suka kusa hallaka mu gaba Daya. Koda Jin wannan tambaya sai Boka HALKAMU ya fusata ya ce, wannan wace irin maganar banza ce? Ashe Baku ga irin gwagwarmayar da muka Sha ba? Ai Ina daga sama na rinka Kai masu farmaki"

sai dai sihirina bayyi aiki a kansu ba.

"Wannan Batu na Boka HALKAMU Bai haifar da komai ba, face Kara harzuka zuciyar jamjus. Kawai sai"

JAMJUS ya daga takobinsa ya kaftawa kafadar HALKAMU Sara. Koda takobin ta bugi kafadarsa sai wata irin Kara ta tashi tamkar akan Dutse ya buga ta. Nan take takobin ta narke ta dige a Kasa. Duk da haka

"ya sake zaro wata wuka zabgegiyar gaske, ya yunkura zai kafawa HALKAMU a wuya, shi ko HALKAMU sai"

"yayi sauri ya zaro hisgar tsafinsa. Kafin Daya daga cikinsu ya ida nufinsa tuni jarumi IMNAS yayi tsalle a sama ya dira a tsakiyarsu. IMNAS ya dubi JAMJUS sannan ya dubi HALKAMU yace haba-haba, Ina hankalinku yake har ku ke kokarin hallaka juna? Ku tuna cewa gaba dayanmu nan 'yan uwan juna ne, Garinmu Daya. Tafiyarmu Daya, Kuma akan tafarki guda muke, tafarkin cika Umarnin Sarki. Duk abinda ya faru a tsakaninmu mun gani Kuma kowa a cikin wannan tafiyar ya taka muhimmiyar rawa. Yakai babban SADAUKI kayi sani cewa a farkon tafiyarmu sa'adda muka Isa dajin FASMULJIB. Ba don Boka HALKAMU ba da gaba dayanmu nan mun halaka, shi ne ya ceci rayuwarmu daga sharrin Muggan Aljanun"

"nan. A wannan dajin da muke ciki kuwa Kai ne ka cecemu, ba don Kai ba da duk mun zama gawa."

Sa'adda IMNAS yazo nan a zancensa sai jikin jamjus da Halkamu yayi sanyi duk suka sunkuyar da

"kawunansu Kasa, cikin alamun kunya. Daga can sai suka dago Kai suka dubi juna kowa ya nemi gafarar Dan uwansa, lokaci guda sukayi murmushi gami da rungume juna. Batare da Bata lokaci ba suka kama binne gawarwakin da aka kashe masu, sannan aka ci gaba da tafiya."

A kwana a tashi can sai da aka shafe wata goma Sha Daya sannan su IMNAS suka fara hango dajin

"HUSUMUL ADAF, a can nesa da su. SADAUKI JAMJUS ya Bada Umarnin a tsaya, take aka tsaya. JAMJUS ya ce ya ku 'yan uwana ku sani cewa Muna daf da shiga dajin HUSUMUL ADAF. Ku tuna cewa da can mu dubu goma ne , muke wannan tafiya Amma Kuma yanzu mun zama mu dubu Daya da Dari da hamsin"

muke wannan tafiya.

"Kamar yadda Boka HALKAMU ya fada mana a baya cewa, wannan daji da zamu shiga babu komai a"

"cikinsu face gungun 'yan fashi rukuni uku. Wadannan 'yan fashi sun kasance sadaukai ne, Kuma zaratan jarumai wadanda suka kware a iya yaki da fada. Kuma sun kasance matsafan gaske ga su da tsananin rashin Imani. Inason kowannenmu ya Karawa Kansa kwarin gwiwa, mu zage dantse iyakar ranmu domin kubuta daga hannunsu. Kai koma Boka HALKAMU ka tsaremu daga sharrin sihirinsu. HALKAMU ya ce na"

rantse da darajar tsafi zanyi iyakar karfina don tsaremu gaba Daya.

"HALKAMU na gama fadin hakan JAMJUS ya kama dokinsa ya haye, IMNAS da HAMZUR ma haka. Sannan"

"sauran Dakarun suka haye dawakansu aka dunguma aka ci gaba da tafiya. Shi ko Halkamu sai yayi masu jagora bisa tsafaffen tsuntsusa. Tafiyar dakika dari biyu da arba'in sukayi suka iso farkon dajin HUSUMUL ADAF. Da shigarsu sai sukaji an busa wani kaho Mai karfin sauti. Kafin a jima gungun 'yan fashin ya zagaye su. Adadin 'yan fashin ya Kai dubu. Su dai wadannan 'yan fashi sun kasance girda-girda tamkar mutanen farko, kowannensu yayi mummunar shigar yaki, tare da muggan makaman yaki iri-iri. Nanfa su jamjus suka zama tamkar barewa a tsakiyar garken dawa. Nanfa zuciyoyin dakarun JAMJUS suka karaya"

don sun tabbatar da cewa ajalinsu yazo. Shi ko Boka HALKAMU har yanxu Yana sama bisa tsuntsun sa sai

kallon kallo ake tsakaninsa da 'yan fashin. Shugaban 'yan fashin ya dubi su jamjus ya ce ya ku wadannan

"rafkanannu kuyi sani cewa yau Kun fado hannun Shugaban Azzaluman duniya. Yanzun nan zansa yarana suyi maku dukan kawo wuka, sannan mu kwace dukiyoyinku harda suturorinku, sannan mu kora ku"

dawa tsirara.

"Koda Jin haka sai IMNAS yayi farat ya ce, Kai Katon banza la'ananne azzalumi. Kayi sani cewa karyarka ta"

"sha karya. Lallai yau zaka San cewa ka debo ruwan dafa kanka. Na rantse da kaifin takobi na, sai mun Karar da ku gaba Daya mun kawo karshen zaluncinku a wannan jeji. Saboda tsananin mamaki da fushin wannan batu na IMNAS sai shugaban 'yan ya naushi wata murgujejiyar bishiya dake gabansa. Take hannunsa ya Burma ya nutse a cikinta ya zaro hannun ko kurjewa bayyi ba. Ita ko bishiyar sai ta kama"

rangaji a karshe ta tumbuke kanta ta fadi Kasa. Cikin tsawa ya umarci yaran nasa da su afkawa su IMNAS.

Nan fa wuri ya yamutse aka fara rubdugu. Shi ko Shugaban 'yan fashin ya tsaya Kikam a waje guda Yana

"kallon abinda ke faruwa. Boka HALKAMU ma ya tsaya cak Yana kallo, wai gaba da gabanta Aljani ya taka wuta. A wannan rana dai Dakarun JAMJUS sunga masifa irin wacce Basu taba gani ba. Da karfin tsiya 'yan fashin nan suka rinka kararraiya su. Sai dai kaga an kama mutum an matse tamkar ana matsar Mai a jikin gyada. Ba zakaji Karar komai ba sai Karar kakkaryewar Kasusuwan bil'adama. Inka dauke jarumi IMNAS da JAMJUS da Kuma zaratan jaruman nan goma babu me iya tabuka komai. Yayinda aka samu dan dogon lokaci ana wannan gumurzu sai ya rage saura su goma Sha uku kacal, daga jama'ar su IMNAS. Su ko 'yan fashin nan mutum dari kawai sukayi asara. Nan fa mutum Sha ukun nan suka gagari mutum dari Tara."

Aka jima ana Artabu ba a samu galaba ba.

Koda ganin haka sai ran Shugaban 'yan fashin ya harzuka. Cikin gaggawa ya zare takobinsa yayi tsalle ya

fada cikin taron fadan kafin a Ankara ya kashe Dakaru biyar daga cikin goman da suka rage. Koda ganin haka sai jarumi IMNAS yayi kukan Kura ya tari Shugaban 'yan fashin suka fara kafsawa. Shi ko JAMJUS sai

ya Kara kaimi ya karfafawa sauran dakarun gwiwa sukayi ta ragargazar 'yan fashin nan.

Jim kadan sai su JAMJUS suka kashe 'yan fashi dari biyar da hamsin. Yayinda 'yan fashin nan suka ga anyi

"masu mummunar barna sai suka rikide suka zama zakuna. A sannane Boka HALKAMU ya sauko Kasa ya tari zakunan ya fara Artabu da su. Sai da aka shafe sa'a hudu ana gumurzu sannan aka kashe ragowar 'yan fashin ya zamana saura Shugaban 'yan fashin shi kadai, a lokacin tuni ya galabaitar da jarumi IMNAS har ma yayi Masa kwararan Sara guda uku. Daya a Kafa daya a hannu daya Kuma a gefen cikinsa. Jikin"

IMNAS yayi fata-fata da jini nan take jiri ya debe shi ya fadi Kasa sumamme....

Tom Masha Allah..

Anan zan dakata sai wani lokacin idan Allah yasa Muna da rai.. @Najibullah Muhammad

Sai mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na BIYU part J don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen

labari Mai dadi da debe kewa

"[7/12, 5:34 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU 2

PART J

AUTHOR:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- Najibullah Muhammad 

08112778656 ( Whatsapp )

"NOTE:- Comments, likes and share are necessary and compulsory to everyone who is reading this"

prestigious book

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...

Shugaban 'yan fashin ya daga takobinsa sama da nufin ya tsire cikin IMNAS. Ala'marin da ya janyo

"HAMZUR ya kwallara ihu kenan. Ihun nasa ne ya fargad da SADAUKI JAMJUS ya waigo da sauri. Koda JAMJUS yaga abinda ke Shirin faruwa sai ya ruga da gudu yayi tsalle sama ya doki Shugaban 'yan fashin da kafafunsa biyu a kirji. Damar da be samu ba kenan ta tsire IMNAS, ya tafi da baya taga-taga kamar zai fadi. Amma sai ya tsaya kyam da kafafunsa. A lokacin ne ya lura da cewa an kashe Masa Yara da yawa sauran Kuma sun arce. Nanfa ya wangame Katon bakinsa ya takarkare ya kwarara uban ihu Wanda kararsa ta cika dajin gaba daya. Sauran nasa da suka tsere suna Jin wannan ihun suka firgice sukayi tsammanin an kashe ahugabansu, don haka sai suka Kara nausawa cikin jeji suna Neman maboya don sun tabbatar da cewa yau Kam babban bala'i ya shigo cikin jejin. SADAUKI JAMJUS ya yunkura da sauri ya daga jarumi IMNAS tsaye Amma har yanxu Bai dawo cikin hayyacinsa ba. HAMZUR ya rugo ya karbi"

IMNAS ya rungume shi yana kuka. Shi ko JAMJUS sai ya fuskanci Shugaban 'yan fashin nan suka fara

"kallon kallo. Ragowar sadaukan nan biyar suka yunkuro da niyyar afkawa Shugaban 'yan fashin, sai"

"JAMJUS ya dakatar da su ya ce ku barni da shi, duk Wanda ya zo gabansa daga cikinku take zai hallaka shi."

JAMJUS ya tari Shugaban 'yan fashin nan suka fara fafatawa. Kowannensu ya himmatu iya karfinsa

"Amma ba a Dade ana fadan ba, JAMJUS ya gane cewa ya gamu da gamonsa domin akwai fifikon karfi juriya da Jarumta a tsakaninsu. IMNAS na kwance bisa cinyar HAMZUR sai ya farfado yaga wannan gumurzu da ake tsakanin JAMJUS da shugaban 'yan fashin a lokacin tuni shugaban 'yan fashin ya samu nasarar yankar JAMJUS a damtsen hannunsa na hagu. Duk da cewar zogi da radadi sun shige shi sai ya daure yaci gaba da fadan. Cikin alamun karayar zuci IMNAS ya dago kai ya Kalli HAMZUR ya ce ya Kai Abbana wannan azzalumin yafi karfinmu. Tabbas yau ajalina yazo Ina mai rokonka da kayi min gafara. Yayinda HAMZUR yaji wannan lafazi sai ransa ya baci Bai San sa'adda ya wirgar da IMNAS ba yace kaiconka Dana Ashe kayi Watsi da nasihar nan da nayi maka? To idan ka manta zan tuna maka yanzu. Duk halin da ka shiga Kar ka fidda rai da samun nasara. Na horeka da ka karfafa zuciyarka Kuma ka ayyana a ranka cewa mu ke da nasara. Idan kayi haka nasara zata zamo a tare da mu. Koda HAMZUR ya zo nan a zancensa sai IMNAS yaji jikinsa na karkarwa zuciyarsa ta tumbutsa, jijiyoyin jikinsa suka kukkunbura sukayi budin-budin. Take yaji tamkar babu wani rauni a jikinsa. Cikin zafin nama ya dauki takobinsa ya nufi inda ake gumurzu tsakanin JAMJUS da shugaban 'yan fashin. Da zuwa ya afka Masa da"

Sara da suka bisa dole Shugaban 'yan fashin ya kyale jamjus ya koma Kan IMNAS.

Shi ko JAMJUS tuni ya cika da mamaki domin bai taba tunanin IMNAS zai rayu ba balle har ya tabuka

"wani Abu. Nanfa IMNAS ya kuntatawa Shugaban 'yan fashin ya hanashi sakat, Kai tun Yana mayar da martani har ma ya zamana cewa sai dai yayi kokarin kare Kansa. Kafin ya Ankara tuni IMNAS yayi Masa mummunan Sara guda uku, Daya aka Daya a cinya Daya Kuma a gadon bayansa. Duk da cewa jini na"

zuba a jikin Shugaban 'yan fashin Bai fadi Kasa ba saboda kasancewarsa namijin gaske.

"Ba zato sai Shugaban 'yan fashin yayi jifa da takobinsa sannan ya kama rigar jikinsa ya yayyaga ta, surar"

"jikinsa ta bayyana. Kato ne na kwatance ga tsawo ga kauri duk jikinsa a mummurde kamar an jera duwatsu. Dan fashin nan ya takarkare ya kwarara ihu fiye da Wanda yayi a baya. Koda Jin ihun sai sauran yaransa da suka gudu sukaji, nan fa suka tabbatar da cewa shugabansu na nan da ransa, don haka sai suka juyo da baya don su kawo Masa dauki. Shugaban 'yan fashin yayi girgiza ya zama wata Katuwar gada Mai tsananin girma. Tsawon jelar kadan ya Kai kamu Ashirin. Nan fa wannan kada ya addabi jarumi IMNAS ya rinka Zane shi da jelarsa Kuma ya rinka kawo Masa cafka da bakinsa Mai zako-zakon hakora."

Koda ganin haka sai Boka HALKAMU ya rikide ya zama jibgegen Guza Mai feshin wuta Nanfa suka fara

arangama.

A dai-dai wannan lokaci ne sauran 'yan fashin suka dawo. Tun kafin su iso jarumi IMNAS da SADAUKI

"JAMJUS sukayi kukan Kura suka tare su. Aka ci gaba da fafatawa, su ma ragowar dakaru biyar suka Kai masu dauki. Sai da aka shafe sa'a biyu cur ana fafatawa tsakanin Katon kada da jibgegen Guza. A hakane Guzan ya samu damar kone idon kadan guda daya, shi Kuma kadan ya samu nasarar cizon Guzan a"

kafada. Kawai sai ji akayi sunyi kururuwa a tare Kuma sun rikide sun dawo ainihin siffofinsu na bil'adama.

"Shugaban 'yan fashin ya rasa idonsa guda, shi ko Halkamu ya samu babban rauni a kafadarsa duk su"

"biyun suka kama tangal-tangal kamar sunsha giya sun bugu. Daga can duk sai suka fadi Kasa, kafin a jima Shugaban 'yan fashin ya kama shure-shure har ya mutu. Shi ko Boka HALKAMU sai faman nishi yake yi dakyar-dakyar. A dai-dai lokacin ne su IMNAS suka gama kashe sauran 'yan fashin nan. Koda suka waigo suka ga Gawar Shugaban 'yan fashin Kuma suka ga Halkamu kwance a Kasa sai suka rugo gareshi. Da zuwa IMNAS ya ciccibeshi da niyyar dorashi a Doki, sai Halkamu ya bude bakinsa dakyar ya ce ya Kai babban jarumi kada ka wahalar da kanka a banza wajen daukata, domin dafin da ke jikina bazai bari na"

Kara dakika dari ba Nan gaba.

"Ina mai Yi maku fatan Alkhairi da samun nasara bisa wannan tafiya, Ina farin ciki da mutuwa ta. Tunda na"

kashe jarumi kuma babban azzalumi Wanda ya addabi fatake shekara da shekaru. Ya Kai babban jarumi ka cigaba da kokari Koda kowa zai mutu a wannan tafiya Kai sai ka rayu. Ina mai tunasar da Kai cewa ka cigaba da tuna nasihar nan ta mahaifinka domin ita ce kadai zata ceceka a wannan tafiya har ka samu nasara. A karshe Ina mai rokonku da ku labartawa Sarki ABULHIYANU da wannan gwagwarmayar da muka Sha. Kuma lallai ya haddace labarinmu ya Kuma sanar da bayansa labarinmu domin Kar a manta

damu a duniya.

"Koda Boka HALKAMU yazo nan a zancensa sai yayi dogon ajiyar numfashi, take idanunsa suka kafe,"

"Gangar jikinsa ta sandare. IMNAS, JAMJUS, HAMZUR, da sauran dakaru biyar suka fashe da kuka. Bayan sunyi kukan sun gaji sai suka tashi suka haka rami binne Boka HALKAMU a ciki. IMNAS ya dauko wani Katon dutse ya ajiye a kabarin Halkamu sannan ya shafa jini a jikin Dutsen don ya zamo sheda. Bayan gama hakan ne, jamjus ya dubi sauran mutanensa ya ce ya ku 'yan uwana ku sani cewa yanxu mu takwas ne kadai muka rage a cikin wannan tafiya. Kuma munsha wahala matuka, gashi har yanxu bamu Kai gacci ba. Ina Mai horo a garemu da mu manta da wadanda suka mutu, Kuma mu manta da wahalar da muka Sha a baya. Lallai mu Kara karfafa gwiwowinmu ba gudu ba ja da baya ko nasara ko mutuwa, wannan ita ce akidarmu. Don haka yanzu kuzo mu Kara nausawa cikin jejin nan don mu sadu da rukunin yan fashi na biyu mu mukurshe su, muje ga na uku su ma mu Karar da su, sannan mu shiga dajin KUZMUL DAUZUM inda manyan kurayen Nan suke mu karkashesu sannan mu karasa kogin BAHARJALLUS. Yayinda jamjus yazo nan a zancensa sai HAMZUR ya numfasa ya ce bai kamata mu tafi ba Yanzu, ka dubi jikinka sannan ka dubi jikin IMNAS kuma ka dubi jikin wadannan Dakaru biyar. Gaba dayanku Kuna da raunika masu yawa, Kuma akwai tarin gajiya a jikinku, zai Fi kyau mu kwana anan kowa yayi jinyar jikinsa inyaso gobe"

da safe sai mu kama hanya.

Koda Jin haka sai IMNAS da sauran dakaru suka ce kwarai kuwa wannan ita ce shawara Mafi Alheri a

"garemu. JAMJUS ya ce na amince Kuma na gode, domin Kun tuna min da daya daga cikin dabarun samun nasarar yaki. Nan take HAMZUR ya gangara bakin wata fadama ya jefa komarsa. Cikin dakiku kadan ya kamo kifaye masu yawa, yazo da su aka kunna wuta aka hau gasa kifin kowa yaci ya koshi. Shi ko JAMJUS sai yaje bakin fadamar ya karyo ganyen wata bishiya ya dawo, da zuwa ya IMNAS guda ya ce ungo"

"wannan ka nike shi ka sa wa kowa a rauninsa magani ne me karfi, Nan take ya cika aiki."

Kashe gari da sasafe suka tashi aka sake kunna wuta aka karasa soya kifin jiya kowa yaci. Daga nan aka

"cigaba da kintse-kintse suna cikin wannan hali ne sai suka ga tsuntsu Boka HALKAMU na ta zarya a gaban kabarin ubangidansa. Tsuntsun yayi ta kewaya kabarin har sai da ya gaji sannan ya zauna, ba zato ba tsammani sai akaga hawaye na zuba a ciki idanun tsuntsun. Ala'marin da ya Basu mamaki kenan Kuma tausayi ya baibaye su. IMNAS ya tsuguna a gaban tsuntsun ya hau shafarsa idanunsa cike da hawaye ya ce ka dauki dangana kamar yadda mu ma muka dauka, tabbas Muma munsha kuka bisa rashin wannan babban gwarzo kuma jarumi. IMNAS na gama fadin hakan sai tsuntsun nan ya rikide ya zama Katon Aljani me manya-manyan fuka-fukai. Cikin tsoro IMNAS yaja da baya ya fadi. Hawaye ya xubo daga idanun Aljanin ya ce kwantar da hankalinka ya IMNAS bn HAMZUR. Kayi sani cewa ni ba tsuntsu bane"

Aljani ne.

"Fiye da shekaru hamsin baya Ina hidima ga marigayi Boka HALKAMU. Na shaku da shi matuka, Kuma ya"

kyautata min ainun. Dole ne nayi kukan rashinsa. Nayi sabo da shi Kuma nayi sabo da mutanen birnin MISRA. Yakai wannan jarumi idan ka amince zanci gaba da bibiyarku har izuwa lokacin da zaku koma birnin MISRA. Koda Jin wannan batu sai farin ciki ya lullube IMNAS sannan yace na amince mu tafi tare

"da Kai, ya sunanka."

Aljanin yayi murmushi sannan ya ce sunana SAKADAMUL KUFA. Nan take Aljanin yayu girgiza ya zama

tsuntsu shi ko IMNAS ya haye Kansa ya zauna batare da fargabar komai ba.

Sannan ya kira HAMZUR yace ya Kai Abbana taho mu tafi tare anan. Cikin sauri HAMZUR ya dane bayan

tsuntsu shi ko tsuntsun sai ya Bude fuka-fukansa ya tashi da su sama sukayi gaba. JAMJUS da sauran dakaru biyar suka bi su a baya. Sai da suka shafe sa'a guda da rabi sannan suka iso rukun 'yan fashi na

biyu. Kamar yadda wadancan 'yan fashin sukayi masu Kawanya haka ma wadannan sukayi.....

Tom Masha Allah..

Anan nake cewa ku huta lafiya sai mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na BIYU part K don Jin cigaban wannan

Kasaitacce Kuma Kayataccen labari Mai dadi da debe kewa

"[7/12, 5:35 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU

PART K

MARUBUCI:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD 

Whatsapp number 08112778656

Note:- Bayan tsawon lokaci da muka dakatar da posting din kundin tsatsuba a yau Kuma a yanzu zamu

cigaba da posting din shi. Muna fatan Allah ya taimakemu akan dukkan harkokinmu na Alkhairi Allah ya karemu daga sharrin mugayen mutane.

Marubucin yaci gaba da cewa...

"Cikin sauri HAMZUR ya dane bayan tsuntsu, shi ko tsuntsun sai ya bude fuka-fukansu ya tashi da su sama"

sukayi gaba. JAMJUS da sauran dakaru biyar suka bi su a baya bisa dawakai. Sai da suka shafe sa'a guda da rabi sannan suka iso rukunin 'yan fashi na biyu. Kamar yadda wadancan 'yan fashin sukayi masu

kawanya haka ma wadannan sukayi.

Adadin wadannan 'yan fashi ya ninka na farko domin su dubu biyu ne. Su ma manya-manya ne Amma

"babu shugaba guda daya a cikinsu. Sun kasance karfafa Kuma matsafan gaske. Ko cacar baki ba'ayi ba, 'yan fashin suka afkawa su IMLAS aka fara turnuku. Sai da aka shafe kwana guda yini Daya ana wannan gumurzu. Aljani SAKADAMUL KUFA ya taka muhimmmiyar rawa a wannan fada domin ba don shi ba, da"

"tuni su IMLAS sun halaka, saboda karfin sihirin 'yan fashin."

SADAUKI JAMJUS ya raunana sosai a wannan fada domin sai da ya Suma ya Kasa tashi. Dakarun nan

"biyar kuwa duk a wannan yakin suka mutu. Tafiyar ta rage saura mutum uku da Aljani Daya. IMLAS yayi matukar bakin ciki bisa ganin halin da JAMJUS ya shiga, domin bayyi kama da Wanda zai rayu ba. Bisa wannan dalili ne ya shawarci mahaifinsa HAMZUR da su tsaya a wannan jeji suyi jinyar JAMJUS har sai ya"

warke sannan suci gaba da tafiya.

"Koda Jin haka sai JAMJUS ya Mike cikin matukar karfin hali, ya ce na rantse da darajar mutanen Misra. Ba"

"zamu Bata lokaci a banza ba. Kuyi sani cewa zan iya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment