You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafiya. Daga Nan kafin mu Isa rukunin 'yan fashi na uku zan warware. Abinda nake so daku kawai, ku duba cikin jikkata ku dauko min ragowar maganin nan na sanyawa raunika na muci gaba da tafiya. Batare da gardama ba IMLAS yayi kamar yadda yace. Har suka Isa inda rukunin 'yan fashi na uku IMLAS na cikin matsananciyar damuwa, domin gani yake a koyaushe JAMJUS zai iya mutuwa. Da zuwansu inda 'yan fashin nan suke sai JAMJUS ya wartsake tamkar"

wani Abu bai taba faruwa dashi ba.

"Wadannan 'yan fashi sunfi rukunin na biyu yawa, karfi da tsafi. Nan fa aka kacame da azababben yaki."

"Wohoho! A wannan rana SADAUKI JAMJUS yayi gagarumar bajinta domin sai da ya kashe kaso guda daga cikin kaso uku na 'yan fashin. Sai da ya zamana Yana Sara ana saransa har aka kaishi Kasa yayi wanwar kamar ya mutu Amma daga bisani sai akaji ya Kurma ihu ya Mike. Kawai sai yaci gaba da girbar Maza, daga karshe ne sukayi Masa rubdugu sukayi ta saransa da sukarsa har suka fatattaka sassan jikinsa"

ya dena motsi.

A wannan ruguntsumin yaki ne HAMZUR ya rasa hannunsa na dama. Yayinda jarumin IMLAS yaga an

"kashe JAMJUS Kuma yaga an cirewa mahaifinsa hannu guda. Sai ya kwarara ihu ya haukace da Sara tamkar Zaki ya shigo gari Yana banke jama'a. Nanfa Aljani SAKADAMUL KUFA ya Kara samun kwarin gwiwa duk da cewa Shima ya raunana sosai. Nan fa suka hada karfi shi da IMLAS sukayi ta ragargazar 'yan fashin nan sai da dare biyu ya shude sannan suka Karar da su gaba daya. Nan take IMLAS da SAKADAMUL KUFA suka zube Kasa sumammu saboda tsananin jigata, basu farfado ba sai bayan zuwan wani daren. IMLAS na bude idanu yayi arba da mahaifinsa HAMZUR babu hannu daya zaune ya kura Masa idanu Yana zubda hawaye. Nanfa IMLAS ya fashe da kuka ya rungume mahaifinsa Yana Mai nadamar fitowa wannan tafiya da sukayi. Cikin tsananin tausayi ya dubi HAMZUR ya ce yakai Abbana yanxu saboda tsananin son duniya yasa muka shiga cikin wannan halin? Yanzu saboda bukatar mutum guda akayi asarar rayuka dubu biyu? A dalilin hakan ka rasa hannunka. Na rantse da girman Qaunar da"

nake maka. Da nasan haka zamu kasance da mun zabi zama a cikin talauci har izuwa karshen rayuwarmu.

Yayinda HAMZUR yaji wannan batu sai ya share hawayensa yace yakai dana kayi sani cewa ba Ina kuka

"bane don mutanen da suka mutu, ko don hannuna da na rasa ko Kuma don wahalar da muka Sha. Ina"

kuka ne saboda na kusa rabuwa da Kai. Tabbas bazan koma gida ba. Koda Jin haka sai mamaki ya kama

"IMLAS yace ya akayi Kasan haka? HAMZUR yayi Ajiyar zuciya sannan ya ce yakai dana inason kayi sani cewa tun kafin mu baro gida an nuna min duk abinda zai faru garemu a cikin Mafarki. Abubuwan sun faru daki-daki Banga sabanin komai ba tamkar rubutaccen labari. Kayi sani cewa zamu shiga dajin HUSMUL GAURUL inda kurayen nan suke. Kai da wannan Aljani zaku kashe kurayen gaba daya Kuma zamu Isa tekun BAHAR ZALLUS. Ni da kaina zan shiga tekun na kamo wadannan kifaye guda dari Kuma zan damka su gareka. Amma ka sani ajalina na cikin wannan kogi na BAHAR JALSUS, Amma kafin na mutu zan Amsa maka tambayar nan da kayi min. Koda Jin haka sai hankalin IMLAS ya Dugunzuma fiye da koyaushe sannan yace aikuwa idan haka ne bazan yarda muci gaba da wannan tafiya ba sai dai mu juya da baya. HAMZUR ya ce ya Kai Dana ai bakin Alkalami ya bushe dole ne mu Ida wannan tafiya babu"

makawa sai mun Isa kogin BAHAR JALSUS.

"IMLAS yayi shiru Yana tunani daga bisani yace yakai Abbana, shin a cikin mafarkin an nuna maka abinda"

zai zamo ajalinka a cikin kogin? HAMZUR ya kada Kai yace ba'a nuna min ba. IMLAS ya fashe da kuka ya rungume mahaifinsa tamkar ba zai sake shi ba. Al'amarin da ya baiwa Aljani SAKADAMUL KUFA tausayi kenan Shima ya kama kukan. Bayan lokaci Mai tsawo sai suka tashi suka hau Kan Aljanin ya tashi da su

sama suka nufi dajin HUSMUL GAURUL inda manyan kurayen nan suke.

Kamar yadda HAMZUR ya fada haka al'amarin ya kasance wato IMLAS da SAKADAMUL KUFA suka gama

da dukkan kurayen cikin rabin sa'a.

Daga nan suka wuce tekun BAHAR JALSUS. Sai da suka shafe tafiyar wata da watanni kafin su iso. Su

kwana nan su tashi can. Amma duk a tsawon wannan lokacin idan ya dubi mahaifinsa ya tuna cewa sun kusa rabuwa sai ya fashe da kuka. A ranar da suka iso bakin gabar kogin BAHAR JALSUS sai HAMZUR ya rungume IMLAS su duka suka fashe da kuka sannan sukayi bankwana. HAMZUR ya dauki komarsa ya nufi cikin kogin. Koda ganin haka sai IMLAS ya ruga ya rike shi yace ya Kai Abbana idan har ya zama dole ka shiga cikin kogin nan to sai dai na bika mu shiga tare inyaso mu mutu tare. HAMZUR yasa hannunsa guda daya Wanda ya rage ya sharewa IMLAS hawayensa yace yakai dana idan kayi haka ka shafe burin rayuwata. Kai ne bayana lallai inason na bar tarihi Kuma na bar abun alfahari. Na umarceka da kaja da

baya ka kyaleni saboda darajar kaunar da ke tsakanina da Kai.

Koda Jin haka sai jikin IMLAS yayi sanyi yaja da baya. Shi ko HAMZUR sai ya fada cikin kogin ya watsa

komarsa ya shiga yin su. Sai da ya shafe sa'a guda Yana yin su sannan ya kamo wadannan kifaye kyawawa guda dari. Koda ya dago komar tasa yaga kifayen sai farin ciki ya kama shi. Nan take ya matso gabar kogin ya ajiye komar kifin. IMLAS sai yayi arba da kifayen suna ta wutsil-wutsil. Kafin IMLAS ya

matso inda komar kifin take sai wani siririn macijin ruwa ya bayyana gaban HAMZUR ya fasa Kai sannan

ya sareshi. Faruwar hakan keda wuya siririn macijin ya bace. Cikin kururuwa da Rusa kuka IMLAS ya ruga

ya rike hannun HAMZUR alhalin sauran Gangar jikinsa na cikin kogin. Idanun HAMZUR sun kada sunyi jawur kamar gauta wata irin farar kumfa ta fara fita daga bakinsa. Cikin matukar karfin hali ya dubi IMLAS ya ce ya Kai dana kayi sani cewa wa'adina ya cika yau ne ranar rabuwarmu Kuma yau ne zan cika

alkawarin da na daukar maka.

Idan baka manta ba ka taba tambaya ta cewa meyasa bazan koya maka sana'ar su ba? Amma sai naki

"baka Amsa. To ka saurara dakyau Kaji Amsar a yanzu. Kimanin shekara talatin da biyar baya sa'adda na auri mahaifiyarka mun zauna cikin tsananin soyayya da kwanciyar hankali. A lokacin mahaifiyarka me arziki ce sosai don haka bana sana'ar komai, domin ita ce ci na da Sha na. Kuma takan bani kudade masu yawa naje nayi mata fatauci, idan na dawo duk ribar da aka samu sai ta raba ta biyu ta dauki kaso guda ta bani guda. Haka mukaci gaba da rayuwa har tsawon shekara goma Amma ko batan wata batayi ba, balle ta sa Rai da samun haihuwa. Wannan al'amarin yayi matukar tayar mata da hankali ta shiga Neman maganin haihuwa. A Kalla mun ziyarci bokaye sama da mutum dari Amma duk wajen Wanda mukaje sai"

yace abun yafi karfinsa....

Tom Nima a dai-dai nan naji matsananciyar gajiya da kasala Wanda yasa bazan iya cigaba da typing ba..

Saboda haka sai mu hadu a KUNDIN TSATSUBA NA BIYU PART L don Jin cigaban wannan Kasaitacce

Kuma Kayataccen labari Mai dadi da burgewa..


Downloaded From https://tknovels.com.ng


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment