You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abincin nan sai JAFARU ya dubi GULZUM yayi masa gwalo sannan ya hau abinci da ci.

"GULZUM ya Bata Rai sannan yace ku ne mayunwata bil'adama shiyasa cikinku ke wahalar da ku. Ni Kam Koda nan da shekara Ashirin ne, ai zan iya rayuwa ba ci ba Sha. Bisa mamaki sai Shima GULZUM yaga an kawo Masa abinci da abun Sha irin nasu na Aljanu. Batare da Bata lokaci ba ya hau kintsa cikinsa. Ita ko budurwar nan sai ta rinka kallonsu tana dariya, hakama sauran fadawan dake fadar har sai da suka kare cin abincin. Yayinda ta fuskanci sun samu natsuwa sai ta dubi JAFARU ta ce babu shakka yanxu Kun dawo"

"cikin hayyacinku. Ina so ku bani labarinku, daga wace duniya ku ka zo? Kuma ya akayi ku kazo nan din?"

Sa'adda JAFARU ya ji wannan tambaya sai yayi gyaran murya sannan ya kwashe labarinsu ya zayyana

mata. Tun daga kan lokacin da mahaifinsa RUZYAL ya hattama Kundin tsatsuba kawo yanzu. Yayinda

yazo karshe sai suka ga budurwar tayi shiru tana tunani daga can sai idanunta suka ciko da kwallah sannan ta dube su ta ce lallai Kun shigo cikin babbar masifa kamar yadda nake cikinta ni da jama'ata...

Mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na BIYU part E don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen

labari Mai dadi da debe kewa

"[7/12, 5:31 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU

PART E

AUTHOR:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD 

08112778656 ( WHATSAPP )

NOTE:- Comments da likes da share ya zama wajibi ga masu bibiyar wannan littafi

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA....

Lallai Kun shigo cikin babbar masifa kamar yadda nake cikinta ni da jama'ata. Yanzu sai ku saurara

"dakyau don kuji labarin tamu rayuwar da Kuma matsalar da muke ciki. Sunana Gimbiya SUWAILA. Ni ce gimbiyar wannan babbar Kasa ta Daulatul duniya. Daga nan zuwa can ainihin duniyar da kuke, tafiya ce ta shekara dubu arba'in. Mutane ne mu kamar ku. Bambancin mu da ku kawai shi ne, fasalin jiki da Kuma wayewar Kai. Inason ku sani wannan duniyar tamu a karkashin Kasa take, tafiyar zango dubu saba'in za'ayi daga Kan duniyar ku zuwa Nan. Ku sani cewa wannan sarauta da nake Kai na gaje ta ne, tun"

zamanin iyaye da kakanni.

Bamu da Addini Kuma bamu da wata cikakkiyar al'ada. A kullum tunaninmu bai wuce na kere-keren

"abubuwan Zamani ba. Ba zan taba mancewa ba da mahaifina Sarki KAMFUZU yace akwai wasu duniyoyi guda dari bakwai da saba'in da bakwai dake karkashin wannan tamu duniyar, Kuma a cikin kowace duniya akwai mutane kamar mu, masu yin irin rayuwarsu. Haka Kuma a Saman tamu duniyar akwai wata duniya guda Daya, Kuma ita ce wadda ku ka zo daga can. Mahaifina ya sanar damu cewa nan da shekaru dari masu zuwa, mutanen dake Kasan duniyarmu zasu shigo cikinmu su yake mu. Ya zamana sun kashe"

mazajenmu gaba daya sun mallake matanmu da duk abubuwan kere-kerenmu.

"Mahaifina yaci gaba da cewa yake 'yata, akwai hanya Daya da zamu iya maganin wadannan makiya, ya"

"zamana mun samu nasara a kansu idan suka so. Hanyar ko ita ce dole ne makeranmu suci gaba sa wasa kwakwalwar su wajen tunanin kera manyan makaman Zamani wadanda babu su a yanzu, idan mukayi nasarar haka tabbas zamu kubuta daga sharrinsu. Yaci gaba da cewa 'yata ni yanzu na tsufa sosai, nasan cewa bazan Kai wannan lokacin ba. Bayan mutuwa ta kece Zaki zama sarauniya a wannan Kasa, inason ki maida hankali akan abinda na fada maki akan wannan babban aiki na kera sabbin makamai. Lallai ku kasance kullum a cikin fafatawa da kaifin basirarku domin kera sabbin makamai saboda shine kadai"

mafitarku.

"Yayinda mahaifina yazo nan a zancensa sai na fashe da kuka nace, yakai Abbana shin idan muka samu"

"nasara akan wadannan makiya namu shikenan mun tsira daga dukkanin wani hari? KAMFUZU yayi dariya har jini ya xubo daga bakinsa, Ala'marin da ya dugunzuma hankalina kenan nayi sauri na tallafo kanshi na dorashi akan cinyata sannan na goge jinin dake bakinsa, Ina Mai cewa yakai mahaifina kada ka mutu yanzu domin ni da jama'ata Muna bukatarka. KAMFUZU yayi ajiyar zuciya dakyar sannan yace mutuwa zanyi 'yata. Saurara dakyau kiji Amsar tambayarki. Idan Baki manta ba a can baya, na gaya maki cewa a karkashin duniyarmu akwai duniyoyi guda dari bakwai da saba'in da bakwai, to a cikin duniyar da ke can karshe akwai wani mashahurin matsafi da ake kira SHAMHARU. Shi dai SHAMHARU Aljani ne ba mutum bane, Kuma bashi da wani buri Wanda yafi ya mulki dukkanin halittun duniya. Yanzu haka ya gina"

fadarsa dake duniyar sama a wani tsubiri da ake kira BAHARZUS.

Wannan matsafi ya halicci wadansu Muggan dabbobi wadanda zai rinka turosu izuwa wannan duniya

"tamu cikin kowace shekara. Idan har sukazo sai sun rushe mana gidaje Kuma sun kashe mana jama'a adadin milyan dubu daya. Haka zasu cigaba da zuwa har tsawon shekara dari. Yake 'yata kiyi sani cewa gaba dayanmu yanxu mutum milyan dubu dari ne, yanxu Kinga Ashe idan sukayi shekara dari suna zuwa zasu Karar damu. Idan har kunaso ku tsira daga wadannan dabbobi dole ne ku mallaki wani littafi me sihirin Sarki SHAMHARU. Sunan littafin KUNDIN TSATSUBA a cikinsa akwai sirrikan tsafi guda dubu daya. A halin yanzu littafin be kammala ba, domin wani mutum ne yake rubuta shi Amma tabbas zai kammalu Nan da shekara goma Sha biyar. Sa'adda mahaifina yazo nan a zancensa sai hankalina ya sake dugunzuma na sake fashewa da kuka fiye da koyaushe. Sannan na ce yakai Abbana yanxu Yaya zamuyi mu mallaki wannan littafin na kundin tsatsuba? Har ya bude Baki zai ce wani abu sai tari ya turnuke shi har ya fara aman jini, kafin mu bashi wani agaji sai mukaga idanunsa sun kafe, jikinsa ya sandare ya zamana babu wata gaba dake motsi. Koda ganin haka sai muka tabbatar da cewa ya mutu, Nan fa muka"

rushe da kuka gaba Daya mazanmu da matanmu.

Lokacin da SUWAILA tazo nan a jawabinta a lokacin idanunta sun cika SHARKAF da hawaye. SUWAILA ta

"dago kanta ta dubi su JAFARU ta ce a labarinku ka gaya mun cewa Kun mallaki wannan littafin a yanzu, to ya za'ayi ku koma duniyarku ku dauko shi ku kawo min? Ku sani cewa yau saura kwana bakwai wadannan Muggan dabbobi su zo mana. Lallai idan suka zo sai sun hallaka mutum milyan dubu daya daga cikinmu Kuma babu mamaki ku ma ku rasa rayukanku. Yayinda JAFARU da YALISA da GULZUM suka ji wannan batu sai hanjin cikinsu ya kada, dukkansu suka rude suka dimauce Basu San sa'adda suka fashe da kuka ba. Dakyar JAFARU ya dago kansa ya dubi Gimbiya SUWAILA yace yake wannan sarauniya ki sani cewa ba mu muka kawo kanmu nanba kundin tsatsuba ne ya kawo mu. Lallai bamu da iKon mu mayar da"

kanmu duniyarmu balle har na dauko kundin na kawo maki.

Koda Jin haka sai Gimbiya SUWAILA ta jijjiga Kai tace shikenan sai mu zauna zaman jiran mutuwarmu

gaba daya. Tabbas damu da ku babu Mai hanyar kubuta daga sharrin Boka SHAMHARU.

Wannan shi ne abinda ya faru da su JAFARU bayan shafi na biyar ya bude Kansa Kuma ya Karanta Kansa

Kuma ya zuke su zuwa cikinsa.

"A can birnin Sin kuwa, tun sa'adda aka gama yaki tsakaninsu jarumi Hubairu da Sarki LU'UMANU."

Jama'ar garin suka shiga cikin wani irin yanayi na dimuwa da fargaba domin Basu San irin abinda ka iya

"faruwa ba. Abu na farko dai an kashe Dakarun Kasar da dama, Kuma an kashe Sarki LU'UMANU. To waya kamata ya zama sarkinsu? Wannan tambaya ce da babu Wanda yasan amsarta."

Tsawon kwanaki bakwai dattawa da sauran masu mulki sukayi ta zaman tattaunawa don yanke hukunci

Amma hukuncin ya gagari yankewa.

Babban abinda yafi Basu mamaki shi ne har yanzu Gawar Sarki LU'UMANU na nan a cikin fadar lafiya

kalau batayi komai ba. Gawar Bata wari balle ta rube ace ta lalace. Shin be mutu bane? Ko kuwa karfin sihirinsa ne ya hana Gangar jikinsa rubewa? Tsawon kwana bakwai ko kiyashi baije kusa da Gawar ba. A tsawon kwana na bakwai ne dattawan sukazo suna shawara. Wadansu suka ce kawai a dauki Gawar aje a binneta inyaso a nada sabon Sarki don jama'a basa kafuwa sai da shugaba. Wasu ko sukace Kar a soma

wannan danyen aiki domin hatsabibancin LU'UMANU ya wuce sanin kowa.

Zai Fi kyau a Kara saurarawa zuwa wani makon. Idan Gawar bata tashi ba sai a dauke ta aje a binne. Da

"wannan shawarar akayi aiki. Nan da nan labarin abinda ya faru a fadar ya cika birnin, jama'a dayawa sukayi ta murna suna cewa shikenan sun huta da bakin mulkin Sarki LU'UMANU. Tabbas nan da kwana bakwai sabuwar rayuwa ta adalci zata kafu a birnin TEHRAN. Wasu ko wadanda suke Jin Dadin mulkin suka rinka bakin ciki domin Sarki LU'UMANU ya rungumesu suna sharholiyarsu yadda suke so. Dayawa daga cikin mutanen sune attajirai da sarakai da Bokaye da masu mulki. A ranar da Gawar LU'UMANU ta cika kwana goma Sha hudu sai dattawan nan da sarakai suka sake hallara. Yau ma kamar kullum Gawar na nan babu abinda tayi, Ala'marin da ya jefa su cikin tsananin mamaki da tambayar juna kenan. Daga can sai wani dattijo Wanda yafi kowa tsufa ya ce, yaku jama'ar birnin TEHRAN ku sani cewa alkawari"

kaya ne. Duk Wanda ya dauka dole ne ya sauke shi.

Kun sani cewa a wancan satin munyi alkawarin cewa idan muka dawo muka iske wannan gawa Bata

"tashi ba, zamu dauke ta muje mu binne hakane? Gaba dayan jama'ar suka Amsa da hakane. ZARUSA ya ce tunda hakane kuwa sai mu cika aiki. Kawai sai ya juya ya dubi wasu karti guda biyu yace Maza ku dauki Gawar nan kuje ku binneta. Cikin dari-dari Dakarun suka kama Gawar suka Dora akan wata makarar icce suka Dora, gaba dayan hannayensu karkarwa sukeyi. Inda zakace kyat, Sakin Gawar zasuyi su ruga. Bayan sun dora Gawar akan makarar sai sukayi kama-kama Daya a gaba Daya a baya sannan"

suka nufi kofar fita daga cikin fadar.

Ba zato ba tsammani sai kawai akaji wata irin guguwa ta taso Mai tsananin karfin tsiya ta turnuke fadar

"gaba daya. Nan fa ta haddasa girgizar birnin gaba daya, har sai da kowa ya kame Kam. Idanuwan mutane ne kawai ke gilmawa a dubi nan a dubi can. Kuma kowa ka duba sai kaga jikinsa na makyarkyata tamkar me zazzabi. Ba zato ba tsammani sai kawai akaga wani irin farin haske ya kutso ta cikin fadar cikin tsananin gudu ya shige cikin bakin Gawar Sarki LU'UMANU. Shigar hasken keda wuya sai bakinsa da hannayensa suka motsa. Koda masu dauke da makarar sukaga haka sai suka yadda Gawar suka ruga."

"Suma sauran jama'a suka yunkura kowa ya nemi hanyar tsira, Amma damar hakan Bata samu ba, domin"

gaba dayan kofofin fadar sun kulle kansu....

Tom mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na BIYU part F don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen

labari Mai dadi da debe kewa naku har kullum wato Najibullah Muhammad

"[7/12, 5:32 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU 2

PART F

AUTHOR:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- Najibullah Muhammad 

08112778656 ( Whatsapp )

Note:- comments da likes da share ya zama wajibi ga masu bibiyar wannan labari....

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...

"Domin gaba dayan kofofin fadar sun kulle kansu. Guguwar nan da ke kadawa ta tsaya cak, kawai sai gani"

"akayi Sarki LU'UMANU ya Mike tsaye tamkar an janyo guga daga cikin rijiya. LU'UMANU ya dubi jama'a, sannan ya dubi kowace kusurwa ta cikin fadar ya bushe da wata mahaukaciyar dariya mai firgitarwa wadda inda mace me tsohon ciki zataji, take zata kama nakuda."

"Da yawa daga cikin fadawan cikin fadar Basu San sa'adda suka rinka fitsari a wandonsu ba, wasu ko sai"

"kyarma suke suna kuka. Bayan LU'UMANU yayi dariya me yawa har ta isheshi sai ya murtuke Fuska. Sannan yace yaku jama'ata, shin Kuna tsammanin na mutu ne? To ku sani LU'UMANU na nan a raye. Yanzu ne ma zan fara rayuwar duniya. Tabbas sai naci zamanina da na 'yayana harda na jikokina da tattaba kunnena. Kuyi sani cewa wadanda sukayi murna da mutuwata zasu dandana Azaba me radadi."

Wadanda sukayi bakin ciki kuwa zasu dandana dadi mara tukewa.

Na umarceku da a cigaba da zartar da komai bisa tsarin mulkina. Yanzu zan shige karkashin Kasa inda

"kurkukuna yake domin na dauko babban makiyina Hubairu nayi Masa mugun kisa. Inaso a Shirya min kasaitacciyar walima gobe don tayani Murnar dawowata, Kuma a wajen walimar ne zan kashe Hubairu."

LU'UMANU na gama fadin hakan sai ya rikide ya zama haske ya shige cikin karkarshin Kasa. Nan take

"'yan majalisar nan suka bada Umarnin aje a Shirya walimar da za'ayi gobe, Sannan a Sanar da jama'a cewa gawa ta tashi. Nan da nan hadimai suka ruga cikin birnin don cika Umarni."

"Ala'marin Sarki LU'UMANU kuwa, yayinda ya bayyana a cikin kurkukun karkashin Kasa, sai ya iske"

"Hubairu a kwance yana barci. A can gefe guda Kuma waziri Qaddaru ne Shima yana barcin. LU'UMANU ya kece da mahaukaciyar dariya sannan yayi nuni da hannayensa biyu izuwa ga Gangar jikin hubairu da Qaddaru. Take wata irin walkiya ta bugesu suka Farka firgigit daga dogon barcin Amma sai sukaji kamar an daddauresu, domin jikinsu babu kwari ba zasu iya Koda magana ba balle suyi wani motsi."

Haka Kuma yunwa da kishirwa ta gallabesu. LU'UMANU ya sake bushewa da dariyar keta. Ya ce yakai

"Hubairu gani na dawo kamar yadda kaima ka dawo min sa'adda nake tsammanin na kashe ka. Lallai sai na dandana maka Azaba me radadi kafin na kashe ka. Kai ko Qaddaru bazan kashe ka ba, har sai na Karbo Gimbiya sima. Hubairu da Qaddaru suka zubawa LU'UMANU Ido kawai Amma sun Kasa cewa"

komai.

"Nan take LU'UMANU ya suresu da hannu daya, dashi da su din suka zama haske suka ratsa Saman Kasar"

suka fice. Washe gari da hantsi gaba dayan jama'ar birnin TEHRAN suka hallara a kofar fada don Amsa Kiran Sarki LU'UMANU. A tsakiyar fadar aka kafe wasu dogayen itatuwa guda biyu masu gwafa. A jikin itatuwan ne aka daure jarumi Hubairu da Qaddaru. Kallo Daya zakayi masu Kasan cewa suna cikin mawuyacin Hali domin dakyar suke bude idanunsu. Idan ma suka bude idon dishi-dishi suke ganin komai. Makada da mawaka ko suka taru kowa na nuna hikimarsa. Sai bayan rabin sa'a sannan aka hango Sarki

LU'UMANU ya fito daga cikin gidan sarautar.

"Yana tsaye bisa wata koriyar darduma tana tafiya dashi cikin iska. A lokacin yayi shigar yaki, wasu"

"bakaken kaya ne a jikinsa, daure a kugunsa wata zabgegiyar takobi ce. Dardumar sai ta sauko Kasa da shi, dai-dai inda karagar mulkinsa take. Koda ya sauka daga kan dardumar nan sai ta nannade kanta ta"

jingina da jikin karagar. Shi ko sai ya zauna akan karagar Yana Mai murmushi cikin annashuwa da farin

"ciki. Zamansu keda wuya wuri yayi tsit, bakajin komai sai sautin iskar da ke kadawa."

"SARKI LU'UMANU yayi gyaran murya yace yaku jama'ar TEHRAN. Ban kira ku nan ba, sai don idanunku"

"suga zahiri ku tabbatar da cewa Ina nan da Raina ban mutu ba. Na umarceku da kowa yayi sujjada a gareni. Kafin LU'UMANU ya gama rufe bakinsa tuni milyoyin jama'ar dake wajen sun sunkuyar da kawunansu Kasa. Shi kadai ne ya rage a sama a tsaye. Koda ganin haka sai murna ta kamashi, yaji dadi a"

ransa. Nanfa ya kama kirari Yana Mai cewa.

Ni ne LU'UMANU Sarkin duniya. Ni ne JARUMIN da ya gagari jarumai. Ni ne Wanda baya mutuwa. Kuma

ni ne Wanda ba a samun nasara a kaina. Na gagari mutanen duniya da aljanun duniya. Ina wani da namiji da ya cika zakara? Ya tashi yayi cara a gabana idan ya Isa. Karya ku ke makiya ga dodon ku LU'UMANU ya dawo. Da jininku zai wanke Kasar duniya.

Bayan LU'UMANU ya gama wannan kirari sai ya Bada Umarni da a Mike daga sujjadar da akayi. Nan take

kowa ya daga sannan ya Bada izinin a fara walima. Nan fa barori da kuyangi suka fara fito da abinci da abun Sha launi-launi. Sarakai da jarumai da attajirai suka hau bushasha. Makada da mawaka sukaci gaba da aikinsu. Wasu kyawawan 'yan mata suka fito tsakiyar fadar tsirara suka rinka tikar rawa. Wasu

kuyangi kuwa suka rinka shayar da manyan Kasar ruwan barasa.

Shi kanshi Sarki LU'UMANU wani Katon tulun giya ya Kafa a bakinsa Yana kwalkwala. Cikin dakiku kadan

"ya shanyeshi, Kuma ya nemi Kari. Sai da ya shanye tulu uku Amma Bai bugu ba. A Ka'idar wannan giya ko cikon kofi mutum yasha sai ya bugu. Sai da aka shafe sa'a biyu ana sharholiya sannan Sarki LU'UMANU yayi tsawa kowa ya natsu."

"LU'UMANU ya dubi wani bawa yace ya dauki ruwa yaje ya hau tsani ya shayar dasu Hubairu, wadanda ke"

"can sama daure a jikin itatuwa. Nan take bawan ya cika aiki, Hubairu da Qaddaru suka farfado idanunsu suka rinka gani sosai harma suka iya ganin komai da kowa. Sai dai ko kadan babu kuzari a jikinsu."

Hubairu yayi arba da Sarki LU'UMANU sai ya cika da tsananin mamaki sannan yace yakai wannan Sarki

"shin ba na kashe ka ba, sa'adda mukayi gagarumin yaki?"

Koda Jin haka sai LU'UMANU ya kece da dariya harda faduwa Kasa daga Kan karagarsa. Daga can sai ya

"Mike ya koma kan karagar ya zauna. Ya fuskanci Hubairu ya ce kwarai kuwa a wancan karon ka kasheni. Amma na sake rayuwa. Cikin tsananin fushi Hubairu ya ce karya kake munafikin Allah, kaiconka. Lallai kana daga cikin Manyan mushirikai makafirtan bayi. Kayi sani cewa rai guda daya ne, Kuma ba a mutuwa"

a dawo. Tabbas Ubangijina ne kadai yake kashewa da rayuwa.

"LU'UMANU ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya murtuke Fuska ya ce karya kake, kayi"

sani cewa ni Raina guda dubu ne. Yanzu ka kashe guda Daya saura Dari Tara da casa'in da tara. Ina sanar dakai cewa a halin yanxu karfina da karfin sihirina ya ninka na da sau dubu. Don haka Koda duniyar nan zata taru a kaina ba za'ayi galaba a kaina ba. Yau ka shiga hannuna Kuma bazaka iya kare kanka da komai ba. Yanzun Nan zan sa ayi maka kisan gilla ta hanyar yankan namanka da kadan-kadan gutsin-gutsin har

sai anyi gunduwa-gunduwa dakai.

Ina Ubangijin naka da kake takama dashi? Yazo Nan ya ceceka mugani. Sa'adda LU'UMANU ya zo nan a

"zancensa sai Hubairu ya ce Ubangijina Mai iya kareni ne daga dukkan sharrinka. Domin shi ne yayika Kuma shine yayi ni da kowa da kowa. Da izininsa kakeyin duk abinda kaso. Tabbas idan lokacinka ya cika zaka zamo ba a bakin komai ba. Koda Jin haka sai LU'UMANU ya sake kecewa da dariya yace babu abinda zaku iya yimin dakai da Ubangijin naka. Taka ta kare, Kuma sai na Karar da dukkanin ire-irenka da ke doron Kasa. Yana gama fadin haka ya dubi bawan nan yace cika aikinka. Bawan ya fito da wata"

"sharbebiyar wuka, wadda girmanta yafi na adda kaifinta kuwa yafi na reza."

Cikin azama bawan ya fara Hawa tsanin da Hubairu ke Kai don ya Kai gareshi. Hubairu ya yunkura don ya

"kwance daurin da aka yiwa hannuwansa da kafafunsa Amma sai yaji ya Kasa domin ko kadan babu kwari a jikinsa. Ya sake Bude bakinsa da nufin yayi addu'a Amma sai yaji ya Kasa, hakoran sama suka hade da na Kasa tamkar an sa kuba..."

Nanfa Hubairu ya rungumi kaddara yaci gaba da sauraren mutuwarsa. Shi ko wannan bawa me

"sharbebiyar wuka sai ya Kara Azama har ya Isa ga Hubairu. Da zuwa ya caka wukar a cinyar Hubairu, kaifin wukar ya ratsa a cinyar jini yayi tsartuwa. Hubairu yaji wani irin mugun zogi ya shige shi. Amma Bai samu damar yin ihu ba kasancewar bakinsa a kulle. Kafin wannan bawa ya jayo wukar kasa da nufin farke cinyar Hubairu, sai akaga an doko shi ya fado Kasa. Nan take wuyan bawan nan ya karye Kuma ya"

mutu ko shurawa bayyi ba.

Cikin hanzari LU'UMANU ya daga Kansa sama sai yayi arba da Aljani AFTARUL-HUDES dauke da masa'ud

"mahaifin jarumi Hubairu. Duk su biyun sun kasance suna masu Karanta wadansu addu'o'i na neman tsari. Koda ganin haka sai LU'UMANU ya dubi tsafaffiyar dardumarsa Nan take dardumar ta warware kanta shi Kuma ya haye kanta ta tashi sama dashi, ya nufi inda su HUBAIRU suke. Kafin su Isa wajen tuni masa'ud"

yayi wata addu'a ya tofawa Hubairu.

Nan take Hubairu yaji wani irin gagarumin karfi ya shige shi. Kawai sai yayi kururuwa ya tsittsinka igiyar

da ta daure shi ya fado Kasa Kuma ya dira da kafafunsa lami lafiya. Cikin gaggawa masa'ud ya cillowa

jarumi Hubairu takobi. A dai-dai wannan lokaci ne LU'UMANU ya iso gabansa ya kawo Masa wani wawan

sara da takobi da nufin ya tsinke Masa wuya.

"Hubairu yayi Maza ya kare saran, Koda takubban nasu suka hadu sai tartsatsin wuta ya tashi, Nanfa suka"

"fara dauki ba dadi suna kaiwa juna sara da suka. Nan fa suka hargitsa wajen, domin duk abinda suka sara sai kaga abun ya lalace ya kama da wuta. Cikin kankanin lokaci gagarumar wuta ta kama fadar gaba daya. Mutane ko sukayi ta guje-guje da iface-iface kowa na kokarin tsira da rayuwarsa."

"Ala'marin Aljani AFTARUL-HUDES kuwa, sai ya tsaya kyam a sararin samaniya har yanzu masa'ud na"

"zaune a Kansa. Kuma duk su biyun Basu dena yin addu'a ba. Fada yayi fada gumurzu yayi gumurzu tsakanin Sarki LU'UMANU da jarumi Hubairu, ya zamana karfi yazo daya. Domin babu Wanda ya samu nasara. Kuma babu me alamar samun nasara. Fadan na Kara tsamari suna Kara samun kuzari, Kai kace ba mutane bane na'urori ne. Sai da suka samu sa'a uku cur suna wannan dauki ba dadi. Yayinda Sarki LU'UMANU yaga wankin hula zai kaishi dare. Sai ya sauya salon fada ya fara Amfani da karfin tsafi Yana"

"watsawa Hubairu mugayen abubuwa, kamar irinsu farar wuta, kibau, masu da sauransu."

Cikin iKon Allah duk abinda ya taba jikin hubairu sai ya narke ya zama ruwa. Yayinda aka shafe tsawon

"lokaci a haka, sai Shima Hubairu ya fara karanto wasu addu'o'i da nufin ya tofawa LU'UMANU. Da zarar ya tofa yawun sai LU'UMANU ya bace, duk abinda yawun ya samu sai kaga dagargaje ya kone kurmus."

Haka dai akaci gaba da wannan badakala har tsawon lokaci Mai yawa dayansu Bai samu nasara ba. Ana

cikin hakane Aljani AFTARUL-HUDES yayi Kasa ya Suri jarumi Hubairu yayi sama da shi....

Tom Masha Allah..

Sai mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na BIYU part G don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen

labari Mai dadi da debe kewa

Najibullahi Muhammad ke maku sallama tare da fatan Alkhairi

"[7/12, 5:32 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU 2

PART G

AUTHOR:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- Najibullah Muhammad 

08112778656 ( Whatsapp )

Note:- comments da likes da share ya zama wajibi ga masu bibiyar wannan labari

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.....

Kafin LU'UMANU yayi wani yunkuri tuni AFTARUL-HUDES ya bace a cikin gajimare. Cikin tsananin fushi

"Sarki LU'UMANU ya shafi dardumar tsafinsa ta luluka dashi sama, yayi ta shawagi a sararin samaniya Gabas da yamma kudu da Arewa Yana Neman su jarumi Hubairu Amma ko alamunsu Bai gani ba."

Ala'marin da yayi matukar hargitsa zuciyarsa kenan ya sauko Kasa ya dira a fadarsa inda ya iske mutanensa na ta kokarin kashe wutar da ke ci. Nan take yasa aka kwance Qaddaru yasa aka kaishi kurkukunsa aka kulle. Sannan ya fito da madubin tsafinsa ya shafe shi. Take Boka SHAMHARU ya bayyana a jikin madubin Yana Mai kyakyata dariyar mugunta. Sai da ya dena dariyar sannan LU'UMANU

ya ce ya Shugabana meyasa baka bani sa'a ba akan makiya?

SHAMHARU yayi guntun murmushi ya ce karka damu LU'UMANU Muna da cikakkiyar hujja akan hakan.

Ka sani cewa komai da lokacinsa. Da Sannu zaka kakkabe ire-irensu daga doron Kasa. SHAMHARU na

"gama fadin hakan fuskarsa ta bace daga jikin madubin. Shi ko LU'UMANU sai ya mayar da mudubin tsafin cikin aljihun rigarsa, ya zauna akan dardumarsa ta tashi dashi zuwa cikin gidan sarautar."

Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin jarumi Hubairu da Kuma Sarki LU'UMANU a birnin TEHRAN bayan

sun gwabza gagarumin yaki a lokacin da Aljani AFTARUL-HUDES ya kawo dauki.

"Ala'marin RUZYAL, Boka HAJARUL MUNKURUS da RAMDAKAGU kuwa sai da sukayi Nisa da tsubirin"

BAHARZUS suna tafiya a cikin gajimare sannan HAJARUL MUNKURUS ya dubi RUZYAL yace shin zaka iya

tunowa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment