You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta Bude wata"

"tsohuwar akwatun karfe wadda tayi budin-budin da Kura harma Yana ta soma lullubeta. SAMARATU ta fito da wani madubin tsafi daga cikin akwatun Shima sai da ta hure kura daga jikinsa da iskar bakinta. Sannan ta fara Karanta wadansu dalasiman tsafi kafin a jima ta jike sharkaf da GUMI, sai dai tayi atishawa sau uku sannan ta ajiye madubin tsafin, ta dubi MARKAHUSSABUS a wannan lokaci idanunta"

sunyi jawur tamkar an bada mata barkono.

SAMARATU ta ce ya Kai dana abun soyuwa a raina hakika banji dadin abinda na gano ba a cikin bincikena.

Domin wahalar da zakasha nan gaba ta ninka wadda kasha sau Dari. Idan har kana son ka Auri wannan

kyakkyawar yarinya to sai kasha wahala. Maimakon jikin MARKAHUSSABUS yayi sanyi sai yayi murmushi ya ce yake Ummina ai kowane da namiji an haifeshi ne don yayi wahala musamman akan mata.

Duk irin abinda mutum ya Tara a duniya karshenta abun ya kare wajen kyautata masu

Ni Ina ganin babu sabon labari don na wahala akan auren Gimbiya sima. Na rokeki da ki sanar dani

"abinda ya kamata nayi don magance wannan matsala. SAMARATU ta numfasa tace zanyi maka tambaya guda daya kafin na sanar dakai abubuwa guda uku wadanda zaka samo a tashi Gimbiya sima. Ka sani cewa dole ne ka samo wadannan abubuwan a cikin mako guda. Idan ka wuce wannan lokaci sima zata mutu. Don Kasan cewa ita bil'adama CE ba kamar mu ba Aljanu. Su bil'adama basa iya doguwar rayuwa muddin babu ci da sha. Kafin nayi maka tambayar inaso na sanar dakai cewa akwai wani babban yaki a gabanka bayan ka Auri Gimbiya sima. Yakin ko ba na komai bane, sai na mallakar zuciyarka ta so ka"

kamar yadda kake Qaunarta. Ka sani cewa tuni ta kamu da son waninka.

Ba wani bane sai jarumi Hubairu bn mas'ud. MARKAHUSSABUS yayi dariya yace haba ya Ummina kin

"sani cewa a gaba dayan kabilar Aljanu babu wani kyakkyawa kamata balle a cikin bil'adama. Ni na tabbatar da cewa sima zata Soni sai dai idan batayi arba Dani ba. Shin kin manta ne cewa tun ganin farko FATISA ta kamu da Qaunata? Samaratu tace ai ba a nan GIZO yake sakar ba. Abinda ka Kasa fahimta shi ne, ita FATISA ruwa biyu ce. Ma'ana akwai jinin Aljan a jikinta. Ita ko sima bil'adama ce zallah, lallai aure"

tsakanin mutum da aljan Abu ne mai wuyar sha'ani.

Anayi Amma baya karko. To Amma ka sani zan iya sihirce Zuciyarta ta so ka fiye da komai. Yanzu ni

"tambaya ta a gareka, Ina battar nan wadda ka debo tsumin dodo kiryanu? Koda Jin wannan tambaya sai MARKAHUSSABUS yayi shiru ya shiga tunani, daga can sai ya Nisa yace yake Ummina lokacin da na gabata da Sarki LU'UMANU na sanar da shi ladan aikina sai yaki Amincewa ya koreni daga fadarsa batare da ya karbi tsumin ba, bayan na baro birnin TEHRAN sai na yada zango a jeji na zauna cikin mummunan bakin ciki. Nan take na tuna da irin wahalar da na Sha kafin na Isa Kogon zuhurum har na samu nasarar"

debo tsumin dodo kiryanu. Amma gashi duk wahalar ta zama ta banza. Kawai sai na fito da battar tsumin

Nan na fyada ta da Kasa cikin tsananin fushi. Nan take battar ta fashe ruwan tsumin ya zube Kasa. Bisa

"mamaki sai naga Kasa ta tsotse ruwan tsumin, cikin abinda Bai wuce rabin dakika ba."

"Nan fa na Mike zumbur na shiga tonon Kasar wurin da nufin naga ruwan, sai da nayi haka me zurfin"

"kamu arba'in Amma ko danshi ban gani ba, Kai ko alamar lema ma babu a wajen. Wannan shi ne yadda tsumin dodo kiryanu ya salwanta a hannuna. Yayinda MARKAHUSSABUS yazo Nan a zancensa sai SAMARATU tayi ajiyar zuciya tace ai kuwa kayi babbar asara. Inda wannan tsumin na nan da yanxu take"

zan tashi Gimbiya sima daga barcin sihirin da take.

Ya Kai dana dole ne ka koma Kogon zuhurum ka sake debo tsumin dodo idan har kana son sima ta Farka

daga wannan barci harka aureta....

Cikin dimaucewa MARKAHUSSABUS ya zazzaro idanunsa gami da dafe kirjinsa tace tabdijammmm. Ai

komawata Kogon zuhurum dai-dai yake da tafiya Neman ajalina.

Yake Ummina kiyi sani cewa ni ne sanadin mutuwar ZARAZU 'yar dodo kiryanu. Zarazu ce kadai 'yarsa a

duniya Amma ni nayi sanadin mutuwarta. Tun daga kanta mashamu matarsa Bata Kasa samun ciki ba. Kuma kafin a samu cikin zarazu sai da akayi shekara dari. Na tabbatar yanxu dodo kiryanu sunsha kukan

bakin cikin mutuwar ZARAZU....

To zakuga yau posting din ba yawa sosai. Yanayin aiki ne ya jawo hakan.

Sai wani lokacin idan mun samu damar cigaba zakuji yadda zata kaya tsakaninsu MARKAHUSSABUS da

dodo kiryanu...

"[7/12, 5:31 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU 2

PART C

AUTHOR:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- Abubakar Saleh Aliyu

Marubucin yaci gaba da cewa.....

IMAM Khalid yayi murmushi sannan ya zaunar da mas'ud bisa shimfida. Shima ya zauna aka fuskanci

juna. Nan take IMAM Khalid ya bawa Hasiyatu labarin dangantakarsa da masa'ud. Koda taji sai taji tana Qaunarsa dashi da Matar tasa. Bayan doguwar hira imam Khalid ya sake bijirowa da tambayar da yayiwa

mas'ud a kofar gida ta Neman sanin abinda ya kawo shi. Nan take masa'ud ya sanar dasu Ala'marin su.

IMAM Khalid yayi shiru yana tunani daga bisani yace ai fassarar mafarkin da kukayi a bayyane take.

Tabbas abinda kuka gani haka yake. To Amma abinda nake so daku shine kuyi hakuri zuwa gobe. Yau da dare zanyi Istikhra sai mu binciko ainihin halin da Hubairu ke ciki sannan mu Kai Masa dauki. Insha Allah

Nima zan bayar da tawa gudunmuwar. Nan fa farin ciki ya kama masa'ud da Maryam sukayi ta godiya.

"Da safe bayan sunyi Karin kumallo. Sai IMAM Khalid yayi gyaran murya don yayi bayani. Masa'ud,"

"Maryam da Hasiyatu suka matso. IMAM Khalid yace jiya nayi Istikhra Kuma Allah ya nuna min halin da Hubairu ke ciki. Hakika danku Hubairu yayi gagarumin yaki da wani shahararren matsafin Sarki. Ba wani bane wannan matsafin Sarki sai Sarki LU'UMANU na birnin TEHRAN. Hubairu ya samu nasara akan wannan Sarki harma ya kasheshi. Bayan ya samu nasarar suka shammace shi suka sumar dashi. Suman da yayi kuwa ba Suma bane irin Wanda kuka sani, Aljani ne ya shafeshi ya kwanta barci me nauyi Wanda ba a san ranar farkawarsa ba. Nagani cewa Hubairu na can a kwance cikin wani kurkuku da ke karkashin"

Kasa a cikin birnin Sarki LU'UMANU. Tabbas nan da mako biyu idan ba a Kai Masa dauki ba zai iya halaka.

Yayinda masa'ud da Maryam sukaji wannan batu sai suka rude hankalinsu ya tashi. Koda IMAM Khalid ya

"fuskanci hakan sai yace abinda nake so daku ku kwantar da hankalinku. Ku sani cewa babu wata Cuta a duniya wadda Allah be saukar da maganinta ba. Da izinin Allah zamu kaiwa HUBAIRU dauki Kuma zai Farka daga wannan mummunan barci. Da akwai wadansu addu'o'i guda uku da zan baku, muddin ku ka yi su ku ka tofa a jikin Hubairu zai Farka. To Amma matsala Daya ce bisa yiwuwar hakan, daga nan zuwa birnin TEHRAN tafiya ce ta wata guda cur a Kasa. Gashi Kuma ana so ne kuje kafin nan da mako biyu."

"Wannan jawabi ba karamin razana su masa'ud yayi ba, don tuni Maryam ta fara zubar da kwallah. IMAM Khalid ya dube ta yace share hawayenki 'yar uwata da izinin Allah zaku Isa birnin TEHRAN cikin mako biyu. Kuyi sani cewa Ina da wani hadimi Wanda ya kasance musulmin Aljani ne, lallai bazai Cutar da ku ba. Zan umarceshi ya daukeku ya kaiku har cikin wannan kurkukun inda Hubairu ke kwance. Nan take"

fuskar Maryam ta washe zuwa annuri saboda Jin dadin wannan jawabi.

IMAM Khalid ya Mike tsaye ya kama hannun masa'ud yace zo ka rakani zuwa gida wajen bakona. Cikin

"mamaki masa'ud yace wane bako Kuma? Yaushe yazo? Ca nake Muna zaune dakai tun dazu Kuma ba a shigo anyi sallama dakai ba. IMAM Khalid yayi murmushi ya ce ai hadimin nawa ne yazo, naji sallamarsa"

Kai ne bakaji ba. IMAM Khalid ya wuce gaba masa'ud na biye dashi har kofar gida kamar rakumi da akala.

"Suna fitowa sukayi arba dashi. Wani kyakkyawan Aljani ne me matsaikacin girma, ya kasance Yana da"

siffa kamar bil'adama. A tsaye yake kyam. Kuma fuka-fukansa biyu tamkar na tsuntsu. Gadon bayansa na da fadi Kuma a shafe yake babu tudu da kwari. Cikin girmamawa Aljanin ya tsuguna bisa gwiwowinsa

"yayi gaisuwa ga imam Khalid sannan ya ce ya Shugabana gani gareka wace bukata kake da ita, fadi naji?"

IMAM Khalid yayi murmushi sannan ya ce gaisheka ya AFTARUL-HUDES. Kayi sani cewa wannan malamin

"da ke tare dani Dan uwanmu ne musulmi sunansa masa'ud. Yanzu haka dansu Hubairu yana can cikin kurkukun Sarki LU'UMANU na karkashin Kasa tsakiyar fadar birnin TEHRAN cikin mawuyacin Hali. Inaso ka daukeshi ka kaishi wannan wuri a cikin abinda be wuce kwana goma Sha hudu ba, domin ya ceto rayuwar Hubairu. Yayinda Aljani AFTARUL-HUDES yaji wannan Batu sai ya numfasa ya ce ya Shugabana kayi sani cewa wannan aiki me sauki ne a gareni to Amma fa akwai matukar hadari a cikinsa. Ina rokonka da ka tayamu da addu'a bayan tafiyarmu. Domin mu samu nasara akan makiya Allah. Ka sani cewa fadar birnin TEHRAN ta shahara a duniya, domin a tarihi babu wani mahaluki da ya taba shiga hannun Sarki LU'UMANU ya kubuta saboda karfinsa da karfin sihirinsa. IMAM Khalid ya dafa AFTARUL-HUDES yace karka samu damuwa, lallai Allah na tare da masu gaskiya. Inason ku kasance masu karfafa zukatanku da"

Imani a duk Inda kuka tsinci Kanku. Lallai zamu tayaku da addu'a har Allah ya dawo daku lafiya.

Koda gama fadin hakan sai ya juya ya dubi masa'ud yace Kai Kuma abinda nake so dakai shi ne kabar

"matarka a wajenmu Amana. Domin be kamata ayi tafiya me hadari da ita ba. Saboda haka yanzu sai kuyi harama don kada lokaci ya kure maku na sallameku. Masa'ud yace Kwarai kuwa na gamsu da shawara taka, Kuma bani da bukatar sallama da matata, kawai inka shiga ciki ka gaya mata cewa munyi gaba."

Batare da Bata lokaci ba Aljani AFTARUL-HUDES ya rankwafa Kasa shiko masa'ud sai yayi Bismillah ya haye bayansa. Nan take AFTARUL-HUDES ya bude fuka-fukansa ya tashi dashi sama. Kafin kiftawar Ido

sun bace a cikin gajimare.

Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin su IMAM Khalid da su masa'ud bayan sun Isa birnin BAHARIM.

"Ala'marin JAFARU YALISA da GULZUM kuwa, bayan iskar nan ta zuke su sun fada cikin Kundin tsatsuba"

"sai suka tsinci kansu a cikin wata sabuwar duniya Mai mugun yanayin sanyi. Ko'ina ka duba kankara ce tsubi-tsubi manya da kanana. Wasu kankarorin sai ka gansu manya-manya kamar tsaunika wasu kuwa kamar duwatsu. Gaba dayan tekunan garin sun bushe sun zama kankara, hakama bishiyoyi. Babu wata Halitta guda daya me Rai face su JAFARU. Su ma suna dira garin sai gangunan jikinsu suka sandare, babu wani Abu me motsi a jikinsu sai kayan cikinsu, irinsu hanta, Koda, zuciya da sauransu. Nanfa azabar sanyi ta cigaba da wahalshe su, yaxamana sanyin karuwa yakeyi a hankali idanuwan nasu ma suka kafe, kayan cikin nasu ma suka dena aiki. Daga wannan lokacin Basu San abinda ke faruwa ba. Sai farkawa sukayi"

suka ga an kawosu gaban wadansu sundukai guda dubu. A cikin kowane sunduki akwai sassanyar ruwa

Wanda saboda tsananin sanyinsa har wani tururi yake fitarwa. Sanyin dake cikin sundukin na biyu ya

ninka na farko haka Kuma na uku ya ninka na biyu haka abin yake har zuwa na karshe.

Koda su JAFARU sukayi arba da wadannan manyan sundukai Kuma suka fuskanci abinda suka dosa sai

"duk suka fashe da kuka. YALISA ta dubi JAFARU ta ce Kai Dan banza hakika ka cucemu, Wai shin menene ma dalilin dayasa ka bijiro da batun littafin Nan?"

Yayinda JAFARU yaji wannan tambaya sai ya bushe da dariya sannan ya ce karambanin da yasa nayi

"sha'awar Karanta shi, shine yasa kika hada Kai da ni. Wahala dai Kam mun siyeta da kudinmu Kuma bamu da iKon fansar da ita. GULZUM ya ce uhm ai ni jinku kawai nake. Kunga nidai bansan Hawa ba bansan sauka ba, haka kawai Kun jefani a masifa. Yanzu ku dubi irin muguwar masifar da muka Sha, na rantse da darajar tsafi indai nasan cewa haka zamusha wahala da tun farko banyi biyayya ba, don gwara ma YALISA ta kasheni na huta da wannan Azaba. Ku dubi irin tururin sanyin da ke fitowa a cikin sundukan nan karku raba dayan biyu sai fa an jefamu a cikinsu. Koda Jin haka sai YALISA ta bushe da dariya ta ce naga alama kukan dadi muke. Yaushe rabon mu da samun damar yin fira haka? Ni nayi mamakin abinda ya hana a sanyamu cikin sundukan nan. Tana gama fadin hakan wata irin iska me karfin"

tsiya ta zuke su izuwa cikin sundukin farko.

"Suna fadawa sai suka narke suka zama kumfar kankara. Take aka Watso su waje, Koda kumfar da zube a"

Kasa sai ta raba kanta gida uku halittun jikinsu suka dawo. Kafin suyi wani yunkuri tuni iskar ta sake zuke su ta cikin sunduki na biyu. Suna fadawa ciki sai jikinsu ya dagargaje ya zama duwatsun kankara. Nan ma aka watsosu waje aka dawo masu da halittar jikinsu. Haka dai akayi ta shigar dasu cikin sundukan nan ana sauya masu siffofin halittunsu har izuwa sundukin karshe na cikon dubu sannan aka Watso su waje

izuwa duniyar su ta Asali.

"Koda suka fado gaban KUNDIN TSATSUBA sai ga tururin sanyi Yana ta fita cikin idanuwansu, bakunansu,"

"kunnuwansu da hancinsu. Kai har a jikin kofofin gashinsu sanyi ne yake fita. Sai karkawar dari sukeyi kamar ransu zai fita. Shi ko kundin tsatsuba na nan a ajiye kamar yadda suka barshi, shafi na hudu ne a Bude. JAFARU na makyarkyatar sanyi zai Bude sai GULZUM yayi farat ya rike hannunsa yace Kai wawan banza yanzu, duk azabar nan da muka Sha Bata isheka ba, har ma zumudi kake ka janyo mana wata?"

"JAFARU ya harareshi yace ai kaine babban Wawa, in banda shirme irin naka Ina amfanin hutun Jaki da kaya? Azabar nan fa dole ne mu Sha ta, tunda mun Riga mun Bude ta. Ai gara mu nausa a cikinta ayita ta kare, tunda dai ance komai nisan gari akwai wani a gabansa. Duk tsiya dai komai daren dadewa sai mu"

"Kai ga shafin karshe na wannan littafi. Inko mukaje karshensa, karshen wahala yazo."

"YALISA ta ce kwarai kuwa na goyi da bayanka tunda dai ko mun Bude shafin ko bamu Bude ba, zai Bude"

"Kansa. To Amma dai ku tsaya Ina Neman wata alfarma guda daya a wurinku, na rokeku da ku hanzarta"

"kasheni yanzu-yanzu kafin shafin gaba ya Bude Kansa, ko na huta da fargabar abinda zamu gani. Yayinda"

"JAFARU yaji haka sai ya bushe da dariya sannan ya ce lallai na yarda da masu iya magana da suka ce, ba a San Maci tuwo ba sai Miya ta kare, yanzu Kai GULZUM bakaji kunyar wannan batu naka ba? Ka tuna fa mu mutane ne bil'adama, Kai ko Aljani ne. Ya kake nema ka bada Mazaje ne? Tayaya zaka ce mu kashe"

"ka, alhalin idan zamu kwana Muna dukanka da yakushinka sai dai Kaji tamkar Muna maka Susa ne?"

Ka sani cewa tsafi ba zayyi aiki ba yanzu balle yaliya ta kashe ka da karfin tsafi. JAFARU na gama wannan

jawabi ne sai shafin kundin tsatsuba ya Bude Kansa zuwa na biyar. Sukayi arba da gabjejen Kayataccen gari me manya-manyan gine-gine wata siririyar murya ta fara bayani kamar haka..

"Wannan gari sunansa Daulatul duniya, an Gina shi ne fiye da shekaru dubu arba'in baya, akwai"

abubuwan Al'ajabi ciki Kuma akwai wata babbar masifa guda Daya a cikinsa. Mai sauraro shigo cikinsa ka

"Sha kallo. Koda muryar ta zo Nan a jawabinta sai wannan siririyar muryar ta zuke JAFARU YALISA da GULZUM, kawai sai tsintar kansu sukayi a wata duniyar cikin sararin samaniya..."

Tom Masha Allah.

"[7/12, 5:31 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU

PART D

AUTHOR:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD 

08112778656 ( WHATSAPP )

NOTE:- Yin comments da likes da share ya zama wajibi ga masu bibiyar wannan littafi. Ta wannan hanyar

ce kadai zaku rinka samun cigaban littafin cikin gaggawa..

Muna fatan Allah ya taimakemu

Marubucin yaci gaba da cewa...

Kawai sai tsintar kansu sukayi a wata duniyar cikin sararin samaniya. Ana ta zabga walkiya da tsawa. Ba

shiri aka Sako su suka fado cikin wannan Kasaitaccen gari Mai kyakkyawan gine-gine. Nan fa JAFARU YALISA da GULZUM suka fara kalle-kalle tamkar 'yan kauye. Lokacin da suka fado cikin wannan gari ana

ta yin iska mai karfi da walkiya da tsawa. Amma Koda suka mike tsaye sai komai ya tsaya cak.

"A dai-dai wannan lokaci ne kofofin gidajen garin da tagoginsu suka fara budewa, sai ga jama'ar garin"

"suna lekowa don suga abinda ke faruwa. Maimakon suga abinda suke tsammani sai sukaga bakon Abu, wato suka ga JAFARU, YALISA da GULZUM."

Su dai mutanen wannan gari sun kasance manya-manya. Ga tsawo ga kauri. Kowane dayansu ya ninka

GULZUM girma sau uku. Duk da kasancewarsu bil'adama ba Aljanu ba. Kuma wani abun mamaki shi ne sun kasance kyawawan gaske mazansu da matansu. Sai dai suturorinsu gaba Daya na karfe ne. Koda wadannan mutanen sukayi arba da su JAFARU sai suka cika da mamaki domin Basu taba ganin kananun

halittu kamarsu ba.

"Nan fa mutanen suka kewaye su JAFARU suna ta kallonsu, harma wadansun su na kokarin taba suturar"

JAFARU da YALISA a tsorace. Ma'ana sunayi suna ja da baya. Suturar dake jikin JAFARU da YALISA gaba

"daya da auduga aka sarrafa su. Mutanen wannan gari basu taba ganin auduga ba, balle su San yadda zasu sarrafa ta. Komai ka gani a garin da karfe akayi shi."

Hatta gidajen nasu da karfe akayi su. Haka dai su JAFARU suka zama tamkar dabbobin dawa a tsakiyar

"wadannan mutane. Kowa sai yazo ya tabasu ya ja da baya, ana tayi masu dariya. Ala'marin da yayi matukar jefa su JAFARU cikin mamaki da damuwa kenan. YALISA ta dubi JAFARU ta ce abun Al'ajabi baya karewa a duniyar nan. Yanzu ka dubi wadannan mutanen, ban taba bil'adama irinsu ba. Ga su da girma ga su da basirar sarrafa karfe, komai nasu da karfe. Wannan abun da ban mamaki. JAFARU yayi murmushi ya ce ai kamar yadda kike mamakinsu Su ma haka suke mamakin ki, dubi fa yadda suke taba suturar jikinmu. GULZUM yace ni abinda yafi bani mamaki da su shine Yaya akayi suka iya kera"

abubuwan Zamani haka?

Ku dubi can ku gani rijiya ce Amma wata na'ura ce a ciki take zuko ruwan Sha. JAFARU da YALISA suka

"waiga wajen da sauri sukaga haka ne. Su ma sai suka cika da mamaki ruwa ne garai-garai yake zuba me kyau. Nan fa su JAFARU suka tuna cewa suna bukatar abinci da abun Sha. Kai tsaye sai suka nufi inda wannan rijiya take. Kawai sai sukaga mutanen garin sun fito da wasu irin makamai na karfe sun tsattsare su. Take JAFARU YALISA da GULZUM suka tsure suka tsaya wuri guda basu yarda suka Kara taku guda ba. Su ko mutanen garin sai suka fara wani irin gurnani da wani irin yare mara dadin ji. Amma abinda JAFARU ya fahimta shine mahawara sukeyi wasu na cewa a kashe su JAFARU wasu Kuma na cewa a kyalesu. Cikin tsananin fargaba GULZUM ya dubi JAFARU ya ce Wai shin kuwa ka fahimci abinda mutanen nan ke nufi damu? JAFARU yace na fahimta suna shawara ne akan su kashe mu ko su kyale mu. Koda Jin haka sai GULZUM ya fashe da kuka yace shikenan tamu ta same mu. Tabbas rayuwarmu ta zo karshe. Yayinda YALISA ta ji wannan batu sai ta bushe da dariya ta ce yau dai naga Ragon Aljani matsoraci shashasha. Wai shin dazu ba Kai bane kake cewa mu kashe ka, ka huta da fargaba? Yanzu ga"

mutuwar tazo maka ka ishi mutane da raki?

"GULZUM yace ya Shugabata shifa rai guda daya ne, Kuma dadi gareshi. Babu me son rabuwa dashi sai"

"dole. Dariyar da YALISA tayi ne yasa mutanen suka tsorata suka jajja baya, domin a tsammaninsu wani Abu zatayi Wanda zai halaka su. Amma bisa mamaki sai sukaga babu abinda ya faru garesu. Kamar hadin baki sai sukayi kukan Kura gaba dayansu suka afkawa su JAFARU da nufin suyi gutsin-gutsin da su, Kai"

kace kiyasai ne suka lullube kwayar hatsi guda.

Ba zato ba tsammani sai suka rinka jiyo wata Karar na'ura daga can sama. Kamar daukewar ruwan sama

"haka mutanen nan suka rinka ja da baya suka bar su JAFARU, Kuma dukkansu suka rinka daga kawunansu sama, suna kallon abinda ke zuwa."

"Koda su JAFARU suka ga haka sai su ma suka daga nasu kawunan, sai Suma sukayi arba da ita. Wata"

"kyakkyawar budurwa ce a cikin wata irin na'ura mai siffar tsuntsu Wanda ake kera da farin karfe. Na'urar da fuka-fukai suna kadawa tamkar yadda tsuntsu ke shawagi a sararin samaniya. Na'ura ta sauko Kasa dai-dai inda su JAFARU ke tsaye, jama'a suka bude mata hanya. Kyakkyawar budurwar na sanye da kayan yaki ne na karfe, a kanta akwai hular karfe. A kugunta na dama wata zabgegiyar takobi ce. Koda ta sauka daga Kan na'urar sai ya Kura wa su JAFARU Ido tsawon lokaci. Sannan ta dubi jama'ar gari tayi masu wani"

irin bayani cikin irin yarensu. Tana gama yi masu bayanin sai duk suka watse.

Kowa ya kama harkar gabansu. Aka bar su JAFARU da budurwar nan a tsaye. Ita dai wannan budurwa ita

ce Mafi kankanta daga cikin mutanen wannan gari. Domin da kadan zata fi Gimbiya sima tsawo da kauri. Amma Batun kyawu kuwa ba za a iya tantancewa ba face an jerasu waje guda. Kyakkyawar budurwar nan ta cire hular karfenta. Sai ga fuskarta kyakkyawa ta bayyana. Dogon gashinta Baki sidik ya zuba har

Kasan mararta. Cikin tattausan murmushi ta dubi su JAFARU tace sannunku da zuwa birin Daulatul

duniya. Ya ku wadannan baki ya akayi ku ka zo nan?

Kuyi sani cewa wasu halittu irinku basu taba zuwa nan ba. Har JAFARU yayi nufin magana sai tayi Masa

"alamar yayi shiru. Sannan tace ku biyoni izuwa fadata hira ta da ku me tsawo ce. Nan take ta Bude na'urar nan mai kama da tsuntsuwa ta shiga ta tsaya sannan ya yafito su da hannu. Cikin alamun tsoro- tsoro JAFARU da GULZUM suka nufe ta. GULZUM ne na karshe. Nan dai sukayi karfin hali suka shiga cikin na'urar. Duk da girma irinna GULZUM Yana zama cikin na'ura nan sai ya zama tamkar an Saka saniya guda a babban garke. Take budurwar ta Bude wani mawani, kawai sai na'urar ta fara aiki fuka-fukanta suka kadawa. Kawai sai gani sukayi anyi sama da su. Nanfa sukayi ta tafiya a cikin wannan babban birni, suna ta keta garuruwa kyawawa iri-iri. Kowane gari suka keta sai suyita mamakin kawatuwarsa Kuma sai"

suka rinka ganin jama'ar garin suna daga kawunansu sama suna kallonsu.

Haka dai suka cigaba da wannan tafiya har tsawon rabin sa'a sannan suka iso wani babban gari Wanda

"yafi gaba dayan sauran garuruwan kawatuwa. Batare da bata lokaci ba, na'urar ta sauke su a wata Katuwar fada inda suka iske sojoji lodi-lodi, sahu-sahu suna gadi. Koda ganin zuwansu sai wasu kuyangi suka rugo suka tarbesu. Sai sukayi masu rakiya izuwa wani Kayataccen gini Wanda akayi shi da zunzurutun danyen zubar daji. Koina ka duba a wajen sheki yake. Da shigarsu wajen su JAFARU sukaga wata irin fada wadda ba zai yiwu a misalta irinta ba. Kuma Basu taba Jin labarin wani Sarki me irin"

"wannan fadar ba, a duniyar da suka baro."

Daga can bangon gabas kuwa akwai wani wuri me tudu Wanda akayi Masa matattakala guda hamsin da

biyu. Akan Tudun ne aka girke wata kyakkyawar karagar mulki guda daya me sheki da walwali. Amma da kasanta gefe aka zube wadansu kananun kujeru. Yayinda budurwar nan ta nufi wannan tudu sai su JAFARU suka bita a baya. Cikin sauri Dakaru suka finciko su kamar mage ta damko bera aka zaunar dasu

a wadannan Kananan kujeru.

Ita ko budurwar sai ta karasa har Kan wannan karagar mulki ta zauna. Zamanta keda wuya sai wani bawa

"ya danna wani makunni, sai wasu mafetan karfe suka kama yi Mata fifita a hankali. Daga nan Kuma sai wata kuyanga ta kawo mata tataccen ruwan inibi cikin wani kofin Zinari."

Koda ganin haka sai JAFARU da YALISA suka hadiyi yawu saboda tsabar yunwa da kishin da sukeji.

Budurwar ta lura da irin halin da suke ciki sai ta kyalkyale da dariya sannan ta tafa hannuwanta sai aka kawo masu abinci iri-iri me Rai da lafiya birjik.

Koda ganin

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment