You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mutumen da ka fara ziyarta? Koda Jin haka sai RUZYAL yayi shiru baice komai ba ya shiga

"tunani mai zurfi. Boka HAJARUL MUNKURUS ya kosa ya ce, yakai RUZYAL wane irin tunanin banza kakeyi haka? Kar ka manta cewa aikin da ke gabanmu ba kadan bane, ba ka da wani lokaci na yin tunani. Kayi"

sauri ka sanar da mu sunan mutumen da Kuma inda yake.

Cikin alamun tsananin fushi RUZYAL ya ce Wai shin Kai kuwa kana da hankali? Don me zakayi tsammanin

zan tuno da abinda ya faru shekara tamanin baya? Ka sani fa cewa a wannan lokacin banfi shekara Tara ba a duniya. Ai dole ne nayi tunani me zurfi. In Banda ma inada kyakkyawar kwakwalwa ai ban Isa na

tuno ba. Mutumin da na fara ziyarta sunansa SARKI MAHABUR Wanda ke mulki a birnin MISRA.

Koda Jin haka sai Aljani RAMDAKAGU ya kyalkyale da dariya ya ce ai ta kwana gidan sauki akan hanya

"muke. Ina tabbatar maku da cewa nan da dakika dari da Ashirin zamu iya birnin MISRA. Haka kuwa Ala'marin ya kasance Aljani RAMDAKAGU ya ajiye su RUZYAL a kofar gidan SARKI MAHABUR. Tsayuwarsu keda wuya a kofar gidan sarautar sai RAMDAKAGU ya rikide ya zama wani tsoho tukuf har da sanda rike a hannunsa yana dogarawa. Yayinda masu tsaron kofa sukaga wadannan mutane guda sai suka hanasu shiga. Shugaban masu tsaron kofar ya dube su yace ya ku wadannan gajiyayyu suwaye ku,"

Kuma meke tafe daku?

"Har RUZYAL ya budi baki zai ce wani abu, sai RAMDAKAGU ya tari numfashinsa yace mu 'yan aike ne"

daga Sarki JALWAR na birnin SUHUFA Abokin sarkinku DUJJALU bn KASIFU bn MAHAFU. Koda Jin sai Shugaban masu tsaron ya gaishesu cikin girmamawa sannan yasa aka bude masu kofa suka shigo cikin gidan sarautar. Yace ku tsaya nan Ina zuwa. Tsoho RAMDAKAGU yace babu laifi muna

saurarenka.Shugaban masu tsaron ya tafi ya bassu a tsaye.

RUZYAL da HAJARUL MUNKURUS suka dubi tsoho RAMDAKAGU cikin tsananin mamaki. A lokaci guda

"RUZYAL ya ce ya akayi Kasan sunan sarkinsu harma Kasan sunan abokinsa? Koda Jin wannan tambaya sai tsoho RAMDAKAGU yayi dariya yace shin Kun manta ne cewa ni Aljani ne, ku kuwa mutane? Ai mu munsan abinda ku Baku sani ba. Ku sani cewa Ina daya daga cikin Manyan hadiman me girma"

SHAMHARU.

SHAMHARU na sanar dani abinda zamu tunkara nan gaba.

"Ina mai sanar daku cewa shi Sarkin da muke San gani, jikan Sarki MAHABUR ne Wanda tuni ya dade da"

mutuwa harma dansa KASIFU ya gaje shi. Shima KASIFU ya mutu dansa ne DUJJALU akan karagar mulki a yanzu. RAMDAKAGU na gama fadin hakan sai ga shugaban masu tsaron kofar ya dawo. Da zuwa yace

"Sarki yace a kaiku gareshi, sai ku biyoni a baya. Nan take ya juya ya nufi cikin fada su ukun suka bishi."

"Sannu-sannu suna tafiya har suka Isa tsakiyar fadar, suka iske Sarki DUJJALU zaune akan kujera fadawa sun kewayeshi ana tafiyar da harkokin mulki. Koda ganinsu sai Sarki DUJJALU ya Mike zumbur ya taryesu cikin girmamawa. Kai kace wasu 'yan uwansa ne ya gani. Ala'marin da ya bawa sauran fadawansa mamaki kenan. Nan da Sarki DUJJALU ya ja su har kusa da karagarsa ya zaunar da su sannan yasa aka kawo masu abinci da abun Sha suka kintsa. Bayan sun natsu sai ya dube su yace ya kuka ya baro Sarki"

SUHUFA da jama'arsa?

RAMDAKAGU ya ce suna nan qalau Kuma Sarki yace a gaisheka dakyau. DUJJALU ya yi murmushi ya ce

"madallah sannunku da zuwa. Ya gyara zama yace duk da cewa kunsha hanya Amma Banga alamar gajiya a tare da ku ba. Kuma a matsayinku na matafiya Baku dauko guzurin komai ba, Ina dawakanku? Ina"

sauran kayayyakinku?

Koda Jin wannan tambaya RAMDAKAGU yayi caraf yace ya Shugabana ai a cikin wannan tafiya tamu

"munsha wahalar gaske. Domin bamu taba tsammanin zamu tsira da rayukanmu ba. Sai da ya zamana guzurinmu ya kare, dawakanmu Kuma yunwa da kishirwa ce suka kashe su, sa'adda muka ratso cikin Sahara. Kuma Kasan cewa akwai Muggan 6arayi a cikin dajin suburki. To su ne suka taremu suka kwashe mana kayyayakinmu, mu kanmu dakyar muka Sha da takonmu. Ba don Muna da rabon Shan ruwa ba da"

tuni tamu ta kare.

Yayinda Sarki DUJJALU yaji wannan labari sai ya kyalkyale da dariya ya ce lallai Kun cika masu sa'a Kuma

"Kun cancanci jinjina. Kuma zan rubuta takarda ga Sarki SUHUFA cewa yayi maku sakayya me yawa. Koda Jin haka sai sukayi godiya. DUJJALU ya ce yanzu sai ku gabatar da sakonku Muji. RAMDAKAGU ya ce yakai wannan Sarki me daraja, ka sani cewa wannan birni naka ya Tara manyan labarun tarihi na"

abubuwan Al'ajabi tun shekaru aru-aru da suka gabata.

"A halin yanzu Sarki SUHUFA ya bamu babban aiki na tattara manyan labarai irinsu, Kuma ya umarcemu"

"da mu rubuce su. Bisa wannan dalili ne ya Aiko mu gareka, Kuma Muna fatan zaka bamu hadin Kai. Ka"

"sanar da mu wannan tarihi. Ni da wannan malamin zamu kasance masu lissafawa, shi ko wancan Mai rike da alkalamin zai rinka rubutawa."

Yayinda Sarki DUJJALU yaji haka sai ya ce tabdijammmm ai kuwa Sarki SUHUFA ya hadaku da Jan aiki.

"Kuyi sani cewa wannan labari da zan baku ba karamin yawa gareshi ba. Ina ganin idan muka fara yau sai mun shafe kwana arba'in Muna yi. Kuma wannan dan karamin littafin da ku ka zo da shi, ba dauke"

"rubutun labarin ba, sai Kun karo irinsa goma. Cikin tsananin mamaki RAMDAKAGU yace munji abinda"

kace Amma Muna da tambaya. DUJJALU ya ce fadi tambayarka Muji.

"Shin shi wannan labari da zaka bamu a rubuce yake, ko kuwa a cikin kwakwalwarka yake? DUJJALU ya"

"bushe da dariya sannan ya ce, gaba dayan labarin a cikin kwakwalwata yake. Kuma na gaje shi ne a wajen kakana Sarki MAHABUR. Inason ku sani cewa a ka'idar sarautar Kasar nan ba a nada Sarki sai Wanda ya haddace wannan Kasaitaccen labari. Bayan mutuwar mahaifinmu Sarki KASIFU mu bakwai ne 'yayansa, Kuma gaba dayanmu ya sanar damu wannan dogon labarin me ababen Al'ajabi, Amma ni kadai"

ne na haddace wannan labari. Wannan ne yasa aka bani sarautar birnin.

"Shi ko mahaifin namu su goma Sha hudu ne a Gidansu, Kuma shi kadai ne ya haddace labarin. Idan Kun"

"Shirya Nima a shirye nake na fara Baku wannan labarin. Amma bisa sharadi guda. Sharadin shi ne, babu"

"abinda zai dakatar da wannan labarin face cin abinci. Babu Batun kwanciya barci, ko yin bayan gida, ko bawali har tsawon kwanaki arba'in."

"Da Jin haka sai RUZYAL ya Mike zumbur yace wannan ai zancen banza ne, a Ina aka taba yin hakan? Ai ko"

"Aljanu bazasu iya zama waje daya ba har tsawon kwanaki arba'in batare da kwanciya barci ba, ko kawar"

da wata bukata. Yayinda DUJJALU yaji haka sai ya kyalkyale da dariya ya ce ya Kai wannan tsoho zauna ka kwantar da hankalinka na rantse da darajar iyayena da kakannina duk abinda na fada zai faru.

Ku sani cewa akwai wani sihirtaccen shayi da zamu rinka Sha anan ni da ku. Duk Wanda yasha shayin ba

"zaiji yunwa ba, Kuma ba zaiji kishirwa ba. Haka Kuma ba zaiji barci ba ko gajiya har tsawon kwana arba'in. Me kuka ce Kun yarda a kawo shayin yanzu asha a fara aikin? Sa'adda su RUZYAL sukaji haka sai suka dubi junansu suka Kasa cewa komai. Daga can sai RAMDAKAGU ya ce yakai wannan Sarki Muna bukatar ka bamu izini muyi shawara tukunna. DUJJALU yayi murmushi ya ce na amince ku kebe kuyi shawarar taku. Nan take RAMDAKAGU, RUZYAL da HAJARUL MUNKURUS suka tashi suka koma gefe guda sunayin"

kus-kus.

"RAMDAKAGU ya ce Kunga dai ni Aljani ne, bazan taba gajiya ba da wannan zama da za'ayi Koda kuwa"

"za'ayi shekara arba'in. Kuma Kun sani cewa Muna Kan bin Umarnin mai girma SHAMHARU, idan baku"

manta ba ya gaya mana cewa duk Wanda yayi kuskure a cikin wannan aiki sakamakonsa mutuwa ne. Ina mai shawartarku da ku amince da duk sharadin wannan Sarki domin bukatarmu ta biya.

Koda Jin haka sai RUZYAL ya ce Amma dai bansan cewa Kai sakarai bane ba sai yau. Wai shin Ina karfin

da kake takama da shi ne? Me zai Hana kayiwa Sarkin nan dole yayi yadda muke so. RAMDAKAGU ya harari RUZYAL ya ce ai Kai ne babban sakarai Kuma sususu. Idan baka sani ba to ka sani a cikin dokokin tamu me girma SHAMHARU ya ce kada mu yaki kowa face ya nemi ya Cutar damu. Bani da iKon yiwa

wani dole.

Wannan Batu yasa jikin Boka HAJARUL MUNKURUS da RUZYAL yayi sanyi. Bisa dole suka amince da

"shawarar RAMDAKAGU. Gaba dayansu suka dunguma suka koma wajen DUJJALU suka zube a Kasa. RAMDAKAGU ya ce Ranka ya dade mun gama shawara Kuma mun amince da sharadinka. Kuma a shirye muke a fara aiki yanxu. Koda Jin haka sai Sarki DUJJALU ya bushe da dariya sannan yayi tafi wata kuyanga ta shigo cikin fadar dauke da wata Katuwar butar shayi da kofuna iya adadin jama'ar da ke wajen. Nan take ta zuzzuba wani irin shudin ruwan shayi a kofunan ta rarraba. Shayin da zafinsa yana tururi, haka kowa ya rinka ya kurba har ya kare. Daga nan sai Sarki DUJJALU ya dubi su RUZYAL yace Yaya"

kukaji da kuka Sha wannan shayin?

"RUZYAL yayi murmushi ya ce na rantse da darajar gemuna, tunda nake ban taba Jin kuzari ba irin na"

yanxu.

Don Ina ganin ni kadai zan iya nome gonar da karti arba'in zasu nome ta. DUJJALU ya kyalkyale da dariya

ya ce dakyau shayi yayi aikinsa. Yanzu sai ku Kasa kunnuwanku ku fara Jin wannan Kasaitaccen labari. Kai ko me rubutu ka dora alkalaminka bisa littafi.

Sarki DUJJALU ya fara Bada labari kamar haka...........

Sai mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na BIYU part H don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen

labari Mai dadi da debe kewa

Najibullahi Muhammad ke maku sallama tare da fatan Allah ya sadamu a karo na gaba

"[7/12, 5:34 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU 2

PART H

AUTHOR:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- Najibullah Muhammad 

08112778656 ( Whatsapp )

"NOTE:- A gaskiya rashin comments da likes dinku, shi ne babbar matsalar da yasa Baku samun littafin"

kullum.

"A duk lokacin da akayi posting din wannan littafin sama da mutum dubu ke Karanta shi, Amma Kuma"

"bayan kammala karantawa comments ko likes sai suyi maku wahala, meyasa?"

To indai Kuna son rinka samun cigaban wannan littafin kullum har muje Kan MATSATSUBI da

"MIFTAHUZZARBIL, to dole sai Kun dage da yin comments da likes. Amma idan Baku so muje har karshen littafin, to kuci gaba da yanda ku ke yi."

"Daga karshe Inayi mana barka da, shigowa wannan wata me albarka. Kuma Ina fatan Allah yasa Muna"

daga cikin 'yantattu makusantan manzon Allah Sallalahu alaihi wasallam Allah yasa watarana mu wayi a cikin gidan Aljannah war haka. Amin summa Amin

Ina fatan Allah ya taimakemu

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...

A wasu shekaru da dama da suka gabata anyi wani mashahurin masunci anan birnin MISRA Wanda ake

"kira HAMZUR bn KAMSUS. Wannan mutum ya cika me tarin baiwa, domin kafin ya tafi suu yana iya fadin adadin kifayen da zai kamo idan yaje. Shekara da shekaru yana wannan Ala'mari. Kuma abinda ya fada"

haka abun ke kasancewa ba a taba samun kuskure ba.

"HAMZUR BN KAMSUS na da wani da guda daya, shekarunsa Basu haura Sha Tara ba. Duk sa'adda"

"HAMZUR zai tafi su yana tafiya ne tare da wani da nasa Wanda ake kira da suna IMNAS. Amma be taba koya Masa yadda ake su ba. Duk sa'adda sukaje bakin koramar da ake yin su, sai ya bar IMNAS a bakin ruwa, shi ko ya shiga ruwan da fatsarsa yayi kamun kifi. Aikin da IMNAS zayyi shi ne kawai yayi dakon"

kifin da aka kamo.

Watarana HAMZUR da IMNAS sun dawo daga su suna Kan hanyarsu ta komawa gida. Sai HAMZUR ya

"lura cewa IMNAS na cikin damuwa domin tunda suka taho yake tunani har suka iso gida. A Ka'idar HAMZUR duk kifin da suka samo basa ci Kuma basa siyarwa da kowa sai Sarki. Bisa wannan dalili HAMZUR ya gaggauta daukar kifayen da ke cikin komarsa, ya tafi gidan Sarki. Yafi shekara Tara Yana kai kifi gidan Sarki. A Ka'ida duk lokacin da HAMZUR zai je gidan sarautar, ba ayi Masa iso, sai dai yayi shiga kawai ana bashi hanya har sai Isa tsakiyar gidan sarautar inda aka Gina wani lafiyayyan tafki da ake kiwon kifi. Da zuwansa sai ya zuba wannan kifi cikin wannan tafkin. Yana gama zubawa zai je ga Sarkin"

gida ya fada Masa ko kifin nawa ya kamo. Shi ko Sarkin gida take zai biya shi kudinsa.

"Yau ma kamar kullum HAMZUR yaje ya Karbo kudin kifinsa ya dawo gida cikin farin ciki, domin kifin da ya"

siyar yau me tsada ne. Da zuwa sai ya iske IMNAS halin da ya tafi ya barshi wato halin damuwa da tunani.

"HAMZUR ya zauna kusa da IMNAS suka fuskanci juna sannan ya ce ya Kai dana, Ina dalilin wannan"

"damuwa da ka shiga? Na lura da Kai tun sa'adda muka baro Rafi. Lallai akwai abinda ke damunka. Yayinda IMNAS yaji wannan tambaya sai ya nisa yace lallai kuwa akwai. Ya Kai Abbana kayi sani cewa a duniya bani da kowa sai Kai, babu wata sana'a da na iya. Shin idan baka nan taya slzan rayu? Menene dalilin dayasa kaki koya min wannan sana'a taka ta su? Shin kana so ne na shiga halin kakanikayi idan"

"baka nan? Ka tuna fa cewa Kai yanxu tsufa ya riskeka, ni ko Ina Kan ganiyar kuruciya ta."

Sa'adda IMNAS yazo nan a zancensa sai HAMZUR ya ce ya Kai dana kayi sani cewa kayi min tambayar da

"nake tsoron amsawa, domin ta shafi wani sirri da nayiwa mahaifiyarka alkawarin cewa bazan taba sanar da Kai ba, sai dai ka sani bayan mutuwa ta."

"Yayinda IMNAS yaji wannan Batu sai hankalinsa ya dugunzuma ya ce haba Abbana, don me zakayi min"

"haka? Tabbas na fahimci abinda kake boyewa. Ina zargin cewa ba Kai ne mahaifina ba. Na rokeka da ka fada min Gaskiya, shin tsintata kayi ko kuwa wani ne ya baka renona? HAMZUR ya share hawayensa yace na rantse da girman iyayena kai dana ne na cikina. Kayi sani cewa mahaifiyarka ta rasu tun baka fi shekara hudu ba a duniya. Yakai IMNAS hakika kana da usuli me kyau Kuma abin takama, Amma ba zaka"

"San usulinka ba, sai bayan mutuwa ta."

"Kada ka damu da cewa zan mutu na bar ka baka iya sana'a ba, ko kayi tunanin zaka Sha wahalar rayuwa."

"Lallai Kai attajiri ne domin zaka sadu da dukiyar da ka gada. Cikin alamun mamaki IMNAS yace haba Abbana wace irin magana kakeyi? Ka dubi gidan nan da muke ciki, ko siyar dashi zamuyi bazai wuce dinari Dari ba. In Banda shi babu wata dukiyar da muka mallaka. 'yan kudaden da muke samowa wajen Sarki da su ne muke ci muke Sha har muyi sutura. Ina gagarumar dukiyar da ka ce min zan gada?"

HAMZUR yayi murmushin karfin hali yace kayi hakuri yakai dana da Sannu zakaga duk abinda na fada

"maka idan lokaci yayi. Nasihata a gareka ita ce, ka kasance me hakuri da juriya bisa duk irin yanayin da ka tsinci kanka a ciki. Haka Kuma kada ka kuskura ka zama rago. A koyaushe ka rinka karfafawa kanka"

gwiwa bisa dukkanin abinda ka sa a gabanka. Ka Sa a Ranka cewa koyaushe kana tare da nasara.

"Yayinda HAMZUR yazo nan a zancensa sai ya Mike tsam, ya koma Kan gadonsa ya kwanta don yayi barci"

"ya bar IMNAS a zaune Yana ta tunanin maganganun da ya gaya Masa. Sarkin da ke mulkin MISRA a wannan lokaci sunansa ABULHIYANU. Yana da matan aure tara Amma 'yarsa daya ce jal, wata"

kyakkyawa ana kiranta da suna ZARISHA.

ZARISHA ta kasance ta gaban kwatance Kuma shekararta goma Sha takwas dai-dai. Tun sa'adda ta cika

"budurwa Sarki ABULHIYANU yasa aka Gina mata wani kebabban wuri a cikin gidan sarautar. Ya zamana babu me shiga wajenta sai shi kadai da kuma mahaifiyarta. Kuyangin da ke mata hidima su goma ne kacal, su ko basa zuwa ko'ina dare da rana suna tare da ita. Tunda aka shigar da ZARISHA wannan wuri"

Bata sake fita ko'ina ba. Duk abinda take bukata na rayuwar duniya akwai shi a wannan wuri.

"Ba don komai Sarki ABULHIYANU yasa aka boye ZARISHA a wannan gida ba, sai don gudun kada taga"

"wani saurayi ta ce tana so. Burin Sarki ABULHIYANU har abada bazai aurar da ZARISHA ba, don baya san rabuwa da ita saboda tsananin son da yake mata. Kuma a tunaninsa duk hannun Wanda zata shiga ba zata samu kulawa da Jin dadi ba kamar yadda take samu a hannunsa. Wannan tsaro da aka yiwa ZARISHA ba karamin kuntata rayuwarta yayi ba, ta sha yin kukan bakin ciki akan hakan. Kuma ta sha rokon Sarki akan ya janye wannan kudiri nasa Amma yaki yarda. Sau tari Sarki na fada mata cewa 'yata ki sani cewa Maza rigar kaya ne, duk macen da ta Sanya sai ta soke ta. Ina kishi ace wani da namiji ya"

wulakanta ki alhalin Ina Raye a duniyar nan.

"Duk sa'adda Sarki ABULHIYANU yayi wannan furuci, sai ZARISHA ta ce yakai Abbana a tsakanin mace da"

"namiji tamkar ruhi ne da Gangar jiki, babu yadda za'ayi daya ya rayu batare da dayanba. Idan ka hanani aure tayaya zan kawar da sha'awata? Ka tuna cewa ba don aure ba da ba a sameni ba. Zancenki Dutse yake 'yata kiyi sani cewa biyan bukatar sha'awa Jin dadi ne na kankanin lokaci, shi ko takaicin halin Maza baya da karshe. Abinda yasa kikaji na fadi haka shi ne na taba aurar da Kanwata GA wani Sarki Wanda ya cusa mata bakin cikin da ya zamo sanadin ajalinta. A duniya ban taba son wani mahaluki ba tamkar wannan kanwa tawa, har ke din nan. Duk sa'adda na tuno da ita sai nayi kuka Mai yawa. Bisa wannan"

dalili ne na dauki alkawarin cewa bazan sake aurar da jinina ba ga wani da namiji.

Yau ma kamar kullum ana wannan muhawara tsakanin Sarki ABULHIYANU da 'yarsa ZARISHA. Wata

kuyangarta Mai tsananin tunani tana kallon abinda ke faruwa. Lokacin da ZARISHA ta dawo turakarta sai ta Kasa zaune ko tsaye tana ta Kai kawo. Tana cikin hakan ne ta iso ga wani karamin tafki Wanda aka

tanada don kawai ya zama abun kawa da debe kewa.

Ruwan da ke cikin tafkin garai-garai ne abun sha'awa. Kuma an gina wani Abu ciki me siffar agwagwa.

"Ruwa na zuba ta cikin bakin wannan agwagwar inda ZARISHA ta zauna a gaban wannan agwagwar ta Kura Masa Ido tana tunani. Ba zato sai kawai taga wani kyakkyawan kifi guda daya jal a cikin tafkin. Kifin guda daya ne bashi da girma Amma siffarsa kala uku ne, fari ja da shudi. Nan take ZARISHA taji sha'awar wannan kifi ya kama ta. Nan take ta ayyana a ranta cewa Ina ma ace irin wannan kifi na da yawa a cikin wannan tafkin. Tabbas inda zata rinka kallonsu duk bakin cikin zuciyarta zai gushe ta manta da tunanin"

komai.

Koda ta gama ayyana wannan Ala'mari a zuciyarta sai ta kwallawa wata kuyangarta kira tace taje ta

gayawa masu tsaron kofar gida cewa tana son taga Sarki. Nan da nan kuyangar ta cika Umarni. Daya

"daga cikin masu gadin ya sanar da jakadiya sakon Gimbiya, ita ko jakadiya ta sanar da Sarki ABULHIYANU."

Lokacin da sakon ya same shi dare ya soma yi har ya kwanta barci. Amma lokacin da yaji cewa Gimbiya ce ke son ganinsa sai ya tashi da sauri ya tafi bangaren da take. Duk da cewa dare yayi Amma ko'ina a haskake yake da fitilu.

"Gimbiya ZARISHA na zaune a gaban wannan tafki Sarki ya iso gareta. Batare da ta daga Kai ta dube shi ba,"

"ta ce ya Kai Abbana inason kayi duba izuwa cikin tafkin Nan, shin kaga kyakkyawan kifi? ABULHIYANU ya dubi cikin wannan tafkin da kyau, yayi arba da wannan kifi me launi uku. Yace Kwarai kuwa yata na ganshi. Idan baka manta ba kayi min alkawarin cewa duk abinda nake bukata zaka bani muddin akwai shi cikin duniyar nan. Ko ba ba haka bane? ABULHIYANU ya ce hakane Amma sai idan har Bai karya sharadin da na gindaya maki ba. Sharadin kuwa shi ne ba ke ba fita daga cikin gidan nan har abada, muddin Ina numfashi a doron Kasa. ZARISHA ta ce hakane. Ya Kai Abbana inason Ka Sa a samo min irin wancan kifin me yawa, Azo a zuba su a cikin tafkin Nan. Domin idan Ina ganinsu zuciyata zatayi sanyi Kuma duk bakin cikina zai gushe. Yayinda Sarki ABULHIYANU yaji haka sai hankalinsa ya tashi, sannan yace yake yata kiyi"

sani cewa babu irin wannan kifi aduk cikin fadin Kasar nan.

Wannan din ma da kike gani acan kogin BAHARZALLUS Sarkin HAMZUR bn KAMSUS ya kamo shi dakyar

ya kawo min shi Nan.

Ki sani cewa daga nan zuwa wannan kogi tafiya ce ta shekara hudu. Kuma inba HAMZUR bn KAMSUS ba

"babu wanda zai iya zuwa wannan kogi ya kamo irin wannan kifi. Sa'adda Gimbiya ZARISHA ta ji wannan sai ta fashe kuka sannan ta ce lallai ba umarceka da ka sa aje a Nemo min irin wannan kifi Koda gaba dayan dukiyarka zata kare, Kuma Koda za'ayi asarar mutanen Kasar nan zasu kare. Inba haka ba kuwa"

bakin ciki ne zai zamo sanadin ajalina...

Yayinda Sarki ABULHIYANU yaji wannan furuci na yarsa sai hankalinsa ya dugunzuma fiye da koyaushe ya

shiga rarrashin ZARISHA kuma ya tabbatar mata da cewa lallai gobe zai aiki HAMZUR bn KAMSUS zuwa kogin BAHARJALLUS don ya debo irin wannan kifi guda dari. Da wannan ne Sarki ABULHIYANU yayi sallama da ZARISHA ya koma turakarsa ya kwanta Amma sai ya Kasa barci yayi ta tunanin Ala'marin har gari ya waye. Da sassafe HAMZUR ya tashi dansa IMNAS don su tafi yin su kogi. Kawai sai suka kwashi

kayan sana'ar su suka fita daga cikin gida .....

Tom Masha Allah..

Zamu takaita anan saboda Azumi.

Sai mu hadu a KUNDIN TSATSUBA na BIYU part I don Jin cigaban wannan Kasaitacce Kuma Kayataccen

labari Mai dadi da debe kewa

Najibullahi Muhammad ke maku sallama tare da fatan Alkhairi

"[7/12, 5:34 AM] INSTRUCTOR: **KUNDIN TSATSUBA**"

LITTAFI NA BIYU 2

PART I

AUTHOR:- ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI

TYPING:- NAJIBULLAH MUHAMMAD

POSTING:- Najibullah Muhammad 

08112778656 ( Whatsapp )

Note:- Comments da likes da share ya zama wajibi ga masu bibiyar wannan littafi

MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA....

"Fitowar su HAMZUR gida keda wuya, suka ci karo da wani badakaren gidan Sarki tsaye a kofar gida. Koda"

"sukayi arba da shi sai badakaren yace masu kuzo Sarki na kira yanzu-yanzu. Batare da gardamar komai ba suka wuce gaba badakaren na biye da su. Bayan 'yar gajeriyar tafiya suka iso fada. Da zuwansu suka fadi sukayi gaisuwa, Sarki ya Amsa. Daga nan sai Sarki ABULHIYANU ya dubi HAMZUR ya ce, ya Kai HAMZUR kayi sani cewa a yau zan tura ka izuwa wani gagarumin aiki Wanda indai kayi nasara to nayi alkawarin mallaka maka dukiyar da ko tattaba kunnenka ba zasu iya Karar da ita ba. Ba wani aiki bane face inason Ka koma Kogon BAHARJALLUS don debo min irin kifayen nan mai launi-launi guda dari. Kuma"

a yanzu take nake so kuyi wannan tafiya.

"Koda Jin wannan batu sai HAMZUR ya zazzaro idanu cikin tsananin razana, sannan ya ce ya Shugabana"

"Kai kanka Kasan irin hadarurrukan da ke cikin wannan tafiya. A halin yanzu tunkarar wannan kogi dai-dai yake da siyen ajalinmu ne da kudinmu. Ina Mai rokonka da ka hakura da wannan bukata ka nemi wata. Cikin tsananin fushi Sarki ABULHIYANU ya dakawa HAMZUR tsawa ya ce dole Kai ne zaka yi wannan aiki, domin Kai kadai ne zaka iya. Ina so ka sani cewa rayuwar 'yata na cikin mugun hadari muddin ba a kawo wannan kifayen ba. Saboda haka lallai a yanzu take nake so kuyi wannan tafiya. Sannan inaso ka kwantar da hankalinka domin zan hadaka da Sarkin yakina me suna JAMJUS tare da Dakaru dubu goma suyi maku"

rakiya.

"Cikin girmamawa HAMZUR ya ce tuba nake ya Shugabana, lallai dole ne muyi wannan aiki ko don ceto"

"ran gimbiya. Amma Ina rokon alfarma akan Abar dana IMNAS ya jagoranci wannan tafiya domin ni yanzu na tsufa jikina babu kwari, saboda haka komai zai iya faruwa tun gabanin mu riski kogin BAHARJALLUS. Lallai

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment