You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajen sannan
ta duba ledodin, murmushi tayi "nidai shawarman
nan zanci kawai na sha ice cream ya isheni, cuz
dazu
na ci abinci" yace "okay Gud." Ya d'an yi jim
kamar zece wani abu can dai ya fasa ya aje mata
ice cream d'in da shawarma d"aya sannan ya
kwashi sauran ledodin ya tafi d'aya d'akin ya
zauna
ya cika cikinsa sannan ya koma falo ya d"an yi
kallo
dagabaya ya koma d'aki ya kwanta abinshi, itama
kuwa rufe k'ofar ta tayi tayi kwanciyarta. Sai
daya dad'e akan gado yanata tunane-tunane
kala-
kala sannan daga baya bacci b'arawo ya d'auke
shi,,, Asuba ta gari ango mijin amarya
Washegari da safe ta fito sanyen doguwar riga
red
da adon golden tayi bala'in kyau, da niyyar gyra
gidan , da mamakin ta sai ta tadda wata mata
tana
shara da alama dai mai aiki ce, suka gaisa anan
take fad'a mana cewa ita mai aiki ce sunanta Kim
dayake matar nada faran faran nan da nan suka
saba suna hira kamar dama can sun san juna.
Tana gama gyran sukayi salama ta tafi, ita kuwa
Mubeena wayarta ta d'auko ta sa number Husna
ta
kira ta, bugu uku ta d'auka, Mubeena tayi dariya
"
'yar rainin hankali bakya neman mutane koh?"
Husna tayi dariya " ke waketa ta neman mutane
inata mijina, ai in gaya miki aure da d'adi wallahi"
Mubeena ta bud'e baki "lallai Husna ko kunya
bakyaji kike fad'an haka,ko kin manta ni surukar
kice? Ta fad'a da zolaya,, Husna ta tuntsure da
dariya " yo wayake ta surika a wannan harkar?
Yauwa ban labari nasan Yayl Abdul daga gani
baze
yi sanya ba, wai shin ya kuka k'are ne?" Mubeena
tayi tsaki 'ke ni banda lokacin ki, ki gaida mijin
naki sai anjima" Husna tace "zeji yanzu ma jira na
yake a d'aki" Mubeena ta kashe wayar tana dariya
tayi mamaki sosaii yadda aure ya canza Husna
matar da ko irin maganar akayi sai ta nuna bata
san komai ba bataso ashe dai ashe dai.
Yau kimanin sati d'aya kenan da zuwansu amma
kuma har yanzu ba abunda ya shiga tsakinunsu
sai
dai su ci abinci wani sa'in tare suyi kallo amma
dare nayi kowa ze tafi d'aki ya kwanta abinshi.
Yau Mubeena ta fara zuwa makarantarsu tunda
suka ganta nakashashiya suke ji da ita, dan su
basa
wulak'anta irinsu sai ka sonsu dasuke yi, hakan ba
k'aramin dad'i ya mata dan ganin yadda mutane
ke
nan-nan da ita kamar wata 'yar sarki ko shugaban
k'asa,, tayi k'awaye sosaii mata malamansu ma
suna shiri sosaii da su.
Ya Abdul shima ya fara zuwa wajen aikinsu, tare
suke fita wani sa'in ma tare suke dawowa,
wataran
inda time itace ke musu abinci wani lokacin kuma
sai dai su siyo ko kuma suje can wajen cin abincin
su
siyo.
Yau ma kamar kullum bayan sallar isha, Ya Abdul
yana zaune a falo yana kallon wani series film,
Mubeena ta shigo falon sanyen da wata doguwar
riga wadda ta kama ta ta kuma bayyanar da surar
jikinta riga ta k'arbi jikinta sosaii, tunda ta shigo
yake kallonta har ta lura ta sunkuyar da kanta
cike
da kunya, a haka ta k'araso har kujera mai facing
dinshi ta zauna ta fara kallo abinta, shikuwa dena
kallon yayi ya tsura mata ido cike da sha'awa
data
lura kallon yayi yawa sai kawai ta tashi ta nufi
d'aki tayi kwanciyarta dan bazata iya jura kallon
dayake mata ba,, shikuwa be ji dad'in tafiyar data
yi ba, ya tashi ya kashe TV din ya nufi d'akinta
har
ze shiga sai wata zuciyar tace masa "aa" jiki ba
kwari ya koma d'akinsa ya kwanta.
Yau Friday, a gajiye ta dawo daga school wajen
k'arfe biyar da rabi 5:30 gashi ba laifi an d'an yi
zafin rana kad'an tana zuwa ta shige d'aki a kan
gado ta cire kayanta, ta janyo towel ta shige
band'aki dan ta watsa ruwa, bayan tayi wanka ta
fito sanye da towel iya gwiwa ta tsaye a bakin
gado tana taje gashinta, dai-dai shigowar Ya
Abdul
kenan ya tsura mata ido yana kallonta nan take
yaji sha'awarta ta mamayeshi,ita kuwa sunkuyawa
tayi zata d'auki ko mayafi ne ta rufa ai kuwa
towel
ya sauko k'asa ta zaro ido ganinta tsurara
haihiwar
uwarta a gaban Ya Abdul, da sauri ta sunkuya
zata
d'auka da sauri shima ya sa hannun ya janye da
towel d'in, rungume tayi nan ya fara kissing dinta
ta koina ita kuwa sai turjewa take tana bashi
hak'uri, nan dai labari ya canza nidai rufe musu
d'akin nayi na fito abina.
A rannar dai ta sha wahala sosaii dan a rannar
suka
zama cikakun ma'aurata, sai shimata albarka yake
yana kuma jin wani sabon santa a zuciyarsa itama
kuma haka.
Kwanci tashi sunkai shekara d'aya 1 a America
suna
zauna zama cike da so da kuma kyautatawa juna,
sai dai 'yan abun da ba'a rasa ba, dan hausawa
sunce zo mu zauna tamkar zo mu sab'a ne...
Yau Mubeena ta tashi da wani zazzab'i me zafin
gaske ga amai datake ta kwararawa tun safe Ya
Abdul kuwa duk ya rud'e ganin ta a wannan hali,,
d'aukanta yayi sukutum ya kirawo drivern motar
kamfaninsu ya sata a ciki suka nufi asibiti bayan
an
duba ta anan ne aka tabbatar da cewa ciki gareta
har na wata biyu 2 zokaga murna wajensu a
rannar
sunyi kwanan farin ciki. Dan dama sun daidai
suna
tsumaye da har sun fara damuwa ma ganin
Mubeena shekara d'aya amma har yanzu shiru ba
ciki, dan ita Husna ma har ta haifi d'anta
santalele
namiji yaci sunan baban mijinta. Basu je gida ba
kuwa har yanzu Ummi ce tace subari sai ta haihu
sai su dawo.
Kullum tana samun kulawa wajen mijinta tana
motsawa zece"meya faru?" Ita kuwa saitayi
murmushi tace bakomai
Yau Mubeena ta tashi da ciwon nak'uda cikin
dare a
rude ya kira drivern kamfaninsu yazo ya kaisu
asibitin da take awo,, aka shige da ita d'akin
haihuwa ba ta dad'e ba kuwa cikin ikon Allah ya
sulub'o 'yayanta guda biyu maza.
Aka sanar da uban 'yaya murna a wajensa kamar
me, sai sumbatun murna yake yana kuma
mamakin
wai yau shine da 'yaya har guda biyu,, nan da nan
aka sanar dasu Umma suma murna ba'a
magana...Ya Abdul ya shirya musu tafiya kwana
biyu da haihuwarsu suka dawo nan gida Naija.
Yara tubarkalah masha Allah masu kamada Ya
Abdul sak, kullum suda Mum d'insu suna samun
kula
sosaii sai bulbul suke abinsu.
Ran suna yara suka ci suna Sulaiman da
Muhammad
anace musu SAHAL DA SUHAIL,, ansha shagali
sosaii
anci ansha don rannar murna ce, anyi rabo
kayayaki
ba'a magana,, kowa ya watse ciki da murna da
kuma fatan Allah ya raya mana 'yayan mu Suhail
da Sahal.
Share
Comment as:
Publish Preview
No comments:
Post a Comment
MissHafcy
View my complete profile
About Me
► 2017 (16)
▼ 2016 (34)
► November (1)
▼ October (33)
WELCOME
ASMAUL HUSNA 6
ASMA'UL~HUSNA
ASMAUL~HUSNA 4
ASMAUL~HUSNA 3
ASMAUL HUSNA 2
ASMAUL HUSNA
AISHATUL MUBEENA 155-160
AISHATUL MUBEENA 145-155
AISHATUL MUBEENA 110-140
AISHATUL MUBEENA 85-105
AISHATUL MUBEENA 60-80
AISHATUL MUBEENA 45-60
AISHATUL MUBEENA 30-40
AISHATUL MUBEENA 20-30
AISHATUL MUBEENA 1-20
WANI HANIN END!
WANI HANIN 26-27
WANI HANIN 24-25
WANI HANIN 22-23
WANI HANIN 20-21
WANI HANIN 19-20
WANI HANIN 15,16,17&18
WANIN HANIN 12,13,&14
WANI HANIN 11
WANI HANIN 9&10
WANI HANIN 7&8
WANI HANIN 5&6
WANI HANIN 3&4
WANI HANIN 2
WANI HANIN 1
....
WANI HANIN
Blog Archive
Miss_Hafcy. Watermark theme. Powered by Blogger .
More
AISHATUL MUBEENA 155-160
◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
©MISS HAFCY
®NWA
[155]-[160].
◆◆ BAYAN SHEKARA BIYU◆◆
Wani hadad'en falo na shigo falon babba ne
sannan an k'awata shi da zane-zane kuwa kala-
kala na paintings sai kamshi falon yake.
A zaune na tadda Mubeena ta k'ara kyau ta k'ara
k'iba ta k'ara fari,ta zama cikakiyar hajiya, tana
zaune Sahal na hannunta shima ya k'ara girma
kamaninsa da mahiafinsa sun k'ara fitowa, tana
bashi abincin yara( Cereal), yayin da shi kuma
Suhail na gefe akan wani mashin na wasan yara
yana ta gwarancinsa, wata yarinya ta fito daga
d'aki yarinyar tana bala'in kama da Ya Ameen,
ganinta yasa Sahal da Suhali suka fara murna
suna wangale baki, ta k'arso wajen Suhail dake
kan keke, ta fara masa wasa, sannan ta kalli
Mubeena " Anty Mubeena kawo na had"a masa
cereal din na bashi " Mubeena tayi murmushi "
zaki iya kuwa Namesy(dayake sunan Mubeena Ya
Ameen ya samata) tace zan iya mana ina bawa
Maama(k'anwarta) Mubeena tace "To wataran kya
bashi shi na fara bawa kan na bawa Sahal anjima
in yaji yunwa kya bashi" taui murmushi "yauwa
anty Mubeena".
Ya Abdul ya shigo shima ya k'ara zama babban
mutum ya k'ara kyau sosaii kana ganinshi kaga
wanda naira ta zauna masa,,, sanye da shadda
golden yayi kyau sosaii, ya kalli Mubeena "Oya
Momin twins time ya kusa yi fa mu kad'ai ake jira
" tayi murmushi "sorry Dadyn twins kaga ni a
shirye nake, Baby Sahal naga yana kuka da alama
yunwa yake ji shine na had'a masa cereal na
bashi, (ta mik'a masa shi) karbe shi na sa mayafi
na, ya k'arbe shi yana masa wasa shikuma yana
dariya, sannan yaja hannun Little Mubeena sukayi
wajen mota ita kuma Mubeena ta d'auko mayafi
da jakarta sannan ta d'auki Baby Sahal suka nufi
wajen mota.
Basu zame ko ina ba sai wata katafariyar
makaranata koyon zane-zane wadda Aishatul
Mubeena ta gina kuma a yau ne za'ayi taron
bud'e makarantar.
Isarsu keda wuya suka yi parking motarsu a filin
parking sannan suka iso wajan da'aka tanada dan
bak'i, mutane ancika kowa jiransu yake family din
su gabad'aya suna can suna jiransu, sukai ta
gasawa da mutane anata Allah sanya alheri.
A kofar makarantar aka sanya wata igiya me
bala'in kyau tasha ado aka zagaye gate din data
ita, Mubeena rik'e da Suhail da Ya Abdul rik'e da
Sahal suka k'araso bakin gate din yayin da Ya
Ameen da Little Mubeena suka mik'a musu wani
dan faranti d'auke da almakashi me shegen kyau,
suka k'arba suna murmushi yayin da yan jarida
suka kara matsowa dan daukan hotuna da
rahoto, Mubeena ta karb'i almakashin Ya Abdul
ya dafa hannunta suka kamo hannun 'yayan nasu
suka dora akai mutanen dake gurin suka k'irga
d'aya har zuwa uku sannan suka yanka igiyar, nan
aka d'au tafi suka shiga cikin makarantar Su
Abba suka bi bayansu sauran mutanen ma haka,
dan ganin makarantar.
Makarantar kuwa Masha Allah tayi kyau gashi
komai da'ake bukata akwae, bayan mutane sun
zagaya makarantar sukaita sa albarka anan ne
kuma Mubeena tayi jawabi akan makarantar a
karshe tace duk wani polio victim wato mai cutar
shan inna dayake sha'awar harkar zane to ze
shigo kyauta ne! Bata bukatar ko sisi daga wajen
masu cutar polio nan mutane suka dinga tafawa
suna shi mata albarka, daga baya aka koma akaci
akasha sannan aka watse. Little Mubeena tabi
iyayenta suka koma gida dan gobe Monday akwai
school.
Suna cikin mota kan hanyar dawowarsu gida,
Mubeena ta kalli Ya Abdul dake tuka motar tace "
Baban twins nikuwa zaka gane gidan su Yusran
nan kuwa daka tab'a kai mu da d'adewa?" Ya
d'an yi jim sannan yace "eh toh bari mu gwada"
ya juya kan motarsa sannan yayi hanyar gida, sun
sha wahala kam kan sun gane gidan sai da
taimakon kwatance, abin mamaki kuma suka
tadda gidan ya canza ya k'ara kyau an canza
fasalin gidan ma, Mubeena na rik'e da Sahal Ya
Abdul kuma na rik'e da Suhail, Mubeena ta fara
shiga gidan shikuma Ya Abdul ya tsaya a kofar.
Da sallama Mubeena ta shiga gidan, sai datayi
salama kusan biyu sannan aka amsa, Maman ta
fito sanye da doguwar riga tana ganin Mubeena
ta fad'ad'a fara'arta da sauri ta k'araso ta
rungume Mubeena da murnarta, sannan ta k'arbi
Sahal " mashaAllah, shigo mana Mubeena sannnu
da zuwa", Mubeena tace yauwa sannan suka shiga
wadatacen falon gidan, Maman ta karbi Sahal
tana tamai wasa shikuma yana dariya, Maman
tace "sannu ke kad'ai ke tafe?" Mubeena tace
"a'ah da mai gidana suna kofar gida" Maman tace
"yo kuma kya barshi nan tsaye ya shigo mana,
bari na lek'a nace ya shigo" Mubeena tayi
murmushi toh, Maman ta lak'e suka gaisa sannan
tace ya shigo, ta kawo musu ruwa da lemo
sannan ta dawo ta zauna itama, tana rik'e dasu
Suhail sai wasa take musu " ikon Allah Mubeena
ashe har kinyi aure hadda 'yaya bamu sani ba"
Mubeena tayi murmushi " eh wallahi kinsan
sha'anin ne kuma ma kinga bayan biki mukaje can
America mu yi shekaru kana muka dawo bamu
dad'e da dawo bama" Mamn tace " Allah sarki
Allah ya taimaka, naji dadin zuwan ku wallahi," ,
Mubeena tace "mungode, nikuwa ina Yusrah
tunda muka shigo ban ganta ba" Maman tayi
murmushi " tana can cafe d'insu itada k'anina
Bello" Mubeena da mamaki tace "cafe?" Maman
ta cigaba "aiy bayan zuwan ku d'inan kun mana
abin alheri k'anina yayi amfani da kudin wajen yin
harkar makarantarsa to dama Computer science
yake karanta kuma yana shekarar k'arshe lokacin,
to cikin ikon Allah sai ya gano cewa itama Yusrah
akwai basira a fagen computer abu kamar wasa
in ya dauko ze koya mata cikin ikon Allah sai
yaga ma wani wajen ma tafi shi kwarewa ,to
shine ya bada shawarar yana so ya bud'e cafe
mukai cikwi cikwi da d'an abinda ya rage mana
muka siyar akasai komai da'ake buk'ata ya bude
shagon yanzu cikin ikon Allah shagon yana nan ya
bunkasa, kuma sannan k'anin nawa ya samu aiki a
wani babban kamfani,, har yayi aure ma, yana
nan da matarsa hada d'a, ya gyra mana wannan
gida nima yaban jari yanzu ina harkar bussiness
na kaya ina sa ran ma a wannan shekarar zanje
Dubai dan na saro kayan da kaina na kuma bud'e
shagon, kunji ikon Allah koh?
Mubeena tayi Murmushi" Alhamdulilah, amma
gaskiya naji d'adi sosaii, Allah shine abin godiya,
dama ance mahakurci mawadaci, kinga da bakuje
kun k'ask'antar da kanku kunyi bara ba, Allah ya
hore muku ya bud'a muku har kuma nasan kuna
taimakon wasu, a gaskiya naji dadi Allah ya sanya
alheri yasa albarka a ciki, dukansu suka ce "Amin"
Ya abdul shima yayi murna kwarai da jin hakan,
Mubeena tace "ina cafe d'in yake ?muje inga
kawartawa" Maman tace "to muje in raka ku" suka
fito a tare dan zuwa cafe din. A kan hanya ne
Mubeena ta bata labari makarantar ta data bud"e
yau, ba k'aramin dadi Maman taji ba ta kuma yi
alkwarin zata ziyarci makaranta gobe.
Sun d"an yi 'yar tafiya sannan suka isa wajen
Katafaren shago ne babba shaguna uku ne aka
had'e suka zama guda d'aya, asaman shagon an
rubuta " YUSBELL INTERNET CAFE" suka shiga
wajen ma'aikatan se aiki suke wajen fal da mutane
customer's can ciki wani ya nuna musu yace
Hajiyar tana can, suka k'arasa wajen.
A kan wheel chair d'inta suka tadda ta tana dan
system din dake gaban ta, ta k'ara cikowa ba
laifi, ta zama 'yan mata, tana juyowa suka had'a
ido da Mubeena ta saki murmushi, farin ciki ya
bayyana a fuskarta k'arara, da mamaki tace
"kamar Aunty Mubeena nake gani ko me kama da
itace?" Mubeena tayi murmushi had'e da dafa ta
"itace Yusra" Yusra tayi murmushi "sannu da
zuwa Anty, nayi murna kwarai dana had'u da
dake, ya bayan saduwa, nan suka fara hira
Sun dad'e suna hira kana Mubeena ta bata
shawarari sannan sukayi exchanging contacts, da
kuma alkwarin zasu dinga ziyarta juna jefi-jefi,
sukayi salama su Mubeena suka koma gida.
◆◆◆◆◆◆◆
Wasa-wasa dai makarnata tana ta samun budi
makaranta ta sharara sosaii mussaman ma
saboda k'wararun malaman da Mubeena da samo
take kuma biyansu albashi me tsoka, itama kanta
tana koyarwa in ta samu lokaci. Wani abin
sha'awa shine yadda polio victims wato masu
cutar shan Inna suke makaranta kusan kaso biyu 2
a cikin biyar 5 sune, wannan ba k'aramin dad"i
yake sa Mubeena ba , saboda ita dama mussaman
dan su ta bud'e makarantar.
Ya Abdul shima yana ta samun cigaba da
d'aukaka uwa uba ga mata ta gari daya samu,
yanzu shima ya bud'e kamfaninsa na kansa, kudi
suna ta shigo mai ya zama babban alhaji haddda
su tumbi irin na manyan masu kud'i yayi(Lol).
Mubeena ce zaune a d'akinsu Suhail bayan ta
gama saka musu kayan bacci kowanensu ta
kwantar dashi a gadonshi, ta tofe su da add'ua
sannan ta musu good nyt ta kashe musu fitila ta
kulo d'akin.
Kai tsaye d'akinta ta shige ta watsa ruwa ta shafe
jikinta da mai da turaruruka masu kamshi, ta taje
kanta ta raba shi gida biyu ta d"auko wata
arniyar rigar bacci da ita gwanda babu ta saka
tayi brush ta kuskure bakinta da mouthwash
sannan ta d'auko wani cewing gum me k'amshi
pineapple ta wurga a bakinta tana taunawa a
hankali, ta k'ara feshe jikinta da turare sannan ta
kulo d'akin ta nufi d'akin Ya Abdul.
A kwance ta taddda shi a kan gado ganin ta
shigo d'akin yayi murmushi yayi ta karaso tana
rangwada sannan ta kwanta gefensa ya jayota
jikinsa "ya akai ne Hun?" Tayi murmushi
"bakomai" ya kad'a kai sannan yace " i Luvv you
soo much my dear wife, ur my everything," ta
cakule shi a kumatu sannan tace "Me too my
man,my husby, my heart desire, i soo much love
you yaya nah, Allah ya barmu tare" yace "amin"
had'e kashe musu wutar d'akin hakan yasa nima
na fito nace:
ALHAMDULILAH!!!
Godiya ta tabbata ga Allah me kowa me komai
da yabani ikon kamala wannan littafi nawa me
suna AISHATUL MUBEENA, tsira da amincin Allah
su tabbata ga shugabmu Annabi muhammad
(swa) da sahabansa da alayensa baki d'aya.
SADAUKAWA: na sadaukar da wannan littafi ga
d'aukancin masu Cutar Shan Inna(POLIO) dake
fad'in duniyar nan musulmai....sannan ina kira da
babbar Murya ga iyaye da su dinga bada 'yayansu
ana musu d'igon rigakafi domin ance prevention
is better dan cure, sannan ina kira ga gwamnati
(Duk da suna iya bakin k'ok'arinu) da sauran masu
hannu da shuni dake wannn k'asa tamu da su
dinga taimakwa talakawa wad'anda wannan cuta
ta riga ta lahanta,
Alhamdulilah tunda yanzu an cire kasar mu
Nigeria daga sahun k'asashen dasuke fama da
wannan cuta amma duk da haka akwai mutanen
da already wannan cuta ta riga ta musu illa a
jikinsu, kuma basu da gata talakawane, ga kuma
rashin sana'a sune a k'arshe suke k'arewa da
bara-barece akan hanya saboda basu da hali basu
da yadda zasuyi su ciyar da kansu balle har su
samu suyi ilimi, ba sana'a sannan kuma ba kudi,
kuma a cikinsu ana samun dayawa masu baiwa
daban-daban(talent) amma saboda kulawa dasu
da ba'a ayi ba'a gano hakan, Allah ya bamu
yadda zamu iya ya k'arawa gawamnati dama
sauran masu hannu da shuni damar taimaka musu
Amin. Sannan wanda wannan cuta ta riga ta
lahanta ina me jajanta musu da iyayensu Allah ya
basu hak'uri jurewa kuma su sani bawai dan Allah
baya san su bane ya dora musu wannan cuta A'A
kawai dai kowanne d'an adam da abinda Allah
yake jarabtarshi dan ya gwada imaninsa, to su
jarabtar tasu kenan,, Allah ya bamu ikon cin
jarabawar daya d'ora mana Amin...
Ina godiya ga duk wandada suka bi wannan littafi
tun daga farkonsa har zuwa k'arashe duk da
tashon lokacin dana dauka kan na gama shi, ba
abinda zance sai Allah yabar so da kauna da
kuma d'akon zumunci.Amin
Domin tsokaci ko kuma gyra kawai- 09097136605
Anan Ni Miss Hafcy nakece muku BISSALAM......s
e mu had'u a sabon littafina nan gaba
Nagode da kulawarku, LOVE YOU ALL
Sh
Comment as:
Publish Preview
No comments:

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT


Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment