You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faru marar
dadi...Yayi wani tsalle ya kalli umma "Yaya
Mubeena ce tazo ta d'aya(ya nuna yatsan sa guda
d'aya) Ummi ta wangale baki "Ai daman nasan a
rina! ina 'yar tawa take? Mubeena ta k'araso tana
murmushi "gani Ummina!" Ummi ta rungumeta
tana murna "Allah ya sanya Alheri" Mubeena ta
amsa, Ameen ummina! Amma kinsan meye?
Ummi ta girgiza kai" next week zamu kuma yin
wata gasar da Nafisa Jameel wanna wadda nake
baku labarinta" Ummi tace "ai insha Allahu zaki
samu nasar 'yata zamu dage da addu'a" Umma
tace "kar kisa tsoro a ranki insha Allahu sai kin
cinye gasar nan" Mubeena tace "Ameen my
mother's" Umma ta cigaba "bari na kira Ameen
na sanar dashi wannan abun arzik'in" ta shiga
d'aki dan dauko wayarta. Murna wajen ya Ameen
ba'a magana sun dad'e suna waya yana bata
kwarin gwiwa akan ta dage zatayi nasara insha
Allahu ta kuma dage da addu'ar daga k'arshe
sukai sallama ta mik'awa Umma wayarta.
Mubeena ce zaune akan carpet din falon Umma
abinci ne a gabanta amma ta kasa ci tayi tagumi
da alama akwai abunda take tunani, Umma ta
k'araso wajen ta tace "Mubeena me ke damunki?
Kinsa abinci a gaba tun dazu kink'i ci? Mubeena
ta d'ago idonta sharkaf da hawaye tace "Umma
wallahi wani labari aka ban yau in na tuno duk sai
naji ba dadi" Umma ta kara matsowa kusa da ita
"na mene?" Mubeena ta share hawayen nata
sannan taba umma labarin da Asiya ta bata na
yarinyar nan me cutar polio data ja mata
paralysed,, Umma itama sai ta fashe da kuka ta
tuno irin gwagwamayar data sha itama lokacin da
Mubeena na k'arama,, Mubeena ta katse mata
tunanin da cewa "Umma wannan dubu hamsin
d'in dana samu a wajen musabak'ar nan nakeso
kiban muje dake muyi mata siyayya kayan abinci
da kayan sawa da kuma daiper size dinta,Atamfar
nan kuma abani guda biyu na kaiwa mamanta
d'aya sannan kuma aba Safi tella ta dinkawa
yarnyar, mu kai gidansu" Umma tayi murmushi
"Kaji d'iya ta kwarai Mubeena ke daban ce!
Kinada zuciya me kyau Mubeena a kullum godewa
Allah nake daya bani 'ya kamar ki, Mubeena Allah
ya shi miki albarka ya kuma albarkaci rayuwarki,"
Mubeena ta ce "Amin Ummana nima ina alfahari
dake, Allah ya saka miki da alheri ya biya miki
duk bukatan ki duniya da lahira" Umma tace
"Amin nagode AISHATUL MUBEENA" amma sai ki
bari Abbanku ya dawo sai a sanar dashi koh?
Mubeena tace "gaskiya kam Allah ya dawo dashi
lafiya"
Comment as:
Publish Preview
No comments:
Post a Comment
MissHafcy
View my complete profile
About Me
► 2017 (16)
▼ 2016 (34)
► November (1)
▼ October (33)
WELCOME
ASMAUL HUSNA 6
ASMA'UL~HUSNA
ASMAUL~HUSNA 4
ASMAUL~HUSNA 3
ASMAUL HUSNA 2
ASMAUL HUSNA
AISHATUL MUBEENA 155-160
AISHATUL MUBEENA 145-155
AISHATUL MUBEENA 110-140
AISHATUL MUBEENA 85-105
AISHATUL MUBEENA 60-80
AISHATUL MUBEENA 45-60
AISHATUL MUBEENA 30-40
AISHATUL MUBEENA 20-30
AISHATUL MUBEENA 1-20
WANI HANIN END!
WANI HANIN 26-27
WANI HANIN 24-25
WANI HANIN 22-23
WANI HANIN 20-21
WANI HANIN 19-20
WANI HANIN 15,16,17&18
WANIN HANIN 12,13,&14
WANI HANIN 11
WANI HANIN 9&10
WANI HANIN 7&8
WANI HANIN 5&6
WANI HANIN 3&4
WANI HANIN 2
WANI HANIN 1
....
WANI HANIN
Blog Archive
Miss_Hafcy. Watermark theme. Powered by Blogger .
More
AISHATUL MUBEENA 110-140
[12:33AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:51AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS A tak'aice dai ansa
rannar Ya Ameen da Faty, da kuma Aisha( Ya
Nana) da Saifulah nan da wata biyu(2) ,, Su
Umma kuwa sai shirye shiryen biki sukeyi.. Ya
Abdul kuwa har ya gama karatunshi Abba ya
samar masa aiki har ya fara yi dan haka ma ba
kullum yake zama a gida ba. Baiwar Allah
Mubeena kuwa tacan duk ta damu dan ta dad'e
da gane cewa tana son ya Abdul ! amma sai take
ganin abun da kamar wuya, na farko dai Umma
tace mata Abba ne babanta to indai har kuwa
Abba ne babanta to ba aure a tsakaninsu saboda
wanta ne uba d'aya kuma ba aure a tsakaninsu
k'anwa da wa.!.na biyu kuwa, tasan halin ya
Abdul shida ko magana bata shiga tsakaninsu sai
ta k'ure,, in ba kwanan nan dayake d'an sakar
mata fuska,,kuma tasan ma baze rasa budurwa
wadda yake so ba,,,,yadda yake d'in nan
tubarkalah gashi kuma d'an gayu,, doleh 'yan
mata suyi rububinsa... dan haka sai ta dinga
addu'ar Allah ya cire mata sanshi a zuciyarta,, a
kullum kuma tana k'ok'arin cire sanshi daga
zuciyarta,, dan a iya tunaninta ko da da aure a
tsakanin su, in ba wani ikon Allan ba,to ko a
mafarki baza ta tab'a zama matarsa ba,, Ita dai
kullum addu'arta shine Allah ya bata miji na gari
ya kuma zab'a mata mafi alheri Yau saura befi
kwana biyar (5) suyi gasar ba,kuma dama sun
gama exams an basu hutu, dan haka lokacin hutu
za'ayi gasar.. Mubeena na zaune a falo tana kallan
musab'akar alkur'ani da akasa a sunnah Tv,,
Umma ta fito daga d'aki cikin shirin fita unguwa,
Mubeena ta d'ago ta kalleta "Umma fita zaki yi
ne?" Umma tace "eh k'auye zani wajen Mama"
Mubeena da sauri ta tashi "Umma dan Allah nazo
muje? Na dad'e banga Mama ba" Umma tace to
maza shirya muje,kafin rigimaman nan yazo(Amir)
dama neman dalilin k'in zuwa islamiya yake yi"
Mubeena tayi dariya sannan ta shiga dakinsu ta
dauko hijab dinta ta bi bayan umma ,, suka yiwa
su Ummi sallama sannan suka nufi k'auye. Bayan
sun isa Mama tayi murna sosaii da ganin su,
bayan sun gaisa sun sha ruwa , Mubeena nakan
cinyar Mama suna wasan su na jika da kaka,
Mama ta kalli Umma," Ma'u kinsan IYA ta samu
mutuwar b'arin jiki kuwa? Gaban Umma ya fad'i ,
"subhanalahi,wacca iyan??" ta fad'a had'e da
dafe k'irji, Mama tace " Iya dai surikarki, wallahi
abun tausayi kuje ki duba ta dan Allah kullum
fad'i take a kirawo mata ke da yarki ta nemi
gafarar ku . Umma tace "Allah sarki Iya, a ina
take zaune? Mama tace "inda dai kika santa tana
nan' Mubeena dake kwance akan cinyar Mama da
sauri ta taso ta tsutsura musu ido ,, ta kalli
Mama tace"Mama wacce ce Iya?" Mama na
k'ok'arin magana Umma ta dakawa Mubeena
tsawa "bansani ba,dake muke magana,ban hanaki
sa min baki in ina magana ba?" Mubeena ta
sunkuyar da kanta , yayin da Mama tace "ke Ma'u
wai meyasa kike haka ne? Daga tambaya saiki
hayayak'o mata?" Umma tace "Mama haushi
taban ai manya na magana ta dinga sako baki,
bari na tashi naje na dubo ta"" ta tashi ta dauki
jakarta tana k'ok'arin saka takalminta, Mama ta
kalleta," Ma'u indai nina haifeki to ki tafi da
Mubeena" Umma ta juyo jiki ba kwari tace "to se
ki taso muje" bata jira amsar Mubeena ba ta sakai
ta fita, Mubeena da sauri tasa hijab dinta tabi
bayanta. Har suka iso gidan Umma bata yiwa
Mubeena magana ba, da sallama suka shiga gidan
amma suka ji shiru,, sai da sukayi sallama yakai
guda hudu(4) sannan suka jiyo wata dashashiyar
murya nacewa "Wa..alai..kum..us..salam...,k
u..shigo..mana,, Umma ta kad'a kai sannan ta
shiga dakin data juyo murya, Mubeena tabi
bayanta. Umma ta zaro ido saboda abinda ta
gani ya masifar tsorata ta, duniya kenan! ... IYA
ce kwance akan wata yagalaliyar tabarma duk tayi
fitsari akai, dakin in banda zarni ba abinda yake
yi. Umma a firgice ta k'arasa wajen Mubeena ta
bi bayanta, Iya ta k'are musu kallo sannan tace
"Wannan kamar Ma'u nake gani kodai mafarki
nakeyi? Umma ta runtse idonta sai hawaye 'Nice
Iya!" Iya ta fashe da kuka "kece Ma'u ! ashe rai
kanga rai? Ina jikar tawa take?" Umma ta nuna
Mubeena "gata nan, tare muke ma" Iya ta k'ara
fashewa da kuka "zo nan 'yar jikalle ta, ni bansan
ma da wani ido zan kalle ki ba, randa aka haife ki
nida mahai....." Umma ta da sauri ta katse ta "Iya
komai ya wuce dan Allah a bar zancen nan baki
yimin komai ba ni kuma koda kin min ma na yafe
miki, garin yaya kika sami wannan ciwon?". Iya
tana kuka tace "rannar ina zaune ni kad'ai a daki
naji mage a gefena, kinsan dama ina tsoron mage
,to tun daga nan na tsorata sosai bakina ya juye
magana ma na kasa yi, hannuna ma na kasa
d'agawa balle na d'aga kafata,, Haka na kwana
ina kuka bame ceto na,, washe gari makota da
suka ji shiru suka zo suka bud'e kofar aka fito
dani aka kaini asibiti anan akace mutuwar b'arin
jiki nasamu,,shine nake kwance anan masa'udu
(dan k'anwar iya) shine kawai yake kula dani,,, ta
sake fashewa da kuka,, Umma ta fashe da kuka
hakama Mubeena dama ga Mubeena da tausayi.
Iya ce ta katse musu kukan da cewa "Ma'u baki
fad'a wa jikartawa ni kakar ta bace ba? Dan daga
ganin alama bata san nice na....Umma ta katse ta
" Iya dan Allah ya isa haka, zancen nan ya wuce
banse tasan komai ba ai" Mubeena duk ta rikice
ta kasa gane maganar tasu, sun caja mata
kwakwalwa....Iya cikin dashashiyar murya tace
"Ma'u RANNAR WANKA BA'A BOYEN CIBI!
Like · 2 · Reply · Edit · 3 February
Khadija Muhamed
[11:52AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [105]-[110] Mubeena
ta shafa fuskarta" bakomai yusra Allah ya baki
lafiya" yusra ta rik'e hannunta "Amin",, sukai
musu sallama suka juya suka bar Maman nata
kukan murna k'aninta mu'az yazo shima murna
kamar me, ya dinga shiwa su Mubeena
albarka,,dama kudin reg din makaranta yake
nema ya cika dubu biyar(5000)amma ta gagara
sai gashi Allah ya share musu kukunsu. A mota ne
Umma ke ba ya Abdul labarin yarinya jaji
tausayinta sosaii shima ya kuma ji dad'i da'aka
musu wannnan taimakon..Suka aje Asiya a gida
suka mata godiya sannan suka koma gida. Kwanci
tashi ,gobe ne Mubeena da Nafisa zasuyi gasar
su, Mubeena tayi practice sosai, a rannar raba
dare tayi tana addu"ar Allah ya bata sa'a su
Umma ma haka duk 'yan gidan ma, Ya Abdul ma
yazo yayi mata fatan alheri,dan yanzu ba laifi
yana sakar mata fuska. Da sassafe ta tashi ta yi
sallolinta sannan tayi zikirorinta ta shirya suka
huce makaranta...bayan an fito break 'yan class
sun zagaye Nafisa dake wa mickey mouse din
data zana musu fenti wai zasu sa a wall bangon
class din ,bayan ta gama ta d'aga zanen "ya kuka
gani friends?" Suka hada baki "Woww..yayi kyau
sosaii amma da Mubeena ce ta zana munsan se
yafi haka kyau" Nafisa ta juyo a fusace "lallai ma,
in sha wahala in muku abu amma kuce da wata
banza ce tayi sai yafi kyau?" D'aya daga cikinsu
tace "a'ah kinga kar ki sake ce mata banza "
Nafisa tace "an fad'a mata d'in, bari ku gani" nan
da nana ta warce zanen ta yayaga shi, sannan ta
fita daga ajin tana zage-zage,sukuwa dariya
sukayi sukace "kanki kika cuta ai,wahalaliya kawai.
Mubeena ce da Nafisa zaune suna jiran akawo
musu abubuwan zanen, Uncle Hashim ya shigo ya
raraba musu sannan yace mutum d'aya ta biyo
shi saboda za'a raba musu aji gudun kar wani ya
kwafi na wani, caraf Nafisa tace zata bishi ,hakan
kuwa akaiyi yabar Mubeena da anty Sa'a sannan
shi kuma suka tafi wani staff room d'in shi da
Nafisa. Cikin minti talatin suka kamala zanen
kowa yayi submitn,, suka koma aji ... aka bawa
wanda suka duba zanen kwanaki dan su duba
wannan d'in shima. Suna zaune a aji suna class
work din maths Uncle Hashim yazo ya kira
Mubeena anan ya tabbatar mata da cewa itace ta
lashe gasar!! Wohoho murna wajen Mubeena
kamar me ta rasa ma me zatai dan murna.
Assamibili aka k'ara hadawa anan aka kirawo
Mubeena gaban assambili aka sanar da sauran
dalibai itace ta cinye gasar kuma ita zata wakilci
makarantarsu a gasar da za'ayi nan da sati biyu2
dalibai aka d'au ihu ana Up Up Up Mubeena!!
Mubeena kuwa sai murmushi take tana godewa
Allah daya bata nasara... Nafisa dajin haka ihu ta
saki ,tana wani fizge fizge daga k'arshe ta tada
aljanun k'arya malamin islamic studies yasa
prefect mata suka d'auke ta zuwa staff room dan
yayi mata ruk'iya nan kuwa be san na k'arya ne
ba. Mubeena kuwa se murna ake mata malamai
kuwa sai wani nan-nan suke da ita kodayake
dama can malamai suna santa saboda
kwazonta...Nafisa kuwa da Ustaz(malamin
islamic) ya gane cewa na k'arya ne,dorina ya
dauko zabgegiya ya shiga lafta mata, bashiri ta
tashi tana kuka sharaf sharaf tana bashi
hak'uri,dariya yayi sanan yace ta koma aji, aka
dinga mata ihu ana cewa me aljanun k'arya a
rannar tayi alkwarin baza ta sake dawowa
makarantar ba, dan abin kunya data aikita baza
su barta ta zauna a makarnatar lafiya ba. Yau Ya
Ameen ya ze dawo murna a wajen 'yan gidan
kamar me,kowa ka gani yana cikin walwala hatta
Ya Abdul... Mubeena kuwa cewa tayi a bar mata
zata mai girki me dadi, dayake yanason abincin
gargajiya fankaso da tuwo ta yi masa da miyar
taushe dan ya fad'a mata a waya ya dad'e be
cisu ba,, su ya Nana kuma suka yi masa kunun
aya da zob'o. Bayan yayi parking din motar shi
ya shigo gida Amir da gudu yazo ya rungume shi
yana masa oyoyo , su Mubeena suka fifito suna
masa sannu da zuwa shikuwa yana amsawa fuska
d'auke da murmushi..ya k'araso cikin gida Umma
da Ummi kuma na falo suna jiranshi suka yi masa
sannu da zuwa sa kuma ya hanya. Ya amsa da
"lafiya lau nagode,,kuma nayi missing dinku
sooooooo much" a tare suka ce "muma munyi
missing dinka". Bayan yayi wanka yayi sallah ya
dawo ya zauna Mubeena tace abincinsa na kan
dinning table( teburin cin abinci) yaje ya zauna
yana budewa ya fara "wow nasan wannan aikin
kine Mubeena", Ummi tace 'ai kuwa kamar
kasani,kayan shan ne su Nana sukayi yimaka" yayi
murmushi "amma kuwa nagode lovely sisters"
Bayan ya gama cin abincin su Ummi ke sanar
dashi Mubeena ce zata wakilci skul dinsu ba
k'aramin murna yayi ba,a rannar ta faranta masa
rai. Washe gari ya sami Umma yake fad'a mata
cewa iyayen Faty sun takura masa daya turo dan
nan da wata hudu (4) za'ayi bikin yarta kuma
sunaso a had'a da na Faty...shikuma yana kunyar
fad'awa Ummi da Abba,, Umma tayi murna dajin
haka, ta kuma yimasa alkwarin zata fad'awa
Abban sannan kuma indai ya shirya to ba
matsala. yayi mata godiya ya tafi. Umma ta sami
Abba ta fada masa yaji dadin haka dama yana
shirin yi masa maganar auren dan a ganinsa
lokaci yayi daya kamata ya zama cikaken mutum
wato yayi aure...yace ta fad'awa ya Ameen d'in
ya kwantar da hankalinsa zasuje shida yan-
uwansa su nema masa auren insha Allahu..
[12:34AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:48AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [125]-[130] Wakilin
shugabanin da suka shirya gasa wanda yazo daga
birnin taraya Abuja wato MR MIKE da shugaban
k'ungiyar masu zanen dake kano ALHAJI AL-
AMIN BAWA sune suka fito dan fad'an result din
bayan manyan-manyan kwararru a harkar zane
sun duba sun fitar da sakamako, Alhaji Bawa shi
zai dinga kiran suna yayinda Mr Mike ze dinga
d'aga zanen dan kowa ya gani. Bayan sun yi d'an
jawabansu, Alhaji Bawa ya fara magana kamar
haka:" zamu fara da na sha biyar (15)" nan ya
fara kiran sunaye yayin da Mr mike ke d'aga
zanen, sai kuma wanda aka kira ya fito bainar
jama'a. Sai mutane su tafa masa/mata . A haka
dai yana fad'a har yazo ta biyu. Wanda ya kira
dalibi Ahmad Huzaifa, aka d'aga zanen shi nan
mutane suka fara ihu sosaii dan zanen nashi yayi
bala'in kyau. Bayan nan yace yanzu za'a d'aga
zanen wanda/wadda ta yazo ta d'aya, mutane
kowa ya baza ido yana jiran ganin wani zane ne
wanda ya zarce had'ad'un zanen da'aka nuna, da
kuma wani tauraron ne ko kuma wata tauraruwar
ce ta samu nasarar lashe gasar? Mr Mike wani
had'ad'en ko nace gaba da had'ad'e zanen ya
d'aga sama, zane ne wanda aka yishi akan al'adar
bahaushe wato , da farko dai , bukka aka zana
yar k'arama me bala'in kyau a gefen ta kuma
tabarmar kaba ce wanda aka zana akushi da
kwanon sha da kuma kwaryar akai, ga butar
alwala a gefe, a d'ayan bangaren kuma atamfa ce
aka zana da kuma dan kwali irin na da, sannan ga
murajani da dai sauran kayan hausawa na mata.
Zanen yayi bala'in kyau mutum in ya kalla sai ya
rantse hoto ne aka d'auka a camera saboda
tsabar tsaruwar da yayi. Nan da nan wajen ya
gauraye da ihu kowa sai washe baki yake yi daga
masu cewa "wow!" Sai masu cewa 'masha Allah"
duk dai, Kowa burinsa be huce yaga wanda/
wadda yayi zanen ba. Yan jarida kuwa da sauran
mutane sai d'auka hoton zanen suke. Mubeena
kuwa suna hira da su Husna taga an d'aga zanen
ta wani farin ciki taji wanda bata tab'a jinsa a
rayuwarta ba,, ta runtse idonta sai hawayen
murna, ta kuma k'i fadawa su Ya Abdul cewa
zanen tane, sukuwa suna gefe sai fama zuzuta
zanen suke,amma kowa a zuciyarshi, ji yake
kamar zanen Mubeena ne. Alhaji Bawa ne ya
dakatar da mutane daga hayaniyae da suke
dakuma ihu, yayi gyran murya yace , "yanzu zan
kira wanda yayi wannan zane, ina me farin ciki
kirin AISHATUL MUBEENA Muhammad Ameen!".
Murna a wajen su Husna kamar me ,sai kallon
Mubeena suke suna k'ara kallonta, fuskarsu
d'auke da farin ciki, Mubeena kasa tashi tayi da
kyar suka lalab'eta ta tashi jiki ba kwari ta nufi
inda aka kirata. Mutane dake ta jiran fitowar ta,
sai hango ta sukai tana cangala kafarta dan
zuwan wajen, mamaki duk ya cika su, amma
wannan ta ciri tuta ashe dama da nakasasu masu
irin talent irinta? Ihun mutane ya k'aru gaba
d'aya suka tashi suna kallonta yayin da 'yan jarida
suka cika wajen suna d'aukar ta hoto, da kuma
hoto mai motsi(video). Isarta keda wuya , Mr
Mike abinka da arne cak ya d'agata sama! Duk
k'ok'arin datake dan ta kwace amma ya rik'e ta
gam, cikin d'aga murya da hausar sa da wadda
bata fita sosai yace " wannan itace ta lashe
gasar, itace tazo ta d'aya!"
Like · 2 · Reply · Edit · 6 February
[11:50AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [115]-[120] Umma
tace "hakane Iya amma..." Iya ta katse ta
"dakata" ta janyo hannun Mubeena ta rik'e gam
sannan tace "Aihatul mubeena nice kakar ki, nice
na haifi mahaifinki SULAIMAN, nida mahaifinki
mun kasance masu wata irin zuciya,masu butulci
kuma wa'enda basu da godiyar Allah,, nan da nan
ta fada mata komai tun daga auren Umma da
Mal Sule har rannar da suka rabu" Mubeena ta
fashe da kuka,kuka take sosaii haka ma Umma.
Mubeena tana kuka tace "Umma dama na fad'a
miki, na fad'a miki cewa Abba ba shine mahaifina
ba!" Umma cikin tsawa tace " shine mahaifinki !
Abba shine mahaifinki! , shine yaso ki a lokacin
da Mal sule ya k'i ki har yake ik'irarin cewa ke ba
'yarsa bace, shine ya ciyyar dake, ya tufatar
dake, ya baki ilimi, daidai da rana d'aya bai tab'a
nuna bambanci a tsakaninku ke da 'yan'yansa ba,,
sabanin Mal Sule da ya firta da bakinsa kar na
sake ko da wasa nace ke d'iyarsa ce , wanda
shine sillar gurguncewa k'afarki, wanda besan cin
kiba, besan shan kiba, besan wahala kiba, besan
komai naki ba! Abu d'aya ne ya miki a rayuwa,
shine sillar zuwan ki duniya , amma bayan haka
ba abinda ya tsinana miki a rayuwa, wallahi kome
Mal sule ze miki yanzu in aka d'auke Silan zuwanki
duniya dayayi baze ko kusa yi miki abinda Dr
Muhammad ya miki ba,, Mal Sule ya amsa sunan
sa na cewa shine ubanki wanda ya haife ki kawai,
amma ko kusa baze amsa sunan , wanda yayi
wahala dake tun kina yar gwililuwa har yanzu,
wanda ya ci dake, ya sha dake,ya tufatar dake,ya
baki ilimi ya kuma baki tarbiya, Shine ya cika
sharud'an zama uba wanda uban naki wanda ya
haife ki ya kasa cikawa!(Ta sassauta murya ta)
amma Mubeena kar abinda nida Iya muka fad'a
miki ya sa ki tsani mahaifinki, ko kusa kar ki fara
domin in badan shiba baza kizo duniya ba!....ta
k'arasa maganar cikin sheshek'ar kuka. Kukan
Mubeena ya k'aru sosai, tama kasa magana, sai
sheshek'ar kukan data keyi,,, Umma ta kalli Iya
dake ta faman sharbar kuka tace "Iya kiyi hak'uri
ban fad"i maganar ba dan ta b'ata miki rai,
gaskiya ce kawai na fad'a, Iya tace" baki b'ata
min rai ba Ma'u, gaskiya ke kike fad'i, nayi dana
sanin abinda na aikata a baya"" Ma'u tace "Iya
bakiyi mana komai ba Iya wannan maganar ta
huce saboda ni tun d'ad'ewa da kika nemi
gafarata na yafe miki, dama ko baki nemi na yafe
miki zan yafe miki dan wallahi ni tamkar Uwa na
d'auke ki!" Ga wannnan ta aje mata bandir din
yan dubu d'aya(1) sannan tace "gobe insha Allah
zan aiko miki da sauran abinda kike buk'ata,
kuma insha Allahu za mu dinga ziyartar ki akai-
akai. Iya ta rik'e hannunta " Ma'u tsaya na fad'a
miki wani abu,, yau tsawon shekaru goma(10)
kenan ban sa Sule a idona ba, tunda yazo yace
min ya tafi birni cirani na nuna ban amince ba
amma sam ya k' jin maganata ya tafi ya barni, be
kuma waiwayata ba, ko yana da rai? Ko ya rasu?
Allahu a'alam,, amma dan Allah in Allah ya had'a
ku dan Allah ma'u ku yafe masa ke da Aiha
(Aisha), ki kuma ce nima na yafe masa, dan ina ji
ajikina kwanan ya kusa k'are da k'yar na k'ara
kwana a duniya ,nima ku yafe min Allah ya had'a
fuskokin mu a aljana..." ta fashe da kuka,,,,jikin
Umma da Mubeena yayi sanyi sosaii Mubeena tayi
dauriyar cewa "ni na yafe miki Iya, kuma ki dena
ambaton mutuwa insha Allahu zaki tashi, cuta ba
mutuwa bace! " Iya ta girgiza kai "kayya! Suka
mata sallama suna kuka tana kuka suka rabu. A
gidan Mama ne, Mama ta kwantar da murya
tayiwa Mubeena bayanin komai, Mubeena wani
sabon kukan ta sake Mama na rarashinta, taji
tausayin Ummanta sosaii sosaii ga wani sonta
dake k'aruwa a zuciyarta,, sannan kuma taji
tsanar Mal Sule a zuciyarta, ji take ba wanda ta
tsana sama dashi..godewa Allah tayi daya bata
uwa ta gari kamar Umma dan ita gani take tafi
kowa dacen uwa a duniya! Haka suka koma gida
dukkansu ba farin ciki da walwala.. ◆◆◆◆◆◆◆
Washe garin rana Allah yayi wa Iya cikawa,, su
Umma sunji mutuwarta sosaii a wannan dak'in
Allah yayi mata cikawa cikin dare. Da sassafe su
Umma suka tafi suna ta kuka abun tausayi
mussaman ma Mubeena, da 'yan gidan suka tafi
gabad'aya har da Abba, dan shima yaji mutuwar
dan ya santa, lokacin da 'aka kwantar da
Mubeena a asibiti da cutar polio ta sameta,,sai
da suka fara sauka a gidan Mama sannan sukaje
gidan marigayiya Iya,, a lokacin ma ko wanka
ba'a yiwa gawar ba, Umma da taimakon Mubeena
su suka wanke gawar tas aka samata likafani aka
fita da ita ,maza suka sallaci gawar aka kaita
kuhewarta , Allahu akbar Allah kasa mu cika da
imani, ka bamu kyakyawan K'arshe Ameen ya
Allah.. Ba wani zaman makoki akayi ba tunda wa
za'ayiwa gaisuwar? Dama Mal Sule ne kawai d'an
data haifa kuma baya nan bai san ta rasu bama,
'yayan mijnata kuwa Bashir da Hauwa sun dad'e
da dena kulata bama sa k'asar gabadaya. A 'yan-
uwanta kuwa ita kad'ai tayi ragowa duk sun
rasu,, sai dai sauran dangi da ba'a rasa
ba..Masa'udu dama shi ake yiwa gaisuwar dan
shine ya kula da ita tun data sami rashin lafiyar
har ta warke, shima kuwa a rannar data rasu
admission dinsa ya fito yaci Ahmadu Bello
unibasiti zaria(ABU zaria) dan haka ya had'a
kayansa ya tafi Umma kuwa kud'i me yawa ta
bashi tace yayi harkar makaranta dashi ya yafi
yana ta godiya.
[12:35AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:46AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [135]-[140] Bayan an
dawo hutun tak'aitacen lokaci. Aysha Amatulah:
to barkan mu da dawowa. Hajiya Mubeena shin
wai ta yaya kika tsunduma cikin harkar zane-
zane? Mubeena: To agaskiya nidai na taso ne
kawai na gani inayi, a lokacin inga abu ya min
kyau sai na zana shi, cikin ikon Allah kuma sai
kiga zanen ya fita sosaii...lokacin da ina primary
kuma in kika duba littafai na na arts zaki ga inaci
sosaii, koda merit za'a bada ma a Art ni ake
bawa. Kuma akwai Yayana Ya Ameen shine ya
cigaba da ban kwarin gwiwa har nazo matakin
danake yanzu. Aysha Amatullah: madalah, to
kafin ki fara wanan zane-zanen mene burinki a
rayuwa? Mubeena: Burin na da shine na zama
likita dan nima na bada gudunmawa ta wajen
yak'i da wannan cutar sai kuma Allah beyi ba.
Aysha Amatullah: to Allah zaba mafi alheri, meye
ya fi b'ata miki rai da kuma abinda yafi faranta
miki rai? Mubeena: Abinda ya fi b'ata min rai
guda biyu ne na d'aya ya shafi personal life dina,
na biyun kuwa shine, idan naga yan'uwana masu
wannan cuta ta polio suna bara ko kuma suna
cikin wani hali na rashin gata a gaskiya raina na
sosuwa kuma ina iya k'ok'ari na dan ganin na
taimake su. Sannan abinda yafi faranta min rai
shine, ina tuno irin nasororin dana samu a
rayuwa, sannan kuma ina ga masu irin cuta ta
wato polio basa fuskantar wani k'alubale a
rayuwa ,suna jin dadin rayuwarsu sannan suna
samin gata daga wajen iyayensu dama al'uma
baki d'aya, to nakan ji raina yayi fari . Aysha
Amatullah: Allah sarki, yanzu zamu d'auki waya
guda biyu(2) duba da yanayin lokaci, zaku turo
sak'o ne ta wannan lambar 064**** sannan zaku
kira mu ta 064****. Mutane an kira an mata
fatan alheri, an kuma turo sak'oni ba adadi.
Aysha Amatulah:wani kira zaki yi ga iyaye da
kuma masu cutar polio? Mubeena: kiran da zanyi
shine dan Allah iyaye su dinga bada yayansu a
dinga musu d'igon rigakafi, sannan iyaye su dage
su dinga gano talent din da suke dashi su
k'arfafa musu gwiwa, bawai su dinga barinsu
suna bara ba, da sauransu. Sannan irina masu
wannan cuta ta polio, ganin suna da nakasa kar
hakan yasa su fidda rai da rayuwa , su d'age suyi
karatu suma su zama wasu a dinga damawa
dasu, in hakan ya faru zan fi kowa farin ciki.
Aysha Amatullah: to duba da yanayin lokaci mene
sak'on ki na k'arshe? Mubeena: to Alhamdulilah
ba abinda zance sai in godewa Allah da kuma
iyayena nakan ji farin ciki sosaii in na tuno da
iyayena,yayena da k'anina, da sauran dangi.
Aysha Amatulah: to masu sauraron mu lokaci
yayi halinsa , anan zamu k'ark'are wannan shirin,
Hajiya Mubeena muna godiya da kika amsa
gayyatar mu, da fatan duk sanda muka sake
neman ki zaki amsa kiranmu. Mubeena: to nima
nagode masu saurarona da kallona ina muku
fatan Alheri,(tayi murmushi) sai anjima. Ahaka aka
gama shirin, ta fito driver yaja suka tafi.
*********** A yau ne aka d'aura auren Ameen
Muhammad Ameen da Fatima Adam, Aisha
Muhammad Ameen(Nana) da kuma Saifulahi
Abdalah. Ansha biki sosaii an kuma kashe kudi
dai-dai misali, Mubeena kuwa lemukan nan da'aka
bata kyauta su ta bada akayi hidimar biki da su,
sannan katuwar jaka da calanda me sunayen Allah
ta musu a matsayin gudunmawa sun sha murna
tare da yi mata addu'ar Allah

Please Login or Register in order to submit comment