You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau
kwanan farin ciki za'ayi a gidan nan" Nana tace
"Aikwa dai" Ya zauna akan kujera yana dana waya,
Nana ta kalleshi "yauwa na tuna,Ya ameen kasan
wata faty? " da mamaki yace "Yes nasanta" Nana
tace " A layin nan take?" Da sauri yace "A'ah a
unguwar nan dai suma suke,,me ya faru wai?"
Tace "Amma ni bansanta ba,Wani ta aiko da
sak'o dazu wai abaka,Am sorry mantawa nayi,,
da sauri yace "sak'on me? Fada min" tace "bari
na dauko maka" yace "yauwa" ala-ala yake ta
kawo masa yaga ko mene ne Bata dade ba kuwa
sai gata da yar k'aramar jaka a hannunta ta mik'a
masa, cike da zumud'i ya karba yana washe baki,
,Mubeena kuwa bata ce musu komai ba shiru tayi
kamar ma bata san abinda suke ba ,, Yana karba
ya fice abinshi ya nufi dakinshi. Kan gadonshi ya
baje da sauri ya dauko jakar yana bud'ewa wani
kati ya gani ya sha kwalliya cikin hanzari ya bude
ya fara karantawa kamar haka "" Remember the
good times we had spent together,And the
beautiful future we had dream of,,Darling i never
wanted to create a distance between us...please
let us bridges the gaps,,. Wani tsale murna yayi
ya rungume kati a fili yace "Bakomai my faty na
hak'ura!" Wayarsa ya dauko yayi dailing number
ta,akace a kashe take,,Yayi tagumi yana sake
kalan katin shi abin mamaki yake basa ma ashe
dai abdul da gaske yake da yace da kanta zata
dawo su shirya!,, Wayarsa yagani tana ruri da
sauri ya dauka,, Ashe faty ce cike da murna Yake
tambayarta ta canza number ne tace masa eh,,
bayan sun gaisa tace "Kayi hak'uri ya ameen
rashin fahimta ne ya kawo hakan, amma yanzu na
gane komai,ina neman yafiyarka" yayi murmushi
"Bakomai faty darling Allah ya barmu tare
sweetheart" tace ameen dear suka cigaba da
hirarsu ta soyayya. Aishatul mubeena bayan ta
gama yiwa Amir assignment din ya tafi wajen su
umma,,ta juyo ta kalli nana, "Ya nana wacce
FATY wai" Nana tayi murmushi "inaga fa
budurwasa ce !Dan dama rannar na labe naji suna
hirarta shi da ya abdul ""Mubeena bata san dalili
ba sai kawai taji gabanta ya fadi a sanyaye tace
"Amma nikuwa bai taba fada min ba" Nana ta
harareta da wasa "Ko ni dana girme ki be fada
min ba saike yarinya" mubeena tayi murmushi "To
yaya baba" nana tace "Kinsan mu akwai san
girma" Mubeena tayi dariya ...Ta tashi ta shiga
cikin daki ta zauna jikin gado tayi tagumi Tana
tunane-tunane kala-kala a zuciyarta.. Umma ce
ta shigo dakin,,kusa da ita ta zauna a hankali ta
dube ta tace "me yafaru naga kin yi shiru kina
tunani? Meke damunki?" Mubeena da sauri tace "
bakomai ummana kaina ne ke ciwo kawai" umma
tace "toh kuma ai se ki sha panadol,bari na
dauko miki magani kisha" Ta tashi ta dauko
mata,, ta k'arba da kyar ta sha maganin duk jinta
take wani iri,, Ta d'an yi jim,Can ta tuno wani
abu da sauri ta kalli umma tace "umma dan Allah
wata tambaya zan miki amma dan Allah umma
kimin alkwarin zaki bani cikakiyar amsar"" umma
ta danyi jim sannan tace "inajinki indai inada
amsar insha Allahu zan baki ita" Mubeena tayi
murmushi "yauwa ummana" sannan tace.. "Umma
DAN ALLAH WAYE MAHAIFINA? Gaban umma ya
fadi sosaii cikin dauriya tace "Wai ke mubeena
me ke damunki ne? Sau nawa kike tambayata
nace miki Abba ne babanki,Abba shine babanki
kar ki sake yi min wannan tambayar tunda kinsan
amsar"" mubeena ta runtse idonta se
hawaye,cikin murya kuka tace "Umma Abba
bashine mahaifina ba, Na dade da sanin haka,"
Ummi cikin muryar masifa tace "to sai ki fada
min waye Mahaifin naki,tunda ni baki yadda dani
ba Mubeena ta fashe da kuka "Umma ba haka
bane,Umma Dan Allah ki fada min,Kar kisa na
fara tunanin ko ni yar shege ce,,Ba ta hanyar
Aure aka haife ni ba!! Umma da sauri ta juyo
idanunta fal da hawaye tace "Auzubillahi" "ke ba
yar shege bace! Ke yar halak ce! Idan bakyason
bacin raina to ko da wasa kar na kuma jin
maganar nan,,tana gama fadan hakan ta fice
daga dakin tana share hawayenta!
Comment as:
Subscribe to: Post Comments (Atom)
Saturday, 15 October 2016
Posted by MissHafcy at 08:00
AISHATUL MUBEENA 85-105
[12:29AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©NA MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [80]-[85] Mubeena
kuwa kukan ta ta cigaba dayi daga baya barci
b'arawo ya sace ta. Da asuba ta tashi tayi
sallolinta da kuma nafila,,Tana zauna tana karatun
Alkur'ani har gari ya washe.. Bayan ta idar da
karatun ta tashi ta nufi dakin Umma,,zaune ta
tadda ita akan sallaya Tana addu'a,A bakin gado
ta zauna tana jiran Umman ta kamalla addu'oin
ta,, bayan Umma ta idar ta juyo ta kalli
mMubeena,da sauri Mubeena ta k'ara duk'awa
k'asa ta gaishe ta cikin sanyin murya "Umma ina
kwana,kin tashi lafiya?" Umma tayi murmushi
"Lafiya lau Mubeena" Mubeena tace "Umma dama
ina neman yafiyarki naga jiya kamar na b'ata miki
rai,insha Allahu baza ki sake jin maganar daga
bakina ba" Umma tace "Ban yi fushi ba
Mubeena,bakomai komai ya wuce" Mubeena ta
washe baki "yauwa Ummana nagode sosaii"
Umma tace "muje muyi karin kumalo(breakfast)"
Mubeena tace "Toh" Bayan sun gama cin
abincin,suna zaune ya Ameen ya shigo sanye da
kayansa na pilot ya rik'e hular a hannunsa sai
murmushi yake yi, Har k'asa ya duk'a ya gaida
umma ta amsa da fara'arta,Mubeena ma ta
gaishe shi ya amsa. Bayan sun gama gaisawa ya
kalli Mubeena"Sis ni kinga yau zan koma aiki" ta
canza fuska "Da gaske bro? ai nazata sai next
week" yayi dariya "Yauwa dan Allah inaso ki
maida hankali akan gasar zanen nan da za kuyi
kinsan Ran monday zaku fara,Ku goma(10 )Aka
zaba kuma a cikinku ne za'a zab'i ta d'aya( 1)
Please inaso ya zamana kece ta dayar nan! Zaki
iya, ga wannan(ya mik'a mata leda) duk wani
items da zaki buk'ata a harkar zane yana ciki
inaso ki fara practice tun yau,,Please ki dage "
tayi murmushi "Toh bros nagode sosaii insha
Allahu zan fara daga yau mu dage addu'a,insha
Allahu bazan baka kunya ba." Yayi murmushi
"Dats my sis,ki kuma sa a ranki zaki iya,indai kin
yadda da hakan to baza ki samu matsala ba insha
Allahu". Sai a lokacin umma tace "Gaskiyane Allah
ya bada sa'a" Dukansu suka ce "Amin."
Gabad'aynsu hadda Abba suka rako shi harabar
gida,Mubeena kuwa daurewa kawai tayi dan ji
take kamar tayi kuka idanunta sun yi rau-rau
alamar me shirin yin kuka, shikuwa sai k'ara
jadada mata yake akan ta dage sosai, itakuwa
tana cemasa "insha Allahu zata dage sosai" su
Abba suka mai fatan alheri suka kuma mai
addu'ar Allah ya kiyaye hanya,sannan suka shige
ciki,suka barshi daga shi sai Mubeena datake jikin
motar tayi jim ta kasa magana ,daga baya ta
kalleshi tace "Yanzu bros sai yaushe? " yace
"Gaskiya for now bansani ba" tace "Okay Allah ya
taimaka ya tsare ka Ameen,A dawo lafiya" yace
"Amin sis nagode" har ta tafi sai ta dawo da
sauri ta kalleshi "Ka gaida FATY in kunyi waya"
bata ko jira amsar shi ba ta shige ciki, shikuwa
mamaki yayi ,ko taya tasan faty budurwasa ce ?
oho. Mota taja suka tafi.. Yau monday da sassafe
suka shirya itada Amir suka tafi skul,Dayake dama
can Husna da ya Nana sun fita aji a makaranta,su
sunyi candy last year kuma Abba yace sam be
yadda su fara unibasiti ba sai sunyi aure,Da kyar
da taimakon su umma ma ya barsu suka fara
zuwa Computer school. Tana zaune a kan bencin
ta ita da k'awarta Asiya suna hira,dayake lokacin
break ne,inda Mubeena ke bata labarin gasar
zanen da za'ayi,, Uncle hashim ya shigo nan take
ajin yayi tsit,suka tashi suka gaishe shi ya amsa
sannan yace duk wanda ya kira sunansu su same
su a Principals office, Ya fara kiran sunan kamar
haka: "Nafisa Jameel, Auwal Isah, AISHATUL
MUBEENA MUHAMMAD AMEEN,, Sai ku
biyoni,"Yana gama fadan haka ya fita,yayin da
yan ajin kowa ya shiga fadan albarkacin
bakinsa,daga masu cewa laifi sukayi sai masu
cewa suspension za'a basu, duk dai, Ita kuwa
Mubeena sam bata damu ba dan tasan dalilin
kiran,Suka jera ita da Nafisa sai yatsine take ita
tana tak'ama an zo har aji an kira suna hada suna
ta. A office suka tadda malamai da sauran
Dalibai guda bakwai(7) suna jiransu,bayan sun
gaida sauran malaman uncle hashim ya fara
magana cikin harshen turanci kamar haka: "Mun
tara kune anan ba dan komai ba dan wata
gagarumar gasa da gwamnatin taraya ta shirya
akan ZANE-ZANE,wato ART, ana neman kuma
mutum d'aya mace ko namiji wanda ze wakilci
kano baki daya,dan haka mukayi registar wannan
makaranta, da farko dai a cikinku ku goma nan
damuka zab'a, gobe zamu fara gasar mu a iya
makarantar mu kuma duk wanda ya cinye shine ze
wakilci makarantar mu a gasar da za'a yi da
sauran makarantu guda biyar(5) da gwamnati ta
tantance, idan Allah yasa wakilin makarantar mu
ya samu ya lashe gasar to shine ze wakilci kano
baki d'aya a gasar da za'ayi da sauran state
(jihohi) dake k'asar nan tamu Nigeria,,da fatan
kun gane?. Gaba ki d'aya suka ce "mun gane".
Principal ya kuma musu wani k'arin bayani tare
da yi musu fatan alheri daga baya aka salame su
kowa ya koma ajinsu Nafisa sai wani iyayi take a
zuciyarta kuwa cewa take aiy tasan ita zata lashe
gasar. Suna shiga aji yan class suka fara
tambayarsu abinda ya faru Nafisa ta k'arfi ta
fada musu ,aikuwa suka d'au ihu "Se kinyi
wallahi!!,se kin cinye nafisa!, ita kuwa sai busa
hanci take yi, cikin murya isa ta fara magana"
hmm ai ni dama sun ban mamaki,ai da basu b'ata
lokacinsu ba wajen cewa sai anyi gasa sun zab'i
gwani,suna b'ata lokacinsu ne amma kowa yasan
nice zan cinye,ko ya kuka ce friends?" Suka kuma
ihu "hakane Artist nafeesa, sai kinje abuja kin
karbo mana award dinan!
Share
[12:30AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:53AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [95]-[100] Uncle
Hashim murmushi yayi yace "To kunyi gueesin
right" Nafisa kuwa iya kulawa ta kulu batasan
sanda taji hawaye ba,dataga abin ya fara isarta
sai ta fara zage-zage "wallahi bazan yadda ba!
Wannan ma aiy sankai ne, aikin banza
kawai,kuma...bata k'arasa maganar ba taji saukar
mari a fuskarta ji kake tas! Kallo ya dawo kan
Nafisa dake rik'e da kuncinta tana hawaye, sai a
lokacin suka gane ashe anty sa'adah (english
teacher dinsu) ce ta wanka mata mari,,wasu suka
hau yi mta dariya yayin dana kusa da ita sukai tsit
dan suna tsoranta. Anty sa'a taci gaba "ke waye
sa'anki a cikinmu saboda tsabar rashin kunya mu
sa'aninki ne?" Uncle Hashim ya k'araso wajen
"bari ni da ita zanyi maganinta" ya kalli Nafisa
dake ta sheshekar kuka yace "shige muje" ba shiri
ta bishi Zuwa staff room...Dama lokacin tashi
yayi dan haka aka sallami dalibai. Mubeena ce
zaune ita da Asiya a bus stop din skul din,
Mubeena da Amir na jiran drivernsu yayin da
Asiya ke jiran skul bus din unguwarsu Asiya ta
kalli Mubeena "gaskiya Mubeena kin burgeni, ni
dama nasan ke zaki cinye,dama nice ke!"
Mubeena tayi dariya "hmm Asiya kenan kema fa
kinada taki baiwar fa" Asiya tace "tame fa?"
Mubeena ta cigaba" na rubuta labarai mana
novels ni kome zaki min bazan iya rubuta
k'agaggen labari ba wallahi,ke kuwa fa kina iya
k'irkira ki rubatasu kala-kala" Asiya tayi dariya
"kema dai Mubeena nan abinda ni kadai nake
rawa ta nake kida na, in na rubuta da sisters dina
kawai nake bawa su karanta sai kuma ke"
Mubeena tayu murmushi "duk da haka' Asiya tace
"kodayake inmunyi candy inason na fara
publishing din wanda wasu danake rubutawa
wasu kuma na fara typing dinsu a whatsapp ko
facebook wato online writeups" Mubeena tayi
murmushi," lallai ashe kema kin kusa zama su'
Benaxir,Lubbatu,Chuchu,Ybk,Jabo,Faty
axland,etc danaji su Ya Nana na fadan su suna
rubuta online hausa novels ,,kinsan su Ya Nana
sun dage da karatun hausa novels,kullum zaki
gansu mak'ale da waya suna karatun littafi" Asiya
tayi dariya "lah ashe kema haka,wallahi nima
sisters dina haka kullum cikin karatu a whatsapp
har group garesu kala-kala na hausa novels"
Mubeena tace "aiy suna k'ok'ari". Drivern su yazo
suka wuce gida. Suna shiga gida Amir da gudu
yayi falo yana kiransu umma,suka firfito a tsorace
dan a zantonsu wani abun ne ya faru marar
dadi...Yayi wani tsalle ya kalli umma "Yaya
Mubeena ce tazo ta d'aya(ya nuna yatsan sa guda
d'aya) Ummi ta wangale baki "Ai daman nasan a
rina! ina 'yar tawa take? Mubeena ta k'araso tana
murmushi "gani Ummina!" Ummi ta rungumeta
tana murna "Allah ya sanya Alheri" Mubeena ta
amsa, Ameen ummina! Amma kinsan meye?
Ummi ta girgiza kai" next week zamu kuma yin
wata gasar da Nafisa Jameel wanna wadda nake
baku labarinta" Ummi tace "ai insha Allahu zaki
samu nasar 'yata zamu dage da addu'a" Umma
tace "kar kisa tsoro a ranki insha Allahu sai kin
cinye gasar nan" Mubeena tace "Ameen my
mother's" Umma ta cigaba "bari na kira Ameen
na sanar dashi wannan abun arzik'in" ta shiga
d'aki dan dauko wayarta. Murna wajen ya Ameen
ba'a magana sun dad'e suna waya yana bata
kwarin gwiwa akan ta dage zatayi nasara insha
Allahu ta kuma dage da addu'ar daga k'arshe
sukai sallama ta mik'awa Umma wayarta.
Mubeena ce zaune akan carpet din falon Umma
abinci ne a gabanta amma ta kasa ci tayi tagumi
da alama akwai abunda take tunani, Umma ta
k'araso wajen ta tace "Mubeena me ke damunki?
Kinsa abinci a gaba tun dazu kink'i ci? Mubeena
ta d'ago idonta sharkaf da hawaye tace "Umma
wallahi wani labari aka ban yau in na tuno duk sai
naji ba dadi" Umma ta kara matsowa kusa da ita
"na mene?" Mubeena ta share hawayen nata
sannan taba umma labarin da Asiya ta bata na
yarinyar nan me cutar polio data ja mata
paralysed,, Umma itama sai ta fashe da kuka ta
tuno irin gwagwamayar data sha itama lokacin da
Mubeena na k'arama,, Mubeena ta katse mata
tunanin da cewa "Umma wannan dubu hamsin
d'in dana samu a wajen musabak'ar nan nakeso
kiban muje dake muyi mata siyayya kayan abinci
da kayan sawa da kuma daiper size dinta,Atamfar
nan kuma abani guda biyu na kaiwa mamanta
d'aya sannan kuma aba Safi tella ta dinkawa
yarnyar, mu kai gidansu" Umma tayi murmushi
"Kaji d'iya ta kwarai Mubeena ke daban ce!
Kinada zuciya me kyau Mubeena a kullum godewa
Allah nake daya bani 'ya kamar ki, Mubeena Allah
ya shi miki albarka ya kuma albarkaci rayuwarki,"
Mubeena ta ce "Amin Ummana nima ina alfahari
dake, Allah ya saka miki da alheri ya biya miki
duk bukatan ki duniya da lahira" Umma tace
"Amin nagode AISHATUL MUBEENA" amma sai ki
bari Abbanku ya dawo sai a sanar dashi koh?
Mubeena tace "gaskiya kam Allah ya dawo dashi
lafiya"
[11:55AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [90]-[95] Mubeena
tayi shiru can sai hawaye suka fara zirarowa,Asiya
a rude ta fara share mata hawayen "yi hak'uri
Aisha wallahi ba dan na saki kuka nayi wannan
tambayar ba kawai dai..." Mubeena ta katse ta
"bake kika sani kuka ba Asiya... bari na fad'a
miki" Asiya tace "toh inaji" Mubeena ta
cigaba"cutar poliomyelitis (polio) ce ta maida ni
haka! Asiya ta zaro ido "polio??,da kina k'arama
ba'a miki rigakafi ba? Mubeena ta share
hawayenta "eh,nidai kawai watarana na wayi gari
naga kafana ta dawo haka,ba zan iya tuna abinda
suka faru da ba,kuma banasan na tambayi Umma
tunda naga itama basan zancen take ba" Asiya
cikin sanyin murya tace "Allah sarki,Allah ya
kiyaye gaba,ya kuma sauwak'e. Mubeena tace
"Amin". Asiya ta girgiza kai cike da takaici tace
"akwai wata yarinya a unguwar su cousins d'inmu
itama polio ne, itafa ya ja mata paralysed,ga
iyayenta talakawa ne,ko wheel chair ba tada, a
k'asa zakiga sun shanya ta,tayi fitsari etc duk
anan sai dai su gyra,yarinyar 12years amma ta
k'ank'ance sai ki rantse bata fi 4-5years ba abun
tausayi,rannar danaje gidan dubu d'aya(1000) ne
a hannuna wallahi duka na basu naji tausayinsu
ita da iyayenta,har takai ta kawo daga karshe
maman bara takeyi saboda sukansu wani sa'in
abincin da zasu ci gagararsu yakeyi,sun ban
tausayi sosaii" ta k'arasa maganar tana kuka...
Mubeena itama sai ta fashe da kukan, zancen ya
matuk'ar bata tausayi,, ta dage tace "Allah
sarki,shi yasa nake godewa Allah kullum dakuma
iyayena,amma zaki gane gidan? Asiya tace "eh
zangane kusa da gidan su cousins d'inmu ne"
Mubeena tace "insha Allahu gobe zan zo ki
rakani" Asiya tace "to bakomai Allah ubangiji ya
kaimu" Mubeena tace "Amin." Akazo aka
kirasu,Nafisa sai wani iyayi akeyi,bayan an musu
bayanin komai aka raraba musu kayan da zasuyi
zanen akace kowa ya zana abu mai kyau amma
banda abu me rai,an basu minti talatin(30mint)
nan da nan suka fara. Mubeena kuwa exactly
abunda ta zana jiya (har ya Abdul yace yayi kyau
daga k'arshe yace yanso tace ya dauka),ta zana
,tunda taji yace yayi kyau to tasan kuwa tabbas
yayi din da gaske,, dan haka ta k'ara zana irinshi
har yafi na jiya ma kyau... Lokaci ya cika,uncle
Hashim ne ya k'arbi zanen aka bawa masana
zanen da hukumar makarantar ta gayyato takanas
don su duba su kuma fad'i sakamakon tun daga
zanen daya zo na d'aya har zuwa na
k'arshe....Bayan sun dade suna duba suka fadawa
hukumar makarantar result din sannan suka tafi..
Uncle Hashim ne yazo yace musu su koma aji za'a
had'a assambili na mussaman wanda anan ne za'a
fad'i sakamakon. Nafisa tana shiga aji yan aji suka
hau tafi suna mata kirari ita kuma sai busa hanci
takeyi can tace "Sai ku shirya anjima za'ayi
assambili anan ne zaku tabbatar dacewa nice na
lashe gasar" Asiya ta tab'e baki "ba giringirin ba
dai tai mai!" Nafisa tsaki tayi ta juya ta mata
wani kallon raini sannan tace "ni bansan shishigi a
rayuwata ita gurguwar da kike shigewa ai itama a
bayana take wallahi,dukanku nan sai da ku zama
'yan amshin shata dan nice gaba da ku akomai"
Mubeena murmushin takaici tayi ta sunkuyar da
kanta. Asiya a fusace ta tashi "keee!! Ba'a aibata
halitar Allah,ke in banda jahila/jahili ma wa yake
yabon kansa? ,kuma da kike cewa gurguwa ai
Allah ne ya haliceta haka,, a haka yaso ya
ganta,kuma kema baki fi k'arfin Allah ya maida
ke haka ba,wai ke da me kike tak'ama ne? eh?
Nafisa a fusace tace "kut! Ke har kin isa ki zage
ni,"tayi wani kukan kura zata wankawa Asiya
mari,da sauri Asiya ta rik'e hannunta cak! Tace
"karki kuskura ki taba min fuska,niba karya bace
irinki bana dambe,"tana gama fadan haka ta
zauna tabar Nafisa nata kumfar baki,,daidai nan
teachern su ya shigo ,yana shigowa a fusace ya
kalli Nafisa "get out!!" Simi simi tabar ajin tana
gunguni. Malami suka dinga shiga aji-aji suna
cewa dalibai sufito za'ayi asambili na musaman
ba'a dad'e dalibai suka cika wajen assembly din
Nafisa kuwa sai wani tak'ama takeyi. Uncle
Hashim dayake shine me kula da harkar gasar ya
fito ya fara jawabi kamar haka "Gud afternoon
students,,abinda yasa muka tara ku nan ba dan
komai ba dam mu fad'a muku sakamakon gasar
zanen iya makarantarmu da muka gabatar yau,, a
cikin mutane goma da suka yi participating a
gasar mutum biyu zamu dauka wa'enda su kuma
zasu yi tasu gasar next week,a cikinsu kuma mu
dau wadda tazo ta d'aya dan ta wakilci
makarantarmu,, wanda yazo ta goma(10) shine:
Auwal Isah na tara(9 ) Jamila Muhd na 8 Iro
Faisal................,,.wadda tazo ta biyu....Nafisa
Jameel sai kuma zakaran wato wanda/wadda ta
lashe gasar ......(ya k'ara daga muryarsa)
AISHATUL....kan kace meye dalibai suka d'au ihu
suka k'arsawa masa "Mubeena Muhd Ameen.
[12:32AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:53AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [100]-[105] Umma
tace "Amin, wannan satin insha Allahu inason
muje k'auye wajen mama bata ji dadi ba ashe sai
jiya yaya Basiru yake fad'amin a waya" Mubeena
tace "eyyah Allah sarki Mamana Allah ya bata
lafiya" Umma tace "Amin" . Abba ya dawo suka
fad'a masa niyyarsu ta ziyarta iyayen yarinyar
Abba yaji dadi kwarai ya k'ara musu dubu ashirin
(20) akai,, ya dau waya ya kira Ya Abdul "Abdul
Hafeez kana ina ne?" Ya Abdul yace "ina dakina"
Abba yace "toh ka shirya yanzu zaka kai su
Ummanku unguwa kasan driver yayi bulaguro"
Yace "toh gashi nan". Ba dad'e ba kuwa sai gashi
bayan ya gaishesu gaba d'aya,Mubeena ma ta
gaishe shi ya amsa ba yabo ba falasa...Su Ya
Nana ma sukace zasu bisu aikuwa suka shirya
abinsu, Mubeena kuwa hijab dinta ta d'auko ash
colour har k'asa tasa abinta hoda kawai ta shafa
sai farin man leb'e ..ta fito suka shiga mota, se
da suka fara zuwa wani babban mall suka siyo su
kayan abincine,kayan makulashe, kayan sawa,
daiper etc sun kashe kud'i dayawa ... dama
already Mubeena ta taho da wheel chair dinta da
take amfani da ita kan ta fara tafiya don ta bawa
yarinyar. Sai da suka fara zuwa gida su Asiya
suka dauko ta dan ta rakasu gidan,basu dad'e ba
kuwa sai gasu a gidan, k'aramin gida ne na k'asa
wasu wuraren na gidan ma duk ya rushe kana
ganin gida kasan na talakawa ne futuk.. Da
sallama suka shiga gidan a lokacin, wata
matashiyar mata ta amsa musu da fara'a,yayin
data aje tsintsiyar datake shara da ita,,
"Sannunku da zuwa" ta fad'a tana fara'a, Umma,
Mubeena, Ya Nana, Husna da kuma Asiya, Ya
Abdul da Amir suna cikin mota su basu fito ba.
Matar ta shimfid'a musu tabarma suka zauzauna,
ta tashi ta nufi randar ruwa ta d'ebo musu ruwa
a kwanon sha ta aje a gabansu, Sannan ta zauna
suka gaigaisa, matar tace "sai dai kuma ban gane
kuba, waccan kawai na gane(ta nuna Asiya) ko
yan gidansu ne?" Umma tayi murmushi sannan ta
fad'a mata dalilin zuwansu, matar sai hawaye
kawai tace "Nagode kwarai Allah ya biyaku dama
in Allah ya kawo makashinka sai ya kawo me
ceton ka" Umma tace "gskiya ne, ina yarinyar"
Matar tace " YUSRA tana cikin d'aki ku shigo"
suka shiga dakin. A kwance suka tadda ita sai
kallonsu takeyi ta kalli Mamanta "Mama suwaye?"
Maman tayi murnushi "bak'i ne suka zo duba ki"
A tare su Mubeena suka had'a baki "ya jikinki?"
Tace "da sauk'i" Mubeena ta kura mata ido sai
hawaye sharr ta sunkuyar da kanta tana kuka a
hankali... ita kuwa Umma godewa Allah tayi da
banda taimakon Allah ba da tuni itama suna cikin
wannan halin... Umma ta dage ta ce "Ina
mahaifinta?" Maman tayi murmushi takaici "Aiy
bama tare yanzu nan gidan iyayen mune da suka
mutu suka bar mana nida k'anina anan muke
zaune, tunda muka rabu da mahaifinta be kuma
waiwayar mu ba" ta fashe da kuka,, Umma ta
runtse ido sai hawaye, a zuciyarta tace "ashe
akwai masu hali irin nan Mal Sule a duniya? Allah
wadaran wannan mumuman hali tur dashi! Itama
da tuni fa tana cikin wannan hali kai dole ta
godewa Allah daya musan yamata da mafi alheri"
Umma ta share hawayenta tace " nima kinga 'yata
nan itama polio ne amma ita kafarta ce kawai"
Maman tace "Allah sarki ita yazo mata da sauk'i
ma". Nan da nan wasu maza suka fara shigowa da
kayayyakin da su Mubeena suka siyo,, Maman
tsayawa tayi tana kallon ikon Allah ta kasa
magana ma saboda tsabar murna,, Umma ce ta
katse dacewa "gashi wannan kyautace daga
AISHATUL MUBEENA ga wannan daiper sai ku
dinga saka mata kinga kin huta da wanki kashi da
fitsari sai dai kawai ki cire a tsaftace, ga kayan
makulashe nan ana bata, ga Wheel chair nan
shima a dinga dora ta ana zagayawa da ita itama
ta zaga gari,, duk dai gasu duk naku ne
malakinku ne ga wannan(ta mik'a mata dubu
ashirin(20) da Abba ya bada) sak'o ne daga
Abbansu kwayi wani abun dasu, Allah ya k'ara
sauk'i" . Maman ta fashe da kukan murna "duk
mukadai? Allahu akbar ashe akwai mutane irinku
AISHATUL MUBEENA mun gode kwarai Allah ya
biyaki ya daukaki bansan dame zan gode muku
ba, bansan da wata kalma zanyi amfani na gode
muku da ita ba, Allah ya biyaku, ya kare ku ya
biya muku buk'atunku duniya da lahira, Mubeena
da za'a sami mutane irinku da yan uwanku masu
wannan masifafiyar cuta ta polio basu wahala
ba,da basuyi bara akan titi ba, da kuma wasun su
basu rasa ransu ba saboda wannan cuta,," ta
k'ara fashewa da kuka. Mubeena ta k'araso
wajenta ta rungume ta tana kuka "Maman ki dena
kuka,a kullum raina yakan baci inda naga yan
uwana masu irin wannan cuta suna wahala ,
inason in taimakawa yan uwa masu irin wannan
cutar mussaman ma wa'enda basu da bud'i
irinku,, kar ki gode min ki gode dan Allah"
Maman tace "Allah sarki Allah me baiwa" Yusra
dake kwance tace "mun gode Anty Mubeena".
*** ina gayyatar ku zuwa sabon group din dana
bude yau a facebook, masu yin facebook sai kuyi
searching "MISS HAFCY NOVELS" Nagode
Like · 2 ·
[11:53AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [95]-[100] Uncle
Hashim murmushi yayi yace "To kunyi gueesin
right" Nafisa kuwa iya kulawa ta kulu batasan
sanda taji hawaye ba,dataga abin ya fara isarta
sai ta fara zage-zage "wallahi bazan yadda ba!
Wannan ma aiy sankai ne, aikin banza
kawai,kuma...bata k'arasa maganar ba taji saukar
mari a fuskarta ji kake tas! Kallo ya dawo kan
Nafisa dake rik'e da kuncinta tana hawaye, sai a
lokacin suka gane ashe anty sa'adah (english
teacher dinsu) ce ta wanka mata mari,,wasu suka
hau yi mta dariya yayin dana kusa da ita sukai tsit
dan suna tsoranta. Anty sa'a taci gaba "ke waye
sa'anki a cikinmu saboda tsabar rashin kunya mu
sa'aninki ne?" Uncle Hashim ya k'araso wajen
"bari ni da ita zanyi maganinta" ya kalli Nafisa
dake ta sheshekar kuka yace "shige muje" ba shiri
ta bishi Zuwa staff room...Dama lokacin tashi
yayi dan haka aka sallami dalibai. Mubeena ce
zaune ita da Asiya a bus stop din skul din,
Mubeena da Amir na jiran drivernsu yayin da
Asiya ke jiran skul bus din unguwarsu Asiya ta
kalli Mubeena "gaskiya Mubeena kin burgeni, ni
dama nasan ke zaki cinye,dama nice ke!"
Mubeena tayi dariya "hmm Asiya kenan kema fa
kinada taki baiwar fa" Asiya tace "tame fa?"
Mubeena ta cigaba" na rubuta labarai mana
novels ni kome zaki min bazan iya rubuta
k'agaggen labari ba wallahi,ke kuwa fa kina iya
k'irkira ki rubatasu kala-kala" Asiya tayi dariya
"kema dai Mubeena nan abinda ni kadai nake
rawa ta nake kida na, in na rubuta da sisters dina
kawai nake bawa su karanta sai kuma ke"
Mubeena tayu murmushi "duk da haka' Asiya tace
"kodayake inmunyi candy inason na fara
publishing din wanda wasu danake rubutawa
wasu kuma na fara typing dinsu a whatsapp ko
facebook wato online writeups" Mubeena tayi
murmushi," lallai ashe kema kin kusa zama su'
Benaxir,Lubbatu,Chuchu,Ybk,Jabo,Faty
axland,etc danaji su Ya Nana na fadan su suna
rubuta online hausa novels ,,kinsan su Ya Nana
sun dage da karatun hausa novels,kullum zaki
gansu mak'ale da waya suna karatun littafi" Asiya
tayi dariya "lah ashe kema haka,wallahi nima
sisters dina haka kullum cikin karatu a whatsapp
har group garesu kala-kala na hausa novels"
Mubeena tace "aiy suna k'ok'ari". Drivern su yazo
suka wuce gida. Suna shiga gida Amir da gudu
yayi falo yana kiransu umma,suka firfito a tsorace
dan a zantonsu wani abun ne ya

Please Login or Register in order to submit comment