You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rasu bama,
'yayan mijnata kuwa Bashir da Hauwa sun dad'e
da dena kulata bama sa k'asar gabadaya. A 'yan-
uwanta kuwa ita kad'ai tayi ragowa duk sun
rasu,, sai dai sauran dangi da ba'a rasa
ba..Masa'udu dama shi ake yiwa gaisuwar dan
shine ya kula da ita tun data sami rashin lafiyar
har ta warke, shima kuwa a rannar data rasu
admission dinsa ya fito yaci Ahmadu Bello
unibasiti zaria(ABU zaria) dan haka ya had'a
kayansa ya tafi Umma kuwa kud'i me yawa ta
bashi tace yayi harkar makaranta dashi ya yafi
yana ta godiya.
[12:35AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [11:46AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [135]-[140] Bayan an
dawo hutun tak'aitacen lokaci. Aysha Amatulah:
to barkan mu da dawowa. Hajiya Mubeena shin
wai ta yaya kika tsunduma cikin harkar zane-
zane? Mubeena: To agaskiya nidai na taso ne
kawai na gani inayi, a lokacin inga abu ya min
kyau sai na zana shi, cikin ikon Allah kuma sai
kiga zanen ya fita sosaii...lokacin da ina primary
kuma in kika duba littafai na na arts zaki ga inaci
sosaii, koda merit za'a bada ma a Art ni ake
bawa. Kuma akwai Yayana Ya Ameen shine ya
cigaba da ban kwarin gwiwa har nazo matakin
danake yanzu. Aysha Amatullah: madalah, to
kafin ki fara wanan zane-zanen mene burinki a
rayuwa? Mubeena: Burin na da shine na zama
likita dan nima na bada gudunmawa ta wajen
yak'i da wannan cutar sai kuma Allah beyi ba.
Aysha Amatullah: to Allah zaba mafi alheri, meye
ya fi b'ata miki rai da kuma abinda yafi faranta
miki rai? Mubeena: Abinda ya fi b'ata min rai
guda biyu ne na d'aya ya shafi personal life dina,
na biyun kuwa shine, idan naga yan'uwana masu
wannan cuta ta polio suna bara ko kuma suna
cikin wani hali na rashin gata a gaskiya raina na
sosuwa kuma ina iya k'ok'ari na dan ganin na
taimake su. Sannan abinda yafi faranta min rai
shine, ina tuno irin nasororin dana samu a
rayuwa, sannan kuma ina ga masu irin cuta ta
wato polio basa fuskantar wani k'alubale a
rayuwa ,suna jin dadin rayuwarsu sannan suna
samin gata daga wajen iyayensu dama al'uma
baki d'aya, to nakan ji raina yayi fari . Aysha
Amatullah: Allah sarki, yanzu zamu d'auki waya
guda biyu(2) duba da yanayin lokaci, zaku turo
sak'o ne ta wannan lambar 064**** sannan zaku
kira mu ta 064****. Mutane an kira an mata
fatan alheri, an kuma turo sak'oni ba adadi.
Aysha Amatulah:wani kira zaki yi ga iyaye da
kuma masu cutar polio? Mubeena: kiran da zanyi
shine dan Allah iyaye su dinga bada yayansu a
dinga musu d'igon rigakafi, sannan iyaye su dage
su dinga gano talent din da suke dashi su
k'arfafa musu gwiwa, bawai su dinga barinsu
suna bara ba, da sauransu. Sannan irina masu
wannan cuta ta polio, ganin suna da nakasa kar
hakan yasa su fidda rai da rayuwa , su d'age suyi
karatu suma su zama wasu a dinga damawa
dasu, in hakan ya faru zan fi kowa farin ciki.
Aysha Amatullah: to duba da yanayin lokaci mene
sak'on ki na k'arshe? Mubeena: to Alhamdulilah
ba abinda zance sai in godewa Allah da kuma
iyayena nakan ji farin ciki sosaii in na tuno da
iyayena,yayena da k'anina, da sauran dangi.
Aysha Amatulah: to masu sauraron mu lokaci
yayi halinsa , anan zamu k'ark'are wannan shirin,
Hajiya Mubeena muna godiya da kika amsa
gayyatar mu, da fatan duk sanda muka sake
neman ki zaki amsa kiranmu. Mubeena: to nima
nagode masu saurarona da kallona ina muku
fatan Alheri,(tayi murmushi) sai anjima. Ahaka aka
gama shirin, ta fito driver yaja suka tafi.
*********** A yau ne aka d'aura auren Ameen
Muhammad Ameen da Fatima Adam, Aisha
Muhammad Ameen(Nana) da kuma Saifulahi
Abdalah. Ansha biki sosaii an kuma kashe kudi
dai-dai misali, Mubeena kuwa lemukan nan da'aka
bata kyauta su ta bada akayi hidimar biki da su,
sannan katuwar jaka da calanda me sunayen Allah
ta musu a matsayin gudunmawa sun sha murna
tare da yi mata addu'ar Allah ya saka mata da
alheri. Bayan biki aka kai amarya Nana gidanta
dake Hotoro, Sannan amaryar Ya Ameen Faty aka
kaita gidan ta dake Janbulo. A yau su Mubeena
sukayi final exam dinsu, sunsha kukan rabuwa da
dalibai, Mubeena da Asiya ma ansha kuka,
malamai sunyi bak'in cikin rabuwa da Mubeena
sosai , hadda masu kwala, bayan sunyi sharing
contacts driver yazo ya d'auki Mubeena suka
koma gida, Mubeena cike da kewayar dalibai,
malamai dama makarantar baki d'aya. Yau ta
kama rannar lahadi kuma dama duk Lahadin
k'arshen wata sukan je shopping... Suna cikin
mota dan zuwa shopping d'in Abba ne ke driving
dan yau yace sha'awar driving yake saboda ya
d'ad'e beyi ba, Umma na gaba, yayin da Husna,
Amir da Mubeena ke bayan mota Ummi kuwa taje
bikin 'yar aminiyata. Suna tafe cikin raha da
anashuwa. Can wata mota ta taho da gudun
gaske, dai-dai lokacin da wani datijjon mutum
yazo tsalaka titi, ai kuwa fuu motar ta bige shi,
bata ko tsaya ba drivern mota ya k'ara falawa da
gudu, cikin 'yan sakani aka dena hango motar sai
k'ura da motar ta tayar... shikuwa dattijon
mutumin nan yana baje a titi jini sai zuba yake.
Abba da sauri ya fito daga motar yana salati
suma su Umma suka fito dan ganewa idonsu, a
firgice suka k'araso wajen da mutumin ke kwance
cikin jini, Umma da ta k'araso wajen da sauri,
dora idonta akan mutumin keda wuya ta kwala
wani k'ara anan ta fad'i k'asa sumamiya!
Lik
[11:47AM, 18/03/2016] Hapsat: ◆◆◆AISHATUL
MUBEENA◆◆◆ ©MISS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [130]-[135] Nan take
wajen ya d'auka sai ihu akeyi su Husna dake gefe
sai dariya suke yi dan sunsan Mubeena yau ta
shak'i haushi itada ko hannunta bata san wani
namiji ya tab'a, sai gashi yau k'aton arne ya
d'aga ta, shikuwa Ya Abdul ji yake kamar yaje ya
wankawa Mr Mike mari dan haushi. Da kyar ta
samu ya sauke ta k'asa, ai kuwa sai tabar
wajenshi ta koma d'ayan banganren, sai
d'aukanta hoto ake. Certificate aka bata ta,
sannan aka buk'aci ta sa hannu taje ta saka kuwa,
sannan aka mik'a mata shi, bayan nan aka shiga
raba kyautuka ga wanda suka yi participating
kyauta kuwa ta samu kala-kala, kamfaanin wani
shahararen lemu ya bata da kuma sauran
participant's d'in kud'i da kuma lemuka, kyauta
dai iri-iri ta sha su wai kuma aka samun tab'i ne
dan ba'a bata babbar kyautar tata ba. Check na
miliyan d'aya(1) aka bata daga hukumar da suka
shirya gasar sannan kuma k'ungiya masu zane
dake kano suka bata kudi naira dubu d'ari(100).
Mr Mike ne ya d'auko wasu sarkok'in medal's
guda uku(3) 'yan k'anana d'aya na gold d'aya na
silver na ukun kuma na bronze. Ta uku ya rataya
wa bronze medal aka fara tafi ana d'aukan
hotuna, sannan ya kira Ahmad Huzaifa ya rataya
masa na silver, shima aka d'au tafi. Bayan nan
kuma wakilin gwamnati ya tabbatar mata da
cewa bayan ta kammala karatun sakandire
gwamntani zata d'auki nauyin ta taje tayi course
din zane a wata makatantar zane-zane(art school)
dake amurka(America) Na gold din kuwa
Mubeena ya ratayawa nan waje ya k'ara d'aukan
ihu 'yan jarida nata d'aukan hoto da kuma hoto
mai motsi(video) domin a yawancin kafafen yad'a
labarai ta talabijin abin live ake nunawa. Su Abba
dake zaune suna kallo LIVE murna a wajensu
kamar me, sun ma rasa me zasuyi saboda murna,
hak'k'ika wannan rana tana cikin rana mafi farin
ciki a rayuwarsu, mussaman ma Umma da
alk'warin da tayiwa Mal Sule ya cika yau, a
zuciyarta cewa take dama Mal Sule ya ji ko ya ga
wannan abin alherin. Bayan an kammala taro aka
rufe taro da add'ua, nan aka fara d'aukan hotuna
dasu Uncle Hashim da bakinsa ya kasa rufuwa
saboda farin ciki, su Ya Abdul ma haka, kana
ganinsu zaka gane irin halin da suke ciki. Zanen
kuwa tafiya Mr Mike zeyi dashi, inda za'a kai shi
wannan babban ART GALLERY dake Abuja. Su
Alhaji Bawa basu so hakan ba dan su sunfi san a
barshi a Art gallery din dake kano amma ba
yadda suka iya. Fitowar su Mubeena ke da wuya
wakilan 'yan jarida da gidajen radio sukawo mata
caa akanta, sai tambayoyi suke mata tama rasa
wadda zata amsa, can dai tace "Alhamdulilah ba
abinda zance sai godiya ga Allah da ya bani
nasara a wannan gasar, sannan ina godewa
iyayena da suka bani k'warin gwiwa har nazo
matakin dana ke yanzu! Nagode.". Tana gama
fad'an hakan tayi hanyar motarsu. Zwan ta keda
wuya ta tadda wakilan wani shahararen gidan TV
suna jiranta, numfasawa tayi tace "wannan shine
anyi gudun gara an tadda zago". Nan suka shiga
yi mata magiya akan suna so su tautana da ita
gobe, saboda gobe ne ta kama rannar masu
cutar polio da duniya wato (WORLD POLIO DAY)
wato ashirin da hud'u ga watan oktoba(24th
october) bata musu musu ba kuwa ta amsa sunyi
farin cika sosaii inda suka bata wani kati na
gayyata. Farin ciki ya dawo sabo sanda suka
koma gida su Umma hadda kukan murna, Ya
Ameen dake can k'asar holland ya sami labari
daya duba news ya kira su aka sha murna,
makarantarsu kuwa dayake tana final year suka ce
sun d'auki nauyin ta har ta gama su waec da
neco duk zasu biya mata, saboda ta fito da
sunan makarantarsu, bayan k'ananun kyaututuka
da suka bata. Yau ta kama 24th october(World
polio day), tun da safe ta ta shirya driver ya
kaita dan Ya Abdul ya tafi wajen aiki. Tana zuwa
dama ita suka jira, aka shirya komai tazo ta zauna
akan kujerar da za'a tautauna da ita.(wasu
gidajen radio suma sun juno dan masu saurarun
radiyo suma suji) Me gabatarwa ta fara:
Assalamu alaikum warahamatul lahi ta'ala wa
barkatuhu masu kallo da sauraranmu. Barkan mu
da sake saduwa a wannan shiri na mussaman da
muke gabatarwa duk a rannar polio ta duniya
duk shekara. A yau shirin namu yayi babban
kamu, domin yau zamu tautauna da AISHATUL
MUBEENA Muhammad Ameen, wadda itama ta
zamo polio victim ta farko tada fara lashe gasar
zane-zane dake gabatarwa duk bayan shekara
hud'u a jihohi dama k'asa baki d'aya... Sunana
Aysha Amatullah wadda zan gabatar da shirin,
Hajiya Mubeena ko nace Artist Mubeena barka da
zuwa. Mubeena: Barka kadai. Aysha Amatullah:
shin zamu iya jin tak'aitacen tarihin ki? Mubeena:
To Alhamdulilah, nidai sunana Aishatul Mubeena
Muhammad Ameen an haifeni a garin Kano na
taso a Kano, kuma a yanzu haka inada shekara
sha bakwai next year zan shiga sha takwas(18),
saboda ban fara makaranta da wuri ba yanzu dai
ina ss3 a sakandire. Aysha Amatullah: Masha
Allahu, shin kina shekara nawa wannan cuta ta
sameki? Kuma mene ne dalili? Mubeena: A
gaskiya wannan cuta ta same ni ina 3-4 years,
dan dama kinsan a yara masu shekara d'aya zuwa
biyar(1-5) tafi kamawa..kuma a gaskiya zan iya
cewa wannan cuta kaddara ce daga Allah, dama
can Allah ya riga ya rubuta cewa a haka zan
tashi, cutar zata same ni. Aysha Amatullah: to
madalah, wani kalubale kika ko kike fuskanta?
Mubeena: Alhamdulilah a gaskiya nidai k'alubalen
dana fuskanta be huce lokacin da ina k'arama ba,
lokacin danake koyan tafiya, amma bayan haka
ban fuskanci wani k'alubale ba gaskiya. Aysha
Amatullah: to masu kallo da sauraranmu, kunji
yadda hirar mu ke kasancewa, yanzu zamu je
hutun tak'aitacen lokaci
Share
Comment as:
Publish Preview
No comments:
Post a Comment
MissHafcy
View my complete profile
About Me
► 2017 (16)
▼ 2016 (34)
► November (1)
▼ October (33)
WELCOME
ASMAUL HUSNA 6
ASMA'UL~HUSNA
ASMAUL~HUSNA 4
ASMAUL~HUSNA 3
ASMAUL HUSNA 2
ASMAUL HUSNA
AISHATUL MUBEENA 155-160
AISHATUL MUBEENA 145-155
AISHATUL MUBEENA 110-140
AISHATUL MUBEENA 85-105
AISHATUL MUBEENA 60-80
AISHATUL MUBEENA 45-60
AISHATUL MUBEENA 30-40
AISHATUL MUBEENA 20-30
AISHATUL MUBEENA 1-20
WANI HANIN END!
WANI HANIN 26-27
WANI HANIN 24-25
WANI HANIN 22-23
WANI HANIN 20-21
WANI HANIN 19-20
WANI HANIN 15,16,17&18
WANIN HANIN 12,13,&14
WANI HANIN 11
WANI HANIN 9&10
WANI HANIN 7&8
WANI HANIN 5&6
WANI HANIN 3&4
WANI HANIN 2
WANI HANIN 1
....
WANI HANIN
Blog Archive
Miss_Hafcy. Watermark
AISHATUL MUBEENA 145-155
[12:37AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆ ©MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS [140]-[145] Abba
cikin rud'ewa ya d'auko wayarsa yayi dailing
numbern drivern asibitin shi, ya mai kwatacen
inda accident d'in ya faru, yayinda ya d'auki
Umma ya sata a motar su, su Mubeena kuwa duk
sun rud'e. Sai da suka jira Motar asibiti tazo, da
taimakon mutanen wajen aka sa mutumin a Mota
suka bi bayan su Abba dan zuwa asibiti.
Emergency aka shige dasu, Umma kuwa bata
dad'e ba ta farfado dan haka aka kaita resting
room, shikuwa mutumin likitoci suka duk'ufa
akansa ana duba shi. Bayan Umma ta farfad'o ta
dawo dai-dai sai kuma kuka, kuka take sosaii
tama kasa magana, Abba dake gefenta sai
lalashinta yake, su Mubeena kuwa suna reception
suna jira. Abba cikin sanyin murya yace "Asma'u
wai meya faru ne? Kinada alak'a da mutumin nan
ne ko kuwa me? Daga ganin mutum sai ki yanke
jiki ki suma, ke da kike da hawan jini, Allah ya
taimaka ma jininki be hau sosaii ba.....Asma'u
magana fa nake miki kin min shiru, kukan nan ba
abinda ze amfana miki dashi fa". Umma kasa
magana tayi kawai sai runtse idonta tayi tana
kuka a hankali, wata Nurse ta shigo sanye da
kayan Nurses ta kalli Abba " Doctor, Dr.Faruk ya
gama dubashi mun samai bandage da komai,
yanzu ma mun canza masa daki, kuma da alama
ya dawo hayyacinsa ma, Abba ya kalleta "okay
nurse Sadik'a, muje d'akin naga jikin nashi"
zumbur Umma ta mik'e tana k'ok'arin binshi,
Abba ya juyo da mamaki " Asma'u ina zaki?", ta
kalleshi "inda zaka je" murmushin tak'aici yayi,
sannan yace" to muje", yana gaba, tana binshi a
baya har suka isa zuwa d'akin mutumin. Yana
kwance idonshi na kan celling sai zubar da
hawaye yake yi, Umma ta k'araso wajen sa a
nutse, tace "ya jiki?" yana had'a ido da ita ya
kauda kansa cikin muryar sa da bata fita yace "
Ma'u yau gizon naki da kike min hadda magana?
Kodai mafarki nakeyi? Ina ne nan?. Ma'u tayi wani
murmushin tak'aici sannan tace "ba mafarki kake
ba, kuma ba gizo nake maka ba, kalle ni da kyau
kagani, nice dai Ma'u mahaifiyar nakashashiya,
nice dai Ma'u wadda ka tsana kake hantara
saboda kawai ta haifa maka d'iya mace kuma nice
dai Ma'u wadda ka wulak'anta daga k'arshe ka
sake ta, nice dai Ma'u tsohuwar Matar azzalumi
MALLAM SULE, ta fashe da kuka.. Abba ya dafa
kafad'arta yace "ya isa haka Asma'u muje gidan ki
d'an huta, anjima ma dawo muyi maganar (ya
kalli Mal Sule, Allah ya k'ara sauk'i) suna k'ok'arin
fita ya kalleta yace, "and inaso ki share
hawayenki", ta kalleshi "toh" sannan ta share
hawayen, Abba yace to muje ta shige suka tafi.
Bayan sun shiga gida Umma kai tsaye dakin ta ta
shige ta kwanta, zuciyarta fal da tunane-tunane
kala-kala, Mubeena ta turo kofar d'akin ta shigo,
a kan gado ta tadda ta tayi tagumi, Mubeena ta
zauna a bakin gadon tace " Ummana wai meya ke
damun ki ? Waye wannan mutumin? Meya miki?
Har ganinsa ya sa ki suma? Umma ta juyo ta kali
Mubeena sannan ta dafa kafad'arta tace "
Mubeena wannan mutumin bakowa bane illa
MAHAIFINKI Mal Sule! , Mubeena ta zaro ido
"mahaifina kuma?" Umma tace " tabbas"
Mubeena ta d'an yi jim sannan ta tashi da sauri
ta nufi d'akinta, tana zuwa ta haye kan gado ta
fashe da kuka, a daren rannar kuwa gabad'ayan
daga ita har Umma kasa runtsawa sukayi.
Washegari........ Da sassafe suka tashi suka shirya
gabad'aya 'yan gidan suka d'unguma suka tafi
asibitin Abba, Mubeena cike da d'okin taje taga
wannan babanta da baya santa. A kwance suka
tadda shi, yau ma kansa na kan celling sai
hawaye yake, daga ganin bayan damuwar dake
tatare dashi akwai zafin ciwo ma, yana kallonsu
ya kauda kai , Mubeena ta k'araso wajenshi da
sauri dan ya bata tausayi sosai, bakin gadon shi
taje ta zauna cikin sanyin murya tace "Baba ya
jiki??? *****ku yi hak'uri na rashin jina da kukayi
kwana biyu, wayata ce ta sami matsala shiyasa,
Nagode.***
[12:38AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
[145]-[150]
©MISS HAFCY
®NWA
Ya juyo cike da mamaki, cikin muryarsa da bata
fita yace "Allahu Akbar, Alhamdulilah ashe akwai
rannar da nima zanji d'an ko 'yar dana haifa ta
kirani da Baba?" Mubeena tace " ai dama can
kane bakso kaji ba da'ace kaso kaji da baka
wulak'antani nida mahaifiyata ba" ya kauda kansa
"hak'ika nayi kuskure babba na kasance mutum
mara godiyar Allah, dan Adam butulu, ku yafe
min dan Allah" ya fashe da kuka.
Mubeena ta runtse ido sai hawaye ta kalleshi "ai
saika fara nemin gafarar Allah domin Allah
gafurur rahim ne" Abba yace "Mal ya jiki?" Mal
Sule yace "jiki da sauk'i".
Mal Sule yace " ni naga rayuwa, naga sakayata,
Allah yaban 'ya mace amma fir nak'i gode masa
sai ma sab'o dana dinga yi kala-kala, ya kalli
Umma datayi shiru tana sauraransa, Bayan
rabuwar mu dake, a k'auye duk inda na nemi
aura ba'a bani, saboda abinda na aikata ya baza
gari sosaii mutane sai suke kyamar hadda jini
dani,,, rannar sai na yanke shawarar komawa
birni wajen yayana Bashir, anan ya bani kudi da
d'an dama yace naje na ja jari, naje na sami d'an
k'aramin gida me d'aki biyu da bandaki na bud'e
shagon kayan masarufi na sami mata na aura,
amma shiru ba haihuwa data gaji tayi tafiyar ta, a
tak'aice dai wallahi sai dana auri mata sunkai
biyar(5) ciki harda masu ciki guda biyu2, wai dan
duk su haifi d'an a gidana na rene shi ya zama
d'ana, amma abin mamaki a cikinsu ba wadda ta
tab'a haifar cikin a raye a mace suke haifosu.
Daga baya auren ya gagara jari na ya cinye na
zamonto banda komai,na koma gidan yayan nawa
shima na tadda basa k'asar ma gabadaya,,,
rayuwa tamin zafi abincin da zanci gagara ta
yake, tun daga nan na fara nadamar abinda na
aikata, nakuma tabbatar da cewa hak'in ku ne ku
da Iya yake bina, na taho neman ku shine mota
ta kad'e ni kuka taimakeni" ya fashe da kuka.
Gabad'ayansu jikinsu yayi sanyi, kowa yayi shiru
Mubeena cema ke kuka a hankali, ya kalli
Mubeena 'yata ki yafeni, ki yafeni dan Allah kar
na mutu da hakk'in ki akaina na cuce ki, na cutar
da rayuwarki,(ya juya wajen Unma) Ma'u kema ki
yafeni dan Allah, a lokacin da kike ce akwai
rannar da zanyi nadama bazata min amfani ba
ban yadda ba, sai gashi yau ga rannar nan tazo,
ki yafeni, kuma dan Allah ki kaini wajen Iyata
itama na rok'i gafararta, kar na mutu da hak'inta
akaina"
Umma tana hawaye tace "bakomai na yafe maka ,
Allah ya yafe mana baki d'aya, Amma Iya babu,
Allah yai mata rasuwa, sai dai kan ta rasu tace ta
yafe maka" ya fashe da kuka " wayyo Allah na iya
ta rasu? Innalalhi waina ilaihi raju'un KAICONA!
Na cuci kaina,, Umma tace "ga dai 'yarka kamar
yadda na fad"a maka zata zamanto abar
kwatance kuma duniya ta santa akan abin alheri
to Allah yayi, yanzu duk shafukan jaridar daka
duba zaka labarinta, gidan rediyo dana talabijin
dama..." Abba ya katse ta "ya isa haka ! Me ya
kawo wannan zancen kuma, komai ya wuce
mubar maida hannun agogo baya".
Ya kwantar da murya yace "kuyi hak'uri kai kuma
tunda sun yafe maka har Iyan ma ta yafe maka,
ka gode Allah,k a kuma cigaba da nemi gafarar a
wajen Allah domin kamar yadda 'yarka ta fad'a
ma Allah gafurur rahim ne"" Allah ya sawwak'e,
mu bari mu tafi,(ya kallesu)"kuzo mu tafi"
Mubeena ta share hawayenta tace "ni ku barni
anan zanyi jinyarsa" da mamaki suka juyo "me?"
Tace "cewa nayi zanyi jinyarsa" Mal Sule yayi tari
"a'ah zan zauna nan ma nagode d'iyar kirki, Allah
ya shi miki albarka, tace "amin, amma zan zauna
d'in anan,,da kyar ya rok'e ta ta hak'ura tace
zata bisu. Da kuma alk'warin kullum zasu dinga
zuwa suna duba shi.
Yau kimanin kwana biyar5 kenan da ganin Mal
Sule, a ranna ta biyar d'in kuwa Allah yamai
cikawa sun sha kuka sosaii da sosaii mussaman
ma Mubeena data rasa Uba, haka dai suka sha
kukansu su gaji suka daina. Tare dayi masa
addu'oi kala-kala.
**********
Admission d'in Mubeena ya fito nan da wata
d'aya zata tafi America.
Abba ne zaune a falonsa gefensa Ummi ce tana
karanta jarida,,ya d'an yi jim sannan yace "nikuwa
Hadiza wata shawara na yanke, amma bansani ba
ko ke zata miki,, Ummi tace "tame fa?" Abba
yayi gyran murya sannan yace
"Akan yarinyar nan ne Mubeena kinsan admission
d'inta ya fito nan da wata d'aya1 zata tafi
America gashi shekara biyu 2 ne sai nake ganin
kamar be dace mu barta ta tafi ba muharami
ba,kuma kinsan ta isa aure shekara sha takwas da
d'ori ai ba kad'an bane, dan haka na yanke wata
shawara......
Ummi ta gyra zama tace "gaskiya ne wannan,
amma shawarar me ka yanke?" Abba yayi
murmushi " ina so zan had'a ta aure da Abdul-
Hafeez ne!, kinga dama already an sa rannar
Husna sai a had'a a d'aura auren tare! Ummi da
mamaki tace "gaskiya ne, amma a gaskiya sai a
kira su yaran aji ta bakinsu in sun amince falilahil
hamd in basu amice ba kuma shikenan sai asan
abin yi"
Abba yace " dad'i na dake garaje baki tsaya kinji
me zance ba kin tari numfashina, dama ya za'a yi
na d"aura musu aure ba amincewarsu? Kuma
bazan musu auren dole ba, yanzu dai je ki kira
min 'yar uwarki Asma'u itama muji ta bakinta,
Ummi a sanyaye ta nufi part d'in Umma ta kira
ta suka nufo wajen Abba a jere.
Abba yayi mata(Umma) bayanin abin itama tayi
mamaki sosaii dan a ganinta Abdul ya wuce ajin
Mubeena amma dai sai tacewa Abba Allah zab'a
mafi alheri yaji dad'i sosaii.
Abba dakansa ya d'au waya ya kira Ya Abdul ya
kuma ce masa yazo yana son ganinsa, yace gashi
nan, sannan ya sa Umma ta kira Mubeena suka
zauna suna jiran Ya Abdul. Mubeena cike da
fargabar ko wani laifin ta aikata..
Be dad'e ba ya shigo sanye da shadar light bleu,
Abba ya kalleshi " kai dai Abdul Hafeez har yanzu
baka girma ba?, kasa shadda manyan kayanmu
na hausawa, kuma kana yawo kai a haka ba hula,
ina hularka? Ya sosa k'eya "tana daki wallahi ina
sauri ne dats y kaga na barta, yi hak'uri", Abba
yace bakomai zauna nan muyi magana.
Ya zauna, sai a lokacin ya lura da Mubeena dake
kan kujera kanta a sunkuye kallo d'aya yayi mata
ya kauda kai.
Abba ya fad'a musu hukuncin da ya yanke,dum!
Gabansu ya fad'i gabad'aya, Mubeena kuwa
murza idonta anya ba mafarki nake ba? Ta fad'a
a zuciyarta, shikuwa Ya Abdul suman zaune yayi
yama kasa magana, Abba dayaji shirun yayi yawa
yace "ya dai? Ya kukayi shiru?" Ya Abdul ya dage
yace " Allah ya zab'a mafi alheri" Abba yace
"Amin Alhamdulilah" kefa? Mubeena tace "Allah
zab'a mafi alheri na amince, Abba yaji dad'i
sosaii ya kuma cewa su Umma su fara shirya
shiryen biki.
Abba ne ya sanar da Ya Ameen shima yaji dad'i
sosaii dan dama ya dad'e yana wannan tunanin,
ya fad'a wa Faty matarsa dake d'auke da ciki
itama tayi murna sosaii, ta kuma musu fatan
alheri.
Umma ta sanar da daginta, suma sukayi fatan
alheri, dagin marigayi kuwa dama basan nan,
kuma dama bama su wani saba ba dan in ta
gansu yanzu ma bazata gane su ba.
Shirye shiryen biki akeyi sosaii, amare kuwa suna
ta shan gyra kala-kala Ya Nana da itama ke dauke
da ciki itama ta taimaka musu da shawarari da
magunguna da sauransu.
Abin mamaki kuwa Mubeena da Ya Abdul har hira
sukeyi sun fahimci junasu ba laifi.
◆◆RANNA BATA K'ARYA SAI DAI UWAR D"IYA
TA JI KUNYA◆◆
A yau ne aka d'aura auren ABDUL HAFIZ
MUHAMMAD AMEEN DA AISHATUL MUBEENA
M. AMEEN akan sadaki dubu hamsin (50) da kuma
na Husna Muhammad Amin da angonta Al'amin
Jafaru akan sadaki dubu arba'in(40) .mutane
dayawa sun hallaci d'aurin auren.
Bayan d'aurin aure ba ai wata bidi'a ba yini kawai
akayi sai kuma kamu kan d'aurin auren , dagin su
Al'amin ne ma suka shirya dinner suka gayyaci
amaryarsu Husna taci kwaliyarta taje kuwa.
Mubeena kuwa kallo d'aya zaka mata kasan tana
farin ciki, dan ta godewa Allah ba adadi saboda
cika mata burinta da yayi. Ta kuma yiwa babanta
da kuma kakarta addu'a sosaii. Sannan a kullum
addu'ar tashine Allah ya basu zaman lafiya mai
d'orewa..
An kai amarya Husna gidan mijinta sun sha kuka
rabuwa da gida, Mubeena kuwa dama tana gida
sai nan da kwana biyar (5) zasu lula k'asar
America shima Ya Abdul cikin ikon Allah kamfanin
dayake aiki suka tura shi wani course can America
hakan yazo daidai, abinsu dagwas!
Yau zasu tafi k'asar America kukan wajen
Mubeena kuwa kamar me, dan a daren rannar
kasa bacci tayi tana tunanin rabuwa da iyayen
nata, amma ba yadda ta iya, idanuwanta kuwa
duk sun kumbura saboda kuka..
Mr& Mrs Ameen, Abba, Umma, Ummi, Amir da
Ya Nana sune suka musu rakiya zuwa airport,, da
kyar aka banbareta daga jikin Umma, Umma na
kuka itama tanayi haka suka rabu, Ya Abdul ya
kama hannunta suka shige jirgi abinsu, nikuwa ina
binsu a baya har muka shiga jirgi, jirgi ya lula
damu sai k'asar America.....
[12:39AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
©MISS HAFCY
®NWA
[150]-[155]
Bayan sun sauka ne motar kamfanin su Ya Abdul
tazo ta d'auke su ta kaisu masaukinsu, inda zasu
zauna , gida ne d'an k'arami falo sai d'akuna gida
biyu d'aya babba d'aya k'arami sai kuma tiolet da
kitchen da dinning,,,Mubeena ce ta kai kayan
d'akin
dan gida baya bukatar gyra saboda ko ina tsaf
dashi. Yayin da shi kuma Ya Abdul ya fita nearby
restaurant dan yayo musu take'away ya dawo , a
lokacin har ta fito daga wanka ma tana kan kafet
tana sallah , gannin haka yasa ya aje abincin akan
dinning shima ya shiga band'akin d'ayan dakin
dan
yin wanka da sallah.
Ya d'an jima sannan ya fito sanyen da wando 3
quater iya gwiwa da riga armless, ya tadda ta
tana
kan kujera tana dana laptop din dake kan centre
table,, ya zauna kusa da ita, ta juyo tace "sannu
da
fitowa Yaya" yayi d'an murmushi "yauwa
Mubeena
ya gajiyarmu?" Tayi murmushi "aiy ta tafi" yace "i
see, me kike yi a system ne? Naga alama dai baki
gaji ba" Tayi murmushi "A'ah Yaya kawai dai naga
ba abinda zanyi ne shine nake duba school din da
yanayinta, ashe ma next week ne za'a fara
registration" yace "Gud Allah ya kaimu" tayi
murmushi "Amin".
Ya dauko musu abincin suka ci, sannan Mubeena
ta
shige d'aki dan shirya kayanta a wadirop
(wardrob
e) ta barshi nan yana kallo a Talabijin(TV).
Da daddare ma fita yayi yaje ya siyo su pizza,
shawarma, da roasted chicken, sannan da su ice
cream, lemuka da yagut(yaghurt) ya shiga d'akin
nata.
Tana zaune akan dressing mirrow, tana taje
yalwatacen gashinta, rigar bacci ce a jikinta iya
gwiwa pink, tana da d'an kauri ba sharara ba, ya
tsaya kawai yana kallonta, ita bata san ma yanayi
ba, sai data duba mirrow din da kyau ta ganshi
tsaye kunya ta kama ta sosaii tayi saurin d'auko
hijab d'inta dake kan gado tasa, dariya abin ya
bashi ma, yayi murmushinsa me ban shawa'a
sannan
a zauna kan carpet din d'akin had'e da aje ledojin
hannunsa.
Cikin sanyin murya yace "Mubeena" da sauri tace
na'am, yace "sakko muci" ta k'araso

Please Login or Register in order to submit comment