You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
COPY N COMPILED BY
ESHAAT SMILER HOM OF
HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176 FOR MORE
AISHATUL MUBEENA 1-20
[12:12AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
[1]-[5]
Na Miss hafcy
©ONLINE HAUSA WRITTERS
A fusace ya shigo gidan yana mita "Haba!!
Mutum dame zeji? Da zafin talaucin dake damuna
ko kuwa da Rashin haihuwa,,Nagaji da wannan
rayuwar! "" Da sauri ta fito daga daki" Haba
malam ai talauci ba hauka bane kuma haihuwa aiy
ta Allah ce,,ka shigo gida bako salama kana
fadan wannan maganganun ai komai yayi zafi
maganinsa Allah"" Ya dago a fusace ya kalleta
"ma'u kinga kimin shiru ki barni naji da abinda
nake ji ace yau duk wahalar dana sha a kasuwa
amma ba wani cinkin kirki dame zanji haba!
Haba!!"" Ma'u tace "Amma ai be kamata wannn
maganar ta dinga fitowa daga bakin kaba,,Kasani
fa Allah yana cewa,, Acikin suratul baqarah Aya
ta 153 "" innalla ha ma^as -
sa biri n .""Ma'ana: Allah yana tareda masu
haquri"",, Ya juyo ya kalleta toh sarkin wa'azi,,
naji shikenan yanzu da abinda zan samu naci??
Tayi murmushi,,Dazu na sami 200 wankin
danayiwa talatu shine na yi mana danwake har
tumatir ma na bada aka siyo min"" Ya washe baki
yauwa mata ta gari nagode an gaishe ki,,Suka
shiga cikin dakin
Bayan ta zuba mai danwaken a plate ya fara ci se
santi yake yi can ya kalleta yace "Duk sanda nake
cikin matsala in na tuna muna tare zan dawo na
ganki se naji wani dadi a raina,,saboda nasan
dole zaki faranta min rai" Tayi murmushi sannan
tace "malam kenan nima ai duk hakan take" Yace
"madalah ni yanzu matsala dayace take damuna
wanan rashin haihuwar dan na tabbata daga
gareni take mata nawa na aura bayanki amma har
yanzu ba wada ta taba ko bari"" Ta nisa "Malam
ba lallai bane hakan ne kawai dai mucigaba da
addua,,,Se kaga cikin yardar Allah mun samu"
Yayi murmushi yace toh mata ta gari na gode
Allah ya amsa adduar mu tace "Amin malam"
Bako sallama ta banko dakin,,ma'u da sauri ta
tashi tana "Ahh iya ce? Sannu da zuwa,, iya ta
balla mata harara "Dallah yimin shiru se shegen
kinibibin tsiya ba wajen ki nazo ba wajen dana
nazo" Ma'u ta sunkuyar da kai bata qara magana
ba....Iya ta kalli Mal,, "Kai kuma mara zuciya
kawai kaqi rabuwa da wannan matar me baqar
kafa ta tsiya na gaji ace har yau banda jika,,nasa
ka auri mata bata ko shekara ka saketa,, se
wannan mayar matar taka,Naga alama so kake na
mutu van sami jika ba "" Ta fashe da kuka,,Mal ya
kalleta "Haba inna,,Ya kikeso nayi? Da sauri ta
katse shi KA SAKI MATAR KA MAU SAKI 3! A
firgice ya juyo ya kalleta "Haba iya,,ki tuna fa a
duk matan da nake aura ita ce kadai me rupa min
asiri take zaune dani a wannan quncin,Ga rashin
haihuwa amma kuma kice na saketa haba iya!,,
Iya ta juyo da mamaki "Auho lallai sule ka girma
ka isa har ina ma magana kana maida min,,ta
fashe da kuka ace dan dana haifa shi muke
musayar yawu dashi na shiga uku ni tani!""Ya nisa
sannan yace "iya ba haka bane ba wlhy abinda
kika bukata ne bazab iya ba,"" Iya ta fusata "to
kaje wlhy matar nan ta qara wata3 bata sami ciki
ba se an raba auren nan,,,Tunda ban isa nasaka
abu ka yi ba,,"" Ta fice cike da fushi Ma'u datake
ta kuka ta juyo ta kalleshi "Bansan me nayiwa iya
ta tsane ni haka ba,,Har yau ta kasa gane cewa
haihuwa ta Allah ce"" Mal ya juyo ya kalleta "Kiyi
haquri ma'u na Insha Allah matsalarmu ta kusa
zuwa qarshe! Ma'u ta share hawayenta "Allah
yasa ameen" Ta dauke kwanukan dake dakin ta
fita dan wankesu shikuwa kishingida yayi akan yar
katifar dakin ina jinjina maganar iya
Share
Recent Posts
[12:13AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
©ONLINE HAUSA WRITERS
NA MSS HAFCY
[6]-[10]
***ASALINSU****
Malam Sulaiman Abubakar me rariya Dan kasuwa
ne sana'arsa bata huce Ta saida rariya ba, yana
yin rariya ya kuma siyar a kasuwa sana'ar kuwa a
wajen babansa ya gada,Alhaji abubakar me rariya
marigayi,,,,
Alhaji Abubakar me rariya yanada mata biyu da
yaya guda 4 guda daya ta rasu,, Balki itace
matarsa ta farko wadda ta haifa masa yaya
biyu,,,Bashir da hauwa,Wanda dukansu sunyi aure
cikin rupin asiri, Se kuma matarsa ta biyu Amina
(Tani) Masifafiyar mata ce ta gaske ga rashin
haquri Ta haifa masa yaya biyu Mal sule shine na
farko se kuma habiba wadda ta rasu tun tana
qarama,,,,,,,,,
Mal Sule matarsa daya wanda suke zaune a halin
yanzu, asmau ma'u wacce sukayi auren soyayya
amma shiru kusan shekara 10 kenan suna tare
Amma ko batan wata bata taba yi ba,,,Hakan
yasa tani wadda suke cewa Iya ta takura masa
akan se ya qara aure,, mata aqala sunkai 5 ta
kawo masa in ya auri wanan ta fita se ta kuma
samo wata yan mata da zawarori amma kuma
sam basa zama Kuma a cikinsu ba wadda ta taba
ko batan wata balle bari,,In suka gaji se su
tafii,Ga talauci ga rashin haihuwa da kansu su
suke neman saki, Wasu kuma in ya gaji da
halayarsu se ya sake su Iya tayi masifar ta
gaji,,,Tayi neman malaman akan nemawa tilon
danta sule haihuwa amma har yanzu shiru
Ma'u matace me haqurin gaske da tawakali
tanada ilimin addini sosaii hakan yasa rashin
haihuwar sam be dame ta ba Duk da talauci irin
na mal sule amma Haka take haquri ta zauna
dashi wataran ma da en dabarunta take ciyar
dasu,Dan itama gidansu ba wasu masu arziki
bane,Ga miji shima ba wani me arziki ba dan da
sana'ar rariya kawai ya dogara ko noma ba yayi
saida gonar gadonsa yayi,,Suna zaune yau da ci
gobe babu.
********CIGABAN LABARI******** Ma'u da
gudu ta fito daga daki tana kwarara amai a
rariyar tsakar gida,,daidai shigowar iya kenan,,iya
da sauri ta isa wajen ta "yar nan meya faru haka
me kika ci" Ma'u Tana huci tace " Wlhy tun da
safe nake jina wani iri ga zazzabi dazu kuma
zuciyata ta fara tashi shine fa na fara jin amai
har nazo nayi" Iya ta dago kanta" Yaushe rabon
da kiga aladar ki? Ma'u tace "Watan daya huce
dai bangani ba""
Iya ta duba idonta sosai aikuwa se ta saketa ta
rangada guda ""Ayiriyiri" Yarinya ki godewa Allah
ai alama ta tabbatar da cewa ciki gareki kai yau
ni nafi kowa murna ayiriririiriiiii"" Ma'u ta zaro
ido maganar iya se tazo mata kamar a mafarki ta
dago cikin dashashiyar murya tace "Iya ciki fa
kika ce?" Iya ta washe baki "Tabbas yar nan kiyi
murna fa"
Daidai lokacin mal sule ya shigo gidn dauke da
rariya a hannunsa ya tsaya turus ganin iya tasa
ma'u a gaba tana rangada guda ya matso yace
"Iya me ya faru ne" Iya ta kuma washe baki "Yaro
albishirin ka?"Da sauri yace goro iya" Iya tace "to
matarka ciki gareta alama ta nuna!"
Mal sule ya yarda rariyar dake hannusa se ganni
Inna tai ya daga hannu sama yana godiya se
kuma hawaye,,Ma'u da take tsugune kuka ta fara
a hankali kukan murna! Yau dai Allah ya amshi
addu'arsu! Mal sule a fili yace "Allah nagode
maka,ya allah daka amshi addu'a ta, Ya Allah
kasa dan dake cikin matata ya zamo namiji! Allah
yasa namiji zata haifaa na samu magaji ameen!!
Ma"u da sauri ta share hawayenta ta kalleshi
"Haba malam Ai ba'a yiwa Allah haka kai dai
kawai kayi fatan allah ya bamu nagari, inma
namiji ne inma mace !"
Ya juyo ya kalleta "A'a fa Ma'u ki banni na roqi
Allah ya ban namiji dan ni banida wani buri daya
huce na haifi da na miji ba mace ba!" Iya se a
lokacin tace " fadi ka kara dana,me za'ayi da wata
mace? Ina laifin da na biyu ta haifo mace amma
wannan cikin Inshaa Allahu namiji ne ehe!"
Ma'u ta tashi ta girgiza kai alamar kalaman basu
mata dadi ba ta shige daki cike da farin ciki A
zuciyarta kuma mamakin furucin su Mal
take,tabar Mal da iya a tsakar gida suna ta Farin
ciki da anashuwar abinda ya faru! Iya tace "ka
dinga kula da ita bari naje na sanarwa da en uwa
da abokan arziqi wannan abin alherin,Ai banga ta
zama ba" Ta fice tana guda shima kuwa cewa
yayi "nima banga ta zama ba kuwa nima bari naje
na siyo mata kayan makulashe!
Share
Recent Posts
WA GARI YA WAYA? 2
WA GARI YA WAYA? 1
WA GARI YA WAYA?? 3
Comments
No comments yet. Why not make the first
one!
New Comment
[]
Name:
Comment:
(Some BBCode tags are allowed)
Post Comment
options
Home
Guestbook
About Me
Feedback
Blogroll
Feed: RSS / Atom
Comment Feed: RSS / Atom
Get a
October 2016
October
13
Thursday
11:12 PM
Go to top
Visitor Counter : total-0060690
© 2016 Hafsat's Mobile Blog .
fmb_Powered by
Copyright 2016 mrs hafcy design by
muhammad abba gana (09039016969)
[12:14AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS
[15]-[20]
Ma'u tana zaune tana cin tuwo mirar kuka da
yajin dadawar da mamanta ta aiko mata, gefe
guda kuma farfesu ne Goggo(k'anwar
babansu,wadda tazo mata zaman wanka) ta kawo
mata,suna zaune ita da goggon suna hira,Babyn
na hannun goggo,, Salamar Mal sukaji,ya shigo
fuska ba yabo ba falasa suka gaisa da goggo tace
"Ahh angon k'arni ne ke tafe ashe" be amsa mata
ba,tamai barka, ciki-ciki ya amsa sannan ta basu
waje
Ma'u da murmushi ta juyo ta kalleshi "Mal
kenan,inata cigiyarka kazo kaga kyauta da Allah
ya bamu,Yau dai Allah ya amshi addu'ar mu,se
mu gode masa"a fusace ya kalleta "ke dallah
sauraramin! Kin tashi kin haifo wata mace,
zakimin dadin baki,bari kiji zuwan nan danayi abu
biyu ne ya kawo ni, ki saurara da kyau kiji""
Ma'u tace "Ikon Allah mal meya yayi zafi haka?
kuma ai bani ce ke bada haihuwa ba,Allah ne ke
bayarwa" Ya katse ta"Abu na farko shine: kinga
wannan(ya fito da dari biyar 5) ita kadai zan bada
ayi hidimar suna da sauran abubuwa,Kaya kuwa
kinsan na gama siya dan haka kyasan yadda
kikayi,,Ragon dana siya ma,zuwa zanyi a cazamin
aban tunkiya dan banga amfanin yankawa mace
rago ba! Abu na biyu, nazo muyi salama domin
tafiya zanyi bayan suna na dawo,Dafatan kin
gane?, Ma'u bata san sanda ta fashe da kuka ba,,
"Mal yanzu abinda kayi ya dace mal? Kayi mana
aladalci nida yarka? ,, Ya katse ta "kinga ni bance
kimin surutun banza ba,in kina da magana ki fada
da sauri, dan tafiya zanyi gidan iya yanzu,,Ma'u
ta cigaba da kuka bata bashi amsa ba
Yana k'ok'arin fita ne cikin dashashiyar murya
tace " Mal dan Allah ina neman alfarma a
wajenka" ba tare da ya juyo ba yace "tame?" Ta
cigaba"Inaso kayi ma yarinyar nan huduba kamar
yadda Kowanne uba ya kamata yayiwa Dansa ko
yarsa,Sannan kuma inaso ka dauketa ta ji dimin
jinkin ka koda na minti 5 ne,,Ta fashe da kuka
Ya danyi jim sannan ya gyada kai,ya koma ya
zauna,Ya turbune fuska, ta dauko babyn, ta mik'a
masa ya karba yana gun-guni,, "Ai se ki fadi
sunan da zan samata," Ma'u ta juyo tace "Da
nazata ai kaine zaka zaba" a fusace yace "ke
bansan bata lokaci" cikin sanyin murya tace
"AISHATUL MUBEENA"" Tsaki yayi ,toh shikenan,,
Ya mata hudubar,ta dan dade a hannunsa sannan
ya mik'a wa ma'u ta karba tana murmushin
yak'e,tace "nagode mal Allah ya kiyaye hanya"
yace ameen, yasa kai ya fita" Ma'u ta k'urawa
AISHATUL MUBEENA ido kawai se jin sabon
hawaye tayi na zuba,Tausayin Yarinyar duk ya
cika mata zuciya,,,Goggo ta shigo ta tadda ta
tana kuka,da sauri ta iso wajenta"Ma'u meya faru
kike kuka?" Ma'u ta share hawayenta "bakomai
goggo" Goggo tace "ban yadda ba,ki fada min
abinda ke damunki,ko wani wajen ke miki ciwo?"
ma'u tace "A'ah goggo kaina ne ke ciwo" goggo
tace "kuma shine kike kuka,bari na dauko miki
magani" ta tashi dan dauko mata maganin
Iya tashigo kamar yadda tasaba yau ma ba
sallama" ke ma'u dama nazo fada miki sak'o ne,
mijinki yaban kudin,Shinkapa da kayan miya na
taron suna,Dan haka bazan baki kudin ba kuje ke
da daginki ku kashe a banza,dan haka ana gobe
suna kome ake buk'ata se kiyi magana,,""Ma'u ta
girgiza kai"A'ah iya ki barshi kawai,Ni bazanyi
taron suna bama,Na hak'ura kawai Allah ya
rayata,Tunda bezo a al'k'urani ba dole se anyi
taron suna ba" Iya ta zaro ido ta dafe k'irji "Lallai
yar nan kin rik'a wato ni kike fadawa magana a
fakaice koh?" Se a lokacin goggo tasa baki " A'a
a'a Tani karki soma,Yarinyar nan a kalamata ba
wanda yayi kama dana zagi ko kuma na bak'ar
magana, iya tace kwaji dashi dai dangin tsiya ta
fita tana masifa",Ma'u ta fashe da kuka "oh ni
asma'u ya zanyi? Da bak'in cikin mijina ko dana
uwarsa?
® OHW
AISHATUL MUBEENA 20-30
[12:15AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS
[20]-[25]
Goggo da sauri ta katse ta"karki soma fadan
wadanan maganganun Ma'u kinji,Kiyi hak'uri
komai lokaci ne" Ma'u tace toh goggo insha Allah
bazan kuma damuwa ba,Zanta addu'a Allah ya
ganar da mal gaskia,,Goggo tace yauwa yar
albarka..
Yan uwa da abokan arzik'i sunata zuwa
barka,Yarinya tana ta samun kaya masu
kyau,,rannar suna kuwa duk da Ma'u tace bazata
yi taron suna ba mutane anzo dayawa...wata
mak'ociyarta wadda suke mutunci sosai khadija
shinkafa dafa duka ta yimata me dadi da
zobo,dayake mijinta nada hali,Ma'u tayi farin ciki
sosai da abinda khadija ta mata tayi ta
godiya,,,dangi aka zo anata kwashar girki ana
santi,hada su Iya,don ita har diba tayi ta kai gida
kowa yaji sunan yarinyar AISHATUL MUBEENA Se
ya yaba sunan ,,,Liman ne ya yanka tunkiyar
suna, Iya kuwa ta tsaya tsayin daka akan naman
k'iri-k'iri ta hana dangin Ma'u da sauran mutane
taba naman,Daga ita se yan'uwanta ne suka
sarafa naman,Wai kada su Ma'u su handame, ita
ma'u ma ko a jikinta...yarinya ta samu kaya kuwa
masha Allah daga ita har Ma'u itama tana samu
kudi da atamfofi,tayi mamaki sosai dan bata taba
zata zata samu abin alherin data samu ba
Bayan suna mal ya dawo,Ba yabo ba
falasa,Amma kuma sam yaqi yadda ya dauki
yarinyar koda wasa,Tun Ma'u tana damuwa har ta
dena,Ta cigaba da kula da yarta da ita kanta
bayan tayi arba'in ta zagaya dangi yawon arbain
shima da kyar ya barta,,Iya kuwa kullum cikin
tsangwamar AISHATUL MUBEENA take,Har yanzu
kuwa bata dauke ta ba,se dai ta kalleta daga nesa
BAYAN SHEKARA BIYU
Mal naezaune a kofar gida suna tadi shida wani
abokinsa sanda,Wasu mata suka nufo gidan su
3,A tare suka gaida Mal ya amsa yana washe baki
daya daga cikinsu tace" Mune masu yak'i akan
cutar poliomyelitis wato cutar polio,Mun samu
labarin kana da ya shine zamuyi mata
rigakafi,"Mal ya kalleta "ke ni banda yaro a
gidana ku fice min daga nan shashasahai kawai"
Dayar tace "kaga malam dan munzo mu taimake
ka kaida iyalinka,baka isa ka zage mu ba,ko
dayake naga alama kai jahili ne!" Ya juyo ya
kalleta" ke wallahi se na kwada miki mari,wa kike
cewa jahili?" Tsaki tayi "kai mana" Taja sauran
suka yi tafiyarsu ...yayin da suka bar mal da
sanda suna ta balbalin masifa Ma'u duk taji
abinda ya faru,AISHATUL MUBEENA tana tsakar
gida abinta tana wasa, Ma'u kuma tana wanki a
tsakar gida, mamakin halin Mal kawai take...
Ya shigo yana balbalin masifa ko salama beyi ba,
ta kalle shi "Mal wannan yar muce fa, tana da
hakki akan mu,Ka tuna fa tunda muka haifi yar
nan bamu taba kaita asibiti ba,ko cuta tai se dai
inyi yan dubaru na,nice zuwa neman maganin
gargajiya,Amma kai ko da wasa baka taba nuna
damuwar ka ba,,,Sun biyo mu har gida don su
mata rigakafin wannan muguwar cutar, sannin
kan kane wannan cuta nakasar da yayan mutane
take,akan me bazamu basu damaba? Basu nemi
ko biyar daga gare mu ba fa,Mal nagaji da wanna
halin naka nagaji!!! " ta fashe da kuka... Ya galla
mata harar sannan yayi tsaki " Ma'u ki shiga
taitayin ki fa,Ya isheki abinda kike yi,rigakafin ne
nace baza'ayi ba!,Ai yata ce nina haife ta kuma
na isa da ita har dake!
Sh
[12:18AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS
[25]-[30]
Ma'u da sauri tadago kai ta kalleshi "au yarka?, se
yau kasan cewa yarkace,Kai yanzu baka ji kunyar
fada bama? Wallahi mal in baka canza halin ka ba
Allah se ya tambayeka,Allah wadaran wannan
mumunan halin naka!" Mal a fusace ya dago ya
wankawa mata mari ji kake Tas!! Aishatul
mubeena se data tsorata ta fara rusa kuka itama,
Mal ya kalli ma'u ya cigaba"Naga alama kin fara
raina ni a gidan nan,Wato yanzu har ina fada kina
fada zan fara maganinki ne mara kunya kawai
wadda batada tarbiya"" Ya sa kai ya fita daga
cikin gidan a fusace......Ma'u ta share hawayenta
tace "Allah ga baiwar ka,Allah ka raya wanna
yarinyar ya Allah"" ta dauki aishatul mubeena ta
fara rarrashinta tana hawaye ahaka har aishatul
mubeena tayi bacci
To rayuwa dai haka ta cigaba yau da dadi gobe
babu dadi,Ma'u kullum cikin hak'uri take da
mijinta da kuma uwar mijinta wanda suka zamo
mata matsala a rayuwarta
Yanzu dai shekarun AISHATUL MUBEENA 3 ta
taso yarinya kyakyawa san kowa k'in wanda ya
rasa,ga farin jini masha Allah,yara har fada ake
akan daukanta saboda kullum tsaf da ita,Har ta
fara magana sosai,abin mamaki kuwa itama
tsoron babanta ma take dan tun tana k'arama
tasaba tana zuwa wajenshi ze hantare ta hakan
yasa ko kusa da shi bata san zuwa..
Yau AISHATUL MUBEENA ta tashi da zazzabi me
zafin gaske ga ciwon kai se kuka takeyi,dagabaya
kuma tace kafarta na mata ciwo ta kasa tafiya
sam kafar ta rik'e ,,Ma'u ta rikice sosai ta rasa
yadda zatayu ga yarinya tana ta rusar kuka, Data
ga abin yayi yawa gashi tasan mal ko me zatai
mai baze kulata ba se ta saba ta a baya ta shiga
gidan khadija bayan sun gaisa ta mata
bayyani,Khadija itama duk ta rude,Can tace
"Inaga gwara mukai ta asibiti,Dan shine kadai
mafita" ma'u tace "Toh shikenan ba matsala"
khadija tasa aka hayo musu mota dan kai su
asibitin garin dayake akwai wanta yana aiki a
asibitin,,,Basu dade ba se ga mota ...nan nan da
nan taja sukai asibitin
Emergency aka shiga da ita aka shiga bata kulawa
ta gaugawa,,Ma'u se kuka takeayi dan ita ganni
take kamar mutuwa zatayi,,Khadija ce ke
rarrashinta
Bayan dan lokaci likita ya fito yana share
gumi,Ma'u tana kuka tace "likita ya take? Ya jikin
nata?" Likita ya ce a gskiya yanzu bamu gano
komai ba,amma dai yanzu zamuyi mata test na
aika lab,Se kujira kan result din ya fito" Ma'u tana
kuka tace "toh likita Allah yasa muga alheri,,"
Yace ameen ya fice,Ma'u kukan nata ya k'aru
sosaii; khadija itama se ta fara kuka dan suna
bata tausayi sosaii, Tace "kiyi hak'uri maman
mubeena komai yayi zafi maganinsa Allah,Inshaa
Allah zata tashi cuta ba mutuwa bace !" Ma'u ta
share hawayenta sannan tace "Toh khadija Allah
yasa amma se nake ganni kamar bazata tashi ba!"
Khadija tce"A'ah insha Allah zata tashi,Bari naje
can gida sena na sanar dasu iya su san abinda
ake ciki"
Tana isa kai tsaye gidan iya ta shiga bayan sun
gaisa ta sanar da iya,Abun mamaki iya se ta nuna
damuwarta ba laifi ta sakko hijabi tace suje
asibitin,sannan tabar sako da a nemo mal sule a
fada mai halin da'ake ciki A kuma fada mai ya
samesu a asibiti!
Har suko isa ma'u kuka take se rarrashinta suke
yi, a dan lokaci nan duk ta fita hayyacinta
idanunwanta duk sun k'ank'ance saboda kukan
datakeyi,
Suna zaune se ga likita ya fito a razane ya kallesu
yace............................
Share
AISHATUL MUBEENA 30-40
[12:19AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: ◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS
[30]-[35]
Likitan ya kallesu yace "ku biyoni office!" Ma'u ko
takalmi bata sa ba ta bishi da sauri suma su
khadija suka biyota
Bayan sun zaune likita yaja numfashi sannan yace
"ki nutsu ki fada min al'momin da ta fara kan
ciwon yayi tsanani, Ma'u ta share hawayenta
sannan tace "Ta fara da ciwon kai da dadewa
amma jefi jefi in na bata magani takanji
dadi,sannan takance kafarta na ciwo,to shine yau
tun safe abin yayi yawa tana ta kuka,Ga zazzabi
ga ciwon kafa" Likita ya share guminsa yana
jinjina kai
Likita ya maida numfashi sannan yace "Ana wa
yarinyar rigakafin Cutar poliomyelitis (polio)
kuwa?" (Gaban ma'u ya fadi)"A'ah ba'a taba yi
mata ba" Likitan a fusace yace ' u see,kun ganni
(ya daga murya) Duk k'ok'arin da gwamnati
takeyi akan yak'i da cutar polio tana turo mutane
su bi gida-gida dan yin rigakafin cutar,Kuna
ina????Meyasa baku basu damu su mata ba,Dan
nasan tabbas suna zuwa amma kuk'i basu
dama,,,meyasa???!!!"" Ma'u ta fashe da kuka
"Wlhy likita BA LAIFI NA BANE laifin babanta ne
ba yadda ban yi dashi ba amma sam yak'i,," likita
yace "Toh shikenan yanzu kun janyowa yarku,A
iya gwajjin da mukayi.....Am sorry to say,,
kwayar cutar polio ya riga ya gama bin
jikinta,kuma kafarta ya taba "A YANZU HAKA
YARKU TA RASA KAFARTA TA HAGU,ZEYI WUYA
TA SAKE TAKAWA DA KAFAR !!DOMIN KWAYAR
CUTA TA FI K'ARFI A KAFARTA!!!
Innalahi waina ilaihi raju'n Khadija ta shiga
maimaitawa iya kuwa kasa magana tayi,,Ma'u
kuwa sulalewa k'asa tayi sumamiya!! Da sauri
sukayo kanta nurses suka zo da gado aka dora ta
Likitoci sun dade akanta,,Anci sa'a kuwa mal yazo
shima yadan damu ba laifi ,Se wani kumbure-
kumbure yake Likita ya fito yace," ku biyoni
office",a gigice suka bishi ya kallesu cike da fushi
yace "wai ku dan Allah meyake damun kune,?
Matar nan tana da hawan jini amma baku taba
kawo ta asibiti an gwada taba,Yanzu jinin ta ya
hau over,,Allah ne yayi kiyaye da wlhy zata iya
samun mutuwar barin jiki stroke! Suka zaro ido
gaba daya banda mal,khadija tace "likita wallahi
bamu sani ba,bata taba fada mana ba "likita ya
nuna mal" kaine mijinta,, Ya galla masa harar
sannan yace "Eh nine ya akai yi ne?" Likita a
fusace yace "Amma wlhy baka da tausayi
sam,wacca irin zuciya ce dakai?? Ka yi sanadin
nakasa yarka sannnaan kana nema ka nakasa
matarka ko ka hallaka ta har lahira,Kai wani irin
mutum ne?
Mal ya kalleshi kallo na rainin hankali sannan yace
"Kaine bakada hankali,Ni nasan abinda
nakeyi,kuma ba ruwanka da harkar
gidana,mutumin banza kawai'' likita yayi
murmushi "Ni bazan tsaya cacar baki da kai ba
saboda ni bana cacar baki da jahilai irinku!
[12:19AM, 14/10/2016] Miss_Hafcy: [1:33PM, 12/02/2016] Miss Hafcy:
◆◆◆AISHATUL MUBEENA◆◆◆
NA MSS HAFCY
®ONLINE HAUSA WRITERS
[35]-[40]
Mal yana nema ya cakumi wuyan rigar likita da
sauri iya ta tare shi" Wlhy ka sake kayi fada dashi
sena maka baki mara hankali kawai' Ya kalleta
yayi tsaki sannan ya fice daga asibitin,likita
girgiza kai yayoi cike da takaici ya cigaba da yi
musu bayani
An sanar da yan gidansu ma'u mamanta da
goggo ne sukazo se kuka sukeyi da kyar aka
lallasheshu,,,Ma'u kuwa bata dan fara dawowa
daidai ba se datayi kwana2 a kwance Aishatul
mubeena kuwa tana can an ware mata gadon ta
daban likitoci ne kawai ke zuwa dubata
Ma'u ta dan murmure,Tana shan magugunata
sosai sannan likita ya mata nisiha sosai aka ta
kwantar da hankalin ta,Addu'a ce ya kamata ta
dinga yi,,Yawan damuwar datakeyi ne yasa ta
hawan jini!
Bayan ta dan warware hankalinta na kan
yarta,,Hakan yasa tace suce wajen likita ya musu
bayani,,bayan sun shiga,Ma'u cikin sanyi murya
tace "Likita yanzu ba wani magani Da za'ayi mata
ta sami sauk'i kafarta ta dawo daidai tunda naji
kace kafarta Ta riga ta shanye"
Likita ya nisa sannan yace "Malama ma'u kiyi
hak'uri,Hanya daya da za'a iya maganin cutar
shine....... RIGAKAFI! wanda ku kuma bakuyi wa
yarku ba! Amma cutar polio in har ta riga ta
kama mutum BATA DA MAGANI!!,Amma yanzu
muna bata painkillers wanda zasu maganin
wannan ciwon kai da zazzabi,da kuma ciwon
kafar,,Kuma Alhamdulilah yanzu ta fara samun
sauk'i,,,,Sannan batun kafarta na fada muku cewa
bazata iya tafiya ba due to weakness na
kafar,Yanzu zamu bata WHEEL CHAIR in ta k'ara
girma kuma se ta fara amfami da FOREARM
CRUTCH,lokacin kafarta ta dama ta k'ara
kwari,Dan kunsan itace me lafiyar kuma yarinya
ce,Kafar ba wani kwarin kirki tayi ba" Ma'u ta
fashe da kuka yayin da mamanta,iya,Goggo,Da
khadija suka Jin jina kai cike da tausauyi,,(Dan
yanzu iya ta saduda ta gane laifinta,Har kuka tayi
da tana bawa ma'u hakurin abinda tamata a
baya)
,Likita ya cigaba "Ba kuka zakiyi addu'a zaki ki
kuma godewa Allah dayasa nata yazo da
sauk'i,Dan akwai wanda take ja musu
paralys,Amma ita ai kafarta ta hagu kawai ta
taba kuma zata iya komai dinta nrml,Nan da sati1
zakiga ta dawo daidai se dai kawai kafarta ta
hagu da ta tabu ne!" Ma'u da murya kuka tace
"shikenan likita,Allah ya raya ta,ya kuma sa
k'arshen wahala kenan! Gaba ki daya sukace
ameen,,
Mama(maman ma'u tace) " Ma'u kiyi hak'uri ki
fawala Allah komai,Yana tare dake kinji kiyi
hak'uri duk da nasan kinayi ki dora akan wanda
kike yi"Ma'u ta rungume

Please Login or Register in order to submit comment