You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah ka fitar dani daga gunnan wayyo iya Abuta kizo Karna mutu kinji
Tausayi matuka ta bashi don dik Wanda yake gidannan yasan da sabon sauyin da
Yazo yanda ake azabtar da marainiyar Allah
Rukota yai da muryar rarrashi yace baby bude idonki Kiga wlh na cireki daga dakin birin .ba aciki kikeba kinji

Ahankali take bude idon .ganinta karkashin bishiya yasata sauke numfashi daga bisani ta saki wani kuka me ban tausayi .
Rarrashinta yashigayi yana fadin ba komai baby kiyi hakuri kinji rayuwa ce wata rana sai labari
A iya shekarunki da uwarki tana Raye biki wuce kiyi rigima ta goyaki ba amma sai gashi dalilin maraici karfi da yaji kinzama mamallkiyar kanki
Yi shiru baby Allah yana gani kuma baya bacci hakika akwai abin dubawa a lamarin gidannan shedan yasamu wajan zama dirshan

Dikda ba fahimtar Yawancin abinda yake fada takeba. Amma tabbas tasan tausaya mata yake

Nan yazauna yanata yi mata hira har wajan karfe daya yaje yai sallah .sannan yace wa me gadin babban gate .dayaga motar da direba yafita da Bilal ta shigo gidan yamai flashing
Koda aka kawomai abincin sa na rana rabi yaci yabata rabi ya tsinko mata goba nunannu taci tai kat tasha ruwan fanfo abinda bata taba shaba tunda aka haifeta sai bayan lalacewar gidan
Haka ta kwanta a kasa tai baccinta ta koshi
Sai laasar ta farka

Zuwa lokacin inuwa yagama shirya dik dabararsa .

Wata waya yasamu ya lankwasar ta dakin birin yai hanya sosai inda mutum zai iya shiga ya fito . sannan yacewa baby idan yayanki ya dawo yaganki anan akwance zai tanbayeki wa yafito dake .saikice masa ta wannan kofar kika fito .karfa kice ni na fito dake inba hakaba zai maidake dakin .kinji ko sannan inya tanbayeki kinci abinci kice masa a a .kinji ?
Gyada kai kawai take .itadai
Wajan karfe biyar yashigo gidan ai kuwa motar nashigowa .me gadi yaiwa inuwa flashing. Da gudu ya shige dakinsa dake bakin kofar zoo din ya kwanta bayan ya sa baby itama kwanciya a karkashin bishiya

Baibi takanta ba yashige fart dinsu saida yai wanka yafito yaci abinci .sannan yashiga dakin momynsa

Bilal kun dawo
Eh mundawo momy

To ya hanya ya jikin baban sadiq din
Da sauki .gaskiya momy garinsu sadiq da nisa tun .muna hira harnai shiru
Ah haba kano da jigawa ba wani nisa Bilal kawai dai don baka saba doguwar tafiya by road bane .shiyasa

Kai momy ya yarinyar nan nifa harna manta na kulleta a Zoo.
Kai nima na manta jeka dubata shegiya Allah yasama ta mutu aciki kowa ya huta


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
24/9/2017
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


BABY KHAUSAR


NA

LAYUZA KABIR ADAM





*Nakune* *wannan*
*Mahaifana* *Allah* *yasaka* *muku* *da* *mafificin* *alkairi*
❀ *my* *lovely* *Dad* *kabir* *Adam*
*Allah* *yaja* *da* *rai*
❀ *my* *sweet* *mahmah*
*Juwairiyya* *yusuf*
( _horo_ _saiga_ _Malami_ ) *momyna*


2⃣4⃣



Yana zuwa dakin inuwa yafara lekawa .yaganshi kwance kan katifarsa .ya lulluba da zani sai makyarkyata. Yake
Ya inuwa ya akaine naganka kwance

Uban gidana ai tun tafiyarka zazzabi yarufeni nake kwance anan
OK sannu
To ina yarinyar dana ajiye an an

Kai aini nama manta da ita .Donni tunda ka tafi ban waiwayi wajanba ina fama da kaina

Ok bani kye din dakin birin .
To yamike jiki na bari ya mikomai .
Kamar me ciwon gaske

Da shigarshi gun yaganta kwance kasan bishiya tana ta bacci .gamai hankali yana kallonta yasan baccin kwanciyar hankali take .don taci ta koshi .batada wata damuwa a lokacin

Amma shi mamaki yake yanda yaganta a waje shida ya sata a dakin biri
Kafa yasa ya mangareta .da karfi

Aikuwa da sauri ta mike tana mutsika ido.

Ubanwa ya baki ikon fitowa daga dakin .monkey dinnan dana saki

Karkar jikinta yadau rawa
Wlh Yaya xan fada maka gaskiya

Kaga can wajan naga kofa wayan ta tattare .shine na fito taciki.

Sabida kin rainani ne yasaki fitowa ko

A a yaya wlh tsoro ne nakeji kayi hakuri
Dalla rufemin bakinki kamar na tsutsa .

Wuce muje banxa barauniyar abinci wlh nakara ajiye Abu kika je ko kusa dashi ne saina ballaki gida biyu
Kinji ko a a

Naji yaya wlh naji bazan karaba

Hannu yakai ya bige mata baki.

Danne bakin tayi da hannayenta .

Suna shiga parlour tashige dakinta da gudu.

Kai tsaye tai toilet. Don. Uban fitsarin dake cinta

Dik da kasancewar Baby Yarinya karama . tanada san sallah .

Abinda zai baka tausayi da rayuwarta . inka shiga dakinta. Ita kadaifa take kwana acikinsa it's takewa kanta tsarkin kashi tayiwa kanta wanka .
Wankanma ba da sabulu ba kawai ruwa take watsawa tunda wa ya kula da rayuwarta balle yasan bathroom dinta ba sabulun wanka

Rabon da kanta yaga ruwa da sunan an wankeshi tun randa iya Abu zata tafi .ta wanke matashi .don yawanci baa fiyemata kitsoba kasancewar .kanta me santsine don haka yanzu dikya . tattare ya cure gu daya

Abinka da yarinta .komai na dakinta inka shiga a hargitse yake . kamar ba wannan dakin da aka aka Tarawa dukiyaba lokacin da zasu dawo cikinsa ita da iya Abu ba
.uwa uba haka kowa zai haye sama ita kadai dakinta na kasa
Dikda kowa 2 bedroom gareshi agidan akwai a sama akwai a kasa

Dik irin tarin uban Kayan datake dashi bazaka siyeta naira dariba don kuwa ba sawa takeba . wardrobe dinta me hudu cike take da Kaya amma kasancewar tsayinta baya kaiwa ta dauko Kayan yasa .iya na steps din farko kawai ta zubo dash kan gado .intasa wannan saita canja .kuma dika Kayan guda biyar ta zubo dogayan rugu a uku Riga da wando biyu
Sune intaga me wanki yazo tadiba takaimai ya wanke mata .insu bushe.ta kwaso abinta
Amma kodewa agunsu baq magana


Yarinyar da bata wuce asata a gado ta kwanta jikin mamanta ba

Kai rashin uwa baiyiba wlh musamman inba Wanda zai dauki nauyi hidimominka


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸



BABY KHAUSAR


NA


LAYUZA KABIR ADAM


GODIYA NAKE MASOYA LITTAFIN BABY KHAUSAR DIK INAJIN SAKONNINKU .
ALLAH YABAR KAUNA



2⃣5⃣





Zuwa yanzu takai ko a school bata wani kokari don inma ana musu lesson. Bata wani maida hankali .

A tinani irin na yaro baya zurfi .iya abinda yazo kwakwalwarshi shiyake tunani kawai
Don haka baby tasa aranta kawai momy .da Dad da ya Bilal basa sonta .don haka itama bata .sonsu ta daina kulasu yanzu frnd dinta Aysha M shareef ce kadai take .sonta itama yanzu bata son kowa sai Aysha

Don haka yanzu taja jiki .ko nacin magana datakewa Bilal ta daina .inma suka hadu ko a gida ko a skl saitai kasa da kanta bata ko kallansa .wai ita a tunaninta .hakan zaisa ya gane bata sonshin.
Shikuwa intai hakanma dadi yakeji .yana ganin kara tsoronshi takeji.

Shikuwa Dad ma baya kasar gaba daya .tunda yai tafiya tsawon wata uku .yau bai dawoba .yanacan harkar kasuwancinsa

Yau wani teacher dinsu yashigo yana musu lesson. Kasancewar karancin shekarunsu yasa dole .sai da wasa zasu dauki abinda yakeson .koya musu .don haka
Dayashigo .saiya fara tafawa da yan maza .da yazo kan mata .Akwai wata hanan a ajin bata son karatu .
Don haka yashiga tafawa ma da matan yana tsokanarsu .yana zuwa kan hanan saiya harareta .ya kauda kansa .
Tanata mikomai hannu ya wuceta .saita sa kuka .tace sir.baka sona ka tafa da kowa ni bandani .baka sona
Matsowa kusa da ita yai yace hanan kinsan me yasa bana sonki?
Ta girgiza kai alamar a a .

Yace sabida bakya son karatu .wasa yamiki yawa .don haka indai .biki daina wasa lokacin lesson ba .kullum nazo saina harareki .na mirguda miki baki
Yafada yana mirguda bakinsa

Dik abinda yake baby na kallansa

Saida aka tashi .sunje gida .kawai tazo fita a mota shima Bilal ya bude gaba zai fito .ta bugamai harara da murguda baki waifa ita yagane bata sonshi yanzu

Ai kuwa caraf akan idonsa

Wata wawiyar danka yakaimata ya makata da jikin motar yana fadin ni zaki harara don uwarki shegiya yar gidan hadiza me aiki .shegiya dangin .Fulani yan gudun hijira .ya karashe yana kaimata naushi abaki

Ya daga kafa zai boll da ita yaji an janyeshi gefe

Da zafin nama ya juyo yaga cikin maaikatan waye da wannan danyan aikin

Ai kuwa idonsa caraf akan Mlm khalili .
Cak yatsaya yana kallonsa don da farko ma bai ganeshiba
Saida ga baya tunaninshi yakai .ai Mlm Khalil ne

Ba yabo ba fallasa ya gaisheshi .ya juya zuwa hanyar ckn gida

Shikuwa Mlm cikin tausayi ya daga khausar yana rarrashinta

Yanzu yakara tabbatar da labarin da masu gadi suka gama bashi na sauyawar gidan .da halin ko inkula da Dad yakeyi ga Baby.

Jijjiga kai yashigayi .yana wani tunani aransa .
Haba shi dama tuntuni ya fuskanci da matsala sosai
Na yanda shima Alh. ya watsardashi tsawon wannan lokaci tun kafin yatafi garunsu gashi har saida yai shekara guda cif ya dawo

Don haka yatako yazo gidan yaga ko Alh lfy
Amma daga zuwanshi

Maaikatan gidan maza suka shiga bashi labarin .yanda rayuwar baby ta koma a gidan



🌸🌸🌸 Takuce Layuza kabir Adam πŸ™‹
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


BABY KHAUSAR

NA

LAYUZA KABIR ADAM



Da _sunan_ _Allah_ me _Rahma_ _me_ jinkai _yabo_ da _godiya_ sun _tabbata_ ga _sarki_ _Allah_ . _tsira_ da _aminci_ su _Kara_ _tabbata_ ga _manzon_ _tsira_ _Muhammad_ _Rasulillahi_ .



DEDICATED DIS PAGE TO U MY LOVELY GRAN FATHER
ALH.ADAMU JAOJI
ALLAH YAJA DA RAI YAKARA LFY πŸ™






2⃣6⃣





Yana shiga gidansa da azama ya daura Alwala .yashige dakinsa .ya Dade yana jero salloli daga bisani yadauki Quran yafara yakaranta wasu surori daga cikinsa nanma yadau tsawon awa guda .sannan yafito yakara Alwala yajeasallaci yai sallar laasar

Dakinsa ya koma yadauki casbaha dinsa. Yaita wuridi

Har lokacin sallar magriba .yafito yaje masallaci
Baishigo gidanba saida akai .ishai

Bayan yaci abincinsa ya gama
Dakinsa yakara komawa donya fuskanci many an shedanu aka hada Alh dasu .suke juya akalar rayuwarsa sai yanda sukai dashi

Aikin zaiyi wuya kasancewar. Alh baya kasa .don akwaibukatar ace yana nan don akwai ayoyin da zaa rubutamai .kuma atofa masa wasu aruwa yasha

To kuwa tunda haka ne .saiya dage yafara karkato da hankalinsa yayo gida

Don haka kwana yai yana salloli da wuridi .na Neman nasara sannan yana rokon Allah yasa adace .bashi ya runtsaba sai bayan gari yai haske .washe gari .sannan ya kwanta ya huta

Ka'in da na'in yake aiki akan Alh .har tsawon sati guda

Yana can China yaji garin yamasa zafi ya isheshi kawai so yataho gida don haka yahada dik wani abubuwansa yayo gida

Baby tana kwance a daki sanyi ya isheta sabida zazzabin daya rufeta tun safe

Jijjiga dikkan jikinta yakeyi .sosai sai kuka take
Batasan ya zatayi ba don haka taga kukan shine magani .yinshi take iya yinta .

Kira momy take kwala mata sabida me wanki ya wanke Kayan baby yan set biyar dinta datake using dasu koda yaushe

To kasancewar har pant dinta take hadamai .wannan karanma hardadu guda biyu
Sai bayan yagama
Wankin tazo ansa bata gansu cikin kayanba
Tace umar baka wankemin su pant dina ba

Kallon inda yai shanyar yayi yace na wanke dasu kinga fadowa sukai cikin ruwan wankin shine na kara wankemiki gasunan na shanya
Anjima kadan sun bushe kizo ki ansa

Tofa ita tunda tashiga daki zazzabi yafara nukurkusarta bata kara bin ta kansuba


To ganin tun jiya batazo ta karba

Yasa yau ya debosu yazo har kofar part din hjy yatsaya yana jiran yaji motsinta yabata


Yananan tsaye sunata hira da Ayuba me kula da shukoki yanabasu ruwa .

Hjy ta fito yiwa Amiyarta hjy maryam rakiya taganshi tsaye a bakin kofa
A wani yamutse ta kalleshi kaikuma ya akayi me kake jira an an a dibirbirce yashiga fadin a a dama dama um wandinan Baby ne data manta batazo ta karba shine nazo um kawo mata

Bata kawo komai arantaba tace .ja jiki da ga nan dallah kazami

Wani kallo hjy maryam tabita . dashi tace gaskiya kawata haryanzu da sauranki .
Wai bikiji me yace bane kika barshi yake shirin tafiya ?
Inbikijiba bari ni inkara tusa miki .
Haka yace wandunan Baby ne data manta agunsa tunjiya shine yazo kawo mata
Kuma ke kika fadamin cewa tun jiya bikiganta ta fitoba
Kinga maana yamata kaca kaca tanacan tana jinya

Wata uwar ashar momy ta lailayo ta muka tana fadin yanzu wannan yar yar hartason takai kanta ga namiji?
To wlh kuwa ysu zankasheta in huta tunkan ta girma tazamemin tsiya

.kai kuma πŸ‘ˆ ta nuno umar dake tsaye jikinsa yanata rawa donshi yama kasa fahimtar me sukenufi

Zakaci ubanka karshan aikinka agidanan yazo
Maza jeka hada kayanka ka barmin gida
[10/2, 11:44 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸



BABY KHAUSAR


NA

LAYUZA KABIR ADAM



ALHAMDU LILLAH DA BAIWARKA .GARENI HAKIKA MASOYI ABIN SONE
NAGODE DA KAUNARKU MASOYA




2⃣8⃣



Abinda ya faru shine Aranar Alh .yataso daga kasar China. Inda hankalinsa gaba daya ya tashi Yaji gida kawai yake nema .Tunani yake wai ina Baby ina yabarta tsawon lokaci shin wai awane hali take .dik yaji kwakwalwarsa ta tushe .don haka yayo gida batare daya sanar da kowa ba.

Saida yasauka a era port. .yakira direbansa yadau koshi yana shigowa .layi ya tarar da motar yan sanda ta fito daga gate din gidansa . cikin tashin hankali yacewa direbansa maza tsayar min da police dinnan me yafaru. Agidan .

Hannu yasa ya tsayar da motar police din ganin me gidanne yasa suka tsaya

Da sauri yafito daga motar ya nufesu yana fadin meya faru

Bayani babban cikinsu yaimai aikuwa dai hankalinsa inyai dubu ya tashi da sauri yace su biyoshi cikin gidan

Aikuwa suna shigowa shine sukai kicibis dasu .

Atare cikinsu yabada kululuuuu don busuyi tsammanin ganinsaba awannan lokacin
Amma dake yan duniyane saisu ka dake
.
Atunaninsu ai tunda .mijin tacene ba matsala sunsan yanda zasuyi dashi .matsalar kawai ta ganin police din sun dawo ne

Amma kana ganin idonsu kasa hankalinsu baya tare dasu atsorace suke matuka

Da sauri yakai hannu yakarbeta yana fadin innalillahi wa inna ilaihi rajiun

Umar ka cuceni ka batamin rayuwar Yarinya tsakanina dakai sharia ce me tsanani wlh saika ce dama uwarka bata haifokaba

Juyawa yai da sauri yafita police din sukabi bayansa suma su hjy suka rufa musu baya

Ganin sun dau hanyar family hospital dinsu ne yasa hjy Amina fadin a a Alh Bazamuje asibitinnanba muje sabon gari akwai wani asibiti da Hjy maryam take zuwa yasan takan irin wannan matsalar. Kai direba juya kan motar nan zuwa sabon gari

Keeeee dallah rufemin baki kibarni da tashin hankalin danake ciki zaki dameni dawani
zancan banza

Kai wuce maza zuwa inda muka saba zuwa

Mamaki matuka ya bayyana akan fuskarta me hakan ke nufi itakewa .Alh. Magana yakemata tsawa
Lalle da Matsala .tunanin dake ranta shike ran aminiyarta wadda take zaune tsugudi agefenta

Dikkansu ba komai acikinsu sai tarin gudawa

Suna shiga asibitin da gudu aka karbi baby zuwa emergency dinsu .kasancewar dama tunkafin su karaso Alh yakira doctor din yafada masa abinda yafaru

Suna nan tsaye a reception dik sun Zauna. Alh kam yana ta zirga zirga dik jijiyar kansa ta tashi idonsa yai jajir don bacin rai
Police guda biyu da suke tare dasu suna tsaye kam anbarsu donsu dauko report din komai tunda sauran sun wuce da umar zuwa office dinsu

Hhhhmnmm mutanan kuwa sun jike sharkaf da gumi don sunsan karyarsu ta gama karewa
Asirinsu ya Toni yanzu mafitarsu guda daya kawai dik yanda zaai su kebe da doctor ya


.

TAKUCE LAYUZA πŸ™‹
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:44 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸



BABY KHAUSAR


NA

LAYUZA KABIR ADAM





2⃣7⃣





Wani kallo ta karamata hade da murmushi tace
Ke yanzu saiki barshi yatafi kin koreshi
Ita kuma kishiga daki ki daketa .shikenan waji wayasan me akai mata
Ai yanzu bari kiga ta daga wayanta takira wani police mutuminta tace maza yazo gidan shahararran Dan kasuwarnan AA ABDALLAH
akwai wani ces

Bayan ta kashe wayan taja kunnan hjy Amina ta rada mata
(Ke ai yanzu wani sabon aikinne yataso mana kinga yanzu nakira police suzo sutafi dashi .akan ana tuhumarsa da hakkewa yar me gidanki .ayada maganar tacika duniya .mushigar da kara court abaza zancan duniya taji Me wankin gidan Shahararran Dan kasuwar nan AA ABDALLAH yaiwa yarsa tilo guda daya fyade kinga tunda ka lokacin anmata number kowa yaji anbata mata rayuwa kinga shikenan ko bayan ta girma bamai auranta .rayuwarta ta nakasa

Kinga ke kuma duniya zatai ta yabonki .kina riketa tsakani da Allah tunda gashi kintsaya kai da kafa kin shigar da kara akan afitar mata da hakkinta )
Wata shewa hjy Amina tasaki tare da rungume .kawarta tana fadin ke maryam ko shedan na tsoronki wajan shirya makirci
(A'uzu billahi minashshai danurrajim)

Suna haka sukaji jiniya .aikuwa da sauri sukai rikidewar karya momy tasa kukan munafirci
Har cikin gidan police din suka shigo hjy maryam tace gashinan maza Ku tafi. Dashi yarme gidannan yaiwa fyade me wankin gidan ne Ku tafi dashi shege Mara imani .

Haka sukasa masa ankwa ahannu suka tasa keyarshi .har sunkai bakin gate daya daga cikin yan sandan ya dawo yace ina yarinyar da akaiwa fyaden

Itama munasan tafiya da ita sabida sheda

Duburburcewa sukai nan nan da nan
Hjy maryam tace
Ai tana asibiti tuni akai asibiti da ita don cecan ranta .yanzu zamuje asibitin .muga halin da take ciki inyaso sai atura wasu can asibitin suganta

To wane asibiti aka kaita um um
Bamu sani ba bari mukira waya muji
Zai kara magana ta dagawa dayan police din data kira gira alamar su tafi

Tsawa yaiwa me shirin kara maganar kasancewar sama yake dashi
Sukasa kai suka bar gidan

Da sauri taja hannun hjy Amina sukai cikin parlour saida sukaje tsakiyar parlourn .suka tsaya .tofa Amina yanzu dole musan abinyi tunkan aikinmu ya lalace mu kwana aciki

Don haka yanzu mushiga dakin yarinyar nan

Mu nada mata duka mu wahalar da ita har sai ta fita hayyacinta

Sannan mu dauketa. Mukaita wani. Private hospital a sabon gari na. Wani inya murine yanada san kudi
Mu siyeshi yayi report akan ces din fyade ne dik yan. Sandan da sukazo. Bincike yasanar dasu fyade akwai mata

Amma yayi treatment dinta

Da sauri suka fada. Dakin. Baby. Tana. Gado. Tanata. Rawar. Sanyi. Suka hauta. Da. Duka hardasu naushi da toshe numfashi

Kasanceawar dama zazxabi. Ya galabaitar da ita .ai kafin me
Harta sume.


Sungumarta. Sukai. Sukayo. Parlour suna fita sukaga Alh yashigo. Da. Sauri. Police na bin bayansa.






Takuce Layuza kabir Adam. πŸ™‹

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:44 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


BABY KHAUSAR



NA


LAYUZA KABIR ADAM




2⃣9⃣




Tsawon lokaci Doctor yafito daga ciki yai office dinsa da sauri Alh yabishi .police dinma suka bishi .

Mutanankuwa . zaro ido sukai agigice suka kalli juna
Hjy Amina tace maryam yazamuyi .nima bansan yanda zamuyiba Amina .dabarata ta kare .daman naso ace mun kebe da doctor. Mun bashi ko nawa yake bukata akan .dik yanda zaai yace anti reping yarinyar nan
Hmmmm wlh koda mun ganshi maryam wannan doctor din bai zama lalle yamana abinda mukesoba. Sabida kinga family doctor dinmu ne amintaccan Alh.ne

Gashi na fuskanci aikinmu yai sanyi tunda gashi .agabanki Alh yamin tsawa .ai kuwa kinga da matsala .dik yanda muke tunanin. Abinnan yawuce nan

Yanzu mafita daya ce . idan doctor ya fada musu baayi reping dintaba. Muce munyi zaton yamata wani Abu ne sabida munkamashi yashigo mana part yashiga dakinta kuma mun kamashi da pant dinta ahannunsa ga kuma Yarinya asume .

Yawwa Amina kema wannan karan kinkawo shawara me kyau yanzu muzauna anan mujira fitowarsu

A office din doctor kuwa bayan yazauna yaiwa Alh iso kan kujera yazauna .police dinkuma suna tsaye akansu

Doctor yacire glass din idonsa ya goge gumin fuskarsa sannan yafara magana

Alh. Kafin Ku karaso kamin waya akan cewa ga khausar nan zaka Kawo anyi Repin dinta amma kuma gashi na dubata ba wani alamar fyade atare da ita .baa mata komai ba

Alhamdulillah shine abinda Alh.yafada yana daga hannunsa sama

Saidai kuma akwai babbar matsala don abinciken da mukayi akwai tarin wasu cututtuka ajikinta .Yarinya karama kamar khausar tanada ulcers tanada nimonia ga typot .banda wasu kananan cutuka .da basu gama tasiri ajikintaba

Kuma abinciken da mukai sanadiyar sumanta shine zazzabi me zafi ne ajikinta wanda ya konar da ruwan jikinta
Don haka khausar tana bukatar taimako sosai da sosai .
Don agaskiya Alh kunyi sake sosai da rayuwar yarinyar nan .don ina tunanin fa rabon da ayimata general checking yakai shekara uku .koda yaushe inkunzo nace ina baby saikuce lta baza amataba lafiyarta qlau ko kuce ankaita wani hospital anmata .

Dafe kai Alh yai cikin tsananin taahin hankali shi baisan ma me zaiceba kwata kwata .yarasa me yadameshi haka
Yanzu don Allah doctor kabar dik wani abinda yawuce tsautsayine yanzu kayi bakin kokarinka .ka kula da ita .dik abinda yakamata ayimata yanzu zan iya shiga inganta
A a gaakiya saidai zuwa nan da 1 hour.
To shikenan doctor na gode .bari insallami wannan police din ina zuwa
Juyawa yai yafice .sukasa kai sukabi bayansa

Suna fitowa su hjy sukayo Kansu suna fadin Alh ya akayi .

Kafesu yai kaf da ido .sannan yace ya akayi kukace. Umar yaiwa baby fyade gashi kuma

Please Login or Register in order to submit comment