You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zauna a waliyin Amarya
Ana sallar ishai Baba matar Mlm da yan tsofaffi kawayenta. Suka kawo hadiza gidan mijinta wanda aka sata a bangarenta dake gefan na hjy

Sudai yantsofaffi nasiha kawai sukewa hadiza da haka suka barta ita kadai sai kuka take don tana tinani. Yanda zata had a miji da uwar dakinta .
Yau kwanan hadiza biyar a amatsayin amarya a gidan zuwa yanzu ta sake jiki ta yarda wannan yin Allah ne .
Kuma da taimakon nasihar iya Abu kullum take mata don yanzu ta dawo bangaran Hadiza da zama .tunda Alh.yace zai samo mata mai tayata aiki tace a a iya Abu ma t isa ta debo kayanta aka bata daki guda akasa .suke zamansu .

Kullum bangaran hadiza a rufe yake sabida tana tsoron haduwa da hjy. Son haka ko Alh.ne zai shigo saidai yai anfani da keys dinsa ya bude

Cikin ikon Allah watan hadiza biyar agidan ta sami ciki aikuwa tunda iya Abu ta lura da cikin ta kira Alh.ta fadamai kuma tacemishi .dik suyi shiru da bakinsu don irin wannan ba ason yadawa sabida maganr mutane

Aikuwa Alh yaja bakinsa yai shiru ba wanda ya fadawa sai Mlm Khalil

Yau da gobe cikin hadiza yakai wata takwas ba ta taba fita ko inaba ko awoma likita ke zuwa har gida ya yaimata Alh yadaukewa hadiza dik wata damuwa .tayi kyau ta kara fari .

Yau tunda ta tashi takeson fita ko harabar gidanne don rabonta da waje tun randa aka kawota .wani irin masifar tsoron hjy Amina takeji .wanda bata fatan ko hanya ta hadasu.

Wajan karfe biyar na yamna .tafito barandar gidan tfy take .ahankali irin ta masu tsohon ciki .tana kallon gidan kamar bashiba yazamemata wani iri tana shirin shiga Gardiner din gidan taci karo da Barira .
Salatin da Barira keyi tana tafa hannu yasata jin faduwar gaba .ah lalle hadiza harcin amanar taki yakai ki dau ciki agidannan .tabdin jamm kafin kace me harta zura da gudu kaiwa hjy.rahoto


Jikinta amace ta koma bangaranta .itama cike da tsoron me zaije yazo

Barira kam ta kaiwa hjy lbr mafi muni da Tayar da hankali
Kamar zata hau iska haka har Alh.yadawo yasameta tanata sababi da masifa akan ya cuceta ya rufe mata hadiza Nada ciki.haka suka kwana tana sababi .shi abin har mamaki yake bashi yanda dik halayen hjy Amina suka canja ta zama . masifaffiyar gaske .
Tinani yake wai shin haka dik mata sukeyi in aka musu kishiya?

Bayan sati biyu .cikin dare hadiza ta farka da nakuda gashi ranar Alh yana dakin hjy.tun tana daurewa har tazo ta tashi Iya Abu .ai kafin iya Abu taje kiran Alh .har ta haihu .


Iyace ta gyarata tsafuhh ta gyara babyn da wajan zuwa sallar asuba har sunyi fes itada kyakkyawar babynta .tubarkallah masha Allah.
[10/2, 11:40 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

BABY KHAUSAR

NA

LAYUZA KABIR ADAM



HHHMMMM RAAYI RIGA .NIKAM NAWA RA'AYIN KENAN .RUBUTA NOVEL.πŸ˜€πŸ™‹


1⃣2⃣


Wayyo haihuwa kyautar Allah .wanda babu me iyai maka wannan kyauta komai son da yakema
Hakika wanda Allah yabawa kyautar haihuwa .yamishi kyauta me girma
Wai dama haka mutum yake tsintar kansa .in akace yau gashi matarsa ta haihu.
Wannan shine subadadin da AA Abdallah
Yaketa yi lokacin daya sa babynsa akirjinsa . yanajin wani irin nishadin da nutsuwa yana shigarsa . zir hawaye yafara bin kuncinsa .

Iya Abuce ta lura da yanayin daya shiga. Tai gyaran mirya .tace ai Alh.ba kuka zakayi ba .godiya. Zakayi ga Allah daya baka sai yakara maka .
Alhamdulillah yashiga fada yana .kara rungume .babyn .har zuwa wani lokci .sannan .yaimata kiran sallah .da Adduoi.

Juyowa yai yaga iya Abu ta fita .ahankali yasa hannu ya rungume hadiza .yana samata Albarka da godiya .

Yace hadiza na baki kyautar .Plaza dina da ke haj kam. Sannan na baki kyautar sabuwar mota ta . na baki kyautar gidan gona ta na kumbotso. Sannan na baki kyautar million daya .kuma zan miki viza .in kinyi arbain .zamuje kasashen duniya daga biyar har zuwa ishirin in kina so. Bayan haka ki fadamin wani abinda kikeso .

Cikin shishikar kukan farin ciki .tace .Alhamdulillahillazi bi niimatihi ta tummassalihat.
.Alh. Na gode ma da kulawarka .Allah yakara budi da arziki me albarka

Wayanshi ya dauka yashiga kiran yan uwa da abokan arziki yana gadamisu.
Daga bisani ya koma part din hjy da fara arsa .yake cewa Amina kina ina ne yau Alheri ya sauka agidannan .hadiza ta haihu .ansami ya mace kyautar Allah .(littafin Ashmaad)

Wani matsiyacin kallo tabishi dashi .sannan tace to Allah yaraya .
Amin Amin yake fada yana kokarin daga wayarsa da aketa kiransa don mishi barka .don haka ma bai lura da yanayin da take ciki ba yafice .yana wayanshi.

Gaba daya ya rasa inda Zaisa ranshi don murna .kara komawa yai .gun hadiza yana fadin .yanxu me ake bukata na baby akaro . a haba Alh. Me zaa bukata yanzu .dik irin tarin kayan dakasa akai oda na baby .ai daga nan har shekara .babyn nan batada da bukar wani Abu .

Gyada kai yai yana leka fuskar babyn .yace ammafa hadiza. Kinmin wayo .babyn nan kamarku daya ba abinda ta baro naki .
Amma nanda shekara daya insha Allah zaki .kara haihuwa saiki haifomin me kama Dani.
Mirmishi kawai take ita dai .


Tofa aiki yasamu a inda ake nemansa .shirin bikin suna ake tukuru .rabon kati Alh yake tako ina na sunan tilon yarshi daya shafe shekaru goma yana fatan samu .

Ranar Asabar din data zagayo .akai gagarumin taron sunan Babyn Data amsa suna KHAUSAR .dik Inda ka kalla. Manyan jakunkuna zaka hango da hoton jinjirar ajiki an rubuta BABY KHAUSAR A.ABDALLAH

abokan kasuwancinsa daga kasa kasa sukazo tayashi murna .kuma ko wanne da irin gagarumar kyautar da zaiwa babyn da mamanta .
Haka dai akasha shagalin suna .aka kashe naira kamar ba gobe .Yarinya fa tayi goshi .don ta Tara abinduniya.matuka kama daga sutturu .mota gida .dakuma tanfatsetsan kanfanin da mahaifinta yaimata .kyautarsa .da sunanta ajiki.

🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:40 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


BABY KHAUSAR

NA
LAYUZA KABIR ADAM


1⃣3⃣


Sannu sannu yau gashi baby khausar .kwananta Arbain a duniya tayi kubul kubul da ita ga wani kyau da Allah yaimata baiwa dashi

Soyayyarta kuwa azuciyar mahaifinta baa magana don indai ya fita .office kafin ya dawo ya kira waya kusan sau goma yana tanbayar lafiyarta

Inkuwa yana gida ko baa dakin mamanta zai kwanaba .sai ya dauketa yaje bangaransa da ita yaita mata wasa .haka zasu shashance shida Bilal gurin mata wasa ita kuma tana bangale baki..
Don shi Bilal yanzu bashi da wani aiki Wanda yawuce wasa da baby .yana dawowa skl zai zo bangaransu .yana knocking .yana fadin. Aunty budemin kofa nazo gun Sister na .baby haka zaizo .yazauna yaita mata .wasa .
Tun momynsa tana hanashi .tamai fada ta bigeshi .amma yana share hawaye zai koma.

Wannan dalilin yasa bakin cikin hjy Amina karuwa don haka .tasami wata kawarta hjy maryam take bata labarin matsalar datake ciki
Mirmishi hjy maryam tai tace to ai hjy Amina tun farko lefinki ne .
Mun Dade muna baki shawara akan kibi hanyarmu . yanzu matsalarki zata warware amma .waike ta Allah saiki rinka barin bakin cikin da namiji yana Neman kasheki

Jijjiga kai tayi tace .gaskiya hjy maryam nikam bazan iya bin malamai ba . sam wannan hanyar bata birgeni .kara dai .inta mai hayaniya muyi fada .akan inbi malamai
. to tunda kuwa haka ne sai kicigaba da zuba ido kina ganin bakin ciki .wlh kina zaune kwanan nan zaki ganta da wani cikin badai tayi arbainba .zakisha mamaki.
Itadai hjy Amina haka ta tashi tayo gida
Jiki a sabule.
Gashi yanzu yayarta hjy halima basa kano .sun koma Lagos .don anyiwa mijinta transfer a gun aiki. Sun koma can gaba daya
Da tana nan ma taje gunta tasan ko ba komai Tamata magana me dadi taji sanyi aranta .koda bazatai aiki da maganarta ba

Shirye shiryen tafiyarsu kasashe shida shida hadiza Alh.yasa agaba kamar yanda yai mata alkawari.
Yanzu saura kwana biyu su tafi.
Don haka .yasami momyn Bilal a daki .yace
Amina kamar yanda kika sani jibi .laraba .zamu tafi Dubai nida hadiza daga nan zamu zazzaga wasu kasashen. Yanzu ga wannan calk din .dik abinda kuke bukata keda .Bilal ku dibi kudi .iya abinda kukeso. Da sauran hidimar gida da albashin Maaikatan gida dik kiyi.

Haba Alh. Yanzu kayimin Adalci Kenan kadauki hadiza .ku tafi ni kabarni agida?
Da mamaki ya kalleta yace banganeba Amina me kikeson cewa .meye abin rashin Adalci anan .sau nawa muka fita kasashen duniya dake .ko saudiya sau nawa kikaje .fitarki bazai kirguba Amina
Amma tunda na auri hadiza .ko Abuja kinga naje da ita?
Kije dik abinda zakice kice .tunda bakiga Adalcin da nake .mikiba.

Fita yai ya koma dakinsa ransa yana suya .
Jin andafashi yasa ya jiyo yasan Bilal ne
Ya akai my son .Dad bacci kakeyi ne .inata maka magana bakajiba .a a .my son ba bacci nakeba . ya akayi. Dad kaje ka dauko mana Baby .muyi mata wasa .
A a Bilal kaina ciwo yake bari zuwa anjima zan dauko mana .ita.
Jibi zamuyi tafiya .ma My son zaka daina ganin sister dinka .
Ware ido yai .kai indai da baby zaa tafi nima zanje .
A a Bilai kaga bukiyu Hutu ba sai zuwa next week. Da kunyi saimu tafi tare.


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:40 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

BABY KHAUSAR

NA

LAYUZA KABIR ADAM

YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA UBANGIJINMU ALLAH .TSIRA DA AMINCI SU KARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD
(S.W.A)



1⃣4⃣


Karfe goma Am jirginsu yatashi .zuwa U.S.A. .Wanda shine karo na farko da hadiza ta taba barin gida Nigeria. Cikin farin ciki suka sauka a hadaddan hotel. Wanda Alh.yakamamusu daki na Alfarma.kwanansu goma a a kasar Sukai gaba haka sukaita zagaya kasashe .sannan sika yada zango a saudiya .inda hadiza taita kuka saboda dadi .yau gata a garin manzo . Haka sukai ummara . sosai takewa iyayenta addua .tana nemarmusu Dacewa da jannatulfirdausi.

Sunyi tsaraba kamar baa San darajar kudiba Baby khausar tasha Kaya don dik inda Dad dinta yaga Kayan yara kama daga suttura zuwa Kayan wasa da Kayan kwalliyar dakin yara haka yake kwasar mata .
Ita kuwa hadiza Bilal da mom dinsa tafi dibarwa .da iya Abu .sai Mlm Khalil da sukaiwa tsarabar Jallabiyu na maza .da huluna .da takalma

Ranar da sukai Wata biyu da kwana biyu suka dawo gida dikkansu sun canja .sunyi wani irin kyau .fatarsu ta kara mirjewa .musammam baby khausar datake Yarinya .yanzu watanta uku da rabi .tayi wayo sosai .

Dawowar tasu ta tsakar darece .don haka ya kwana dakin hadiza .yana fitowa daga masallacisallar asuba . yashiga bangaran Hjy Amina .lokacin tana toilet. Tana fitowa
Taganshi gefan. Kujera dake dakin zaune .yanajan casbaha dinsa .kallo daya tamai ta kauda kai ta dauki praye mat .tashinfida tare da tada sallah .
Baice mata uffaanba .saida ta idar .sannan ya dubeta .yace .Amina bikiganni ba ne.
Na ganka .meya faru .ko kaga wani Abu ne
.a a banga komaiba na sameku lfy?
Ya hidima da gida ya my son .dik lfy .ko bakaga alamar hakamba .

Mamaki ne yake cin ransa .matuka na yanda gaba daya Amina ta canja rayuwarta .rabon dayasami kwamciyar
Hankali.daga gareta tun randa .taji maganar auransa.
Amina daya sani da hankali da nutsuwa .amma yanzu dik babu sai wulakanci da raini. Wanda da dik ba dabiunta bane .
Shin wai. Daman dik mata haka suke
Da irin wamnan banzan kishin .
Amma ai ko kishinne. .yakamata ace xuwa yanzu ta hakura .tsawa shekara da rabi .da .auran amma haryanzu .kullum wulakancinta . karuwa yake .akanshi....... Tsawon mintina yana wannan tunani .daga bisani yamike yashiga dakin Bilal yasameshi .bai tashi a bacciba. Shafa kansa yai sannan yafito yashiga .bangaransa .
Dik yai kura .don haka .ya dawo falon .hjy ya kwanta kan 3 sitter. Yaci gaba da .jan casbahansa.


Rayuwa .gudu take .yanzu .gashi baby khausar .takai shekara 2 a duniya .kuma tuni an Dade da yayeta tafiyarta take ko ina .gwanin shaawa da ita . shakuwa ce bata wasa ba tsakanin ta da Bilal . wanda da gwarancin ta take cewa .broth. Shikuma yace mata sis baby. Inya shigo gunsu .da gudunta take rungumeshi. Tana zillo.shikuma ya goyata yaita mata doki .abinda tafiso Kenan.

Shikuwa Bilal ko a school. Kullum ko islamiyya koda yaushe .sister na baby kaza kanwata dik tafi kannanku kyau ni kanwata .kama take da Fulani da larabawa.don haka dik wanda yasan Bilal yasanshi da labarin baby khausar.

🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:41 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


BABY KHAUSAR

NA

LAYUZA KABIR ADAM



Wannan shafin nakune .kawayena Aminaina .
Hauwa'u Alhassan usman

Saadatu bayaro Jaoji.



1⃣6⃣






Haka ma in antashesu .zaije yadaukota dake ana riga tashin yan nursery akansu .yakawota aji yasata a kujerarsa .har Karin awa daya da zaa tashesu suma.dikda akwai katon reception da dalibai ke jiran yayyansu . amma ita baya barinta a gun.tin ran farko .data zauna gun .wata Yarinya ta tureta
Ta fadi .yazo yasameta tanata kuka.
Sina zuwa gida yafadawa dad dinsu .ai kuwa take yakira me makarantar yace .abar khausar tarinka jiran Bilal cikin class dinsu don yara sina bugunta .ai kuwa nan da nan principal yatara malamai yace dik wanda yashiga j.s.s two ajinsu Bilal yaga kanwarsa a ajin kar a koreta.inta zauna a reception yara na bugunta. πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€(kaji aikin nera ko)


Don haka dai Baby ta zama tauraruwa tun tana pree nursery. Dik malaman secondary section sunsanta .

Haka duniyar take canjawa kuma take zabga gudu me rai yake mutuwa Kuma ake haifar na ciki yakai har anyi exam na fest term. Anyi gajeran Hutu andawo .
Sosai Bilal yakewa Baby khausar lesson a gida .iya wanda kwakwalwarta zai iya dauka
Kasamcewarsu a skl daya yakara musu shakuwa sosai .tunda in sunkoma gida .daga .anyi laasar karfe hudu kuma direba zai kaisu islamiyya dake gaban layinsu in shida tayi yaje yadaukosu don haka zamansu agida yanzu gajerene. Sai week end ko Alhamis da jummaa da yamma asannan suke samu yajata filin gidan suyita wasa ya goyata .yai mata doki.

Yauma yakasance Alhamis .Sun gida da yamma .yajata suka shiga .cikin zoo dinsu dake gidan suna .shiga Dan biri .yayo Kansu da tsallansa .ai kuwa baby ta zuba wata razananniyar kara .saigani yai ta fadi .Ashe ta suma .dariya yake .amma dayaga bata motsi sai shima yasa ihu me kula da wajan yashigo .yana zuwa yaganta kwance yadagata .yaga ai ta suma .aikuwa da gudu yai bakin fanfo da ita .yasakar mata ruwa .lokaci kadan ta ja numfashi

.iya Abu ta fito nemansu taga me kula da zoo yasabota a kafada .ruwa na yarari ajikinta ga Bilal sai kuka yake .da salati ta taresu tanafadin .meyafaru lfy .karbarta tai tai ciki suna shiga ta fara kwadawa hadiza kira daga .sama ta sakko tana cewa iya metafaru .ganin khausar kan cinya sharkaf da ruwa yasa tace .meyasameta haka .ba tare da damuwa ba take tanbayar don hadiza akwai fillanci akan khausar .cikin gigita Bilal yace Aunty zoo fa mukashiga shine taka monkey tafadi ta suma .
Jijjiga kai tai tace tsorata tai iya canja mata Kaya ta kwanta . a a hadiza akaita dai asibiti a duba lafiyarta .


Kai iya wane irin asibiti kuma bagashi ta farfadoba .kawai kyaleta .rawan kanta ai .

Bilal ne yajuya da gudu yai bangaransu dakinsa yaje yadauko wayarsa .kiran family doctor nasu yai yace kazo gidanmu doctor sister batada lafiya kuma Dad dinmu baya gari.to ganinan Bilal cewar doctor

Baafi 30mint ba doctor yazo ya duddubata .ba wata Matsala yabata paracetamol. Ya wuce

Tundaga wannan ranar baby ke tsoron biri .ko a t.v aka nunoshi runtse ido take taita kuka.

🌸🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:41 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

BABY KHAUSAR

NA

LAYUZA KABIR ADAM


DEDICATED πŸ‘‡to
My kawa HALIMATUSSADIYYA. (mmn twins) ALLAH YA SAUKEKI LFY AMIN


1⃣5⃣

Bilal yanzu shekararsa goma .yana. J s s. One.
Boss ne sosai a dik inda yake baya wasa .kuma dariya ma saiya so tun a primary section teachers suke kiransa da. Sunan .don kirar karfafan maza gareshi .ga hade gira kamar. Wani babba. Inyana wani abun saika dauka katon surayi ne.
Balle yanzu dayake ganin ya tsallaka secondary section. .kamar yanda yake . class caftin a .pri.section hakama yanzu dake dik cikin. Schoo dinne. Kuma. Yawancin yan class dinma dai sune .sai Karin da suka samu na news students .

Cikin dabiun BILAL A ABDALLAH da teachers dinsu keso shine kokari yana da kokari matuka da gaske na biyu respect ga dik .na gaba fashi ga displing ga na kasa dashi . na uku tausayi .in dai zaiga wani cikin matsala dik da kankantar shekarunsa saiya bi dik yanda zaiyi ya rarrasheka inyaga abin babbane to saiya kai report ga malamai . sai kuma Abu na gaba .wanda yakara sai mai kaina da power a schoo din shine .sakin hannu da Dad dinsa kewa malaman .don lokaci zuwa lokaci .yakan kawo ziyara school din .kuma dik sanda yazo 20k dinnan yana bawa kowanne teacher dayake school a ranar .don haka wannan yasa ko kuda baa son aga ya taba Bilal cikin school dinnan.

Abangaran students kuwa .su. Seniors dinsa suna sonshi don kyansa da kuma acting dinsa yana birgesu .yayin dasauran Junior suke sonsa don kyautarsa . don Kullum jakar Bilal cike take. Da tarkacen zaki .kuma inyaxo haka zaita rabawa students dik da suma mafi yawansu yayan masu hannu da shuni ne .hakan baisa su kin karbar kyautar Bilal boss

Hhhmmmm Bilal boss Kenan .

Agida kuwa bata chanja zani ba haryanzu Hjy Amina zuciyarta nanan da tsanar hadiza da Baby khausar kuma tanan tana shan ziga kullum daga gun mu gayen kawayenta

Abangaran Alh kuwa kullum burinsa yaga yayi adalci tsakanin matansa . yana iya bakin kokarinsa kuma .gashi yanzu bai samin ishashan zama agida Nigeria. Don kusan harkokin kasuwancin kara tunbatsa suke sosai arzikinsa yake gaba.
Don koda yaushe yana China. Ko Dubai zuwa India



Baby kuwa tananan tana kara girmanta. Yanzu shekararta uku .kuma wannan term dinne akai mata shirin sata a pree nursery a skl din su Bilal .kasancewa tanada tsayi masha Allah saidai ba kiba .ga Dan karan surutu .koda yaushe bakinta .Dady na mamy na brother na and iya Abu na . I love u All. Dik Bilal ke koya mata surutu .
Da karatu .ya koya mata fatiha .dasu Alifun ba'un .su A b c d. Su 123. Haka zaisata agaba .yace tace wannan tace wannan.

Ai kuwa tunda aka kaita Pree nursery. Kowa yasani a school din an kawo sister din bilal .skl. Sunanta Baby khausar
Dik da ba section dinsu dayaba don harma da karamin gate tsakaninsu Amma ana fita break zaije ya daukota .yaita tsagayawa da ita.yana fadin ga sister dina . sai ankoma class kuma ya maidata.

Haka kuma in an tashesu .dake ana riga tashin yan nursery. Kafin primary da secondary. Zai daukota ya kawota ajinsu .yasata akujerarsa .har Karin awa daya suma da zaa tashesu. Dik da akwai waje na musammam da aka ware don students masu jiran yayyansu ko driver. Kafin yazo daukansu. Amma ita .baya barinta zama anan .tun ran farko daya kawota aji wani Malami yana ajin yace yafita da ita.ya ajiyeta .inda sauran dalibai suke jira suna fita taita kuka.
[10/2, 11:41 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


BABY KHAUSAR

NA

LAYUZA KABIR


TUKUCIN KAUNA GA DIKKAN MASOYANA .
NA GODE DA SAMUN GOYON BAYANKU AKODA YAUSHE.ALLAH YABAR KAUNA



1⃣7⃣


_Rana_ _mafi_ _muni_ _garesu_

Annobar amai da gudawa aketayi agari
Cikin dare hadiza ta farka da gudawa tun tana iya tashi tashiga toilet da kanta harta gagara tashi .don haka taja wayanta takira .layin Alh. Cikin bacci. Yaji kiranta . da sauri yadaga yana fadin hadiza ya akai .jin tana fidda numfashi da kyar. Yasa yatashi da sauri ya dauki jallabiyansa yasa .yafito da matukar sauri.


Da key dinsa ya bude yashiga . yanda yasameta kwance male male cikin amaine yamatukar razanashi .yasaki salati .yana dagota .

Rungumota yai .yasauko da ita daga sama yana fadin

iya Abu iya Abu .da gudu ta fito tana mitstsika. Ido .na masu bacci .
Subhanallahi Alh meya sameta .

Nima haka na taddata .zamuje asibiti ki kula da Baby kuma kishiga dakinta ki gyara inda ta bata.

To hadiza sannu Allah yasauwake
Ciwo farat daya lfy fa mukai sallama taje ta kwanta .ikon Allah Kenan.


Likitoci manya suka tsaya akanta .akasa mata ruwa da alluran. Tsaida amai da kuma gudawar. .

Ga ruwa yana tafiya amma fa tana kasayardashi
Gudawa take .kamar ruwa . karama aman ya tsagaita .kadan

Ta galabaita matuka don ko idonta bata iya budewa .sai numfashi .sama sama

Hankalin Alh fa yakai matuka wajan tashi tun yana salati .har yasoma hawaye .
Awa uku ana Abu daya . zuwa sallar asiba kuwa .ranta yafita .



Please Login or Register in order to submit comment