You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Likitan dake kanta ne yai salati .tare da jan zani yarufe mata fuska .
Wannan ne yafargar da Alh. Ai kuwa ya kaiwa doctor n .danka yana fadin me kakeso kacemin wai .kana nufin hadiza ta rasu

Hannunsa doctor din ya riko . yashiga. Bibbiga kafadarsa yana be a man Alh .kayi hakuri Allah daya karbeta ya fika sonta .

Wani irin kuka yasa .yana fadin wayyo Allah na .hadiza hasken rayuwata kin tafi kinbarmu .nida baby cikin maraici .wayyo mata ta .Allah ya hadaki da manzon tsira .

Tsawon lokaci yana kuka sannan yai ajiyar zuciya .yace doctor Ku .bani gawar nan yanzu intafi da ita.
Nan da nan suka gama cike cikensu sukasata Ambulance. Shima yashiga . aka kulle motansa aka ajiyeta ana Abu .don bazai iya tuki awanna halinba.


Ganin ambulance tashigo gidan yasa .dik maaikatan gidan da suka fito daga masallaci .karasowa jikin motan don sunsan Alh.ya tafi da me dakinsa asibiti.
Toba sai anmusu bayani ba daga ganin .yanda Alh ke rizgar kuka .
Suka hau salati .nan da nan aka fito da gawar akan makarar. Asibi kama kama sukai zuwa bangaranta .


Bubbuga kofar falon da ake ne yasa Iya Abu saurin zuwa ta bude .ganin maza dauke da makara .yasata sakin salati hade da wani gigitaccen kuka .haba hadiza meyasa zaki mana haka .daga ciwon kwana daya saiki mutu........
Don Allah ki tashi kinga fa Baby
Karki tafi kibarta cikin maraici mana.

🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

BABY KHAUSAR

NA

LAYUZA KABIR ADAM


1⃣8⃣


Malam haruna ne .yace bari fadin haka Abu .wannan bashi yadace musulmi yafada ba .inyai rashi maza yi ta fadin Innalillahi wa inna ilaihi rajiun
Allah shi yabukaci abarsa a wannan lokacin kuma .dole miyi hakuri.

Nan dai aka shiga fadawa mutane sarkin gidane ya dauki wayan Alh.yarinka kiran .mutanansa yana fada musu .

Ita kanta hjy ta razana da jin mutuwar hadiza farat daya .nan dik jikinta yai sanyi lalle Allah abin tsoro rayuwa abin tsoro.

To haka dai aka shiryata aka kaita gidanta na gaskiya .

Kullu nafsin za' ikatul maut(dikkan me rai mamaci ne )

Mutuwa dai kam mutum uku akayiwa mijinta .yarta.da kuma iya Abu data dauka amatsayin uwa.

Su hjy.Halima ma da me gidanta dik sunzo daga Lagos
Haka akai zaman makoki tsawon kwana bakwai .kowa ya koma .inda ya fito

Kuma aranar ne Hjy Amina ta shigo part din na marigaiyiya . a falow ta sami Alhajin zaune ya rungume baby khausar yanata kuka .ga iya Abu ma tana kasan kujera tana .rusa nata.kukan.
Waje tasamu ta zauna .tsawon 10mint sannan tace Alh.dama wata shawara ce nazo da .ita .ina ganin zaman Baby da iya Abu agunnan su kadai bazai yuyuba .sabida matukar suna zaune anan to zuciyar su bazata taba yin sanyiba kullum zasu rika tunaninta.
Yanzu su koma bangaranmu ga dakuna nan akasa saisu .zauna a daya .tunda kaga khausar bazata yarda ta zauna ba iya Abu ba .
Ko ko ya kace?

Jijjiga kai yai yana fadin hakan zaayi Amina nima insun bar nan sai hankalina yafi kwanciya.

Don haka iya ki had a muku dik wani Abu da kuke bukata .zuwa gobe .sai akara shirya muku dakin ko_?
Yafada yana shafa kan baby dataketa kallonsa . itadai baby tunaninta bai kai yagane mata tana cikin rashiba saidai . dik Alhini ya damu jikinta .kulum da xaxkabi take kwana tayi sanyi qlau .ko abinci bata son ci sai an takura mata

Da wannan shawarar.ya mike rike da hannun baby yai stairs da ita .don tunda akai rasuwar adakin hadiza yake kwana rungume da baby .

Da safe yakira masu aiki suka ziba sabbin Kaya da gadon yara acikin dakin aka shirya musu .komai itada iya Abu .suka kwaso sutturunsu .da sauran abinda suke bukata. Aranar sika koma bangaran hjy Amina. Alh. Ya kulle part din hadiza.

Tofa tunda ga wannan lokacin zaman baby yadawo nan.kullum inba makaranta suna tare da yayanta Bilal a fallow wannan yakara musu shakuwa.

.yanzu Alh.ya rage tafiye tafiye kullum yana tare da baby khausar .yana kokarin debemata .kewan mom dinta .
Dik wani motsinsa .yace baby dik tausayinta yakeji.

.wata rana da yamma yana zaune a a harabar gidan Rungume da baby .yazuba uban tagumi. Yana tunani. Hjy. Maryam tashigo. Gidan .bayan tayi farking din motanta
Harta karaso besani ba tana ta gaidashi amma ina .baima sani ba.
Jijjiga kai tayi .ta wuce .ciki.
Bayan sungaisa da aminiyarta .ta gayara zama tana fadin hjy Amina wai shikenan haka zakiyita zama da mutumin nan ya zamemiki kamar mutum mutumi. Kefa da kanki kikace yanzu ko hiran kirki baya yi dake .tunda akai rasuwarnan .bashi da lokacin kowa saina wannan aljanar yar.

To wlh bari kiji infada miki wani labari najiyo cewa jamaa sunata . yimai tallan yayansu ya aura .
Kuma kinsan yanzu .yana karbar ayinsu. Ya zo yakara aure . dik wadda ta shigo .itama haihuwa zatayi.
Kinga Kenan alamu sun nuna kece bakya haihuwa an tara kudi dake .
Wasu zasu Tara magada .ke kina zaune .ga wannan yaron Bilal haka zaku tashi ba komai.

Don haka kawata ina jan hankalinki akan .lokaci yayi da yazama dole .kicire akidar kin bin bokaye
Asamu ajanye hankalinsa akan kowace .mace .yaji Sam baya shaawar kara yin wani auran
Sannan akau da hankalinsa akan wannan yar tasa .yazama ke . kadaice agabansa
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸



BABY KHAUSAR

NA

LAYUZA KABIR ADAM





Allah ina rokonka da sunayanka tsarka da ikonka madaukaki
Da ka jikan ginshikai biyu a rayuwa ta.

*Mlm* *Dahiru* *Ibrahim* *mar* *mara*

*Amina* *Yusuf* *(Aunty Amina)
Allah ka sasu cikin Aljanna madaukakiya πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™





1⃣9⃣




* Jibeki don Allah .kina zaune namiji zai hargitsa mini kwakwalwa

Dik cikinmu ba Wanda mijinta ya kama kafar mijinki a rziki.nesa ba kusa ba .tsakaninsu. Amma kuma dik munfiki kwanciyar hankali

Abin nufi bamu da wata damuwa tsakaninmu da mazajanmu .sai yanda mukace suyi zasuyi .(wa'iya zu billah)

Don haka kamar yanda na fada miki. Lokaci yayi da zaki tashi ki nemi kanmijinki
Inba hakaba wlh kina gani zaicemiki zai kara kaure. Kishiyoyu suyita zuwa suna cika miki gida da yaya

Shi Kenan ke kintashi a banza a iska.
Don haka ki saki jiki ki kawo kudi . kinadaga gida aiki zai ta zuwarmiki .zakiga canji .wlh sai abinda kikace. Shi zaiyi. Ke ko yanda zai tafiyar da dukiyarsa .saiya tanbayeki yanda zaiyi.

Tofa ziga ta gama shigar hjy Amina .jiki na mazari tashiga bedroom dinta ta debo dami damin kudi Wanda batasan adadinsuba ta baiwa hjy maryam tana fadin kawata ayi dik abinda ya dace

Aha itakuwa hjy maryam aiki yasamu bata bata lokaciba ta mike sai hanyar gidan bokansu cike da murnarta .na tayi nasarar dora kawarta a hanyar malamai
(Allah ka rabamu da mugun aboki.πŸ™)

Sunkai tsawon wata biyu suna tafka asiri ba dare ba rana kudi .hjy Amina take durawa boka kafin asirinnan yafara cin jikin Alh don shima ba azaune yakeba yana tsare jikinsa


To amma dake su tsafinnasu harda kauce hanya .kuma sunyi amfani da kasurguman Aljanu sai gashi sun fara cin riba .
Kuma cin ribarsu ya kara samin karfi ne .ta sanadiyar sanyi da yayi .da adduoinsa na azkar . wannan yasa suka kara samun dama akansa.

( _Sabida_haka yan uwa mu kula da addua.)

Sai gashi yanzu Alh.sai abinda hjy tace .yakeyi ko fita zaiyi saiya fada mata inda zashi .inta yarda yaje intace a a kuwa dik himmanynci fitar ya fasa ta Kenan.

Zuwa yanzu ko saiya kwana biyu bai nemi Inda baby take ba.

Dik wata nutsuwarsa an kau da ita
Yazama susu su.
Su jamaa dik tunaninsu har haryanzu zafin mutuwa ce bata gama sakinsaba

Haka aka dau watanni .duniya ta samu ga hjy Amina.

Zuwa lokacinkuwa baby tazama abin tausayi ta rasa kulawar uwa da uba

Sai iya Abu mace me rike amana ita take mata komai .dikda yanzu ba wani abinci arziki ake basu agidnba .don haka dik sun hadu sun rame .saidai iya taje gun masu aiki insun dafa .abincinsu si Dan kara musu.

Shidai dama Alh.bashida obokin shawara in matsalarshi ma ta ciyoshi Mlm Khalil yake zuwarwa da ita . to Mlm dinma .anshiga tsakaninsu .kwata kwata baya son zuwa gunsa


🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


BABY KHAUSAR

NA

LAYUZA KABIR ADAM



MY AFREEN ALLAH YA BAKI LFY .YA KIYAYE GABA.πŸ™


2⃣0⃣




Bilal abin da ke faruwa agidansu yana damunsa ganin yanda kanwarsa ta zama kamar wata yar masu aiki agidan ko shi yanzu in yana tare da ita momyn nasa tsawa take sakarmishi .
indai yasamu damar sakewa da ita to a skl ne .amma agida tsakaninshi da ita sai ido . wani lokacin haka zai shiga dakinsa yaita kuka dik rayuwar gidan tamai zafi shima dik ya rame

To ganin irin damuwar da Bilal ke ciki yasa su hjy shawarar. Shima akai sunan shi gaban boka akan shima acire mai kaunar baby arnsa asanya mai tsanarta .

To haka kuwa akai lokaci guda Bilal yaji Sam baya son yiwa khausar magana .ko kallon ta bai kaunaryi .
Inma ta isheshi da magana saiya daka mata tsawa .tun bata damuwa anjima haka zata koma yakuma hantararta .
Daga karshe kuwa saita daina .zuwa kusa dashi.saidai taita kuka tana kallonshi .

Ana tsaka da haka .labari yazowa iya Abu daga kauyansu .babban danta .ba lafiya don haka dole tafiya ta kamata zuwa garinnasu.
Bata soba haka ta tafi tabar baby tanata rizgar kuka .shikenan yanzu zata kara shiga kunci .
Da rarrashi ta tafi tana fadin ina zuwa inna duba jijinnasa zan dawo baby .ko kwana goma bazanba insha Allah.

Tun tafiyar iya Abu komai yakara tsinkewa ya lalace .rayuwa ta kara kunci ga khausar . ko abincin arziki bata samu .arana sau biyu take ci. Abata in zata tafi school to sai kuma da magriba shikenan


Tafi tafi iya ta dawo shiru har tsawon wata guda .sai daga baya mummunan labari ya kara zuwar musu ai ahanyar dawowarta .ta baro garinsu kadan sukai hadari .ko shurawa bataiba .
Nanfa khausar ta kara shiga wata rayuwa .

Har amakaranta kowa ya fahimci yanzu Bilal baya shiri da kanwar tasa .don ko break aka fito .saidai taita zama a aji tana kuka to ko abinci yanzu baa .bata tatafi dashi .balle yan Kayan kwadayi da ake zubawa yara a jaka sutafi dashi kowa haka zai fice abarta ita kadai

Wata Aisha M shareef ce a ajinsu wadda zasuyi saanni. Ce bata iya cin abincinta iya kadai . haka zata sata agaba taita .cewa baby khausar muci abincina tare .to dake tana tare da yunwa haka zata sa hannu suci kuma su shanye Kayan kwalamar tare.
Don haka bata samin wata walwala a duniya inba taje mkrnta ba.

Labari Aisha m shareef ta bawa mom dinta kawarta mamanta ta rasu bata zuwa da abinci don haka ake kara mata abinci Wanda zai rinka isarsu ci su biyu.

A wannan matsin rayuwar lokaci yaita tafiya .wata ranar asabar baby yunwa ta isheta hjy tana parlour a up stairs
Ta lallaba ta shiga kitchen. Abincin dake cikin food flask ta bude tasa spoon ta fara ci .aikuwa dika lomarta uku hjy ta shigo kitchen din salati sosai tasa kamar wadda taga miciji . au khausar tsiyar taki har ta kai ki shiga kitchen kinamin satar abinci ni zakiyiwa sata .to wlh yau sai na lahira yafiki jin dadi .

Wata danka datakai mata tazuba mata mari ta gwara kanta da bango da kafa ta wullota waje aikuwa ta bugu da jikin kujerar dining ai kuwa nan kanta ya gashe jini kamar me haka yaita zuba ya wanke mata fuska amma sabida rashin imani haka taita jibgarta kamar ta samu wata katuwar budurwa.

Tun tana kuka da hawaye harta koma ajiyar zuciya ahaka numfashinta ya dauke ta suma .
Sarai tasan suuma tai amma saita koma kan kujera tazauna ta kunna TV abinta .tsawon 30mint taga Yarinya. Bata motsaba .sai kuma taji fargaba don haka ta kira wayar dakin masu aiki tace Barira tazo .


Tana shigowa tace jeki duba yarinyar can kiga.

Barira ta tsorata da ganin yanda jini ya wanke fuskarta kuma ya daskare

Agigice taje ta debo ruwa ta watsamata afuska tsawon minti biyu ta farfado .kaita bakin fanfo tayi ta wanke mata fuska .
Sannan sika dawo parlour. Tace hajiya .ko zaa kaita asibiti ai mata treatment.
Ke ba wani asibiti da zaa kaita sami kyalle ki daura mata agun jinin ya tsaya shikenan.
Don ubanta ai ita tajawa kanta barauniyar banza da wofi.
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸



BABY KHAUSAR

NA
LAYUZA KABIR ADAM



2⃣1⃣


Sabida rashin gata haka ciwonnan ya gama yayinsa ya warke ba wata kulawa . har wani wari wari yakeyi to ciwo a cikin gashi .shi kanshi gashin yafi wata bakwai ba kitso ba wankewa dik ya daddan kare .ba kyan kalla.
Wayyo Allah ka rabamu da maraici a shekarun kuruciya.

To Yarinya fa ta zama ba kyan kalla .dik wannan farin da kyan dik babu .bazaka kalleta .kaga abin ban shaawa tare da itaba .ba wanka wankima saidai intaga me wankin yazo yanayi ta dibi kayanta .takai mishi .ya wanke mata .
Ga Dan karan duka da takesha gun hjy .dik kankantar Abu in tayi a duka yake .wani lokacin ko hada ido sukai .saita bugeta .

Haka Bilal wata rana yana cin abinci .
Tazo gefan kujerar da yake . ta rakube tana jiran yagama ci ta karashe sauran .
Aikuwa yana cikin ci yaji motsi a gefansa .juyowar da zaiyi yaganta .
Wani wawan mari yasakar mata
Yana fadin ni zaki zo kisa agaba ina cin abinci .don uwarki da wannan war in kan naki da warin jikinki .
Banza bakinki .kamar Masai .matsa anan ko na karyaki na huta shegiya kazama .

Jiki na bari tashige dakinta .tana kuka kamar ranta zai fita .
Yarinya karama .amma matsalar manya akanta .

Mlm Khalil .ganin tsawon lokaci Alh bai nemeshiba. Yai tunanin aiki ne yamai yawa don yasan inda matsala ai da gudu yake zuwanmishi
Don haka shima ya kaleshi. Ana haka mahaifinshi ya kwanta ciwo acan garinsu don haka ba shiri suka hada kayansu sukai garinsu can barno .


Ahaka rayuwa taci gaba da tafiya .yayinda baby khausar ta kasance kullum cikin rashin gata da maraici.ga kuntatawar matar uba .data Dan uwa .ba inda takejin dadi sai a school. Gun kawarta Aisha.

Tsautsayi yasa wata rana .hjy Amina tai bakuwa .tazo da yarta karama .ba daki baby itama ta rama .
Yarinyar tasa kuka . me akai miki tace baby ce ta daketa .
Hhhhmmmn ummmmm .wata shawara ce tazo zuciyar hjy .aikuwa nan da nan .ta kira barira .tace maza ki doramin ruwan zafi .kisa barkono da citta suji sosai
Aikuwa baa jimaba .ta dawo tace .ruwan ya tafasa .
Jeki bangaranku ki kawomin buta

Ruwan tajuye a buta ta ajiye
Bayan bakuwar ta tafi .ana kiran sallar magriba zuwa lokacin ruwan ya salance .
Ta kwadawa baby kira jiki na rawa tazo
Yawwa maza dauki wannan butar kije kiyi tsarki kiyi alwala ankira sallah
Daukan butqn tayi tashiga toilet din dakinta baafi minti biyu ta kwala ihu .wayyo Allah na zafi yaji momy kizo ki taimakeni .wlh zafi yaji
Da dariyarta tashiga toilet din .ke dalla yiwa mutane shiru ubanme akaimiki.zaki cika mana gida da ihu.

Momy ki taimake ni yajine acikin wannan ruwan danai tsarki. Wlh yaji nakeji .wayyo momy zan mutu

Yawwa ai nafiso ki mutum in huta sabida ganinki bakantamin rai yake

Dik me imani ya dubi yarinyarnan yasan tanajin azaba a lokacin kuma saiya tausaya mata .
Amma dake zuciyar ta kekashe ko agefan zaninta bata damuba haka .taita dariya .ta fice ta Barta a toilet din
Dabara Allah ya sako mata da sauri ta kunna fanfon ruwan sanyi ta tara .taita tsarki dashi .
Ba lefi ta danji dama dama .haka .ta fito . tanata matse kafa .
Gadonta ta hau taci gaba da kuka ahaka barci ya dauketa .



🌸🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


BABY KHAUSAR


NA

LAYUZA KABIR ADAM



DEDICATED. TO
HUBBY NASS❀



2⃣2⃣

*Da wata irin matsananciyar yunwa ta farka kasancewar .jiya ko na magibar da ake sammata. Bata samu Ciba baccin. Wahala ya dauketa .

Jitai yunwar na shirin kaita barzaku .don haka ta fito .zuwa dining. Ai kuwa cikin saa .ta tararda hadadddan dilutions. A flate. Sai tiriri yake harda spoon aciki

Hhhmmmm abinka da yarinta bata tsaya tunanin komaiba tasa. Hannu ta fara. Biga. Loma. Ci take hannu baka hannu kwarya. Ai. Kuwa ta doka saa harta. Gama ci tayi kat ta bude standing fridge dake .dining area din ta dauko bottle na ruwa me sanyi. Ta. Kwankwada
Ahhh tai ajiyar zuciya .rabon data ci abinci me dadi irin wannan ta koshi harta. Manta .

Taku taji. Daf daf ana saukowa daga stairs. Ai kuwa da sauri ta juya
Bilal ne yake saukowa yana dannan wayarsa
Kam ta Kame jikinta ya hau Mazari ganin yana tun karota da mamaki ya tsaya yana kallonta ganin flate din abincinsa dayayi ba komai shi daya tafi yabarshi a rufe amma gashi bude ba komai

Keee.
ya daka mata tsawa . don uwarki ina abincin dake aje anan

Cikin muryan kuka ta fara fadin don Allah. Yaya kayi hakuri don Allah karka dakeni please my broth

Keee rufemin baki ko na karyaki don kan babarki .
Kinsan ina zanje da safannan nasa akamin girki. Shine na ajiye inje. Indauko. Phone dina kikasa agaba kika cinye
Wai ke gaki mayya ko .to yanzu zanyi maganinki

Kai mata shaka yayi ya rike. Mata makogaro waishi dole saita amayo da abincin
Amma dake Allah Allah ne .
Ko kadan abincin bai fitoba

Ganin yayi iya yinsa abincin ya fito yaki haushi ya kamashi ya kifa mata mari ta kife zuwa kasa
Bol yashiga yi da ita yana takata

Ahaka. Dad ya sakko zai fita ya tararda wannan aikin .amma kallo daya yai musu ya kauda kai

Harya. Kai kofar fita a parlour n ya juyo yace. Bilal zan wuce. Baka bukatar wani Abu .
Kasan nacema zankai wata biyu a can ko

Bani da bukatar wani Abu inma akwai wani Abun .zan sanar dakai ta waya
Dad Allah ya kaika lfy
Ameen my son bye

Wayyo Allah Dad dina ina zaka tafi .don Allah ka dawo ka rika min wanka kamar da karika bani abinci abaki ka rika fita dani .yawo a mota . Dad ka dawo ka rinka sona kamar yanda kake sona da
Kuka ta kara saki me karfi. 😭😭😭 ganin yasa kai yafice .

Yanajin kuna matuka azuciyarsa .dik sanda yaga tana cikin wani yanayi ko kuma yaga hjy ko Bilal tana dukanta tana kuka
saiyaji shima kamar yayi kukan

Amma kuma ko kusa ko alama bazai iya yin komaiba
Yanzunma jin zuciyarsa na kuna yasa ya fice da sauri.

Kee rufe wa mutane baki ubanme akai miki da har zaki rikaiwa mutane wannan ihun cewar hjy data sauko kasa yanzu

Momy kinsan kuwa me wannan tunkiyar yarinyar nan tamin
Wai abincina ta cinyemin daga na je dauko phone dina shine ta cinyemin

Kan ubancan .kaikuma shine ka tsaya kana kallon ta bazaka dau mataki ba

To ai momy kinsan sauri nakeyi yanzu inna tsaya hukuntata bata wa kaina lokaci zanyi

To bari inbaka shawara maza jeka sata a zoo ka kulleta inka dawo saika San me zaka mata

Good good momy na kin kawo shawara me kyau kuma kinsan banzar tsoron .monkey take . don haka a dakinsa zan sakata .

Jin abinda suke fadi yasata sakin wata mahaukaciyar kara tana girgiza kai .

A a momy karki bari ya kaini zoo banso
Momy help me momy ki ji tausayina don Allah

Janta yai kamar jaka tana ihu tana birgima
.
Dik wannan Nisan dake tsakanin su da zoo din. Akasa yajata .

Yana zuwa ya umarci me kula da wajan daya bude mai
. tunkan su karasa dakin monkey din ta daina kukan ta kulle idonta matuka numfashinta yazo wuya don tsoro da razani
Cillata yai cikin dakin monkey din .ya rufe .
Sannan ya kalli me kula da gun yace ban yarda afito da itaba harsai na dawo .
Jinjina kai yai yace angama uban gidana


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
[10/2, 11:42 PM] Spouse 2: 🍑🍑🍑🍑🍑
🍑🍑🍑🍑🍑🍑
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


BABY KHAUSAR

NA

LAYUZA KABIR ADAM



DEDICATED TO πŸ‘‡

All students 2013 /.Sa'adatu rimi college of education kano



2⃣3⃣



Tunda ya wullata dakin birin nan ya juya ta sume


Shidai inuwa bin bayan Bilal yai suka fita
Yana tsaye daga can nesa ya hango direba yaja Bilal a mota sun fice .

Ajiyar zuciya yasaki da gudu ya koma cikin zoo din ya shiga dakin birin
Abinda yake tinani shi yagani
Wato ta suma . da sauri ya daukota ya fito da ita karkashin bishiya ya ajiyeta ya debo ruwa
Yana kwara mata taja numfashi da kuka ta tashi da sauri ya riketa
Yana fadin yi hakuri Baby kinji yanzu ba a dakin biri kikeba bude idonki kiga

A a nidai bazan budeba don

Please Login or Register in order to submit comment