You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda zai tsaya miki."?

Cikin Izzah! Nace."Eh Ina dashi ba kowa bane face Uncle Nura." Shahid ransa ya 'baci kishi ya rufe masa ido yace."Nasan zai tsaya miki kiyi karatu tunda shine Ubangidanki ai ina da labarin duk irin hidimar da yake muku to ina rokon Allah yasa karatu kawai zai tsaya miki kada yace zai aure ki."

Naji kamar ya soka min wuka a makoshi ido jawur nace."To idan yazo zai aure ni don Allah ka hana aikin banza kawai."

Ya fusata mutuka yace."Ni kike zagi Surayya ashe dama baki da kunya To wallahi sai na rama abinda kikayi min kuma sai kun biya ni hidimar da nayi muku.

Nace."Shahid duk abunda kayi mana babu wanda ya saka kai kayi niyya don haka babu wani abu da zamu biya." Girgiza kai yayi yana hura hanci ya dauko wayarsa daga aljihu yana danne-danne.................Malam ne ya karaso gurin akan kekensa ganinsu a tsaye cikin 'bacin rai yasa yace."Ina fata dai lafiya."? Hawayen fuskata nagoge na shige gida ba tare da nace komai ba. Ya kalli Shahid din da fadin." Me yake faruwa ne."? Shahid na hura hanci yace." Malam ina ganin girma da mutuncin ka amma yarinyar nan tana so ta janyo maka bacin rai." Malam yace."Kayi hakuri kayi min bayanin abinda yake faruwa.

Shahid ya sauke ajiyar zuciya yace............Tsaf ya kwashe duk abinda yake faruwa ya fada masa. Malam ransa ya b'aci yace."Kayi hakuri kaji ko Surayya bata isa ta mayar dani 'karamin mutum ba kamar yanda mukayi magana da ita shekara daya data wuce ta tabbatar min da cewa kai ta za'ba a matsayin abokin rayuwarta to alkawari yana nan babu gudu babu ja da baya kaje ka cigaba da shirye-shirye." Shahid cike da farin yace."Nagode sosai Malamai Allah ya kara girma.'' Malam ya amsa da ameeen ameen ya tura kekensa domin shiga cikin gida.....Shahid kuwa cike da karsashi da kuzari ya bar gurun.


Ban ta'ba ganin bacin ran Malam ba sai yau yana shigowa gidan ya rufe ni da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita. Ya cigaba da cewa"To baki isa ki mayar dani k'aramin mutum ba wannan yaro ke kika amince da auransa muka zauna da mahaifinsa mukayi magana sai yanzu kuma da aski yazo gaban goshi sannan zaki bijire to baki isa ba wannan aure sai an anyi shi."

Cikin kuka nace."Ni wallahi bashi nake so ba Malam kada kayi min auran dole." Innah ta bude baki tana kallona tace."Yanzu ke baki ji kunyar fadar wannan maganar ba."?

Hanci na shaqa cikin dashewar murya nace."Innah ai kema kin san gaskiya a cikin al'amarin nan ina Shahid yaga sana'ar da zai iya aurena bashi da aiki sai buge-buge yak........Gwa'be min baki tayi tace."Ashe kin san bashi da sana'a amma idan ya kawo miki abin duniya kike kar'ba kina washe baki a gidan uban wa yake samo kudin."

Malam yace."Duk abinda zakiyi sai dai kiyi ba zaki mayar dani k'aramin mutum ba."

Da sauri na mike na shige daki na fad'a saman gado ina kuka Wallahi ba zan ta'ba amincewa da wannan al'amarin ba ta yaya ma za'ayi nayi rayuwar aure da wani namiji ba Uncle ba na riga na sanyawa raina auransa insha Allahu sai Allah ya cika min burina.


Washe gari a makaranta na zayyanewa Samira duk abinda yake faruwa jikinta yayi sanyi tace."Surayya da zakiyi hakuri ki auri Shahid din watakila shine alkairi a tare dake tunda dai kinga duk wannan abun da kike akan Uncle be san ki nayi ba."

Cikin 'bacin rai nace."Samira kada ki 'bata min rai don Allah wannan wace irin banzar magana ce nifa na fad'a miki koda Allah bai bani nasarar auran Uncle ba to wallahi ba zan auri Shahid ba saboda haka kima daina wannan maganar."

Tace."To shikkenan Allah ya za'ba miki abinda yafi alkairi." Na amsa da ameeen da fadin." Ina fatan kinzo da wayar ki."

Tace."Nazo da ita amma ki bari a fita break sai mu samu gurin da babu kowa muyi abinda za muyi." Nace."Ni don Allah bani wayar na shiga karkashin tevur nayi abinda zanyi."

Tace."Surayya kin san yanzu Malamar English zata shigo kuma kin san halinta bata da mutunci."

Tsaki naja da fadin." Kinga Samira idan zaki bani waya ki bani wallahi kwana biyu da ban ji muryarsa ba duk wani iri nake ji."

Girgiza kai kurrum tayi ta dauko wayar a 'boye ta bani ni kuma na fakaici idon 'yan ajin da sauri na shiga karkashin tevur............Number shi nasa ina kokarin kira Malama Sa'adiyya ta shigo a maimakon na fito sai na cigaba da abin da nake.............Muryarsa ce ta doki kunnune yana sallama had'e da kiran sunana."

Shuru nayi ina lumshe ido wani irin a zababben feelings ne yake taso min........"Assalamu alaikum Surayya ko ba da ita nake magana ba."? A firgice! na d'ago kaina sai kawai na hangi wucewarsa ta window sai da wayar ta kusa fad'uwa daga hannuna saboda tsabar razana! Kafin ma nayi wani yunkuri ya shigo ajin.......Gabadaya kowa yayi tsit! babu mai kwakkwaran motsi. Har yanzu wayar na mak'ale a kunnansa yana magana idonsa tsaye a gurin zaman ta. Ganin babu ita a gurin sai ya gazgata zarginsa. cikin nutsuwa ya cire wayar daga kunnansa ya fara tafiya zuwa gurin......Samira tamkar ta saki fitsari a wando saboda fargaba da tsoro ni kuwa ta tsakankani nake hango zuwan shi sai kawai nayi saurin sa wayar a cikin breziyya ta nayi kwance a 'kasan gurin ina rike ciki had'e da birgima a gurin..........


*A taimaka da Shearing👏🏾*



*MAR'ATUS-SALIHA*
_(Itace Cikakkiyar Mace)_

*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu👫 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*
1- Maganin Sanyin mara
2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa
4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba
5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa
6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa
7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)
8-Maganin Basir mai tsiro
9-Maganin Basir mai kulle ciki
10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)
*11- Maganin Karin Ni'ima
12- Maganin K'iba mai kyau
13- Maganin Cikar Nono (Breast)
14- Maganin Hips
15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!
16- Maganin Matsi mai kyau
17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)
19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba


*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*
*07084653262*
*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*
Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp




_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[7/31, 11:08 AM] Bintu🍒: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

*Last Free Pege*
*29&30*
Sosai na dinga birgima a gurin ina rike da cikina tare da kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! Yanda nake zabga gumi zaku dauka da gaske nake nan kuwa tsabar tashin hankali ne ya sanya gumi ke yankowa daga sassan jikina.......Muryarsa naji yana magana da Samira.

Cikin inda-inda tace."Bata da lafiya tun dazu ta shiga 'kasan tevur wai cikinta ne yake ciwo."

Ajin yayi shuru kowa ya shiga hankalinsa.......Sunana ya kira da fadin.'' Na fito daga gurin. Cikin kuka nace."Uncle ba zan iya ba." Ya kalli Samira babu walwala a fuskarsa yace."Ki taimaka mata ku same ni a ofis." Yana gama maganarsa ya bar gurin. kafin ya fita daga ajin sai da ya tsaya sukayi magana da Malama Sa'adiyya sannan ya fita.

Cikin tsawa tace."Surayya Malam Habu ki fito kije ki kar'bi magani." Da sauri na fito daga kasan tevur din aikuwa ido yayi caaa! a kaina...Gumi kawai nake sharewa ga jikina yayi fururu da 'kura. Ya mutsa fuska nayi na rike hannun Samira muka mike a tare.....Har muka fita daga ajin basu daina bin mu da kallo ba.

Jiki a masifar sanyaye nace."Samira ji nake a jikina kamar 'karya ta ta kare." Tace."Saboda me kike ce haka."? Cikin fargaba nace."Guy nan ya gane nice me kiransa dayi masa text." Tace."To menene abin fargaba dama haka muke so.'' Cikin nauyin baki nace."Wallahi Samira tsoro nake kada yaci mutunci na." Tace."Dallah ki kwantar da hankalinki duk ta inda ya bullo ki kare kanki ki nuna 'karya yake."
Kallonta nayi ina mamakin maganarta. Tace."Eh haka zakiyi sai ki kwaci kanki." Girgiza kaina kawai nayi ina cigaba da fargabar abinda zai biyo baya.


Tamkar wani soja haka muka sameshi a tsaye a tsakiyar ofis din ya zuba hannuwansa duka a cikin trosser din dake cikinsa........Muna hada ido naji kamar an buga min ta'barya a gwiwa kafafuna suka fara rawa kokarin zama nake a kasan ofis din ya buga min tsawa da fadin." Tashi ki tsaya da kafafunki." Tsayuwa na gyara ina kallonsa Yasha wani irin kunu yana watsa mana wani irin kallo!

Jin ya kira sunana yasa da sauri na kalleshi yace." Fito min da wayar nan yau Allah ya tona miki asiri." Cikin inda-inda nace."Uncle wace irin waya kuma."?

Ido ya tsira min! yace."Tambayata kike bayan naga komai da idanuwana." Kuka nasa murya na rawa nace."Uncle me ka gani ni wallahi bani da waya cikina ne yake ciwo shine na shiga kasan tevur na kwanta.

Ya kalli Samira da fad'in." Ke bana san gardama ki fada min gaskiya wayar kice ko kuma wayar ta."

Da sauri tace."Wayar ta ce Uncle." A gigice na kalleta bakina na rawa kafin ma nayi magana ya bata umarnin tafiya. Samira da sauri ta fice daga ofis din.......Key yasa a jikin kofar ya durfafo inda nake tsaye Gabana ya dinga duka yana daka! Ido jajawur yace." Yau Allah ya bayyana min *S-R-Y* Mylove d'ina." Naji cikina ya wani murd'a! sunkuyar da kaina nayi ina addua a zuciyata....Daf dani ya tsaya har ina jin hucin numfashinsa Yace." Ni kike so ko."? Na kalleshi hawaye na zubo min..."Uncle wace irin magan......Kafin na 'karasa ya buge min baki da bayan hannunsa. Na fashe da kuka ina kallonsa. A zafafe! Yace."Sai naci Ubanki yau tunda kin zama 'Yar iska kina bibiyar maza da text din soyayya."

Cikin kokarin ceton kaina nace."Uncle kayi binkice sosai wallahi bani bace watakila suna ne yazo iri daya amma ni yaushe zan ce ina sonka ai na san kai ba sa'a na bane."

Lumshe idonsa yayi ya bude su a kaina naji tsigar jikina ta tashi yanda yake kallona yana lumshe ido yasa jikina ya shiga karkarwa..............A hankali yace."Kin ce kullum kina mafarki gamu a bargo daya ina biya miki bukata ko." ?

A tsaroce nace." Wa...Wallahi Allah na rants..........Hannu yasa ya datse min baki sai na hau kifta ido irin na marasa gaskiya. Ya tsira min lumsassun idanuwansa da suke masifar kassara ni........" Idan kika karya ta maganata sai na zane miki jiki mara kunya wacce bata jin kunyar rantsuwa da Allah."

Jikina yayi bala'in sanyi dama sai da naji a jikina yau karyata ta kare 'karshen Tika tiki tik hausawa suka ce karya fure take bata 'ya'ya..................Babu zato naji yana magana." Kullum kina mafarki na a cikin baccin ki kina ciwon ciki da ciwon mara saboda feelings to gani yau a gabanki sai ki biya bukatarki."


Na rasa abinda zance sai zazzare ido nake tamkar 'bera a ruwan zafi a rayuwata ba zan ta'ba mancewa da wannan ranar ba."

Hannunsa yasa a 'kuguna ya matseni sosai a jikinsa.Fashewa nayi da kuka ina bashi hakuri.......Naji hucin maganarshi a kusa da kunnena yana fadin." Yanzu Wace kallar soyayya zamuyi."?

Ji nayi tamkar na kurma ihu!!! jikina ya dinga rawa ina tureshi yana sake matseni a jikinsa hannuwansa akan mazaunaina.

"Wayyo na shiga uk.......Da sauri ya sake ni ya rufe min baki da hannunsa yana harara ta nayi saurin zubewa a gurin ina bashi hakuri ya zuba hannuwansa a aljihu yana kallona Yace." Fito min da wayar nan na jita a jikin ki." Da sauri nasa hannu cikin rigata na d'auko na mi'ka masa. Ya kar'ba yana watsa min harara yace." Da kuma kika karya ta."

Hanci naja cikin dashewar murya nace."Wallahi ba tawa bace ka duba da kyau wayar Samira ce kuma tare da ita muke shirya komai."

Ba tare da yace uffan ba ya bar ni a gurin saman kujera ya zauna ya bude wayar yana dubawa...........Ya kalle ni babu sukuni a tare dashi yace." Tunda aure kike so Sha'awa ta dame ki zan samu Malam mu tattauna dashi a samu wani a bashi domun kada ki dauko abin kunya."


Gabana ya fadi! Da sauri nace."Uncle don Allah kada kayi min haka wallahi ba zan iya rayuwar aure da kowa ba sai da mutum d'aya."

Ido ya tsira min na minti biyu kafin Yace." Waye." ? Sunkuyar da kaina nayi a sanyaye nace."Wani ne." Yace." Yarinya idan ni ne ma kina wahalar da kanki dan bana da ra'ayin auran mace me bleaching. "

Kallonsa nayi ya gyad'a min kai domin so ya tabbatar min da maganarsa.......Cikin jin haushi nace."Uncle nifa ba kai nake so ba wani ne Kamili mai hankali da nutsuwa kuma mai tausayi.'' Yace."Koma wanene Ni zan samu malam da maganar ayi miki aure dashi."

Sai naji wani irin farin ciki a lullu'be ni. Na dinga godewa Allah a cikin zuciyata.....Ya kalle ni da fadin." Ki tashi kije magana ta 'kare kina Candy za'ai miki aure da wanda kike so amma ki sani Wutsiyar rakumi tayi nesa da 'kasa."


Cikin farin ciki na fito daga ofis din ina jin wani irin nishad'i a tare dani kai amma gaskiya banyi tsammanin al'amarin zai zo sauki irin haka ba shikkenan yanzu Uncle ya gane abinda nake nufi a kansa ya fahimci cewa ina sonsa zai je ya samu Malam su tattauna maganar auranmu lallai babu abunda yafi karfin Ubangiji Allah ya amsa min addua cikin sauki.

Ana fita break naja Samira muka samu guri muka zauna na warware mata duk yanda mukayi dashi....A sanyaye tace."Surayya da ina murna amma tunda naji wannan kalmar sai jikina yayi sanyi *Wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa* shin kin san meye manufar wannan maganar."? Gabana ne ya fad'i! Nace." Ban sani ba Samira ni dai a karshen maganarsa yace amma na san da cewa Wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa.

Samira tayi murmushin takaici tace." Yana nufin Yafi karfin ya aure ki kuma Wutsiyarsa tayi nesa dake Ma'ana ke baki kai matsayin da zai had'a makwanci dake ba.

Na dinga kallonta ina mamakin maganar...Tace." Ni dai wallahi a iya fahimtata haka na fahimci maganarsa."

A raunane nace." To Samira me na rasa na matantaka a jikina meye bani dashi da har zai fadi wannan maganar." Tace."Surayya kina da mantuwa ai dama tun kafin tafiya tayi nisa sai da na fada miki cewa Guy nan ba tsaranki bane amma kika nace to gashi nan yanzu ya fada miki da bakinsa sai ki shiga hankalinki.

Wasu zafafan hawaye suka kwace min nace."Samira yanzu abinda yake nufi kenan."? Tace."Wallahi kuwa ai ya gane kina sonsa kece me kiransa dayi masa text shiyasa ya nuna miki yafi karfin ki kije ki nemi daidai dake."

Hawaye na goge nace."Samira mutukar Uncle be aure ni ba to rayuwata tana cikin garari wallahi ni kadai nasan irin masifar son da nake masa."

Tace."Kin ga Surayya ni wannan Game din ya ishe ni haka gwara muyi abunda zai yuwu mutukar zan baki shawara ki dauka to ki cire Guy nan daga ranka ki fuskanci Me sonki tsakani da Allah."

Girgiza mata kai nayi nace."Samira ba zan iya ba wallahi.'' Taja tsaki da fadin." Shikkenan ai sai kije kiyi kece wahalalliya." Tana gama maganarta ta bar ni gurin cikin halin damuwa.


Koda muka tashi daga makaranrar kowa tafiyarsa daban saboda 'bacin rai! A galabaice na isa gida na zube kan tabarma jikina na wani irin rawa.


Innah ta fito daga kicin da kwando a hannunta a tsorace ta tsaya tana kallona dan bata san na shigo gidan ba Tace." Surayya wace irin tsiya ce wannan kin shigo gida babu sallama sai kace gidan kafurai."

Cikin rawar murya nace."Innah Nayi sallama ba kiji ba kina kicin zazzabi ne a jikina." Tace."Allah ya sawake sai ki tashi kici abinci kisha magani kafin yamma tayi kije Chamis dama ai yanzu lokacin Maleria ne abinda ake ta fama dashi kenan." Lumshe idona nayi ina jin wani irin d'aci a bakina.


Sai da Malam ya dawo sannan muka je Chamis da ita A ka bani magani da allura ta kwana uku sosai zazzabin yayi karfi a jikina a galabaice muka dawo gida naci abinci da kyar nasha magani Na kwanta tana matsa min ruwa a jikina. Malam yace." Idan zazzabin be sauka ba gobe da wuri sai muje asibitin Murtala likita ya duba ni." Innah tace."Hakan shine yafi amfani.


Yaro ne yayi sallama da fadin." Wai Uncle Nuraddin yana sallama da Malam." Da sauri na bude idona na fara kokarin tashi zaune. Innah tace."Menene ko jikin ne."? Girgiza kaina nayi na tsirawa malam ido wanda yake kokarin fita akan kekensa.

Jiki a mace na koma na kwanta ina addua a cikin zuciyata.........Malam ya kai minti ashirin a waje kafin ya dawo gidan na sake mikewa zaune ina kallonsa so nake kawai naji abinda ya shigo dashi.


Ya kalli Innah da fadin." Yaron nan Nura yana da hankali da nutsuwa dan haka babu abinda zai nema a guri na banyi masa ba." Innah tace." Wani abu ne ya faru.''? Yace." Babu abinda ya faru sai alkairi Yazo da maganar auran yarinyar nan Surayya."

Wani irin sanyi ya ziyarci zuciyata Allah kawai nake godewa......Malam ya cigaba da cewa." Ashe yarinyar nan a makaranta babu abinda suke sai shashanci da shirma da bibiyar maza."

Naji gabana ya fadi! da sauri na kalleshi Ya cigaba da cewa." Surayya kin bani kunya kin kuma zubar min da mutunci a gari kin 'bata irin tarbiyar da mukai miki saboda haka za'ayi miki abinda kike so tunda dama akwai maganar Shahid gobe insha Allahu zan kar'bi sadakin auranki a daura miki auran a huta makaranta dama saura abinda ya rage ki kammala wannan shine hukuncin da Nuraddin ya yanke nima kuma na yanke irinsa gobe zan kar'bi sadakin auranki daga hannun Shahid Ranar juma'a idan an sauko daga massalaci a dauran.

Wani irin ihu! na kurma! na fad'i a gurin ina birgima da kiran Innalillahi wa'ina ilahi raji'un!!!! Innah ranta ya 'baci! ta gaura min mari a zafafe tace." Surayya kina so ki tona masa asiri a unguwa ko? me akayi miki kike wannan ihun."?

"Wallahi Innah bana son Shahid kada kuyi min haka idan kuka daura min aure dashi zan lalace mutuwa zanyi." Innah tace." Me yasa tun farko kika amince dashi? me yasa kika yaudari kanki bakya sonsa me yasa kike dinga cin kud'insa? dama irin wannan ranar nake gudu sabida na san halin ki saboda haka ni ba zaki janyo min zagi da cin mutuncin jama'ar unguwa ba Uwa uba Mariya matar da bata da hakuri makota da sauran 'yan unguwa sun san irin hidimar da yaron nan yake miki rana tsaka ki bijiro da wata magana ai dole a zage mu don haka wannan aure dole sai anyi tunda ke kika amince."

A gigice! na mike jikina na wani irin rawa na janyo hijabi na dake kan igiya nasa babu takalmi a kafata na kama hanyar fita.......Malam ya kwala min kira da fadin." Ina zakije da wannan daran."? Ko sauraransa ban yi ba Innah ta mike da azama! da gudu na karasa ficewa daga gidan.........Kamar wata sabuwar mahaukaciya haka na zama na kama hanya ina tafiya ban san inda nake jefa kafata ba.........Tsintar kaina kawai nayi a gaban motarsa yana kokarin shiga da ita cikin gidan nayi tsaye a gurin hasken fitilar motar na haske min idanuwa na da sukayi jajawur saboda azabar kuka......Cikin nutsuwa ya kashe motar ya fito yana bina da wani irin kallo kafin ya tako ya karaso inda nake tsaye...

*To to to*😃
_Laifin dadi 'karewa anan karshen free pege ya kare ko ya zata kasance anan gaba? Wai shin yaya take ne? Shin Surayya tana samun nasarar auran Uncle ko kuwa? idan ta aure shi me zai biyo baya? wace irin rayuwa za suyi Uncle dai ba tsaranta bane tunda ya fad'a mata cewa *Wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa* gata ita kuma jarabbiya😂 To Wace irin rayuwa za suyi? Ya makomar Shahid zata kasance? Shin wace badakala ce zata faru anan gaba.....Me zai biyo baya a tsakaninta da Aminiyarta Samira? Shin Hajiya Sabuwa zata amince D'anta ya auri yar talaka muskini? idan hakan ta faru wane irin kalubale Surayya zata fuskanta? Wa!!!!!! Akwai hargitsi! akwai rikita-rikita! akwai zazzafar soyayya akwai zazzafar kiyayya!! akwai! akwai! akwai!!!😃 da yawa sai dai kun kasance da BINTA a cikin littafin zata warware muku yaya abin yake......Kada ka/ki a baki labari._




_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment