You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye da saurin gaske. karfen barandar ya rike yana so ya tantance su waye.

Securities ne suka zo inda muke duk munyi tsuru-tsuru ganin yanda malamai da dalibai suke bin mu da wani irin kallo sai kus-kus ne yake tashi a gurin.

"Kai me yasa zaka karya mana doka ka wani fafaro mashing da alama dai farin shiga ne." Daya daga cikin securities ne yake wannan maganar.

Mansur murya na rawa yace."Ranka ya dade ayi min afuwa ban san dokar makarantar ba domin yau na fara kawo dalibai."

Yace."Okey to anyi maka uzuri amma kada ka kuskura ka qara yi mana goyon biyu doka ce mai karfi daga shugaban makarantar."

Mansur yana kokarin magana ya 'karaso gurin hannunsa goye a bayansa. gabad'aya kowa ya sunkuyar da kansa. Ya kalli Mansur rai a 'bace yace."Kai bakasan sharia ba ko."?

Mansur yayi shuru yace."Kai a matsayin ka na musulmi abinda kayi a yanzu shine daidai ka goya mata biyu a bayan mashing d'inka alhalin duk ba muharaman ka ba.

Mansur a sanyaye yace."Ranka ya dade nayi kuskure a gafarce ni." Tsaki yaja yace."Kada ka sake kwatantawa idan na kara ganin ka shigo min makaranta da goyon biyu sai nayi sharia da kai.'' Da sauri yace." Insha Allah ba zan sake ba.

A wulakance ya kallemu yace." Dube su shashashai kawai marasa sanin ciwon kansu." Gabadaya idanun dalibai da malamai ya dawo kan mu Muka muzanta kwalla ta cika kwarmin idona.

Yace."Duk sanda kuka sake aikata wannan abu sai nayi muku hukunci mai tsaurin gaske." Murya na rawa nace."Uncle kayi hakuri wallah........"Rufe min baki.''? Cikin tsawa ya katse ni.'' sai na sake muzanta tuni hawayen da nake makalewa suka k'wace sharara suka dinga zuba.

Ya kalli gate Man da fadin." Ka rufe kofar nan kada ka sake bari kowa ya shigo." da sauri ya amsa ya bar gurin.....Cikin zafin nama ya juya da fadin." Ku same ni a ofis.'' Simi-simi muka bi bayansa gwiwa a sanyaye.


Yana tafiya muna biye da bayansa yayin da malamai da dalibai ke ratse masa hanya suna gaisheshi......Daf da bakin ofis din ya juyo da sauri muka sunkuyar da kan mu ya kira sunan wata malama da sauri tazo inda yake Ya kalleta da fadin." Wad'annan yaran sabbi ne ki kai su Ss1 amma kada ki had'a su guri daya." Ta amsa da "To ranka ya dade." Ofis din ya shiga ba tare da ya kallemu ba.

Ta kallemu fuska babu walwala tace."Ku biyo bayana." Da sauri muka rufa mata baya giwar mu a sanyaye a gaskiya makarantar tana da tsanani hatta da malamai tsoronsa suke gudun kada suyi laifi.


Ni Class A Samira Class B hakan yayi mana dadi tunda muna kusa da juna......Koda aka fito break guri guda muka samu muna mayar da magana Nace."Samira al'amarin guy nan ya soma bani tsoro ki duba kiga irin rashin mutumcin da yayi mana a gaban jama'a."

Samira ta fashe da dariya da fadin." Ni wallahi Mansur ne ma ya bani dariya ya tsorota sai zare ido yake yana gudun kada a k'wace masa mashing d'insa.

Murmushi nayi nace."Ai Uncle din ne yake da mugun kwarjinin tsiya ni wallahi idan yana kusa dani gwiwata sanyi take."

Samira tace."Na lura Surayya soyayya ce ta kawo ki makarantar nan gashi kuma wallahi da za mu tsaya muyi wa kan mu gata da zamu samu karatu a makarantar sosai."

Murmushin takaici nayi nace."Samira soyayyar Uncle ba zata bari na fahimci komai ba." Tace." To yanzu ke a wane matsayi kike Surayya mutumin nan fa da wuya ya aure ki wahalar da kanki kawai kike."


Murya na rawa nace."Samira ba zan iya hakura da Uncle ba zan kara zage dantse idan rabona ne zan aureshi.

Dariyar takaici tayi tace."Surayya mun rubuta masa wasika sama da biyar babu amsa yanzu wace dubara za'ayi masa kuma." Shuru nayi ina tunani akan al'amarin.

Tace."Idan kuma zaki same shi gaba da gaba ki fada masa manufarki hakan yafi.'' Kallonta nayi ina Mamakin maganarta.

Tace."Wannan shawarar itace daidai.'' Girgiza kai nayi nace."Samira ba zan iya ba wani irin kwarjini yake min za dai mu cigaba da rubuta masa wasika akwai numbers d'inshi a jikin form na makaranta zamu dauka muyi amfani da wayarki gurin tura masa text na soyayya.

Tace."To shikkenan Allah yasa a dace." a sanyaye na amsa da ameee ya Allah. Muna nan a zaune muna saka wasikar jaki aka kad'a kararrawa hakanan muka shiga aji ba tare da mun sayi wani abu mun ci ba.........


*Please a taimaka da Sharing*






_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[7/25, 11:53 AM] Bintu🍒: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*21&22*
Washe gari da wuri muka fito bakin titi domin samun abun hawa jin horn a bayan mu yasa da sauri muka juya motarsa ce ke kokarin fitowa daga ciki sai muka matsa gefe muna rige-rigen gaishe shi. Cikin nutsuwa ya sauke gilashin motar da hannu yayi mana alamar mu shiga......Ba tare da 'bata lokaci ba Samira ta bude motar ta shiga na zauna a kusa da ita yace."Ku rufe motar sosai." Da sauri na rufe motar ina sake gyara zamana....... Sanyi da kamshin motar ne suka saukar min da wata irin kasala na dinga satar kallonshi yana draving cikin nutsuwa komai nasa babu baragada da shirme a cikinsa gefan fuskarsa na tsirawa ido babu ko kiftawa hakika ina mutukar kaunar Namiji mai saje da gemu daidai misali Uncle yana da wani irin saje mai kyau wanda ya qayata masa fuskarsa kalar fatarsa kuwa irin me wahalar samu ce yana da wani irin kyau wanda sai ka tsira masa ido sannan zaka tantance.

Duk irin kallon kurrulan da take masa yana kallonta da gefan idonsa sai al'amarin ya dinga bashi mamaki yana nazari da tunani akan kallon da take masa................Zazzafar ajiyar zuciya na sauke wanda yayi daidai da lokacin da ya kunna karatun al'kur'ani a cikin motar....Zuciyata ta sake narkewa sai kawai naji hawaye na kokarin kufce min hakika Allah ya jarrabe ni da abinda yafi karfina.


Tun daga bakin gate ake gaishe shi har muka shiga cikin makarantar a gurin parking ma Malamai da dalibai masu mu'kami sunyi dafifi a gurin suna jiran ya fito.

Ya kallemu babu walwala a fuskarsa yace."Kuje aji.'' Da sauri na bude motar aikuwa idanu yayi caaaa! a kanmu a take naga sauyin yanayi a fuskokin wasu malamai mata da daliban makaranar...... gurin muka bari da sauri kamar yanda ya umarce mu.


Tunda na zauna kan kujera na kifa kaina kasa ban kara sanin abinda ake gudanarwa a class din ba....Tunani na gabadaya ya tafi gurin ganin hanyar da zan samu muradin zuciyata....Malamai uku suka shigo sukayi abinda za suyi suka fita ban gane komai ba Allah-Allah nake a fita break mu zauna da Samira.


A sanyaye nace."Samira guy nan kamar kara masa kyau ake wallahi dazu a cikin motarsa ji nayi kamar naje na sumbaci gefan fuskarsa ina tsananin kaunar namiji mai gemu da saje.

Samira na kallona tace."Surayya kin makance gaskiya wallahi ina tausayi miki wani abu." Rai a bace nace."Samira kada ki 'bata min rai don Allah wallahi ni ji nake kamar na aureshi na gama sam yanzu bana jin tsoron na furta masa kalmar so.

Tace."Kamar gaske wallahi ba zaki iya ba abinda kina ganinsa jikinki yake mutuwa ina kallonki fa dazu a motarsa kina goge hawaye." Girgiza kaina nayi nace."Samira ni kaina ban san sanda hawayen ke fitowa ba shiyasa nace miki Allah ya jarrabe ni."

Tace."To yanzu dai ga waya kuma akwai kudi ina fatan kin dauki number." Wayar na kar'ba daga hannunta nasa number. Cike da mamaki tace."Lallai har kin haddace number sa a kanki."

Murmushin takaici nayi nace."Meye number waya Samira shi kansa na haddace shi dan idan na rintse idona shi kadai nake gani.

Girgiza kanta kawai tayi tace."To yau kuma wasu irin kalamai zamu tsara masa." kallonta nayi da fadin.'' Kalaman soyayya masu zafi amma fara kiranshi muryarsa kawai nake so naji.

Baki bude take kallona nace."Idan kin kira shuru za muyi kawai inaso naji muryarsa.....Samira ba tare da shakka ba ta fara kiran number.

Tana kokarin katsewa ya d'aga muryarsa mai cike da amo da sauti ta bayyana.......da sauri na kar'bi wayar na bude hands free nasa wayar a kunnena ina lumshe idona "Salamu alaikum wake magana." Na lumshe ido tare da sauke wani irin nishi!!!!

Da saurin gaske ya cire wayar daga kunnanshi yana duba number Nishin! da yake fita daga wayar shine ya bashi mamaki! wayar ya mayar kunnanshi cikin tsawa! yace."Waye akan layi."?

Hannu na rawa na kashe wayar! muka tsirawa juna ido ni da ita........'bangaran shi kuwa shuru yayi da wayar a hannunsa yana mamakin al'amarin wace 'yar iskar yarinya ce ta kira shi a waya take masa nishi!!!! ya dinga bin number da kallo yana jimanta al'amarin.

Samira ta fashe da dariya tana kallona tace."Gaskiya Surayya kina da matsala duba don Allah yanda idanuwanki sukayi jawur! shin wai soyayya ce ko jaraba."? Cikin wani irin yanayi nace." Samira nima ban sani ba kawai ina jin wani irin feelings ne a duk lokacin da zanji muryarsa.

Tace."Lallai to Allah dai ya cika miki burinki.'' Cikin farin ciki na amsa da ameeen 'kawata nagode sosai yanzu sai mu fara rubuta masa text din.

_Assalamu alaikum_
_Ya farin cikin zuciyata ina rokon Allah ya mallaka min kai a matsayin mijina uban 'ya'yana hakika na san na samu gwarzon namiji wanda ko wace mace take muradi.....Wallahi na kan gigice na d'imauce a duk lokacin da zanyi tozali da kai kana sanya ni cikin wani irin hali na bukatuwa ban ta'ba sha'awar d'a Namiji ba sai kai kullum sai nayi mafarkinka da tunaninka nake kwana dashi nake tashi Masoyi na ina tunanin kaunarka ce ajali na amma zan tsananta da addua akan Allah ya mallaka min kai domin na more rayuwar duniya Gwarzon maza D'aya tamkar da dubu jarumin jarumai Allah ya nuna min ranar da zan mallake ka mu kasance a cikin bargo daya a ranar babu wanda ya kaini farin ciki.......Na barka lafiya Habibi Allah ya tsare min kai a duk inda kake_
*DAGA S-R-Y*

Na jima ina karanta text din nace" Samira komai yayi daidai kawai a tura masa." Tace."To shikkenan." sai da text din yaje ta nuna min wayar da fadin." Gashinan ya tafi." Ajiyar zuciya na sauke da fadin." Tashi muje mu samu wani abu mu siya kafin a kada kararrawa." Ta mike tana kokarin mayar da wayarta cikin jaka.......Ikilima 'yar ajinsu ta karaso gurin tana kallonta tace."Ke Samira wallahi ki daina zuwa da wayarki idan ba haka ba za'a kwace miki

Nace."Ikilima kwacen waya aka a makarantar."? Tace."Eh mana ai ba'a zuwa da waya da kayan siyarwa saboda haka sai ku kiyaye.'' Tana gama maganarta ta bar gurin.


P-A d'insa ne ya shiga ofis din da ledar take away a hannunsa suka gaisa cikin mutunci ya ajiye masa abincin ya fita sai da ya kammala ayyukan dake gabansa tukkuna ya sauka daga kujerar kan wata katuwar kujera dake girke a ofis din ya zauna ya bude abincin yana ci yana duba wayarsa......Text din ne ya shigo sai ya fara dubawa......Number dai itace ta dazu wacce aka kira shi ana Nishi!! Ya dinga nanata karanta text din yana mamaki.........SRY Wannnan harufan sune suka fi daukar hankalinsa yayi - yayi ya had'a sunan ya kasa gabadaya kwakwalwarsa ta toshe babu shakka yarinyar nan ce data jima tana tura masa da wasikar soyayya ta hanyar Haruna maigadi yanzu ta samu number wayarsa Murmushin takaici yayi yana girgiza kansa lallai babu shakka duk ranar da ya gane ko wacece sai ta gane kuranta kamar shi da baya shiga sabgar ko wace 'Yar iska za'a kawo masa wannan shirman babban abinda yake 'bata masa rai shine duk cikin text d'in sai tayi maganar had'a shimfida da shiga bargo d'aya gaskiya yana mamakin tsagerancin yarinyar..


*****
Yau Juma'a ce da wuri aka tashi daga makaranta Cikin adaidaita sahu ta kalleni da fadin." Wallahi Surayya kada ki cutar da kanki kina ganin alkairi kina gudu jiya da muka had'u da Shahid yace yana so yazo gidanku amma yana jin tsoro kada ki wulakantashi.

Ta'be baki nayi nace."Samira idan kina min maganar Shahid wallahi haushi kike bani ni me zanyi da Shahid." Tace."Ai ba cewa nayi ki aureshi ba kawai muci kudinsa." shuru kawai nayi mata tace."Idan kuma kina jin tsoron yazo gidanku to kawai kizo gidanmu sai ku hadu." Girgixa kai nayi nace."Kawai kice masa yazo gidanmu." Tace."To shikkenan yanzu bari na kira wayarsa na fada masa.

Ina ji suna waya Shahid sai murna yake sai ya bani tausayi saboda na san shima Allah ya jarrabeshi da irin abinda ya jarrabeni son maso wani.

Tana dariya tace." Kina jin yanda yake murna ko.'' Nace."Ni wallahi tausayi ma yake bani Samira babu kyau yaudara." Tace."Ai shi yasa kansa ba wani ne ya aikoshi ba duk abinda ya baki ki kar'ba shi yasa kansa." Kaina kawai na girgiza da fadin." To Allah yasa yazo da alkairi."


Bayan Isha'i gabadayanmu muna zaune a tsakar gida har Malam muna cin abinci yaro yayi sallama da fadin." Wai ana sallama da Surayya a waje." Da sauri Innah ta kalleni na sunkuyar da kaina kasa. Malam yace."Je kace wanene."? yaron ya juya ya fita minti biyu ya dawo da fadin." Wai inji Shahid na gidan Malam Ado." Malam yayi murmushi da fadin.'' Jeka kace gatanan zuwa." da sauri yaron ya juya fita.

Ya kalleni da murmushi a fuskarsa yace."Tuntuni na fahimci yaron nan yana sonki Surayya ba zanyi miki dole ba idan kina sonsa kina iya zuwa ki saurareshi domun na fahimci yaron yayi hankali ba kamar yanda na sanshi ba gashi ubansa mutumin Kirki ne za'a iya had'a mu'amula ta aure dashi.

Ba tare da nace komai ba na mike simi-simi na shiga daki nasa hijabi na fito Innah ta dinga bina da kallo har na fita daga gidan.....Ta kalli mijin nata da fadin." Malam ni kam gabadaya wannan al'amari beyi min dadi ba saboda na san halin mahaifiyar yaron nan Mariya bata hakuri gashi surukanta suna kuka da ita bayan haka kuma yaron nan bashi da sana'a."

Yace."Duk wannan abu ne mai sauki Habiba shi aure albarka gareshi rashin sana'ar yaron ba zata hana abinda Allah ya hukunta ba addua kawai zamu tsananta akan Allah ya za'ba abinda yafi alkairi." Tace."To Malam Allah ya za'ba mana abinda yafi alkairi ya amsa da ameeen ya Allah.


Tunda muka gaisa na sunkuyar da kaina sai dai gabadaya hankalina yana kan katuwar ledar da yazo da ita sai magana yake banda E da Aa babu abinda nake iya fad'a.

Yace."Surayya tun kina yarinya Allah ya jarabce ni da Kaunarki dan Allah kada ki watsa min kasa a ido ki aminci na turo iyayena a tsayar da magana.

Kallonsa nayi tare da kokarin saisaita fuskata nace."Shahid ka kwantar da hankalinka nima ina sonka idan Allah ya kaddara aure a Tsakaninmu za muyi amma ba yanzu nake so ka turo iyayenka ba tunda kaga ban gama makaranta ba da sauran lokaci."

Yace."Surayya bana so wani yayi min shigar sauri ne shiyasa nake so iyaye su shiga maganar."......Girgiza kai nayi nace."Kada ka damu Shahid mahaifina ba zaiyi min aure dole ba sai da wanda nake so dan haka ka daina damuwa."

Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Shikkenan Surayya nagode sosai ni zan tafi." Ina murmushi nace."To Shahid nima nagode." Ya miko min katuwar ledar dake shaqe da kaya Yace."Ga wannan babu yawa." Ina murmushi nasa hannu na kar'ba da fadin." Shahid kenan harda wata hidima to nagode." Yace."Babu komai Surayya babu abinda ba zan miki ba." Dariya nayi ina kallonsa yace."Na tafi insha Allah zan siya miki waya koda kypad ce sai mu dinga gaisawa." Nace."Eh hakan yana da kyau Allah ya yassare." Ya amsa da ameeen yana kokarin tafiya. na daga masa Hannu da fadin." Sai anjima a gaishe da mutan gida." Ya amsa da zasuji insha Allahu." Cike da murna da farin ciki na shiga cikin gida hannuna rike da ledar sauri nake na bude naga abinda yake ciki..


*A taimaka da Sharing👏🏾*




_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[7/26, 7:31 PM] Bintu🍒: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*23&24*
Kusa da ita na zauna da ledar a hannuna, cikin rashin walwala tace."Menene acikin ledar ne."? Babu karfin gwiwa nace."Nima ban sani ba yanzu dai zan bude naga ni." Girgiza kai tayi tace."Surayya bana son shiga sabgar Mariya shiyasa kwata-kwata wannan alaqar dake tsakaninki da yaron ta bana so." Shuru nayi mata ina firfito da kayan dake cikin ledar.....Tace."Ko a gidan uban wa ya sami kudi da har yayi miki wannan siyayyar nasan dai uwarsa bata sani ba domin da ta sani ba zata barshi ba."

Nace."Innah don Allah kiyi shuru da maganar nan haka nifa bani nace yayi min hidima ba shine yayi ra'ayi.

Tace."To duk kulafucin ki babu abinda zakiyi amfani dashi a cikin kayan nan tunda nasan dai ba sonsa kike ba babu amfani kici abinsa.

Murya na rawa nace."Haba Innah har guda nawa kayan suke duk rabi fa kayan kwalliya ne sai mayafai da takalmi amma kuma kice ba zanyi amfani dashi ba.

Tace."Ni dai na fada miki ki mayar da kayan cikin leda ki daure." Kuka nasa ina kallonta bakina sai rawa yake saboda tsabar takaici.

Malam ya mike zaune da alamun bacci a maganarsa yace."Menene kuma naji ana kuka."? Da sauri tace."Ai gwara daka tashi idonka ya gane maka ka duba kaga uban kayan da yaron nan ya kawo mata bayan babu wata tsayayyar magana a tsakaninsu."


Malam ya haska kayan da torchlight d'inshi yana dubawa. Kai ya girgiza yace."Surayya nima ban goyi da bayan kiyi amfani da kayan nan ba ki bari insha Allahu zan samu mahaifinsa mu tattauna maganar

Da sauri nace."Aa ni dai kada kuyi wata magana yanzu sai na gama makaranta tunda nace shi nake so to akan me za'a ce ba zanyi amfani da kayansa ba."

Da sauri ta zaburo kamar zata kai min duka tace."Don Ubanki rashin kunya zaki mana."? Girgiza kaina nayi ina bata hakuri. Malam yace."To shikkenan tunda kince haka Habiba ki zama sheda kada daga baya tazo ta sauya magana.

Cike da takaici tace."Malam wannan al'amarin babu sanya hannuna a ciki dan gabadaya maganar bata gamsar dani ba tunda kun amince ai shikkenan.

Kallona yayi yace."Ki shiga da kayan daki kiyi amfani dasu tunda dai kin za'bi Shahid a matsayin abokin rayuwarki to kada ki kuskura daga baya ki sauya magana.

Ba tare da tunanin wani abu ba nace."Eh insha Allahu babu abinda zai faru." Ajiyar zuciya ya sauke ya koma ya kwanta ni kuma cike da farin ciki na dauki ledar kayan na shiga daki ina murna na samu mayukan da zasu sanya ni fari dama na tsani naga fuskata tana maiko duk da baki na ba mai muni bane amma ina sha'awar fuskar Ummiyo saboda man da take shafawa yayi mata kyau.


Da sassafe sai ga Samira...Innah da kyar ta amsa gaisuwarta ta shiga daki ta same ni jikinta duk a sanyaye tace."Surayya na lura Innah bata so nake zuwa gurinki."

Da sauri nace."Wai Samira me yasa har yanzu kika kasa sabawa da halin Innah ne itafa wata iri ce mai wuyar sha'ani nima hakuri nake da ita sam bata da fara'a."

Tace."Ai ni idan naga tana shan kunu tana min wani irin kallo duk sai na zargi kaina." Nace."Nima da ta haife ni haka take min.

Dariya tayi tace."Ya kukayi da Shahid kuwa."? Hannu na bata muka tafa nace."Samira wallahi da babu Uncle a zuciyata da zan iya auran Shahid saboda ni a rayuwata ina masifar so naga namiji na masifar sona baki ga uwar hidimar da yayi min ba.

Tace."Ai na fada miki dama Shahid ne masoyinki na hakika amma kin tsaya kina 'bata wa kanki lokaci.''

Rai na 'bata ina watsa mata wani irin kallo tayi murmushi da fadin.'' Allah ya baki hakuri yanzu dai dauko min kayan na gani."

Girgixa kai na kawai nayi na janyo mata ledar kayan ta zazzage a gurin tana dubawa sai murna da tsalle take da fadin ta samu mai."

Nace."Ki dauki k'aramin sai ki bar min babban turaran ma ki dauki kwali daya sabulu ma ki dauki kwali daya." Tace."To mayafin fa." ? Nace."Ki dauki daya dan dama ni mayafi bai dame ni ba nafi son hijab.

Ta dauki takalmi guda tana dubawa nace."Kin san dai duk cikin takalman nan babu wanda zaiyi miki saboda haka sai ki hakura." Tace."Ai shiyasa na dauka ina dubawa ke kam k'aramar kafa ce dake.'' Nace."Nima nayi mamaki da har ya gane sizi d'ina Yace ma zai siya min waya." Sai kawai ta rangwada guda ta wani rungume ni tana kyalkyala dariya." Innah ta leko dakin tana fadin." Kuna da hankali kuke wannan shashanci ko kuwa a gidan biki kuke."?

Shuru mukayi taja tsaki tare da sakin labulan dakin ta bar gurin....Nace."Samira yau akwai Isilamiyya fa." Tace."Ni wallahi ko uniform din ban wanke ba na manta.'' Nace."Ai dama kin saba asha ruwan tsintsaye yau kije gobe ki zauna yana da kyau kije ki wanke kayan kafin zuwan lokacin.

Ta mike da sauri da fadin."Bani leda nasa kayan nan a ciki yau nima na zama me 'yanci Ummiyo zata daina hura min hanci." Dariya nasa da fadin."Hajia Ummiyo kenan." bakar leda na dauko mata tasa kayan a ciki.

Har waje na rakata ina sake jadadda mata cewa ta wanke inform d'inta kada lokaci yayi.


Yau Innah wake 'kulu da man gyada tayi mana abinda na tsana kenan a rayuwata da kyar naci ina ya tsine fuska ........Tana kallona uffan ba tace min ba sai da na mike domun wanko hannuna tace."Wallahi Surayya kiyi sabo da cin komai kada anan gaba kisha wahala domin baki san inda zaki je ba.


Ina kokarin sanya hijabi a wuya na nace."Innah ashe bakya min fatan auran mai kudi." Ta'be baki tayi tace."Yo ai juma'ar da za tayi kyau tun daga laraba ake gane ta Shahid ne fa d'an gidan Mariya matar da take takurawa surukanta."

Nace."Ni wallahi Innah babu wata suruka da ta isa ta takura min ai ba ita nake aure ba." Kallona tayi tana girgiza kai tace."To maganin ayi kada a fara ki hakura da yaron nan Shahid dan mahaifiyarsa masifaffiya ce."

Nace."Innah addua zaki cigaba dayi min." Tace."To Allah ya zaba miki abinda yafi alkairi." Na amsa da ameeen Innah ni zan tafi makaranta." fatan alkairi tayi min tare da adduar dawowa gida lafiya.


Abin mamaki koda na biyawa Samira makaranta tana zaune durshan suna hira da 'yan gidansu. Na kalleta rai a bace."Nace."Samira meye haka na dauka kafin nazo kin shirya amma dube ki a zaune ko wanka baki ba."

Tace."Surayya kalli igiya ki gani wallahi yanzu na wanke kayan dan ina dawowa daga gidanku bacci ya dauke ni sai yanzu na tashi." Igiyar nabi da kallo

Please Login or Register in order to submit comment