You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin tawa ban tsinkayi komai ba sabida yanda yake magana kasa-kasa sai kace wani basarake.....Ji nayi wani abu yana bin jikina na zabura! na buga tsalle ina karkade-karkad'e. gazarzar! naji a fatar wuya na alamun tafiyar kadangare.

Wani uban ihu! na kurma a maimakon na shiga gidan tsabar rud'ewa kawai nayi waje ina ihu! had'e da buga tsalle zani a hannu dankwali a hannu.

Malam ya gigice! har sai da ya kusa fadowa daga kan kekensa fadi yake." Surayya menene me ya faru." ?

Cikin rawar jiki da tsabar firgici nace."Wayyo kadangare ne a cikin rigata."

Malam yace." Subahanallahi Surayya a'ina kika sam....Kafin ya karasa maganarsa naji motsinsa a cikin rigata a guje naje inda nake mukayi ragas! dan saura kiris mu fadi dani dashi.....Fitilar wayarsa ya kunna fuskar nan tamkar wanda aka aikowa da mala'ikan daukar rai yace."Wai ke wace irin yarinya ce mara nutsuwa."?

Sama-sama nake jin maganarsa tunda na samu nasarar kwanciya a kirjinsa jikina ya mutu kafafuna suka dinga kyarma tsabar fargabar kadangare da kuma shaukin so.

Ba tare da tunanin wani abuba ya fara lalube jikinta da hannuwansa nan ya rike karamin kadangare (dan ta milo) ya sanya daya hannunsa cikin rigar ya daukoshi can gefe ya jefar dashi ya cire ta daga jikinsa yana haskashi da hasken wayarshi.

Malam ya girgiza kai cike da bacin rai yace."Yanzu Surayya wannan abun kike wa ihu! sau nawa zai zo yabi ta kanki ya wuce hankali a kwance amma yanzu saboda tsabar sangarta sai ihu kike wa mutane.

Tana gyara rigarta tace." Wallahi Malam dole naji tsoro ban sani ba ko aljani ne."

Uncle yaja tsaki yana ji tamkar ya buge ta a gurin ya kalli Malam din da fadin." Zai wuce gida da safe zai turo da sako."

Malam yace." To shikkenan Nuraddin mungode kwarai Allah ya saka da alkairi.'' Ya amsa da ameeen Malam sai da safe."
Da sauri tace."Uncle sai da safe." tsabar yanda yake jin haushinta ko amsawa beyi ba ya bar gurin.

Ya kalleta rai a bace yace." Surayya wai shin yaushe ne za kiyi hankali? yanzu abinda kika yi a yanzu kin kyauta ina tare da yaron arziki kin fito kina tsalle da ihu."


Jiki a sanyaye tace." Malam kayi hakuri wallahi firgita nayi shiyasa amma ba zan k'ara ba dama nazo ne domin na shiga da kai gida.

Yace." Da kin bari ma da kaina zan shigo gashi kinzo kin zubar min da mutunci.

Hawaye ta share a sanyaye tace." Kayi hakuri ba zan sake ba insha Allah." Girgiza kansa kawai yayi ya fara kici-kicin tura kekensa da sauri ta kama masa suka shiga gidan yana kara yi mata nasiha akan rayuwa.


Ya jima yana mamakin jin abinda yake ji a cikin tafin hannunsa ashe kallon kitse yake wa yarinyar a zahiri sai ka dauka bata da mamora ashe a lullu'be take sai da hannuwansa sukayi yawo a cikin jikinta sannan ya gazgata cewa cikakkiyar macace.......Har yayi wanka ya fito yana tunanin al'amarin.


Washe gari da safe Kafin Malam ya fita yake sheda masu yanda su kayi da Uncle cewa da kanshi zai je can *Adamu na Ma'ajin* Ya kar'bo mata transfer zai kai ta can makarantar shi mai suna *ADAPT SCIENCE AND TECHNOLOGY* Babbar makaranta ce wacce gwamnati ta san da zamanta Secondary and primary ce a had'e akwai kwararrun malamai a makarantar cikinsu harda wa 'yanda suka fita waje sukayi karatu wannan dalilin yasa iyayen yara suke wa 'yayansu rijistar da makarantar saboda karatu da tsaro da tarbiya Uncle Nuraddin bashi da wasa shiyasa duk malamansa da dalibansa suke da nutsuwa babu wani kangararre a cikin dali'bansa.



*WANENE UNCLE NURA?*
Alhaji Aminu (Sabo) Wani mutumin kirki ne a garin kano cikin unguwar Goron duste (bayan gidan Malam Isiyaka Rabi'u) Alhaji Aminu yana arziki daidai gwargwado kuma yana aikata abinda Allah ya fada akan dukiyarsa. sai dai kuma Allah bai azurta shi da mace Ta gari ba. Ya auri Hajia Sabuwa auran saurayi da budurwa tunda ya aureta ta raba shi da kowa sai yayi da gaske take barinsa ya ziyarci 'yan uwansa har yayi musu ihsani.

'Ya'yansu Hudu Mata biyu maza biyu Babbarsu itace. Aunty Jamila sai me bin ta Aunty Nafisa to sai shi Uncle Nura sai k'aninshi Imran wanda yake can Egypt yana karatu.

Hajia Sabuwa gabadaya tayi wa 'ya'yan ta mata tarbiya mara kyau koda akayi musu aure basa lan'kwasuwa a gurin mazajensu kowacce abinda taga dama shi take yi saboda gabad'aya sun riga sun gama da mazajensu kamar yanda mahaifiyarsu ta gama da mahaifinsu da Asiri Hajia Sabuwa muguwar 'yar shige-shige ce babu inda bata zuwa yawan kar'bo asiri mutukar zata samu biyan bukata to ko nan da birnin sin ne za taje ta kar'bo mugun abu.

Nuraddin yana bala'in Jin ciwon abinda suke aikatawa a matsayinsu na musulmai amma basu da aiki sai yawon tsubbace-tsubbace duk ranar da ransa ya 'baci yayi musu magana a ranar sai tayi kamar ta tsine masa wannan bacin ran ya sanya yake zuba musu ido....amma watarana idan ya gansu sun had'u yasan wani gurin za suje sai kawai ya zauna a tsakiyarsu ya kunna musu wa'azin *MALAM UMAR SANI FAGGE* Wayyo Allah kamar su d'ora hannu aka jikinsu ya mutu suyi ta zazzare ido saboda yanda wa'azin Malam din yake tsorata su Malam na bayyana irin azabar da Allah ya tanadarwa masu aikata shirka a ranar lahira. Yini suke jikinsu a mace sai dare kowacce zata kama hanya ta tafi gidanta tana nadama. amma cikin ikon Allah sati biyu zasu warware su koma ruwa sun manta saboda duniyar ce kawai a gabansu uwarsu zata su a gaba su tafi neman taimako a gurin wanin Allah bayan sunyi da jikinsu da kudinsu (Allah ya shiryar damu)

Uncle Nuraddin ya k'are karatunsa a can Uk ta kasar waje(America) gabadaya yayi karatunsa ne a 'bangaran Ilimi Inda ya fito da kyakkyawan result mahaifinsa yayi farin ciki mutuka wannan dalilin ne ma yasa suka had'a karfi da karfe suka gina wannan katafariyar makarantar dake bakin titin (KABUGA) Bayan duba cancanta da dacewa Gwamnati ta shiga cikin al'amarin itama ta bada taimakonta Uncle ya dauki malamai kana kuma ya fara bin gidajen marayu da marasa galihu yana kai su makarantar.........Bayan wannan jihadin da yayi sai manya mutane da malamai suka dinga yi masa kyauta suna yaba kokarinsa da yawa daga cikinsu suka dinga kai yaran su makarantar abinda zai baka mamaki shine har da yaran sanatoci 'yan majalisu da sauran masu kudin dake garin Kano.........Wannan Dalilin ya sanya kafafan sadarwa tattauna dashi ta bangaran Ilimi. Uncle Nuraddin yayi fice sosai dan ko Seminar suka je irin ta malamai shike jagorantar 'bangaransu.

*Wannan kenan*

Wani irin farin ciki ne ya rufe ta tana kallonsa tace."Malam to yanzu yaushe zan fara zuwa makarantar kai amma wallahi naji dadin haka.

Yana murmushi yace." Sati mai zuwa zaki fara zuwa da yardar Allah." Kawai sai ta rungume! Innah dake gefanta a zaune ta dinga kyalkyala wata irin dariyar farin ciki.....zata koma zuwa makarantar Uncle wannan hanya ce mai sauki wacce za dinga samun ganinsa a kai a kai." Sai dariya take tana ji tamkar ta zuba ruwa a kasa tasha dan farin ciki.




_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[7/22, 2:58 PM] Bintu🍒: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*17&18*
Ina jin su Samira suna hira a tsakaninsu amma na kasa sa musu baki hankalina gabad'aya yana kansa da tunanin irin rayuwar da zamu gudanar idan munyi aure
" Surayya ki daina tsawwala wa kanki shi fa aure nufin Allah ne kuma mafi a kasari abinda kake so baya zama alkairi a gare ka" Zuciyata ce ke tunasar dani. Sai kawai zuciya ta ta karye hawaye suka zubo min da sauri na goge ashe Ummiyo ta gani tace."Ke kuma lafiya kike kuka."?

Da sauri nace."Ba kuka nake ba wani abu ne ya shiga idona shine yake fitar da ruwa." Ummiyo ta yarda da magana ta amma banda Samira saboda tafi kowa sanin halin da nake ciki.

To a gurin bikin ma bani da walwala ina kallo ana ta gudanar da shagulgula Ummiyo da Samira sai rawa sukeyi a tsakiyar Mai DJ sai manna musu kudi ake saboda Ummiyo ta iya rawa ta shaid'anci. Al'amarin ya dinga bani mamaki da kunya dan ganin yanda ta dage take karye-karye nononta sai tsalle yake sabida tsabar rawa.

Ta kusa dani na tambaya lokaci wayarta ta fito dashi ta duba ta kalle ni da fadin." Tara da rabi." Zumbur na mike tsaye gabana na faduwa.........Kutsawa nayi gurin me DJ din na kamo Samira nasa bakina a kunnenta murya na rawa na fada mata lokaci....Cikin shau'ki tana girgiza jiki tace."Ai Surayya sai dai ki tafi ke kadai dan wallahi ba zan tafi ba sai lokacin da me DJ d'in nan ya tashi kina kallo dai yanzu ne ma yake sanya wakoki masu dadi.

Murya na rawa nace."Samira haka zaki min ko."? Tace."Surayya dama ai sai da na fada miki ban munafurce ki ba kinga bani da laifi." Tana gama maganarta ta bar ni a gurun.

Cikin tsananin fargaba da damuwa na fito bakin titi gashi babu ko kwabo a hannuna hawaye suka wanke min fuska babu shakka duk wanda bai ji maganar na gaba dashi ba yana tare da matsala.

Wani mai babur ne ya tsaya a gabana yana tambaya ta nace." Goran dutse zaka kai ni." Yace."To kudin ki dari biyu." Babur din na shiga da fadin." Muje." yaja da sauri muka bar gurin.......Rintse idanuwana nayi na cigaba da addua akan Allah ya sassauta zuciyar Innah na san tana can cikin bacin rai uwa uba Malam da baya son nayi dare a waje.

"Hajia mun zo" Muryar direban ce ta dawo dani hankali na nace."To dan Allah ka shiga dani ciki ka ajiye ni a kofar gidanmu sai na baka kudin."

Yace."Ai ba haka muka yi dake ba ni ba zan shiga wannan lokon ba kawai ki fito ki bani kudina.....Muryata na rawa nace."Don Allah ka taimaka min ni wallahi yanzu babu ko kwabo a hannuna dama sai ka ajiye ni a gida sai na baka kudin.

Zagi ya kurma! yana wani irin fito! ya fito daga babur din ya tsaya a kaina yana fadin." Wallahi zanyi miki rashin mutunci a gurin nan mutukar baki bani kudi na ba ni zaki rainawa hankali."

Nace."Haba dan uwana ka kar'bi uzuri na wallahi babu kudi a hannuna." Cikin hayaniya yace." Me yasa tun farko baki fada min ba ni ba zan kar'bi Uzurin ki ba kawai ki bani hakki na."

Magana zanyi kawai ya fara kokarin janyo hijabi na a fusace! nace."Dallah Malami sakar min hijabi." Yace." Ba zan saki ba sai kin biya ni kudi na wall.........."Wai me yake faruwa ne." Wani mai siyar da fetur a gurin yake wannan maganar. ba tare da bata lokaci ba ya shiga fada masa yanda mukayi


Fitowa nayi daga babur din ina kalle-kalle a gurin wai har jama'a sun taru saboda tsabar sa'ido

Yace."Ke ya akayi kika shigar masa babur baki da kudi." ? Rashin abin cewa yasa na fashe da kuka babban takaici na jama'ar da sukayi dafifi a kaina suna kallona............................K'amshin turaransa ya tabbatar min da cewa yana gurin. gabana na faduwa na dago kaina muka had'a ido dashi suna magana da direban yana fada masa abinda ya faru.

Dari biyar ya bashi ya kalle ni da fuska tamkar ta zaki Yace." Wuce muje." Da saurin gaske nabi bayansa zanin jikina na kokarin yar dani.

Bayan motar na zauna ya tayar muka bar gurin.....Kaina a sunkuye naji sautin muryarsa." Yace." Ina kuka je ke da wad'ancan 'yan iskan yaran."?

Shuru nayi bakina yayi min masifar nauyi! "Surayya ba dake nake magana ba."?

Murya na rawa nace." Gidan biki." Yace."Wace."Unguwa ne."? "Can rijiyar zaki." Girgiza kansa yayi yace."Lokacin da zaki fita daga gidanku mahaifiyarki ta sani."? da sauri nace."Eh na fada mata." Ta mirror ya watsa mata wani irin kallo ya girgiza kansa da fadin." Kin raina iyayenki ko kina basu wahala saboda kawai kina ganin ke kadai suka haifa shiyasa kike yin duk abinda kike so sai kiyi musu karya ki tafi yawo kisa hankalinsu ya tashi sabida baki da mutumci to wallahi wannan shine na farko kuma shine na karshe kada na sake ganin ki da wa'innan yaran marasa tarbiya ni ba zanyi miki da sauki ba sai naci mutuncin ki."

Cikin kuka nace."Uncle dan Allah kayi hakuri kaji." Tsaki yaja yana gyara parking yace."Duba dan Allah haka kawai kin tashi hankalin bawan Allah saboda kawai kinga yana sonki."

Da sauri na kalli gurun Malam yana zaune kan kekensa kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake......Nace."Uncle don Allah kace yayi hakuri sannan ka shiga gidan ka bawa Innah hakuri wallahi ba zan kara ba.

Yace." Ni na zama dan aiken ki kenan."? Da sauri nace."Aa ba haka nake nufi ba.'' Yace." To maza fice min a mota shashasha kawai." Da sauri na bude motar ina jin takaicin kira na da shashasha da yayi.



*MAR'ATUS-SALIHA*
_(Itace Cikakkiyar Mace)_

*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu👫 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*
1- Maganin Sanyin mara
2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa
4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba
5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa
6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa
7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)
8-Maganin Basir mai tsiro
9-Maganin Basir mai kulle ciki
10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)
*11- Maganin Karin Ni'ima
12- Maganin K'iba mai kyau
13- Maganin Cikar Nono (Breast)
14- Maganin Hips
15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!
16- Maganin Matsi mai kyau
17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)
19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba


*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*
*07084653262*
*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*
Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp



Har na isa inda yake idonsa na kaina. sai kawai na zube a gabansa na rike hannunsa hawaye na ambaliya a fuskarta nace."Malam don Allah kayi hakuri wallahi ban san dare yayi ba.

Shuru yayi kawai yana kallona, na rintse hannunsa da fadin." Malam kada kayi fushi dani tsautsayi ne." Girgiza kansa yayi yace."Surayya me yasa kike tayar min da hankali na." Nace."Malam kayi hakuri tsautsayi ne." Yace."Kin yaudari mahaifiyarki kan cewa zaki je gidansu 'kawarki ashe yawo kika tafi." Shuru nayi domin bani da abin fada.

Yace."Wannan yaron Nuraddin babu abinda zan ce dashi alkairinsa nada yawa a gare ni tun bayan La'asar dashi ake neman inda kike sai daga baya muka samu labari cewa kun je gidan biki keda wa'innan yaran masu soye-soye a waje me yasa kike so ki zubar min da mutumci na."

Shuru nayi hawaye na cigaba da gudana a saman fuskata Yace."To mutukar kina son farin ciki na ki dinga jin magana kuma ki daina k'arya a cikin al'amuranki sannan kuma Nuraddin din ya yanke hukunci a kanki ya raba ki da Samira tunda ita take koya miki rashin kamun kai."

Nace."To Malam naji insha Allahu zan kiyaye." Shuru yayi min ya fara kokarim tura kekensa na mike da sauri na taimaka masa muka shiga cikin gidan.


Innah ta cika tayi fam! nace."Innah kiyi hakuri kinji.'' ko kallo na ba tayi ba." Malam daki ya shiga ya kwanta Sunanta na kira tayi min banza, a sanyaye na mike na shiga daki domin cire kayan jiki na.

Babu zato naji duka da wayar redio a fatar baya na wani irin gantsarewa nayi ina ihu! ina kokarin rike wayar tana fizgewa da fadin.'' Ai tunda na rantse to sai na dake ki ni ba shashashar uwa bace da zaki dinga raina min hankali."

Zabga min wayar take ta ko'ina ina kwarma ihu tare da so na kwace wayar amma tayi mata rikon tsauri gaskiya ban ta'ba tsammamin haka Innah take da karfi ba........"Habiba ki kyale yarinyar nan kada kiyi mata rauni dukan ya isa haka." Shuru tayi masa ta cigaba da labta ta kawai sai na fad'i a gurin ina turjiya kamar me aljanu. hakan da nayi shi ya taimaka min sai ta yar da wayar ta fita daga dakin tana numfarfashi.

Laga-laga na kwanta a kasan dakin na dinga kuka yaushe rabon da Innah ta dake ni sai yau gaskiya banyi wa kaina a dalci ba domin nasan komai ya faru ni na janyowa kaina...

Sai dana sha panadol na kwanta bacci mara dadi ya dauke ni da safe da kyar ta amsa gaisuwa ta Malam kafin ya fita sai ya sake min fada da nasiha akan abinda ya faru.

Bayan kwana biyu sai ga Samira tazo tana washe min baki tana bani labarin irin shagalin da akayi bayan tafiya ta naja tsaki da fadin." Malama ya isa haka ni ba zan sake zuwa sabgar ku ba."

Tace."Saboda me."? Murya na rawa nace."Naci duka a gurin Innah sannan Uncle ya farfad'a min bakar magana.'' A sanyaye tace." Kiyi hakuri 'kawata wallahi ban san haka zata faru ba." Shuru nayi mata. Tace."Amma dai ranar litinin zaki je makaranta."?

Girgiza mata kai nayi nace."Uncle ya mayar dani makarantarsa dake KABUGA da sauri ta kalle ni da fadin." Yaushe hakan ta faru babu labari."?


Duk yanda al'amarin ya kasance na fada mata a sanyaye tace." Wallahi nima da zai dauke ni da naji dadi." Nace." Nima zanso hakan dan har na yanke shawarar fadawa Malam ya nema miki alfarma sai wannan matsalar ta faru wai yace kada ma na sake Mu'amula dake.

Tace."Saboda dame wani mugun abu nayi."? Shuru nayi tace." Na san dai Laifin Ummiyo ne ya shafe ni amma ni kowa ya sheda bana iskanci nida Ummiyo ciki daya muka fito amma kuma halin kowa daban."

Nace."Ki rabu dashi Samira bana jin zan daina Aminta dake domin kina bani shawarwari masu amfani dan haka ki kwantar da hankalinki."

Tace."Shikkenan Surayya ni zan tafi amma nima zan samu babanmu nace masa ya nema nin alfarma a gurun Uncle din domin ya kaini makarantar sa." Nace."To hakan yayi Samira Allah yasa a dace."

Koda muka fito daga dakin.... da sauri Innah ta dauke kanta. Samira tace." Innah na tafi." a dakile ta amsa jiki a sanyaye na rakata soro na dawo cikin gidan babu kuzari a jikina.



*Please a ayi shearing*


_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[7/24, 6:36 PM] Bintu🍒: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege

*19&20*
Ranar litinin tsaf na shirya cikin kayan makaranta na fito domin tafiya Malam ya dauko dari biyu ya bani yace nayi kudin mota sauran kuma na sayi wani abun.

A marairace na kalleshi da fadin." Malam dari biyu tayi kadan ka kara min hamsin kai." Innah dake kokarin fitowa daga daki tace."Haba Surayya har nawa ne kudin mota daga nan zuwa kabuga Naira Hamsin zuwa haka dawowa sai ki sayi wani abu da sauran kudin........Nace."Wallahi Innah baki san yanda ake jin yunwa a makaranta ba Allah naira dari tayi min kadan.

Tace."To ai kowa da sandar hannunsa yake kai duka mahaifinki talaka ne daidai gwargwado yayi miki kokari ina laifi." A marairace nace."Dan Allah Innah ki kara min hamsin." Wata uwar harara ta watsa min..Malam yayi murmushi hade da gyara zaman sa hannu yasa a aljihu ya dauko naira hamsin ya miko min da sauri na kar'ba ina dariya. Innah ta girgiza kai da fadin." Wallahi Malam ka daina sangartar yarinyar nan da kudi yanzu ce naira dari bata isheta ba.

Yace."Habiba bana so yarinyar nan ta shiga damuwa acikin 'yan uwanta idan ina da iko to zan bata abinda yafi haka saboda haka ki daina maganar sangarci."

Girgiza kai kawai tayi ta shige daki. Na kalleshi cike da kauna nace."Malam sai na dawo kayi min addua.'' Cikin kulawa yace."Surayya Allah ya tsare Allah ya baki ilimi mai amfani." Ina kokarin daure igiyar takalmina na amsa da ameeen ameeen Malam.



Daga can nesa na hangi Samira cikin Uniform irin na jikina sai abin ya bani mamaki tun kafin na karasa inda take take washe min baki. Na kalleta da fadin." Samira ya haka."? tana dariya tace."Ai dama na fada miki nima sai na san yanda nayi na samu shiga makarantar nan.

Muna tafiya take bani labarin yanda al'amarin ya faru Babarsu ce taje ta gurfana gaban Hajiya Sabuwa tayi mata kirari da bambadanci ta roki alfarma a gurin ta to dama ita Hajia Sabuwa macace mai Izzah! ganin yanda Zuwaira ta gurfana a gabanta kamar me neman gafara sai kawai tace ta kwantar da hankalinta zata san yanda tayi 'yarta ta samu shiga makarantar.......Uncle kuwa ba da san ransa ba ya amince da al'amarin domin sam baya bukatar marasa tarbiya a cikin makarantarsa dan dai kawai Umarni ne na iyaye babu yanda zaiyi.

Nace."Amma naji dadi wallahi dama ina jin rashin dadi a zuciyata Allah yasa a kai mu aji daya." Cike da farin ciki ta amsa da "Ameeen. Bakin titi muka fito muna neman abin hawa sai ga Mansur saurayin Samira yayi parking a gaban mu yana murmushi yace." 'Yan mata kun canza skull ne."?

Samira na firirita tace."Eh wallahi dama muna neman adaidaita sahu makarantar a can Kabuga take." Yace." Ayya gashi mashing din yayi muku kad'an da na dauke ku."

Da sauri tace."Haba babu wani kad'an ai sai mu hade jikinmu dama Surayya bata da qiba.'' Da sauri na kalleta na kalli mashing din.

Yace."Surayya kin ji shawarar kawarki kada ku makara kawai kuyi goyo na dauke ku dama hanyar zanyi sai kawai na sauke ku."

A sanyaye nace."Samira duba mana time idan da sauran lokaci sai mu tsaya jiran abin hawa. Ta fito da wayarta ta duba. da sauri tace." Takwas da rabi ta kusa.'' A sanyaye nace." Kuma karfe takwas ake rufe gate dan na karanta dokokin makarantar." Tace." To kin gani kawai mu hau Mansur ya rage mana hanya.

Nace."Shikkenan sai ki hau.'' Mansur da sauri ya gyara mata mashing din ta hau nima na dafa kafadarta na hau ya figa da gudun gaske.............

Tunda muka doshi bakin gate din makarantar gabana ke fad'uwa! a bude yake motoci na shiga wasu na fitowa da alama direbobi ne.....Da sauri nace."Mansur ba sai ka shiga damu ciki ba sauke mu." ai ko saurarata beyi ba ya fige mashing din cikin makarantar.

Daga can saman baranda ya hangi shigowarsu ya mike

Please Login or Register in order to submit comment