You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Uniform d'inta jagab da ruwa. Tsabar takaici yasa na juya ba tare da na sake wata magana ba na fita daga gidan.......A gaskiya su Samira ba suyi sa'ar uwa ba Zuwaira shashasha ce duk abinda 'ya'yanta sukayi daidai ne shiyasa gashinan Ummiyo ta lalace.



Biyar da rabi na yamma muke tashi a makaranta tun a hanya nake addua akan Allah yasa ya fito tunda dama duk weakened yake zaman karatu a bakin gate na gidansu.......Ajiyar zuciya mai sanyi na sauke ganinshi zaune a kujera da tarin littafai a gabanshi. Kafin na ankara naji abokanan tafiya ta suna maganarsa ko wacce sai gyara tafiya take. raina ya 'baci naji kamar na buge musu baki a ganina duk me zaiyi dasu da har suke wani sanja tafiya saboda shi.......Har muka wuce k'ungiyar mu guda bai dago kai ya kallemu ba hankalinsa na kan littafin hannunsa....Ni dai jikina a masifar sanyaye na isa gida na zube kan tabarma tare da cusa fuskata cikin hijabi kuka ya kwace min da alama 'yan matan dake son Uncle suna da yawa 'ya'yan masu kudi manya mata kyawawa masu kwarjini ni kuwa 'yar musaki takala nakasashe na san ko gasa ya yasa nice zan fad'i tunda bani da kyau bani da kudi babana talaka mai nakasa gani baka dole na kasance koma baya.

Maganarta naji a kaina." Surayya menene kin shigo babu sallama kawai kinsa kai cikin hijabi kina kuka."

Cikin dauriya nace. " Innah ba kuka nake ba kaina ne yake ciwo.'' Tace "Ai ni ba yarinya bace da zaki raina min hankali yana da kyau ki koyi hakuri da juriya komai akai miki sai ki dinga kuka wannan ba rayuwa bace."


Nace."Nifa Innah ba kuka nake ba." Girgiza kai kawai tayi ta bar gurin ni kuma na tashi jiki babu kwari na shiga daki domin cire uniform din jikina.


*Bayan sati uku*
Na dage da shafa man caro white wanda Shahid ya kawo min a maimakon ya sani fari sai wasu irin irin kuraje suka fito min fuskata ta sake baki hankalina ya tashi sai na ajiye man na daina shafawa ita kuwa Samira man ya kar'beta fuskarta tayi luwai tayi haske mai kyau kullum nayi ta sha'awar fuskarta yanzu dai na siyar mata da nawa man ta bani kudin mun shirya zuwa kasuwa domin siyan wani ko za'a dace.


Ranar litinin gurin Assembly aka firfito da masu bleacing aka ware su a gefe cikinsu harda Samira duk sun muzanta ko wacce sai zare ido take sosai na tausaya musu muna kallo a ka tasa keyarsu zuwa ofis din mai gayya mai aiki.


Uncle fad'a da nasiha yayi musu sosai ya nuna musu illar abinda suke ya kuma ce hakan ba zai hana ayi musu hukunci ba ya had'asu da dispelling master yace yaje dasu ya basu horo mai tsanani Uncle Bash dama abinda yake jira kenan ba tare da 'bata lokaci ba ya sauka dasu 'kasa can bakin band'akuna inda rana ta k'walle yace susa gwiwarsu a kasa su d'aga hannu sama kuma su kalli fuskar rana babu kiftawa so yake fuskokinsu su 'kone da da zafi rana inda nan gaba fuskar ba zata dauki mai ba.

Ya nemi kujera ya zauna yana kallonsu..........Kuka wiwi suke suna bashi hakuri azaba ta ishesu fuskarsu sai k'aikaiyi take tana maiko babu damar sosawa dan Uncle Bash mugu ne daga sunyi motsi zai zabga musu bulula sai da ya tabbatar sun galabaita sannan ya basu umarnin mi'kewa aikuwa a lokacin wata daga cikinsu ta yanke jiki ta fad'i iskokai suka tashi Uncle Bash ko a jikinsu ya bar gurin....Malamai mata sune suka taimakawa yarinyar ta dawo daidai sai kuka takeyi......Koda Uncle ya samu labarin abinda yake faruwa yace."Maza a kira direbansu a waya yazo ya dauketa ya kaita gida.

Tun daga ranar da wannan al'amari ya faru kowa ya tsorata masu shafa man bleating suka daina masu shirin farawa suk daina nima dana siyo nawa na ajiye ina jin tsoron shafawa.



*****
"Babangida naga kamar sauri kake ka zauna akwai maganar da nake so mu tattauna da kai."Hajia Sabuwa mahaifiyarsa itake wannan maganar.

Agogon dake daure a hannunsa ya duba a nutse yace."Hajia duk Uzurin da nake dashi ai dole na saurari naki.''

Tayi murmushin jin dadi tace."Babangida shiyasa nake alfahari da kai domin kuwa kana min ladabi da biyayya akan komai." Murmushi ya gyara zamansa da fadin." Ina sauraranki."

Tace."Ina fatan ka fahimci Munufar yarinyar nan Fadila akan ka."? Ya kalleta yana neman karin baya ni.'' Ta gyara zama fuskarta babu walwala tace."Fadila dai sonka take kuma ta jima da fad'a min sanin halin ka yasa ban nema ka da maganar ba sai yau naga ya dace na fad'a maka hukuncin dana yanke akan ku Hausawa suna cewa gida bai koshi ba to kuwa ba za a kaiwa dawa ba saboda haka ga Fadila nan itace macan da na za'ba maka a matsayin matar da zaka aura."
Cikin wani irin yanayi ya dago kansa yana kallonta Yace...........


*A taimaka da Shearing*





_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[7/27, 12:17 PM] Bintu🍒: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*25&26*
"Hajia Babu Fadila kwata-kwata a cikin tsarin rayuwata bana sha'awar auran zumunci dan Allah ki janye wannan kudirin naki." 'Bata fuska tayi tace."Babangida kaifa yanzu ba yaro bane ka kai matakin aure har ka wuce shekaru talatin da biyar ba kadan bane duk sa'onin ka sunyi aure amma kai kana zaune ko sha'awar auran ma ba kayi wai shin ko dai baka da lafiya ne."?

Girgiza kanshi yayi cike da damuwa yace."Hajia shi aure lokaci ne ki daina damuwa sannan ni lafiyata lau kawai lokaci ne beyi ba amma tunda kinyi magana yanzu zan fara duba matar aure amma inaso ki janye maganar Fadila dan kwata-kwata bana sha'awar auranta.

Tace."To shikkenan tunda kace haka yanzu zuwa wane lokaci zaka kawo min matar auran naka." Shuru yayi yana nazari tace."Kayi shuru kai nake saurare.'' Yace."Ki bani lokaci zan duba." Murmushin takaici tayi tace."Babangida wannan itace damarka ta karshe idan baka kawo min matar aure ba to babu shakka Fadila ce uwar 'ya'yanka."

Mikewa yayi babu walwala a tare dashi yayi mata sallama ya fita ta bishi da kallo tana girgiza kai tabbas idan ba tayi masa da gaske ba to haka zai ta zama babu aure duk ga abokanansa da 'ya'ya amma shi yana zaune.

Koda Maigidan ya dawo ta sheda masa hukuncin data yanke sai ya nuna farin cikinsa yace."Fadila yarinya ce mai tarbiya da nutsuwa kuma 'yar uwarsa ce akan ya fita ya dauko wata to gwara ya aureta.'' Cike da farin ciki tace."Nima abinda nayi tunani kenan sannan kuma zumuncinmu da 'yar uwata zai kara karfi." Alhaji Sabo yace."Kwarai kuwa Allah ya tabbatar da alkairi.'' Ta amsa da ameeen ya Allah.


*BAYAN WATA BIYU*
Shahid ya siya min waya kamar yanda ya fad'a kuma duk abinda ya samu yana rawar jiki zai kawo min hidima babu irin wacce ba yayi min Innah ta dinga bala'i tana fadin ita ta gaji da wannan shashancin bata neman fitina sai kawai na yanke shawarar a duk lokacin da Shahid ya kawo min wani abu bana shiga dashi gidan gidansu Samira nake 'boyewa wasu muyi amfani dashi wasu kuma mu siyar mu kar'bi kudin mu kashe.....Magulmata sukaje suka kai wa mahaifiyarsa gulma da irin facakar da yake min da kudi.

Iya Mari ta fusata ta kumbura yana shiga gidan ta rufeshi da fad'a ta inda take shiga ba tanan take fita ba yace." Iya Mari kiyi hakuri ki daina wannan fad'an maganar aure tsakanina da Surayya tayi nisa domin Baba ya sani kuma sun tsayar da magana da Babanta yanzu ana jira nan da shekara daya lokacin za tayi Candy sai a daura aure.

Ajiyar zuciya ta sauke tace."To yanzu naji magana ai na dauka babu wata tsayayyar magana a tsakaninku kake kashe mata kudi a banza.

Girgiza kansa yayi yace."Akwai magana mai karfi a tsakaninmu.'' Tace."To Allah ya sanya alkairi yanzu sai ka tsagaita dayi mata hidima ka fara kokarin gyara gurin da zaku zauna.

Yace."Inna Mari da inaso na fita na kama haya ne." A fusace! tace."Ashe baka da hankali Shahid yanzu duk girman gidan nan ka rasa gurin zama a cikinsa babu inda zakaje a cikin gidan nan zaka zauna kamar 'yan uwanka." Yace."To shikkenan Innah haka za'ayi." Abinci ta bashi ta zauna sai fada take masa shi dai abincinsa kawai yake ci yana gyada kansa inda sabo ya saba da masifarta.

****
Ganin yanda wasu da cikin 'yan ajinmu suka manta da abinda ya faru yasa nima na dauko White scret d'in dana siyo na fara laftawa a jikina da fuskata cikin ikon Allah sati guda fuskata tayi haske nayi ta murna ina jin dadi sai dai duk shafawar da nake a hannuwa da kafafu na ba suyi haske ba. Nace."Samira bana so fuska tayi haske jiki ba'ki kamar wata 'kazama.''

Dariya tayi tace."Sai a hankali ai kedai ki cigaba da shafawa ai baki da matsala tunda kina da Shahid." Murmushi nayi nace."Samira wallahi Shahid mugun tausayi yake bani sai ci masa kudi muke alhalin ba sonsa nake ba.

Tana dariya tace."Rabu da shashasha mara wayo kawai ai wasu mazan sune suke janyowa kansu suna da kudi iyayensu basu isa suci ba sai 'yan mata ni wallahi bana tausayinsa.

Nace."Allah ya kyauta dai kwana biyu bamu waiwayi Uncle ba yau mu rubuta masa text mai zafi."

Tace." To shikkenan me za'a rubuta."? Wayar na kar'ba daga hannunta ina murmushi lumshe ido nayi tare da saukar da ajiyar zuciya na fara rubuta text din ina jin wani zazzafan feelings a tare dani.

Bayan na gama rubutawa na mika mata wayar a sanyaye nace "Karanta." Ta karba da sauri tana dubawa.

Ta kalleni da mamaki a tare da ita tace."Ke Surayya ki goge wasu abubuwan kamar bai dace ba." Harararta nayi nace."Dallah ki tura masa ni babu abinda zan goge.'' Murmushi tayi tace."Surayya kenan wallahi ni abin ma dariya yake bani.

Tsaki naja nasa hannu da niyyar kwace wayar ta janye da fadin.'' Bari a tura masa tunda kince ba zaki goge ba." Ajiyar Zuciya na sauke lokacin da naga text din ya tafi nace." Tashi muje mu sayi abinda zamu ci." Wayar tasa a jaka ta mike muka bar gurin.


Lokacin da ya karanta text din sai da tsigar jikinsa ta tashi abinda ya kwana biyu bai Ji ajikinsa ba ya tashi Sha'awa mai tsanani ta tayar masa hakika text din ya tayar masa da hankali mutuka......Ga abunda yake rubuce a text din.

_Assalamu alaikum Habibi ina fatan kana lafiya to Allah yasa haka ameeen. Nice dai wannan mayyar mai nacin sonka da begenka ba zan gaji da fad'a maka cewa kai d'in kaine rayuwata dan kai aka hallice ni shiyasa yau nake so na tabbatar maka da cewar kaunarka da sha'awar ka su zasu zama ajalina Jiya nayi mafarki muna bargo daya muna rayuwar aure kana cikin biya min bukata na farka daga bacci yanzu haka ina cikin mawuyacin hali cikina sai ciwo yake mara ta tana ciwo Breast d'ina suna bukatar agaji daga gurinka tun asubah nake kwance ina murkususu saboda sha'awarka Mylov my heartbeat kayi wani abu a kaina kada na rasa rayuwata._
*Daga S-R-Y*

Cikin mutuwar jiki ya mika hannu ya dauki wayar text din yake nanatawa.......Da sauri ya mike yana bin harufan da kallo *S-R-Y* yau dai sai yayi binkice akan al'amarin.

Ya jima yana mamakin abin *S-R-Y* Yana nufin Surayya ya tsirawa kasan kafet ido yana nazari da tunanin akan yarinyar a iya tunaninsa yarinyar bata da wayon da za tayi wannan shaid'ancin yafi zargin wata Surayyan ba ita ba amma dai zai tsaurara binkice akan al'amarin.

Number ya kira yasa wayar a kunnansa....Lokacin muna kokarin shiga Class gabanta na faduwa ta nuna min. Naja hannunta muka 'boya a bayan bishiyo kar'bar wayar nayi nasa a kunnena amma banyi magana ba. Muryarsa ce ta doki kunnena na zabura! wayar ta kusa faduwa. shuru nayi jikina duk ya mutu.

Yayi gyaran murya da fadin."Surayya ko ba da ita nake magana ba."? Shuru nayi gabana na dukan uku-uku......Murmushi yayi sai naji wani yarrrrrr! na zube kasan ciyayi ina sake makale wayar a kunnena.

A hankali yace."Ina samun messages d'inki nagode kwarai kina wane gari ne."? Shuru nayi jikina sai kyarma yake...........Ya cire wayar daga kunnanshi yana dubawa yace."Surayya kina jina." ? Da sauri na kashe wayar ido jawur! na zuba mata ido. Tana dariya tace."Alhamdulillhi Nasara ta fara samuwa.'' A sarqe nace."Samira ina jin tsoron ya gane nice."


Tace."Ki cire tsoro kawata ai soyayya ba karya bace yanzu dai tunda har mun samu ya fara amsa mana sai mu sake zage dantse." Na mike ina karkad'e jikina nace."Gaskiya ne wallahi ba kiji farin cikin da nake ciki ba Samira nagode ke d'in 'kawar amana ce ina alfahari dake." Murmushi tayi tace "Muje kawai kada wannan masifaffiyar malamar ta shiga ajin.

Muna fitowa daga tsakanin ciyayi muka hangoshi can saman baranda da waya a hannunsa yana dubawa......Cikin sauri nace." Samira yi maza ki boye wayar hannunki ga Uncle can saman baranda.....Hannu na rawa take kokarin sanya wayar cikin jaka aikuwa ta fadi a gurin.....Cikin tashin hankali na kareta ta tsuguna da sauri ta had'e wayar tasa a jaka.

Duk abinda suke yana kallonsu kuma ya fahimci abinda suke 'boyewa abin ya bashi mamaki mutuka ashe duk tsaurin sa da jajurcewarsa akwai masu karya masa dokar makaranta Lallai sai ya kara tsaurara tsaro don ya lura masu bleaching sun dawo har da ita yarinyar da yake zargi duk da ba wani cikakken kallo yake mata ba amma ba haka ya san ta ba ita din baqa ce amma cikin kwanakinan ya ga fuskarta tayi haske lallai dukkaninsu zasu ci ubansu.

Sai da ya bari kowa ya sankankace ya saki jikinsa ya shedawa Uncle Bash abinda yake ayi Ranar litinin a gurin Assembly Uncle Bash yayi mana bazata gabadaya ya fito da mu mu kusan Talatin da bakwai aka taru a guri guda sai zazzare ido muke.

Ana tashi daga assembly ya tasa 'keyar mu zuwa ofis din mai gayya mai aiki.....Ni dai rasa bakin magana nayi ina jin sauran 'yan uwana suna ta surutai ko wacce tana kare kanta bakina ya mutu muna zauna muna jiran fitowarsa.


Tunda ya fito na kasa dauke idona daga kanshi yana sanye da kananun kaya wanda sukai masa mugun kyau as'usul kamar koda yaushe idonsa sakaye da farin gilashi ya dinga bin mu da kallo yana girgiza kansa wasu daga cikinmu har sun fara kuka suna bashi hakuri Uncle Bash yana tsaye a gefe da murtukekiyar bulala a hannunsa.

Babu walwala a fuskarsa da maganarsa yace."Wato kune gagararrun makaranta ko."? gurin yayi tsit!!! Ya cigaba da cewa." Anyi-Anyi daku ku daina abinda kuke amma saboda taurin kai kunqi shin wai don ubanku waye yake siya muku man bleaching ne."?

Kowacce tayi shuru yace."Na san dai da yawa daga cikinku samari ne suke siya musu ko ba haka bane."? Babu wacce tayi magana a cikinmu.

Yace."To yau idan akwai wacce ta shirya tayar da sarkin aljanu a makarantar nan ba zan fasa hukuncina ba." Ya kalli Uncle Bash da fadin." Bashir inaso da wannan bulalar ta hannunka ko wacce kayi mata ciki ashirin sannan ka kai su fuskar rana ka ajiye har a tashi.

"Uncle don Allah kayi hakuri wallahi mun daina don Allah uncle ka gafarce mu." Kujera ya nema ya zauna ya dora kafa daya kan daya babu fara'a ko ta kwabo a fuskarsa yace."Bashir ka fara aikin ka."

Uncle Bash ya murtuke fuskarsa ya gyara bulalar ta kan Samira ya fara ta dinga ihu! tana kokarin rike bulalar yana fuzgewa sai da yayi mata ashirin ciff! sannan ya fara laftawa ta kusa da ita.....Ofis din ya kaure da hayaniya da koke-koke da bada hakuri.......Ganin an kusa zuwa kaina sai hawaye suka kwace min na dinga sanya gefan hijabina ina gogewa jikina sai karkarwa yake......Ta gefan ido yake kallon duk abinda take ya dauke kansa tare da kokarin barin gurin.....Gurfana nayi gabansa murya na rawa nace."Uncle don Allah kayi hakuri wallahi ni bana bleaching haka kalar fatata take."

Ido ya tsira min fuska a had'e yace."Sakar min kafafu.'' Da sauri na saki dan ban san ma sanda na rike masa kafa ba.....Ofis d'insa ya bude ya shige abinsa.


Lokacin da Uncle Bash ya fara lafta min bulalar daskarewa nayi a gurin na takure jikina guri guda hawaye na zuba Uncle Bash a ko'ina duka na yake yi lokacin daya zabga min bulalar a kirjina na zabura da sauri na rike bulalar hawaye na karakaina a fuskata nace."Uncle Bash kayi hakuri ka dube fuskata da kyau wallahi sharri akai min bana bleaching. "

Ya fizge bulalar a zafafe! yace."Don Ubanki waye yayi miki sharri? ga zahiri nan fuskarki tafi jikinki haske sai naci ubanki yau." Ya daga bulalar zai zabga min na kurma wani uban ihu!!! na fad'i a gurin ina makyarkyata Uncle Bash ko a jikinsa ya zabga min bulalar hannunsa kan nonowana." Rintse idanuwa nayi ina kiran sunan Allah............... Hankalinsa a tashe ya fito ganinta a sheme a kasan gurin tana rike kirji sai hankalinsa ya tashi da sauri yace."A'ina ka dake ta ne."? Uncle Bash na huci! yace."Yallabai a jiki na doke ta kamar yanda na doki sauran 'yan uwanta."

Ya kalleni na sake lanjarewa a gurin ina janyo numfashi da kyar cikin kuka nake kiran wayyo kirjina zan mutu na shiga ukuna."


Hankalinsa gabadaya ya tashi ya kalleshi rai a bace yace."Ka doke ta a wani gurin da za kayi mata lahani ka san inda zaka dinga hukunci." Yace."Insha Allah za'a kiyaye." Hankalinsa a kaina yace."Kaje dasu ka basu horon dana ce." Da sauri ya amsa tare da kokarin barin gurin..........Ina kwance ina kallonsu ko wacce ta ta tashi tana matse fuska suka bi bayansa.

Ya kalleni da fadin."Tashi zaune." A raunane nace."Uncle ba zan iya tashi ba Kirjina ne yake zafi." Ya zuba min ido babu kiftawa. rintse idona nayi gabana na faduwa! maganarsa naji dab dani sai nayi saurin bude idona na ganshi tsugune a gabana ya k'urawa kirjina ido.....A zabure na mike zaune ina zazzare ido. harara ya watsa min da fadin." Kika ce ba zaki iya tashi ba." Shuru nayi ina kallonsa ya gyara fuska da fadin." Waye yake siya miki man bleaching...........!


*A taimaka da Shearing*





_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[7/28, 6:59 PM] Bintu🍒: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*27&28*
Diriricewa nayi na fara inda-inda! ya buga min razananniyar tsawar da ta kusa sa fitsari ya kufce min murya na rawa nace."Uncle ka dube ni da kyau wallahi bana shafa man bleaching ni tun asali haka kalar fatata take.

Ya tsira min ido da bacin rai a fuskarsa yace." Don Ubanki! makoho zaki mayar dani kome."? Jin zagin daya kurma min yasa jikina ya mutu sai na sunkuyar da kaina hawaye na nema ya 'kwace min.....Ya cigaba da cewa." Kin raina Allah har kike rantsewa dashi ko."? Uffan ban ce ba sai kokarin mayar da hawaye nake. Yace."Zaki fada min wanda yake siya miki man bleaching ko kuwa."?

Murya na rawa nace." Babu kowa ni haka skin d'ina yake." Da azama! ya mike nayi saurin kallonsa gabana na faduwa naga ya dauko bulalar Uncle Bash. Da sauri na mike Tsaye ina zazzare ido jikin bango na makure Jikina hawaye kuwa kamar an kwance famfo murya na rawa nake bashi hakuri.

Rai a bace yace." Zaki fad'a min ko kuwa."? Hanci na shaqa cikin inda-inda nace."Saurayina ne sunansa Shahid." Ido ya tsira min. Nace."Wallahi da gaske nake shine yake siyo min kayan kwalliya." Babu sukuni yace."Ashe har kinyi girman da zakiyi samari."? shuru nai tare da sunkuyar da kaina ya girgiza kai cike da takaici yace."Babu mamaki tunda kina tare da wad'annan yaran marasa kunya zakiyi abinda yafi haka to wannan shine na farko shine kuma na k'arshe kada ki kuskura ki kara shafa man bleaching ki bar hallitar da Allah yayi miki komai ba'ki da muninki ba zaki rasa mai auranki ba rashin wayo da dubara shine yake cutarku kuyi ta shafe-shafe saboda wai ku samu mazajen aure to wannan ba dabara bace saboda haka ki kiyaye ni wallahi daga yau kada ki sake shafa man karin haske idan kuma kika sa'bawa umarnina sai nayi miki mummunan hukunci."

Cikin mutuwar jiki gami da dana sani nace."Uncle kayi hakuri don Allah insha Allah ba zan kara shafawa ba."

Hanya ya nuna min da hannu alamar na tafi....Da sauri na sanya takalmana nayi gaggawar fita daga ofis din.

Can bakin band'akuna na hangosu a gurfane hannu a sama fuskokinsu a idon rana da saurin gaske nayi nufin sanja Hanya wata 'yar ajinsu Samira ta gan ni ta nunawa Uncle sunana ya kira na dawo da baya yace."Zo don ubanki ki shiga cikin 'yan uwanki." Tamkar na kurma ihu! saboda bakin ciki naje nasa gwiwata a kasa tare da daga hannuwa sama kamar yanda sauran sukayi.


Ranar nan mun galabaita mutuka mutum kusan bakwai suka tada aljanu Uncle Bash ya rabu dasu sukayi suka gama suka tashi Sai da aka tashi sannan Uncle Bash ya kyalemu muka tafi gida tun daga ranar kowa ya kiyaye saboda Uncle ya tsananta da yawa ya hana bleaching ya hana zuwa da waya bayan haka ya kafa dokoki masu tsauri yanzu karatu muke sosai babu wasa dan idan ka sake aka samu wani kuskure ta gurinka to kashin ka ya Bushe gurin Uncle Bash.

****
Muna daf da zana jarrabawar Nyco Shahid yazo min da wata magana raina a bace nace."Kaga Shahid ni don Allah ka kyale ni naji da abinda ya dame ni jarrabawa ce a gabana kai kuma kazo kana min wata magana nifa ko nayi Candy ba aure zanyi ba karatu zan cigaba dashi.

A sanyaye yace."Haba Surayya ya zaki karya alkawari kuma. Kada fa ki manta shekara guda mukayi dake a kancewa kina gama secondary za'ayi maganar aure amma yanzu sai ki sanja magana.

D'auke kaina nayi ina kallon hanya ni sam ba wannan damuwar ce a gabana ba burina kawai Uncle yace ya sona da aure. Yace."Surayya kinyi shuru baki ce komai ba alamu ya nuna kin amince na turo da sadaki na.

Wani banzan kallo na watsa masa da fadin " Aa ni kada ka turo kowa na fada maka ba yanzu zanyi aure ba sai nayi degree. "

Murmushin takaici yayi yace."Surayya kenan kin san wahalhalun karatu kuwa? ko kina da

Please Login or Register in order to submit comment