You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*
*07084653262*
*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*
Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp


Cikin wani irin yanayi na damuwa ta shiga gidan ta samu Innah na bakace gero kusa da ita zube sai kawai ta fashe da kuka wannan masifa ta isheta.

Innah Habiba ta ajiye fefan hannunta cikin fargaba tace."Ke menene haka babu sallama kawai kin shigo gida kin fashe da kuka.

Rufe fuskarta tayi da hijab ta cigaba da rizgar kuka tana neman daukin Ubangiji a cikin ranta babu shakka soyayyar guy itace ajalinta.

Innah Habiba ta rike hannunta murya na rawa tace."Me akayi miki Surayya wani ne abu ya faru a makarantar."? Shuru tayi ba tace komai ba sai shashshekar kuka takeyi.

Innah Habiba ranta ya baci ta buga matsa tsawa da fadin." Bafa nasan sakarci kin san halina bana daukar shirme ki bude baki ki fada min abinda yake faruwa.

Murya na rawa tace."Wallahi Innah ina tausayawa Babana da ina da yanda zanyi da na hana shi zama a cikin rana yana wannan sana'ar ta wuta."


Innah ta girgiza kanta cikin damuwa tace."Surayya ya za kiyi da ikon Allah kowa akwai hanyar abincinsa ki godewa Allah da ya bawa mahaifinka rai da lafiyar da yake fita ya nemo mana abinda zamu ci ai kowa da inda Allah ya ajiyeshi.

Ajiyar zuciya ta sauke tana girgixa kanta abubuwa da yawa sun taru sunyi mata yawa gashi bata kwanjin da za tayi maganinsu.

Tace." Yau Naga kin dawo da wuri.'' Tace."Sunyi korar kudin makaranta." Innah tace."Ikon Allah ashe har lokaci yayi.'' Tana goge fuskarta tace." Eh Innah wata uku ai kamar yau ne.''

Innah tace."Allah ya kyauta yanzu ya kukayi da malam din.''? Tace." Da har ya dauko dubu daya ya bani yace na kai musu zai cika sauran wani satin sai kuma Uncle Nuraddin yace na dawo gida."

Innah Habiba tace."To Allah yasa alkairi ne sai ki cire kayan makarantar kizo ki siyo mana Man gyada yau burabusko nake so nayi.

Ta 'bata rai da fadin." Nifa ina wallahi bana san cin wannan abin ke kuma baki da abinci sai shi.

Tace."Surayya a yanda kike fingi-fingi irin wannan cimar ce ta dace dake domin ta gina miki jiki amma ke na lura bakya so kinfi ga kayan kwadayi da kwalama."

Shuru tayi tana zumb'ura bakinta Innah tace."Gobe idan Allah ya kaimu sai ayi dambu ko bakya so." Ta'be bakinta tayi tace."Innah ai har gwara shi akan wannan burabuskon." Murmushi kawai tayi tace." Allah dai ya dauke ki ya kaiki gidan hutu da jin dadi sai kiyi abinda kike so.'' Babu kunya ta amsa da ameen ta mike ta nufi daki domin cire kayan makarantar jikinta.


Cikin tsabta ta fito da hijab mai mayafi a jikinta Ta kalleta da murmushi a tare da ita tace."Kwana biyu naga sai girma kike ko dai na kusa samun suriki ne."?


Dariya ta kyalkyale dashi tana boye fuskarta cikin hijab tace."Ke Innah."

Innah Habiba tana murmushi ta mika mata kudin da fadin." Man gyada zuryan zaki siyo gwangwani biyu sai ki siyo kuli-kuli gwangwani d'aya."

Ta kar'bi kudin da fadin.'' To shikkenan Innah sai na dawo." Tana kokarin fita ta kira sunanta ta juyo tana kallonta fuska babu walwala tace."Kada fa ki shiga gidansu Samira nasan halinki." Tace."Ba zan shiga ba ai." Tace." Na dai fada miki idan kika shiga zamu 'bata dake." A sanyaye ta fita daga gidan.......Tasan halin mahaifiyarta mafadaciya ce sam Innah Habiba bata daukar raini ko ga waye tana zaune a matsayinta na talaka bata nema a gurin kowa ba sai a gurin Allah kuma kullum cikin neman na kanta take ko a makota bata yarda wani yaci mutuncinta kullum cikin takatsantsan take.


Aikuwa kafin taje gurin siyo man sai da ta shiga gidansu Samira suka dasa hirar samari kamar yanda suka saba tana murmushi tace."Samira kin san me."? Tace."Sai kin fada.'' Tace." Dazu bayan mu rabu dake naje bakin titi gurin Baba domun kar'bar kudin makaranta kawai sai Uncle Nura yazo gurin a cikin motarsa........Duk abinda ya faru ta fada mata.

Samira ta zabga gud'a da fadin." Wallahi sakon mu ya fara isa gare shi tunda har kika ga yana miki kallon kasan ido kuma yace ki koma gida zai zo su tattauna da Baba to babu shakka sonki yake.

Cikin farin ciki tace."Wallahi Samira lokacin da yake min wannan kallon ji nayi kamar naje na rungumeshi saboda tsabar shauki mtwws guy nan ya tafi da imanina."

Samira ta bata hannu suka tafa tace." Wallahi ai Uncle din ne ya had'u ko wace mace zata so ya zama mallakinta gashi miskili mai aji da nutsuwa ko da yake Surayya kema kyakkyawa ce kawai abinda yayi miki cikas baqi da rama amma dubi hancin ki dogo ga ido da uban gashi sai kace wata 'yar itofia."

A sanyaye tace." Allah ni kuwa bana ganin kyau na da har ina cewa ki sato min irin man bleecing da Ummiyo take shafawa naje na siyo nayi haske ko zai ga kyawuna.

Samira tace."Aikuwa Surayya zaki kyau wallahi nima ina d'an gogawa idan na fakaici idonta sunan man white scret yana da kyau sosai kuma bashi da tsada ki siya ki gwada.''

Tace."Aikuwa zanyi wa Malam Wayo na karbi kudi a hannunsa sai nazo muje ki rakani kasuwa na siyo.''

Tare suka je suka siyo man gyadar a hanyar su ta dawowa suka ci karo da Shahid ya fito zai tafi kasuwa a kan mashing dinsa d'an kasa.........Surayya ta sha kunu tana dauke kanta.

Shi kuwa ganinta duk sai jikinsa ya mutu ya dinga bin ta da wani irin kallo yana lumshe idonsa.

Samira ta tsaya tana masa magana ita kuwa gaba tayi tana zum'bura baki waye kuma Shahid idan da akwai su Uncle a guri


Samira da sauri ta iske inda take tace." Ke Surayya wallahi baki da wayo waye ya fada miki haka ake rayuwar duniya ai ko baka san mutum baka fitowa fili ka nuna masa kawai ki kwantar da kanki gurin Shahid kiyi masa wayo ki samu abinda zaki samu nasan dai Malam ba zaiyi miki auran dole ba to kawai kiyi lufff kici kudin Shahid tunda na lura bashi da wayo.

A sanyaye tace."Samira Idan bana san mutum wallahi abin hannunsa ma bana so shiyasa ki kaga bana sauraran Shahid."

Tace." Eh ai ba nuna masa za kiyi ba kawai dai ni ina baki shawara ne kiyi kwance-kwance kici kudinsa.

Tace."To shikkenan Samira zan duba maganarki." Da wannan hirar suka isa gidan.....Innah ta kallesu tana girgiza kanta abotarsu har mamaki take bata gashi sam ita bata so saboda sanin halin mahaifiyar yarinyar bata da kyau Hajara munafuka ce ga biye-biyen malamai da bokaye.

Samira bata bar gidan ba har sai da Innah ta sauke burabusko ta zuba musu suka ci tare sabida rashin kwaici irin na Samira sai da tambayi Innah wai ta zuba mata wani ta tafi dashi gida daddare za taci....Innah Habiba ta dauko sabuwar silba ta cika mata taf da burabuskon......Samira tayi musu sallama ta tafi gida zuciyarta fes yau da daddare ta huta cin towon dawan gidansu.




_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[7/22, 2:58 PM] Bintu🍒: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*15&16*
Malam na kokarin fita ta shigo gabad'aya gidan ya gauraye da wani masifaffan kamshin turare tana sanye da abaya baka tayi rolling da pink din mayafi kafarta sanye da takalmi mai tsayin dunduniya tayi ado sosai tamkar wacce za taje gidan biki amma kuma kallo daya kacal za kayi mata ka fahimci cewa bata da tarbiya dan tunda ta shigo gidan take wani ya tsine ya tsine tana taunar cingum sai kace tsohuwar karuwa.

Da yake dama can na san ta amma magana ta fatar baki bata ta'ba had'a ni da ita ba sai kawai na zuba mata ido ina kallonta da tunanin abinda ya kawo ta gidanmu.

Ledar hannunta ta ajiye kusa da Innah tana dauke kanta tace."Gashinan in ji Uncle yace a kawo kayan makarantar Surayya da sauran abinda zata bukata.

Malam yace." To masha Allah Yarinya ya sunanki." ? tana ta'be baki tace."Fadila." Sai kawai ta kama hanyar fita cikin wata irin tafiya irin ta marasa kunya. gabadaya muki bi bayanta da kallo......Innah tace."Amma gaskiya wannan yarinyar bata da tarbiya kuma daga gani ba 'yar Alhaji Sabo bace."

Ajiyar zuciya na sauke nace."Eh 'Yar kanwar Hajiyar ce sunanta Fadila sa'i da lokaci tana zuwa hutu gidan nima a bakin Samira na sani wai gidan mahaifinta na can ungwar fagge."

Innah tace."Koda naji dama ai unguwar tayi k'aurin suna da marasa kuny......Malam ya katse ta hanyar fadin." Habiba bana son kananun magana ya isa haka yaran yanzu sai addua iyayensu na tarbiya suna watsar wa ke dai kawai kiyi addua.

Cike da takaicin abinda yarinyar tayi tace."To shikkenan Malam Allah ya shirya mana zuria." Ya amsa da ameeen ya yana kokarin tura kekensa.

To koda na bude ledar Kayan makaranta ne a ciki da littafai gami da dukkanin abinda zan bukata ba tare da 'bata lokaci ba na zuba duka littafan cikin jaka na kwashe kayan na kai daki ina Allah-Allah Monday tayi na fara zuwa makarantar sai dai kuma nasan zanyi kewar Samira tunda da ita nake zama komai namu a tare yanzu kafin na saba da wasu zan sha wuya wata shawara na yanke ina ganin zan samu Malam da maganar domin itama Samira a nema mata alfarma tunda dai duk rabin makarantar tasa marasa galihu sunfi yawa.


Kallonta nayi a lokacin da take kokarin kulle kofar gidan nace."Innah wallahi tsoro nake ji kada muje gidan nan a wulakanta mu gashi kin dauko daddawa zaki kai musu.

Girgiza kanta tayi tace."Surayya wannan umarnin Malam ne nima bana san zuwa gidan sabida gudun zubewar mutunci dan dai ya matsanta ne kawa."

Nace."To dan Allah ki mayar da wannan daddawar da kika dauko me za suyi da daddawa su da basa towo.

Tace."Waye ya fada miki basa cin towo ai masu kudi a wannan zamanin daddawa itace take musu wuya shiyasa na yanke shawarar kai musu nasan za tayi musu amfani.

A sanyaye nace." Shikkenan Innah tunda kinqi daukar maganata muje kawai." Hanyar gidan muka nufa muna sake tattauna maganar.


Tana hakimce a kan kujera mai cin mutum daya mukayi sallama a falon. babu walwala a tare da ita ta amsa tana bin mu da wani irin kallo duk da tasan mu hakan bai sa ta saki fuskarta ba da hannu ta nuna mana gurin zama kasan kafet.

Muka zauna kusa da juna nice na fara gaisheta ta amsa tana yatsine fuskarta tace."Habiba warin me nake ji? daga shigowarku sai kace an bud'e shadda(masai).

Jikina yayi wani mugun sanyi dama nasan za'a rina. Innah na ya'ke tace."Hajia sabuwar daddawa ta kalwa na kawo miki kin san idan tana sabuwa haka take wari kafin ta bushe."


Ta wani ya mutsa fuskarta da fadin." Ni nace miki ina bukatar daddawa."?

Innah jikinta yayi sanyi sai ta sunkuyar da kanta kasa. ta cigaba da cewa " Me yasa wai mutane suke haka ne? ni tunda nake ma ban ta'ba amfani da daddawa a miya ba me za'ayi da kayan wari kuma ma ko bukatar daddawar nake me zanyi data hannuniki."

Idanuwa na suka ciko da hawaye kafin ma nayi wani yunkuri su kwace suka shiga sauka a saman fuskarta. Murya Innah naji tana fadin." Hajia Kuturta ce dani da ba zaki bukaci abin hannuna ba a zato na wanda yayi ki shine yayi ni kuma babu wani wanda ya fifita akanmu sai wanda yafi bauta masa."

Hannu ta daga mata a fusace tace." Kinga Habiba dama kin saba mayar min da magana yanzu me ya kawo ku gidana."?


Innah ta girgiza kai cikin takaici tace." Hajia kin san hausawa suka ce yaba kyauta tukwici idan baki manta ba duk lokacin da yaron ki yayi mana abin alkairi Malam yakan turo ni nazo nayi muku godiya to wannan karon ma godiyar muke tafe da ita."


Tsaki taja da fadin." Da kun sani kunyi zamanku wallahi domin wannan zuwan naku ya janyo min bacin rai duk wani abu da Babangida yake muku yin kansa ne shi yayi
Niyya sabida haka ku dai na zuwa kuna damuna don Allah.

Innah tace."To ai shikkenan Hajia tunda bakya bukatar mu zamu daina zuwa inda kike dama kuma saboda karamci da mutunci yasa muke zuwa inda kike amma insha Allahu daga yau mun daina zuwa gidanki.

Tabe bakinta tayi ta dauke kanta daga kan mu. A sanyaye nace." Innah tashi mu tafi." Ta yunkura ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta tace."To Allah ya bamu alkairi." Inda muke bata kalla ba ballantana mu samu amsa. Jiki a mace muka fita daga gidan.



*MAR'ATUS-SALIHA*
_(Itace Cikakkiyar Mace)_

*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu👫 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*
1- Maganin Sanyin mara
2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa
4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba
5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa
6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa
7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)
8-Maganin Basir mai tsiro
9-Maganin Basir mai kulle ciki
10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)
*11- Maganin Karin Ni'ima
12- Maganin K'iba mai kyau
13- Maganin Cikar Nono (Breast)
14- Maganin Hips
15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!
16- Maganin Matsi mai kyau
17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)
19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba


*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*
*07084653262*
*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*
Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.
*07084653262*


Ko a hanya da muna tafiya kasa tsayar da hawayen idona nayi saboda tsabar bakin ciki me za'ayi da wasu masu kudin kwata-kwata Hajia Sabuwa ba ta san meye mutunci ba ai arziki na Allah ne sai yaso yake bawa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso ba wai dan ba ya sonsa ba tunda iyayena suka haife ni ban ta'ba tsintar kaina cikin halin k'unci da damuwa irin na yau. Na tsani aci mutuncin iyayena ko kadan amma babu komai rayuwa ce.

Tana kokarin bude kofar gidan tace."Ai sai kiyi shiru haka ni ai wulakancin Hajia Sabuwa ba sabo bane a guri na."

Nasa hannu na goge fuskarta a sanyaye nace."Wallahi ji nake tamkar zuciya ta za ta fashe banta'ba tsammanin rashin mutuncin matar ya kai haka ba. ko da yake Inna kema kina da laifi tunda sai da nace miki ki ajiye daddawar nan amma kikayi fir kinga kin janyo mana cin mutunci.

Girgiza kanta tayi tace."Surayya ko da daddawa ko babu dama hajia Sabuwa 'yar cin mutunci ce saboda haka wannan al'amarin ya daina 'bata miki rai kiyi hakuri saboda d'anta Nuraddin.


Ajiyar zuciya na sauke nace."Shikkenan Inna Allah yayi mana maganin abinda ya dame mu." Ta amsa da "Ameeen ya Allah haka nake so ki kasance mai mayar da al'amuran ki ga Allah.


To koda wasa da Malam ya dawo ba mu fada masa abinda ya faru ba gudun bacin ransa duk dai shi ya kasance mutum ne mai saukin kai da mayar da komai ba komai ba amma dai tilas yaji irin cin zarafin da matar tayi mana ransa ba zai masa dadi ba.



Washe garin ranar da yake Juma'a ce sai nayi ado sosai nace." Innah don Allah zanje gidansu Samira.

Ta kalleni da fadin." Surayya nifa bana san yawo ina ce shekaran jiya kike je gidansu ita me yasa bata zuwa sai ke."?

A sanyaye nace."Innah kin san suna aikin awara shiyasa babarsu bata barin ta fita." Tace."Ayyo kece kenan mara aiki to babu inda zaki ki nemi guri ki zauna."

"Innah don Allah ki bari naje wallahi ba zan dade ba." Shuru tayi min ta cigaba da sabgarta na cigaba da yi mata magiya tace." Kije amma kada ki dade kinji abinda na fada miki ko."?

Da sauri nace."Eh insha Allahu zan dawo da wuri tace." To a gaishe da mutan gidan." Ina 'kokarin fita na amsa da zasuji."

Lokacin dana isa gidansu Samira suna shiryawa ita da Ummiyo za suje gidan bikin 'yar kanwar babarsu Nace." Samira idan ba zaku kai dare ba zanje." Tace." Eh to ya danganta da lokacin amma idan ana DJ zamu zauna muyi kallo. "

Nace." Ina ne gurin bikin."? Tace?" Rijiyar zaki ne." shuru nayi inaso naje amma kuma bana so na b'ata ran iyayena

Tace."Surayya ki daina tunani kawai idan zaki je baki da matsala damu idan magariba tayi kawai sai mu dawo."

Nace." To shikkenan muje." Ummiyo ta gama shiryawa tana sanye da wani material anyi mata wani irin dinki na banza fuskarta taci mai tayi gau! ta lafta hoda da bakin jan baki(daba-daba) kanta cunkus da attecement tayi daurin ture kaga tsiya kai kana ganin Ummiyo kasan idonta a bude yake.

Tana fesa turere ta kallemu da fadin." Idan kun shirya ku sameni a waje.'' Samira tace." Kaya na kawai zan sanya fa."Ummiyo na kokarin fita tace." Nace dai ku same ni a waje.'' Samira ta bita da harara bayan fitar ta tace.'' Mutsiyaciya kawai dama haka take duk sanda tayi kwaliyya sai ta fita ta zauna a waje tana nunawa maza."

Murmushi kawai nayi ina mamakin al'amarin Gidansu Samira sam babu tarbiya kowa abinda ya ga dama shi yake.

Atampa ta sanya riga da siket itama sun matse ta amma ba kamar na Ummiyo ba ta dauki karamin gyale tasa nace."Ke kuwa Samira ki sauya mayafi mana." Tabe baki tayi tace.'' Meye illar wannan din."?

Nace."Duba fa mazaunanki a waje ga siket din ya matse ki.'' Tace."Aikuwa wallahi ba zan sauya gyale ba domin shine mahadin kayan."

Girgixa kaina kurrum nayi na mike tare da gyara hijabin jikina ta kalle ni da fadin."Kema ai ya kamata kisa mayafi ki cire hijabin jikin ki tunda gidan biki zamuje"

Girgiza kai nayi nace."Samira kyale ni da hijabi na." Ba tare da damuwa ba ta dauki turare tana fesa wa ni kuma na fita daga dakin na tsaya ina kalle-kalle a tsakar gidan nace."Samira babarku bata nan ne.''? Tana kokarin fitowa tace."Eh itama taje gidan bikin amma na manya." Nace."Ayya shiyasa tunda na shigo gidan ban ji motsinta ba"

To koda muka fito sai kawai muka samu Ummiyo ita da wasu maza sai cafkewa suke sun sanyata a tsakiya sai hira suke tana kyalkyala dariya gashi mutane masu wuce wa domun tafiya massalacin Juma'a sai kallonsu sukeyi ni kaina al'amarin beyi min dadi ba Gabadaya Ummiyo bata da tarbiya da kamun kai.


Bakin titi muka fito domin samun abun hawa muna tsaye mu uku a jere muka ji horn a bayanmu da sauri muka juya...........Sai da fitsari ya kusa kufce min ganinshi yana sauke gilashin motarsa yana mana wani irin kallo mussaman Ummiyo da yake ji tamkar ya fito daga motar yaci mutuncinta.........A sanyaye na sunkuyar da kaina kasa gabana na wani irin fad'uwa mummunan kallon da yake mana shine ya kashe min jiki. mayar da gilashin motarsa yayi ya bar gurin. na sauke zazzafar ajiyar zuciya tare da tsirawa kasan gurin kallo.

Ummiyo taja tsaki da fadin."Wannan guy fa dan rainin hankali ne wallahi duba don Allah sai kace wanda yaga tumakai sai kallon banza yake mana."

Samira Murmushi kawai tayi tace."Ni kuwa guy birgeni yake wallahi kuma insha Allah ya kusa zama mijin kawata."

Ummiyo ta watsa mata wani irin kallo tace."A gidan uwarki ko an fad'a miki irin wad'annan mazan kowace irin mace suke aure."

Samira ta kyalkyale da dariya tace."Wallahi Ummiyo sai dai idan babu so amma idan so yana tasiri babu abinda za'a fasa.

Tace."Shashanci banza da wofi wannan ko wacece ta had'a kanta da wahala dan wannan guy da yake da masifar girman kan tsiya ba zai aureta ba."

Samira ta kalleni da fadin." Surayya kinji maganar da Ummiyo take ko.''? A sanyaye na daga kai gabadaya ni hankalina na kansa fuskarsa tana tayi min gizo da alama massalaci zai tafi dan yana sanye da farar shadda hade da farar hula da farin gilashinsa na qa'ida. yayi min kyau sosai sai dai yanayin fuskarsa shine kadai ke sanyayar min da gwiwa.


Wani mai babur ne yayi parking a gabanmu Ummiyo ta fada masa inda za muje ya fad'a mata abinda za'a bashi ba tare da 'bata lokaci ba ta bashi kudin muka shiga babur yaja muka dauki hanyar rijiyar zaki inda ake gabatar da shagalin bikin.




_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[7/22, 2:58 PM] Bintu🍒: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_






*MAR'ATUS-SALIHA*
_(Itace Cikakkiyar Mace)_

*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu👫 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*
1- Maganin Sanyin mara
2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa
4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba
5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa
6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa
7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)
8-Maganin Basir mai tsiro
9-Maganin Basir mai kulle ciki
10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)
*11- Maganin Karin Ni'ima
12- Maganin K'iba mai kyau
13- Maganin Cikar Nono (Breast)
14- Maganin Hips
15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!
16- Maganin Matsi mai kyau
17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)
19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba


*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*
*07084653262*
*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*
Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp




*13&14*
Bayan sallar isha'i yazo kamar yanda ya fada cewa zai zo su tattauna da Babana, tsuru-tsuru nayi a zaune a tsakar gida ji nake tamkar na zauna a tattauna dani cikin zuciyata sai nake ji tamkar zai ce da Malam yana sona da aure. Murmushin takaici nayi ina girgiza kaina nasan ko al'amarin zai tabbatu to sai an kai ruwa rana.

Fakaitar idon Innah nayi a hankali na mike na kamar hanyar fita inayi ina waiwayen bayana.

Jikin bango na lafe nasa kunne na domin naji abinda yake fada sai dai duk kwa-kwa

Please Login or Register in order to submit comment