You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kokarin mikewa da ta yi daga jikin nasa, ɗan riƙo hannunta ya yi yana faɗin "Baki bani amsa ba, na ce maki I love you" "Ni ban san me zan ce ba daddy" hannu ya kai ya matse mata baki yana faɗin "Idan kika sake cewa daddy sai na...." Bai karisar da maganar ba ya yi shiru tare da sakinta ya miƙe ya nufi waje yana faɗin "Gobe dai zaki fara zuwa school" daga nan ya fice abinsa, ita kuma tattare kayan ta yi ta bawa Irfan kulan abincin da miya sai plate ɗaya da spoon ɗaya, ta ɗauki wanda suka ci zuwa cikin gida.

Yadda ta bar aunty haka ta shigo ta same ta, Kitchen ta shigar da kayan sannan ta zo ta zauna tana faɗin "Aunty daddy ya ce gobe zan fara zuwa school" sai murmushi Aunty take yi ta yi mata fatan alkhari daga nan suka shiga duniyar hira tana bata labarin yadda zata rinƙa yi wa daddyn Jelly da shawarin da suka dace.

A wannan Hali Abbi ya dawo ya same su, sannu da zuwa suka yi mashi, abin mamaki sai suka ga ya amsa da fara'a ya kuma ɗaura da cewa "Ina A'afia? Akil ya kirani a waya ɗazun da safe akan ta wuce ta koma kafin ya zo ya yi mata ɗan banzan duka".

Cike da murnan Abbi ya sauƙo Aunty ta ce "A'afia ai bata dawo nan gidan ba, tun fa kwana huɗu da suka wuce da ta tafi gidan su Umaisha akan za su yi kwana ɗaya sai suka yi biyu, to ni daga ranar ma dana tambaya sai Irfan ya ce mani ta koma gidan da zama" wucewa Abbi ya yi ya nufi sama yana faɗin "E a gidan take dama, ina ga yaune ta fita ta ce masu zata zo nan, shine Akil ɗin ya ƙirani akan ta dawo, to na kira layinta ma a kashe, yanzu haka bai wuce tana tare da su Rufaidah bane, amma dai bari na kira Irfan ya je gidan su Rufaidah ɗin ya ɗauko ta ya mai da ta gidan yayan". Da zumuɗi Aunty ta amsa da to sannan ta tashi ta bi bayansa suka shige ɗaki a tare.

Ita kuma Ayla ta gyara kwanciyarta a saman sofa tana murmushi, idan ta tuna cewa daddynta yana sonta, kuma ya ce zai aureta sai ta ji wani mugun daɗi, baiwar Allah ita ma tana matukar son shi sosai da sosai.

(Uhm soyaya kenan, soyayya taburmar kaya, idan ka iya zama ka ji daɗi, idan kuma baka iya ba....😭💔)
[11/17, 12:27 PM] +234 906 579 6460: 💖💖TRIPLETS💖💖



*Idan kun samu typing error amin afuwa 👏 keyboard ɗin tana bani matsala sosai kwana biyun nan, to na yau ma ya fi tsananta, sai na danna A sai ya koma B😭*




🔥Washington DC🔥


Rai a ɓace Tga ya ɗaga shi sama ya buga shi da ƙasa, wani wahalallen ihu ya saki tare sa sakarwa Tga ɗin wayan nan kwarin nasu na Triplets.

Duk abin sa suke yi Lion na kallonsu ta cikin laptop nasa, abin da ya sanya bai shiga faɗar ba, yana son kallon a iya ina hankalin da kuma natsuwar Michael ta tsaya, sannan yana son sanin shin Michael zai iya kwatawa kansa yanci ne ko yaya, a lokacin shi kuma Imran ya shiga toilet dan yin wanka.

Ihu Tga ya fara yi yana bubbuge kwarin, amma ina kamar kara hura masu wuta akeyi, sai wani kara hawa kansa suke yi, suna bashi a jikinsa, da dai ya ga da gaske zasu lahana shi, sai ya kwasa da gudu ya bar wajen ya yi cikin gida.

Yana barin wajen jibga-jibgan sojoji biyu suka iso wajen, kowannan su ya ɗaki ɗaya, ɗaya ya ɗauki Michael ɗayan kuma ya ɗauki Musharraf dake a sume, kai tsaye cikin gida suka wuce da su.

Umarni Lion ya yi masu akan su kai su word room, haka kuwa suka wuce da su word room ɗin, saman kyawawa lausasan kuma tsadaddun gadajen dake a cikin word room ɗin suka kwantar da su, sannan suka juya suka fita.

Da fitarsu ba'a fi minti goma ba sai ga su sun dawo tare da manya-manyan likitoci sanye da kayan aikinsu, suna zuwa suka fara duba su.

Shi kuma Tga Lion ya dakatar da kwarin saboda suna da aiki gobe, yau za su bi jirgin dare zuwa Nigeria gobe za su yi wa wajen da James yake dirar mikiya, su tarwatsa kowa su fito da James, kuma Lion ya riga ya tsara cewa da Tga ɗin za'a yi tafiyar, idan ba ku mance ba kuma, baya magana ya canza, hakan yasa ya dakatar da kwarin, amma dai ya tanadawa Tga hukuncin da ta dace ya yi mashi bayan sun gama aikin da zasu yi na ɗauko James, ya zama dole ya hukunta shi saboda ya cutar da Musharraf, shi kuma baya goyon bayan a cuci mutun ba tare da ya yi maka komai ba, baya bin bayan zalinci ga koma wace addini.

A ɓangaren daddy da Uncle Herry kuwa, duk wannan badakala da ake yi a cikin gidan basu sani ba, suna can cikin lambu, dan dama mayun zama a lambu ne, hakan yasa aka yi masu katafaren lambu a gidan, dan su rinƙa sakata suna walawa son ransu.

Su kuma John da Jay basa nan, John ya tafi party, shi kuma Jay ya tafi yawonsa.

Wannan kenan abin da yake faruwa a Washington DC kenan, idan kuma muka koma wajen*JEHAN*

Wunin ranar Jehan da yunwa ta wuni, ta ki cin abincin dan ta ce lallai dole abin da ta ci shi Adiva zata ci, hakan yasa ta wuni da yunwa, dan sun ƙi yarda Adiva ta ci abincin.

Ganin haka yasa Jehan ta fara zargin lallai akwai wani abin dan gane da wannan abincin, ace lallai sai ita kaɗai za'a bawa kamar ba lafiya ba, sai tunani take a kan hakan har can yamma, su Aisha dai sun ci sun ƙoshi kayan su, sunci na safe da rana.

Da yamma sun yi wanka su A'isha anci uban kwalliya kamar yadda aka saba, an sha su eyelashes ga jambakin nan ba'a magana, kamar wata aljana haka ta zama domin ta lapta uban attachment a kanta.

Ita ma Jehan ta yi kwalli amma bata sanya irin su eyelashes da kunba kamar Aisha ba, simple make up ta yi kamar yadda Adiva ma ta yi, ita kuma Maryam baiwar Allah, ko kaɗan bata yi kwalliyar bama.

Ita kwata-kwata ma bata saki jikinta da kowa ba, da alama akwai ciwo a cikin rayuwarta sosai, ganin haka yasa Jehan ta Matso kusa da ita tana tambayarta ko lafiya.

Kamar jira take yi a tambayeta sai ta fashe da kuka, da sauri Adiva ta matso kusa da ita suka fara rarrashinta.

Sun ɗan jima suna rarrashinta sannan suka samu da kyar ta yi shiru. Ruwa Adiva ta ɗauko mata daga ɗan madaidaicin fridge dake a cikin ɗakin, dan ɗakin nasu kusan komai a akwai, duk gidan ɗakin su shine na uku a kyau, ɗaku nan hawa hawa ne, kamar yadda suma matan suke hawa hawa, akwai ɗakin yan 14 years, wadda ya fi kowanne kyau saboda su ne kananan yara, za'a jima ana zan zare da su, za su kawo kuɗi sosai, (a cewar Hajiyar daɗi fa tom, ba ni ba) Sai kuma ɗakin yan 15 years wadda suma nasu yana da kyau, sai dai bai kai na yan 14 years ba, dan yan 14 sune farko, daga shi sai na su Jehan, sai yan 17, haka ɗaku nan suke, na yan 14 katon freezer ne a ciki, da kuma manyan gadaje, yara su sakata su wala, kamar gidan ubansu, na yan 15 kuma mabi da shi ne.

Karɓar ruwan ta yi ta sha tana sauƙe ajiyar zuciya. Sai da suka barta ta ɗan huta sannan Jehan ta ce muna jin ki me ya faru.

Idonta cike tab da kwalla ta fara magana kamar haka, "Ni dai yar asalin garin Kano ce, kuma mu biyu iyayen mu suka haifa, ni da yayata wadda ita ma ta bar gida a yanzu haka, dan tare muka baro gida, wani iftilai ya afka mana mu ka rabu". A ƙage Jehan take da jin kan zance dan haka sai ta ce "Maza ki gaya mana da wuri"

(D.P.O ba wasa, akwai san jin kan zance da wuri🤣)

"Babana yana sai da rariya da itace a bakin kasuwar kauyenmu, yana da kuɗi sosai, saboda yana noma sosai da sosai, yana da dabbobi irinsu raguna, kuma kullum kara aihuwa ragunan nasa suke yi, sun yi yawa sosai ga awaki, amma duk da wannan tarin niimomi da Allah ya mashi, mun taso cikin bakar wahala, wai kawai dan saboda maman mu ta haifa mashi ƴaƴa mata, shi wai maza yake so wayan da zasu taya shi zuwa gona, hakan yasa ya rinƙa azabtar da mu da yunwa, ga duka da zagi, kyara idan muka zo kusa da shi, baya son ganin mu, maman mu tana shan wahala wajen neman abin da zata ba mu muci, yaya Asma'u ta sha wahala kamar ba zata yi rai ba, akwai lokacin da na kamu da rashin lafiya, kamar zan mutu, amma haka baba ya sa kafa ya yi fatali da ni, a wannan rana ma sai da ya yi mani dukan tsiya, bakin cikin yau da gobe yasa maman mu ta fara rashin lafiya, yan kauyen mu sun san baya bamu abin ci, amma basu san menene dalili ba, kuma sun yi mashi magana akan abincin, amma yaki canza hali, sai cewa ma ya yi babu ruwan kowa da gidansa, kowa ya yi harkar gabansa, maman mu kuma bata da mama sai babanta da matarsa, hakan yasa ta zaɓi zama a gidan mu da zaman gidansu, domin tasan ma ko taje sai babanta ya koreta saboda shi irin mutanennan ne ma su zafi sosai, baya ɗaukar maganarta gaskiya, kai in ta kai ce maki ma ko gidan ta je sai ya tambayi menene ya kawota, wani zubin ma daga kofar gida zai korata, ya ce ta koma gidanta, baya ma bari ta shiga cikin gida, haka muka yi ta fama da bakar wahala, kullun muna yawon neman abin da zamu ci, a haka har yaya Asma'u ta fara sata, lokacin da muka fara sanin daɗin abinci da sauransu kenan, yaya Asma'u tana shiga gidan mutane idan ta ga abu zata ɗauka ta gudu, ko abinci aka ajiye ta gani zata sace ta gudu, ta kawo mana mu ci, hakan ba karamin tayarwa da mama hankali ya yi ba, ya kara mata ciwo kan ciwo, akwai wata rana da aka biyo yaya Asma'u har gida, akan ta shiga gonar mutane ta saci masara kusan rabin buhu.

Har cikin gida suka biyota masu gonar, suka jata zuwa waje suka fara dukanta, sai kuka mama take yi tana basu hakuri, amma basu kyaleta ba sai da suka naɗa mata duka kamar za su kasheta, sannan suka kyaleta suka tafi, sosai mama tasha kuka, daga karshe ta ɗaura ruwan zafi a saman kiraren da muka samo, ta tafasa ruwan ta gasawa yaya kijinta.

A haka har nima na fara ɗaukar abin mutane, domin yunwa na neman kashe mu, dole idan munga abu mu ɗauka dan mu sami abin ci kada mu mutu, haka muke sata, duk abin da muka gani, ko da kuwa ba naci bane ɗauka muke yi saboda sabo da satar.

Akwai wata rana da na kasa mance wa a idona, wannan ta zama rana mafi muni a rayuwata, lokacin mun girma, ina da shakara 15 a lokacin, mun je kauyen kusa da mu biki, ana biki lokacin, muka ga kuɗin wata mata a jakarta ta ajiye, muka ɗauka muka gudo zuwa gida, ashe akwai wadda ta gammu, da akazo ana cikiya ana ta kalawa wasu daga cikin jama'ar wajen sharrin sata, abin har ya kusa haifar da faɗa koma nace maki sun yi faɗa da baki ba da hannu ba, daga baya wannan da ta ganmun sai ta gaya masu cewa mune muka ɗauka. Lokacin kuma har mun sai bread da kuɗin naira ɗari biyu ce, muna tsaka da cin bread ɗin muka ji hayaniya, daidai lokacin kuma baba ya shigo, dama ita mama tana ɗaki tana barci bata san me yake fatuwa ba.

Baba yana shigowa kawai ya ɗauki wani katon itace a cikin itacen da muke yo wa mama idan Allah ya bamu abin da za mu girka. Dukan mu ya fara yi da wannan itace yana tsine mana yana faɗin, tsinannu yan asara, ku tashi ku fice mani daga gida, ɗiyar banza ɗiyar bala'i, ku dai kun zame wa mutane annoba da bala'in , to dan ubanku sai ku tashi ku fita waje, bala'in da kuka jajumo suna can suna jiranku. A wannan hali mama ta fito ta same mu, kukan da muke yi ne ya tashe ta daga barcin ta, kuka ta fara yi tana kokarin kwace sandar hannun nasa, da karfi ya hankaɗeta ta yi baya baya ta faɗi kasa, mu kuma sai da ya yi mana duka sannan ya ja mu zuwa waje ya miƙa wa mutanen dake a wajen tare da gaya masu su yi mana dukan tsiya, domin mu bamu da aiki sai sata kullum, to shima ya ga ji da halin mu, haka jama'a suka hau dukan mu, bakin cikin hakan yasa mama ta faɗi ta mutu a wajen, wannan rana na kasa manta shi a rayuwata, haka suka yi mana dukan ɗari biyun su, bayan sun tafi muka dawo cikin gida da kyar, muna shigowa ni ban wani damu ba na nufi bread na da yake yashe a kasa, na ɗauka na cigaba da cusa shi a cikin baki na ina ci domin bala'in yunwa muke ji, ita kuma yaya Asma'u wajen mama ta nufa, da yake ta fini shekaru ita zata kai 18 years sai ta gane cewa mama ta rasu, mun gwammaci mutuwar mu a wannan lokaci da muka samu labari, ba karamin tashin hankali muka shiga ba, haka muka daure har sadakar uku na mama, a jama'ar unguwa, babu wanda ya kula mu, ko zaman makoki ba wanda ya yi wa mama, tun da aka je aka binneta shikenan, kuma duk saboda muguntar babana ne yasa ba masu kula mu.

Babban abin tashin hankali da ya jefamu cikin matsala shine, baba ya zo ya fara kwanciya da yaya Asma'u a maimakon mama, shi ya ɓata mata budurcinta, kullun yana kwana da ita ɗaki ɗaya, tun tana kuka har ta hakura, domin idan bata yarda sun kwanta ba, baya ba mu abinci, kuma ko sun kwanta sau ɗaya yake bamu abincin a rana, duk da haka mun jure bamu damu ba, wata rana da daddare muna barci ya zo ya tasheni akan wai mu tafi ɗakinsa yau da ni zai kwana, shine yaya Asma'u ta ce ba zai yi wu ya lalata ta kuma nima ya yi mani hakan ba, zaginta ya fara yi yana faɗin ina ruwanta, idan bata yi mashi shiru ba sai ya kasheta a cikin daren nan, shine ta ce ya kasheta ɗin idan zai kashe ta, amma ni dai ba zai lalata mani rayuwa tana ji tana gani ba, haka yasa ya ɗauki itace ya buga mata ta faɗi kasa kamar baya numfashi nikuma ya jani zuwa cikin ɗakinsa, ina tsoron yi mashi wata magana dan kada nima ya buga mani itace ya kashe ni, sai na yi shiru ina kuka ina tuna abin da mama take yawan gaya mana, na muriƙe mutuncin mu duk wuya duk daɗi, idan har muka yarda muka zubar da mutuncin mu a titi bata yafe mana ba, sai kuka nake ita tuna mama, shi kuma baba ya cire mani riga zai cire mani zani kanan yaya Asma'u ta buga mashi wata itace ta baya, ya faɗi kasa kanshi ta fashe yana jini, hannu na ta riƙo tare da miƙar da ni muka fita da gudu, cikin wannan dare muka keta daji muna gudu.

A hanya muna tsaka da gudu aka daki yaya Asma'u ta baya, ta faɗi kasa tana faɗin na gudu, ni bansan waye ya dake ta ba saboda duhun dare, na dai ga ta tashi suna faɗa da mutumin, a haka na gudo na barta a wajen, na fito bakin hanya, a nan nakwana, ba riga sai dai zanina dana ɗaura a saman kirjinta, washegari da safe a na rinƙa tafiya da kafa, na ci bakar wahala, jama'a suna ta yi mani kallon mahaukaciya saboda babu riga a jikina, har na shiga cikin birni wuraren la'asar haka, ban ci komai ba, kuma ban wani damu ba, saboda mun saba da yunwa, a takaice dai na sha bakar wahala ka fin na samu wasu bayin Allah su ɗauke ni, har makaranta suka sanya Ni, suna bani kulawa sosai da sosai saboda basu taba haihuwa ba, ita kuma yaya Asma'u ban sake jin labarinta ba, shekarata ɗaya cikin na biyu na yi a wajen su, na canza na fara samun ilimi, satin da ya wuce ne suka zo mani da wata magana wai suna son na haifa masu yaro, dan basu taɓa haihuwa ba, matar ba zata iya aihuwa , shine suka ce zaa sanya kwan haihuwarsu a cikina, yaron zai girma na haifa masu, wannan dalilin yasa dama suka ɗauke ni suka sani makaranta dan na iya yadda zan kula masu da cikinsu.

Ban nuna masu a kan cewa ba zan yi ba, sai da na bari dare ya yi kowa ya yi barci, na kwashi kayana da yan kuɗin dake a gareni, na lalaɓa na buɗe gate ɗin gidan na gudo, ina fita na kwana a teburin mai shayin gaba da unguwar mu, da safe na wuce tasha na hau motar Abuja, ban san kowa a nan ba, kawai na hau mota, da muka shigo sai na rasa ina zan je, to ina tafiya a hanya ne muka haɗu da hajiyar da ta kawo ni nan, a takaice wannan shine kaɗan daga cikin abin da ya faru a rayuwata" ta kai karshen maganar tana kara sakin matsanancin kuka mai ratsa zuciyar mai sauraro.

Har wani tsuma Jehan ta ji jikinta yana yi, ji take idan ta tamki wannan uban nasu zata iya yi mashi yankar rago, bakin mugu azzalumi, ta kuduri niyar wlh ba zata barshi ba, matukar dai yana raye sai ta nemeshi ta ɗaukawa Maryam da Asma'u da mamansu fansa, dan ire-iren su take son zama yar sanda. Duk dakiya da dauriya irin tata sai da ta matsawa Maryam kwalla, abin akwai taɓa zuciya sosai, ace uban ka da ya haifeka, kai duniya ina zaki da mu?.

Rungumar Maryam ɗin ta yi tana mai bata hakuri tare da rarrashinta, da kyar suka samu ta yi shiru. Jugum-jugum suka zauna kowa da abin da yake tunani na rayuwa.

After some minutes

A wannan hali Zinariya ta shigo ta same su, sai tashin wani azababben kamshin perfume take yi mai sanya mutun ciwon kai, bata wani da mu da halin da suke a ciki ba kawai cewa ta yi "Ke Aisha ke da Maryam da Adiva ku shirya kuna da bako a palon hajiya nan da minti talatin, zai zaɓa ɗaya ne daga cikin ku, ita kuma Jehan sai Hajiya ta dawo musan awani part take, namu jinsin ce ko dai mazan za'a barmawa!" Ta kai karshen maganar tare da juyawa ta fice daga cikin ɗakin.

Ba musu suka tashi suka hau shiri, haka kawai Jehan ta tsinci kanta da kasa hanasu tafiya, tana ji tana gani suka gama shiri suka fice daga ɗakin. Abin dake faruwa shine akwai wani tunaren da Zinariya ke shafawa idan zata zo kirawa costumers mata su zaɓa, duk wanda ya shaki Kamshin turaren to fa ba zai iya yi mata kaddama ba, dole kawai su bi abin da take so.

Haka suka shirya suka fice daga cikin ɗakin har ma da yar zumuɗin su, bayin Allah sun shaki turaren Zinariya ta cuci rayuwarsu.

Kasancewar Alhajin da ya zo ɗin masoyin mata masu ɗan giba ne sai ya zaɓi Maryam, domin ta ɗan fisu kiba, Adiva kam kamar Jehan take, ba su da wani kiba ko kaɗan, ɗan gara ma A'isha ta fisu auki.

Bayan ya zaɓi Maryam ne A'isha da Adiva suka dawo cikin ɗakin, cikin zuciyarta Adiva kukan ɗaukar Maryam ɗin take yi, amma kuma a zahiri ta kasa nuna hakan, sai ma tsintar kanta da murmushi a kan fuskarta da ta yi, abin ya ɗaure masu kai, ga abu a cikin zuciyarsu suna ayyana wa amma yaki fitowa filli, haka ita ma Jehan ɗin ta kasance, sai kukan zuci take yi tana addu'ar Allah yasa kada ya lalatawa Maryam yaruwarta, yadda ta sha gwagwarmaya akan kare budurcin tan nan, Allah ya taya ta kare shi.

A ɓangaren ita ma Maryam ɗin a zuciyar ta tana jin ba zata iya barin shi ya aika abin da yake da niya ba, amma kuma a zahiri ta kasa hana shi, sai faman shafa ta yake yi tun ma a cikin palon Hajiyar kafin su shiga daga cikin ɗakin da ya kama, dan ya ce a nan zai yi amfani da ita, sai wani murza mata breast yake yi, ga bakin nan nasa bakin kirin kamar zunubi, da alama ɗan buguwa ne.

(To fa Maryam Allah ya kuɓutar da ku dukkanku na haɗa kaya na zuwa wajen mai Rimsha, sai na dawo dan ganin ya ake ciki)

🔥🔥GIDAN ABBA🔥🔥

Kamar yadda Dr Nawid ya faɗa kuwa bayan sallar isha sai ga shi nan ya zo, ya ci wanka ya sha dakakkiyar shadda blue color, ya yi kyau ba karya, amma fa ko kallo da ido bai samu daga wajen gimbiyar tasa ba, sai tashin kamshi yake yi yana ta zuba murmushi, ita kuma tana zaune saman sofa ta tsare gida ta haɗe rai, bai damu sosai ba, saboda yasan bata da lafiya...gaisuwa suka yi, daga nan suka zauna shiru, Rimsha ta yi kasa da kai shi kuma ya zuba mata idanu yana lallonta.

A haka Akila ta shigo ta same su, wani irin haushin Dr Nawid ne ya kamata, dan bata son abin da zai ɓatawa Rimsha rai kwata-kwata, kusa da ita ta zo ta zauna tana ɗagawa Dr gaisuwa, da fara'a ya amsa tare da tambayarta ya school, lfylou Alhadulillah ta amsa mashi da shi, daga nan ta dawo da kallonta kan Rimsha, ganin yadda ta yi kasa da kai kamar zata yi kuka ne yasa ta ce mata

"Meesha mu je ki nuna Mani in da kika ajiye kayan mun can" to ta amsa a tare suka miƙe Akila tana faɗin "Yaya Nawid ina nan dawo maka da ita" bai kawo komai a ransa ba, sai murmushi ma yake yi ya amsa mata da tayi sauri fa.

Suna shiga ɗaki Akila ta ja ta rungume ta, kasa-kasa ta fara magana "Rimsha ki dai'na ɓata rai kin ji? Ba ke kaɗai ce baki son shi ba har da ni, dan Allah ki saki ranki, idan kun ɗan yi hira na 30mins sai ki ce mashi kanki na ɗan maki ciwo zaki kwanta, kinga a haka za ku rabu lafiya, amma a duniyar yanzun nan baa fitowa mutun filli anuna ba'a son shi, wlh zaki ga uwa ɗaya uba ɗaya kuka fito da mutun ma a zamanin yanzu yana iya kashe ki akan abin duniya, dan haka ki sani ba'a shedan ɗan adam, ki san taya zaki zauna da kowa, kada ki damu In Sha Allah idan Lion ya fara son mu ba sai ma kin yi masu magana ba, ina da tabbacin sunan shi ma kawai idan suka ji daga ranar wlh ko millon nawa za'a basu, babu mai kara zuwa wajen ki ko ya kira ki a waya, so dan haka ki kwantar da hankalin ki, kuma yadda kike bala'in kaunar Lion mijin mu, dan ni na bashi ke, na san wlh ba zaki taɓa son kowa ba, bana son ki nuna musu tsanar da kika yi masu a fili, duk da yake abokin yaya Imran ba zamu yi shedar shi ba, ke bama su ba, mi sali ko yaya Akil ba zaki yi shadar abin da zai iya aikatawa akan abin da yake so ba, dan haka ki natsu komai cikin taku zaki bishi, yaya Imran ya ce zai zo wajen gyaran jiki ya same gobe da yamma idan yaya Akil ya kai mu, wai da na

Please Login or Register in order to submit comment