You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce ba bare ma ta bugeka saboda komai da aka dakatar,

Umarni Romeo ya bada da a kashe duk wani Tv dake gidan su kuma Tga ya karɓa wayar dake hannun daddy dan karya samu labari, shima zai iya mutuwa idan naji labarin kai tsaye dole sai a hankali za'a faɗa masa, haka kuwa akayi duk wani Tv dasu laptops dake cikin gidan William jacop sai da aka kashe su, Tga ne yaje ya karɓi wayar hannun daddy cikin dabara ba tare da daddy ya kawo wani zargi a ran saba, sosai Tga yayi kuka kamar ransa zai fita, Jay da John kam basu samu labari ba tukun nan, Tga ne kawai ya sani shima dan yaje ya karɓa wayar dad kuma ya kashe su Tv dake gidan yasa Romeo ya sanar masa.

Romeo ya kasa bari ayi wa Michael sutura ya zauna ya zuba masa ido, ga idon nasa yau abun tsoro saboda riƙiɗewa da sukayi, ya kasa wani kataɓus

Manya manyan ministoci da yan majalisu governors duk sun hallara a cikin asibitin amma babu wanda ya samu damar shiga wajen da su Romeo suke, asibiti ya cika makil har bakin titin waje motoci ne na manya manyan masu faɗa a ji a kasar tare da security su.

Shugaban kasa tare da wani ɗan jarida ɗaya wadda ya kasan ce kanin sa ne suka samu daman shiga wajen su Romeo nan ma sai da Romeo ya bada izinin a barsu su shigo.

Ɗan jaridan da ya shigo tare da sugaban kasa ne ya tinkari in da Romeo ke zaune da camera a hannun sa, a tunanin sa tun da tare suka zo da shugaban kasa ba wani abu, Romeo ya duker da kan sa kasa, dan bai son ɗago idon sa, in ya ɗago ido mai ƙaramin zuciya ya gansa zai iya mutuwa, bai ankara ba yaji alamar ɗaukan hoto, kafin ya ɗago kai yaji murya ɗan jaridan yana cewa "Sir ko zaka iya gaya mana wani irin hali ka tsinci kanka lokacin da kaga ɗan uwan ka kwance cikin jinin nan?" Tashin hankali shugaban kasa yana ganin katoɓarar da ɗan jaridan sa yayi sai ya ja baya kaɗan, yana tausayawa ɗan jaridan yasan duk da cewa ɗan jaridan kanin sane na jini tofa lion ba zai raga masa ba, kuma kafin su zo sai da ya ja kunnen kanin nasa a kan karya kuskura yayiwa lion wata tambaya ya ɗauki hoto kawai tun da daman hoto yace zai je ya ɗauka.

Shugaban kasa yayi nisa cikin tunanin da yake bai ankara ba sai ganin kanin sa yayi a saman iska yana reto yana kokarin faɗuwa kasa ga cameran sa can gefe ta ragargaje, abun mamaki kuma abun da ya kullewa shugaban kasa kai shine ga dai Romeo yana zaune kamar yadda yake bai motsa ba, kenan to waye ya daki kanin sa har yayi sama haka, wannan tambaya ce da bashi da amsar ta

Abun da ya faru lokacin da ɗan jaridan yayiwa Romeo tambayar, Romeo ya ɗago kai da ido kawai ya kalli wayan nan jibga jibgan sojojin sune suka lillisa ɗan jaridan suka masa pata pata suka ragargaje cameran.

Allah sarki ɗan jarida kanin shugaban kasa, shi yazo samun hoton gawan Michael tun da ba wani gidan jarida dake da hoton gawar, dan ba wanda ya samu damar shiga wajen, labarin mutuwar ne kawai jama'a keji amma basu samu daman ganin hoton gawar ba, ko hoton shi Romeo.

Jina jina sojojin nan suka yiwa ɗan jaridan nan, wannan ma dan sun yiwa shugaban kasa kara ne yasa basu kashe ɗan jaridan ba, lion kuwa ya kasa fita daga cikin hospital ɗin, tamkar shine wanda ya mutu ba Michael ba ko motsin kirki ya kasa yi, banda zazzafan huci da yake fitarwa ba abun da zakaji yana fita daga wajen shi, yayi mutuwar zaune, time to time yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya.

Jiki ba kwari shugaban kasa yazo ya dafa kafa ɗun lion tare da zama kusa da shi ya ɗan rungumo shi cikin muryan rarrashi yace "My lion please and please kayi hakuri, nasan dole akoi zafi muma mukaji zafi bare kai, amma ka daure kamar yadda na sanka da dauriya kayi hakuri ka bari ayiwa Michael sutura dan ba abun da yake buƙata sama da wannan a yanzu.

Kamar wadda alluran sojan sa ya tashi haka ya juyo a fusace ya damki wuyar shugaban kasa, yana zaro ido cikin tsawa yace "No uncle, no Michael bai mutu ba, ka daina dangan ta shi da gawa, kuma babu in da za'a kai shi" tashin hankali president matsayin kakan su yake, dan kani ne ga kakan su jacop amma yau Romeo ya shake masa wuya kamar zai kashe shi dan kawai yace aje ayiwa Michael sutura

Sai zaro ido waje shugaban kasa yake yana jin kamar zai mutu, daman yasan za'ayi haka mawuyacin abune Romeo ya yarda yana ji yana gani a saka Michael cikin rami shiyasa ma ya hana kowa zuwa ɗakin, dan bai son su kawo masa maganar, duk wanda yayi gigin kawo masa maganar saka Michael a kabari zai iya kashe sa.

Sai da Romeo yaga president na faman sumewa sannan ya sakar masa wuyar sa, cikin tsawa yace da "get out uncle" kasan cewar shugaban kasa yasan halin jikan nasa sai ya miƙe ya fice daga ɗakin hannun sa riƙe da wuyar sa dan yasha shaƙa.

Kifa kan sa Romeo yayi a saman fuska Michael yana jin zuciyar sa na tafasa tamkar zata fasa kirjin sa ta fito waje, saboda dakiyar zuciya irin na Romeo baiyi hawaye ba, ya daure dan shi cewa yake hawaye faɗuwar namiji ne, amma fa daga ta ciki yayi hawayen a zuci ya shiga tashin hankali da bai taɓa shiga ba.

To masu karatu muje mu leƙo Akil sannan mu dawo, sai muga ko ya zata kaya, ya za'a karƙe da Romeo wajen bari ayiwa Michael sutura.

💞💞KADUNA STATE NIGERIA💞💞

Sai bugawa Akil kofa mum take amma yaki sauraron ta, dan baya duniyar mutane, ya shiga Umaisha sai aiki yake, sai kuka take tana zagin sa tana dukan sa amma yaki kyale ta, ya dage sai ya mai data cikakkiyar mace.

Jin da gaske far ma Umaisha Akil yayi yasa Hajiya Umaiya komawa palo ta sake kiran Abba a waya ta sanar da shi wlh Akil yayiwa yar mutane fyaɗe kuma a cikin gida a cikin ɗakin sa, tashin hankali, Hajiya Umaiya ta tsorata sosai har Imran sai da ta kira a waya, ta sanar da shi, duk tabi ta ruɗe ga Akil baya jin kira.

A wannan hali Aafia ta shigo cikin gidan da gudun ta tana neman Umaisha, nan Hajiya ke Tambayar ta wace ce ita daga ina take, wace yarinya Akil ya ɗauko, tsabar rashin zumunci itama Aafia bata san Hajiya ba, cike da rashin kunya tace "Ke ni ban sani ba kanwata kawai nazo ɗauka" da farko Hajiya kamar zata mare ta sai kuma taga rashin dacewar hakan domin koma me Akil ya ja musu.

A takaice dai Akil bai kyale Umaisha ba har sai da ya mai da ita cikakkiyar mace, sai dai fa taci wuya kamar ba zakayi rai ba da kyar da kyar take numfashin, kuma ta zubar da jini sosai, yayin da shima ɗin ya sha wahala sosai sama sama yake numfashi yayi aiki wajen nan over, felling iya felling hankali ya kwanta wani daddaɗan barcine ya kwashe sa, ita kuwa Umaisha sai nishi take, yanzu babu bakin yin ihun ma ta kwanta shiru kawai tana jin raɗaɗin azaba a jikin ta.

Barcin 10mins yayi kamar wadda aka tsikara ya tashi da sauri yana kallon ɓarnan da yayi ga Umaisha kamar ba zatayi rai ba, da sauri ya miƙe ya wuce toilet ya haɗa mata ruwa mai zafi ya fito ya ɗauke ta cak kamar yar baby suka wuce toilet.

Sai nishi take tana masa kukan wahala kasa kasa, sosai ya gasa mata jiki sannan ya mata wanka ya fito da ita ɗaure da towel ya shinfiɗe ta saman sofa, sannan ya cire bed sheet ɗin nasa da yayi baca baca da jini ya ajiye a gefe ya ɗauko wani ya shinfiɗa sannan ya dawo da Umaisha saman gadon ya kwantar da ita ya wuce ya koma toilet dan yayi wanka.

A ɓangaren Hajiya da Aafia kuwa, Hajiya bata sake tankawa Aafia ba ta yi shiru kawai ita ma Aafia shiru tayi tana jira taga ta in da Umaisha zata fito, dan a nata tunanin dole ne Akil ya kyale Umaisha ai ta koma gida tun da ba matar sa bace ba a ɗaura auren ba tukun nan, bata san shi kam Akil tuni ya ɗaurawa kan sa auren ba har ma ya raya Sunnah abun sa, sai dai jiran sakamako wato baby kenan.

A wanna hali Abba ya dawo ya same su, hankali tashe Abba yace "ina Akil ɗin yake muje" da sauri Hajiya tayi gaba Abba ya bi bayan ta, Aafia ma bata bari an barta a baya ba tabi bayan su da saurin ta.

Kofar bedroom nasa suka tsaya suna bubbuga wa da karfi, lokacin yana kokarin saka kayan sa ya fito daga wanka, wani nishaɗi da farinciki na musamman yake ji yau, Umaisha kuma barcin wahala ne ya ɗauke ta

Jin bugun kofan yasa ya zura jallabiya kawai ya nufi kofar yaje ya buɗe, yana buɗewa su Abba suna cusa kai cikin ɗakin Hajiya tana faɗin "Yar waye kaje ka ɗauko?" Shafa kan sa yayi kafin yace "Matata ce" Mata Abba ya furta da karfi, eh Akil yace, tashin hankali Akil manya naka ba irin nasu bane

Wucewa Abba yayi ciki dan yaga wace ce Akil ya ɗauko, bayan sa Hajiya da Aafia suka bi dan suje suma su gani, shikuwa oga Akil yana tsaye a bakin kofa, wai yaji kunya su Abba zasu je sugan masa mata kwance Allah ma yasa ya lulluɓeta da bargo, kai jama'a Akil manyan kasa oho Allah wai kunya yaji hmmm

Kallo ɗaya Abba yayiwa fuskar Umaisha yace "Kai Akil amma wannan ai kamar yar gidan Zahraddeen ce ko? Dan ga kamanin Deen sosai fuskar ta" ɗan sunkuyar da kai Akil yayi yana ɗan shafa kan nasa irin kunyar nan yace "Eh Abba ita ce matata ce ai, naje na ɗauko tane" salati Abba yasa kafin yace "Matar ka waye ya aura maka ita? Ko dai kana da wani uban bayan nine?" To fa, ita kuwa Aafia saman gadon ta haura tana kuka tana jijjiga Umaisha, ganin Aafia na kokarin yaye bargon daya rufe Umaisha da shi ne yasa ya daka mata tsawa wadda yasa ta ja da baya daga kusa da Umaisha

Hajiya Umaiya ce ta jawo Aafia tana faɗin "Ya isa kiyi shiru" Abba kam ya rasa bakin magana wai yau Akil ne da hankalin sa da ilimin sa ya yayiwa yarinya fyaɗe, fyaɗen ma ya rasa wadda zai yiwa sai yar kanin sa, kuma fyaɗen ma har gida ya kawo ta gaban kowa yadda zasu gani da idon su bawai suji labari ba, lallai Akil ya cika ɗan duniya mai lasisi

Duk dakin sunyi shiru anrasa mai bakin magana, shi dai Akil ko ajikin sa, soma yake su fice masa daga ɗaki ya samu dama ya sawa matar sa kaya, yau ga ɗan duniya.

Da kyar Abba yace "Yanzu Akil da hankalin ka zaka yiwa yar mutane fyaɗe?" "Abba fyaɗe kuma? A'a ni ba fyaɗe na mata ba dan matata ce ai" a kule Abba yace "Matar ka uban waye ya aura maka ita?" Akil zai yi magana Hajiya Umaiya tace "A'a Alhaji ni kada ka sake yi masa tsawa, dan kawai yayiwa wata yar talakawa fyaɗe shine zaka fara wani ɗaga masa murya, ni bana so, idan iyayen ta sunji ba zasu iya yafewa ba, sai su faɗa min nawane kuɗin budurcin yar nasu sai na biya, kai wannan yar ma da gani ba budurwa bace ka duba bed sheet da suka kwanta mana babu wani alama da zai nuna cewa budurwa aka yiwa fyaɗe a nan" to fah gaba da gaban ta, su Aafia suna ganin su hamshaƙan masu kuɗi ne to ga Hajiya Umaiya ta kira su da talakawa

Kasan cewar shi Akil yana son Umaisha da gaske sai bai ji daɗin abun da Hajiya tace ba ran sa ya sosu sosai, rai a ɓace yace "Haba Ammie bai kamata kice wa matata haka ba, nifa da gaske nake son ta ba wasa ba, kuma bayan ita ba wata mace da nake so, babu wadda kuma zan so" zaro ido waje Ammie tayi a kule tace "Wace ce matar taka? Ba dai jinin Abban kaba sai dai wasu ƴaƴan manya shuwagabanni ko sarakuna, amma wannan yarin ba dai ina raye ne zata zama matar kaba" tirkashi, shi dai Abba bawan Allah shiru yayi ya zuba kusu ido kawai yana kallon ikon god

Turo baki Akil yayi yace "Ni ita nake so kuma ita ce zaɓi na, sannan ita ba kamar yadda kike tunani bace tana da hankali ba namijin daya taɓa taɓa ta sai ni" yana kai karshen maganar ya fice daga ɗakin da sauri dan ma kar Ammie ta masa baki a kan Umaisha ko wani abu dan yasan halin Ammie sarai yadda bata son family Abba ko kaɗan ɗin nan ba abun da bazata iya faɗa ba in dai a kan sune

Sakin Aafia Hajiya tayi ta bi bayan Akil dan ita bazata taɓa yarda da ya auri Umaisha ba, Allah sarki Abba yana tsaye shiru ya zubawa sarautar Allah ido, ita kuma Aafia sai kuka take.

Ko da Ammie ta fita bata ga Akil ba dan ɓuya yayi baya son su sake maganar Umaisha da ita, sama yayi kasa yayi wallahu a'alam bata gan shi ba, shima Abba jiki ba kwari ya fito ya wuce bedroom nasa dan ya rasa bakin magana abun yafi karfin sa.

Yana shiga bedroom nasa ya isko Akil kwance saman gadon sa ya ɗaura hannu a saman fuskar sa kamar mai tunani, Ammie kuma tana can tana neman shi a cikin gida

Kusa da shi Abba yazo ya zauna a gefen gadon cikin nitsuwa yace "Haba Akil me yasa zaka yiwa yar ɗan uwana haka?" Miƙewa zaune Akil yayi cikin nitsuwa shima ya fara magana "Kayi hakuri Abba na, amma magana ta gaskiya shine Umaisha mata tace, da igiyar aurena uku a kan ta" juyowa da kyau Abba yayi suna fuskantar juna cike da murna yace "Yaushe hakan ya faru?" Yar murmushi Akil yayi kafin yace "Tun kafin na koma school, naji ba zan iya tafiya ba tare da an mana aure ba, dan ina ganin kamar idan na tafi bappa zai aura mata wani, shine bayan naje munyi sallama da ita, na wuce wajen Bappa na rokesa daya aura min ita kafin na tafi, da farko bappa yaki yarda sai da yaya Imran da yaya Irfan suka sa baki sannan ya yarda na bashi sadaki, a masallaci bayan sallar la'asar aka ɗaura mana aure, daman abun da yasa ban sanar daku ba, na bari sai na dawo ne in ɗauko ta in kawo muku ita, to ina shigo kasar nan kuma na wuce school nasu dan naje na ganta na ɗauko ta na kawo muku ita ku ganta, shine ta ɓata min rai har hakan ta faru tsakanin mu" kallon gefen ido Abba ya masa irin hararar wasan nan ya masa kafin yace "A'a ba dai ta ɓata maka rai ba, dama can da muguntan ka kadawo" ɓuye fuska Akil yayi a jikin Abba yana dariya kasa kasa, cakulkuli Abba ya shiga yi masa yana faɗin "A'a baka isa ba ai sai ka buɗe fuska muga juna ido da ido zai fi, dan rashin kunya ka kwaso zafin ka kazo tsakiyar rana ka sauke a kan ƴata gidan nan duka suna jin ka bakaji kunya ba sai yanzu zaka wani ɓoye fuska to wlh baka isa ba maza ɓuɗe muyi ido biyu" a shagwaɓe Akil yace "Kai Abba ka bari mana ni wlh kunyar ka nake ji" "Eyee kunyata ba, ai dole kaji kunya ta irin wannan ɗanyen aiki daka yiwa ƴata to Allah dai yasa ina da rabon jika" kara ɓoye fuska Akil yayi yana dariya yana jin farinciki

Jin motsin Ammie na zuwa ne yawa dukan su suka yi shiru Abba ya ɗan matsa gefe yayin da shi kuma Akil ya diro kasa daga saman gadon ya nufi hanyar fita

A bakin kofa sukayi karo da Ammie da sauri ya wuce ta ya koma bedroom nasa, kafin ma ta ɓuɗe baki tayi wani magana ya wuce ta, girgiza kai tayi tace "Zamu haɗu ne" ta kai karshen maganar tare da wucewa cikin bedroom ɗin Abba.

Akil kuwa yana shiga ya samu Aafia zaune kusa da Umaisha tana hawaye, kusa da ita yazo ya zauna yana faɗin "Kiyi shiru ki dai na kuka ki tashi kije ɗakin Akila ki kwanta ki huta kafin Akila ta dawo school sai kuyi hira zan kira bappa a waya na faɗa masa kina nan" banza tayi da shi ta ci-gaba da kukan tana mai jin kamar ta shaƙe shi dan haushin ya raba kanwar ta da budurcin ta a banza ba auren ta yayi ba, kuma ga maman sa tana cewa ba zai auri Umaisha ba shikenan ya cuci rayuwar Umaisha a tunanin Aafia kenan.

Ganin taki tashi ta tafine yasa ya miƙe ya riƙo hannun ta ya miƙar da ita, tana kokarin kwace hannun ta a fusace ya ɗaga hannu kamar zai mare ta sai kuma ya dakata, da ɗan karfi yace "Karki fara wuce mu tafi!" ganin ya haɗe rai sosai ne yasa ta hakura tabi bayan sa suka tafi ya kai ta ɗakin Akila ya dawo ya ɗauki jallabiyar sa ya sanyawa Umaisha ya wurzawa kofar ɗakin su key ya dawo ya kwanta kusa da ita yana mai jin matikar farinciki da annashuwa har cikin ransa.

Ita kuma Aafia kwanciya tayi saman gadon Akila tana kallon sama tana hawayen bakin ciki, har barci ɓarawo ya ɗauke ta

Ammie kuwa bala'i ta tsayar wa Abba wai dole yasa Akil ya dai na zancen auren Umaisha dan ba zata taɓa yarda ƴaƴan ta su aurin ƴaƴan talakawa kamar family sa ba, ayya Abba da yake tariga ta shanyesa yana son yan uwan sa amma babu halin nuna musu soyayya, sai kawai ya shiga bawa Ammie hakuri yana ce mata dole Akil ya bar zancen auren Umaisha, ba zai aure taɓa, ya nemi wata, sai daɗi Ammie take ji, bata san Umaisha kam already matar Akil bace.

Wannan kenan mu leƙa Daular mutuwa mu ga meke faruwa sai mu dawo

👹👹DAULAR MUTUWA👹👹

Gudu Rimsha take sosai kamar zata tashi sama Kausar na biye da ita a baya, kasan cewar cikin ramin akoi hanyoyin da dama sai suka kauce hanyar da suka bi da farko suka kama wata hanyar daban saboda tashin hankali da ruɗu, su kuma su barbushi sunyi gudu mai nisa a wajen basu haɗu da su Rimsha ba, suma su Rimsha ɗin sunyi gudu sosai har suka kasa ci-gaba da gudu basu ga daular mutuwa ba ya ɓace musu, zama sukayi kasa a wajen suna numfashi sama sama kamar ba zasu yi rai ba bayin Allah.

Suna zaune a wajen tun suna ganin haske kaɗan kaɗan har suka fara ganin duhu alamar dare kenan, kasan cewar wajen a karkashin kasa yake ba zaka iya wani banban tashi da yamma ba, danma akoi wasu wurare dake da huji kamar Windows a wajen hakan yasa ake ɗan samun haske kaɗan a wajen, ga yinwa ga kishin ruwa ga gajiya duk abun ya haɗe musu, banda sunan Allah ba abun da suke ambata a zuciyoyin su.

A takaice dai kwana sukayi zaune a wajen, basu samu ganin Ayla ba, suma kuma su Barbushi basu samu damar ganin su Rimsha ɗin ba saboda addua'o'i da suke samu ta ɓangarori daban-daban, dan ko Jehan ta dukufa sosai kwana biyun nan tana yiwa Rimsha addu'a dan kwana biyun tana yawan mafarkin Rimsha ɗin shiyasa ta dukufa da yi mata addu'a sosai, a ɓangaren gwaggo ma haka ne ta dukufa sosai wajen yi ma Rimsha addu'a dan dukkan su kwana biyun nan suna mummuna mafarki a kan Rimsha ɗin, ta gefen guda kuma ga malaman da mum ta bawa kuɗi suyiwa Rimsha saukan Al Qur'ani mai girma suma yau suka gama saukan Al Qur'ani shine ma dalilin da yasa Allah ya bawa su Rimsha damar kuɓuta daga daular mutuwa, sannan ga baba da Mustapha suma ba'a barsu a baya ba sosai suke wa su Rimsha addu'a a zuciyar su, hakan yasa su Barbushi basu samu daman ganin su ba.

Washegari ganin Kausar na kokarin mutuwa ne saboda yinwa da kishin ruwa yasa Rimsha tayi ta maza ta miƙe, Allah sarki itama yinwan take ji amma da ɗan sauran karfin ta tafi Kausar kwari, haka ta tattara karfin ta dukka ta goya Kausar a bayan ta tana jan kafarta a hankali hankali, dan duk kafar nata ya faffashe tun jinin ta na zuba har ya bushe wajen ya dai na zuba, tafiya take kamar zata faɗi kasa dan Kausar ta mata nauyi amma haka ta daure ta cije tana hawaye ta nufi hanyar da sukabi suka zo, ma'ana suka koma in da suka fara tafiya da farko.

Rimsha tayi tafiya mai ɗan nisa da Kausar a goye a bayan ta kafin su iso wata kofar dafaffiyar karfe, da kyar ta iya sauke kausar ta zaunar da ita a kasa, ta sa hannun ta ta kwance ruwan tsafin da duna ya bata wadda ta kulle sa a jikin igiyar rigan ta dan karya faɗi kasa, kamar yadda ya faɗa mata haka ta zuba ruwan kaɗan a jikin kofar sai ga kofar ta buɗe nan take wani haske ya kaure musu ido, lokacin rana ya ɗago tsakiyar duniya, da sauri suka rintse idon su dan sun jima basu ga haske irin haka ba

Sun ɗan jima a haka kafin Rimsha ta buɗe dara daran sleeping eyes nata da sukayi ja sosai, duk sun faɗa kamar ba wayan nan kyawawan idon nata masu kama da audiga dan haske ba, banda zara zaran eyelashes nata dake ɗan taimaka musu wajen fito da su da bazaka taɓa gane su ba saboda wahala da azaba da ta sha

A hankali ta fara bin wajen da kallo, bata ganin komai sai bishiyoyi masu cikar ganye, juyowa tayi tasa hannu zata ɗago Kausar ta goyata, Kausar tayi sauri dakatar da ita ta hanyar yunkurawa da kan ta ta miƙe, rungume juna sukayi dan su tallafawa juna suka fara jan kafafun su da kyar da kyar zawa wajen wurin

Sai kuma me, kungurmin daji ne sosai a wajen wadda baka gane gabas baka gane yamma, ga dogayen bishiyoyi masu abun tsoro, lokaci guda tsoro ya dira musu a ransu, tunani suka fara yi gara musu cikin daular mutuwa da wan nan wajen, domin koba komai cikin daular mutuwa akoi mutane nan kuma fa, sai karan tsuntsaye kuma da alama ba za'a rasa yamun dawa a wajen ba, macizai kam ma guarantee ne sai an same su ba adadi a wajen.

Shin nan ɗin ma wace kasa ce? Wani gari ne? Tashin hankali

Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu
[11/11, 8:51 PM] +234 906 579 6460: TRIPLET'S💞






# BOOK 2📚📙✍️


💔💔Episode 3💔💔


💔RIMSHA💔


A hankali suka fara kutsawa cikin dajin nan suna tafiya suna tangal tangal kamar zasu faɗi kasa, saboda wahalar da suka sha, duk sunyi wani iri dasu, sun koɗe futu futu, kamar ba su ba, kamar wayan da aka tono su daga rami, ko aka kwato su daga bakin kura, har wani duhun wahala sukayi, gashi sun manne junan su sosai saboda tsoro.

A wannan lokaci da suka fito sun samu damar kiran sunan Allah a baki, gaba ɗaya dark black curly hair Rimsha ya cukurkuɗe kamar bashi ne wannan kyakkyawan bakin gashi mai shekin ba, mai tashin kamshi, yanzu ya dawo duk dattin, kuran daular mutuwa ya buɗe shi, sai warin datti suke saboda wanka ma da ruwa kawai suke ba sabulu, bare kuma mayukan gyaran jiki, ita kam Kausar daman ba gashin gare taba, abunku da kan yarbawa basu da gashi sosai aguiguye kan nata

Please Login or Register in order to submit comment