You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rungumo ta tana faɗin "Rufee ya mukaji da hakurin rashin Amal" hawayen munafurci Rufee ta fara yi tana faɗin "Wlh ji nake kamar na mutu nabi Amal yanzu ma saboda ke nazo school nan, nazo na baki maganin nan ne sai na koma ana can ana zaman makoki" Allah sarki Aafia da yake ba yin kan ta bane sai ta karɓa maganin da Rufee ta kawo na zubar da cikin Aunty, kuma daga nan Abbi zai tsane ta, sai murna Aafia take Abbi zai tsani Aunty ya koreta daga gidan, ita kuwa Umaisha yar ba runa ko ajikin ta dan da zaman Aunty a gidan da babu duk ɗaya ne a wajen ta bata da matsala da hakan, sai kitsawa Aafia mugun abu Rufee take, nan Aafia ke sanar da Rufee'n zuwan daddyn Jelly gidan su, ko kaɗan Rufee bata ji daɗi ba musamman ma da Aafia tace mata daddyn Jelly zai hana su fita da ko wani kaya sai atamfa da kuma hijabi, ba haka Rufee take so ba, ita tana son ne ta koyawa Aafia bin maza dan haka sai ta fara shirya yadda zasu yi da daddyn Jelly.

Suna tsaka da wannan zancen nasu ne kamar daga sama, sukaga wani handsome guy ya diro wajen ya danki hannun Umaisha, ita kan ta Umaisha bata gane Akil ɗin ba dan ya canza sosai ya kara girma ya kara tsawo da cika yayi bul'bul gwanin ban sha'awa, daman Akil ba baya ba wajen kyau, duk da ita ma Umaisha ɗin ta canza dan shakara uku ba wasa ba hakan bai hana Akil gane taba, dan Imran na tura masa hotunan ta, shi kuma Imran wajen Irfan yake samun hotunan nata.

Kokarin kwace hannun ta tayi dan bata gane saba kwata kwata musamman dayayi shigar kananan kaya abun ba'a magana, wani mahaukacin mari ya sakar mata wadda yasa ta game ko wanene, cikin fushi yace "Kina matata ne zaki fita da wannan ɗan iskan shiga ko? To yau zan koya miki hankali sai kin yi nadama wlh" sai da yayi magana sannan Aafia ta gane wanene, da farko ta ɗauka wani saurayi ne daban har ta fara kamuwa da son shi dayake basu da aiki sai faɗawa soyayya da kyawawan maza, ita kuwa Rufee baki ta sake tana kallon Akil taga kyau nan take taji ta kyatsa da shi kuma tana son shi amma ba da aure ba da iskanci kawai dan ta sawa ran ta Abbin su Aafia kawai zata aura bayan ta gama barbaɗancin ta da tambaɗancin ta a titi.

Cak Akil ya ɗauki Umaisha kamar yar baby ya saɓata a kafaɗar sa tana ta bubbuga masa bayan sa tana faɗin "Ka sauke ni bana so" bai saurare taba ya wuce wajen motar sa, yana zuwa yayi wurgata gidan baya na motar ya shiga gidan gaba ya datse marfin motar tare da tada motar da gudun gaske ya figeta suka bar cikin school ɗin, sai wani hucin ɓacin rai yake, kamar shi ace matar sa ta fita da wannan kaya kai ina dole yayi maganin ta yau, makarantar ma daga yau anyi cancel na shi ba zata sake zuwa ba, sai saka zancen zuci yake a zuciyar sa yana zuba uban gudu da mota.

Ganin Akil ya tafi da Umaisha ne yasa Aafia ta nufi motar ta da sauri dan tabi su taga ina zasu je, sai tambayar ta Rufee take waye Akil? Aina yake? Shima a School ɗin nan yake ne Amma ina Aafia bata bata amsa ba dan hankalin ta a tashe yake burin ta kawai ta isa wajen su Akil, da gudu itama ta ja motar ta tabi bayan su ta bar Rufee tsaye a wajen,

Juyawa Rufee tayi tana faɗin "Tun da kin saka maganin a jakar ki ai bukata ta tabiya shi kuma guy ɗin can ko ki faɗamin wanene ko karki faɗa sai na nemo ɗan gidan uban waye ne dan na ji shawarar sosai ya kamani gaskiya" sai surutu take har ta isa wajen tsohon motar Irfan da Abbi ya bata ta shiga itama ta bar school ɗin.

Akil kuwa kai tsaye gidan su ya wuce da Umaisha sai ihun rashin kunya take masa tana maganganu marasa kan gado, hakan ba karamin fusata shi yake ba, yana parking a parking space na gidan su ya fito ya ɗauke ta kamar yar baby sai zagin sa take, bai kula taba ya wuce cikin gida, a palo yaci karo da Ammie su tana zaune, da sauri Ammie ta miƙe tana tambayar sa wace ce wannan ya ɗauko

Ina hankalin sa baya jikin sa part nasa ya wuce kawai, da sauri Ammie tabi bayan sa cike da tashin hankali, ita da take zaune take jiran anje ɗauko shi a airport ko ina kuma ya samo yar mutane oho masa, tana tafiya tana zancen zuci kafin ta isa bakin part nasa, tuni ya shige ya murzawa kofar key, tsayuwa Hajiya Umaiya ko in ce Ammie tayi tana ɗan bubbuga kofar tana kiran sunan sa, amma ina ya shige can cikin bedroom nasa

Yana zuwa yayi wurgi da Umaisha saman gado tana kokarin tashi ta gudu ya sake mai data, yasa kafa ɗaya ya take mata hannaye dan kar ta tashi, a fusace ya cire kayan jikin sa duka yayi wurgi da su gefe, ya rage daga shi sai Short, hayewa saman gadon yayi ya damkota, Ammie na tsaye a bakin kofa tana buga mashi kofa, amma ina baya jin ta.

Jin Umaisha na kuka ne yasa Ammie ta tsorata dan tasan halin Akil sarai baya son reni tun yana yaro, idan ka rena shi to ba abun da ba zai iya aikatawa ba, son girman bala'i gare shi

cikin sauri ta koma palo ta ɗauko wayar ta, takira Abba ta sanar dashi abun da yake faruwa, shima Abba ya tsorata sosai yace yayi nisa amma ba zai wuce 1h ba yana zuwa, amma kafin nan Hajiya ta dakatar da Akil dan basu ma san ko yar waye yaje ya sankamo ba, sai zare ido Hajiya take.

To jama'a ta ko ina ba sauki Washington DC Triplets suna can cikin tashin hankali gashi shima Akil yana neman ɓata komai, bari dai mu leƙa daular mutuwa mu dawo kila a can mu dace mu ɗan samu sassauci, amma idan ba haka ba akoi matsala, wannan tashin hankali dame yayi kama🥺

👹DAULAR MUTUWA👹

Wani irin turnukin bakin turɓayan kasa ne ke tashi kamar guguwa, gaba ɗaya girman Daular mutuwa sai da ko ina ya karaɗe da wani masifaffen duhun bala'i, ga wani iska mai karfin gaske mai karfin ɗaukan ɗan adam sama abun gwanin ban tsoro, wasu muryoyi mara sa daɗin ji masu bata amo mai sauti ne ke tashi daga fadan Queen, sai juyawa gaba ɗaya gidan yake yadda kasan ba daga kasa a ka yi ginin ba sai ka rantse da Allah a saman iska gidan yake saboda yadda yake juyawa, wannan guguwa mai bala'i karfin gaske ne yasa gaba ɗaya wayan dake cikin gidan kowa ya shige cikin ɗakin sa

Ihun wasu halittu masu kama da zakuna ne ya fara tashi a cikin gidan mai bala'i sautin doɗe kunnen ɗan adam

Duk wannan duhun da iska da guguwa duna na tsaye a tsakiyar part nasu, yadda kasan an dasa shi ko motsi bayayi ya tsaya kekam

kamar daga sama Rimsha ta faɗo gaban sa, tana faɗowa yayi saurin sake tsafin nasa ya duka gaban ta yana kiran sunan ta

Yana sakin tsafin nasa kuma cikin kankanin lokaci gidan ya fara washe wa, sai dai kuma me, nan fa jiga jigan matsafan Queen suka biyo sahu dan basu barin bashi

Ganin yana yin gidan ya fara canzawa alamar jiga jigan mutanen Queen suna zuwane yasa duna miƙewa da sauri ya riƙo hannun Rimsha ya miƙar da ita sai nishi take da kyar da kyar, dai dai lokacin Ayla da Kausar suka fito dan sunga gidan ya ɗan wastsake

Ganin Rimsha yasa suka kwasa da gudu sukaje suka rungume ta, itama ganin su ya kara mata karfin jikin ta, gidan nasu kuwa sai kara riƙiɗewa yake zuwa jawur kalan jini dan dama ita Queen kalar jini ce shiyasa komai nata yake ja kamar jini

Wasu irin halittu ne suka bayyana a tsakiyar wajen masu bala'i girman gaske wadda zasu iya haɗiye dan adam kamar paracetamol, wayan nan halittu su shidda ne suna da kafofin guda huɗu kamar damisa, sai dai kafofin nasu kanana ne jikin su yafi kamar basu girma, munin wayan nan halittu kawak ya isa ya kashe mutun idan ya gansu, gadan gadan wayan nan halittu suka nufi su Rismha yayin da su Barbushi suke biye da wayan nan halittu a baya

Ganin haka yasa duna yaja hannun Rimsha da gudu ita kuma tana riƙe da hannun Ayla yayin da Ayla ke riƙe da hannun Kausar, da gudu wayan nan halittu suka rufa musu baya, suma su Barbushi suka rufawa halittun baya

Duna ya ɗan yi gudu a cikin gidan mai nisa dasu Rimsha kafin ya tsaya dai'dai wajen wani katon gunkin Queen tare da sakin hannun Rismha ya caka hannun sa cikin kasa da iya karfin sa yana ihu ya ɗago wata kofa ya buɗe wajen, cikin sauri yace da su Rimsha ku fi ta wannan hanyar idan kuka fara gudu karku tsaya kuma karku juyo baya, kuyi gudu ku ceci ranku, ni nasan kashe ni zasu yi ba zan rayuwa ba, amma dai ki sani ina son ki ba zan iya bari su kashe ki ba dan haka ki gudu, ya kai karshen maganar tare da fitar da wani ɗan gora mai ɗauke da ruwan tsafi yace "Idan kuna da rabon tsira in kuka kai kofar karshe na hanyar nan, ki buɗe wannan ruwan ki zubawa kofar kaɗan zata buɗe sai ku fita, ragowar ruwan kuma ki ajiye wata rana zai miki amfani ku gudu" sosai su Rimsha suke hawayen rabuwa da duna musamman ma da sukaji yace yasan kashe shi zasu yi sai Rimsha taji wani irin duk babu daɗi a jikin ta

Ganin ta tsaya shiru taki tafiya ne ga kuma wayan nan munanan halittu sun kusa cin musu hakan yasa duna ya turata ta cikin ramin mai kama da rijiya

A tare Rimsha suka faɗa da Ayla da Kausar dan suna riƙe da hannu juna

Yana turasu wayan nan Halittu na isowa wajen, riƙiɗewa shima yayi ya koma irin su suka fara gwabza faɗa a tsakanin su, sai dai daya ke suna daya sai suka fara dukan sa suna ji masa rauni abun tausayi, su kuwa su Barbushi bayan su Rimsha sukabi dan su kamo su su cinye su ɗanye, dan ba zasu barsu su karya musu tarihin gidan Daular mutuwa ba, a tarihin Daular mutuwa duk wanda ya shiga baya fita ya shiga kenan sai a lahira.

Su Rimsha kuwa gudun cetan rai suke, tsabar gudun da suke basu san lokacin da suka saki hannun juna ba, kasan cikin ramin duk kasusuwan jikin ɗan adam, sai suke musu kafofin su kashin yake jini na zuba, duk da haka basu damu ba, sun daure suna ta gudu.

Kamar ance Rimsha ta juya, ta manta duna yace karsu kuskura su juya kome zai faru da su, tana juyawa sai taga babu Ayla iya Kausar ce kawai, ihu Rimsha ta saki wadda ya sa Kausar dakatawa da gudun da take tare da juyawa, a guje Rimsha ta nufi hanyar komawa Daular mutuwa dan ba zata iya tafi ba tare da Ayla ba, itama Kausar bata da zaɓi dole tabi bayan Rimsha dan su gudu tare su tsira tare. Tashin hankali

Abun da ya faru shine lokacin da suke cinkin gudu Ayla ta taka wani kashin mutun mai bala'i tsini ya fasa mata kafa, hakan yasa ta faɗi kasa, taki yin ihu tayi shiru dan bata son ta dakatar da su Rimsha har azo a kama su dukan su, tafi son ko ba ita ba wani daga cikin su ya tsira, kashin ya fasa mata kafa sosai ta yadda ba zata iya gudu ba har su Barbushi suka cin mata a wajen, shine suka kama ta, Barbushi ya goyata a bayan sa ya ci-gaba da bin su Rismha, ga kuma su Rimsha sun juyo suna tinkarar su.

Wayyo ni jikan mutun huɗu gaba ɗaya ta ko ina ba sauki, zuciyata ba zata iya jure ganin wannan azaba da my Rimsha take ciki ba.

Masu karatu nan na kawo karshen Book 1 wato The beginning kuma shine free, yanzu zamu shiga The struggle masu son ci-gaba da karanta Book nan ku hanzarta kuyi payment naku dan wasan yanzu zai fara, ya kuke ganin wannan cakwakiya, ya kuke tunanin rayuwar lion zai kasan ce bayan mutuwar Michael da ɓatar James?!!, Ya kuke ganin anya Rimsha zata tsira kuwa? Dan ita da kan ta ta juya ta koma Daular mutuwa ga kuma su barbushi ɗauke da Ayla a kan hanya suma suna tinkaro ta!! Yaya Akil zai kare da Umaisha? Meke shirin faruwa tsakanin su?! Anya Abbi zai bawa Akil auren Umaisha kenan? Ya makomar cikin Aunty? Shi zai sube kuwa? Yaya rayuwar Jehan zai kasan ce? Yaya makoman Jelly da Abbo? Yaya makoman Musharraf a gidan Dr William jacop? Gashi dai ya sa hannu a takarda zai yi zaman 4 years, gashi mai tausaya masa wato James baya nan ya ɓace!! Wanene Alhajin dake bibbiyar Aafia?!! Yaya bakoman baba da Mustapha a Daular mutuwa?!! Anya lion zai yafewa mum ɗin sa kuwa?! Anya akoi wanda zai iya rusa Daular mutuwa kuwa?!!!! Shine wace ce ma Queen?!!! Waye ya kafa Daular mutuwa?!!! Menene kama sudin kafa shi?!! Anya kuna ganin Jehan zata iya aikin restaurant har ta biya Ibraheem kuɗin sa?!!! Ina James ya tafi?!! Shine sace sa akayi ko menene?!! Abbo zai auri Jelly kuwa?!!! Idan ta kasan ce ya Imran zai yi?!!! Cakwakiya ziryan domin samun amsoshin ku dole ku kasance da alkalamin *PRINCESS TEEMA*

Domin ci-gaba da karanta book ɗin *TRIPLETS* ki hanzar ta kiyi payment naki 500 Naira ne only 👌3167987863 Musa Fatima Zahra first bank,, sai ku turo shaidar biya ta wannan number 0816 139 0581 kada ki bari a baki labari dan yazu wasan zai fara, na barku lafiya Much kauna 🥰


Share fisabilillah 👏

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai🤪

💞PRINCESS TEEMA💞





[11/11, 8:51 PM] +234 906 579 6460: TRIPLET'S💞



💔THE STRUGGLE💔



Dasunan Allah mai Rahma mai jin kai tsira da Amin sukara tabbata ga manzon mu manzon Rahma Annabi Muhammad SAW farkon ƙaga karshen aika, Allah ina mai godiya daka bani iko da dama na kammala book 1 na littafin nan Alhadulillah Alhadulillah, ya Allah ka bani ikon kammala littafin gaba ɗaya lafiya, ya Allah kasa sakon da nake son isarwa ya isa in da nake son isarwa, ya Allah ka yafe mana kura kuran mu Amin 🤲

Yanzu wasan zai fara muje zuwha, please masu taya ni sharing yanzu kam ya isa haka dan mun gama Free wannan paid ne, nagode da tayani sharing na free da mukayi Allah ya bar zumunci!!!.

Duk wanda ya karatamin book na bai biyani hakkina ba na bar mutun da Allah shi zai saka min!!!.

Ya Ubangiji bamu da wayo bamu da dabara mun miƙa wuya a gareka ya Allah ka kawowa kasan 🇳🇬 mu zaman lafiya, babu wani mahaluki da ya isa ya bawa kasar 🇳🇬 mu zaman lafiya sai kai ya Ubangijin, dan karfi ikon ka ya Allah dan isar ka da izzan ka ya Allah ka bamu zaman lafiya da kwantatciyar hankali, Allah ka karemu da kariyar ka, Allah ka bawa duk wasarasa lafiya na gida dana asibiti lafiya, Allah ka buɗawa duk wani mai neman halak ɗin sa hanyar samun sa hagun sa da daman sa gaban sa da bayan sa, ya Allah ka bamu arziki mai albarka mai amfani


O Allah, guide me along with those whom You have guided, pardon me along with those whom You have pardoned, be an ally to me along with those whom You are an ally to and bless for me that which You have bestowed. Protect me from the evil You have decreed for verily You decree and none can decree over You. For surety, he whom You show allegiance to is never abased and he whom You take as an enemy is never honoured and mighty. O our Lord, Blessed and Exalted are You.


# BOOK 2📚📙✍️


💔💔Episode 1-2💔💔


Kukan mai Tsananin Lucky, Winston, Copper, wato karnukan Michael, sosai suke haushi suna ɗaga murya wadda sai da ya bawa kowa dake cikin gidan mamaki, Romeo yana can part nasa yana aiki yayin da dad kuma ya fita ya je dan ya bawa Pasto agajin gaggawa karya mutu,

Kukan su Copper ba karamin razana su Tga sukayi ba dan basu taɓa jin su suna irin wannan kuka mai sauti haka ba, Tga da kan sa ya shiga cikin ɗakin nasu yayi, yayi amma sunki yin shiru, ya rasa me matsalar su, ya rasa ya zai yi da su dan shi ba wani damuwa da kare yayi ba bare yasan halayen su.

Romeo yana aiki a laptop amma zuciyar sa na bugawa da karfi sanna kukan da su Copper suke ya dame sa, dan har ga Allah basu taɓa kuka haka ba, banza yayi dasu dan bai kawo komai a rasan saba, ya zaci Michael ne ya musu laifi, bugun zuciyar nasa ma ya dangan ta da James, ci-gaba yayi da aikin sa yana ciza laɓɓan sa.

Da gudun gaske Brady ya shigo cikin ɗaki, kai tsaye jikin Romeo ya nufa yana ta tattaɓa shi da bakin sa yana jan shi alamar yazo ya gani, ganin Brady a haka yasa Romeo ya san ba lafiya ba, dan Brady ma baya shiga harkan kowa har su Copper baya shiga karkan su, haka Romeo ya koya masa, idan kaga Brady yayi wani yunkuri a kan abu tofa abun abun dubawa ne.

Miƙewa Romeo yayi yabi bayan Brady suka nufi waje dan yaje yaga menene ke faruwa.

Tsaye cirko cirko ya isko su Tga a tsakar gidan sunyi shiru kawai sun zabawa kofar ɗakin su lucky ido, ganin Romeo yasa suka ja baya duk suka sha jinin jikin su, suka nitsu tsit.

Kai tsaye cikin ɗakin su lucky Romeo ya nufa, yana shiga suka fara tsalle suna kama jikin sa suna daka haushi mai bala'i sauti, kasan cewar Romeo ya musu farin sani, dan yanzu a kalla su lucky sun kai 12 years tare dasu, tun suna jarirai Michael ya sayo su, su huɗu Brady shine babba sai Lucky sai Copper da Winston, kasan cewar Brady yafi girma kuma yafi kyau yasa Romeo ya ɗauke shi ya dawo nashi ya barwa Michael su copper, to karnukan basa kuka haka kawai sai da dalili mai karfi ya san halin su sosai.

A sukwane Romeo ya juyo ya dubi su Tga "Where is Michael?" Yar waige waige suka farayi alamar suna neman Michael ɗin, sai lokacin suka tuna da Michael ɗin, da sauri Romeo ya fito daga cikin ɗakin, lucky na kokarin bin sa yayi saurin rufe kofar yana faɗin "I said whare is Michael? What happened to him?" Lokaci guda tsoro ya bayyana a kan fuskar kowa dake wajen, dan sunji Romeo yace me ya faru da Michael, ina kuma yake, dama kuma tun da sukaji yadda su copper ke wannan daka haushi mai razana kwakwalwar suka san ba lafiya ba, sai dai basu yi tunani wani abune ya faru da Michael ba.

Romeo ya san su Copper ba zasu yi kuka haka kawai ba, dan karnuka daban suke da ɗan adam suna da kaifin gani mai nisa, idon su na ganin abun da ɗan adam baya gani.

Da sauri Romeo ya koma cikin gida, part ɗin Michael ya nufa dan ya duba shi, ko da yaje part ɗin Michael Michael ɗin baya nan, part nasa ya koma ya ɗauki wayar sa ya kira layin Michael, tana ta ringing amma bai ɗauka ba.

Ɗauko laptop nasa yayi ya shigar da number Michael ɗin dan yabi diddigin ina Michael ɗin yake

Yana shigar da number ta nuna masa wayar Michael na *Medstar Washington hospital center* kara zaro dara daran blue eyes nasa yayi har sai da suka kara kyalli sosai, shi dai yasan yanzun nan ba jimawa Michael na gidan nan har ya mare sa, to me ya kai sa hospital kuma.

A sukwane ya ajiye laptop ɗin ya ɗauki wayar sa ya fice daga bedroom ɗin.

Yana fitowa ya bawa sojojin sa umarni a kan su tashi motoncin zuwa *Medstar Washington hospital center* ji kake dip, dip, dip, jibga jibgan sojojin nan na gudu suka haye saman bayan motoncin su, shi kuma Romeo farar motar sa kirar *Bugatti La voiture* ya shiga

Kamar ɗazun jerawa sukayi cikin dankara dankaran motoncin su sukayi layi a jere suka bar gidan, sai mamakin meke faruwa su Tga suke suna son sanin abun dake faruwa amma ba halin tambayar Romeo domin babu dama ba mai karfin zuciyar tinkarar sa dan yadda sukaga wannan fusataccen fuskar nasa abun ba'a magana.

Suna isa asibitin jibga jibgan sojojin nan suka diddiro kasa daga bayan motoncin su, a guje suka je suka kewaye gaba ɗaya asibitin ga hannun su riƙe da manya manyan makamai masu numfashi wadda kusan kare dangi za'a kira jibga jibgan makaman nasu.

cikin sauri lion ya fito ya nufi cikin hospital ɗin jinga jibgan sojoji 6 suka take masa baya, sai furzar da iska mai bala'i zafi yake daga bakin sa, yana wani huci.

Duk wanda ya hango lion daga nesa a cikin asibitin tofa a sukwane yake canza hanya yabi wani wajen saboda tsoro ga fuskokin wayan nan fusatattun sojijin nan masu razanar da mai rai

Kai tsaye office ɗin babban dr suka wuce, duk wani hallitar dake cikin asibitin nan wanda yaga shigowar motoncin su lion sai da ya razana kowa ya nitsu ya ɓoye kan sa a ɗakin sa, ji kake tsit duk girman asibitin kowa ya nitsu suna tsoron ruwan wuta.

Kai tsaye ɗakin da Michael ke kwance dr yayiwa su lion jagora, yana kwance saman gado bawan Allah fuskar nan tasa tayi wani fayau da ita, har wani yellow yayi, fuskar nasa ta kunbura sosai, ga jinin sa na malala kamar fanfo har kasan gadon da yake kwance a kai, kallo ɗaya zaka masa ka san babu rai a jikin sa.

Gaban gadon Romeo yaje ya tsaya yana kallon fuskar Michael ɗin, ganin abun yake kamar a mafarki kamar ba gaskiya bane, lokaci guda idon lion ta rikiɗe tayi jawur kamar jini, har wani mimmiƙewa zara zaran eyelashes nasa suke saboda tashin hankali da ya shiga, zuciyar sa dukan uku uku take ji yake kamar ya fasa ihu ko zai samu sauki a ransa, gaba ɗaya jijiyoyin dake jikin sa sai da suka mimmiƙe, jikin sa har wani tsuma yake saboda ɓacin rai da tashin hankali, lokaci guda ya sauya kamar ba shi ba, wasu zara zaran jijiyoyi ne suka bayyana a wuyar sa, ga wani zufan wahala dake karyo masa a gefe da gefen kunnen sa, zuciyar na tafasa kamar an ɗaurata saman wuta mai bala'i ci da zafi.

Cikin kankanin lokaci labarin mutuwar Micheal ta karaɗe ko ina a birnin Washington DC lungu da sako, ba karamin girgiza Washington DC tayi ba


Ba iya lion ne kawai ya girgiza ba, ba gaba ɗaya birnin Washington DC sai da ta girgiza da mutuwar ɗaya daga cikin family William jacop, cikin family ma, ɗaya daga cikin Triplets tashin hankali, lungu da sako ko ina sai da ya girgiza saboda sakon mutuwar Michael ya kewaye ko ina cikin kankanin lokaci yan jarida da gidan Tv suka baza zancen, duk wani harka a cikin birnin sai da ya dakata cak, komai ya tsaya cak, duk kasuwanni an rufe su, shugaban kasa da kan sa ya fito yayi magana a kan a dakatar da komai a cikin kasan, saboda The general of the army yayi rashin Triplets nasa ɗaya, duk wasu makaratu a ranar sai da aka rufe su, duk yadda Washington DC keda girma ga harka ranar tsit kake ji, zaka iya kwanciya a kan titin ka jima mota bata zo ta

Please Login or Register in order to submit comment