You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana zama da ita yana bata hakuri ya yi ta tausanta, shi kuma Irfan da ta bukaci wani abin shi yake biya mata bukata, ya sawo ya kawo mata, iya shine kawai ke haɗa su, bacin haka baya shiga harkar ta, dan bai son reni, ya girmeta kusan da shekaru biyar zuwa shidda.

"A'afia tana gidan bappa babba, amma zata dawo" ya bata amsa tare da miƙewa, shima daddy'n jelly miƙewa ya yi suka nufi waje suna kara gayawa Aunty da ta shirya anjuma zasu wuce sabon gidan.

To ta bisu da shi, sannan ta kira mai aikinsu da Abbi ya kawo, a kan yazo ta shiga da Ayla ɗakin su Aafia ta je ta yi wanka ta huta, kafin a kawo mata abinci.

Cikin hanzari mai aikin ta zo ta mata jagora suka tafi zuwa bedroom na A'afia.

Sai da suka shiga Ayla ta ɗan zauna ta huta, sannan ta fara tunanin ina wayarta bari ta sake kiran yaya Ahmad dan ya taimaka ya tura mata layin Rimsha ta kirata ta gaya mata mamanta ta rasu, amma ina bata ga wayar ba.

Cikin sauri ta buɗe trolley ta fara dubawa, wasu tsadaddun kaya ne a cikin trolley, dukka kuma dogayen riguna ne masu kyau, sai hijabai da kuma mayuka da turaruka, sai wani haɗaɗen plat shoe guda ɗaya, sosai ta wargaza kayar amma bata ga wayar ba.

Kuka ta sa mara sauti mai tsuma zuciyar mai sauraro, hanya ɗaya da take da shi na yin magana da Rimsha, shikenan shima ya salwanta, idan ta tuna hakan sai ta ji zuciyarta tamkar zai fashe ya fito waje. Allah sarki wannan baiwar Allah akwai ciwo sosai a tattare da Rayuwar ta.

Mai aikin da ta mata jagora tana nuna mata ta fice daga ɗaki, dan haka bata samu damar ganin kukan da take yi ba, saman gadon su A'afia ta kwanta, tana hawaye har barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, ga kayanta a watse, ko wankar bata sami damar ta yi ba, haka ta yi barci.

A ɓangaren Rimsha kuwa.

Sai wuraren karfe 2:30 suka isa Katsina.

Suna isa ba ɓata lokaci ta tari abin hawa ta ce ya kaita unguwar farin yaro, domin kunnuwanta sun kasa mance mata da sunan unguwar, tun ranar da suka zo Katsina, ta kasa mance wa.

Ana kaita ta sallami mai mashin, sannan ta sanya wayarta a silent ta nufi cikin anguwarsu tana jan trolleyn ta, dan a bakin daidai wajen da aka tare Jehan ranar, a nan mai mashin ya sauƙeta, duk da cewa bata san anguwar sosai ba, amma tana iya kar bakin kokarin ta wajen tuna hanya.

Kasan cewar akwai face mask a fiskar ta hakan yasa jama'a wajen suke mata kallon wata ma'aikaciya, ga kuma kyakkyawar trolley a hannunta, abin ya kayatar, tana cikin hijabi har kasa.

Tun daga nesa ta hango gidan su, saboda tsabar murna ji tayi tamkar ta zura a kuje ta karisa gidan, wani farinciki na musamman ne ya dira mata a ranta, duk da tana cikin face mask amma bakinta yaki rufuwa saboda murmushi da take yi, tsantsar farincike ne a tattare da ita yau.

A hanzarce ta karisa wajen, turus ta tsaya ganin katon kwaɗo a jikin kofar, an rufe gidan, sakin trolley ɗin hannunta ta yi ta fara bubbuga kofar tana hawaye, tana surutai kamar haka ",Mummy, gwaggo, Jehan, ina kuka je? Ina kuka tafi kuka barni?". Abin gwanin ban tausayi

Yusuf ne ya hangota daga in da yake tsaye a kofar gidansu, a tunaninsa wata ce can daban, sai ya kariso wajen yana tambayar ta waye take nema.

A razane ta juya murya na rawa ta gaya masa, ga wayan da take nema, girgiza kai ya yi yana faɗin "Eyya ki yi hakuri ai sun barnan". Zaro dara-daran sleeping eyes nata ta yi har tana haɗe words wajen ce masa "Ina suka koma dan Allah, ka gaya mini, ni yarsuce".

Cikin sauri ya ce "Ke ce Rimsha wace ta ɓata?" A hanzarce ta gyaɗa masa kai alamar E ita ce.

"Allah sarki ai su mum sun sha wahala wajen neman ki, har suka godewa Allah, yanzu dai muje na kai ki wajen mamana ki zauna har yaya Sadiq ya dawo daga wajen aiki, wata kila shi yasan in da suka tafi, amma ni dai ban sani ba, domin shekaranjiya, yaya Sadiq da ya dawo da daddare yake ce mini ai su mummy sun bar nan, wlh bakina kuma ya mini nauyin na tambaye shi ina suka tafi".

Sosai Rimsha ke kuka tana tunanin ina su mummy suka tafi. Jiki a mace ta bi bayan Yusuf, ya ɗauka mata trolley ta suka wuce gidansu.

Sai kallonta yan unguwa suke yi.

Ko da suka shiga gidan, sai kallonta Amarya da su Hanan suke yi.

Kai tsaye ɗakin mamansa ya wuce da ita, kwance suka iskota saman yar katifarta.

Sallama Yusuf ya yi mata sannan suka shige ciki, da kallo ɗaya maman Sadiq ta yi wa Rimsha ta gane yar mummy ce, domin idan baku mance ba, ita Rimsha babu in da ta bar mum a kamanni, ita kuma Jehan daddy ta ɗauko.

Tarbar mutunci maman Sadiq ta yi mata sannan ta bata ruwa cikin sakin fuska.

Rimsha ta kasa shan komai, abu biyu take bukata, na farko ta ji ina su mum suke, na biyu kuma ta je a wanke mata kannan nata ya yi datti sosai, tun ranar da ta wanke a gidan su Kausar bata sake samun dama ta wanke ba.

Saboda tsabar ƙaguwa, ta kasa hakuri har sai da ta ce "Mama dan Allah ina su mummyna suke?" Cike da tausayinta ta ce "Kiyi hakuri yar nan su mummynki sun bar nan shekaranjiya, bayan an tafi da Jehan kenan".

Kara zaro idanuwanta waje ta yi, cike da matsanancin tashin hankali mara misaltuwa ta ce "Mama ina suka koma?" Ajiyar zuciya maman Sadiq ta sauke kafin ta fara magana "E gaskiya dalilai biyu ya sanya suka bar nan, na farko an tafi da Jehan mummynku tana a halin rashin lafiya, to a ranar da aka tafi da Jehan ɗin a ranar mymmyn ku ta farfaɗo, kuma anyi sa'a ta farfaɗo cikin koshin lafiyarta, jin cewa antafi da Jehan sai ta ce ba zata yarda ba, baki nan ga mahaifinku baya nan, sannan Jehan yar ɗaya ɗayan ma a ce an tafi da ita, gaskiya ba zai yiwu ba, ya zama dole Jehan ta dawo, shine suka nemi aron waya suka kira number da matar ta basu bata shiga, suka je ɗakin jinyar da matar take jinyar yar uwarta, a nan ake gaya musu cewa, ai ba yar uwarta bace, ashe wai kanwar kawarta ce ke jinya tazo duba ta, da suka tambayi kawar a ina za su ga matar, sai ta ce musu ita ma bata sani ba, domin a online suka haɗu, address ɗin da ta rubuta musu ma, ashe address ɗin gidan su wannan kawar tata ce, shine fa hankalin su mum ya yi muguwar tashi ko in ce miki hankalin mu ya tashi, muna tsaka da Wannan tashin hankali kuma bayan na dawo gida na baro su a asibiti dan ba'a sallamosu ba, da daddare wasu mutane suka shigo gidan nan, hannunsu riƙe da bindiga wai suna neman Jehan da iyayenta, ba su kira sunan Jehan ɗin kai tsaye ba, amma kwatancen da suka yi ya tabbatar da Jehan ɗin suke nema, da kyar muka sha a gidan nan, dan sunce sai mun gaya musu ko kuma su kashe mu, ga shi mu kuma ba zamu iya gaya musu cewa mummy na asibiti ba, hakan yasa Sadiq ya ce musu ai su mummy sun gudu ne sun tafi Kano, shine muka samu muka tsira, washegari da asuba Sadiq ya je asibiti ya sanar da su mummy abin da ya faru da mu, shine fa daga asibitin basu dawo nan ba, gari na yin haske ba su ma jira sallama ba, suka bar Katsina, mu dai sun ce mana neman Jehan za su je yi".

Tun da maman Sadiq ta fara magana Rimsha ke hawaye har ta kai karshen maganar, ta kasa yin shiru, tunani kawai take yi me Jehan ta yi suke nemanta, ko dai mutanen da suka kashe mata daddyn tane suka biyosu har nan.

Tana tsaka da wannan tunani bata kai karshen ba ta yanke jiki ta sulale kasa sumammiya.

(Nima kuma na tattare kayana zuwa Washington DC dan naje naga yaya baby Michael ya yi buɗa baki, sai mun dawo🛫🛬)

Misalin karfe 5 na yamma, gaba ɗayan su zaune suke a palon kasa, ban da Lion and James su ba su nan, sai Michael da Musharraf, suma suna part nasu, Uncle Herry yana zaune ga hannunsa duk bandeji, yau aka dawo da shi gida ba jima, daddy zai cigaba da ba shi kulawa, ita kuma Jennifer yan uwanta sun ɗauke ta, uncle T yana zaune yana fama da laptop, da alama wani aiki mai muhimmanci yake yi, John yana rike da wayarsa yana kallo, Jay kuma dama kunsan yana word room yana fama da jinya, daddy kuma yana kishingiɗe yana kallo.

Da kyar da kyar Michael ke sako kafarsa a benen yana saukowa palon kasa, dukkan su sun zuba masa ido, ban da John da ya kafe waya da ido, har daddy sai da ya miƙe zaune suna kallon yadda Michael ke wani irin layi kamar wadda yake cikin maye.

Bai bi da kan kowa ba, ya wuce saman sofa, ya yi bismillahi a bayyane zai zauna, daddy da Uncle T ne suka daka masa tsawa a tare suna tambayar me ya ce, ko kallon in da suke bai yi ba, bare ma su saka ran zai basu amsa, ya yi zaman sa kusa da John, yana jin cikin sa na mashi ƙugin yunwa.

"Michael na ji kamar kayi wani yare ne da zaka zauna yanzu" Tga ne ya tambaya, daddy kuma shiru ya yi yana maimaita kalmar bismillahi a zuciyarsa, domin shi ya ji abin da Michael ɗin ya ce.

"Uncle T please leave me, i don't want to talk now". Kallon daddy uncle T ya yi yaga alamar daddy fa ya lula duniyar tunani ne.

Michael kuwa yana kokarin kwanciya karaf idanuwansa suka sauka kan John, mamaki ne ya bayyana a kan fuskar sa, a zuciyarsa ya ce.

"Wai nikam me John yake yi da waya ne, kullun ba shi da aiki sai latsar waya, sai ya yi shiru a waje, ba zaka taɓa jin motsin sa ba, tamkar baya nan". Yana zancen zuci yana karewa John kallo, kara zaro idanuwansa waje ya yi ganin yadda John yake wani mammatse jikinsa. Cikin dabara ya kai hannunsa ya fusge wayar John ɗin, ya kawota sai tin fuskar sa dan ya ga me John ke kallo.

Shiru ya yi sumar zaune, gaba ɗaya palon kallon shi suke yi, suna so suji akan me ya kwace wayar John, amma ina ya kasa motsi, basu ankaraba kawai sai ganin wayar John ɗin suka yi ya faɗi kasa, alamar Michael ya sume musu awajen.

A sukwane Tga ya ajiye laptop ɗin sa, ya taso da sauri ya zo ya taɓa shi yana faɗin "Michael are you okey?" Yana taɓa shi Micheal na sake masa jiki ka faɗo jikinsa.

Jijjiga shi Tga ya fara yi sosai, tuni su daddy ma suka yo kansa, shi ma John ɗaukar wayar tasa ya yi ya yi kan Micheal ɗin, sai kiran sunan shi suke yi amma ina, sai da daddy ya ce a bashi ruwa domin Michael suma ya yi.

Kwantar da shi Tga ya yi ya damko wuyar John yana tambayar sa menene a wayar tasa da ta sanya Michael suma, John ya ji shaƙa da kyar ya iya miƙa masa wayar a kan ya duba ya gani, dan shima bai sani ba.

Tga na karɓar wayar John ya wuce da wuri ya je ya kawowa daddy ruwa dan a yayyafawa Michael.

Yana kawo ruwa daddy ya karɓa ya buɗe tare da tarfo ruwar a hannun sa, Tga na kokarin duba wayar John, bai san lokacin da daddy ya zubawa Michael ruwa ba, sai dai ganin Michael suka yi ya tashi da sauri ya diro kasa daga saman sofar, yana haki kamar wadda ya yi gudu.

Zuba masa ido suka yi har shi Tga ɗin, ya dakata da duba wayar ya koma kallon Michael, abin da ya basu mamaki shine, Michael na saukowa daga saman sofa sai ya fara ƙoƙarin cire wandon sa.

Abin da ya faru abin da ya gani a cikin wayar John ta sanya shi suma, film ɗin batsa John ke kallo wato bf, tun da yake a rayuwarsa bai san da wannan ba, shi kwata-kwata ma bai taba lura me a cikin wandonsa ba. Bawan Allah bai san komai ba saboda ciwon nan nasa, amma yau sai ga shi ya ga abu muraran ga mace ga namiji tsirara, shine ya diro kasa dan ya cire wandonsa ya duba shin shima abin da ya gani a video a tattare da namijin nan shine a wandonsa ne ko yaya.

Yau su daddy sun ga iko god, domin kuwa Michael dai ya ga abin da ya kwance masa lissafin ƙwaƙwalwarsa, cikin sauri Tga ya riƙe hannunsa yana faɗin "Michael what is wrong with you ne?". Kunsan Turawa basu da kunya ko kaɗan, a nan tsakar palo gaban kowa Michael ke son cire wandonsa dan ya duba.

"Uncle T I want check something inside my trouser". "What is This that you want to check".

Shiru ya ɗan yi kafin ya nunawa uncle T abin da ya gani da hannunsa, yana yi yana magana bawan Allah ya ce abin kato ne kamar hannusa.

Kallon daddy uncle T ya yi dan ya gane me Michael yake son dubawa, shima daddy ya gane. Allah sarki ciwon Michael bata yi masa adalci ba, domin ko abin da yake cikin wandonsa bata bari ya iya samun damar sanin menene ba, bare kuma har aje ga sauran abubuwa, ashe ba abanza shi Micheal ya fi kowa ganin mace a matsayin katon gardi ba, duk da cewa dukkan su gidan kusan haka ne, idan ban da Jay ba wani mai wani tunani a kan mace, barema Lion da James sun fi kowa yi wa mace kallon namiji, sai dai su da lafiyarsu suke yi mata kallon da ita da namiji duk ɗaya ne, kuma bata da wani amfani, tsaɓanin shi kuma Michael na shi ya haɗu da ciwo, su ko dan saboda aikin da suke yi ma ba za su so ganin mace a kusa da su ba, James yana ta'addancin ina yake da lokacin mace, shi kuma Lion a yanzu dai baya wani aiki a matsayinsa na babba, sai dai ya sanya yara su yi aiki, amma ba shi da wani feeling a kan mace, kuma hakan ya samo asaline saboda tun baya lokacin da yake aiki sosai irin horon da ya yi wa kansa kenan, a lokacin ya tsani mum ɗin su over, lokacin zuciyar yaranta, hakan yasa ya tsani mata gaba ɗaya, yanzu kuma daya girma sosai ya mallaki hankalin kansa, ya rage tsanar da ya yi wa mum ɗin, saboda a cewarsa bashi da lokacin ta yanzu, to amma saura mata kuma yariga ya faro gininsa babu su a tsarinsa, sai ginin nasa ta tafi a kan hakan kawai, har wa yau, bai taɓa ɗaga ido ya kalli wata mace ba, saboda shi tun asalinsa in da yake tafiya nan kawai yake kallo, baya kalle kalle haka zalika baya son a kalle shi.

(Mu koma cikin labarin mu)

Sai kokarin cire wandon Michael yake yi, da kyar Tga ya dakatar da shi, amma shi ya dage sai fa ya ga me a wandorsa shi ma, tun da yau yaga zahiri, a saman wuya Tga ya ɗauke shi yana ƙoƙarin fara kewaye palon da shi dan ya lallaɓashi, kamar daga sama suka ji daddaɗar kamshin perfume nan, wadda mutun ɗaya ke amfani da shi.

Cikin sauri Tga ya sauƙe Michael gaba ɗayan su suka natsu, ban da daddy duk kan su sun kasa ɗaga ido su kalli saman benen, domin ganin fuskarsa a wani yanayin gara maka ka kalli fuskar Tiger a tsakiyar dokar daji, kuma dama ba ko wani lokaci suke iya kallonsa idan sun ji kamshin perfume nasa ba, domin idan ka sake ka kalleshi ka bari kuka haɗa ido tofa kai kam ka shiryawa hukunci, dan kwata-kwata baya son kallo a rayuwarsa.

Sai wani nuku-nuku suke yi, suna son sanin shin su yake kallo ne ko kuma dai ya aka ciki, shi John ya fi kowa shiga tashin hankali da ruɗu.

Michael zama ya yi yana turo baki, ɗan wannan hirar da ya yi a palo, tasa ya rage jin yunwa.

Lion ya jima tsaye yana kallonsu yana tunanin irin hukuncin da ta dace da su, bf kuma a gidan nan, abin ya ɓata mashi rai, yana kwance a saman bed nasa a ɗaki ya ga abin da suke yi a cikin Tv, amma hakan kuma da suka yi ya ɗan sa ya fahimci wani abin dangane da ciwon Michael, ya lura kamar sarrafa Michael ake yi, wasu abubuwa ba yin kansa bane, saboda yanzu zaka iya ganin Michael tamkar cikakken mutum anjima ka ganshi kamar a birkice, yau da Michael ya ce bai san asalin me a wandonsa ba, kuma bayan yana wanka abin ya ɗan bawa Lion mamaki, ya kuma kara darsa ayar tambaya a kan Micheal ɗin sosai.

Sun kwashe 10mins a haka kafin ya ce da Tga ya hukunta John yadda ya kamata, shi kuma Michael yazo su wuce ɗaki.

Cikin sauri Michael ya miƙe ya bi bayan sa, shi kuma Tga da yanzu ya gane me Michael ya kalla a wayar John sai ya fara da fasa wayar sannan ya ɗauki John a kafaɗar sa suka fice waje.

Yin hakan da John ya yi a wajen Turawa ba laifin bane, amma su a tsarin gidan su, laifi ne, domin ko Lion baya nan, Tga sai ya hukunta John, saboda su basa son ire-iren waɗan nan abubuwa, kuma Lion bai shiga hakkin kowa ba, ya ce duk mai son aure ya yi magana ayi mashi, kuma yana yin pastor ko in ce yana yin church da suke bi, basu yarda da ganin ire-iren su Bf ba, domin a Kristen ɗin ma, ko wani church da abin da suka fi bawa karfi, to su church nasu bai yarda da yin hakan ba, domin sun san biyawa kai bukata babbar illace ga lafiya, hakan yasa suka tsawata, bayan kuma an tsawatar a church daddy ma ya kara tsawatar musu a gida, da yake sun rena daddy shine shi John ya aikata.

Lion kuwa suna shiga bedroom nasa Micheal ya yi maza ya haye bed, domin yanzu ya fara mancewa da zancen yunwa da yake ji.

Dama Lion yana da aiki a gabansa, dan haka sai ya ɗauko laptop nasa, ya zauna a saman bed ɗin kusa da Michael, bayan ya kunna laptop ɗin ya gama komai ne ya ɗauko ɗaya daga cikin watch nasu na Triplets,

A hankali ya zaro memory's ɗin, ya ciri guda ɗaya ya sanya cikin system ɗin, videos sosai ya fara cin karo da su, kan vedio na farko ya fara dannawa ya yi Play, Michael na kwance a gefensa kamar a mafarki ya ji muryan James a cikin video yana faɗin "Idan ka je lahira ka sanar da su Roshan ni na kashe su" a sukwane Michael ya miƙe zaune yana kallon system ɗin, ya yin da shima Romeo ya kafe video da idanuwansa, James ne ke tsaye a gaban camera daya kunna da kansa, ya na riƙe da gashin wani dattijon Bature, wadda da ka gan shi ka san mutumin kirkine dan ya yi shigar mutunci, kuma da alama yana da mukami a gomnatance, sannan kuma ya tsufa dan zai kai 50 to 55 years haka, sai hawaye mutumin nan yake yi, ga shi ba halin ya yi magana domin James ya ɗaure masa bakin sa, sai dai hawayen sa kawai zaka gani, abin tausayi.

Babu tausayi babu imani da iya karfinsa James ya sanya wukar dake hannunsa mai bala'in kaifi ya yanka wuyar mutumin nan, sai jini ya fara feshi kamar fanfo. Ihu Michael ya kurma yana faɗin "No this is not my blood, wannan ba shi bane wani ne mai kama da James" Romeo kuwa ko a jikinsa dan kisan da ya fi wannan muni ma ya saba gani, shi ba ma James yake kallo ba wani tambari hoto dake bayan su yake kallo, yana son gane wace kungiya ce, ihu da Michael yake yi kamar zararre ne ya sanya shi juyawa ya daka mashi tsawa a kan ya yi mashi shiru, yana takura mashi yana aiki. Tsabar tsorata da tsawar ta sanya Michael sumewa a wajen.

Bayan James ya yanka mutumin sai ya ɗauko fake face na sa ya sanya sannan ya wuce ya kashe cameran. Video na biyu lion na sake yin playing, a nan ma dai James ɗin ne ke zaune a sansanin su na yan ta'adda, sai dai a wannan video da fake face a fuskar sa, yana zaune suna haɗa boma bomai, wasu gunguma gumguman yan ta'adda ne a cike a wajen, mai ɗaukar su video yana bin su ɗaya bayan ɗaya yana basu hannu suna dunkule nasu su bugi na juna.

Ko da yazo kan James ko kallon in da yake James bai yi ba, sai faman haɗa bom nasa kawai yake yi, ga tarin wayoyin lantarki a gabansa, idan ka kalli James a wajen, ya saje da su, barema da ya sanya wannan fuskar robar tasa, ba zaka taɓa cewa shi ɗin bane, ya shige cikinsu sun saje da juna, sai famar aiki yake yi, ba dan Lion ya kalli video na farko, ya kalli yadda James ya sanya fake face ɗin ba, da shima ba zai gane fuskarsa ba, sai dai ya gane shi da jikinsa.

Karewa mutanen wajen kallon Lion ya yi, suna nan kamar wasu yan yinwa, ya faɗa a ransa, kuma haka ne, a kaidar ta'addancin akwai kuɗi amma ba damar su iya zama suci kuɗin nasu, kullun suna cikin fargabar za'a kawo musu hari dan ɗaukar fansa, kullun tunanin yadda zasu farmaki waje kaza suke yi, dan su zama don a kasa, abincin kirkima basu iya zama su ci.

Fita daga video lion ya yi ya sake shiga wani, nan kuma James da kansa yake ɗaurawa kananan yara bom a jikinsu, yaran da basu fi 15 years ba, runtse ido Lion ya yi ya fita daga wannan video, gaba ɗaya ya zare Memory ya ajiye ya ɗauki ɗayar ya sanya, bayai ne a kan ta'addancin, da kuma kungiyoyin da James ya kai wa hari ya taɓa su, ya kashe musu mutane, jerin kungiyoyin Lion ya zubawa ido yana kallon, manya-manyan kungiya uku James ya kaiwa hari ya kuma kashe wasu daga cikinsu, kuma dukka mai gidansa ya sanya shi wannan aiki, shiru Lion ya yi yana tunanin dole a cikin wayan nan kungiya ukun ne ɗaya suka kama James dan ɗaukar fansa, to su waye?

Bashi da isashen lokacin da zai yi bincike a kan ko wace kungiya, hakan yasa ya yi watsi da su gaba ɗaya ya cire memory ma gaba ɗaya ya zube su cikin drawer, dan ba abin da za su kara masa sai zafin kai, dama idan baku manta ba, shi Lion baya karɓar taimakon kowa, aiki da ƙwaƙwalwarsa kawai yake yi, dan hakan yasa ya yi watsi da wayan can, a cewarsa faɗuwa ce ya karɓi taimakon wani, dan haka sai ya cigaba da aikin da nasa ƙwaƙwalwar kawai ba tare da ya dubi wani taimako daga wani wajen ba.

Michael kuwa ba shine ya farfaɗo ba sai karfe 7 nan ma Lion ya fito palon kasa ne ya cikaro da Tga a Palo, sai ya bashi umarnin a kan yazo ya zubawa Michael ruwa.

Yana farfaɗowa, da sunan James a bakinsa ya farfaɗo, sosai Tga ya rinƙa rarrashin shi yana lallaɓa shi, da kyar ya hakura ya miƙe ya nufi part nasa.

Nan ya isko Musharraf yana buɗa baki, zama ya yi a kusa da shi yana faɗin "Uncle ɗin James lokacin cin abinci ya ne?" Gyaɗa masa kai Musharraf ya yi sannan ya ce "Tun ɗazun na fita na nemeka a palo ban ganka ba, shine na haɗo tea da kayan fruits nace bari nazo na yi buɗa baki na".

Miƙewa ya yi ya nufi hanyar fita yana faɗin "Kazo muje palon kasa mu ci abinci mai kyau". Kasan cewar Musharraf

Please Login or Register in order to submit comment