You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake yi a kan A.E.A shiyasa ya tarasu a ɗakin bincike suna duba wasu gunjiyoyin dake kewaye da A.E.A.

Tyrone ne ya ɗago kai cikin girmamawa murya kasa kasa a nutse yadda kasan wanda yake gaban mahaifinsa, wani ma ko mahaifinsa ba zai yi wa irin wannan biyayya ba, muryarsa har sarkewa take yi ya ce "Sir meyasa zaka tafi next week, why ba zaka bari sai nan da 3 weeks ɗin kamar yadda suka rubuta nan da 3 weeks za su yi gangami a wajen ba, kaga a lokacin zaka iya bamu umarni mu yi musu dirar mikiya mu kashe kowa mu ɗauko James".

Shiru Lion ya yi yana mamakin ma ya akayi mutun mai ƙaramin kwakwalwa irin Tyrone ya zama lieutenant General kwakwalwarsa sam bata da kaifin gudu na hangen nesa, ya zama dole ya rinƙa kara musu hangen nesa idan ba haka ba wata rana za su yi shirme.

Ya jima shiru bai yi magana ba, sai da ya kwashi good 15 mins san nan ya ce "Saboda C.I.A"

Kallon Tga Tyrone ya yi, yana son karin haske amma yana tsoron sake yin wata tambayar saboda ya san Lion baya son yawan surutu, idan ka cika saka shi magana sai ya jefaka ta window kowa ya huta.

Sarai Lion ya san suna sun karin haske, kuma yasan tambayar da za su yi mashi, hakan ya sa ya ce "Idan har C.I.A suka riga mu isa ga James to fa zasu har be shi ne lokaci guda ya mutu, ni kuma ba haka nake so ba, ina bukatar wasu amsoshin daga wajen shi kafin na hukunta shi". Tga ne ya yi karfin hali cewq "To why not ba zamu tafi tare ba? Please Lion ka taimaka ka bari mu bika, ina bukatar kama James da hannuna". Wucewa Lion ya yi ba tare da ya sake yi musu magana ba, dama kuma sun san hakan domin baya magana biyu. Shi dai Tyrone mutuwar tsaye ya yi yana zancen zuci "lallai James ya cika tantirin ɗan ta'adda, irin wannan kisa da yake yi kamar ba mutane yake kashe wa ba, shi kawai da sun ba shi aiki sai ya karɓa, baya duba waye zai kashe, kai anyama James jinin Romeo ne kuwa? Domin Romeo da Michael dai ba haka suke ba, sannan Romeo da yake The General of the Army ma ba ya yin irin kisan rashin imanin da James ke yi ba.

Wucewa Tga ya yi ya bi bayan Lion dan yau ko dukan shi Lion zai yi sai dai ya duke shi, amma sai ya roƙe shi akan su tafi tare.

Zaune saman bed ya isko shi ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin. Gefen shi Tga ya zo ya zauna, shiru suka yi na tsawon mintuna ashirin.

Sannan Tga ya ce "Lion ka bari ku tafi tare mana, ina son kama James da hannuna".

Shiru Lion ya yi mashi kamar ba shi a wajen, zuba mashi ido Tga ya yi yana jiran amsa, tsawon mituna biyar sannan in a cool voice a nutse ya fara magana "Ba tare za mu tafi ba, amma dai ku zaku tarwatsa sansanin, sai dai ina son kasan wani abu ɗaya, James ba zai kamun maka ba, domin ya wuce yadda kake tunani, zata iya yiwu wa ku iya tarwatsa wayan da suka kama shi, amma fa ka sani daga lokacin da ku ka kuɓutar da shi daga hannunsu tofa kai kuma ba zaka iya kama shi ka dawo da shi gida ba".

Zaro ido Tga ya yi yana mamakin kalaman Romeo, cike da tsoro ya sake tambayarsa "Me yasa ba zan iya kama shi ba?". Nan ma dai shiru na ƴan mintoci Lion ya yi kafin ya ce "Bawai ba zaka iya kama shi ba ne, kunema zaku yaki kungiyar amma dai ina son ka sani James ya fi General training mai karfi, sannan ya fi General ƙwaƙwalwa saboda jinane shi, ba bu wata hukuma da zata iya kama shi cikin sauƙi, mutane biyu ne training na su yake gaba da James a yanzu, na farko The general of the army, ajiye muƙamina a gefe, na biyu Ni da kai na, bayan ni ba mai iya kama James cikin sauki". Kasa magana Tga ya yi domin Lion ya ɗaure mashi kai dayawa, shi dai ya san koda James yana kashe mutane shi da yake matsayin uncle nasa ba zai kashe shi ba, amma me yasa James ba zai kamun musu ba? Shine abin da ya tsaya mashi a rai.

Miƙewa Lion ya yi ya nufi Balcony yana faɗin "General kada ka rikita kanta dayawa, James ba zai kamun muku cikin sauki yadda ka ke tunanin nan ba, domin kuwa kungiya daban daban ne suke neman shi ruwa a jallo, sannan ni ma yanzu idan na fita kasar nan bawai kai tsaye kama James zan je yi ba, no bam ma tabbatar a wani waje takamaimai yake ba, saina natsu". Ya kai karshen maganar tare da shigewa cikin balcony ɗin ya shige cikin karamar pool nasa dake wajen, ya lumar da jikinsa gaba ɗaya a cikin ruwan, ya bar iya kai kawai a wajen, sannan ya lumshe idanuwansa kamar mai yin barci.

Shi kuma Tga tashi ya yi, jiki ba kwari zuciya cike fal da tunani ya wuce ya koma wajen Tyrone dan su ci-gaba da aikin da ya sanya su.

Shi kuma John yana word room dan ya ci kwakwa wajen Tga, ba karamin horashi ya yi ba, hakan yasa daddy yake bashi kulawa a word room.

Shikuma Michael sai karfe takwas bayan ya gama gym ya dawo ne ya gabatar da sallar asuban shi, Musharraf na zaune yana kula da shi yadda yake Sallah har ya idar, sannan Musharraf ya gaya masa ba'a tsallake lokacin yin Sallah, da lokacin ya yi to dole ne ayi, dan haka ya koyi tashi da asuba, kasan cewar yana son abin sai ya ce da Musharraf ya yi masa alwarin zai rinƙa tashi da asuba, sosai Musharraf ya ji daɗi, kuma yasan wannan nasara da yake samu akan Michael ba komai bane face addu'ar da yake yawan yi ne Allah yake ɗaura shi a kan Micheal ɗin. Daga jiya da daddare da Michael ya karɓi musulunci zuwa yanzu, har wani haske fuskarsa ta kara, sai kyalli yake yi, har gashin kansa sai da ta san ya shiga addini kai tsarki, domin gashin nasa har wani kwanciya ta karayi tana wani curly kamar me, idanuwansa duk sun sauya, wasu sihirtattun kyau suka kara yi, idan ka gan shi kai kace ba shi ba ne, ya kara wani sihirtaccen kyau sosai abin shi, lokaci guda haiba ta bayyana a tattare da shi, ga kwarjini na addinin musulunci ya bayyana, ya ƙara natsuwa, ga shi ƙwaƙwalwar tasa tana ta kara buɗuwa saboda karatun Alkur'ani mai girma da suka yi da Musharraf jiya da daddare, Suratul Fadiha Musharraf ya koya masa jiya, bawan Allah da yake babu wata hayaniya a ƙwaƙwalwar tasa, har ya haddace surar, yanzu ba shi da damuwar komai, ya dai na fita Palo ma, yau tun safe suna tare da Musharraf ya dage a kan sai Musharraf ya kara koya masa wata surar, haka suka wuni yana koyar nasi da falaki, sai farinciki yake yi abinsa bawan Allah.......

Nima sai farinciki nake yi na tattara kayana na wuce sai mun haɗu gobe a sabon gidan Abbi idan Allah ya kai mu da rai da lafiya
[11/17, 12:27 PM] +234 906 579 6460: 💖💖TRIPLET'S💖💖


Takowa Ommu ta yi, irin takun nan na nuna isa, har gaban shi ta zo ta tsaya, from head to toe ta kare masa kallo sannan ta ce "Kayi kaɗan Maik, kuma ka kwana da shiri kamar yadda na gaya maka, next week ina nan dawowa, domin wannan gidan gidan Khadijat ce" ta kai karshen maganar tare da fice daga cikin palon fuuu kamar kumfa.

Dawo da kallonsa kan Aunty da ta yi mutuwar zaune ya yi "Ki yi hakuri Sadiya, kuma kada ki ɗauki zancen nan nata kin ji?". Gyaɗa mashi kai kawai ta yi alamar ta ji, amma cikin zuciyarta ita kaɗai ta san me take ji. Karisowa cikin palon ya yi, ya zauna saman sofa yana faɗin "A kira mini babyn daddy mu ɗan yi hira".

Murmushi Aunty ta yi tana faɗin "Yaya Maik ko dai za mu aura maka ita ne? Dan ka fita daga cikin wannan gwabrancin na shekara da shekarun, Wlh tana da hankali sosai". Dariya ma abin ya bashi, abu kamar wasan yara, cikin raha da wasa ya ce "To ai dama aurentan zan yi, kinga idan Allah ya yi muka gane Jelly sai na haɗa su na riƙe su sanya mini hawan jini da ciwon zuciya na mutu da wuri ku huta". Yar dariya Aunty ta yi kafin ta ce "Kai yaya Maik yanzu me jalila take yi maka da za ta iya sanya maka hawan jini? Sannan ita ma Ayla banga wata matsalar a tattare da ita ba" "Ke dama ta ina zaki ga matsalarsu, ai ina rokar Allah ya sanya a gane Jelly, zan baki ita na kwana biyu, ina ga ko kwana ɗaya ma ba zata yi ba, zaki dawo mini da aba ta" kara faɗa murmushinta tayi tana kwalawa mai aikinta kira.

Da sauri yarinyar ta zo tana faɗin gata nan, umarni ta bata a kan ta kira mata Ayla, to ta amsa da shi, sannan ta tashi ta haye sama.

"Yaya Maik ni fa ba zan taɓa gajiya da Jelly ba, ni ban ma san me ta ke aikatawa da kake cewa babu mai iya ta ba sai kai ba, ban taɓa zama da ita ba, amma ina ji a jikina tana da kirki da hankali sosai" jinjina kai ya yi irin alamar abarkaza cikin gashin ta, sannan ya ce "Ai ni yanzu ma ina tausayawa duk wayanda Jelly ke hannunsu, addu'a nake yi Allah ya dawo mini da abata lafiya" Amin ta amsa da shi, sannan ita ma ta kara mashi da nata addu'ar.

Tun daga Ayla ta sako kafarta a sama benen daddyn Jelly ya tsareta da wayannan dara-daran idanun nasa irin na Jellynsa, sai kallonsu Aunty take yi tana murmushi.

Kusa da shi ta zo ta zauna dan yanzu sun saba, gaishe shi ta fara yi sannan ta tambaye shi batun school, dan ya ce Irfan ya sanya ta makaranta, tana son yin karatu sosai.

Sai kallonta yake yi ya ce "Sarkin son karatu ba, to yaya Irfan ɗin naki ya gama komai, saura mu jira narar Monday kawai ta yi" kayatatcen murmushi ne ya bayyana a kan fuskarta, sannan ta sanya hannu ta rufe fuskarta. "To jeki ki shirya mu je shopping a sayi wasu abubuwan buƙata na school dana gida". Da sauri ta miƙe tana faɗin "to daddy".

Binta da ido ya yi har ta kurewa ganinsa, sannan ya dawo da kallonsa kan Aunty dake ta kallonsu tana murmushi.

"Kina bukatar wani abin ne idan muka je shopping ɗin Sadiya?" Ya tambaya yana ƙoƙarin miƙewa. Cikin sauri ta ce "Yaya Maik zauna mu yi magana", ba musu ya koma ya zauna yana kallon Tv dake magana kasa kasa, dan shi dama idan ba dole bama baya son shigowa part ɗin Abbi, sai dan ya zamar mashi dole, haka idan ya shigo ko ɗaga ido baya yi ya kalli Aunty har sai idan bisa kuskure, ko zai kalli wani abin, kallonsa ya faɗa kanta.

"Yaya Maik wlh Allah kana son Ayla, me yasa kake ɓoye mana?" Wani irin murmushi ya yi wadda take fita da ɗan sauti kamar dariya. "Yanzu Sadiya ni na ce maki ina son Ayla? Me yasa kike haɗa ni da yar cikina ne? Kawai wlh tausayin ta nake da kuma kaunarta kamar yadda nake son Jelly, sannan kuma tana da hankali sosai, ga son karatu shiyasa nake jin ta a rai na, kuma nake son ganin ta kusa da ni tana farinciki, daɗin daɗawa kuma, ita marainiya ce a halin yanzu".

Ita ma Aunty kara faɗaɗa murmushinta ta yi ta ce "Yaya Maik wlh ba iya kaunar uba da ƴa kake yi wa Ayla ba, wlh kana son ta, so na soyayyar miji da mata, kai ne dai ba zaka yarda ba, amma tun jiya na fahimci hakan".

"Sadiya baki son zaman lafiya na lura" ya kai karshen maganar yana miƙewa, "Yaya Maik cewa fa na yi ka zauna muyi magana, to ai bamu kammala maganar ba, ina kuma zaka je?". Ba musu ya koma ya zauna yana faɗin "To maganar taki ce na lura kwata-kwata bana tsayawa a saurara bane, saboda zancen naki bai ɗauki hanyar da hankali zai kama ba".

Aunty zata yi magana Ayla ta sauƙo kasa, jikinta na sanye da hijabinta har kasa, wadda Ahmad ya saya mata, zuba mashi ido Aunty ta yi tana kallon yadda yake kallon Ayla, a cikin zuciyarta tana faɗin "Wlh yaya Maik ko kana so ko baka so ka kamu da son yarinyar nan, garama ka yi sauri ka auri abarka tun kafin arigaka, gamu da matasa a gida, suma kuma suna zuwa da abokan su, kana yin sake wani zanyi wuff da wannan santaleliyar yarinyar, ka dawo kana gwara kai da bango kana dana sani".

Kusa da shi Ayla ta sake dawowa ta zauna tana faɗin "Daddy na gama shi" ɗan ɗaure fuska ya yi kafin ya ce "Waye ya ce maki ki sanya perfume a jikin ki?" Kasa ta yi da kanta, cikin girmamawa ta ce "Kayi hakuri daddy".

Kara ɗaure fuska ya yi ya ce "A'a ba zan hakura ɗin ba, koma ki canza kayan kisa wasu wadda ba perfume sai ki zo mu tafi". To ta amsa mashi da shi sannan ta miƙe ta koma sama, Aunty dai tana ganin ikon Allah kishi karara daddyn Jelly yake nunawa a fili amma sai ya ce ba son Ayla yake yi ba tausayinta yake yi, ina aka taɓa yin hakan?.

Shiru suka zauna har Ayla ta canza kaya ta dawo. Miƙewa ya yi, ya yi gaba ta bi bayansa tana yi wa Aunty sallama. Fatan alkhari aunty ta yi musu a bayyane, daga ta ciki kuma ta yi musu fatan Allah yasa kafin su dawo sun kullu soyayya, dan tana bala'in son daddyn Jelly ya auri Ayla, ta san idan ya aureta zata samu farinciki fiye da tunanin mai tunani, mutumin kirkine sosai daddy, ga son mutane, sannan ya iya aikin komai na gida, yana da kula da yan uwansa ma bare kuma matansa, ga riƙo da addini, ya san darajar mace, ta ko'ina ya haɗa, idan Ayla ta same shi zata fita daga wannan kukan maraicin nata da take yi.

Haka Aunty ta zauna tana ta tunane tunane. Su Ayla kuma sun wuce shopping. Ni kuma na tattara kayana na wuce izuwa Washington DC dan jin wace waina ake toyawa.


💖💖Washington DC💖💖

Misalin karfe 8 na dare, Musharraf na kwance saman bed nasa, shi kaɗai a ɗakin, shi kuma Michael ya fita palon kasa. Kamar a mafarki ya rinƙa jiyo motsi kamar na mutun, idan ya tashi ya duba kuma, sai ya ga wayam ba bu komai, wani lokaci ma inuwar abu yake gani kamar mutun kamar wata halittar da ban, ta bakin kofa, amma idan ya tashi zai duba sai inuwar ta ɓace, abin har ya fara bashi ɗan tsoro-tsoro, tunani ya fara yi a kan mafarke mafarken Michael da ya rinƙa yi daren jiya, abin ya fara ɗaure mashi kai, shin meke faruwa acikin wannan gidan ne? Ya faɗa a cikin zuciyarsa.

Kamar a mafarki ya ji an kara masa karfin gudun Ac ɗakin, cikin sauri ya miƙe yana kallon yadda Ac ke gudu, ɗaukar remote ya yi ya rage gudun. Yana ragewa tun bai ajiye remote ɗin ba Ac ta sake kure gudun da kanta, a sukawane ya zaro idanuwansa waje yana kallon samar.

Da karfi-karfi Ac ke futa har kamar zata tarwatsa kanta, banda sunan Allah ba bu abin da yake iya faɗi a cikin zuciyarsa, ya tsorata sosai, wutar ɗakin ne ya fara rawa ya kawo ya ɗauke kamar spark na wutar nepa, bai ankaraba ya ga samar ɗakin nasa yana ƙoƙarin faɗo mashi a kansa, runtse idanuwansa ya yi yana ihu tare da furta sunan Allah a cikin ihun nasa, ya aza hannun bisa kayinsa yana jiran faɗowar ɗakin kawai a kansa.

Tsawon minti ɗaya ya ji shiru, ba wani abin da ya faɗo mashi, cikin sanɗa da dabara ya yi kokarin buɗe idanuwansa. Ai kuwa yana buɗe wa ya yi arba da wata iriyar halitta mai bala'in munin gaske, yar karama kamar mage, ga idanunta kamar na mutun, sake runtse idanunsa ya yi ya kurma wata razananiyar ihu da karfi!! Wadda da ka jita kasan ba ta lafiya bace.

Yana tsaka da ihun sai ya ji an taɓa shi, a zabure ya buɗe idanuwansa, a zuciyarsa yana ayyana yanzu kuma dame zai yi arba.

Tga ne tsaye a kansa, ga su John a gefe. Wata uwar tsawa Tga ya daka mashi wadda ta sanya shi haɗiyar wata bakar wahalalliyar yawu mai wuyar wuce maƙogoro, "Why are you shouting for us here?". Tsuru-tsuru ya yi da idanu ya kasa ko motsi bare kuma magana.

Ganin ya ki magana ya sa ran Tga ya kara hasala sosai, wato Musharraf ya raina shi, cikin fushi ya ɗaga hannu zai mare shi, da sauri Michael da ya shigo yanzu ya yi maza ya riƙe hannun nasa yana faɗin "Sorry uncle T, uncle ɗin James whapped kake ihu haka?".

Bin ɗakin da kallo Musharraf ya yi, komai ya koma yadda yake, wannan halittar ma ta ɓace, ga kuma Ac ya koma normal gudun da yake yi, cikin sauri ya kai kallonsa saman ɗakin dan ya ga shin shima saman ya komane ko dai ya faɗo, gaba ɗayan su da suke ɗakin suma ɗaga ido sama suka yi dan suga me yake kallon.

Sakin hannun Tga Michael ya yi, ya koma kusa da uncle ɗin James, ya zauna yana faɗin "Uncle lafiya me yake faruwa ne?" Kasa magana Musharraf ya yi, dan bai san me zai ce musu ya gani ba, wannan wace iriyar musifa ce ya faɗa a zuciyarsa.

Wucewa Tga ya yi rai a matukar ɓace ya nufi hanyar fita daga ɗakin yana faɗin "Zan turo sojoji su ɗauki mutumin nan zuwa gidan mahaukata". A zabure Michael ya miƙe tsaye,

"Uncle T uncle ɗin James ba haukaci bane, dan haka ba bu wanda zai fita da shi daga gidan nan, ai ni a gani nama ya fi ku hankali.....". Kai daga jin yadda Michael ya yi maganar kasan a matukar tsorace yake, sai wani haɗe words yake yi.

A sukawane Tga ya juyo jin yadda Michael ɗin ke ta faman haɗe masa words ɗin kamar ba lafiya ba "Michael are okey kuwa?" Gyaɗa musu kai ya yi alamar yana lafiya, shi ma John kallon tuhuma yake bin Michael ɗin da shi, domin sun ga canji sosai a tattare da shi, sannan yanzu baya shiga cikinsu suyi hira, baya zama a palo, kuma ga yawan fita da yake yi, saɓanin da a baya da baya fita, daga school sai white house, kuma babban abin da ya kara basu mamaki kuma ya ɗaure musu kai shine, na farko da ka taɓa Musharraf gara shi ka yi masa dukan tsiya, na biyu kuma jiya da kansa ya samu Lion da maganar zai koma school, abu na uku idan yana magana kamar pastor su, a cewar su, dan pastor kawai suke yi wa ganin yana magana kamar malami, to yanzu haka Michael yake yi musu magana, cike da ilimi, babu shirme kuma babu shagwaɓa sosai, duk da cewa shagwaɓar ta bishi, amma dai ya ragu sosai, yanzu idan kaga yana yin shagwaɓar ma sai idan yana bukatar wani abin daga wajen su, shine sai ya yi ta musu magana cikin shagwaɓa dan su bashi, sannan yanzu ga bala'i kaunar yan uwansa da yake yi, idan sun yi abin da ba daidai ba sai ya zauna yana ce musu hakan da suka yi babu kyau su tuba, abaya suna ɗauka cewa karatun pastor ne ya fara shiga kanshi, sai daga jiya zuwa yau sai suka fahimci ilimin Michael ya wuci na pastor, hakan yasa suka fara zargin shi, ga shi kuma idan sun tambaye shi waye ya koya mashi hakan, sai ya ce musu kawai a bakinsa ya ji ta zo masa, daga sama take zuwa.

(Dama ilimi na zuwa daga sama ne? Gaskiya Michael ka iya rainin hankali)

Amma fa duk wannan abin da Michael yake yi, Musharraf ya yi nasarar rufe bakinsa ne ta hanyar addu'a da kyakkyawar niya, hakan yasa Allah ya taimake shi ya rufe mashi bakin Michael ɗin, baya iya gayawa su Tga ga mai koya mashi abubuwa, a yan kwanaki biyun nan ya iya abubuwa sosai dan gane da addinin musulunci, ga ƙwaƙwalwar tasa sai kara buɗuwa take yi, da angaya mashi abu zai haddace, hakan ma yasa ya ce zai koma school ya ci-gaba da karatu.

"Michael you are not okey!!" Tga ya faɗa tare da dawowa cikin ɗakin, "Uncle T like how am not okey? I didn't understand" ya kai karshen maganar tare da komawa ya zauna.

Zuba musu ido Tga ya yi shi da Musharraf ɗin, yana yi musu kallon tuhuma tare da rashin yarda da su. "Where are you coming from?" Ya yi tambayar yana kallon Musharraf.

Cikin sauri Michael ya ce "he is from england" ɗaure fuska sosai Tga ya yi alamar babu wasa a tattare da shi, cike da izza da bada umarni na uncle da yaronsa ya fara magana. "Michael i don't want to hear your mouth again, hey man i said where are you coming from?". "I'm from England". Musharraf ya ba shi amsa daidai da abin da Michael ɗin ya faɗa, sai dai ya yi maganar a cikin wani irin yana yi na matsananciyar tsoro da fargaba, gabansa sai faɗuwa yake yi, dan ya san basu da imani da tausayi ko kaɗan, idan suka san shi musulmi ne ba karamin azabtar da rayuwarsa za su yi ba.

Furzar da iska mai zafi Tga ya yi daga bakinsa kafin ya ce "impossible!!" Satar kallon Michael Musharraf ɗin ya yi, daidai lokacin da ya miƙe yana faɗin "Uncle T please mana ka kyale shi ka ji? Shi ba mugu bane, kuma ba shida komai a ziciyarsa sai alkhari". Wucewa Tga ya yi ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake yin magana ba, hakan da ya yi kuma ba karamin jefasu cikin ruɗani ya yi ba, musamman shi Michael dan yasan uncle T ɗin nasa da bakar zuciya kamar me, yasan ba zai yi wu ya kyale Musharraf haka kawai ba, wannan shirun da ya yi dole akwai abin da ya ayyana a ransa.

Wucewa shima John ya yi ya bi bayan Tga, shi kuma Michael zama ya yi gefen Musharraf yana bashi hakuri, akan kada ya damu, haka yan uwansa suke, basu son baƙo ko kaɗan, amma kada ya damu ya kyalesu suyi su gama, ba komai Musharraf ya ce masa, shi ba ma su Tga ne a gaban sa ba, babban abin da yake damunsa shin wanene ke razanar da shi? Wanene zai iya kasancewa matsafi a cikin family William jacop? Domin wannan abin da suke yi tsafice, to waye ne zai yi hakan? Me yasa suka takurawa Michael shi kaɗai? Ko dan sauran basa magana ne? Me yasa tun ranar da ya musuluntar da Michael abubuwa suke ta faruwa da shi marasa kyau? Sannan meyasa kullun mace ce ke aiwatar da hakan? Hakan na nufin zancen James gaskiya ne, mum ɗin su tana da alaƙa da magicians? Ko kuma ita ke yin tsafin da kanta? To me yasa take tsafin akan ƴaƴanta na cikinta? Sannan kuma tana ikirarin tana bala'in kaunar su? Ko dai a nata haukan hakan yana nufin tana basu kariya ne?.

Wayan nan tunanin su suka cikawa Musharraf ƙwaƙwalwar kansa, wadda kuma ko kusa ko alama bashi da amsoshin su.

Idan muka koma ɓangaren Lion kuwa.

💖Bayan wasu ƴan awanni.💖

Ruwan sama ne ke zuba kamar da bakin kwarya, ga shi ruwan zuba yake yi babu iska ba tsawa, kawai shaaaa yake zuba.

Tsaye yake a balcony bedroom nasa, yana kallon yadda ruwan saman nan ke zuba Kamar da bakin kwarya, kasan cewar wutar dake a wajen blue light ne, ga kuma wajen ya yi duhun hadari, da kuma duhun dare, sai abin ya kara kyau da kawatuwa, hasken wutar

Please Login or Register in order to submit comment