You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kawo ruwa ta shiga
motar da zafin nama ranta a b’ace. Idi ya shiga ya tayar da motar yana furta “Sai hak’uri Hajja K’arama, in
dai aka ce yaro maraya ne yana rayuwa a koma ina ne sai ya yi hak’uri Allah yaji k’an mahaifiyarku
mutuniyar kirki.” “Ameen ta furta tana lumshe idonta ta jingina da jikin kujera. Haka kowa yake ce mata
amma ita ta kasa yarda, ba yarda za’a yi don uwarta bata raye a dinga takata

A gidan Ubanta ta hak’ura ina wallahi ba’a yi mata ba. Hawayen da ya fara zubo mata ta saka tissue ta
goge don ma kar a cigaba da ganin gazawarta..




A k’ofar gidan Didin ya tsaya babban gida ne irin ginin zamanin da don Didin sam ta k’i yarda a yi
renovating d’insa daga waje. Babu gate a gidan sai maka makan zaure. Daga wajen gidan kuma akwai
bishiyoyi guda biyu na guava da na mangwaro. Sai garejin ajiye mota guda d’aya.




Zaure uku zaka wuce kafin ka isa faffa’dan tsakargidan da ya ji malalan suminti mai santsin gaske tun na
zamanin Da don shima Didi ta k’i yarda a zamanantar da shi ta ce ba za’a canja mata fasalin gida daga
inda Uban Moddibo ya bar shi ba, ba za’a kawar mata da tunaninsa ba a goge memory d’insa. Bishiyu ne
a tsakar gidan guda uku maka-maka, daga gefe can kitchen ne irin dai namu na gargajiya.




Parlourn Didin jibgegene d’auke yake da wani carpet mai taushin gaske a saman carpet d’in kuma
Dadduma ce ta manyan

Mutane sai tun-tun da aka zagaye parlorn da su ba kujera a parlourn. A jikin bango kuwa T.V ce plasma
babbar gaske ita ka’dai ta yarda a sabunta mata da ta Zamani don Didi akwai son kallo. Amma daga gefe
ga ta Uban Moddibo nan da ya bar

Mata gado. Da radio irin ta da babba.




A zauren da zai sadaka da cikin gidan Amani ta ja tunga da akwatin ta ta tsaya ta daddage ta rusa ihu..
“Na shiga Uku Didi na, Dada da Safna suna shirin kasheni don an ga bani da Uwa wayyo Allah na….”
Hajja Didi da tada sallahr azahar d’inta kenan ta yi saurin sallame sallahr ta fito a guje tana furta “Wa
nake ji haka kamar muryar magajiya Uban waye zai kashe kin?” “Buzuwa da Mijin Buzuwa…” Amani ta
amsa mata da irin sunan da take kiran Moddibo da matar tasa.. Didi ta ce “Jar uba, to shigo magajiya in
dai ina raye ba mai tab’a ki ya kwana lafiya mik’o min Salula ta ki kira min Mijin Buzuwar na ji dalili….




JIKAR NASHE ✍🏽🥳HADARIN GABAS….👌
NAZEEFAH SABO NASHE.★ ✍️

𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ ✍️

08033748387.



★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ6️⃣




——-

Salular ta mik’a mata sai kuma Hajja Didin ta wurga mata harara tana furta “Duba kiga zaki ga k’wallo
guda shidda itace lambar Uban naki..” Amani ta kuwa duba sai ta ga an yi saving da hotunan ball guda
shidda murmushi ta saki wato ta inda Hajja Didi take gane numberr yaranta kenan. Dahda shine d’a na
shidda a wajen Didi ya biyo bayan mata biyar cur! Ta danna numberr kafin ta saka a handsfree don ta san
a haka Didin take waya. A duk sanda zata duba wayar sai Didi ta canja wani abin da yake banbanta mata
yaranta. A da tambarin hula ce alamar da take gane Dada, yanzu kuma ta

Mayar da shi 6Balls.




Dahda da yake tsaye kan Imani da take wani irin kuka ya kai dubansa kan wayar hannunsa yana d’an tsaki
“Ba zaki min shiru ba ne?” Ta yi k’asa da kanta kawai ba don ta daina kukan ba still idanunta na zubar da
hawaye. Yana ganin numberr First Love kamar yarda ya yiwa Didin saving ya d’an saki guntun murmushi
don ya san yau kam tunda ya tab’a Magajiyar Didi ba zaman lafiya. Wayar ya kara a kunnensa yana k’asa
da muryarsa kamar yarda ya saba “Hajja Didi….” “Tsaya Moddi ban buk’aci gaisuwarka ba, Uban me
Magajiya ta yi ka koreta daga gidanka?” Ya d’an fesar da hucin numfashi yana murza goshinsa abinda ya
zame masa al’ada, sannan cikin wata murya da bata fiye fita sosai ba ya furta “Bata gaya miki irin rashin
kirkin da take a gidan ba? ta fitini kowa ita shikkenan ba zata zauna lafiya ba?” “Bata gaya min ba, ba
kuma na buk’aci a gaya min d’in ba, yo Ai yarinta ce kuma kowane yaro da irin yarinyartarsa abu guda da
zan gaya maka ana iya canza mata banda d’a balle kai da sukkenan k’walli biyu Jalla ya baka, a haka ya
kamata ka kula da su? To kazo yanzu ka d’auketa Ai na sha gaya maka ba ta yarda za’a yi kana raye ace
y’ay’anka ba zasu zauna a gidan ka ba saboda son zuciya irin na matarka to bata isa ba gida dai gidan
Ubansu ne sai dai ita Buzuwa ta fice fit daga gidan. Mintuna ashirin na baka kazo ka d’au Magajiya Ka
mayar da ita gida….. Zan kuma zo har gidan na ja kunnen buzuwa..” Daga haka ta zame wayar a
kunnenta ba tare da ta kasheba don yana jin ta ta ce “Yi shiru kin ji Magajiya yanzu zai zo ya

Mayar da ke, ba a yi matar da zata hanaki zama gidan Ubanki ba..” “Ni gaskiya ki daina ce min Magajiya,
Ni wallahi Dahda ya cuceni da ya saka min sunanki…” “Ai inye ni kike gayawa haka? Bayan na gama
kwatar miki y’ancinki yanzu..” Dahda da yake jin komai ta cikin wayar ya saki murmushi a zuciyarsa ya ce
da’din abin kema bata kyaleki ba. Wannan yarinyar lamarinta sai addu’a sai kace Mai jinnu. Ya saka wayar
a aljihunsa yana kallon Imani ya ce “Sai ki rufe min baki yanzu zan je na d’aukota ke kanki wahalar da ke
take amma koda yaushe kin fi son ki

Ganki a tare da ita. Ya saki tsaki yana furta ranar da aure zai rabaku zan ga ya zaku yi?” Iman dai
murmushi take sai a lokacin hankalinta ya kwanta jin zaa d’auko mata Amanin. Ta bi bayan Dahdan da
kallo da ya fice cikin shigar black

Jallabiya da ta masa kyau sam ba zaka ce Dahdan ya diresu ba wani irin murjajjen jiki ne da

Shi mai kyan gaske da kullum baya tsufa ko don abin ya ha’du da arziki ana kuma cin mai kyau… Ta shige
kitchen don k’arasa abinda take ranta ta furta “Saura Inna Talatu In sha Allah itama sai ta dawo a yau.”
“Ta kori Inna Talatu ma ta ce a yau ta bar mata gidanta.” Didi ta ware ido tana furta “Ita buzuwar? Eeh to
lallai lamarin nata azimin ne, ban san sanda da na haifi Moddibo nace mata na bar mata shi ba? Irin
wannan iko haka da k’afafa sai kace ita ta min wahalar Moddibon? To Bari yazo na ji ko shine ya sahhale
mata ta dinga ikon da ta ga dama a gidan. Talatu kam ko bayan raina ba zata bar gidan Moddibo ba,
matar da tun daga k’uruciyarta take wahala da ni sai kawai don Moddibo ya yi arziki ya auro Hurul aini sai
ta koreta bari yazo na ji dalili?” Amani ta saki murmushi don ta sake kunna Didi ta furta “Didi wai wacece
Uwargida ne da Mamanmu da Buzuwa?” Didi ta saki tsaki don ko zancen bata so ta furta “Allah dai ya
gafartawa Uwarku mace ta gari salihar baiwa. Ita mai sunanta Ai kwafinta ce kwabo da kwabo Ke kuwa
ba wanda kika gado sai Dijatu itace na sha wahala da ita tana yarinya kai Allah dai ya yafewa Dijatu amma
ta yi abin da tayi lokacin yarinta shi yasa nake cewa Moddi ya k’yaleki kema zaki daina duk da har yanzu
idan Dijatu ta tubure sai kowa ya ji a jikinsa… Sallamar Dahda ce ta katse musu hirar. Didi ta amsa a
k’asan mak’oshi Amani kuwa ido ta zuba masa tana hango yarda ya gimtse fuskarsa kamar bai tab’a
dariya ba. “Tashi Magajiya ki samo masa bulala don a fuskarsa na hango so yake da ni da ke ya rufe mu
da duka, idan banda haka meye na shigowa fuskarsa a turb’une kamar dai an sanar da shi na mutu…”
Moddi d’an murmushi ya yi ya zauna a gefenta yana kama hannayenta ya furta “Allah ya rufa min asiri ba
dake nake ha’da rai ba, ni ba zan dakeki ba amma idan aka cigaba da tafiya a haka Magajiayr taki tana daf
da fara dukan mu ni da matata…” Didi ta ware ido tana furta “Allahumma ajirni! Mugun fatan da kake
mata kenan, to ba zan ga wannan ba, d’a dai kiwonsa Allah yake bawa Bawa, idan ka k’i kula da shi Allah
kai zai kama, kuma gida ba zata bar shi ba tunda gidan Ubanta ne ba na Uban buzuwa ba, don haka ka
d’auketa ku tafi a yi ta mata addu’a kurwar Yayarka Dijatu ne a tare da ita…” Moddi ya wara ido jin
abinda ta ce ya furta “Wallahi Didi ki bar maganar nan anan Kada Adda Dija ta ji ki…” “Ba zan bari ba
Dijan Uwata ce? Ai ba k’arya na fa’da ba, ba ta inda ta baro kaf halayenta, sawunka a likkafa ka d’auketa
ka bar min gida…idan ta gagareka ka kaiwa Dija ita nima ba zan iya ciwon kai ba..”

Amani ta zuba mata ido tana turo baki ta furta “Ni nake saki ciwon kai kenan? Kuma wallahi sai na
gayawa Umma Dee abinda kika ce mata.” Didi ta sake ha’de fuska duk da a ranta ta ji d’an fargabar a
gayawa Dijatun abinda ta ce sai dai bata nuna ba, ta furta “Ki gaya mata d’in tsoronta nake? Uwata ce

Ko Ubana ko kuma ita d’in ta maye gurbin Uban Moddibo ne?”

Shi dai Dahda a k’asan ransa yake murumushi a bayyane kuwa harara ya zubawa Amanin yana cije
leb’ensa. Amanin ta d’an turo baki tana kallon Didi ta furta “Allah ya kai mu asabar zaki amsa da bakin
ki…” (Asabar itace ranar da duk ahalin Didin suke bayyana a gidanta da yaransu da jikokinsu. Sak Jikin
Didin ta yi kafin ta furta “Magajiya fitina dai barci take Allah kuma ya tsinewa mai tayar da ita….” Ta

D’auke kai tana furta “Oho ashe ba kya son na gaya mata sai a bayan idonta ki yi ta zaginta

Kina ce mata mai bak’in hali amma a gaban idonta ba abinda kike iya yi sai abinda ta zartar kamar dai
Umma Dee d’in Uwarki ce?” Dahda ya waro ido kafin ya furta “Amani zagin Didin zaki yi?” “Ah to yau Kai
ka fara jin ta zageni, ai ba sabon abu bane wajen Magajiya kai kanka Ubanta ma idan ba ka nan ce maka
take Mallakak….” Wata irin sufa Amani ta yi ta dira a gabanta tana toshe mata baki “Allah ki ka gaya
masa sai na fa’dawa Umma Dee maganar rannan da kika gaya min…” Tsaf Dada ta shanye zancen. Dada
dai lumshe idonsa ya yi kafin ya

Mik’e yana wurga mata harara don yana da wajen zuwa da yamma ba zai iya da Didi da Magajiyatta ba
“To Didi bari mu wuce..” “Allah ya yi maka albarka, Yauwa Moddi ya maganar mu ta kwanaki ne? Baka
samu matar auren ba ne har yanzu? Ko sai na tara maka y’an uwanka, wace irin masifa ce ta sameka ace
kana zaune da mace ba haihuwa ta hanaka aure balle ka samu magaji, ka san dai y’ay’a mata ba naka
bane gidan wasu zasu ko?” Moddi ya koma ya zauna ya rik’e kansa kafin ya d’ago yana kallon Didi ya furta
“please Didi ki bar maganar nan, kin san dai sau uku ina neman aure bai yiwu ba to ba mamaki k’addara
ta ce a haka?” Ba wata k’addararka a haka, ni na samo maka mata yarinyar arziki shekaranjiya suka zo da
Kakarta k’awata Bintalo, ina ganin yarinyar na ji na maka sha’awarta don haka in dai ba so kake na
ha’daka da Dijatu ba ka yi azamar zuwa ku daidaita da yarinyar nan…” Yarinya kuma Didi ni zan auri
yarinya k’arama ina da wa’dannan y’an matan a gabana na auro sa’arsu ai abin kunya ne..” Didi ta saki
baki tana kallonsa kafin ta ce “Mhmn! To sannu Moddibo ina fatan ba kai ka yankewa k’asa cibiya ba? Ce
maka na yi sa’arsu ce? To nauyin aure ta yi don na san a k’alla zata yi shekaru ashirin da shidda idan ma
bata fi ba, a haihuwar tumaki ai ta haifi yaran naka.” Dahda dai ya yi shiru ba don yana jin zai iya ba. Ya
mik’e yana furta “Ke wuce mu tafi, kina zaune idanunki k’uri a bakunan mutane suna magana.” Ta mik’e
tana k’unshe dariyarta don ta san yau Didi ta kunno Dahda idan da abinda ya tsana bai wuce a masa
zancen aure ba. Ta bi bayansa bayan ta yiwa Didi sallama ta d’auke mata wani kwalin Biscuit da Didin take
ji da shi don tana cinsa sosai “Zo ki bani abu na

Ja’ira Mamuda ne ya kawo min..” Ta tsaya cak da biscuit d’in a hannunta jin abinda Didin tace don bata
son Mahmoud shine kuma ya mak’ale har da zuwa kawowa Didi Biscuit Mahmoud d’an Umma Dee ne
Yayar Dahda ta farko. Mayar da biscuit d’in tayi ta ajiye a gefen Didi “Ga abinki nan…” Didi ta saki baki
tana kallonta “saboda nace mak’iyinki ne ya kawo? Ai kuwa ko kin k’i Allah sai kin auri Mamuda…” Bata
wa Didin magana ba ta fice da sauri ta bi bayan Dahda da yake ta zabga mata horn…




Ta bu’de front seat ta shiga Dahda ya d’an kalleta ganin yarda fuskarta ta nuna b’acin ranta. Ya cigaba da
tuk’insa

Hankalinsa a kwance kafin wayarsa ta yi ringing. Ya d’aga kiran bayan ya saka wayar a bluetooth ta yarda
yake Jin maganar mai wayar a cikin radion motar. “Mun kawo paint D’in yallab’ai, masu kitchen ma duk
sun gama na part ukun ko zaka shigo ka gani?” Moddibo ya d’an Saci kallon Amani da take ta murmushi
Jin abinda aka ce a cikin wayar. Ya furta “Okay zan shigo, ka bani 30minutes zan yi dropping yarinyata, are
you sure sun gama da kitchen D’in?” “Definitely sure.” Aka ce a cikin wayar. Sai ya kashe wayar yana
juyawa don cigaba da driving Amani ta furta “DADA sabon gida kake ginawa? Are we going to live our
House?” Ya d’auke Kai yana ha’de girar sama da k’asa ya furta “Bana son surutu, me yasa ko me ake
kunnenki na kai?” Ta d’an turo bakinta idanunta na kawo ruwa, wani sabon yanayi yana bak’untar ta
kamar yarda ta Saba sometimes idan suna tare da Dadan.” Ta d’an runtse idonta har hawaye na son zubo
mata. Moddi ya d’an zuba mata ido. Ya saki murmushi kawai yana furta “Barbie, open your eyes.” Ta turo
bakinta tana bu’de idonta da suka fara canja launi. “Why are you crying?” Ta yi saurin d’auke kanta rasa
me zata ce masa ta yi. Da kunya ta ce masa ina kuka ne because na rasa yarda zan yi da sha’awarka. Sai ta
kawar da zancen ta hanyar cewa “Am crying, Saboda ka k’i kai ni sabon gida.” Kallonta Ya yi kawai ya saki
murmushi sai taga Ya juya kan motar sun nufi wata ha’daddiyar unguwa da ake kira Rail way a kano. Suna
shiga babban gate D’in gidan Amani ta ware ido ganin kyau da tsarin gidan a cikin motar ta buga tsalle
tana furta “Wow! Dada wannan gidan fa?” Bai amsa mata ba ya fita kawai yana murmushi. Hakan yasa ta
bi bayansa da sauri tana furta “It looks great Dada. Allah yasa namu ne.” Har cikin gidan suka shiga tana
k’auyanci ganin yarda gidan yake d’auke da duk abubuwan da take so. Swimming pool. Ga garden ga
komai ma da yake cikin mafarkin Amani. Irin gidan da ta sha zanawa a takarda tana gayawa Imani duk
wanda zata aura zata gaya masa irin gidan take so. Bata San ta isa wajen Dada ba har ta kama hannunsa
wani irin farin ciki ne Ya saka fuskarta Blushing take tama kasa rufe bakin. A haka suka shiga cikin gidan
hannunta rik’e da na Dada. Suka gama zagaye gidan da yake part Uku Har Da part D’in Didi. A d’ayan part
D’in ne ta kalleshi tana murmushi ta furta “Dada Are you going to get married?” Dada ya waro ido yana
kallonta kafin ya ja bakinta Ya furta “To whom?” Sai ta yi dariya tana shigewa gaba. Zuciyarta na wani irin
bugu. Inama dai Mafarkinta Ya tabbata….. sai dai ta San Har abada shirme ne kawai irin na zuciya. Ta
Yaya Y’a zata auri Ubanta? Ta fita daga gidan haka kawai ta ji k’walla na son zubo mata.




Bai bita ba har sai da Ya gama sallamar masu aiki sannan ya nufi wajen motar. Yarda ta yi zurfi cikin
tunani ya tsaya yana kallonta kafin ya yi tapping hannunsa a fuskarta ta saki ajiyar zuciya tana dawowa
cikin hayyacinta daga can wata duniya da ta fa’da. Ido ya tsura mata yana noticing yanayinta. Sai dai ya yi
shiru Ya tada motar ya juya a hankali yana furta “Bana son surutu, bana son ki gayawa kowa ina gina
gida,I have a planned….” Ta turo bakinta a hankali tana furta “But why?” Bai mata magana ba ya cigaba
da driving d’insa.




“Dahda don Allah ka aureta…” Da sauri ya juyo yana kallonta kafin cikin mamaki ya furta “Ita wa d’in?”
Tana murmushi ta furta “Wacce Didin ta ce…” “So duk abinda ake fa’da kina ji ko? To wallahi idan kika
fa’da Safna ta ji sai na zaneki.” Ta d’an turo bakinta don ta tsani Mommy sosai bata sake magana ba har
suka isa gidan ya sake juyawa yana kallonta ya furta “Kin dai ji me nace ko?” Ta d’aga kai “Kada ma ki ji, ki
yi creating wani scene d’in kiga abinda zan miki fita min a mota….” Ya fa’da yana parking daidai parking
space na cikin gidansa. ta fice da sauri ba tare da ta d’au akwatinta ba… a hankali take kallon y’ar
k’aramar harabar gidansu tana mamakin arzikin Dadan da za’a iya kira na DARE DAYA…. Amma sana’ar
me yake yi da ta bashi ku’di lokaci guda haka? Shine tambayar da ta kanainaye zuciyarta… haka ta shige
gida da burin dole zata tambayi Dadan.
Tana shiga ta tarar da

Mommy zaune a parlorun ita da k’awayenta, ta ji shigowar Amani da sauri ta d’aga kai tana kallonta ta
furta “Kan Uba! Uban waye ya dawo da ke cikin gidan nan?” Amani ta mata wani kallo kamar ta ce
“Ubanki ne sai dai ta gintse ta ce “Ubana, mai gidan shi ya dawo da ni, akwai wani abu ne?” Shiru suka yi
k’awayen Safnan wasu hamshak’an mata suka bu’de baki suna bin bayan Amanin da kallo. “Cab amma
lallai k’awa kin yi sakaci, ji fa idanun yarinyar nan ba kunya take furta mana abinda ta so….” Safna ta yi
k’wafa “Ki bar Ibilishiya amma ba da ita zan yi ba, da shi da ya dawo da ita gidan zan yi… kafin na

Koma kanta, lokaci guda nake jira da zan yi ruining rayuwarta, sai ta gwammace bata zo duniya ba, ku jira
ku ga..” Amani da ta ji komai ta dawo ta tsaya daga gefe ta bi su da kallon d’aya bayan d’aya. Kafin ta saki
dariya ta furta “Before you ruin my life ki jira kwana ka’dan za ki bar gidan nan, don Dada ya kusan yin
aure muguwa kawai……



A firgice suka bita da ido, ita kuwa ta shige bedroom zuciyarta fara k’al. Ko bakomai ta kuntata mata
kamar yarda itama ta mata.




Masifa k’awayen nata suka shiga yi, suna furta Cab amma Safna kin yi sake, ai kuwa in dai kika bari aka
miki kishiya ki tabbatar barin cikin group d’in mu ya zama dole gareki. Kin san taken mu… BA MU BA
KISHIYA….




Shigowar Dahda ce yasa suka yi shiru da zancen illa Mommy da ta zuba masa ido tana masa kallon
tuhuma. Tsare girarsa ya yi sosai yana amsa gaisuwar da k’awar Mommyn take masa kafin ya shige part
d’insa don duk zancen da suke a cikin kunnuwansa, baya son raini amma ya lura Safnan kwana biyu nema
take ta raina shi. Yana jin knocking d’in k’ofarta ya mata banza har ta gaji ta koma d’akinta ranta yana
sake fisga da halin ko in kulan da yake mata…
A bakin gado ta zauna tana kallon Imani da take kallonta duk da fuskarta ta kasa b’oye murnar ganin y’ar
uwarta da ta yi hakan bai sa ta k’i yi yin kicin-kicin da fuska ba ta k’i kallon Amanin. Amanin murmushi ta
saki tana zama daf da ita ha’de da rungumota a jikinta “Kada dai kice fushi kike da ni Adda na.” Ta kirata
da sunan data son Imanin tafi so, don tana mugun son ta bata girma kamar ba tare aka haifesu ba… “Ba
dole na yi fushi ba Amani, gaba d’aya ni ban san wace irin zuciya ce da ke ba? Rashin kunya fa Amani? Yau
rashin kunyar taki har ta kai kan Mahaifin da ya haife mu?” Amanin turo bakinta ta yi ka’dan kafin ta furta
“Shi ya jama kansa, komai matar nan zata yi Dada baya gani wallahi wata rana idan bata yi wasa ba sai na
mata tabo a fuska tabon Da Dadan zai ji ya tsani ko ganinta….” Imani ta saki baki tana kallonta kawai
bata san sanda hawaye ya fara wanke fuskarta ba, Jikin Amani ya yi sanyi ta d’an ware ido tana kallonta
tana furta “To me nayi kuma? Ce miki aka yi yanzun zan mata illa?” Bata fasa hawayen ba kamar yarda
tsoron da take ji bai fasa bayyana akan idanunta ba… “Ba zaki daina irin wannan kalamin ba? Kina
tunanin da Mami tana nan zata ji da’din abinda kike yi? Ya zama dole ki amince da Mahmoud ki yi aure
Wallahi ko wasu halayen naki zaki canja su shima Dada ya huta da saka shi magana da kike.” Amani bata
mata magana ba ta koma gadon ta kwanta idanunta a lumshe wani irin barci take ji sosai don da daddare
ba barcin take samun yi sosai ba idan ba irin wannan lokacin ba saboda tsabar b’acin rai ko abinci bata
nema ba tun wanda ta tsakura da safe. Imani ta bita da addu’ar shirya a ranta kafin ta mayar da kai itama
ta kwanta idanunta akan hoton mahaifiyarsu da ta zuba mata ido kamar ta san a cikin kewar rashinta
take wani abin da tana raye ta tabbata Amanin ba zata yi shi ba.




Sai Yamma can Dada ya fito daga d’akinsa jikinsa sai baza k’amshin turare yake. Idanunsa suka fa’da kan
na Mommy da take zaune ta fece wanka sai zabga k’amshin turare take. Murmushi ta sakar masa tana
furta “Sannu da fitowa Moddi Allah yasa dai ka bar fushin da kake yi a cikin d’aki.” Ya d’an saki ajiyar
zuciya yana zama a can gefe kansa ne yake d’an sara masa. Mommy ta taso gefensa ta zauna tana saka
jikinta ka’dan a nasa ta shafa k’irjinsa ta furta “Moddi ka yi hak’uri please In sha Allah ba zaka sake samun
b’acin rai ta dalilina akan Amani zan rik’eta kamar y’ar cikina….” Ajiyar zuciya ya saki yana jin kaso casa’in
na cikin b’acin ransa yana tafiya ya shafa kanta a hankali ya furta “Promise..” Ta saka hannunta cikin nasa
a kunnensa ta ra’da masa “Yes promised!” Ya lumshe idonsa yana kai mata peck a lab’banta “Allah ya baki
iko…” “Ameen ta furta tana ji a ranta wannan abinda ta yanke a zuciyarta shine abinda ya dace
tuntuni…
Mommy mayaudariyar mace ce data san salo salo da take bi wajen mallakar Moddi, shi kuma a
rayuwarsa baya son hayaniya don haka sam baya son maganar k’ara aure, ya lura kuma shine abinda y’an
uwansa suka fi so a yanzu, sai dai shi da kansa ya san bai isa ba, bai isa ya yi maganar k’ara aure ba, bayan
masifar Mommy shi kansa ya san yana yin kasuwancinsa ba zai bar shi ya ha’da mata biyu ba, bayan haka
ma akwai wani b’oyayyen dalili mai girman gaske da zai hana shi kasa auren……




🧏🏽‍♂️🤗
Hadarin gabas….. Mai hankali ya lek’a yamma yanzu aka fara ku bini a hankali kada mu yi garaje a
cikinsa, abu guda da na sani ba zaku yi Dana sani a cikin bibiyarsa ba.




JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS…

NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️



‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/HBqR4GFrqIMH7TjAy8IYgj



(ku yi joining group. Ba mamaki daga yau iya groups Dina Zan dinga posting.)



𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ ✍️
08033748387.



★★★★★ 7️⃣




Safna sam hankalinta kasa kwanciya ya yi, hakan yasa ta shiga tunanin yarda suka dinga yi dai Malamai
kala kala akan aikin Amanin, kowane Malami gaya mata yake aikin ba zai yiwu ba saboda yarinyar

Please Login or Register in order to submit comment