You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya saka ni ba, amma yanzu
zuciyata tana jin zan iya fin haka ma, zan iya sakawa Moddi ya yi zina da Uwarsa ma ba y’arsa ba. So nake
na samu Makamin da zan hana shi aure. Na shirya wannan karan Lady Boss, kuma Didi ko da bala’i sai na
rabata da D’an nata, sai ta gwammace bata ma haifeshi a duniya ba….” Lady Boss da take jin komai ta
saki dariya ta ce “Yanzu za ki iya kenan da kika ji Uwar bari, dama can ai ke kika saka tausayinsa a ranki da
kishin ba kya son Ya kusanci wata matar. Idan banda haka Uwar me ye a cikin Uba ya yi zina da y’ar sa,
y’ar ma da ba taki ba, y’ar da ba kya so. Ai ko da Uwarsa aka ce ya yi Ban zata za ki yi wannan da’dewar
baki aikata ba. Riba biyu fa kenan ga ku’di ga b’ata masa suna.” Safna ta ja ajiyar zuciya tana furta “Ki jira
nan da kwanaki ka’dan za ki ji dadda’dan labari, zan saka zur’ar Lamid’o a cikin Bak’ar rayuwa, da sai sun
gwammace ba su takale ni da fa’da…” “Bana jin ki, na San za ki iya.” Lady Boss ta fa’da. Safna ta Zare
wayar kafin ta sake mayar da kiran kan Malaminta. Ya tabbatar mata zai yi aikin da take so, zai kuma aiko
mata da kayan aikin ta birne a cikin gidan inda kowa ba zai ganta ba. Amma ta tabbatar a sanda zata yi
aikin kowa na barci cikin tsakiyar dare. Ba shakka ba komai ta ce ta amince…..




Da tafiyar sassarfa Ya koma sashen Didin, inda ya bar y’an uwansa. Yau kam zuciyarsa fresh yake jinta,
cikin tarin soyayya da k’aunar y’an uwansa. Kamar wani labulai ne aka yaye a cikin zuciyarsa ya bu’de
idonsa daga duhun da ya mamaye ganinsa. Ya dinga Jin abubuwan da Ya aikata bai kyauta ba. Jikinsa a
sanyaye ya zauna daf da Didi da Kan Amani yake samanta. Tana sosa mata gashin. Idanun Amanin a
lumshe tana shak’ar k’amshin Dahdan. “Zan yi magana da ku, yaran nan su bani waje.” Moddi ya fa’da
cikin wata irin Husky Voice da take d’auke da karyewar harshe mai da’din sauraro. Duk yaran wajen suka
mik’e, banda Amani da ta yi kamar barci take. Ta gefen ido ya kalleta kafin ya furta “Ke ba zaki tashi ba
ne?” Don ya san sarai ba barci take ba. Idonta ta sake lumshewa sai kuma ta mik’e daga jikin Didin ta tafi
cikin d’akunan da suka kasance nasu. Moddi sai da ya ji rufe k’ofarta sannan ya mayar da kallonsa kan
y’an uwansa. “Da ku zan fara, Don Allah idan da Wanda yake rik’e da ni a ransa ya yi min uziri Ya yafe
min..” Ba Wanda bai zuba masa ido a wajen ba cikin wani irin tsananin farin cikin dawowar d’an uwansu
cikin hayyacinsa. Didi kuwa murmushi take saki hannunta cikin na Moddi da ya damk’e sosai. Tana jin
yarda jikin nasa yake rawa. “Mun yafe maka.” Shine abinda suka dinga fa’da. Sai kuma ya zube a gaban
Didi. Ya kama hannayenta kasa furta komai ya yi sai hawaye da ya fara zuba sharrr daga idonsa. Didi ta
kama shi tana girgiza maka kai. “Ban tab’a rik’e ka da komai ba Moddi, na yafe maka abinda na San ka
aikata da Wanda ban sani ba…” “Na amince Didi zan yi aure, zan auri duk matar da kike son na aura na
amince ko gobe ki d’aura min aure…” zallar farin cikin da zuciyar Didi take ciki ta kasa b’uya a saman
fuskarta kawai sai ta rungume Moddin a jikinta tana furta “Barakallahu fika Moddibo, Allahu Akbar Allah
ka nuna min girmanka, ka nuna min komai yana faruwa ne cikin buwaya da izzarka tabbas kai Alhakimu
ne mai yawan hikima… ka cancanci a kiraka Alwahhabu mai kyauta da k’ari. Almujibu mai amsar addu’ar
bayansa. La Sharika laka, Allah ka cigaba da kare min zuri’ata. Ba ni da boka bani da Malam.” “Ameen”
suka amsa gaba d’aya Umma dee ce kawai bata wajen.

Moddibo ya d’an saki murmushi kawai kafin ya mik’e ya bar parlorn. Shikkenan hirar ta koma kan kalar
matar da ya kamata su samowa Moddibo kowa ya dinga fa’dar albarkacin bakinsa. Na irin matar da ta
dace da Moddin.
★★★★




Driving d’in take idanunta sanye da black shade da ya yi masifar yi mata kyau, ya kuma sake bayyana
gayunta. Chewingum take ci. Fuskarta cike take da damuwa. Ta samu gefen Titi ta yi parking hannunta ta
saka ta Zare shades D’in da ya saka ba’a ganin jan idanunta suka yi. Muryarta a dashe ta ce “Alwan ka
kasa cika min buri na, me yasa? Da Kai na yarda duk wani hope d’ina yana wajenka. Ka San dai rashin
cikar burina yana nufin komai ko?” Alwan ya saki ajiyar zuciya ransa a b’ace ya fara furzar da huci shi
kansa zuciyarsa bata masa da’di Akan hakan, amma ya zai yi? Duk ta inda ya b’illowa Imaam sai ya
waske…. “Ko wata dabarar zamu canja?” Ta fa’da idanunta suna lumshewa. Sai kuma ta bi Alwan da kallo
cikin karyayyan harshenta da bai gama k’warewa da Hausa ba ta furta “Ina Jinka? Ya kake ganin zamu
b’illowa lamarin?” Alwan ya saki murmushi bayan ya lumshe idonsa sai kuma ya ware da sauri ya furta
“Done! Wannan karan na samu mafita na San ba zai tsallake wannan tarkon da zan d’ana masa ba.” Shiru
ta yi tana binsa da kallo kafin ta cije leb’e ta furta “Kai ne Last Hope d’ina, bana son loosing dukkan
opportunity d’ina a wannan karan.” Daga haka ta ja motar a fusace ta hau Titi tana furta “Ina son barin
Nigeria in the next Five months, kafin nan ina son na tabbatar da cikinta a jikinsa, idan ta Kama zan iya
tafiya da ita can don ta haihu…” Alwan ya gya’da kansa “In sha Allah hakan zata faru…” “Rabbi Ya sha’a
ta furta tana sake danna motar da gudu, don da haka ta k’ure da tuk’inta…




★★
Cikin daren da ya yi tsit ya kuma nuna alamun dare ne sosai. Kamar an tashi Amani haka ta farka tana
kallon windown da yake cikin sabon d’akin nasu. Gefenta Imaan ce da ta kasa yarda su raba d’aki… zafin
da take ji a zuciyarta na yanayin da take cike ne yasa ta mik’e don isa kitchen ta samu ruwa ta sha. A part
d’in su Dahda suka kwana cikin d’akunansu na sashen don b’angaren Didi cike yake taf da y’an uwanta da
suka zo yi mata murna. Shiru parlorn baka Jin k’arar komai sai na A.c. Ta dinga Jin wani tsoro yana
shigarta Amma yarda take Jin k’ishi yasa ta k’i yarda ta koma ba tare da ta sha ruwan ba. Ruwan ta sha
sosai kafin ta zauna a parlorn idanunta a lumshe. A hankali ta bu’de idonta Jin motsin da take ji yana sake
yawaita. Ta kai dubanta zuwa wani walk way, inda ta nan ne za ka shiga b’angaren Dahda. Duk da tana Jin
tsoro sai ta ji tana son sanin menene ake yi a wajen. Ta mik’e don isa k’ofar da da rana suka shiga suka
tarar da wani garden mai kyawun gaske. Labulan windown ta ‘daga kafin ta Ware ido tana kallon abinda
ya kusa dugunzuma kwanyarta. Da sauri ta waro ido. Sai kuma ta yi saurin toshe bakinta tana son sani me
Safnan take a wannan tsohon Daren. A tsaye take zigidir hannunta rik’e da wani kasko da wuta a ciki tana
zagaye wani waje da ta tabbatar rami ne… jikinta har rawa yake Amma hakan bai saka ta bayyana kanta
ba. Ta toshe bakinta tana sake jaddada rashin Imani irin na Safna idan har ba idanunta ba ne ya gane
mata ba daidai ba wannan abinda take Kai tsaye za’a kira shi tsafi… Tana kallonta har ta gama ta mayar
da k’asar ta rufe… A fili da kuma d’an k’arfi ta ji tana furta “Imamu na rabaka da Uwarka har abada! Na
rabaka da aure har abada!! Na rabaka da y’ay’anka da matarka har abada. Ni ka’dai zan yi rayuwa da
Kai….” Sai kuma ta saki wata dariya. Kafin ta mayar da kayan jikinta. Amani ta runtse idonta tana sake Jin
haushin kanta da bata fito da wayar ta ba. Da tabbas sai ta yi vedio D’in komai ta nunawa kowa don
hakan ya zama tsanin da zata raba Safna da Dahda har abada… tana kallo ta mayar da kayanta jikinta
sannan ta kashe wutar kaskon ta nufi k’ofar da zata mayar da ita cikin gida. Da sauri Amani ta sake
takurewa waje d’aya don bata son Safna ta ganta. Lamarin matar yanzu tsoro yake bata. Tana kallo ta
shigo har ta shiga cikin d’akinta ta kullo k’ofa. Zubewa Amani ta yi a wajen hannunta dafe da k’irjinta. Ta
kasa aikata komai sai zufa da take zubo mata. Sai da ta samu nutsuwa sosai sannan zuciyarta ta tunatar
da ita … “Idan baki cire abin nan ba komai zai iya faruwa, zata samu nasara a kanku ki je ki cire Amani ki
lallata sihirinta, ki cire duk wani tsoro da fargaba da take ranki…” Cikin k’warin gwiwa ta fice daga wajen.
Ta isa wajen duk wani tsoro da take ji ta ji ta nemeshi ta rasa. Daidai wajen ta hak’a ta Ciro abinda yake
ciki wasu irin tarkacen abubuwa ta gani, ga wani irin Abu mai warin gaske. Ta toshe hancinta ganin har da
jini yana d’iga a jikin abin. Da sauri ta tsuguna a kai ta yi fitsari don ta karanta a wani littafi hakan yana
karya ko wani irin sihiri. Gigicewar da ta yi da warin da take ji na abin yasa ta manta bata mayar da Ramin
ta rufe ba, ba kuma ta lura da mayafinta da zoben ta Sun fa’di a wajen ba. A Gigice ta shige cikin gidan.
Abinka da sabon wuri sai bata lura da inda take saka k’afarta ba, bata San d’akin da ta shiga ba ita dai taga
d’aki a bu’de ta danna kai ciki. A razane ta dinga kallon Dahdah da abinda yake yi a cikin d’akin da sauri ta
bu’de baki zata saki ihu da saurin gaske Dahdah ya toshe mata bakinta cikin tashin hankali a tsawace ya
ce “Waye ya ce ki shigo d’akin da na jaddada muku kada koda wasa ku shigo shi? Yanzu kin shigo ko kin
ga abinda bana son ku shigo ku gani, kin ji da’di? Na ce kin ji da’di yau kin gane min sirrin da na yi shekara
da shekaru ina b’oye shi?” Ina Amani ma bata San yana yi ba don tuni ta sume a jikinsa….. shi D’in ma
yarda yake Jin Kansa kamar ya suman, dama zai Mutu da shi da ita duk su bar duniya su huta…..
To fa! Me Amani ta gani ne da ya fitgitata har ta suma?




JIKAR NASHE★ ✍️HADARIN GABAS…….
27.




NAZEEFAH SABO NASHE★ ✍️

08033748387.



Bright pens second batch….



★★★★



Jikinsa har rawa yake, cikin tashin hankali ya dinga jijjigata yana kiran sunanta. Ganin dai da gaske ta
suma ne yasa ya d’aga ta cak ya shiga da ita ta wata k’ofa da zata sadaka da wani babban bedroom d’insa.
A gyare d’akin yake tsaf sai zabga k’amshi yake ya kuma sha kayan more rayuwa masu masifar kyau. A
hankali ya shinfi’deta a saman gadon kafin ya cigaba da jijjigata cikin tashin hankali yana kiran sunanta.
Bata koma motsa ba. Da sauri ya shiga toilet ya ‘Debo ruwa ya watsa mata. Ta farka idanunsa cikin nasa.
Kamar majigi abubuwan suka shiga dawo mata a kai. Kamar yanzu suka faru kamar kuma irin mafarkin da
ta saba. Ba mafarki ba ne! Haka wata tsawatacciyar zuciyar ta ta tunatar da ita. Dahdahnki Amani,
Dahdahnki ne yake amfani da mutum mutuminki yana wasu abubuwa da ta tabbatar having sex yake da
ita. Da mutum mutumin yake saduwa. Ta runtse idonta tana jin wani irin k’una a ranta. Da gaske wannan
ne dalilin da yasa kullum take jin sha’war Dada da k’aunarsa a ranta…. Wasu kalar hawaye masu zafi suka
shiga zubo mata. Idanunta cike da hawayen ta sake zubesu cikin na Dahda. Da shima yake kallonta
fuskarsa cike da tausayinta ko ya ce tausayin kansu duk su biyun. Hannu ya

Saka zai kama hannun nata Amma cikin zafin nama ta janye hannunta da sauri tana jifarsa da wani irin
kallo mai bayyana tsana murararan… da gaske ta tsani Dahdah a wannan daren ta tsanin kallonsa as
mahaifinta. Bata kuma k’i Allah ya ‘d’au ranta ba da wannan tashin hankalin da take ciki. Sai yau ta
tabbatar da Dahdah matsa fi ne! Matarsa Matsafiya ce!! A gidan matsafa suke zaune, matsafa ne suka
rainesu suka ciyar da su da abincin haram… “Aman… ki tsaya….” Dahda ya furta cikin rarrabewar
murya. Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar toshe kunnenta da wani irin k’arfin murya mai bayyana tashin
hankalinta ta furta “Bana son ji! Bana son jin komai Dada. Na tsaneka na tsani dukkan abinda za ka ce,
idona ya bayyana min gaskiya yau. Ashe tsaface ni ka yi, ka cika zuciyata da tarin k’aunarka, ashe tsaface
ni ka yi kake biyan buk’atarka da ni shi yasa duk duniya nake jin sha’awarka abinda sam yake haram ne
gare ni, na tsaneka kuma zan bi duniya a yau na tsani in kalleka a matsayin mahaifina Mugu kawai!” Ta
furta tana sake sakin wani irin kuka mai k’arfin gaske. Dahda runtse idonsa kawai ya yi yana fisgar lips
d’insa da suka sake wani irin ja, idanunsa suka dinga k’ank’ancewa… Har suka lumshe don kansu. Yana jin
Amani ta sauka daga gadon cikin wata irin tafiya mai bayyana galabaita da raunin da zuciyarta da gangar
jikinta take ciki ta fice daga d’akin. A diririce take neman k’ofar da zata fitar da ita waje. Idonta ya sauka a
kan Babyn robar da tsayin da komai kama suke da ita ba ta yarda za’a yi idan ka ga y’ar tsanar nan ka ce
ba Amani ba ce, don kamar ita ce a tsaye. Hawaye ya dinga zuba mata. Tana sake kallon y’ar tsanar da
take kwance ba kaya a jikinta yarda ka san itace don suffa da komai irin ta mutum ce hatta yanayin
fatarsu… kuma jikin da laushi ba kamar y’ar tsana ba… ta runtse idonta. Tana jin zafin da zuciyarta take
yi yana sake hauhawa. Har ta na bugewa garin fita tsabar yarda idonta suka rufe bata cikin hayyacinta.
Dahda da yake tsaye yana kallonta ya cije bakinsa wata irin fisga zuciyarsa take yi, fusgar da ya tabbatar
da za’a auna jininsa a yanzu za’a tabbatar ya hau kuma zuciayrsa ya san k’iris take da ta samu attack. Ya
zube a saman kujerar cikin takaicin kansa da dana sani fal da ya cika zuciyarsa. Tsoronsa guda kada Amani
ta bayyana wani sirrin nasa. Da wani ido zai yiwa mutane bayani har su fahimce shi. Fusgar gashin kansa
yake kawai yana datse lips d’insa kamar sune suka masa laifin…




K’afarta rawa kawai take sanda ta isa d’akinsu. Ta zube saman gadon tana sake sakin kuka sosai idonta
cikin hoton mahaifiyarsu da take ta zabga murmushi. Cikin wata irin murya Amani ta furta “Ina son na
biki Ina son na Mutu, na gaji da halin da nake ciki zuciyata ciwo take Maahmeey. Wayyo Allah!” Ta fa’da
tana sakin nishi ha’de da dafe zuciyar… wannan ne ya farkar da Imani ta farka a razane ganin kamar
Amanin bata cikin hayyacinta. Da sauri ta kama hannayenta tana furta “Gaya min Amani menene?” Bata
mata magana ba illa fa’dawa da ta yi jikinta tana sake sakin kuka furucin Ina so na Mutu shine kawai a
bakinta. “Mutuwa nake so Imaan, na gaji da gidan nan. Na gaji da halayya da ‘dabi’a irin ta mutanen
cikinsa, a wannan daren na tsani Dahda na kuma tsani na cigaba da kallonsa a matsayin mahaifina,
Moddi da Safna matsafa ne, wallahi Imani a gidan Matsafa muke rayuwa….” Sai kuma ta rungumeta
jikinta na cigaba da kakkarwa tana sake kallon abinda ta gani cikin duhun idonta… da k’arfin ta sake furta
“Matsafa ne, mu gudu mu bar gidannan Imani kafin su shanye jininmu…” Imani ta shiga wani irin shock
tun kafin Amanin ta bata labarin abinda ya faru, ta san koma menene tashin hankalinsa ya kai inda ya kai.
A idon Amanin take hango rashin nutsuwa, so take ta ji koma me ye don haka da wani irin hanzari ta
shiga jijjiga ta tana furta “Tashi ki gaya min, kin bawa Dahda kan ki ne? Ya kusance ki ne?” Amani ta
lumshe ido tana d’aga kai ta furta “Ya kusance ni, kuma ba tun yau yake kusantata ba wallahi….” Wani
irin Zare ido Imaan ta yi, tana jin yarda zuciyarta ta wani irin bugawa ga wani nauyi da ta mata. Bata San
sanda ta yi baya ba tsabar jirin da take ji, duk da a zaune take. Da k’yar bakinta Ya furta “Innalillahi wa
inna ilaihirrajiuna! Amma baki tab’a gaya min ba, Amani, me yasa? Me yasa kika b’oye min?” Amani ta
runtse idonta tana fusgar leb’enta ta furta “Nima ban sani ba sai yau, sai yau na San dukkan wannan halin
da na shiga Dada ne sila, amfani yake da mutum mutumina yana having sex da ita, wallahi tana nan a
d’akin sirrin sa, irin d’akin da ya hana mu shiga a gidansa, yau k’addara tasa na shiga ashe Allah yaso Ya
bayyana min gaskiya ne, yaso ya nuna min wanene Dahda…” ta runtse idonta kafin ta furta “Sai na gansu
da ita, yana sex da ita, wallahi Iman kamar ni a zaune haka Toy D’in take…” Imaan ta runtse ido kafin ta
mik’e a fusace ta yi hanyar waje tana fincikar hannun Amanin “Mu je, zo mu je mu gani. Wallahi idan
haka ya tabbata da kaina zan tonawa Dada asiri, sai na gayawa Duniya waye shi?” Amani bata ji wani
shakka ba tabi bayanta. Suka fita zuwa parlorn. Sai dai ba alamar k’ofar zata tab’a bu’duwa haka suka
dinga buga k’ofar Amma shiru. Jikinsu a sanyaye suka koma d’akin su. Idonsa fal hawaye…




Juye-juye kawai yake a gadon. Yana jin yarda zuciyarsa take wani irin zafi… a hankali ya dinga Jin bugunsu
ya tabbatar su ne, amma ba zai iya bu’dewa ba. Yana jin kunya tabbas yana jin kunyar ya kalle su don ba
zai iya yi musu bayani ba. To ya ce musu me? Ya runtse idonsa kawai kafin ya mik’e hannayensa a aljihu
ya fita daga bedroom D’in. Tafiyar yake kamar Wanda ba damuwa a ransa da k’arfinsa ya isa bedroom
D’in nasu. Ya ci sa’a ya samu k’ofar a bu’de. Idonsu suka sauke a kansa suna masa kallon tuhuma, kallon
da yake bayyana tarin tsanarsu gare shi. Hannayensa a aljihu ya isa wajensu. K’ok’ari yake sosai wajen son
sarrafa zuciyarsa sai dai bashi da makamin da zai kare kansa. Don haka ya lumshe idonsa kawai. A karo na
farko a gaban yaransa hawayensa ya d’iga. Hawayen da yake bayyana ragwantakarsa a yau, duk da
kasancewarsa jarimi mai k’ok’arin b’oye damuwarsa Amma yau kam ya kasa, ya bayyana rauninsa a gaban
yaransa. Jikinsu ya yi sanyi, zafinsa da suke ji ya fara narke wa zuwa tausayi, tausayin da basu San
dalilinsa ba, basu San me yasa ba? Musamman Imani da ta dinga jin kamar taje ta rarrashe shi. Ya da’de a
haka yana hawayen suma suna nasu. Duk zafin da zuciyar Amani take yi sai ta neme shi ta rasa. Tsanarsa
da take ji ta gudu, wata irin tarin k’aunarsa ta sake ji a ranta soyayya mai zafin gaske da take jin zata iya
aikata komai saboda taga ta kawar masa da damuwa. Ta dinga binsa da kallo tana lumshe idonta jin
husky voice d’insa yana furta “Am sorry Ama…. It wasn’t my fault, zuciyata ce In sha Allah komai zai
zama labari duk da na San Nine silar afkuwar halin da nake ciki, Soon zan maku bayani Amma kafin nan
please keep this a secret….” Daga haka ya lumshe idonsa sai kuma ya fara tafiya da baya da baya. Amani
ta dinga kallonsa tana jin kamar ta tashi ta rungumoshi ta lallashe shi. Tana kallo ya fice ya bar musu
k’amshin sa a cikin d’akin. Sai kawai ta rungume pillow tana sake sakin kuka. A sannan take jin zuciyarta
bata mata adalci ba… Imani bata lallasheta ba don itama kukan take kanta a saman bayan Amani ta furta
“Sister, mu rufawa Dada asiri, a idonsa na hango ba laifinsa ba ne, da gaske yake ba laifinsa bane, ban san
wace kalar k’addara ba ce take bibiyar rayuwarku daga ke Har shi…” Bata mata magana ba, don ita
abinda ya dameta ya dameta, bakomai ba ne sai wani irin k’aunar Dahda soyayyarsa da k’iyayyar sa da
suka caku’de mata a zuciya ta rasa a wani muhalli zata ajiye Dahda masoyi ko mak’iyi, ko kuma Mahaifi?
A daren ranar kam basu yi barci ba, sun tashi sun yi Sallah kowannensu Ya dinga gayawa Allah
damuwarsa da son ya magance masa ita. Sai sannan suka ji sanyi, suka kuma samu sauk’in abinda suke ji
a zuciyarsu, bayan Asuba barci ya d’auke su.




Shirun da Didi ta ji basu fito ba, yasa ta gaji da jira ta kalli Fateemah ta ce taje ta taso su. Time D’in k’arfe
10:00 na safe. Da k’yar Amani ta bu’de nauyayyen idanunta da suka kumbura fiye da na Imani, ta zube su
a cikin na Umma Teey da take kallonsu cikin matuk’ar fa’duwar gaba. A kasalance ta ce “Me ya same ku?
Me ye haka? Me ya faru?” Lumshe ido Amani ta yi tana kokawa da hawayen da ya kasa tsayawa daga
idonta. Hakan yasa fargabar Umma teey ta sake yawaita ta zauna gabanta na fa’duwa sai dudduba jikinsu
take. “Ku gaya min mana.” Imani ce ta sauke ajiyar zuciya kafin ta kama hannun Umma Teey D’in. Tana
sakin ajiyar zuciya da k’ok’arin kawar da damuwarta ta furta “Bakomai fa, waccan matsalar ce dai ta
Amani har yau bata daina ba.” Umma Teey tausayin yaran ya sake kamata sai kawai ta jijjiga kai tana furta
“Soon, zata daina In sha Allah, ina nan ina addu’a, lamarin ne akwai sark’ak’iya. Ina so dai ku cigaba da
rufawa mahaifinku asiri Har muga abinda hali zai yi, kun ji?” D’aga kansu suka yi. Suna furzar da huci
kusan a tare. Umma T,ta ce ku tashi maza ku shirya Didi na can hankalinta yana nan, duk ta damu, kuma
daga yau ina son ku koma sashenta da kwana gwara kuna kusa da ita, Ya fi wannan zaman naku anan da
hankalina sam bai kwanta da shi ba.” Basu musa mata ba, suka yarda da abinda ta ce, don kam zamansu
anan su da kansu sun san bai kamace su ba.




****

A daidai lokacin Safna na tsaye gaban Ramin data aikata komai, cikin tashin hankali take bin Ramin da
kallo tana cije yatsa. “Kan Uba!” Ta furta tana kallon yarda aka tone komai. Tashin hankalinta yana
hauhawa bata manta garga’din bak’in bokan ba, “Kada ki bari kowa ya san kin birne abin nan, idan har
wani ya gani tabbas kina cikin matsala. Zufa ta dinga zubo mata, ganin ko alamar kayan sihiran nata,
“Akwai Matsala Safna, duk wani sihirinki ya warware asirinki Ya kusa tonuwa!” Ta dinga jin muryar bokan
a kunnenta… jikinta na rawa ta zube a wajen. Zuwa ta yi dama a lokacin ta zuba rubutun da ya sanar
mata idan safiya ta yi taje ta zuba a kai. Sai dai taga wannan tashin hankalin. An tone Ramin an kuma
kwashe tarkacen Sihirin. Zafi zuciyarta take yi irin zafin da take jin da zata ga Wanda ya mata hakan, sai ta
kashe shi Har lahira… Idonta ne ya sauka akan hular Amani da zobenta… da sauri ta saka hannu ta
‘dauke su cikin zafin nama kamar wacce ake wa Gangi ta juya a zafafe ta nufi cikin gidan. Kai tsaye
d’akinsu Amani ta nufa ta tura k’ofar da dukkan k’arfinta. Idonta ya sauka a kansu suna yafa mayafi da
alama Sun shirya zasu fita daga d’akin. Ta watsa musu kayan a gabansu tana furta “Na Uban waye a cikin
ku?” Imani da sauri ta kalli Amani don ta San nata ne, hularta ce ta jiya data kwanta barci da ita… ta
waro ido ganin Amanin ta mik’e cikin taku mai nuna isa da rashin kunya zalla ta isa gaban Safnan tana
mata wani irin fisgaggen kallo, mai bayyana wulak’ancinta zalla… a gabanta ta tsaya tana sakin wani
murmushi ta nuna kanta tana furta “Na Amani Imaam Moddibo ne….” Safna ta k’ank’ance idonta cikin
na Amani, tsanar yarinyar na sake girmama cikin zuciyatta ta dinga jin tamkar ta shak’ota ta mutu, amma
idanun yarinyar a yau Sun razanata Sun kuma firgita ta. A idanun Amanin ta dinga hango rashin kunya
zalla da wani irin kwarjini da ba shakka idan ta cigaba da tata masifar Amanin zata iya tona mata asiri.
Zata iya fallasa sirrinta ta sanar da zuri’ar Lami’do wacece ita? Sai kawai ta cije baki, k’walla tana shirin
zubo mata. Ba k’wallar komai ba ce sai ta rashin sanin madafa, da rashin sanin abinda zata aikata… cikin
k’unar zuciya ta furta “Kin cuce ni Amani, kuma wallahi ba zan barki ba sai kin biya abinda kika aikata
min, sai na saka ki

Please Login or Register in order to submit comment